Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ukku zan fada miki"

Kai jana ta daga tana sauraren hajiya kaman gabaki daya duniya bata da wani aiki da ya wuce hakan.

Har ranta tanajin yanda ruwan da take ciki yakawo har bakinta. Bata da abin kamawa ta fito daga cikin shi daya wuce shawarwarin mahaifiyarta.

Hajiya taci gaba da fadin.

"Karki yarda zafin kishi ya canza kaunar da tausayin dake tsakaninki da mijinki.

Karki bari addu.a ta kubce miki a kowanne hali da kika tsinci kanki.

Ki zauna da ita da zuciya daya. Ko zata cuceki Allah zai zamana yana tare dake saboda babu mugun abu a zuciyarki.

Ko koma gidanki batare da tsoron nan a zuciyarki ba murjanatu. Kaddararki ta jima da bushewa. Tsoro ko rashin hakan bazai canzata ba.

Hanyoyi na Ubangiji suna da girma. Kiyi addu.ar alkhairi. Ki mika ma Marubucin kaddararki komai naki. Zai nuna miki hanya idan kin rasa ta"

Wata irin nutsuwata daban jana take ji a cikin zuciyarta. Hannu tasa ta goge fuskarta. Ta sake kwantar da kanta kan cinyar hajiya. Muryarta a dishe saboda kukan da tayi tace.

"Madallah da mahaifiya irinki hajiya. Madallah da mahaifiyar datake kama hannuna a koda yaushe zuwa hanyar gaskiya.

Ina kaunarki hajiya. Allah yabarmin ke"

Dariya hajiya tayi.

"Ke dai kice Allah ya hadani da mahaifinku a aljanna. Ita nafi bukata"

Murmushi jana tayi tana ma mahaifinta addu.ar samun Rahma a zuciyarta. Kamun ta sauke numfashi.

****
****

Da safe wajen karfe goma duk sun gama shiryawa daga shi har abbah. Lukman da haneef ma sunzo gidan.

Nana da camera a hannunta su haneef sun biye mata sai shiririta suke. Kar lukman yaji labari. Fu.ad ya kalle su ya girgiza kai.

Gaba daya nana ta mayar dasu yan yara. Har ya juya ya maida hankalinshi wajen abba ya sake juyowa da sauri.

Kallonsu yake sai yake tunanin shima kenan haka yake zama yaro in yana tare da ita kenan?

Ya bude baki zai magana yaya babba ya shigo. Su duka gaishe dashi sukai shikuma ya gaishe da abbah da momma.

Fu.ad ya kalla. Jeans ne blue a jikinshi da riga fara sal da ita. Ya girgiza kai hadi da fadin.

"Kai haka zamuje gidan surukai dakai da kananan kaya?"

Sosa kai fu.ad yai yana ware idanuwa hadi da fadin.

"Banda ko daya ne"

Haneef babban yaya ya kalla.

"Kayanka ba zasuyi ma fu.ad ba?"

Girgiza kai haneef yayi. Dan fu.ad ya fishi tsayi yanzun kam. Na lukman kuma daga tsayin har girman ya mishi kadan.

Sauke ajiyar zuciya babban yaya yayi.

"Allah ya rufa asiri to"

Abbah da momma kam dariya suke musu. A hankali nana ta mike ta taka har inda babban yaya yake. Kallonshi take.

Sai lokacin ya kula da ita.

"Ina kwana baba babban yaya"

Tace mishi dan haka taji suna kiranshi babban yaya. Lukman ya fara kwashewa da dariya kamun si haneef su dauka.

Har babban yaya saida ya murmusa. Kallonsu nana take cikin rashin fahimtar me suke ma dariya.

Kamo hannunta babban yaya yayi.

"Rabu dasu nana. Kina lafiya?"

"Lafiya kalau nagode"

Ware idanuwa yai da dan mamakin wayan yarinyar. Kamun ya kalli su haneef yace

"Muje ko?"

Ba musu suka mike. Lukman ne ya kama hannun Nana suka fice. Momma na musu Allah ya bada sa.a.

