Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewar karyane. Son shi da yake mata na karyane inhar baya son hada jini da ita.

Inna! Baba! Yaya! Usman! Zuciyarta ke jero mata a hankali. Duk danginta duk wata rayuwa tata.

Yanda ta fito daga gida tabi fu.ad take gani cikin idanuwanta. Yanda tabar komai ta biyo soyayyarshi ta karya take hangowa.

Komai karyane. Duniyarshi tashi ce shi kadai. Karya yake dayace ta shigo ciki. A bakin kofa ya ajiyeta saboda babu wani waje a zuciyarshi da duniyar shi sai son kanshi.

Cikin muryar da bata gane tata bace idanuwanta cikin nashi tace.

"Saika baro gidan? Kabar kowa?"

Cikin rashin fahimtar tambayar ta yace.

"Me zan zauna inyi sofi? Bani na zabi in tafi ba? Abbah ya koreni saboda na zabi tsara rayuwata ba tare da shawararsu ba"

Sai yanzun tagani. Sai yanzun taga fu.ad sosai. Sai yanzun taga babu komai a tare dashi sai son kanshi.

Shi yasa ya aureta. Shi yasa ya yanke musu hukunci kaman shi kadai yake da haqqi akan hakan.

Kallon safiyya yake. Yanda take matsawa baya. Rikota yakai hannu yayi ta ture shi da wani irin karfi.

"Ashe baka sona?!!!....."

Wata guduma yaji ta doka cikin kanshi.

"Ashe karya ne duk kalamanka?"

Wanna karin zuciyarshi ce yaji ta rabe gida biyu. Dakyar ya iya cewa.

"Sofi....."

Cikin tsawa tana wani dafe kai tace

"Bana son ji fu.ad!!! Waya baka ikon yanke mana wannan hukuncin?

Ka taba tunanin inkai baka son yara ni ina so?

Ashe duk karyane. Duk karyane komai?"

Sauran lemar dake cikin zuciyarshi yaji ta karasa bushewa tsaf. Dariyar takaici yai yace.

"*Akan so*nki nai wanna abin. Saboda bana so ke kiyina jikinki ki cutu.

Ki rasa inda zaki dora darajar sona sai kan karya sofi?"

Girgiza kai take wasu hawaye na bin fuskarta.

"Karka gayamun me kai *Akan so* ni safiyya ya kamata in bada wannan labarin fu.ad.

Nabar komai *Akan so* ashe karya ne baka son hada jini dani"

Kai ya dafe a tsawace yace.

"Enough safiyya!"

Saida ta razana. Ji yake kamar kanshi Zaiyi bindiga. Wai dame zaiji ne. Kallonta yake kaman bai taba ganinta ba. Kamun yace

"I don't do happily ever after. Daga randa kika yarda da soyayyata ya kamata kisan banyi kalar wanda zai dinga zarya da yara da pampers ba.

Ban kama da wanda zai asarar lokaci da soyayyar shi akan yara ba. Inada su haneef. Ina da su pha.iza. A duk sanda naji marmarin ganin yara zanje gidansu inga nasu"

Karasawa tai inda yake ta cakumi wuyan rigarshi. Tana wani kukan dana sani.

"bansan baka da soyayyar bawa kowa ba sai kanka da banyi kuskuren yarda da karyarka ba.

Ka cuceni fu.ad. ka rabani da kowa. Ka sa zuciyata ta yarda dukkan alkawurranka"

Hannunta ya kama yana jin yanda zuciyarshi ke tarwatsewa. Bai taba zaton safiyya zatai mishi haka ba.

Cikin idanawa ya kalleta yace.

"Baki san me kike fada ba sofi. Zamuyi magana in kin nutsu"

Wucewa yazo yi ya fita daga gidan dan yadan sha iska ta riko shi gam. Wata irin tsanar shi da bata san cewar akwai irinta ba a duniya na ziyartarta.

"Bana son ganinka wallahi. Bana son sake ganinka"

Kafafuwanshi yaji suna wani irin rawa. Rike hannayenta yai muryarshi na rawa yace.

