Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amsa tambayoyin nan. Itama a wahalcen take saurarenta.

"Bako da yaushe ba"

Daga kai nana tayi alamar ta fahimta

"Thank you anty jana. You are the best doc"

"Hmm"

Kawai ta iya fadi kamun nana ta kashe wayar. Lumshe idanuwanta tayi kamun ta tashi ta fice daga falon zuwa harabar gidan.

Hango su fu.ad tayi suna zazzaune su dukansu suna hira. Babban yayane kawai baya wajen.

Ko takalmi babu a kafarta ta ruga da gudu. Kaman ance fu.ad ya dago idanuwa ya kuwa sauke su kan nana.

Ita take gudun shi zuciyarshi ke dokawa karta fadi. Da alama ganin yanda gaba daya hankalin fu.ad ya bar kansu yasa gaba dayansu suka maida kallonsu inda na fu.ad din yake.

Tana karasowa jikin fu.ad ta fada ta kankame shi. Riketa yai yaba shushing dinta da alamar lallashi duk da baisan abinda ya sameta ba ji yake har zuciyarshi.

Ko ina na jikinta kyarma yake. Yanajin yanda hawayenta ke jika mishi riga. Ya sake riketa yana rocking dinsu hadi da lumshe idanuwanshi.

"It is ok princess. Ina tare dake. Fadamun menene?"

Su haneef kallonsu suke. Gaba daya yanayin su yasa jikin kowa a wajen yayi sanyi. Dago Nana fu.ad yayi daga jikinshi yana sa hannuwa ya tallabi fuskarta.

Cikin idanuwa ya kalleta yana son taga yanda yake jin zai iya bata komai in yana da halin hakan.

"Talk to me. Menene?"

Muryarta na rawa tace.

"Bana so kuje dady. Bana so kuje asibiti gobe. Bana son transplant din"

Wani irin dokawa zuciyar fu.ad tayi wannan karin shi jikinshi ke kyarma. Girgiza mata kai yake

"No..... No nana. Ba zaki barmu ba kina jina. Za.a samu match in shaa Allah"

Hannunta tasa ta ture nashi daga fuskarta. Kallonshi take da wani irin yanayi dake nuna cewar bazai fahimta ba. Bazai taba fahimtarta ba.

Baya son kallon da take mishi. Baya son ganin irin wannan kallon a fuskar yarinya kamarta. Hannu yakai zai kamo nata ta ture shi tana matsawa.

"Bana so dady. Da gaske nake karku je bana so"

Gabaki daya ta birkita mishi duniyar cikin yan mintina.

"Nana calm down muyi magana."

Da ihu tace.

"Nooooo!"

Haneef ya kalla da yanayin neman taimako. Girgiza mishi kai yayi dan baisan me zai ba. Ya maida kallonshi kan lukman. Baima wani tsaya ba dan yasan lukman yafi shi rauni.

Kasa Nana take kallo kaman zata iya samun wata mafita daga yin hakan. Muryarta can kasa tace.

"I am sorry dady. Kai kadai zaka fadama mumy karta daga burinta kaman yanda take fadamun.

Bazanyi ba. Bana so kowa yaje"

Fu.ad ji yake kaman zuciyarshi tabar kirjinshi yadan huta na wani lokaci. Ya bude baki zai magana Nana ta matsa kusa dashi.

Kamo hannunshi tayi.

"Dady ko anyi ba warkewa zanyi ba. Zai karama kwanakin mutuwata nisa ne.

Zai karamun wahala fiye da wannan. Ba zaku gane me nake ji ba dady. Komai ciwo yakemun........"

Zafi yakeji a wajaje na jikinshi da bazai iya fada ba. Hannunta takai tana zame hijab din jikinta.

"Kalli dady. Gashina bazai kara fitowa ba. Kowa na zuwa school ni bana zuwa yanzun.

Na daina jin taste din wasu abincin a bakina. Dady please bana son zama sick duka rayuwata.