Mota daya suka shiga da babban yaya da abbah. Su kuma su haneef suka shiga mota daya. Fu.ad ke tuqin dan shi yasan gidan.

*

Kofar gida suka tsaya fu.ad ya sake kiran safiyya yace musu suna kofar gida. Ko mintina biyar ba ai ba tsakani ta kira tace su shiga.

Kwace hannunta nana tayi daga na lukman ta ruga da gudu cikin gidan lukman yace.

"Au nana dan munzo ko? Zaki fito ki same ni"

Bata juyo ba dariya kawai tayi. Suka shiga ciki su dukansu. A falon da suka shiga jiya aka tare su. Ware idanuwa fu.ad yake ko zaiga safiyya amman babu alamar ko Nana ma balle yai tunanin zai ga safiyya.

Inna ma suna gaisawa dasu abbah ta kawo musu lemuka da ruwa da fice daga dakin. Su dukansu ruwan kawai suka sha.

Babban yayane kawai ya fasa lemon exotic guda daya ya sha. A nutse suke magana tsakanin abbah da baba.

Fu.ad kam bayajin me suke fada kwata kwata saboda hankalinshi ba akansu yake ba. Zuciyarshi bata tare dasu.

Tana wajen safiyya a yanzun. Mamakin yanda rayuwa ta canza musu lokaci daya yake. Canji tai musu me kyau.

Kaddararsu ta sauya su daga duhun data jefa su zuwa haske mai ban mamaki. Lukman ya zungure shi. Da sauri ya dago kai ya kalle shi.

Ware mishi idanuwa yai alamar ya dawo da hankalinshin kan maganar da ake yi dan ya kula baya tare dasu.

Yanajin su abbah suka tsayar da magana cewa ranar za.a daura aure karfe hudu. Saboda a samu damar sanarma mutane.

Babu ma yanda basuyi da baba ba akan ya karbi sadakin ya rike yace aa kawun safiyya ne zai amsa sai an kira shi tukunna.

Mikewa sukayi akai sallama gabaki daya. Su abbah suka fara ficewa. Fu.ad ya kalli haneef daya zare mishi idanuwa alamar ya wuce su tafi.

"Bara in kira safiyya ta turo nana"

Tura shi haneef yayi. Kasa kasa yake fadin.

"Ba wata Nana. Kabarta anjima inmun dawo mun tafi da ita"

Hakoranshi fu.ad ya bude haneef gabaki daya saikace mai tallar abin goge hakori hadi da fadin.

"To ko nima in zauna anjima in kunzo saiku tafi dani"

"Fu.ad!"

Lukman ya fadi. Daga kafada fu.ad yai yana ware idanuwa yace ma lukman.

"What? Meye dan kun barni?"

Swatting dinshi haneef yai a bayan kai ya tsugunne yana fadin.

"Ouchhhh me nai ne wai ku?"

"Wuce mu tafi"

Haneef ya fadi yana hade fuska. Turo baki fu.ad yai kaman yaron da aka kwace ma sweet. Ya wuce yana fadin.

"I so don't like ku biyun nan"

Dariya sukai suna tusa shi gaba haneef na fadin.

"We so don't care!"

*#TeamAS*
[7/15, 7:34 PM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[7/17, 6:46 PM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: AKAN SO 44
*πŸ’˜πŸ’–AKAN SOπŸ’–πŸ’˜*

~Written by~ :Luβπα SufyΞ±Ο€



Wattpad: LubnaSufyan

44

*I know you guys will want to kill me after reading this chappy. But karku manta i promise. A HAPPY ENDING*

*Ina godiya da kaunarku. ILYA*

*#AnaTare*

Wayarshi ke ringing. Yadan ja karamin tsaki saboda sam bayajin magana koma wacce iri ce. Hannunshi yasa ya tallabi goshin shi.

Wayar ta sake daukar ringing. Daukota yayi da niyyar kashewa gabaki daya. Ganin sunan dake jiki yasa har hannunshi ke rawa wajen picking.

