Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jiki tace.

"Ka fara ko ta ina"

Numfashi ya sauke.

"Kin tuna nace miki ball nake ko?"

Ta daga mishi kai alamar ta tuna. Dan bata manta komai da yake fada nata game dashi ba.

"Tam kwanakin nan da kikaga nayi. Wani dan hutu ne na samu. Yanzun kuma zan koma"

Hannunta ta dora kan nashi dake fuskarta. Dan bataga abin kasa bayani a maganarshi ba. Tunda ya fara ta karanci damuwa a muryarshi.

"Allah yasa a koma lafiya ya kuma bada sa.a"

Yasan bata gane ba.

"Amin....."

Ya rasa ta yanda zai gaya mata. Shi kanshi harya soma kewarta tun kamun ya tafin. Muryarshi can kasa yace.

"Ba anan kasar ba. Tafiya zan jibi. Sai nan da sati shidda zan dawo......."

Mikewa zaune tayi ba shiri. Lokaci daya idanuwanta suka ciko da hawaye. Shima zaune ya mike yana fadin.

"Haba sofi. Zamuyi waya kullum zan kiraki. Kuma......."

Kuka tasa. Kuka sosai hawaye wani nabin wani. Tafiya zai yabarta har sati shidda. Kamo ta yai yana lallashi cikin kuka tace.

"Wa zai kaini makaranta?"

Kaman hakan kawai ya isa dalilin dazai sa ya fasa tafiya.

"Zan samo driver. Kuma zanma laurat magana kullum ta biyo ta nan a kaiku tare. A dauko ku tare"

Kukan ta ci gaba dayi taba girgiza masa kai alamar bata yarda ba. Sake riketa yai jikinshi yana jin yanda ta wani kankame shi.

"Bana so ka tafi"

Lumshe idanuwanshi yai. Shi kanshi da hawayen zasu zubo daya danji saukin abinda yake ji.

Kamo fuskarta yai. Daya bayan daya ya sumbaci idanuwanta. Da duk fuskarta. Hannu yasa ya goge mata hawayen.

Kallonta yake sosai. Kamun ya hada bakinshi da nata. Yanajin yanda ta rike jikinta kamun ta sake a hankali.

Saboda shine rana ta farko da bakinshi ya hadu da nata. Ya rasa yanda zai mata ne kawai. Sai da ya tabbatar bata da wani karfin kara mishi damuwa tukunna.

Janta yai kan kirjinshi ya kwantar da ita. A hankali cikin muryar da kunnenta ne kadai ke ji yake kwantar mata da hankali da kalamai masu taushi.

A haka yai musu addu.a yana lallabata har bacci ya dauke su.

*#TeamAS*
[7/5, 11:15 AM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[7/5, 11:16 AM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: AKAN SO 26
*πŸ’˜πŸ’–AKAN SOπŸ’–πŸ’˜*

~Written by~ :Luβπα SufyΞ±Ο€


26

*I don't know what is more sad. That i am in love with a fictional character or that i am in love with a fictional character who is the creation of my own imagination......*

Hannunta take kokarin kwacewa daga cikin na fu.ad amman gam ya riketa. Fuskarta cike da kunya tace mishi.

"Mama indo fa na kitchen"

Daga mata gira yai dake nuna cewar sai me? Shi bai damu ba. Dayan hannunta tasa ta cire nashi daga nata.

Wani shagwabe fuska yayi.

"Gobe warhaka saikin nemi hannuwana kin rasa sofi"

Da sauri ta kamo hannuwanshi duka biyun ta rike. Har ranta take jin tafiyar nan. Idanuwanta da suka ciko da hawaye ta sauke masa.

Da sauri yace.

"Yi hakuri. Na daina"

"Ina sane da tafiyar nan. Ba saika tunamun ba...."

Hannunshi ya zame daga nata ya kama kunnuwanshi duka biyun.

"Afuwan. Na daina amman kar hawayen nan ya zubo. Bana son ganinsu"

Murmushin karfin hali tai masa. Ta dai kasa cewa komai. Dan tanayin magana kuka zatai.

