Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

san nagane ba"

Dariya fu.ad yayi.

"I love you......"

Da sauri ya ware idanuwanshi akanta. Yana jin yanda zuciyarshi ke ta tsalle tsalle cikin kirjinshi. Baisan wanne abin arziqi ya aikata ba a rayuwarshi daya cancan ci wannan kalaman da Nana ta fada mishi.

Wasu irin akwatina ya bude ya rufe su ciki dan bazai so ya batar dasu ba. Kallon shi nana tayi ta ci gaba da fadin.

"Ina kaunarka kaman yanda nake kaunar mumy tun kamun in sanka"

Sake sumbatar ta yai a goshi yana riko hannunta. Baisan kalaman da zai amfani dasu ba dan ya gaya mata kalar yanda yake jin kaunarta daga randa ya dora idanuwanshi a kanta.

Hannun ya kamo ya dora kan kirjinshi. Wasu emotions ne yake ji ta ko ina suna danne shi. Muryarshi nadan rawa yace.

"Kaunar da nake miki ta girmi abinda kenan ciki"

Dariyar nan dayake jin sautinta yafi na komai daya taba ji cikin kunnuwanshi tayi. Kasa tai da murya tace.

"Ta fi ta mumy?"

Ware idanuwanshi fu.ad yadan sake yi akanta. Itama nata a ware suke cikin nashi kamun su bushe da dariya a tare.

Haka safiyya ta turo kofar ta same su. Tun daga bakin kofar take jin sautin dariyarsu. Suna kallonta suka sake wata sabuwar dariyar.

Da mamaki take kallon su. Girgiza kai kawai tayi ta karasa gefe ta ajiye kayayyakin dake hannunta.

"Nana tashi muje in miki wanka"

Daquna fuska tayi. Tana turo baki.

"Na iya fa"

Kallonta safiyya take.

"Muje in tayaki to"

Daka kallo fuskarta kasan bata so. Kawai dai ta sakko ne daga kan gadon. Saida ta sumbaci fu.ad a kumatu sannan.

Kallon shi tayi sosai.

"Kaje gidansu please. Nima zan mishi addu.a"

Kai fu.ad ya daga mata hadi da fadin.

"I promise"

"Thank you"

Ta fadi. Tana wucewa toilet din.

*

Ita kanta safiyya tunda taga doc jana tazo ta dudduba Nana bata ce musu komai ba ta bita taji maganar result din tace mata sai karfe hudu haka ta dawo ta zauna gabanta na wata irin faduwa.

A haka fu.ad ya fita yai sallar azahar ya karbi key din motarta ya fita ya siyo musu take away da lemuka ya dawo.

Amman daga shi har safiyya sun dan taba ne kawai saboda Nana ta musu magana. Bawai dan suna jin dadin abincin ba.

"Mumy baki kiramun su ba fa har yanzun?"

Sauke numfashi safiyya tayi. Ta dauko wayarta da jakarta. Lalubo dan katin da yusra fari ta bata tayi. Ta duba number dinta a jiki.

Text tai mata sannan ta dago ta kalli nana.

"Na masu magana yanzun"

Daga nan kan gadon inda take tai kissing tafin hannunta ta hura ma safiyya hadi da fadin.

"You are the best mum ever"

Dariya tadanyi. Fu.ad dake gefe ya tabare fuska.

"Princess mumynki kawai kika sani ko?"

Dariya Nana tayi. Ya sa hannu ya dan taba kuncin shi. Babu musu ta matsa kan gadon ta sumbaci kuncin shi. Yace.

"Ko kefa"

Wayarshi dake gefe ta dauka. Bai hanata ba. Ta mika mishi saboda akwai key a jiki. Kallonta yai yadan kalli safiyya sannan ya ware mata idanuwa.

Hannu tasa ta rufe bakinta tana danne dariyar da take ji. Sannan ta saka 'Safiyya' a jikin wayar sai dai ga mamakinta wrong password.