Wani irin dokawa zuciyarshi take. Dakyar ya nemo muryarshi ya iya fadin.

"Nuriyya"

Shiru tadanyi. Yasan tana jinshi dan haka ya sake cewa.

"Are you okay?"

Maimakon ta amsa tambayarshi sai catayi.

"Mafarki nake ko da gaske ne kacemun ba anty bace mahaifiyata?"

Yasan yanayin da take ciki. Baya son kara mata damuwa.

"Please muyi wannan maganar idan kin kara nutsuwa kin....."

Katse shi tayi da fadin.

"Ka fadamun kawai. Ina son sani ne"

Muryarshi a dakushe yace.

"Ba ita bace mahaifiyarki nuriyya. Ta tsince ki ne ta rike ki"

Yanajin kukan daya kwace mata. Tabashi take ta ko ina na jikinshi batare datai amfani da hannayenta ba.

Kukan ta na shiga har kasan zuciyarshi yana yawo.

"Nuri..."

"Karka sake kirana da Nuri please.....Na... Haka yake cemun..."

Ta karasa maganar muryarta na rawa da alamun kukan da take yi. Gaba daya bayajin dadi. Ya bude baki zai magana ta kashe wayar.

A hankali ya ciro wayar daga kunnenshi ya bita da kallo. Ajiyewa yayi yana sauke numfashi.

****

Kan gado ta saki wayar ta kwanta. Kuka take mai taba zuciya. Abu dayane yake mata yawo akai.

Ada tasha dauka cewar anty ce mahaifiyarta. Yafi a kirga tana tambayarta waye mahaifinta tana shan jibga harta hakura ta daina.

Duk tsahon lokacin nan tana ma kanta kallon wadda aka samu ta hanyar banza. Ta dade da making peace dinta da wannan bangaren.

Ada tasan wacece mahaifiyarta. Yanzun komai ya canza mata. Bata san wacece ita ba. Batasan ina aka samo ta ba.

Har yanzun tabon samu ta hanyar banza bai bace mata ba. Shin yarda ta akai? Ko me ya faru da ita. Wani tsoro ne yake shigarta.

Jan kafafuwanta tayi ta hade jikinta sosai kan gadon. Nawaf din da take kallo take tunanin tana da wani a fadin duniya shima baya nan.

Ya tafi inda bazai taba dawowa ba sai dai ita taje ta same shi. Bata da inda zata kama. Bata da inda zataje.

Ba zata ce ga makomarta ba idan tagama takaba. Tasan darajar hakan take ci a gidansu nawaf.

Fadar sunanshi kawai wani ciwo take ji marar misaltuwa. Wanda baisan yanda dacin mutuwa yake ba bazai fahimci halin da take ciki ba.

Text taji ya shigo wayarta. Hannu takai ta dago da wayar ta duba. Farhan ne dan haka ta bude.

'Idan kina bukatar wani abu. Ina nan. Kirana kawai zakiyi. Please ki kula da kanki'

Ajiye wayar tayi ta lumshe idanuwanta tana rasa exact abinda take ji.

****

Zuciyarshi wani irin dokawa take tun da su abbah suka tafi ya kasa samun nutsuwa. Ji yake kaman kaddara zata sake kwace mishi safiyya.

Ji yake kamar ba za.a daura auren nan ba. Ya kasa zama. Sai kai kawo yake yi cikin dakinshi. Kama handle din kofar yai zai fito wayarshi ta kama ringing.

Zarota yai daga cikin aljihunshi. Ganin lukman ne ya kara ma zuciyarshi gudu da dukan da take yi. A sanyaye ya daga hadi da fadin.

"Lukman...."

"An daura fu.ad. An mayar da aurenku da safiyya"

Lumshe idanuwa fu.ad yayi ya jingina jikinshi da kofar dakin yana jero ma Ubangiji godiya. Muryar lukman ta katse shi da fadin.

"Fu.ad....."

"Ina jinka lukman"

Wani numfashi lukman yaja kamun yace.

