Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kamun ta kasa tai saurin tura mishi wani sakon.

"Ya amarya ta kwana?"

Ta dauko glass dinta kenan tana fesa turaruka masu saukin kamshi dan ita kadai kejin abinta inba gab da ita mutum yazo ba sosai.

Ta kama handle din kofar zata bude taji an turo. Hakan yasa ta danyin baya. Jabir ne. Idanuwanta take yawatawa kanshi.

Sanye yake da jallabiya. Ya mata kyau murmushin dayai mata yasa taji wani irin kishi ya rufeta. Musamman da ta tuna bata san adadin kalarshi da ayna ta samu ba a daren jiya

Saurin rintse idanuwanta tayi tana korar shaidan dazai hada mata fitina da sanyin safiyar nan.

"Ina kwana"

Ta fadin kanta a kasa. Hannunshi taji yasa jikin habarta ya dago da ita.

"Jana kinsan bana so in anamun magana aki kallon fuskata ko?"

Murmushin karfin hali tayi

"Afuwan. Ya kuka tashi?"

"Alhamdulillah. Harkin gama shiryawa?"

Kai ta daga mishi tana fadin.

"Eh kam. Ga breakfast dinku can a kitchen sai kaima atika magana ta shirya muku komai in kun tashi.

Zata iya hada muku lunch. Yara suna bacci yau bq zasuje school ba"

Kai ya daga mata.

"Mungode sosai jana. Sai munyi waya ko?"

Kamun ta amsa shi ya manna mata peck a labbanta ya juya. Sauke numfashi tayi ta fice hadi dayin addu.a.

*

Tana shiga asibitin tai sign in ake fada mata Nana tana nan. Saida taji zuciyarta ta doka. Yau din nan tai niyyar kiran safiyya taji ya jikinta.

Saidai itama abubuwa sun mata yawa akai. Yanayin yarinyar kawai yana sa taji kaman bata da matsala a tata rayuwar ko kadan.

Jakarta kawai ta ajiye office ta dauki abubuwan da take bukata ta dauki file din Nana da aka ajiye mata kan table dinta ta nufi dakin........!

****

Kaman yanda rayuwa ke tafiyarma su fu.ad haka ma take a wajen nuriyya. Washe garin data fita takaba kaman yanda farhan yai alkawari yaje sukai magana.

Tayi kuka sosai dayai mata maganar aure sai take ganin kaman hakan cin amana ne wajen nawaf. Kaman yayi kusa.

Saidai shi kanshi farhan yai mamakin yanda family din nawaf sukai tsaye akan abin. Yanda tare da taimakonsu suke nuna ma nuriyya auren da zatayi ba komai bane a wajensu.

Ba zasu dauka taci amanar nawaf ba ko kuma hakan yayi kusa ganin watanni ko biyar ba a cika ba da rasuwarshi.

Sun fahimci tana bukatar kulawa kuma su bazasu iya bata ita ba. Gabaki daya abinda nawaf ya mallaka tun kwana bakwai da rasuwar shi da akace za.a raba yan uwanshi suka yafe ma nuriyya.

Dan haka su suka shige gaba aka daura auren farhan da nuriyya. Ba ta da wasu da zata kira yan uwanta balle ace za.ayi wani shagali.

Bangaren farhan kuwa yasan yana da yan uwa bawai bashida su ba. Sai dai zumuncin dake tsakanin su ya dade dayin nisa. Baima bi takansu ba tunda family din nawaf sun musu wakilci su duka biyun.

Shi kanshi yaji wani iri dayaga daga shi sai ita a mota lokacin daya zo daukarta. Har suka kai gidanshi tana wani irin kuka da yake ji har zuciyarshi.

Suna shiga gidan ya kama hannuwanta yana kokarin riketa jikinshi. Kuka take sosai tana ture shi.

"Yaya farhan bazan iya ba wallahi. Dan Allah kayi hakuri"

Ganin yanda ta rikice yasa shi rikota gam. Karfi yasa ya riketa jikinshi gam yana kokarin nutsar da ita.