Kallon fu.ad tayi ta daquna fuska alamar baiba. Yadan daga mata kafada yana murmushi dake nuna ta sake guessing dai.

Dan daga idanuwa tayi tana tunani. Can tace.

"Yes......"

A fili. Dariya yai. Safiyya ta kalle su. Su biyun nan bata gane yanda suke magana. Saidai ko taji sunyi dariya.

'Sofi' ta rubuta sannan tai masa πŸ‘Œ sign da hannu alamar ya bude. Images takai. Hotunan ta ta fara gani duk tana bacci.

Ta dago ta kalle shi. Bai ce mata komai ba ta ci gaba da swiping gaba tana kallon hotunan dake ciki. Yawanci duk shida abokanshi ne da kayan ball.

Gaba daya hotunan babu wanda yai fara.a a cikinsu. Fita tai ta shiga wata folder din daban amman key ne a jiki. Sake kallon fu.ad tai da tambaya a cikin idanuwanta.

Ta juya mishi wayar yaga folder din. Wani numfashi yaja sannan yadan yi gefe da kanshi cewar ta sake saka sunan dazun.

Ware mishi idanuwa tai yasan so take ta fadi kalar son da yake ma sofi. Ya girgiza mata kai yana dakuna fuska.

Dariya ta kamayi ta bude folder din. Hotunan sune shida safiyya a ciki lodi guda. Tasa hannu ta shafi screen din tana kallon yanda suke dariya a tare.

Haka taci gaba da wucewa sa duk hoton da zata gani da qarin karfin alkawarin da take daukarwa kanta na saita zama silar komawarsu koda shine karshen abinda zatayi.

Saida ta kai karshe sannan ta koma ta bude video record ta soma daukar fu.ad dake zaune yana kallonta.

"Me kike?"

Ya tambaya. Dariya ta kamayi. Ta juya wayar saitin safiyya data ce mata.

"Nana ki bari fa"

Sauke wayar tayi tai saving video din. Mikewa fu.ad yayi yana miqa da jikinshi yace ma nana.

"Karfe nawa"

Duba wayar tayi.

"Karfe uku da minti arba.in"

Da sauri ya fita baima san lokaci yaja ba haka.

*

Yana dawowa daga masallaci yana hango motar lukman. Dan haka suna gaisawa suka shiga ciki tare.

Da fara.a Nana tace.

"Uncle lukman...."

Gefen gadon ya zauna ya shafa kanta. Sai da suka gaisa da safiyya sannan ya maida hankalinshi kan Nana da fadin.

"Ya jikinki"

Dan daga mishi kafa tayi dayaga ta masa yanayi sosai da fu.ad. Bata san ana ce mata ya jiki saboda bata son ganin yanda idanuwan mutane ke canzawa in zasu mata tambayar.

"Ina uncle haneef?"

Lukman ya amsa da.

"Nasan zai zo"

Yana rufe baki suna jin turo kofa da sallama. Mikewa lukman yai yana fadin.

"Momma sannu da zuwa"

Su dukansu gaishe da ita sukai. Fu.ad ya janyo mata kujera ta zauna suna hira da Nana.

Doc jana ta shigo suka gaggaisa ta sake duba Nana tace ma safiyya.

"Zaku iya tafiya gida ma. Inda wata matsala dai ku dawo"

"In shaa Allah. Mungode sosai"

Yar ledar data shigo da ita ta mika ma nana da ta karba tai hugging dinta hadi da fadin.

"Thank you anty jana"

Da murmushi ta amsa da.

"Don't mention sweetheart."

Hankalinta ta mayar kan safiyya tace.

"Zan ganku yanzun kamun ku tafi"

Wani irin dokawa fu.ad yaji zuciyarshi tayi kaman zata fito daga kirjinshi. Binta safiyya tayi. Fu.ad ya kalli lukman sannan ya fita shima.