I want to die. I want all of it to stop in huta. Dady komai ciwo yakemun dan Allah kar kumin abin nan. Kubarni in huta dady"

Ta karasa maganar hawaye na zubo mata. Mikewa lukman yayi yana barin wajen saboda yanda yake jin hawaye na shirin zubo mishi. Hassan ma barin wajen yayi.

Janta jikinshi fu.ad yayi yana rungumeta. Haneef kam dafe kanshi yai cikin hannayenshi yaba fitar da numfashi da matukar wahala.

Cak fu.ad ya daga nana jikinshi ya mike tsaye har ranshi yanajin shekarun daya rasa tare da ita. Da wani irin yanayi ya nufi cikin gidan.

Ko sallama baiba ya shiga falon. Ya wuce su pha.iza dake tsaye suna magana ita da anty fati.

Baya ganin kowa sai safiyya. Ita yake hangowa zaune. Ita kadai idanuwanshi ke gani. Zuwa yanzun hankalin kowa ya koma kanshi.

Yana karasawa inda safiyya take ya sauke mata Nana kan cinyarta. Dan dafe kanshi da hannu daya yayi yana sauke shi cike da frustration.

Kallon safiyya yake. Muryarshi a dakushe yace.

"Ki kalleta sofi. Bata son transplant ko da an samu match. Ta hakura da rayuwa saboda ta mata wahala."

Ware idanuwa safiyya tana rungume Nana jikinta hadi da sumbatarta. Ji yake kaman kanshi zai tarwatse.

Ta samu wannan na shekaru sha daya.

"Kina da wannan na shekara sha daya sofi. Bani da komai dazan rike and fuck it! She is dying!"

Kuka safiyya take. Ita fu.ad yake dorama laifin shekarun daya rasa tare da nana.

"Kai ka tafi. Kuma na nemo ka ban sameka ba......"

Ta fadi hawaye na sake zubo mata. Anty fatima ce ta karaso ta daga fu.ad a kafada ya ture hannunta.

"Ba wani. Na rasa yarinyata saboda ke! Na rasa ganinta da lafiyarta. Na rasa kaita makaranta. Na rasa best moments tare da ita"

Goge fuska safiyya tayi tai murmushin takaici hadi da fadin.

"Tabbas duk ka rasa wannan. Tare dashi ka rasa ganinta lokacin da batada lafiya. Ka rasa ganin lokacin da she was so sick bata ko iya tashi daga gadon ta.

Ka rasa ganin lokacin da gashinta ke kakkabewa daga kanta. Ka rasa ganin lokacin da take tisa uniform dinta na islamiyya dana boko tana kallonsu saboda ita ba zata iya zuwa ba.

Ka godema Allah daya sa baka ga duk wannan lokuttan ba fu.ad saboda su kadai sun ishi zuciyarka ciwo har karshen rayuwarka"

Tana karasa magana tasa fuskarta cikin hannunta tana fashewa da wani irin kuka. Zainab ma dake kusa da ita kukan take ballin anty fatima sarkin kuka.

Saukowa daga jikin safiyya nana tayi. Ta zo dai dai wajen fu.ad ta tsaya. Muryarta can kasa tace.

"Stop it dady. Ka daina ba laifinta bane ba. Ba laifinta bane da nake da cancer. Baka ga nima na rasa duk abin nan da dady na ba? Da lafiyata?

Karka sake mata fada bana so. Tamun komai"

Bude bakinshi fu.ad yayi yana fitar da iska saboda ta mishi wahalar fita ta hanci. Yanayin da yake ji babu wanda zai fahimta. Yanajin gabaki daya babu wanda yakaishi son kai da rashin adalci.

In akwai wanda zaiji ba a kyauta mishi ba Nana ce. Ita ce da ciwon a jikinta.

Yasa matan daya fi so bayan momma kuka hankalinshi ya kwanta. Bude baki yai zaiyi magana nana ta juya wajen safiyya tace.