"Sofi....."

Kai take girgiza mishi tana wani irin kuka.

"Nasan ba zaka taba iya bani soyayyarka ba saboda ban taba ganin mai son kai irinka ba.

Ba kuma zaka iya bani yaran dazan sami soyayarsu ba?

Na rabu da iyayen da suke sona na biyoka bayan baka da abinda zaka bani"

Kallonta yake. Kallonta yake sosai yana auna maganganunta yana ganin tsantsar sonkan dayai mata.

Hannu yasa yai cupping fuskarta dam. Kwacewa take so tayi saidai bata da karfin hakan.

"Ina sonki sofi. Wallah ina sonki"

Kallonshi take hawaye ba sake bin fuskarta.

"Kabani yara. In har kana sona da gaske ba karya kake ba"

Numfa shin shi dake kokarin kwacewa yake kokarin kamawa. Zai iya bata yara ne ta hanya daya.

Kallota yake yana girgiza kai. Sai lokacin wasu hawaye suka zubo mishi. Sosai yake girgiza mata kai.

"Kabani yara in kana sona fu.ad......."

Lumshe idanuwanshi yai wasu hawayen suka sake zubowa yana jin dirarsu tare da dukkan zuciyarshi.

A maimakonta wani irin abu na maye gurbin data bari. Dakyar ya iya fito da kalaman da suke shirin kashe shi har lahira.

"Na sake ki saki daya sofi......."

Kwacewa tai daga hannunshi tana yin kasa. Saboda yanda kafafuwanta suka kasa daukarta.

Baya son sake kallonta karya kasa tafiya. Karya kasa bata abinda ta nema saboda yana da son kanshi kamar yanda ta fada.

Wani irin gunjin ihunta ya daki kuncin shi.

"I hate you fu.ad. Bana fatan sake ganinka a rayuwta."

Wani numfashi yaja ya na takawa zuwa waje

"Mayaudari......!"

Takawa ya sake yi

"Na tsaneka fu.ad nayi dana sanin kaddarar da duk tasa na fara ganin fuskarka a rayuwata....."

Kofa ya bude batare daya juya ba. Ko kalamanta basu kashe shi ba sun kashe abinda yai saura ba zuciyarshi.

Motarshi ya bude ya dauki jakar system dinshi. Komai da yake bukata yana ciki. Fita yai daga gate din gidan ya miki hanya yana jin shi kaman bashi ba.

Ya fita titi baima kula da motar lukman ba sai da yai parking ya fito ya biyoshi ya dafa shi.

Juyowa yai. Gaba daya a firgice yake. Lukman yace.

"Yanzun haneef ya kirani. Fu.ad me kayi?"

Murza kanshi yai kamun ya kalli lukman sosai.

"It is my life saboda me kowa zai kasa fahimtata"

Fu.ad yake fadi cikin hargowa.

Girgiza kai lukman yakeyi cikin ganin wauta da rashin hankalin abinda fu.ad din ya aikata.

"Wallahi duk yanda kake fadar rashin son haihuwa ban taba kawo wa yai kamari haka ba fu.ad. Ban kuma taba zaton cewa a zamanmu zaka yanke hukunci irin haka ba tare daka shawarce ni ba"

saima kaji abinda na sake yi zakai mamaki tunda rayuwa tace bata wani ba. Fadar fu.ad din cikin ranshi a fili kuma yace.

"Na saki sofi!!!"

Lukman baisan sanda ya dauke fu.ad da wani irin mari ba. Fuskarshi dauke da wani yanayi daya girmi tsana da kyamata yace

"Fu.ad anya baka haukace ba? Ko dai makiya sun maka asiri?

Na dauka akan auren sofi kawai Allah ya gama jarabtarka.

Na dauka ka gama girbar mugayen halayenka"

Wata irin dariyar takaici fu.ad yai hadi da fadin.

"Zan bar muku kasar gabaki daya. I have set her free. Ta auri wanda zai iya bata yara. Kaima bankwana nazo inyi maka"

Kallonshi lukman yake. Ya zo ya rabashi yana wucewa. Murya a dake yace.