Juyowa safiyya tai idanuwanta cike taf da hawaye ta hade hannayenta duka biyun cikin sigar roqo. Muryarta a sauke tace.

"Ina bukatar yin wannan nikadai. Please......"

Saida yaja numfashi ya fitar dashi sannan yace.

"Ki daina irin wannan maganar sofi. Bana so wallahi"

Kai ta daga mishi.

"Na daina. Ba zaka gane ba. Ina son fara ganin result din ni kadai....."

Juyawa tai tana goge hawayen da suka zubo mata. Binta zaiyi yaji an rike mishi hannu.

Juyawa yai lukman ya sake shi yana fadin.

"Ka kyaleta. A karo na farko a rayuwarka kaji rokon da akai maka mana"

Jingina fu.ad yai da bangon wajen baice komai ba. Yaga yarshi ce yana da right din dazaiga result din baisan me yasa safiyya zata dage ita kadai zata gani ba.

*

Sanda ta shiga office din doc jana na zaune da takardun a babban envelop. Waje ta samu ta zauna jikinta babu karfi ko kadan.

Ita kanta bata bude result din ba tunda ta karbo shi daga lab. Dan har ranta tana kaunar Nana. A shekarun nan biyu yarinyar ta wani shiga ranta.

Gabanta na faduwa ta bude envelop din ta zaro takardun da na Nana dana fu.ad din. Kallonta safiyya take idanuwanta cike da buri.

Runtsa idanuwa doc jana tayi. Lokaci daya wata irin zufa ta karyo mata. Kallon safiyya tayi.

Da kallo dayan datai mata komai ya tarwatse. Da wannan kallon taji dalilin rayuwarta ya kare. Da wannan kallon datai mata taji ta karasa rasa komai na duniya.

Cikin wata irin murya da bata gane tata bace tace.

"Wata nawa nake da?"

Bude baki doc jana tayi safiyya ta daga mata hannu hadi da sake maimaita tambayarta.

Sauke numfashi doc jana tayi tana jin idanuwanta na cika da hawaye.

"Da yanayin yanda komai ke spreading kasa da wata hudu"

Mikewa safiyya tayi. Tana jin yanda kafafuwanta ke takawa sai dai komai take ji kaman ba nata bane ba. A haka ta fice daga office din bata ko kula da cewar bata ja mata kofar ba.

*

Tsaye suke nesa da office din kadan shida lukman yana jin yanda yake fada mishi komai zaiyi dai dai in shaa Allah.

Baice uffan ba. Shi kadai yasan halin da zuciyarshi take ciki. Ganin safiyya ta fito ya sa daga shi har lukman suka karasa inda take.

"Sofi......."

Juyowa tai ta kalle shi kamun ta ci gaba da tafiya. Zuciyarshi yaji ta ci gaba da dokawa. Ita kanta bata san inda zata ba.

Wani waje take son zuwa inda ba kowa. Inda babu wanda ke ciki sai ita da halin da take ji. Da sauri fu.ad ya bita.

Tare hanyar yayi. Yana mata wani kallo cike da bincike. Idanuwanta ta dago ta sauke cikin nashi tana son yaga yanda zuciyarta ke ciwo.

Girgiza mata kai yake yi.

"No sofi. Dan Allah karki fadamun. Please na roqe ki banda sauran zuciyar da zata dauki wani rashin"

Kafafuwanta taji sun kasa daukarta. Durqushewa tai a wajen tasa fuskarta cikin hannunta tana sakin wani irin kuka marar sauti.

Matsawa yake da baya. Ya kasa gane meke shirin faruwa dashi. Babu abinda yake gani cikin idanuwanshi yana gilma mishi banda fuskar Nana.

Lukman ya dafashi a tsorace yace.

"Fu.ad ya akai?"

Ture hannunshi yai yana ci gaba da ja da baya a hankali kamun ya juya da gudu ya nufi hanyar office din doc jana bai damu da yanda lukman ke kwalla mishi kira ba.