"Gaskiya dady ya fadi mumy. Zaki iya fiye da kokarin da kikai wajen nemo shi"

Kai safiyya ta daga mata. Itama tasan da hakan data kira shi bata same shi ba zata iya zuwa gidansu a nemo shi bawai ta hakura ba.

Saboda Nana din badan ita ba. Takowanne fanni Nana akaima rashin adalci.

Takawa Nana tayi ta karasa inda momma ke tsaye tana zubda kwalla. Kamo hannunta tayi.

"Ki kaini in kwanta bacci nakeji"

Goge fuskarta momma tayi ta kama hannun nana suka wuce bangarenta. A hankali fu.ad ya taka zuwa inda safiyya take zaune. Tsugunnawa yayi.

Hakan yasa zainab dafa kujerar ta mike dakyar saboda cikinta ya shiga wata na bakwai kenan. Hawayen dake fuskarta ta goge. Da kai ta nunama su anty binta dasu bar musu falon.

Su dukansu bangaren momma suka wuce suna barin fu.ad da sofi. Kamo hannuwanta fu.ad yayi.

Wani irin abu taji har tsakiyar kanta. Shekaru sha biyu rabonta da fu.ad sai yanzun da ya tabata tasan babu abinda ya canza.

Dago fuska yai ya kalleta kamun hawaye su zubo mishi. Baisan me zaice mata ba. Kalamai duk sun tsaya mishi. Ta karance shi tsaf.

Su dukansu suna cikin yanayi marar misaltuwa. Hannunta ta zame daga nashi ta na tallabar fuskarshi. Hawayen take goge mishi tana girgiza kanta duk data kasa tsayar da nata.

Matsawa ya karayi ya dora kanshi kan cinyarta hawaye na sake zubo mishi.

"Ki yafemun safiyya. Bana nufin dukkan abinda na fada dan Allah ki yafemun"

Kanta ta dora kan nashi dake cinyarta.

"Na yafe maka fu.ad. Ka yafemun daban trying sosai ba"

Sake makalewa yai a jikinta yanajin yanda yai rashinta sosai. Kuka suke tare na shekarun da suka rasa. Na yanda kaddara ke gara su..........!

*#TeamAS*
[7/17, 6:46 PM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[7/17, 7:15 PM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: AKAN SO 45
*πŸ’˜πŸ’–AKAN SOπŸ’–πŸ’˜*

~Written by~ :Luβπα SufyΞ±Ο€



Wattpad: LubnaSufyan

45

*Please ku kara hakuri dani. 5 more chapters to go in shaa Allah. Ina godiya da kaunarku*

*Hussaina ubandiya kaunarki a gareni ba zata fadu ba. Ban kuma da bakin dazan miki godiya. ILYTDMAB*

*Mum bilki Allah ya shirya miki zuri.a Allah ya baki abinda kike nema duniya da lahira*

*TASKAR NOVELS this page is for you guys. #AnaTare*

Fu.ad yakai su gida da kanshi. Nana ma bacci take dan haka ya sabeta a kafada yakaita har dakin sofi ya kwantar da ita.

Yana fitowa ya samu sofi tsaye bakin kofar. Idanuwanshi yake yawatawa kan fuskarta ba tare da yasan abinda yake son gani akai ba.

Kallon nata na nutsar dashi ta fanno ni da yake kasa fahimta. Da duk wani abu dake jikinshi yake son sake jin duminta ko na minti biyu ne.

Baya son takura ta. Yarda da aurenshi datai bayan tasan bashida abinda zai bata kadai ya ishe shi. Beside zuciyarshi ciwo take kaman me.

Lumshe idanuwanshi yai yana fitar da wani numfashi mai nauyi kamun yace mata.

"Zanyi tafiya gobe in shaa Allah. Zan dawo may be zuwa next week ko kamun...... "

Yana bude bakinshi ya fara magana taji zuciyarta na wani irin dokawa cile da tsoro. Zai sake tafiya zai sake barinsu.

Yanzun kam sam zuciyarta ba zata iya daukar wani rashin nashi ba. Katse shi tai da fadin.

"Karka tafi......."