Dab da ita sosai ya karasa. Ya tallabi fuskarta cikin hannuwanshi yana kallon cikin idanuwanta.

"Ki kira laurat. Ba lesson yau"

Ware idanuwanta tayi cikin nashi tana son ce mishi bata yarda ba. Goshin shi ya hada da nata.

Kusan lips dinshi kan nata suke. Wani miyau da bata san da shi ba cikin bakinta ta hadiye.

Yana ganin yanda idanuwanta ke yawata wa kan fuskarshi. Hucin numfashinta na karuwa kan fuskarshi.

Kan labbanta yai magana da fadin.

"Yau ba lesson. Lokacina ne duk yau. Kinji?"

Kai ta daga masa gwiwarta nayin sanyi. Wata sumba mai taushi ya manna mata a lips sannan ya saki fuskarta.

Wannan karin shi yake maida numfashi yana kokarin maida yanayin dake son kwace masa ciki.

"Bara inyo alwala inje la.asar. ki shirya kamun in dawo mu fita"

"Nima barin yi sallar. Ina zamuje?"

Yatsun shi yai running kan fuskarta. Yana bin inda duk suka taba da kallo kamun yai kasa da idanuwanshi kan labbanta ya tsayar dasu nan.

"Sirri ne."

Idanshi ya mayar cikin nata ya dora da.

"You are gonna be dah' death of me sofi"

Fuskarta tadan daquna tana maimaita kalamanshi cikin kanta tana so ta gane ma.anarsu.

Wucewa yayi yabarta nan tsaye. Numfashi ta sauke wani sonshi na shigarta. Karasawa tai ta dauki wayarta kan kujera ta kira laurat.

Bayani tai mata cewar zasu fita da fu.ad insun dawo da wuri zata kirata.

Bedroom ta shiga. Sai da ta watso ruwa tukunna tai alwala ta fito tayi sallar la.asar.

Mai ta shafa. Ta murza hoda. Kallon fuskarta take a mudubi. Yanda tai wani haske tai bulbul. Kaman ba ita ba.

Mikewa tai kamun tunani ya haye mata. Ta dauko wata doguwar riga ta atamfa ta saka.

Dinki ya zauna mata. Simple ta daura dankwalinta ta ta dauko mayafi kalar kayan ta ajiye.

Sanda mamansu fu.ad ta aiko mata da kayayyakin kusan kowanne da mayafinshi da takalmi da jaka.

Kayan kadai tai amfani dasu. Tunda babu inda take zuwa. Koda take jajen mai kitso wa laurat catai ta kwance ta wanke zatai mata.

Haka kuwa akai. Banda makaranta. Ta kwana biyu bata je ko ina ba. Sallamar fu.ad taji yana turo kofar.

Ta amsa hadi da fadin.

"Sannu da dawowa"

Kallonta yake yi. A hankali ya taka zuwa inda take tsaye. Tun daga kafafuwanta ya soma yawo da idanuwanshi har fuskarta.

Wani numfashi yake ja yana fitarwa ta bakinshi.

"Kinyi kyau. Kinyi kyau sosai"

Murmushi tai mishi. Ta dauki mayafinta tana fadin.

"Muje ko?"

Fito da idanuwa yai yana wani tura baki gaba.

"Um um. Kinga kyan da kikai? Nima saina sake kaya"

Yanda yakanyi mata tai mishi. Tasa hannuwa ta tallabi fuskarshi tana daga kafafuwa saboda ya mata tsayi.

Dariya ya dinga yi mata. Hannunshi ya dora kan kugunta ya dan yi sama da ita.

Har mamakin yanda yake dagata takeyi. Ko numfashi bai mayar ba. Saikace dagata din wani abune mai sauki.

"uhum sofi....."

Yace yana kallonta. Makalo masa wuya tai ta na boye kanta cikin kafadarshi saboda kunyar da ta kamata.