Tura kofar taji bana wasa bane. Da sauri ta dago kai ta sauke idanuwanta kan fuskar fu.ad.

"Yes ko No?"

Ji take da da yanda zatayi da tayi. Sai dai babu. Ko da anyi transplant dinma ba wai warkewa zatai ba. Lokaci ne ake sa ran zata kara samu.

Muryarta can kasa tace mishi.

"No"

Lumshe idanuwanshi yai. Yana jin yanda zuciyarshi ke rugujewa kala daban dana lokacin barin shi nigeria.

Juyawa yai hannuwanshi cikin aljihun wandon shi. Yana jin yanda girman kalmar da jana ta fada ke samun waje cikin jikinshi.

A hankali komai ke tafiya kamun yakai inda zai zauna daram. Iskar asibitin ta mishi kadan. Lukman yaga yasha gabanshi.

"Fu.ad..... "

Kallon lukman yai. Kallon shi yake da roqo cike da idanuwanshi kaman hakan zai sa lukman ya taimaka ya karbi kadan daga cikin nauyin da zuciyarshi tai mishi.

"Fu.ad kaimun magana please. Safiyya ma taki cemun komai. Wai menene?"

Yana jin yanda iskar tai mishi kadan. Dan numfashin shi harya soma samun matsala. Yana fitar dashi da sauri sauri yace.

"Lukman my little girl. Yarinyata...... Yarinyata lukman....."

Yanda yake watsa hannaye yana jan numfashi yasa lukman kama shi yaja shi gefe yana jingina shi da bangon wajen.

"Calm down. Me yake faruwa?"

Numfashin shi yaqi kaiwa inda yakamata har yanzun. Yana jin yanda komai yake amsa wa cikin kanshi.

"Mutuwa zatayi lukman......."

Ware idanuwa lukman yayi yana jin yanda tashi zuciyar ke karyewa. Kallon fu.ad yake da ko ina na jikinshi kyarma yake.

Haneef ya hango yana tahowa. A hankali ya karaso inda suke. Kallo daya yai musu yasan ba lafiya ba.

"Lukman?"

Ya tambaya a dan tsorace. Cike da wani irin yanayi lukman yace.

"Nana....."

"Inalillahi wa ina ilaihi raji.un......"

Haneef ya fadi yana kallon fu.ad dan in shi yana jin zuciyarshi na mishi wannan zafin baisan yanda ta fu.ad take ba a yanzun.

Hannu yakai a hankali ya dafa kafadar fu.ad din sai lokacin ya dago. Hawaye ne suka biyo fuskarshi. Abinda rabon da haneef yagani tun suna kanana.

Zame jikin shi fu.ad yayi ya hada kanshi da gwiwa. Kuka yake kaman karamin yaro. Nana mutuwa zatayi. Shine abinda yake ta masa yawo.

Dafa shi lukman zaiyi haneef ya rike shi yana girgiza masa kai. Wannan ba abu bane da kowa zai iya taimaka mishi.

Dole subar shi. Shi da kanshi zai accepting abinda ke faruwa. Fu.ad kam bai taba jin duniya ta mishi kunci ba sai yau.

Yar shi da ko damar saninta bai samu ba. Kuma wannan ba laifin kowa bane saina safiyya. Sofi ta boye mishi ita gashi yanzun mutuwa zatai.

Mikewa yai yasa hannu ya goge fuskar shi yana shaqar iska mai nauyi kamin ya fitar da ita. Daga haneef har lukman kallo suka bishi dashi.

Hanya ya nufa da lukman kadai yasan safiyya ce a wajen. Dan haka yabi bayansh. Hakama haneef. Tana nan zaune inda suka barta tana wani irin kuka.

Karasawa fu.ad yai dab da ita. Ta dago da jajayen idanuwanta da fuskarta data kumbura ta kalle shi. Wani irin abune cikin idanuwanshi.

Muryarshi a dakushe yace.