"Ka kula da ita. Zai wahala inta kubce maka ta sake dawowa. Ba kowa bane yake sa.a irin taka a rayuwarshi"

A sanyaye ya amsa da.

"In shaa Allah. Nagode lukman"

"Allah ya sanya alkhairi"

Lukman ya fadi yana kashe wayar kamun fu.ad din ya amsa. Baisan me yasa yaki zuwa ba.

Babu yanda babban yaya baiba yace kanshi ciwo yake. Abbah yace a kyale shi aiba dole saiyaje ba.

Takawa yai ya karasa kan gadonshi ya zauna. Safiyya yaima text da kalma daya.

'NAGODE'

Batai mishi reply ba. Baikuma saka ran daya ba. Dan haka bai damu ba. Nan ya zamanshi yanajin dawowar su abbah bai fita ba.

Yana son kasancewa shi kadai dinne na wani lokaci. Koda na iya ranar ne. Bai fito ba saida ya dauro alwalar sallar magrib tukunna.

****

Tunda baba ya dawo ya fada mata an sake daura auransu da fu.ad ya fice da Nana take kwance daki tana kukan da bata san dalilinshi ba.

Inda ance rayuwa zata sake maidata matsayin data dade da goge shafinshina zuciyarta ba zata yarda ba. Tana jin sallamar inna ta shigo dakin.

Da sauri ta mike tana goge fuskarta hadi da amsa sallamar a sanyaye. Gefen gadon inna ta zauna da wata leda a hannunta.

Ta dora ledar kan gadon ta budeta. Atamfofine guda biyu a ciki. Takalma sai abin hannu da sarka. Da hawaye cike taf idanuwan inna muryarta na rawa tace ma safiyya.

"Bayan usman ya kammala aji shidda jarabawarshi batai kyau ba. Akace saiya gyara wata shekarar.

Sai ya bukaci zai dinga zuwa aikin kafinta da ya soma yi tun dawowarmu makaranta tasa dole ya ajiye.

Cikin kudin dayakan samu yana mana siyayya dasu. Kama daga kaya zuwa abubuwan ciye ciye......"

Shiru inna tayi tana goge hawayen da suka zubo mata. Tun da inna ta kira usman wasu sabbin hawaye ke zubo ma safiyya.

Nata zaman makokin ne take yanzun. Ciwon mutuwar usman sabone a wajenta. Su inna suna da shekara ukku su ririta nasu ciwon. Itakam yau kwana daya kenan da samuwar nata.

Turama safiyya kayan inna tayi.

"Ko da muka hakura da nemanki. Usman yafi kowa sa ran dawowarki. Shi ya siyo kayan nan yaban in ajiye.

Da daidai ya siyo yana sa ran zaki dawo ko yaushe karya zamana kin dawo bai siya miki komai ba.

Yakance kuna hirar sana.a tare yakan fada miki bashida sha.awar karatu......."

Kasa karasawa inna tayi dan haka ta mike kawai ta fice daga dakin. Kayan safiyya tasa hannu akai.

Kaman taba kayan datayi ya bude mata hotunan usman a zuciyarta. Fuskarshi take kallo. Murmushin shi take gani.

So take ta tuna yanda sautin dariyarshi yake. Yanda muryarshi take cikin kanta ta kasa. Wani irin tsoro taji ya shigeta.

Sosai take jin tsoron har cikin tsokar jikinta. Lokaci ya kwace mata wannan bangaren na usman.

"Ya Allah...."

Ta fadi wasu irin hawaye masu dumi na zubo mata. Da gaske ta manta yanda sautin muryar usman yake. Atamfafin ta janyo jikinta hannuwanta na rawa.

Fuskarta ta hada da kayan tana kuka marar sauti tana fadin.

"Allah ya kai haske kabarinka usman. Ban samu bankwana dakai ba balle in roki gafararka...."

Sosai take kuka tana rike kayan a jikinta. A haka yayanta ya shigo ya sameta. Bataji sallamarshi ba saboda gabaki daya duniyar a birkice take jinta a lokacin.