Cikin kunne ta rada mishi.

"Kayi kyau sosai. Ko baka sake kaya ba"

Dariya yai yana sake gyarata a jikinshi. Muryarshi can kasa yace

"Indai kince na miki a haka. Zaka iya fita dani. Fine muje"

Kaji shi fa. Wai in zata iya fita dashi ma yake fadi.

"Kai baka ji kunyar jerawa da yar karkara ba.......wayyoo"

Ta karasa saboda cizon dayai mata gefen kafada. Sauketa yayi. Fuskarshi babu alamar wasa yace

"Waya fada miki bazan yi rigima da duk wanda ya rainamun ke ba? Ko da kuwa ke dince da kanki"

Kanta ta sadda kasa hadi da fadin.

"Na daina..."

Hannu yasa ya dago mata da haba.

"Kar in sake ji. Ke matar fu.ad ce. Kin wuce raini a ko ina"

Kai ta daga mishi. Fuskarshi yakai ya sumbace ta sannan yace.

"Good. Muje"

Mayafinta ta dauko tana maimaita yanda ya fadi 'good' cikin kanta. Saboda taji kalmar tafi a kirga a makaranta.

Amman yanayin yanda ya lankwasa ta ya mata dadi. Maimaitawa take tayi. Bakinta dake motsi ya ke kallo. Da mamaki yace

"Magana kike"

Da sauri ta girgiza masa kai tana yafa mayafinta.

"Sofi.....?"

Ya kirata yana jan sunan. Murmushi tai a kunyace sannan tace.

"Kalmar daka fada nake maimaitawa saboda tamun dadi"

Dariya yai kawai a ranshi yake fadin yama za.ai da duk lokuttan da suke wucewa son sofi bazai karu a zuciyarshi ba.

"She is fucking amazing"

****

Suna mota ya kira wayar anty fatima ya fada mata gasu nan hanyar gidanta. Shi kanshi ya manta rabonshinda gidan.

Zaima iya kirga zuwanshi gidan anty fatima. Kome zai siyo saida ya bama momma a aika mata dashi.

Saida sukai parking cikin gidan suka fito sannan safiyya tace mishi.

"Tsoro nake ji"

Dariya yai mata.

"Karki damu. Anty fatima bata da matsala"

Shiru tai tabi bayanshi. Da sallama suka shiga gidan. Aikam safiyya taga bata da matsala dan da fara.a ta tarbesu.

Taja safiyya suka zauna. Fu.ad ta kalla tace

"Ina nan ai kule dakai wallahi. Tunda momma ta fadamun shisa kaga ban kira ba"

Dariya fu.ad yayi. Hakuri take so ya bata bai kawo mata safiyya sun gaida ba. Ta kuma san saidai tagaji da mitarta dan ba samu zatayi ba.

Gaisawa sukai sosai da safiyya danma tanajin kunya. Ko lemo da soyayyen nama da meat pie din data kawo musu kasa ci tai.

Mikewa fu.ad yayi yaba fadin.
"Anty wucewa zamuyi"

Bude baki tai sannan tace.

"Kai fu.ad kasa Allah a ranka. Tun yanzun?"

Dariya ma ta bashi.

"Ba kun gaisa ba?"

Mikewa anty fatima tayi. Da ido ta nuna mishi alamar tana son magana dashi in private.

Dakuna fuska yayi. Bai dai musa mata ba yabi bayanta zuwa wani dan corridor.

Ba wani bata lokaci anty fatima tace.

"Bazan judging kome ya faru daku ba fu.ad saboda nasan kaddara kowa da tashi.

Allah kuma ya rigada ya rubuta taku tun kamun a haife ku"

Wani juya idanuwa fu.ad yai hadi da fadin.

"Sai nai kewar islamiya...."

Hararshi tayi dan tasan rainin wayau ne yasa shi fadar haka. Ganin tai shiru tana kallonshi ya sa shi fadin.