Idanuwanta ta sauke cikin nashi ta tabbata yaga tsoro da shakkun da ke cikinsu. Kasa hakuri yai da sauri ya taka ya hade space din dake tsakaninsu.

Hannu yasa ya tallabi fuskarta yana jin jikinshi ya dauki wani irin dumi. Sosai ya kalleta.

"Zan kare komai ne sofi. Zan dawo gabaki daya. Ki yarda dani karshen abinda zuciyata zatayi shine nisanta dake"

Hawayen da ke rike cikin idanuwanta suka zubo. Muryarta a sarke tace mishi.

"Usman ya rasu......"

Kallonta yake da mamaki yana juya maganarta cikin kanshi yana tunanin inda ya taba jin sunan da alakar sunan da ita.

Lokaci daya ya tuna. Ware idanuwanshi yai kamun yace.

"Allahu Akbar. Sofi. O. M. G. Sofiiii"

Ya rasa me ya kamata yace mata. Langabe kanta dake cikin hannuwanshi tai gefe cikin wani irin sanyin murya tace.

"Nagode....."

Ji yake kaman ya dauke mata ciwon daya san take ji. Ciwon da har yanzun baisan asalin dacin shi ba sai dai ya kamanta. Rikota yai jikinshi yana hugging din.

Tsam tai a jikinshi tanajin sanannen yanayin da ke tattare da hakan datayi tunanin ya bace mata. Hannuwanta ta zagaya tana sake rike shi.

Kadan kadan take ji yana hura mata wajajen dake mata zafi batare da wata iska na fita daga bakinshi ba. Sunkai mintina biyar a haka.

Kamun tadan zame jikinta ta dago tana ware idanuwanta a kanshi

"Ka kwana tare damu yau"

A tausa she yake kallonta.

"You don't have to........ Bana son takura ku sofi. Zamu iya bin komai a hankali"

Girgiza mishi kai tayi

"Nana zata so hakan. Indai zaka kwana batare daka zaci wani abu da ya wuce hakan ba banda matsala"

Kai ya daga mata. Ya fahimci komai.

"Zanje gida sai in dawo. Ki kula dake da Nana"

Kai ta daga mishi kawai tana jinta daban ta wajaje da dama. Yanayin ba bako bane a wajenta amman ya mata wani iri.

Sai daya sumbaci kumatunta yanajin son yin fiye da hakan ya danne sannan ya juya ya nufi kofar yana ficewa.

Sauke numfashi safiyya tayi ta wuce cikin daki inda Nana take.

*

A gida yaci abinci da sallar isha. Yai sallama da kowa dan bayajin zai biya da safe sannan ya wuce daga can zai tafi.

Komai da yake bukata ya dauka yasa a mota ya wuce gidansu safiyya. Yana shiga nana ta rugo da gudu ta rike mishi kafafuwa.

Dago ta yai zuwa jikinshi.

"Princess bakiyi bacci ba"

Girgiza mishi kai tayi tana dakuna fuska.

"Mumy tacemun zaka kwana anan. Shine nake ta jiranka"

Murmushi yayi yana cire takalman kafarshi kamun ya karasa da ita tsakiyar falon. Idanuwanshi ya sauke kan safiyya da take sanye da doguwar riga ta farar shadda.

Ta mishi kyau ba kadan ba.

"Sannu da gida"

Yace mata yana zama gefe gare da nana daya zaunar kan cinyarshi.

"Yasu momma?"

Safiyya ta bukata.

"Suna lafiya suna gaisheki"

Kamun ta amsa shi Nana tace

"Dady zaka tafi gobe?"

Ya jinjina kai alamar eh. Yana dorawa da fadin.

"Da wahala inyi sati daya. Idan na dawo shikenan bazan sake komawa ba"

Dariya nana tayi alamar taji dadin hakan kamun kuma ta dakuna fuska.

"Zanyi missing dinka kuma"

Shima dan dakuna fuska yayi. Badan yana tunanin safiyya ba da ya fasa tafiya gobe yai booking musu waje ya tafi da Nana.