"Ba abinda zan miki nuriyya. Wallahi ba abinda zan miki. Ki nutsu zan zame miki duk abinda kike bukata a yanzun har lokacin da zaki so fiye da hakan.

I promise kome kike so in zama"

Ya sauke ajiyar zuciya jin tayi luf da ita a jikinshi tana kuka a hankali. Da gaske yake mata zai zama duk abinda take so.

Son da yake mata mai girma ne. Yasan tana bukatar lokaci mai yawa. Ya aureta ne da wuri haka saboda yana son tasan koda bata da kowa a duniya tana dashi.

Yana son kula da ita irin kulawar da bata taba samu ba a rayuwarta. Tana jikinshi ya jata har zuwa kan kujera ya sa hannunshi ya goge mata fuskarta.

"Kiyi shiru kar kanki yai ciwo please nuriyya"

Kai ta daga mishi tana kokarin hadiye kukanta. Ya mike ya shiga kitchen dinshi ya dauko mata fresh milk ya ajiye sannan ya fice ya dauko naman daya siya tun dazun.

Dakyar ya samu nuriyya tadan ci. Ya tambayeta ko tayi sallah. Ta daga mishi kai. Mikewa yai ya kama hannunta. Dakinshi yakaita ya tabbata ta kwanta bata bukatar komai sannan yai mata saida safe ya fice.

Sake shigewa cikin bargo nuriyya tayi tana ajiyar zuciya. A karo na farkona rayuwarta ta samu wata nutsuwa da bata taba sanin akwaita ba.......!

****

Kwanansu hudu a asibiti. Cikin kwanakin nan babu wanda baizo yaga nana ba. Daga kan abokan arziqi har yan uwa.

Cikin kwana hudun nan tun tana bude idanuwanta tai magana har takai ga sai dai in taji muryarsu ta bude idanuwanta dakyar ta mayar dasu ta lumshe.

Daga fu.ad har safiyya ba kuka suke ba amman kallo daya zakai musu kaga ramar da sukayi saboda tashin hankali.

Yauma kaman kullum wajen nana suka kwana sai dai me. Tun jiya rabon data bude idanuwanta. Fu.ad yai maganar duniya amman shiru kake ji.

Hannunta ya murza yaga bata motsa shi ba. Mikewa yai ya taba goshinta. Ya sake kama hannunta ya murza.

"Dammit nana wake up please....."

Tasowa safiyya tayi su duka suke kokari amman nana taqi ko motsi. Da gudu safiyya ta fita dan ta kira jana......!

#*TeamAS*
*#AnaTare*
[7/18, 6:07 PM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[7/18, 6:08 PM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: AKAN SO 47
*πŸ’˜πŸ’–AKAN SOπŸ’–πŸ’˜*

~Written by~ :Luβπα SufyΞ±Ο€

www.Loobnerh.blogspot.com

Wattpad: LubnaSufyan

47

*Tabbas babu wani abu da yake da tabbas a cikin duniya. Babu komai cikinta sai tarin dauda da rashin kwanciyar hankali*

*Ba zaka gane hakan ba sai lokacin da kaddararka ta jarabta ya juyo kanka*

*Gabaki dayan littafin nan yana tabani fiye da yanda yake taba ku. Saboda kaso 60% cikin 100% ba fiction bane gaskiya ce*

*Yana tabani ta yanda babu wanda zai fahimta. Ta wani fannin yana fifitamun ciwuka da raunikan dana samu a tsahon rayuwata*

*Ciwukan da basu gama ciwo ba. Ciwukan da nasan in har ina duniya ban gama samun kalarsu ko fiye dasu ba*

*Godiya ta tabbata ga Allah a kowanne hali*

*zainab Askira. Rukayya Abdulkadir. Mardiyya isyaku and Nasiba. Amina mashasha. Yasmeen Tafeesu. Ummie khaleel. Fatima Aliyu(childhood friend). Sha.afatu saleh. Da wanda ma ban lissafo ba kusan AnaTare. Like AnaTare sosai sosai*

Doc jana na shigowa dakin na.u.ororin dake manne jikin Nana ta shiga dubawa. Kallonta fu.ad yake cike da tashin hankali.