"Ina ji. Just cut it short"

"Hmm. Kawai ka rike ta amana. Dan Allah karkai mata butulci"

Hade hannyenshi yai waje daya kawai. Sannan ya juya ya wuce. Ya gaji da jin kalaman nan da kowa ke fada mishi.

Safiyya ya samu zaune inda suka barta yace mata.

"Taso mu tafi"

Mikewa tai. Anty fatima ta karaso tana fadin.

"Ku dan jira inzo"

Lumshe idanuwa fu.ad yai alamar jiran da zasuyi an takura shi.

Bata fi mintina sha biyar ba ta fito da leda a hannunta ta mikama safiyya hadi da fadin.

"Bansan zaku zo ba"

Hannu biyu tasa ta karba tai mata godiya sannan suka tafi. Suna shiga mota fu.ad yace

"Anty fatima tafi sonki dani. Bata taba bani komai ba"

Dariya ya bata.

"Ai mu biyu taba"

Turo baki yai yace.

"Oh-OH banji tace dani ba"

Ya tashi motar suna fita daga gidan. A hanya tace

"Nagode."

Da mamaki yace

"Godiyar me fa?"

"Yanda kake kokarin yan uwanka su karbeni"

Shiru yai dan baisan me zaice mata ba. Tsayawa sukai yai musu take away sannan suka wuce gida.

*

Yau a gida yaja musu sallar isha.i bayan sunci abinci sannan yace mata sannan ya kulle musu kofarsu ya dawo ya kama hannunta sukai bedroom.

Cayai mata ta watso ruwa. Zai wuce dakinshi ya watsa ruwa dan so yake su gama tare su kwanta.

Haka kuwa akai. Bata jima da fitowa ba ya shigo dakin. Kamshin turarukanshi na wani kashe mata jiki.

Kwanciya yai kan gadon ya kamota ya dago ya kwantar kan jikinshi ya lumshe idanuwanshi.

"Kewarki nake ji sosai sofi. Tun kamun in tafi nake jinta har raina"

Itama lumshe idanuwanta tayi tana sake kankame shi. A hankali zuciyarta ke hada mata kalaman yanayin da take ji kamun tace.

"Lokaci zai tsayamun in baka kusa. Komai zai canza. Bana tunanin zan gane hanya ni kadai a duniyarka baka tare dani"

Wani nauyi kirjin shi yai mishi. Yana jin yanda zuciyarta ke dokawa a jikinshi.

"Duniyata da taki iri dayace yanzun sofi. Bana tunanin nisa zai canza haka.

Bakyajin yanda bugun zuciyata ke tafiya dai dai da naki?"

Nutsuwa tai tana kokarin jin abinda take cewa. Hannunshi ta kamo ta dumtse.

"Bance nisa zai canza yanda bugun zuciyar mu yake ba. Sai dai zai canza yanayin komai a tare dani"

Jan numfashi yai. Inta ci gaba da magana haka bazai iya tafiya yabarta ba.

"Ki fadi sunana sofi. Sau daya na taba jinshi a labbanki. Ban manta yanayin shi ba. Ina son kari ne.

Inason tattara duk wani yanayi in tafi dashi ko zai rage mun kewarki"

Hawayen da take rikewa suka zubo. A hankali ta sumbaci wuyanshi saboda dai dai nan kanta ya tsaya.

Baisan lokacin da dan sauran control dinshi ya kwace ba. Sosai yake nuna mata yanda sonta ya gama zauna mishi.

Yanda zai kewarta. Jikinta ya shiga bari saboda bakuwa ce sosai a wannan salon soyayyar nashi.

Riketa yai. Cikin kunnuwanta yake gaya mata kalaman da sirri ne a tsakaninsu. Haka ya riketa a jikinshi yana saukar mata da nutsuwa.

Duk yanda yake ji bai danne rashin son tsorata ta ba. Yafi son yabi komai a hankali.

Kaman yanda zuciyarshi ke fada mishi. Bai samu lokaci a soyayyarta ba. Lokaci daya tai masa illa.