"We are done fu.ad. Banga me ya rage ba. Be safe"

Kallonshi kawai fu.ad yayi ya wuce abinshi. Yana ganin motar lukman din tazo ta wuce shi fuuu.

Wata irin dariya fu.ad ya kwashe da ita yana jin cewar ya samu matsala. Dariya yake sosai kamar mahaukaci..............!!!"

*

*21/02/2017*

Yanzun ma dariyar ya kwashe da ita sabo da baiga haukan da ya sake tako da kafarshi nigeria ba bayan shekaru sha daya............!

*#TeamAS*
[7/5, 11:21 AM] ๐Ÿ…ฐ "๐Ÿ…ฐ " D'๐Ÿ…ฑโญ•Y๐Ÿ”›๐Ÿ”: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ ๐Ÿ“š๐Ÿ“š_*
[7/5, 11:22 AM] ๐Ÿ…ฐ "๐Ÿ…ฐ " D'๐Ÿ…ฑโญ•Y๐Ÿ”›๐Ÿ”: AKAN SO 30
*๐Ÿ’˜๐Ÿ’–AKAN SO๐Ÿ’–๐Ÿ’˜*

~Written by~ :Luฮฒฯ€ฮฑ Sufyฮฑฯ€

30

((Oh my!!
This love story is a different one!
So unique๐Ÿ‘Œ๐Ÿป in its own way...
I must confess Sis Lubnerh you're indeed a genius when it comes to writing about any aspect of life!๐Ÿ˜

Labarin Fu'ad da Sofi ya samu matsuguni a zuciya ta.There love its surreal! So pure in its own way but full of flaws which are yet to emerge.

Bijirewa umarnin iyaye ba karamin laifi ba ne, dole sai ka ga consequences din shi nan gaba,ko da kuwa kuna son juna ne tamkar Ku hadiye juna,sai Allah ya jarrabce Ku for going against their wish...

Ina tsoron ganin ranar da Sofi zata farka ta ga Fu'ad din ta ya nisance ta..Ina tsoron ranar da komai da suka dade su na ginawa ya ruguje........Allah Sarki Sofi...I wish this wouldn't happen amma dole a nuna miki kuskuren ki......

Loobnerh you gonna take it easy on Sofi plzzzzzzz...

#NowTeamSofi๐Ÿ˜”))

*Thank you ummie jafar*

Tun jiya ya kasa samun wani wadattaccen bacci. Haka ya daure yaje aiki. Yana tasowa ya wuce gida. Wanka kadai yayi.

Abincin ma dan zee ta tusa shi gaba babu inda zai fita babu komai a cikinshi yasa shi danci kadan.

Wani irin abu yakeji cikin zuciyarshi daya jima da manta yanda yake.

Tunani da mamakin yiwuwar samun ya a wajen fu.ad kawai yake yi. Tunani yake zuwansu nawa da shi da haneef gidan fu.ad.

A kulle sai maigadi. Karshe ma cayai musu an siyarma da wasu gidan. Har bichi sukaje asalin gidansu safiyya akace musu sun tashi.

Baisan ko haneef ba. Amman shi ya sake gwadawa bai samu safiyya ba sannan ya hakura. Wayarshi ya dauko ya kira haneef yaji ko yana gida.

Dan bayason ya karasa kuma ya samu baya nan. Kanshi tsaye ya wuce rijiyar zagi inda gidan haneef yake.

*

"Wai lukman sai kace wani bako"

Cewar haneef bayan sun gaisa da lukman din. Murmushi lukman yadanyi hadi da fadin.

"Ba jimawa zanyi bane shisa. Ya su ummie?"

Jingina da mota sannan ya amsa shi da.

"Suna nan lafiya. Ina junior da zainab?"

"Yana islamiyya daga nan zan biya in dauke shi."

Wayarshi lukman yasa hannu a aljihu ya dauko ya budo sakon da hamza ya turo mishi kamun ya mikama haneef.

Karba yai ya karanta saqon. Cike da rashin fahimta dakin yarda da abinda idanuwanshi suke ganar mishi ya dago ya kalli lukman.