Da gudu yaga ta fita basu fi mintina biyar ba suka dawo su hudu. Kama hannun safiyya yayi tana tirjewa tana ce mishi.

"Ka sakeni. Kabarni babu inda zan tafi....."

Gam ya riketa jikinshi tana wani irin kuka. Tashi zuciyar ta bushe. Wani iri yake jinta yanda babu kalaman da zai bayyana ta dashi.

Bakin kofar dakin da Nana take ciki suka tsaya har lokacin safiyya dake kuka tana jikinshi. Habarshi ya dora saman kanta ya lumshe idanuwanshi yana fadin.

"Allah kabamu juriya. Allah duk yanda kai damu dai dai ne...."

Baisan iya lokacin da suka dauka a haka ba sai da yaji bude kofar. Da sauri safiyya ta zame daga jikinshi tana kallon doc jana.

Ta gabansu sauran likitocin suka fito suka wuce. Safiyya bata jira komai ba ta wuce cikin dakin. Shikam fu.ad tsayawa yayi ya zuba mata idanuwa.

Nata idanuwan taji sun cika taf da hawaye. Daga kan Nana tai alkawarin ba zata sake karbar wani cancer patient ba. Zuciyarta ba zata iya dauka ba.

Muryarshi a dakushe yace.

"How many days?"

Saida takai mintina biyu tana kokarin controlling emotions dinta sannan tace mishi.

"A few hours max......"

Tana rufe bakinta ta juya da gudu tana barin wajen saboda bata son fu.ad yaga hawayen dake zubar mata. Bata son yaga yanda take ji ita da bata hada jini da nana ba kenan.

Bangon wajen yasa hannu ya laluba jikinshi na bari. Kalmomi hudu ta fada amman shi a wajenshi gabaki daya farin cikin su ta tarwatsa.

Cikin kunnuwanshi yake jin amsa kuwwar da kalmominta suke mishi. Yasan yana cikin shock saidai baisan yanda zai ya fita ba.

Wata dariya ce yaji ta kubce masa da baisan ta inda ta fito ba. Wayarshi ya dauko ya kira haneef ya daga da fadin.

"Fu.ad ya Nana din?"

Cikin muryar da bai gane ko tashi bace yace.

"Kuzo ku mata bankwana haneef. Awanni kadan take dashi"

Yanajin yanda haneef yaja numfashi ta cikin wayar ya sauketa daga kunnenshi bai damu daya kashe ba ya sata a aljihunshi.

Handle din dakin ya kama zuciyarshi na wani irin yawo da zai iya rantsawa yanajin bugun da take har cikin kunnuwanshi.

Turawa yai a hankali. Safiyya na rike da hannun Nana tana tsugunne kasan gadon tana wani irin kuka da yaji ya tsaya mishi a wuya.

Gefen gadon ya zauna ta dayan bangaren yana kama hannun nana daya ya rike shima. Jiyai kaman tayi motsi hakan yasa shi fadin.

"Princess......"

"Daadyyy......"

Ta fada. Da sauri safiyya ta dago ta na zama kan kujera. Hannunta daya tasa tana goge hawayenta.

"Nana kina jina"

Idanuwanta a rufe take.

"Mumy ya aljanna take?"

Ta tambaya muryarta na rawa tana wata irin kokawa da numfashinta. Kuka ya hana safiyya magana. Fu.ad ya hadiye wani miyau yace.

"Princess babu wanda yasan exact yanda take. Waje ne mai cike da ni.imomi fiye da zaton dan adam.

Wajene da yake da farin ciki. Kwanciyar hankali da natsuwa ta har abada"

Murmushin da Nana tayi har cikin ranshi yaji shi.

"Babu rashin lafiya?"

Kai fu.ad ya girgiza duk da bata ganin shi.