"Saboda ke bazan san abubuwa da yawa ba akan Nana.

Saboda ke na rasa shekaru goma sha daya na rayuwa tare da ita.

Bake ya kamata kiyi kuka ba sofi. Saboda ko da ace yau babu Nana kina da shekaru goma sha daya a cikin kanki da zaki dinga dubawa kina samun sauqi.

Banida komai!!!

Banida abinda zan duba nata banda watanni!!!

Wallahi bansan yanda akai zuciyata tai kuskuren sonki ba!!!"

"Fu.ad...."

Haneef ya kira shi dan yasan yanayin da yake ji zai iya saka shi fadar abubuwan da zai zo yana nadama daga baya.

Mikewa safiyya tayi taba kallonshi cike da tsanar da take ji tashi da rashin adalcin da rayuwa take mata ta ko wanne fanni.

Batare data kalli haneef ba tace.

"Kabarshi! Kabarshi ya fadi duk abinda yake so ya fada. Kabarshi ya fadin son ranshi dan baisan kowa ba sai kanshi.

Kana da bakin da zaka doramun laifi fu.ad?"

Ji yake kaman ya makareta. Taya zata iya tsayawa gabanshi tana masa wannan kallon kaman shine da laifi.

"Kai ka tafi. Ban kama ka na turaka waje ba! Kai ka zabi kabarni. Saboda me zaka ga laifina?"

Sosai yake kallonta.

"Saboda me zaki kasa ganin a kowanne zabi danayi kece a cikinshi?
Kina son yara nikuma bazan iya baki ba. Sai nayi laifi dan na barki ki auri wanda zai iya baki abinda na kasa?"

Girgiza kai safiyya take tana jin wasu hawayen na zubo mata.

Kama shi haneef yai yana fadin.

"Wannan bazai baku mafita ba fu.ad......."

Kwacewa yai yana kallon shi da fadin.

"Ni nai mata laifi inma laifi ne haneef saboda me zata hukunta mu harda Nana? Saboda me zata hanamun rayuwa da yata?"

Ya karasa maganar da wani sanyin murya daya karyama daga haneef har lukman zuciya. Muryarta can kasa safiyya tace.

"Na nemeka. Na nemeka daga lokacin dana gane ina da cikin Nana. Na nemeka fu.ad gaba daya numbers dinka a kashe"

Kallonta yake yana tuna yanda ya kashe wayoyinshi gabaki daya na tsayin watanni. Kamun cikin daga murya da kukq safiyya tace.

"Ya kake so inyi?! Meye banyi *Akan so*nka ba? Saboda me zaka dauka kai kadai ne zaka rasa Nana? Ko ka dauka ka fini sonta?"

Kallon lukman yai.

"Kaji ta ko? Kaji ta ko lukman. Zan dauki yarinyata. Zan kaita ko wacce kasa ta duniya. Zan kashe komai dana mallaka dan ta samu lafiya"

Wata dariya safiyya tayi da bata san daga inda ta fito ba.

"Welcome to reality fu.ad muhammad arabi. Inda tarin dukiya bazai maka amfanin komai ba!

Zunubanmu ne muke girba ta wannan hanyar. Wallahi fushin iyayene muke gani"

Kuka take sosai. Kalamanta sun girgiza shi. In haka rasa da yake me su abbah suka ji da ya tafi? In haka soyayyar yara take wacce iri su momma ke masa dayake dauka a arha?

Tabbas safiyya ta fadi gaskia. Gaskia sofi ta fada. Barin iyayenshi ne ke bibiyarshi. Fushin abbane yake bibiyarshi.

Kallonta yai da wani irin nauyi.

"Zamu gyara komai. Babu wanda zai iya saving Nana. Allah daya dora mata ne kawai zai iya.

Sofi zamu gyara komai. Zamu ba kowa hakuri. Inna da baba. Su abbah. Zamu fara ganin dai dai in suka yafe mana"

Hawayen dake zubo mata tasa mayafinta tana gogewa. Da wani sabon kwarin gwiwa ta kalli fu.ad.