Saida taji ya zauna gefen gadon sannan ta dago fuskarta dake jikin kayan da usman ya siya mata ta sauke su kan yaya.

Sama sama taji numfashinta nayi. Jiya taita sa ranshi ya kira inna yace mata bazai samu zuwa ba.

"Yayaa......."

Ta kirashi cikin yanayin ciwon da zuciyarta takeyi. Da sauri ta sakko daga kan gadon ta zauna kasa. Hannuwanshi ta kama.

"Yaya ka yafemun. Yaya babu usman yau. Usman ya tafi ya barmu...."

"Shhhhhhh safiyya ya isa. Ya isa haka"

Ai kaman ma ya sake bude mata wani sabon shafin kukan. Tana rike da hannuwanshi.

"Dan Allah safiyya kiyi shiru. Soyayyarmu usman yake bukata ta hanyar addu.a"

Dago jajayen idanuwanta tayi.

"Ba zaka gane me nake ji ba yaya. Kai ka mishi sallama....."

Kallonta yake. Shi kuwa zai gane me take ji fiye da ita. Dan uwa daya ta san ciwon rashin shi.

"Karki fara safiyya. Karki sake ki yankema abinda baki sani ba hukunci.

Ba zaki taba sanin me ake jiba lokacin daka mutuwa ta dauke maka dan uwanka guda daya.

Kaddara ta watsa yar uwarka duniyar da baka sani ba. Karki yankema abinda baki sani ba hukunci"

Fuskarshi take kallo. Hannuwanshi ta saki tasa hannu ta goge tata fuskar.

"Ka yafemun yaya. Naji rashin ku fiye da zatonka. Wallahi na horu da rashinku. Ciki harda bacewar muryar usman daga gareni.

Na rasa abubuwa da yawa......"

Wayarshi taga ya dauko. Yana daddanawa. Mika mata yayi ta karba hannunta na rawa. Videos ne.

Da sauri ta danna play. Idanuwanta lokaci daya suka sake cikowa da hawaye. Usman ne yana dariya.

Da alama shi yake daukar kanshi video din yana fadin.

"Bansan me yasa nake ji a jikina bazan sake ganinta ba. Koma menene Allah ya fini sanin shi."

Murmushi yayi cike da wani yanayi dayasa safiyya mikama yaya wayar tana hade kanta da gwiwa. Muryar yaya a dishe yace mata.

"A wayarshi na dauka bayan ya rasu. Date din jiki ya nuna yai recording kwana biyu kamun rasuwarshi.

Dake a zuciyarshi ya rasu safiyya. Usman na kaunarki fiye da yanda kike zato.

Mu duka munyi rashin shi. Addu.armu yake bukata a yanzun"

Ai bata jin nasihar yaya. Yabarta kawai tai kukanta. Yabarta taji mutuwar usman saboda shi ya rigada yaji tashi.

Tana jin ya mike bata dago da kanta ba.

"Naji dadi da na sake ganinki kamun mutuwa ta gifta mana. Allah ya sanya alkhairi"

Bata amsa shi ba. Tanajin ya fice daga dakin ta koma kan gadon ta ci gaba da kukanta.

Saida tadaina jin hawaye ba fita sannan. Tana kwance tana tunanin yanda rayuwa da duka duniyar ma ba komai bace text din fu.ad ya shigo.

Dubawa tayi ta ajiye wayar. Tana rasa abinda ya kamata taji.

****

Har ya tashi da safe bazaice ga abinda yake damunshi ba. Kawai yanajin wani irin yanayi ne daya kasa fassarawa.

Koda anty fati tazo gidan gaisawa sukayi. Ita da momma suka shirya suka tafi gidansu safiyya su taho da ita.

Haneef zai kira yaje suyi magana sai gashi ya shigo gida. Kallo daya yaima fu.ad ya karanci yanayin fuskarshi. Saida ya zauna sannan yace mishi.

"Me ke faruwa?"

Gyara zama fu.ad yai ya fuskanci haneef sosai.