"Babu ko kishin ruwa Nana. Babu komai banda farin ciki.........!"

Yana kallon yanda kirjinta ke dagawa dakyar saboda yanda take kokawa da shigar iska abin na mishi wani iri.

"Duk ciwon nan zai tafi?"

Wannan karin kasa amsata yayi. Saboda wani abu ya rike kalamanshi. Bakinshi ya bushe tas.

Muryar safiyya na rawa wasu sabbin hawayen na zubo mata tace.

"Zai tafi Nana. Babu kunci ko kadan a cikinta. Wajene da mai laifi da marassa laifi ke da burin shiga"

Murmushin Nana ya sake fadada. Hannayensu dake rike a cikin nata da dan sauran karfin da take ji ta dumtse.

"This is not a good bye. Wannan na nufin sai kun taho. Yana nufin ina jiranku a aljanna......"

Lumshe idanuwanshi fu.ad yayi. Safiyya ta kife kanta jikin gadon in tana zaton taji mutuwar usman abinda take jina yanxun ya linka wancen fiye da zatonta.

Wani irin daci ne har cikin naman jikinta. Wani ciwo ne marar misaltuwa.

"Ya Allah......"

Nana ta fadi kamun fu.ad yaji ta saki hannunshi. Bude idanuwanshi yayi lokaci daya da dagowar safiyya. Jikinta na bari da wata irin fargaba marar misaltuwa take kallon nana.

Kaman tana bacci da murmushi a fuskarta.

"Nana...."

Ta kira a hankali muryarta dauke da fargabar da take ji. Idanuwanta cike taf da hawaye ta dago ta kalli fu.ad da tashi zuciyar ke son fitowa daga kirjinshi.

Sam basu ji turo kofar haneef da lukman ba ballantana sallamarsu. Idanuwansu na kafe da juna. Kamun safiyya ta sake maida hankalinta kan Nana.

Wani irin abu fu.ad ya hadiye daya tsaya mishi a wuyanshi. Haneef na kallon nana yakai hannunshi ya dafe kanshi.

Lukman ya kalla ya girgiza mishi kai yana son gaya mishi ba abinda suke zato bane ba. Bashi bane sam.

Karasawa lukman yai ya dafa fu.ad. Ya juyo ya kalle shi ya sake maida hankalinshi kan Nana daga shi har safiyya tsoron tabata suke ji.

"Nanaaaa"

Safiyya ta sake kira muryarta na karyewa. Lukman yakai hannu ya tabata kafarta. Dumtse kafar yai cikin hannunshi.

Yaji tayi sanyi. Da sauri ya saki kafar nana yana goge hannunshi sosai jikin kayan jikinshi yana son cire yanayin dayake ji manne jiki har lokacin.

"Barin kira doc"

Haneef ya fadi a tsorace yana fita daga dakin. Ko mintina biyar baiyi ba ya dawo da wani doc.

Aune aunen shi ya shiga yi. Kamun yadan runtsa idanuwa ya dafa kafadar lukman dake tsaye sannan ya girgiza ma haneef kai.

Yana ficewa daga dakin. Mikewa tsaye safiyya take tana ja da baya tana girgiza kanta.

"Dan Allah ku cemun lafiyarta kalau. Dan Allah kucemun wani abu bai sami Nana ta ba.......!

Kar kucemun tabarni. Kar kucemun wannan shine bankwana.......!

Wallahi ban shirya ba. Ban shirya ba....."

Hannu fu.ad yakai a tsorace ya dora kan kirjin Nana dai dai zuciyarta. Wani irin shiru yaji. Ya dago idanuwanshi ya kalli lukman.

Hawaye yaga sun zubo daga idanuwan lukman din. Cike da wani yanayi yace ma lukman.

"Ta rasu ko?"

Juya baya lukman yayi. Haneef ne ya karaso yana dafa fu.ad din. Ture hannunshi yayi still dayan nakan kirjin Nana.

"Em okay. Kawai ku fadamun. Ina so wani ya tabbatar mun ne. Ta rasu?"