"Komai zai gyaru in suka yafe mana. Munyi kuskure na daukar zamu iya tsara rayuwarmu da kanmu"

Jinjina kai fu.ad yayi. A karo na farko yana ganin laifukanshi a shimfide. Haqiqa babu mai iko sai Allah. Babu wanda ke tsara komai sai Shi......!

*#TeamAs*
[7/9, 1:20 PM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[7/9, 1:21 PM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: AKAN SO 38
πŸ’˜πŸ’–AKAN SOπŸ’–πŸ’˜*

~Written by~ :Luβπα SufyΞ±Ο€

38

*Ina godiya da fatan alkhairi kaman ko da yaushe. Ba sai na ce komai bama kunsan #AnaTare*

Juyawa fu.ad yai safiyya ta dakatar da shi da fadin.

"Please ka dauki mukullin motata kuje gida da Nana. Bazan iya ganinta ba yanzun......"

Ta karasa maganar muryarta na rawa. Kai ya daga mata alamar yaji ya dan kalli haneef da yake masa wani kallo dake kara karya mishi da zuciya.

Sannan ya wuce. Shi kadai yasan yanda yake jin zuciyarshi. Yakai mintina biyar tsaye riqe da handle din kofar yana maida numfashi.

Addu.a yake Allah ya bashi karfin gwiwar fuskantar nana batare da zuciyarshi ta sake karyewa ba. A hankali ya tura kofar yana jin sallamar da yake sonyi tsaye a ranshi taqi fitowa.

Idanuwanshi ya sauke kan momma. Muryarshi a dakushe yace.

"Gida zamu tafi. An sallameta"

Da fara.a momma tace.

"Alhamdulillah. Aikam nima bara na tashi......"

Kai yadan daga mata. Nazarin shi take kwata kwata a birkice yake hankalinshi kaman baya jikinshi.

"Fu.ad?"

Ta kira cike da alamun tambaya. Kallonta yai sosai yana roqonta da idanuwanshi da karta tambaye shi komai. A hankali ya girgiza mata kai.

Shiru tayi tana mikewa tace ma nana.

"To yar tsohuwa nikam zan wuce sai nazo duba ki ko?"

Dariya Nana tayi da sautinta yasa fu.ad jin zuciyarshi ta wani matse kaman zata fashe. Baya son tuna karancin lokacin dayake dashi najin wannan sautin.

"Ni zan zo ai. Mumy zata kawo ni in kwana gidanki"

Murmushi momma tai mata.

"Allah ya kawo ku lafiya. Ya kara sauqi"

Ta amsa da.

"Amin. Allah ya tsare hanya"

Momma na tafiya ta amsa ta da.

"Amin thumma amin"

Raba fu.ad tayi ta wuce batare data ce mishi komai ba. Yaji dadin hakan dan baya jin zai iya wata magana a yanda yake jin shi.

Kayan su ya fara tattarawa dan baya son ko kallon inda Nana take. Saukowa tai daga kan gadon tazo inda fu.ad ya saka warmers dinsu a babbar leda ta kamo hannunshi tana ja.

Sai da ya ja wani numfashi ya sauke shi batare daya kalle ta ba yace.

"Princess ina jinki...."

Sake jan hannun shi tayi. Bata son yanda yake kin kallonta din nan sam. Tasan me hakan yake nufi. In tun yanzun zasu fara mata irin hakan nan gaba bata san me zai faru ba.

A hankali ya juyo ya sauke idanuwanshi da suka sake launi kan fuskarta.

"Ina mumy?"

Ta tambaya tanajin komai baya mata dadi. Bata son ganinsu cikin damuwa ko kadan. Da da yanda zatai ta cire musu da tayi. Dakyar yace mata.