"Em' quitting?"

Cike da rashin fahimta haneef yake kallonshi.

"Me kenan? Bangane ba"

Jan nunfashi fu.ad yayi ya sauke shi a hankali.

"Football. Zan quitting......"

Katse shi haneef yai da fadin.

"No. No fu.ad ba zakayi abinda zaka zo kai dana sani ba"

Murmushi fu.ad yayi. Muryarshi kasa kasa yace.

"Bazan dana sani ba haneef. Ko ban dawo ba na kusan ajiyewa. Ko da bankai inda nake da buri ba. Nayi. Nakuma ji dadinta.

Yanzun kunfi mun komai muhimmanci. Ina son kasancewa tare daku. Na rasa shekaru sha daya. Bana son rasa kwanaki ba a kusa daku ba.

Contract din danai signing ya kare. Sabone zan signing karshen watan nan. Em' done. Zanje in kare komai in dawo"

Sosai haneef yake kallonshi da alamun maganganun fu.ad din basu zauna mishi daidai ba.

"Are you sure?"

Ya bukata. Kai fu.ad ya daga mishi yana murmushi. Haneef ya lumshe idanuwanshi ya bude su.

"Allah ya tabbatar da alkhairi to"

"Amin ina khadee?"

Murmushi ya kwace ma haneef dajin sunan yar tashi.

"Tana islamiyya"

Hira suke kamun hassan ya shigo. Da murmushi a fuskarshi ya gaishe dasu ya nemi waje ya zauna.

Yanayin zaman ya sake karfafa niyyar fu.ad. Yanda yake ji a zuciyarshi bai taba jin hakan akan ball ba.

Yan uwanshi sunfi mishi komai muhimmanci.

****

"Daka shigo ciki"

Cewar ayna bayan sun gaisa da jabir. Girgiza mata kai yayi.

"Wucewa zan na biyo mu gaisa. Ba jimawa zan ba"

Murmushi tayi a kunyace.

"Ina su ikram da anty?"

Murmushin ya mayar mata.

"Duk suna lafiya. Jana tana gaishe dake"

Dagowa tayi tadan ware mishi idanuwanta da alamun mamaki. Ya daga mata girarshi duka biyun hadi da fadin.

"Kina mamakine? In batace ba bazan fada miki ba"

"Kawai dai.... Bansan ma me zance ba"

Murmushi jabir ya sake yi.

"Jana mutuniyar kirki ce ayna. Ina sonta fiye da yanda zan iya fada miki.
Zan aure kine saboda ina sonki badan na rasa komai a wajenta ba.

Banda haufin zata girmamaki duk da ta girmeki. Bance ki tayani son jana ba. Saidai ina son ki tayani girmamata saboda tana da muhimmanci a rayuwata"

Sauke ajiyar zuciya ayna tayi. Wani son jabir da kimarshi na kara shigarta. Cikin fuska ta kalle shi.

"Kaima mutumin kirki ne jabir. Daga lokacin da maza suke neman aure saikaji suna kushe matansu na gida dan su burge yan matan da zasu aura din.

Da ace ka bude bakinka da mummunar kalma akan anty kimarka zata ragu a idanuwana. Bansan ko kaddararka ba akan mata biyu ta tsaya ba.

Saboda zanji a raina yanda kake fada akan anty haka zaka fada akaina. Allah yabani ikon tayaka bata girma gwargwadon iyawata.

Bazan maka alkawarin komai ba saboda bana so ka daga zatonka fiye da yanda zan iya"

Yar dariya jabir yayi. Hankalin ayna da yanayinta shi ne abinda ya fara so tattare da ita kamun ya kula da kyawunta.

Ba fara bace kamar jabarshi. Bakace kuma bata da dogon hanci kaman na jana saidai idanuwanta na burge shi sosai.

Intai murmushi yanda dimples dinta ke fitowa yana mishi kyau. Komai nata ya sha banban dana jana. Yana son su su duka biyun.

"Nagode ayna. Nagode da karamcinki. Zan wuce sai munyi waya ko?"