Shisa yai alkawarin bama nuna mata ita dukkan lokacin sa take bukata.

****

"Sofi da kin shirya nakai ki makaranta"

Girgiza masa kai tayi.

"Na hakura da zuwa yau. Ina son ganin tafiyarka"

Kyaleya yai. Tunda suka tashi yake fama da ita ta shirya yakaita makaranta takiya.

Ita a dole sai taga tafiyarshi ba zata makaranta ba. Tare sukai breakfast. Ya shiga ya sake yin wanka.

Lukman ya kira a waya. Dan driver din da aka samo musu sunyi sai gobe zai fara zuwa. Saboda haka shi zai sauke shi airport.

Tana zaune tana kallonshi yana ta kaikawo. Harya gama shirin shi tsaf. Kukan da take ta daurewa tun dazun ya kwace mata.

Lumshe idanuwanshi yayi. Sannan ya karasa wajenta ya rikota. Muryarshi dauke da wani yanayi yace.

"Nace bana son kukan nan. Kullum fa zamuyi waya. Ko so kike in tafi zuciyata da hoton fuskarki jike da hawaye?"

Girgiza mishi kai tayi. Hannu yasa yana goge mata fuska. Dakyar ta iya samu hawayen suka tsaya.

"Nace miki kome kike so ki kirani ko? Zansa lukman ya kawo miki. Kudi na nan inda na nuna miki.

Dan Allah banda yawan damuwa"

Muryarta a dakushe saboda kukan da tai tace masa.

"Duk na rike fa"

Dariya yadanyi. Wayarshi yaji tana ringing. Yasan lukman ne dakyar ya samu ya janyeta daga jikinshi yana daukar yar jakar shi.

Mikewa tai ta rike hannunshi tana bude wani sabon shafin kuka. Hugging dinta yayi. Gaba daya kalamanshi sun kare.

Shi kanshi bukatar lallashin yake. Sun jima a haka yana rike da ita tana kuka. Wayarshi data sake daukar ihu ya sa shi dago safiyya daga jikinshi.

Fuskarta ya rike. Sumba yake manna mata ko ta ina a fuskarta batare daya damu da hawayen dake jike a jiki ba.

Yau martani take mayar mishi saboda yanda take jin kaman ta bishi. Dakyar ta iya raka shi bakin kofa.

Kissing dinta ya sake yi.

"I love you. I more than alot love you sofi"

Saboda yana tunanin abinda yake ji a zufiyarta yai kadan a dora shi kan kalma uku kacal.

"I love you fu.ad"

Wabi kumburi yaji zuciyarshi tayi ta cika mishi kirji saboda wani sonta daya karu a lokacin.

"Ki kulamin da kanki sosai"

Kai ta daga mishi bata son kuka ya sake kwace mata. Tsaye tai harya fice. Da sauri ta koma wajen window ta bude tana kallon shi.

Hawaye nabi mata fuska. Har duniyar shi ta zame mata bakuwa ko nisa baiba tsaye tai a wajen har ya shiga motar suka fice.

Jikin window din ta hade kanta tana wani irin kuka. Bama taji zuwan mama indo ba sai da ta dafa ta.

Juyawa tayi. Wani sabon kukan na zuwa mata. Kamata mama indo tayi ta kaita daki tana lallashinta.

Wayarta taji ta dauki ihu. Ta lalubo taga shine ya kira. Mikewa tai zaune tana goge fuska kamun ta dauki wayar.

Hakan yasa mama indo bar mata dakin. Murya a dakushe tai masa sallama. Tanajin yanda ya sauke ajiyar zuciya kamun yace

"Sofi kuka kika sake yi ko?"

Duk yanda take ji bai hanata murmushi ba.

"Tun dazunne....."

"Hmm yan zun lukman ya sauke ni airport. Saida na biya naima momma sallama tukunna"

A sanyaye tace

"Aikam ka kyauta. Gidan yayi shiru baka nan"

Ya amsa da

"Kinga da kinje makaranta zai rage miki kewa"

Girgiza kai tayi kaman yana ganinta.