"Sunyi gaba dasu lukman ni dake zamu tafi"

"Hmmm"

Nana ta fadi ta saki hannunshi taje tana saka takalminta da hijab. Sannan ta dawo ta kama hannunshi suka fita tare.

Saida ya bude bayan motar ya zuba kayayyakin ciki sannan ya bude ma nana ta shiga ya zagaya shima ya shiga.

*

"What is wrong?"

Nana ta tambaye shi kaman daga sama. Dan kallonta yai sannan ya maida hankalinshi kan tuqi da fadin.

"Bakomai me kika gani?"

Sake lafewa tai cikin kujerar motar tace.

"Kayi shiru tun dazun"

Shi kanshi bai kula da cewar tunda ya soma tuqin baice komai ba. Yanajin yanda hannuwanshi ke wata zufa duk da AC din motar a kunne yake.

"Bako....."

Da sauri ta katse shi da cewar.

"Please kar kamun karya. Na tsani aimun karya"

Sauke numfashi yai.

"Tsana is not a nice word princess"

Sauke murya tayi tace

"Kayi hakuri"

Kai yadan daga.

"Yau dinne babu dadi shine kawai"

Ba karya ya fadi ba. Gaba daya ranar bata mishi dadi. Tun kamun a fada mishi wannan mummunan labarin.

Hankalinta ta mayar kan titi sosai tana kallo hanya. Da wani irin yanayi mai nauyi da bai taba ji a murya yarinya mai shekarunta ba tace.

"You are not a match ko?"

Motar yaji tana kokarin kwace mishi. Kamun ya samu yadan dai daitata yana rage gudun da yake. Wani irin yawo zuciyarshi take yi cikin kirjinshi.

Wani abu daya tsaya mishi a wuya ya hadiye. Zufa yake ji ta wajaje da dama tana fito mishi. Baya son mafa karya ko kadan.

Saidai baisan ta inda zai fara gaya mata gaskiya ba. Tsoro ne cike fal a zuciyarshi. Koda Nana zata sani baiso daga shi sai ita ba.

Tafi sabawa da sofi. Zata so kasancewa da ita a wannan lokacin bashi ba. Duk da fadar hakan a kanshi kawai ba karamin ciwo abin yake mishi ba.

"Princess......."

Ga mamakinshi gyara zama tai ta zuba mishi idanuwan nan nata iri daya da nashi.

"Ya mumy take? Ya ta dauki hakan? Bata ji dadi ba ko?"

Nana ta jero mishi tambayoyin lokaci daya. Damtse steering wheel din yayi kaman zai karya shi. Tagane. Tasan bai matching ba.

Muryarshi a sarqe ya amsa ta da.

"Pretty bad"

Shiru yai dan baisan kalaman dazai dora yanayin safiyya akai ba. Dashi kanshi. Dan har yanzun jiyake gabaki daya duniyar shi tayi wata irin girgiza da komawarta dai dai abune mai wahala.

Ko yanzun da yake tuqi kokawa yake da zuciyarshi da duk wani abu nashi ya yarda cewar babu abinda zai iya yi ma Nana.

Shiru tai na lokaci mai tsayi. Tukin yake amman ji yake kamar garin zasu bari. Kwata kwata yaki masa sauri. Yama manta da ya rage gudun motar sosai.

Ta gefen idanuwanshi yaga ta cire hijab dinta. Yadan kalleta ya maida hankalinshi kan tuqi yana jin wani irin yanayi da bashida kalaman misaltawa.

Hular dake kanta da tunda ya ganta irin sune a kan ko yaushe bata taba cirewa ba tasa hannu ta fitar.

Kanta ta shafa da babu gashi ko kwara daya. Ya sake juyowa ya kalleta. Ji yake kaman wani abu na matse mishi zuciya. Kirjinshi zafi yake sosai.