Wani murmushin takaici lukman yai hadi da fadin.

"Yar fu.ad ce haneef....."

Girgiza kai haneef yake cikin rashin yarda.

"Bazai yiwu ba lukman. Kawai dai wata ce daban. Ta ina?"

"Wallahi yar shi ce. Naganta da idanuwana. Idanuwanshi. Fuskarshi komai haneef........"

Sau uku haneef na bude bakinshi yana mayarwa ya rufe. Ya rasa meya kamata yaji.

"Na kira shi jiya. Na fada mishi ya dawo kamun ya sake wani kuskuren.

Bamu kadai zai rasa ba wannan karin. Inajin ba tada lafiya yarinyar. Tana bukatar shi"

Wayar haneef ya mika ma lukman yana jin wani abu ya tsaya mishi a wuya.

"Da baka bata lokacinka ba. Ba dawowa zaiba lukman. Kanshi kadai yasani. Bana tunanin zai dawo saboda wannan yarinyar"

Jinjina mishi kai lukman yai. Dan yafi kowa sanin halin fu.ad. Ga shi baima fada mishi dalilin daya sa yace ya dawo ba.

Saikace baisan yanda fu.ad yake da umarni ba. Sauke numfashi yai yace.

"Safiyya na garin nan haneef"

Wani abune ya fadoma haneef. Kar dai ace safiyya bata bar gidan nan ba. Kawai tasa ace bata nan ne.

Kallon lukman yai yace.

"Kasan me. Jeka dauko junior daga islamiyya. Zan dubo safiyya i will call you ko me ake ciki.

Zan manta yanda na tsani fu.ad a yanzun saboda indai wannan yarinyar yarshi ce tana bukatar family dinta"

Dariya lukman yai ya girgiza kai kawai ya bude motarshi ya tafi. Tsanar fu.ad itace abu na karshe da yasan zuciyarsu ba zata iya ba.

Haneef dinma mota ya shiga ya fice. Text yaima ummie ya fada mata ya fita dan bazai iya komawa ciki ba.

Koya ya rufe idanuwanshi a hanya fuskar fu.ad yake gani. Yanayin shi. Komai na kanin nashi.

Sauke ajiyar zuciya yai. Yana marhabin da duk memories din da suke dawo mishi. Yaushe rabon daya barsu haka.......!

****

Zaune suke suna cin abinci a tsakiyar falon suna kallon Harry Potter a mbc 2.

"Nace miki wannan ne na karshen fa mumy. Inda suke canza kala suyi kaman harry...."

Saida ta hadiye abincinta sannan tace.

"To ni banganshi bama....."

Jinjina kai Nana tayi abincin da take ci na mata wani iri a baki. A hankali ta ajiye cokalin cikin plate din da suke sharing ita da sofi.

Abincin bakinta take taunawa tana kokarin hadiye shi a hankali a hankali. Amai taji yana neman taho mata.

Da gudu ta mike ta nufar bedroom dinta. Sofi ta ajiye cokalin ta bita tana fadin.

"Nana....."

Toilet ta sameta tana kwara amai kaman zata fito da yan cikinta. Dafa bayanta tai harta gama aman tsaf tana mata sannu.

Zuba mata ruwa tayi ta wanke bakinta da fuskarta. Ta taimaka mata ta cire kayan jikinta. Saboda galabaitar datai sofi tai mata wanka.

Ta nadota da towel ta kamota suka fito. Wata doguwar riga marar nauyi ta dauko mata ta bata ta saka.

Kallonta sofi takeyi. Yanda idanuwanta suka shiga ciki. A satin nan ta kara ramewa. Sai hasken fatar. A sanyaye tace.

"Muje asibiti nana"

Ware idanuwanta tai akan fuskar sofi da saida taji gabanta ya fadi. Ko a zuciyarta bata son kiran sunan shi saboda ciwon da take ji.

"Ba sai munje ba. Nikam kwanciya kawai zan in huta"

Sam bata son takura mata. Taba jikinta tayi taji babu zazzabi. Hankalinta yadan kwanta kadan.