"Ganinka anan kusa dani ne kawai zai ragemun kewarka"

Hira sukai na dan wani lokaci kamun yai mata sallama da alkawarin zai kira daya isa.

Sosai tai mishi addu.ar da bata samu ta mishi ba dazun.

Da kewar shi takai makaranta. Duk da sunyi waya da safiyar amman jinta take kamar marar lafiya.

Dan dakyar ta iya bacci jiya. Sai da taci kuka ta more. Da safe ma data bude ido taga baya nan sai da tai wani.

Anty laurat office tayi abinta. Safiya kuma ta shiga aji kasancewar talata ne ba assembly suke ba. Da fara.a wasu daga ciki mazan ajin suka gaisa da safiyya.

Ta karasa ta zauna wajen zamanta. Sosai khadija da aisha sukaji dadin ganinta.

"Anty safiyya Allah dai yasa lafiya. Munyi jaje jiya mungaji. Ga wani rashin dabara bamu taba tunanin karbar number dinki ba"

Cewar khadija. Aisha ta karba mata da.

"Wallahi kuwa. Allah dai yasa lafiya"

Safiyya taji dadin karamcinsu. Sai take jin sun rage mata kewar su jummai. Duk da girman jikinsu zaizo daya da su khadija. Dan Aisha na tafita tsayi tasan ta girme su.

Antyn nan tun tana hanasu harta hakura.

"Maigida na ne ya koma wajen aiki. Kuma bana dan jin dadi"

Dariya aisha tayi.

"Umm su anty an samo mana baby"

Wata kunya ta kama safiyya. Da sauri ta girgiza musu kai.

"Nikam dai ba wani baby"

Khadija tace

"Mukam munji dadi ko aisha? Zamu sha suna wallahi. Har anko sai munyi"

Gani tai da gaske suke yi. Da sauri tace.

"Kai ni bama mu taba....."

Shiru tai saurin yi. Ta kasa karasawa. Lokaci daya kunya da tuna girman rike sirrin aure da suka tabayi a islamiyya ya zo mata.

Su khajida da sun gama gane inda ta dosa kallonta suke kaman maganar datai itace mafi girma da ban mamaki da suka ji duk shekarar.

Da wani yanayi khadija tace.

"Tafdi. Anty kina so wata ta kwace miki miji ko?"

Wani rass safiyya taji gabanta ya fadi. Ita sam bata taba wannan tunanin ba. Aisha ta jinjina kai.

"Sosai ma kuwa. Gashi so hot"

Duka khadija takai mata. Tai saurin cewa.

"Ke bakya karantawa a litattafan hausa?"

"Wallahi kuwa. Ji cikin NI DA DIYATA na anty ayna yanda yasmeena ta kwace ma deela miji"

Cewar khadija. Kaman safiyya zatai kuka take kallonsu. Muryarta a sanyaye tace.

"Ni ban taba karantawa ba. Ina ake samu...."

Da mamaki khadija tace.

"Baki na da waya ba?"

Ta daga musu kai.

"Kin zo da ita?"

Girgiza kai tai wannan karin ma. Dan maganar a kwace mata fu.ad. Hango fu.ad nama wata murmushi ma balke magana kawai yasa kirjinta na wani zafi.

Akwai ma abubuwa da yawa da take son koya. Bata iya kalar abincin shi ko daya ba. A rauna ne tace musu.

"Ina son in iya kalar abubuwan da yake ci ma. Ban iya dafa ko daya ba"

Dafata khadija tayi. Hadi da fadin.

"Karki damu zamu koya miki. Gobe in Allah ya kaimu kizo da wayarki da kudi a siya kati.

Zamu bude miki whatsapp mu koya miki amfani dashi. Zaki karu sosai wallahi.

In shaa Allah weekend din nan zanzo gidansu aisha saiki bamu address dinki muzo gidanki mu yini duk mu koya miki wasu girki"

Kallonsu take ta rasa bakin da zatai musu godiya ma.