"Ko zaku rakani?"

Nana ya tambaya amman idanuwanshi nakan safiyya. Murmushi kawai tayi.

"Nikam bana son jirgi fa. Bazani ba dady"

Ware idanuwa fu.ad yai dake tambayar da safiyya ko da gaske Nana take. Kai tadan daga mishi.

Dariya yayi.

"Da gaske? Me yasa?"

Dan daga mishi kai tayi.

"Kawai tunanin hawa ina ciki can sama. Owww a daina maganar jirgi please"

Dan ja mata hanci yayi yana dariya.

"An daina princess"

Hira suke a hankali tana jikinshi safiyya kam kallonsu take shi kadai
ya isheta nishadi.

Har nana tayi bacci a jikinshi dan magungunan data sha ma sun isa daukarta. Safiyya ya kalla. Sannan ya mike da Nana.

Bayanshi tabi. Ya kwantar da nana kan gado. Yana gyara mata kwanciya ta juya ta rike mishi hannu gam. Kokarin zamewa yake amman yanayin rikon da tai mishi in ya motsa ta sosai zata iya tashi.

Zama yai kan gadon yana jan kafafuwanshi a hankali ya kwanta gefenta. Safiyya ya kalla.

"Bana so in tashe ta"

Kai ta daga mishi. Ta zagaya dayan gefen Nana ta zauna tana jingina bayanta da gadon ta lumshe idanuwa.

Badan fu.ad din ba da sun manta da sunyi bacci. Dan Nana ta koya mata bacci da wuri sai dai ko in sun zauna kallo ne.

Kwanciya ta gyara idanuwanta a rufe tana fadin.

"Bacci nake ji fa"

Dariya ta bashi.

"Ina ne dakina?"

Ya tambaya shiru yaji ya sake fadin.

"Sofi"

"Umm"

"Ina zan kwanta"

Da alamar bacci da takura a muryarta tace.

"A kwance kake fa. Ni ka barni bacci nake ji"

Murmushi yai.

"Good night to"

"Oww ka daina magana"

Dariya yayi. Yanajin ta sauke ajiyar zuciya tana kara gyara kwanciya. Hannunta daya ta dora kan Nana da alamun ta saba da hakan.

Nana najin hannun safiyya kanta ta saki na fu.ad ta juya kwanciya tana kara matsawa jikin safiyya din. Kallonsu yai yana jin daban.

Kaunarsu mai girma ce. Bond din dake tsakanin su bazai taba kamo shi ba. Matsawa yai kusa da Nana ya zagaya da hannunshi ya riko su ita da safiyya yana sauke wani numfashi.

Addu.a yai musu su dukansu ya tofa musu kamun ya lumshe idanuwanshi cike da kaunarsu.

****

*BAYAN SATI DAYA*

Kallonta yake. Tana sanye da material blue mai haske da mayafi dark blue hakama takalman kafarta.

A hankali ta tako zuwa inda yake ta hura mishi iska cikin idanuwanshi. Ya dago hannunshi kaman maison kare iskar yana dariya.

"Kaman baka taba ganina ba?"

Ta fadi tana dariya.

"Anya jana zamu fita kuwa? Kinyi kyau bana so kowa ya kalle ki"

Daga mishi gira tai da fadin.

"Eyen? Nikam ka wuce mu tafi"

Bata fuska yai yana kallonta. Da gaske har ranshi yana kishin wani yaganta haka. Janyota yai jikinshi tana ture shi ya hada bakinsu.

Sun dauki lokaci a haka kamun ya sake ta yana maida numfashi.

"Honey j mana. Ka gogemun jan baki"

Murmushi yayi.

"Bana son kowa ya kalleki dashi a bakinki. In nace ki goge batamun lokaci zakiyi"

"Shine zaka shanye?"

"Yafimun sauki ai. Muje"

Batai musu ba tasa hannunta cikin nashi suka fice tare. Shiya bude mata mota ta shiga sannan ya zagaya.

Suna hanya ne yace mata.