Kwanciya nana tai. Sofi ta gyara mata blanket sannan ta zauna gefen gadon tana sauke numfashi.

Jitai kaman ana kwankwasa kofa. Tadan kara saurarawa. Kwankwasawa ne. Da mamaki a fuskarta ta mike.

Waye zaizo a wannan lokacin. Tasan dai idan Ansar ne kiranta zaiyi a waya kamun yazo. Mikewa tayi tace ma nana.

"Barin ga waye yake buga kofa....."

Bata jira amsar nana ba ta fice daga dakin tana fadin.

"Ana zuwa....."

Karasawa tai wajen kofar batare da tunanin komai ba ta bude. Wani irin tsalle zuciyarta tayi tana shirin fitowa daga kirjinta.

Batasan lokacin da kafarta taja da baya ba. Da mamaki karara a fuskar haneef na ganinta.

Itace kuwa. Safiyya ce. Lokaci daya ya hango ta tana yar karamarta wannan kuma ta zama babbar mace.

Banbancin waccen safiyyar da wannan a bayyane yake. Waccan akwia yarinta. Tsoro da kauyanci a tattare da ita.

Wannan safiyyar babu alamar yarinta ko kadan a tattare da ita. Wannan safiyyar ta mishi kwarjini saboda tayi kama da wadda wani abu bazai razana ba.

Safiyyar nan babu kauyanci a tare da ita. Sosai take kallonshi tana girgiza kai. Shekaru goma sha daya ta boye musu.

Sai yau ne za.ace kwatsam sun ganota. Muryarshi a sarqe yace.

"Why safiyya? Saboda me kikai mana haka?"

Bataji taruwar hawayen ba. Zubar su kawai taji. Muryarta na rawa tace.

"Kaimun adalci haneef. Bayan abinda kaninka yaimun wanda ya taba ganinshi ma bana son alaka dashi........."

Lumshe idanuwa haneef yayi yana jin nauyin tambayar da yayi mata. Kawai ya kasa jurewa ne.

Saboda yana jin kaman da hannunshi a abinda fu.ad din ya aikata dan haka yaso ya nemo safiyya ya taimaka mata ko zai rage yawan laifukanshi.

Bude baki yai zai magana ta makale. Idanuwanshi suka kafe kan yarinyar dake tahowa.

Bin inda yake kallo saffiya tai taga nana da take kallon haneef itama. Sannan ta maida kallonta kan sofi tana karasawa kusa da ita.

Riketa a jikinta sofi tayi tana kallon haneef da dakyar ya iya janye idanuwanshi daga kan nana.

Saboda duk wani shakku kan maganar da lukman ya fada mishi ya gama gogewa da ganin nana da yayi.

Wata kewar fu.ad ta ziyarce shi. A hankali nana tace.

"Mumy?"

Tana son tambayarta waye haneef din dan bata taba ganinshi ba.

Kallonta safiyya tayi tadan daga mata kai. Alamar babu damuwa zata iya karasawa wajen haneef tai mishi magana.

A hankali ta taka zuwa inda haneef yake saboda batajin karfin jikinta. Idanuwanta ta sauke kan fuskarshi hadi da fadin.

"Ina wuni....."

Ya kasa magana. Ya kasa cewa komai da irin abinda yakeji. Tsugunnawa yai dan tsahonshi yazo daya da nana.

Hannuwa yasa yai cupping fuskarta yana son ganin da gaske ne ko mafarki yake. Idanuwanshi ke yawo a fuskar nana.

Kamun ya kalli safiyya dakyar yace.

"Ya sunanta?"

Fuskarta ta goge kamun a sanyaye tace.

"Safiyya. Muna kiranta Nana"

Jinjina kai haneef yayi yana jin yanda lokaci daya son yarinyar ya shigar mishi rai. Mikewa yayi ya kalli safiyya.

Ta fahimci yana son magana da itane. Hannun nana ta kamo tana fadin.

"Kije ki kwanta ki huta nana. Zanzo yanzun"

Haneef ta kalla tai masa murmushi hadi da fadin.

"Sai anjima....."