"In fada maka wani abu ba zaka fada ma kowa ba? Kayi alkawari"

Kai ya daga mata ya kasa magana. Wannan wacce irin rayuwa ce. Shekararta sha daya. Kamata yai ace tana can tana wasanta tana tunanin wanne Disney movie ne yafi wani kyau.

Wanne riga yafi burgeta. Bawai zaune anan ba da kanta babu gashi ko kadan. Ji yake zai iya bayar da komai dan ta samu hakan ciki harda tashi rayuwar.

"Ina tsoron in mutu"

Jiyai wani abu ya tsane a fuskarshi. Dayake da tabbacin duka jinin dake jikinta ne ya koma wani waje. Kamun lokaci daya wani abu mai yaji ya mamaye mishi idanuwa.

Hannunta ya kamo da nashi guda daya ya dumtse gam dayan nakan steering motar. Yasan shi ba mai yawan kuka bane. Amman wannan yarinyar ta zaune kusa dashi ta taba mishi zuciya.

Yarinyar shi. Jininshi. Yarinya kwal daya da kaddara ta miko mishi kuma yanzun zata sake karbewa. Wasu hawaye ne yana jin taruwar su da ke da wani irin ciwo.

Yana jin yan kananan fingers dinta sun matse mishi hannu gam kamun tace.

"Kar kai kuka. Please. Kawai ina son in samu wanda zan fada ma ne. Bazan iya fada ma mumy ba. Tana cikin damuwa mai yawa bana so in kara mata.....nasan daka zo ta kara sama ranta zan ji sauqi kuma........"

Shiru tai. Saida yadan yi gyaran murya ya hadiye wani yawu yana maida hawayen dake son zubo mishi kamun yace.

"Kuma me?"

Sauke ajiyar zuciya tayi.

"Kawai ina so in fada ma wani inajin tsoro ne ba tare da yace mun komai zaiyi dai dai ba"

Kai yadan daga mata cikin fahimtar abinda take fada din. Shi kanshi a tsorace yake saboda me zai kasa fahimtar nata tsoron.

Sauke murya tai tace.

"Kawai ina son kowa ya zama dai dai ne"

Da sauri ya fadin abinda yasan karya ne.

"Zamu zama dai dai. Kina iya fadamun kome kike so Nana......zamu zama dai dai.... Duk da....."

Saida yaja numfashi a jere yafi sau uku yana fitarwa kamun ya iya karasawa cikin rawar murya.

"Duk da hakan baya na nufin ba zamuyi kewar ki duk rana ba"

Ya juyo yadan kalleta yana jin yanda zuciyarshi ta rabe gidaje da dama. Murmushin da tai mishi sam bai rage masa radadin dake kirjin shi ba.

Da gudi in aka bashi zabi zai karbi cancer dinta. Ya riga da yayi rayuwa. Wannan lokacin daya kamata ace tayi tata ne.

Saidai zuwa yanzun idan akwai abinda rayuwa ta koya mishi shine bai da iko da tsari na rayuwarshi. Alkalamin kaddara ya rigada ya dade da rubuta mishi tashi.

Da wannan tunanin ya karya corner har suka karasa gida. Maigadi ya bude musu. Suna parking din motar safiyya na fitowa tai tsaye bakin kofar shiga gidan.

Kama murfin motar nana tayi tana sauke wani irin numfashi me nauyi hadi da fadin.

"Daren yau mai tsayine......."

****

Kwance take tana juya text din da jabir yai mata tun da yammaci kan maganar ayna. Rayuwa take dubawa.

Ta lumshe idanuwanta. Tasan yana wajen ayna zance ya fada mata. Sai dai maimakon ta hango shi babu komai cikin kanta sai fuskar Nana.

Babu abinda take tunawa sai yanayin tashin hankalin da iyayenta suke ciki. Sai take ganin rayuwa babu wanda tazo ma da adalci irinta.

Babu wanda ke da kwanciyar hankali irin nata tunda har tana da nutsuwar da zata zauna tana kishi. Godiya ta shiga

Please Login or Register in order to submit comment