"Allah ya biyaku da kalar karamcin da kuke nunamun"

Dariya ta basu suka amsa da amin.

****

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiyarma safiyya. Da duk rana kewar fu.ad na karuwa a zuciyarta.

Sai dai a hankali su khadija ke wayar mata dakai. Kaman yanda sukai alkawari haka suka zo gidanta suka yini ranar.

Sosai take karuwa dasu. Littafi ta samu suke rubuta mata girgike girke ga groups na girki da suka sakata.

Duk da bata iya cewa komai saboda yanda typing ke mata wahala da qwerty din nan. Tana budewa tabi tana karantawa kuma tana karuwa.

Ga litattafan hausa da take samu. Suna ma rage mata kewa da daddare. Taita shan karatu.

Mama indo na taimakawa wajen kara koya mata wasu girkin. Haka in taga wani a waya ta cire kunya ta nuna ma anty laurat.

Yanzun lesson din awa daya suke sauran awa dayar a kitchen suke yinta tana koya mata girki.

*

Kwanci tashi har satin dawowar fu.ad yayi. Safiyya ta kagu ya dawo ta tarbe shi da sababbin abubuwan data koya sabo dashi.

Pha.iza tazo dubata yafi a kirga. Haka lukman duk da baya shigowa sai dai ya tsaya a harabar gidan tasa hijab ta fita su gaisa.

Indai zaizo saiya kawo mata abubuwa. Wani lokacin harda kaji ko biscuit da chocolates kala kala.

Wannan kenan.
[7/5, 11:16 AM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[7/5, 11:18 AM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: AKAN SO 27
*πŸ’˜πŸ’–AKAN SOπŸ’–πŸ’˜*

~Written by~ :Luβπα SufyΞ±Ο€


27

Kallon kanta take a mudubi. Wannan ne kaya na biyar data saka tana cirewa. Yanzun riga da skirt ne na atamfa brown.

Ya karbeta sosai. Ba wata kwalliya a fuskarta banda jagirar datai. A sati dayan nan da khadija ta koya mata jagira ta zama kwararriya.

Kaman ba ita ba. Ga hannunta ya sha kunshi. Har gida su khadija suka kawo mai kunshi jiya tai nata jan lalle da baki. A hannuwa da kafa.

Murmushi take ita kadai. Ba karamar kewar fu.ad take ba. Ji take yaki sauri ya karaso.

Sai kamshin turaruka take. Musamman humrar da anty fatima ta bata. Inta shafa saita wuni da ita a jiki.

Falo ta fita ta sake duba dining. Komai a shirye yake. Mama indo ta tayata gamawa tun dazun ta koma nata bangaren.

Window ta leqa ko zata ga ta inda zai bullo. Ta gaji da tsayuwa a wajen ta koma bedroom.

Sam ta kasa zama waje daya. Sai yawo take cikin gida. Dakin shi ta shiga da ta feshe da turaruka.

Ta zauna kan gadon. Ta lumshe idanuwanta ta bude su. Ta kagu yazo yaga yanda duniyar shi ta canza ta.

"Sofi........."

Muryarshi taji da sauri t bude idanuwanta. Baya cikin dakin. Zuciyarta na son fita daga kirjinta tabi inda taji kiranshi da yanda take doka mata.

"Sofi........."

Ta sake ji. Bata san sanda kafafunta sukai hanyar fita dakin ba. Tsakiyar falo taganshi tsaye hannunshi rike da akwati.

Sai jaka rataye a hannunshi. Tun daga takalmin kafarshi ja ta soma kallo zuwa crazy jeans din dake jikinshi blue. Sai hoodie din da yake sanye ita fara da ja.

Sannan ta tsaya kan fuskarshi. Hannuwanshi ya bude mata yana tarbarta da wani murmushi daya sa zuciyarta ci gaba da kokarin fita daga kirjinta ta same shi.