"Ya Rabb...."

Haneef ya fadi yana binta da kallo harta shige ciki. Kamar ta daya da fu.ad. Komai nata.

"Ka shigo"

Safiyya ta bukata a hankaki tana wucewa cikin falon. Bakin kofa haneef ya ajiye takalminshi sannan ya bita.....!

****

Necktie dinshi ya warware ya jefar dashi gefe. Ya cillar da suit din dake hannunshi kan gado.

Gidan yayi wani shiru yasan duka yaran suna islamiyya. Jana kuma tana wajen aiki.

Waje ya samu gefen gadon ya zauna yana dafe kai. Kwata kwata jinshi yake ba dai dai ba. Baisan haka ayna takai a zuciyarshi ba sai yau.

Sau shidda yana zuwa office dinsu suce mishi bata zo ba. Tun dazun yake kokawa da zuciyarshi kan kiranta a waya.

Dawowar dayai ya samu gidan ba kowa ya kara mishi damuwa. Waya ya dauko ya lalubo number dinta ya kira.

Ringing biyu tayi ta daga hadi da mishi sallama cikin sanyin muryar nan tata dake saukar mishi da kasala hadi da gaishe dashi.

"Lafiya kalau. Yau dai lafiya ko? Bakizo wajen aiki ba"

Ya bukata. Ta amsa shi da fadin.

"Mama ce bata jin dadi. Ga gidan sai mu kadai da muka dawo asibiti shine na zauna kar inbarta ita kadai"

Lumshe idanuwa jabir yayi yanajin wata nutsuwa. Har hankalinshi yadan kwanta.

"Allah sarki. Ya jikin nata yanzun?"

"Da sauki sosai. Nagode da kulawa"

Murmushi yaji yadan kwace mishi.

"Allah ya bata lafiya. Kimun text na address din inzo in dubata"

A hankali tace.

"Da kabarshi kar dawainiyar tai yawa"

"Haba bakomai. Ki turomun yanzun fa"

Ta amsa da.

"In shaa Allah. Nagode"

Ya kashe wayar yana mikewa. Jinshi yake wani iri. Harya ajiye wayar ya dauka. Jana ya kira harta gama ringing bata dauka ba.

Jefar da wayar yayi kan gado. Ya shiga wanka.

*

Wata shadda ya saka ruwan kasa mai cizawa. Ya dora hula da bata kai shaddar haske ba da takalmi ya daura agogonshi.

A shekaru talatin da takwas jabir nada wani kwarjini naban mamaki. Mutum ne shi mai son rike girmanshi da bawa kowa hakkin shi.

Baki ne. Sai dai yana da kyau dai dai nashi da tsayi matsakaici. Sajen dake fuskarshi ya kara mishi wani kwarjini na daban.

Kasancewar shi da na farko a gidansu ya riga ya saba da dawainiyar kannenshi guda biyu da duk mazane tun bayan rasuwar mahaifinsu.

Kusan komai shi yake musu musamman da mamansu ta rasu. Shine uwa da ubansu duka. Ya auri murjanatu tana level 2 tana karantar medicine.

Haka rayuwarsu ta ci gaba da tafiya da ci gaba mai inganci. Duk da ba zaa kira jabir mai kudi ba yanda rufin asiri daidai gwargwado.

Wannan kenan.

*

Saida ya tsaya ya siyi kayan marmari leda biyu mai layi layi sannan ya wuce unguwar court road inda ayna tai mishi text.

Gidansu bai mishi wahalar ganewa ba. Yana zuwa ya kirata a waya ta fito. Sanye take da atamfa a bazai iya fadar skirt bane ko zani saboda hijab din da take sanye da ita doguwace har ta kai kwaurinta.

Murmushin nan ta tarbe shi dashi da har saida kumatunta ya lotsa duka biyun. Komai na ayna burge shi yake matuka.

Gaisawa sukai ya sake tambayarta jikin mama. Tace su shiga ciki ya dubata. Haka kuwa akayi ya dauki kayan marmarin daya siyo.