Dakyar haneef yace.

"Ta rasu fu.ad"

Hannunshi ya dauke daga kirjinta ya mike daga kujerar dayake zaune ya koma gefen gadon ya zauna.

Hannunta dayake karara ya kamo ya sumbata. Sannan ya tsugunna ya sumbaci goshinta yanajin wani yanayi da bai taba ji a jikinta ba.

Batare daya dago ba yace.

"Allah yasa mutuwa hutu ce a gareki Nana. Allah yai miki Rahma. Allah ya sadaki da fiye da abinda kike zaton Aljannarki ta kunsa"

Yana karasawa ya mike tsaya. Wajen safiyya dake girgiza mishi kai ya nufa. Hannuwanta ya kama yana kallonta.

"Safiyya zo ki mata addu.a"

Wasu hawaye masu ciwo da dumi suka zubo mata.

"Ku duba sosai. Dan Allah ka duba. Bata rasu ba"

Kamata yai ya rungume tsam a jikinshi yana rocking dinsu. Yasan shirun nan da yakeji cikin kanshi da zuciyarshi ba na lafiya bane.

Yasan dole ne koma ina ya adana ciwon daya kamata ace yana ji zai dawo mishi. Zai dawo mishi batare da shiri ba.

Wani yawu ya hadiya. A hankali yake ce ma safiyya.

"Dukkan mai rai mamaci ne sofi. Bakiji me Nana tace ba? Wannan ba bankwana bane ba. Kizo ki mata addu.a"

Kai take daga mishi tana jin zuciyarta na wani irin tsaitsayawa da ciwon da take ji.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji.un....."

Fu.ad ya fadi cikin kunnenta. Ai kaman ya tuna mata abinda ya kamata tayi ta shiga jero wa jikinta na wani irin bari.

Wani kwarin gwiwa taji ta samu wanda batama san daga inda ya fito ba. Tare da fu.ad suka taka wajen da Nana take kwance.

Kallonshi tai ya daga mata kai alamar zata iya.

"Ki mata addu.a tana jinki sofi. Taji yanda kike kaunarta"

Muryarta na rawa tace.

"Allah ya sadaki da Rahmarshi Nana. Allah ya baki hutun da kike ta nema. Zamuyi kewarki.

Allah ya haskaka kabarinki kamun ki karasa mishi....."

Yanda ta karasa maganar yasa fu.ad kamota yana janyeta daga wajen nana.

"Bangama ba fu.ad banga mata bankwana ba"

Kanta yakama ya kwantar a kirjinshi yana janta a hankali yana fadin.

"Zaki kara wani in munje gida"

Da kanshi ya fita da ita ya bude mota ya sakata a baya ya kullo sannan da gudu ya dawo.

Lukman na jingine da bango idanuwanshi kafe kan Nana da take kwance kan gado. Fuskarshi ta wani irin kumbura.

Fu.ad ya sauke numfashi.

"Lukman taho ku tafi gida da safiyya"

Girgiza mishi kai lukman yayi yana kasa magana. Kama hannunshi fu.ad yayi kaman karamin yaro har lokacin idanuwanshi na kafe kan Nana.

Yana sake ganin yanda duniya ba komai bace ba. Yar yarinya kenan da bata da wasu tarin zunubai. Ballantana kai babba da gulmar wasu ma kadai ta isheka tashin hankali.

Bude mishi gaban motar fu.ad yayi ya shiga ya mika mishi mukullin motar.

"Can you drive?"

Ya tambaya. Kai lukman ya daga mishi. Ya sauke numfashi yana kallon safiyya data hade kanta da gwiwa a bayan motar.

"ka kaita wajen momma gamu nan zuwa"

Sake komawa fu.ad yayi yana mamakin kanshi. Ya kamata ace yanajin wani abu amman kawai dai ya rasa ko me yake ji.

Inda yabar haneef nan ya same shi. Baibi takanshi ba ya shiga tattara kayayyakinsu yana zubawa cikin jakar da suka fito.