Kai ta daga mishi tana murmushi.

"Ka kula da kanka. Ka gaishe dasu ikram"

"Zasu ji in shaa Allah. Ki kulamun da kanki"

Ya fadi yana bude murfin motarshi. Addu.a tai mishi dayaji dadinta kamun suyi sallama.

*

Fita yazo yi daga motar yaga deposit slip a ajiye. Janyo su yai da mamaki dan yasan baije bank ba duk satin nan. Yana niyyar zuwa biyama su ikram kudin makaranta bai samu zuwa ba yabari sai weekend.

Dubawa yayi. Ya ware idanuwanshi. Girgiza kai yayi ya fito daga motar yana shiga cikin gidan.

A kitchen ya samu jana tana soya doya da kwai. Ya shiga da sallama ta amsa shi.

Ta baya ya rungumeta jikinshi. Tai dariya tana ture shi.

"Honey J aiki nake"

Gam ya riketa jikinshi. Cikin kunnenta yace.

"Ban hanaki aikinki ba ai"

Hararshi tai duk da baya ganinta.

"Please. Ka sakeni in karasa"

Dariya yayi. Ya saketa yana matsawa suka jera. Kwanon kwan yaja gabanshi ya shiga zuba mata wata yankakkiyar doyar a ciki.

"Ina kaje haka?"

Ba tare da tunanin komai ba yace mata.

"Wajen saminu naje saina biya muka gaisa da ayna. Tace tana gaishe daku ma"

Wani tafasa taji zuciyarta nayi ga wani irin kishi daya turnuqeta. Shiru tayi tana jero addu.o.i cikin kanta. Tanajin idanuwan jabir na yawo a fuskarta.

Taki bari su hada idanuwa ta kafe su kan aikin da take. Saida ta tabbatar zata iya magana batare da kishin da take ji ba cikin muryarta kamun tace.

"Muna amsawa mungode. Tana lafiya dai ko?"

Kai kawai ya daga mata. Saida ta karasa kwashe doyar ta rufe warmer din ta sauke man sannan ya sake janyota jikinshi.

Slips din ya zaro daga aljihunshi ya kamo hannunta yasa su a ciki.

"Janaaa...."

Ya kira da wani irin yanayi. Dubawa tayi. Ta lumshe idanuwanta babu inda bata neme su ba. Sai yanzun ta tuna da motar jabir din ta fita ranar.

"Jana hidimar tana yawa"

Hannuwanshi ta zame daga jikinya ta juya suka fuskanci juna. Idanuwanta ta sauke cikin nashi.

"Meye hidimar a ciki? Biyama yaranmu kudin makaranta? Honey j baka barina in tayaka da komai.

Ko mai na zubama motata sai kayi fada. Please ina so in taimaka nima"

Hannu yasa ya murza goshin shi.

"Bawai taimakawa bane baba so kiyi jana. Bana so ki sangartani ne da yawa. Kar inzo in kasa sauke nauyin da Allah ya doramun.

Hakkin kula daku akaina yake"

Sumbatarshi tayi a hankali kamun ta janye da fadin.

"Nasani. Kuma kanayi ina son yin wani abune nima. Meye amfanin aikin da nake in baka bari ina kashe kudin?"

Murmushi yayi. Ya dora hannuwanshi kan kafadarta.

"Nagode jana. I love you kinsani ko?"

Kai ta daga mishi da murmushi. Har ranta take jin sonshi.

"Kamun yara su dawo zo mu siyo ice cream"

Ya karasa maganar yana jan hannunta. Riko shi tayi.

"Honey j. Ice cream kawai. Promise?"

Dan dakuna fuska yayi. Taja iska mai nauyi taba fitar da ita hadi da girgiza kai. Tasan shi sarai. Inhar zata siyi wani abu sai ya kashe mata rabin kudinta.

Ba yanda zatai da halin jabir.