"Kayan lefe fa zamu siyo"

Shiru tadanyi kamun cikin sanyin murya tace mishi.

"Ina zamuje?"

"Ban sani ba fa. Shisa na taho dake"

"Mu shiga kantin kwari kawai. Akwai inda nake siyayyar kaya sai mu duba idan sun maka"

Dan jim yayi sannan yace.

"Hakan ma yayi"

*

Aikam hakan sukayi. Sosai jana ta ture kishin da take ji gefe ta taya jabir suka zabi kyayyaki daga kan atamfofi zuwa lesses zuwa shaddoji dai dai karfin shi.

Shagwabe mata yai yagaji zasu dawo su karasa wani lokacin. Dan haka suka juyo suka dawo gida. Wanka ya shiga. Jana kam tayo alwala tai sallar la.asar sannan.

Yana fitowa itama wankan ta shiga. Yana kwance kan gado sanda ta fito. Ta kalle shi ya wani tabare fuska.

"Nagaji fa"

"Tabara kawai kakeji. Ba yawo mukai ba waje daya ne muka tsaya"

"Nikam sauran ke zaki karasa please"

Girgiza mishi kai tayi

"Zan dai rakaka in kana so"

Baice komai ba. Baya son kure hakurin da take yi. Hakanma ya gode. Hannuwanshi ya bude.

"Zo muyi magana"

Ba musu ta karasa ta zauna gefen gadon. Kama hannunta yai ya kwantar da ita. Gidan yayi shiru kasancewar yaran suna gidan hajiya weekend.

Juyawa yai suka fuskanci juna. Ya kama hannunta ya sumbata kamun yace.

"Please i need you to be honest with me. Ki fadamun ra.ayinki kan wannan. Ni na baki zabi"

Kai ta daga mishi dake nuna zatayi yanda yace kamun ya dora da fadin.

"Yawwa. Kinga bangarena ba amfani nake dashi ba. Kusan komai anan nakeyi. In bakida matsala ayna zata zauna anan.

If kina da matsala da hakan zata zauna a gidana na dakata"

Shiru tayi tana nazarin maganarshi kamun tace.

"Zan amsaka. Me kake so a ranka kai?"

Ganin alamar gardama zai mata yasa ta fadin.

"Please ka amsani. Ina son sani ne"

Sauke ajiyar zuciya yai.

"Zanso ganinku waje daya. Rabakun ba matsala bane a wajena. Bana son takura ki ne kawai"

Matsawa tai tana dora kanta a kirjinshi. Taji dadin wannan karamcin dayai mata har ranta. Bakowanne namiji bane yake baka zabi irin wanda jabir ya bata.

Sosai take juya maganarshi a ranta. Bata son ta kasa cika rokon dayai mata nata fada mishi gaskiya.

"Bakomai bane inta zauna anan din. Roko daya nake maka. Addu.a daya nake maka honey j. Allah ya baka ikon yi mana adalci"

Lumshe idanuwa yai ya bude su akanta cike da yanda yake jin sonta.

"Amin Ya Allah. Nagode jana. Allah yai miki albarka"

Yatsanta ta saka ta rufe bakinshi.

"Amin. Ka manta babu godiya a tsakaninmu?"

Hannun ya kama yana cizon yatsan a hankali. Kwacewa tai tana yarfe yatsu.

"Haba mana. Da zafi fa"

Daga mata gira yai kawai dake nuna yasan da zafin ai. Naushin kafadarshi tadanyi a hankali.

Kamun muryarta da fuskarta babu alamar wasa tace.

"Idan kana da hali muje gobe in raka ka karasa siyayyar nan"

Girgiza kai yayi.

"Me yasa? A bari zuwa next week nikam nagaji. Ko kije ke kadai"

Jan numfashi tayi ta fitar

"Saboda ina so kagama komai yabar gidan nan. Ina son jin zuciyata free kadan. Bansan ko kagane me nake nufi ba.

Inajin kishinka sosai. Bazan iya dauka inajin maganar auren nan ba kullum. Nasan yana nan.