Saida ga gama tas sannan ya mikama haneef daya karba yana kallon fu.ad din da mamaki.

"Fu.ad?"

Ya kira cike da shakku yana son tabbatar da ko yana lafiya. Saida ya dauki takalman nana dake ajiye a kasa ya hada su waje daya sannan ya amsa da.

"Na.am.......sa takalman Nana a ciki kar abarsu"

Jinjina kai haneef yayi ya karbi takalman yasan akwai matsala tare da fu.ad din. Yana kuma tsoron sanda mutuwar zata gama zauna mishi.

Karasawa kan gadon da Nana take fu.ad yayi ya dagota a hankali kaman tana bacci ya sabeta a kafadarshi. Ya kalli haneef hadi da fadin.

"Muje ko"

Ba musu haneef ya kama hanya jikinshi a sanyaye. Suna fita daga dakin suna cin karo da doc jana. Kallo daya tai musu tayi baya.

Fu.ad yace mata.

"Doc......!"

Dawowa baya tayi. Kallonta yai.

"Ki mata bankwana. Kina da muhimmanci a wajenta"

Sai da ta lumshe idanuwa sannan tace.

"Allah ya jikanta ya baku hakurin rashin ta"

"Amin mungode. Sai wata rana"

Ya fadi suna wucewa. Mamakin shi haneef yake. Akwai babbar matsala.

*

Kofar gida haneef yai parking saboda mutane har sun fara taruwa kofar gidan. Ya zagayo ya bude ma fu.ad bayan motar.

Ya fito sannan ya tallabo Nana ya sake sabeta a kafadarshi. Haneef kadai ya tsaya gaisawa da mutane suna mishi gaisuwa. Cikin gida fu.ad ya wuce.

Saboda baya son yanda kowa ke kallonshi din nan. Lokaci daya maganar nana ta fado mishi. Haka suke kallonta cike da wannan yanayin a idanuwansu kenan?

Sake tallabeta yai jikinta yana rasa menene yai mishi daban cikin hakan. Yana sallama yasa kafarshi cikin gidan anty fatima na sakin wani irin kuka.

Momma ma fuskarta harta kumbura. Tasowa tayi ta karbi nana daga hannun fu.ad din tana nazarin fuskarshi.

"Fu.ad...."

"Em okay momma. Kuyi mata wanka bara mu siyo abinda ya kamata.

"Hassan ya tafi"

Momma ta fadi tana goge fuskarta da dayan hannunta. Kai fu.ad ya daga mata.

"Abbah fa?"

"Yana waje. Bai jima da fita ba"

Kai ya sake daga mata ya juya. Yana shirin fita inna na shigowa tana goge fuska. Kaucewa yai gefe dan yaga yanda tana ganinshi wasu hawaye suka sake zubo mata.

Da sauri yabar dakin.

*

Su haneef ya samu suna alwala. Kofar gidan ya cika makil da mutane. Shima alwala yayi yace ma haneef.

"Ina lukman?"

A sanyaye haneef yace.

"Yaje ya taho da zainab"

Kai ya daga mishi kawai yana mikewa. Ansar ya hango ya nufo su. Tsayawa yai ya karaso ya mika ma haneef hannu sannan fu.ad din.

Muryarshi na rawa yace.

"Yanzun naje asibiti ake fadamun. Na kira safiyya ta sai wata ta daga taban address din nan. Ya Allah. Oh Nana......"

Kasa karasawa ansar yayi sai fuskarshi daya sa cikin hannayenshi yana wani irin jan iska. Mutuwar nana yake ji har cikin zuciyarshi.

Dafa shi yaji anyi ya bude fuskar ya sauke idanuwanshi kan fu.ad.

"Sai hakuri. Kai mata addu.a shi tafi bukata"

Kai kawai ansar ya daga ma fu.ad din. Sai kuma ya sake kallonshi sosai wannan karin. Girgiza kai yake kamun ya maida dubanshi kan haneef.