Kafafuwanta har sarkewa suke kamun ta karasa inda yake. Taimaka mata yai ta hanyar kamo hannayenta.

Su ya fara kaiwa bakinshi yana kissing babu kakkautawa. Ji yake kaman ya hadiyeta ya ciccike ramukan missing dinta dayai sannan ya fito da ita ya kare mata kallo.

Lumshe idanuwa tai tana jin dumin hannayenta cikin nashi. Labbanshi kan hannuwanta.

Sai taji kaman wani abu ya dan matsa cikin zuciyarta da batasan ba dai dai yake ba sai yanzun.

Dagowa yai ya kalli fuskarta. Wani abu ya fadi can kasan makoshi da ta kasa gane wanne yare ne. Kamun ya jata jikinshi yai hugging.

Tana jin yanda ya sauke wata ajiyar zuciya. Hannuwanta tasa a bayanshi tana kankame shi.

Cikin kunnenshi take fadin.

"Sannu da zuwa. Nayi kewarka sosai"

Kissin gefen fuskarta yayi kamun yace

"Ba sosai ba tunda kina iya dorawa akan kalamai"

Murmushi tayi. So take ta sake kallon fuskarshi amman zuciyarta na mata ihu saboda tunanin rabata da jikin fu.ad data keyi.

A hankali ya kamota yana dawo da ita zuwa ga dubanshi. Idanuwanshi ke yawo kan fuskarta.

Sai kace ba sofin shi daya tafi ya bari ba. Ta kara wani kyau. Sai yaga kaman yankan idanuwanta sun kara girma da wani haske.

Sumba ya manna mata a kowanne ido. Muryarshi can kasa yace.

"Kinyi kyau sosai"

Itama tashi fuskar take kallo. Akwai abinda ya canza mata. Gashin kanshi take kallo. Haba tasan ya canza ko yaya ne.

Maimakon askin data saba ganin shi dashi wannan karon suma ce cike da kan ko ina. Irin old school din nan.

Hannunshi ta kamo taba fadin.

"Muje kayi wanka"

Jakar dake rataye a hannunshi ya sauke tsakiyar falon. Ya dago da hannunta. Dayan ya kamo yana kallon su.

"Banson ina son kunshi ba saida na fara ganin hannuwanki dashi"

Murmushin nan da yake bala.in so tayina kunyace. Juya idanuwanshi yayi. Sofi na karasa kashe mishi zuciya ba kadan ba.

Ta gefe ya zagaya hannunshi ya tsayar dashi kan kugunta suka yi dakinshi a haka. Yana turawa wani kamshi mai sanyi ya daki hancinshi.

Kallonta yadanyi. Yai murmushi kawai saboda bai da abinda zaice. Gefen gadonshi ta zauna ya dauki towel ya shiga wanka.

Tuna abinda ta karanta tayi. Da sauri ta mike ta bude wardrobe dinshi. Rasa kayan da zata dauko mishi tayi.

Irin wandon jikinshi tagani baki. Ta dauko masa sai wata porlo fara kal ta ajiye masa kan gado.

Turaruka ta dauko ta feshe kayan dasu sannan ta samu waje ta zauna. Har yanzun zuciyarta ta kasa tsayawa waje daya.

Tana nan zaune ya fito daure sa towel da singlet. Lokaci daya bugun zuciyarta ya karu. Ga wata kunya data lillibeta.

Daurewa tayi ta dauki cream din data ajiye a gefe ta karasa inda yake kanta a kasa. Dora shi tai kan tafin hannunta ta mika mishi kanta na kasa.

Murmushi yake tunda ta taso saboda banda kafafuwanshi babu inda idanuwanta ke iya kaiwa. Hannunta da man ya hada ya rike ya jata jikinshi.

Yai wani kasa da murya kamun yace.

"Ba tayani zakiyi ba?"

Hakan ne niyyarta amman sai taji kunya duk ta rufeta. Kai ta daga mishi. Man ya saka cikin hannunta ya jata.

Sam

Please Login or Register in order to submit comment