Believe me nasani kuma bana jayayya dashi. Saidai bana so ana mikomun shi gaban idona kullum"

Saurin dumtse hannuwanta yayi cikin nashi da fadin.

"Dan Allah kiyi hakuri. Ban sani ba wallahi. Zamuje gobe mu karasa in shaa Allah"

Yar dariya tai ganin yanda duk ya nuna baiji dadi ba da tunanin kaman yana hurting feelings dinta.

Sumba mai taushi ta manna mishi.

"Nagode da fahimta"

Janta yai jikinshi.

"Yanzun nan kika ce ba bu godiya ko. Zo nan to"

Dariya take tana ture shi. Kamun ya kashe mata jiki da wata irin soyayyarshi mai wahalar mantawa.

****
Sallah ta idar. Wani irin kadaici ke damunta wanda ta kasa fahimtar daga inda yake fitowa.

Lumshe idanuwanta tayi tana tuna fuskar nawaf da murmushin shi. Cikin kunnuwanta take jin muryarshi yanda yake fadin.

"Ina sonki Nur"

Murmushi tayi ta bude idanuwanta kamun lokaci daya gaskiyar ba zai taba dawowa ba ta sake zauna mata.

"Allah ya haskaka kabarinka nawaf. Ka tafi kabarni da kewarka mai yawa"

Ta fadi a sanyaye dan zuwa yanzun lokutta irin hakan neman hawaye take ta rasa.

Saita wuni ita kadai a daki abinta. Inba mumyn nawaf din tazo tace mata ta fito suci abinci ba. Ko dacan ita bamai yawan magana bace ba. Balle kuma yanzun.

Jinta take duniyar ita kadai kaman bata da kowa. Bata da wanda zata duba ta kira shi da nata. Sai yanzun taji hawayen na taruwa.

Gara da tana da anty. Duk da dacin gaskiyar hakan in ta juya duniya zata ce ga jininta komin bakinshi. Amman yanzun bata san daga ina ta fito ba.

Yaya ansar yace anty tsintarta tayi. A ina? Ta yaya? Shine bata tsaya tambaya ba dan tasan shima da wuya idan ya sani.

Ya akai ta bata? Su waye asalin iyayenta. Su waye danginta? Suna da rai? Basu da shi duk bata sani ba.

Wani abu ne take jin ya kulle a cikinta. Sai yau data dan nutsu tasan tashin hankalin rasa nawaf daban dana sanin bata da asali.

Batada wani da zata duba ta kira nata. Wannan tashin hankalin daban yake. Ta tuno yanda yan uwan nawaf suke zagaye dashi cike da kauna kaman su yi karo karo na ranakunsu na duniya su kara mishi.

Yanda suke kuka na rashin shi. Yanda a kullum daga kanta har su mamanshi suke wuni yimishi addu.a.

Hawayen da suka taru idonta suka zubo da wani dumi. Wazai nuna mata wannan kaunar? Wa zai mata irin addu.ar nan idan ta mutu.

Da ace suna da yaro ne ita da nawaf ko ba komai in dangin nawaf suka kalli yaron in bata zasu iya tunata suyi mata addu.a.

Kira taji ya shigo wayarta. Ta dauko wayar dake kan gado tana zama. Yaya ansar tagani rubuce a jiki. Tadan murmushin takaici.

Kaman wani zai kirata banda shi din. Ta fadi cikin ranta. Daga kiran tayi ta kara a kunnenta. Yai mata sallama data amsa da wani yanayi.

"Nuriyya menene? Kukan ne baki daina ba har yanzun ko? Sau nawa zan fada miki addu.arki yake so?"

Ai kaman maganganunshi sun bude mata sabon shafi ne. Cikin kuka tace.

"Bashi bane yaya farhan. Kawai ina tunani ne"

Tana jin yanda yaja numfashi hadi da fadin.

"Tunanin me? Saikin sama kanki ciwo ko?"

Ta girgiza kai kaman yana ganinta.