Abbah fu.ad ya hango yabarsu haneef nan tsaye. Ansar yace ma haneef.

"Is he okay?"

Dan daga kafada haneef yayi hadi da girgiza kai.

"Allah dai ya rufa asiri"

"Amin. Oh Allah"

Cewar Ansar yana samun waje ya tsugunna dan rasuwar na tabashi ba kadan.

*30 minutes later*

Su hudu suka shigo cikin gidan. Dashi da lukman,haneef sai babban yaya dan su dauko gawar nana.

Ai nan tashin hankalin yake. Suna nufo inda take kwance an hadata. Safiyya ta taso da gudu ta rike nana jikinta.

"Dan Allah ku tsaya. Ku tsaya ban gama ganinta ba"

Momma dake wani irin kuka ta taso ta kama safiyya.

"Kiyi hakuri safiyya. Kiyi hakuri"

"Momma dan Allah kice su kara tsayawa. Kar su tafi da ita....."

Riketa momma tayi a jikinta. Kamun anty fatima ta taso ta tayata. Fu.ad da kanshi yasa hannu ga dago Nana yana jin shiru cikin kanshi da ko ina na jikinshi.

Sosai gidan ya sake rikicewa banda.

"Inalillahi wa ina ilaihi raji.un....."

Babu abinda suke fadi. Haneef ya runtsa idanuwanshi yana bude su. Yana jin dadin yanda basu saki Allah ba.

Yana kuma da tabbacin zai saukaka musu dacin rashin Nana. Hakika sabo ake yiwa kuka. Safiyya ba kallon sun nufi kofa da nana ta rarrafa dan ta kasa tashi.

Ta karasa wajen inna tana boye kanta cikin cinyar inna hadi da sakin wani kuka da takejin fitowarshi daga wani waje na zuciyarta da bata san yana nan bama.

Shikenan ita da Nana har abada.....!

Inna ta riketa itama kukan take saboda yanda mutuwar nana ta sake fama mata ciwon mutuwar usman. Tasan me yarta take ji. Tasan halin da take ciki.

Abu daya inna take da yaqini akai. Allah daya dora musu yasan dasu. Inhar suka rike shi zai basu mafita.......!

****

Dakyar ta iya kai kanta gida. Dan lokacin tashi baiba ma tace gida zataje bata da lafiya.

Ko sallama batai ba ta zauna falon ta na ajiye komai anan. Dafe kanta tai cikin hannayenta.

Tun mutuwar mahaifinta rabon da ai mata wata mutuwa data tabata. Sai yau rasuwar nana ta girgizata sosai.

Hawaye ke zubo mata. Wani nabin wani. Bata ji fitowar ayna ba sai maganarta taji.

"Anty? Yaushe kika dawo? Sannu"

Dagowa tayi wasu hawaye na sake zubo mata data sa hannu ta goge su. Ware idanuwa ayna tayi ta karasa inda jana take ta zauna.

Kusan sati daya kenan da zuwanta gidan nan. Banda gaisuwa babu abinda yake hada su da jana din. Hakama yaranta zasu gaishe da ayna din kullum.

Ko bata fito ba sanda zasuje school zasuyi sallama bangarenta su gaishe da ita sannan su wuce. Kuma hakan ya mata dadi yanda jana tasa suke bata girma.

"Anty lafiya dai ko? Ko wani ya rasu?"

Kai jana ta daga mata. Ba zata ce ta tsani ayna ba. More like tana kishi da ita ko tace tana kishin jabir da soyayyarshi.

Cikin sanyin murya tace.

"Wata yar yarinyace. Nana sunanta patient dina ce kusan shekaru uku. Mun saba sosai yau ta rasu"

Dafa ta ayna tayi tana jin duk babu dadi. Ita mutuwar yara na mata wani iri. Jikinta sanyi yake.

"Allah sarki. Allah ya jikanta ya ba iyayenta hakurin rashi"

"Amin ayna nagode"

Kayan da jana ta cillar tsakar dakin ayna ta tattara mata waje daya hadi ta kauda mata gefe tana wucewa.