"Allah ya shiryamun kai"

Dariya yayi yana jan hannunta suka fita daga kitchen din tare.
****

Ya fara damuwa kuma. Su momma sun kusan awa hudu yanzun. Baisan me yasa suka dade ba. Shi kewar nana ma ta dame shi.

Wayarshi ya dauko ya kira safiyya. Ringing din farko ta kashe. Da mamaki yake kallon wayar. Zai sake kira text dinta ya shigo.

'Ina tare da su Momma"

Murmushi yayi. Yasan sarai kunyar daga wayarshi take gabansu momma dan haka ya sake kira wannan karin ko ringing din farkon batai ba ta sake kashewa. Text din ta ya sake shigowa.

'Please mana.

Reply ya mayar mata.

'Kun taho?'

Bata bashi amsa ba ya sake tura wani.

'Zan ta kira har saikin daga sofi.'

Reply tai mishi. Yai murmushi.

'Muna hanya'

Ajiye wayar yayi ya lumshe idanuwanshi. Tattare da wata nutsuwa da take saukar masa akwai wani irin yanayi daya kasa fahimtar ko na menene.

Yanajin kaman wani abu mai girma zai faru dashi.

"Allah kai kasan iya abinda zamu iya dauka. Allah ka bamu juriya a duk lokacin da zaka jarabcemu"

Ya fadi yana sauke muryarshi kasa kasa. Yana ganin yan aikin gidan nata hidima. Hussaina ce da wannan rigimar. A dole sai sunyi walima iya su kawai.

*

*Karfe 4:00*

Ko ina ka duba na gidan cike yake da farin ciki. Zainab da safiyya zaune sunata hira. Zaka rantse sunyi shekaru tare bawai ranar kawai suka hadu ba.

Nana ta karaso wajen safiyya.

"Mumy aramun wayarki in kira anty jana"

Lokaci daya safiyya ta mayar da hankalinta kan Nana. Hannuwa tasa tana taba fuskarta da wuyanta. Murmushi nana tayi hadi da fadin.

"I am ok mumy. Kawai ina son tambayarta abu ne"

Sauke ajiyar zuciya safiyya tayi.

"Kin tabbata?"

Kai Nana ta daga mata kamun ta mika mata wayar. Wucewa Nana tayi da dan saurinta tana barin area din gabaki daya.

Kasan kafar benen da zai kaika sama ta shiga ta zauna. Number din doc jana ta nemo ta kira ta kara a kunnenta. Zuciyarta dokawa take yi.

Taso ace tana kusa da dadynta zatai kiran nan saboda tana jin wani kwarin gwiwa idan tana tare dashi. Sai dai wannan abune da take bukatar yinshi ita kadai.

Hukunci ne akan rayuwarta data ke son yankewa ita kadai batare da kowa ba.

"Assalamu alaikum. Maman Nana"

Aka fadi daga dayan bangaren.

"Wa alaikumussalam. Anty nice ba mumy ba"

Da mamaki a muryar jana tace.

"Nana lafiya dai ko? Ba jikin bane ba?"

Girgiza kai nana tayi kaman tana ganinta kamun muryarta a sanyaye tace.

"Ina so in tambayeki ne kawai"

"Ina jinki nana"

Numfashi nana taja tana son zuciyarta ta rage dukan da take kamun tace

"Nasan dady is not a match. Naji suna maganar zuwa gobe a auna kowa agani.

Ina so in tambayeki. In an samu match. Zan warke ne gabaki daya?"

Shiru jana tayi na dan mintina kamun tace.

"Ki kaima mumynki wayar Nana muyi magana da ita"

Girgiza kai nana take.

"Aa please. Ki fadamun kawai ina son sani ne. Baki san yanda nake ji ba amman kinsan me yake damuna fiye da mumy

Ina so in sani ne. Zan fahimta idan ba zaki gayamun ba"

Da wani irin rauni a muryar jana tace.
"Aa. Zakiji sauki sosai ne"

"Amman zan ci gaba da rashin lafiya irin wannan?"

Tana jin yanda jana ke fitar da numfashi alamar a wahalce take

Please Login or Register in order to submit comment