Mamansu ayna ta karbe shi da karamci abin har mamaki ya bashi. Daga ita har ayna godiya sukai ta mishi kaman ya kai musu wani abu mai girma.

Sannan ayna ta rakoshi har wajen motarshi.

"Nagode sosai yallabai. Allah ya saka da alkhairi."

Murmushi jabir yayi.

"Yallabai din nan yaki fita bakinki ko ayna?"

Murmushin nan dai tayi dayaji shi har zuciyarshi. Yasan lokaci yayi daya kamata ya fadama ayna yana sonta. Kuma da aure.

Saidai yana auna nauyi da ma.anar hakan a rayuwarsu shi da jana. Farko gani yake kamar yawan nisantar shi da jana take yine yasa son ayna ya shiga zuciyarshi.

A yau kam ya gane koya yaso ya karyata zuciyarshi son ayna ya samu waje daram. Kuma dole ya sanar da wuri kar a samu matsala.

Harya bude baki zai furta mata saikuma ya ce

"Shikenan. Ni zan wuce Allah ya kara sauki. Zaki samu shigowa gobe in Allah ya kaimu ne?"

Kai ta daga mishi hadi da fadin.

"Eh in shaa Allah. Ai ta warware ma. Ka gaishe dasu ikram da madam. Nagode"

Ya amsa da.

"Zasu ji. Sai munyi waya"

Ya shiga motar ya tayar ya tafi. A hanya ya yanke hukunci fara sanar da jana kamun ya gayama ayna.

Bazai iya ci gaba da jan rigima da ita ba kan aikinta tunda yasan karya yake ma kanshi cewar aikinta ne yasa shi son ayna.

****

A daddafe nuriyya ta gama girki. Ta jera komai a dining table din sannan ta koma kitchen ta wanke kayan duk da ta bata.

Tana maida komai wajenshi ne taji takun tafiya a bayanta. A tsorace ta juya. Ta sauke idanuwanta kan kyakkyawar fuskar nawaf.

Murmushi yai mata da shakku a idanuwanshi. Dan matsawa tai baya kadan. Tana tsoron kowanne kallar nawaf ne ya shigo tunda ba tantancewa take ba.

A hankali ya taka inda take. Ya dora hannayenshi akan kafadarta. Goshin shi ya hada da nata. Kamar zaiyi kuka yace.

"Ki yafemun nuri. Bazan sake ba. Dan Allah ki yafemun"

Hannunta ta dora kan nashi dake kafadarta ta rike sosai.

"Ina sonka nawaf. Kaima kasan ina sonka sau nawa zakaimun alkawarin ba zaka sake ba? Sau......"

Dan yatsan shi ya dora kan labbanta yana fadin.

"Shhhhhh. Kinfi kowa sanin matsalata. Kinsan bana iya controlling temper dina. Musamman *Akan so*nki. Bana son jin sunan farhan a labbanki ko kadan"

Kauda kai tai gefe bata son yaga hawayen dake taruwa a idanuwanta. Ta rasa me yasa yakasa gane girman farhan a rayuwarta.

Fuskarta ya kama ya juyo da ita yana sauke idanuwanshi cikin nata. So yake yaga ko tunanin farhan din banzar nan take yi. Ya rasa me yake dashi da shi nawaf bashi da.

Me yai mata dashi bai mata ba? Makaranta ce. Sai me kuma? Yana ina lokacin daya sha kwatarta a hannun mazan dake son lalata mata rayuwa?

Farhan bashi bane ya fito da ita daga gidan karuwan nan. Shi ne. Ya rasa me zaisa ta dinga fifita farhan daya tafi yabarta akan shi.

Yanayin idanuwanshi nuri ta kalla. Tasan abu kadan zai iya birkita mishi sauran tunanin dayake dashi. Kuskure kalilan yake jira

Light kiss ta manna mishi a labbanshi sannan tace.

"Kayi hakuri nima. Bazan sake ba. Muje muci abinci"

Ta karasa maganar tana kokarin wucewa. Hannunta ya riqo ya janyota tana komawa.

Kallon fuskarta yake. A hankali yasa hannu ya shafi inda jini ya kwanta. Da sauri ta rike hannunshi tana janye fuskarta.