Dawowa tayi da ruwa da cup. Ta bude ta zuba ta mikama janar. Ta karba tasha. Sosai taji dadin karamcin da ayna tai mata.

"Nagode ayna"

"Bakomai anty. Kiyi hakuri ki mata addu.a sai tasan kin damu da ita sosai.

Ko kije kidan watsa ruwa ko zaki samu natsuwa"

Mikewa jana tayi ta kalli ayna tace.

"Nagode fa. Bara in shiga daga ciki"

Kai ayna ta daga mata hadi da murmushi. Jakarta ta dauka ta wuce ciki. Ayna ta bita da kallo.

Tana fatan wannan zaman lafiyar da suke ya da jana da ganin girman juna ya dore. Yanda bata shiga harkarta bata damu da harkarta ba kawai yana burgeta.

Bata son tashin hankali sam. Ta kuma kula jana bata da matsala. Sai yanzun taga dalilin dayasa kullum sai jabir ya yabi halayyarta.

Tai ma kanta alkawari zata sa ido ta karanci jana tsaf ko itama zata dinga samun koda rabin yabon da jabir yake mata ne.

****

Tun daga hanyar dawowa daga makabarta lukman ke kallon yanda fu.ad ke ta duba hannayenshi kaman yana son ya tabbatar da su na nan ne ko yana mamakin ganinsu a jikinshi.

Haneef ya tabo ya nuna mishi fu.ad din daketa jujjuya hannunshi sauri sukayi suka karasa wajenshi suka jera tare.

Lukman ya kira sunanshi a hankali. Baiko juyo ba balle suyi zaton yaji. Kawai tafiya yake yana kallon hannuwa shi daya dago su.

Haneef ya kai nashi hannun ya kama daya na fu.ad. Sai lokacin ya dago ya kalli haneef idanuwanshi cike da wani irin ciwo da yake ji a kirjinshi.

"She is gone haneef. Da hannuwana na kamata na sata a kabarinta. Da hannuwana na dibi kasa na taya aka zuba mata.

Haneef wannan shine soyayyar ko? Da kaina na dinga duba ko an manta ba a rufe wani waje da kyau ba. Iya kaunar dazan nuna mata kenan ko?"

Lumshe idanuwa haneef yayi.

"Ya Allah...."

"Itama haka tace kamun Allah ya dauki abinshi......."

Fu.ad ya fadi yana juyawa ya kalli lukman.

"Daman aronta aka bamu ko lukman? Kaga Allah ya dauki abinshi tunda yafi mu sonta"

Hannunshi dayan lukman ya rike yana matsewa dam. Dayai magana hawayen dayake ji zubo mishi zasuyi. Fu.ad na bukatar dukkan strength din dazai samu daga gare su.

Haneef addu.a yake su karasa gida lafiya kar fu.ad ya samu break down a hanya. Hankalinshi bai kwanta ba sai da yagansu kofar gidansu.

Sai da yaga sun shiga harabar gidan tukunna. Fu.ad dake tsaye idanuwanshi kafe a kasa ya kalla ya sauke numfashi. Saida ya dafa kafadarshi sannan yace.

"Fu.ad kayi hakuri. Dukkanmu babu mai tabbacin bazai bi Nana yanzun nan ba. Ita mutuwa ba sallama take ba.

Ba kuma jira take ka shirya ba. Idan bata zo kanka ba kasa a ranka a kullum kaine ko wani makusancinka ko wani wanda baka sani ba.

Bazan ce nasan ciwon da kake ji ba. Amman kayi hakuri dan Allah"

Girgiza kai fu.ad yake.

"Haneef ta rasu. Shikenan ko?"

Har ranshi ciwo yake ji marar misaltuwa. Ganin fu.ad din cikin yanayin da yake yanzun. Amman yasan gara yanzun da dazun.

Dazun sam ba cikin hankalinshi yake komai ba.

"Ta rasu fu.ad da gaske

Please Login or Register in order to submit comment