"Banida kowa a duniya dazan kira nawa yaya farhan. Dana gama takaba bansan menene mako mata ba.

Bansan ina zani ba daga nan. Bansan wacece ni ba. Bansan asalina ba ban......"

"Shhhhhh please nuriyya. Bana son wannan tunanin da kike. Ki daina fadin haka.

Kina da inda zakije. Kina da ni. Kina jina kina dani. Ba zaki taba rasa inda zakiyi ba in ina nan.

Ina so zamuyi magana amman da sauran lokaci saikin gama takaba kina jina. Bana son irin tunanin nan"

Cikin sanyin murya har lokacin hawayen basu daina zubo mata ba tace.

"Na daina. Yaya farhan dan Allah ka tayani duba wacece ni. Ka tayani dubawa ko zan samu dangina. Ko nima zanga wani nawa"

"Ki bari nuriyya. Zan tayaki. Zan dubo miko na miki wannan alkawarin please ki daina damuwa har haka kinji"

Kai ta daga tasa hannu tana goge fuskarta.

"Na daina in shaa Allah"

"Uhum. Ko ke fa. Zan fita yanzun. In kina son wani abu ki kirani"

"A dawo lafiya"

Ya amsata yana kashe wayar. Ajiyeta tayi gefe ta zame ta kwanta tana lumshe idanuwanta cike da tunani kala daban daban.

****

Yau kwananshi biyu da dawowa. Duka kwana biyun wajen su safiyya ya yisu. Kusan komai nashi na gidan. Hakan ba karamin dadi yake mishi ba.

Sun gama magana da abbah kan zuwa karshen satin daya kara samun nutsuwa zasu fara tafiya dashi dan yaga yanda harkar kasuwanci yake.

Tunda ya dawo safiyya ta koma aiki abinta sai tabar mishi Nana. Haka zai wuni biyema shiriritarta. Ko suyita yawo abinsu.

Yanzun hakan ma ice cream suka fita suka sha. Fu.ad din ya siyi kaji gasassu suka biya da Nana yagaishe dasu Inna.

Sun kuwa ji dadin ziyarar duk da ba dadewa sukai ba. Da gida zasu koma nana tace aje wajen momma.

*

Suna shiga gidan yaga momma da anty fatima da alama anty fatima fita zatayi. Gaisawa sukai da fu.ad din.

"Mun zo ke kuma har zaki tafi"

Dan dakuna fuska tayi tace.

"Asibiti ma zan wuce fu.ad"

Ware idanuwa yai.

"Ya Rabb. Waye ba lafiya?"

"Hamza ne yayo waya sun kai hussaina tana nakuda yanzun can zan tafi"

Jiyai zuciyarshi na dokawa. Momma ya kalla.

"Is she okay?"

Dariya tadanyi duk da damuwar dake fuskarta. Anty fatima ce tadan daki goshinta.

"Fu.ad Allah ya shirya mana kai. Ance maka tana nakuda kana tambaya if she is okay. Kasan she is not. Allah dai ya sauke ta lafiya.

Momma bara in tafi karya zama ba yan uwanta tare da ita. Ki kira pha.iza inata kira taqi shiga tunda na fito"

"To shikenan. Allah ya sauke ta lafiya"

Cewar momma. Anty fatima ta amsa da amin.

"Ko inzo muje tare?"

Fu.ad ya bukata. Kamun anty fatima ta amsa momma tace.

"Ba abinda zakai mata. Ko ita da wuya subarta ta shiga balle kai namiji. Kai mata addu.a kawai daga nan"

Shiru yai yana dakuna fuska har anty fatima ta fice. Yana kallon momma da nana suka wuce abinsu.

Babban falo ya zauna shiru yana tunani. Anan hassan ya shigo babu ko sallama.

"Bro ina momma?"

Kallonshi fu.ad yayi.

"Lafiyarka kuwa?"

Hannu yasa cikin gashin kanshi ya yamutsa kamun yace.

"Inata

Please Login or Register in order to submit comment