"Da zafi ko?"

Ya tambaya. A hankali ta daga mishi kai. Jiyai ya tsani kanshi gabaki daya. Rungumeta yai a jikinta cikin kunnenta yake fadin.

"I am so so sorry Nuri. Dan Allah ki yafemun"

Matse shi tai sosai. Zaman gidanshi ya fiye mata inda ta fito. Ko banza tasan babu mai cutar da ita sai shi.

"Na yafe maka. Muje muci abinci"

Sakinta yai. Ya kama hannunta suka wuce dining din tare.

****

Taxi ya tara yace yakaishi wani hotel me kyau. Har lokacin mamaki yake ba kadan ba.

Ya rasa tsatsayin dayasa yai abinda lukman yace. Meye yake dashi ma a nigeria da ya dawo ma?

Momma kadai ke son shi. Ita kadai ce ta neme shi bayan watanni shidda da tafiyarshi. Harsu haneef babu wanda ya taba nemanshi yaji yana da rai koya mutu.

Duk yanda yake kaunarsu suka watsar dashi. Suka ki fahimtarshi ko kadan. Saboda sun cika son kansu.

Haka ya biya kudin kwana biyu a hotel din ya wuce room dinshi. Wanka ya fara yi. Yai sallar azahar da baiyi ba ya mayar da la.asar dan yaga ukku harda rabi.

Ordering abinci yayi. Dakyar ma ya iyaci dan jiyai taste din na mishi wani iri saboda ya jima rabonshi dajin shi. Sannan ya fito.

Yana tunanin meya kamata yayi daga farko. Da kafarshi ya taka yana kallon yanda garin kano yabi ya canza gabaki daya.

Wani waje yagani da ake siyar da simcard ya karasa ya siya dan bashida sim din Nigeria. Ya rigada ya karya shi tuntuni. Ya siya kati.

Sannan ya saka. Number din da lukman ya kirashi da ita jiya ya sake trying. A kunne take wannan karin. Ya lumshe idanuwa yana jin ringing din wayar.

Sake jin muryar lukman ya sa shi jin wani daci daci a zuciyarshi. Dana sanin bin abinda lukman ya bukata bayan duk sun guje shi.

"Hello....."

Lukman ya sake fadi a karo na biyu kamun fu.ad ya hadiye wani abu daya tsaya mishi a wuya yace.

"Bansan meya sani yin abinda kace ba. Ban kuma san dalilinka na nemana bayan duk shekarun nan ba. Buh' koma meye gani a nigeria...."

Da sauri lukman yace.

"Fu.ad? Da gaske kazo? Alhamdulillah"

"Hmm...."

Kawai fu.ad ya fadi yana sauraren lukman din kamun yaji ya dora da fadin.

"Kaje gidanka. Koma menene dalilin zaka gani"

Yamutsa fuska fu.ad yayi.

"Wanne gidana kuma?"

"Wanne gida kake da?"

A kufule yace.

"Lukman bana son rainin hankali kasani. Kawai kamin bayani yanda zan fahimta"

Shiru lukman yai. Fu.ad ya duba wayar yaga tana reading. Dan zatonshi ma ko network ya katse kiran.

"Kana jina fa lukman"

Cikin sanyin murya yace

"Wai ka gama masifar. Dan nafara dana sanin kiranka danai"

Dafe goshi fu.ad yai yana jin alamar ciwon kai ya fara mishi sallama.

"Dayake ma ban roki ka kirani ba. Duk tsahon shekarun nan saina fasa rayuwata da babu kiranku a ciki?"

Wani numfashi yani lukman ya sauke. Kamun yace.

"Allah yasa abinda zaka samu ya canza rayuwarka gabaki daya. Kaje gidanku kaida safiyya......!"

Kashe wayar lukman yayi. Gabaki daya fu.ad yaji jikinshi yayi wani sanyi. Jin sunanta a bakin lukman.

Gidansu shida safiyya. Sofinshi tana gidansu.......!
[7/5,

Please Login or Register in order to submit comment