Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abubuwa na mishi yawo. Shekaru sha daya na rayuwar Nana ya rasa.

Mikewa yai. Yana son fita yadan sha iska kamun ya fadi wata maganar da baya so Nana taji. Jiyai an riko hannun shi. Juyowa yai ya kalli Nana da idanuwanta suke cike da hawaye.

Girgiza mishi kai tayi.

"I am sorry na kiraka M. Bansan wanne suna kake so ba. Please karka tafi"

Wani irin rauni zuciyarshi tayi. Numfashi yake fitarwa da sauri sauri saboda yanda yake jin gara ace asibitin nan ne ya baje da hawayen dake cikin idanuwan Nana.

Da sauri ya samu waje gefenta ya zauna. Hannuwanshi yasa ya tallabi fuskarta. Muryarshi a dakushe yace.

"Babu inda zani Princess. Ina nan tare dake........."

"Ummmm"

Safiyya ta fadi alamar bata kama zancen ba. Yana jinta hakan kuma ya mishi ciwo ba kadan ba. Zai sauke mata in basa gaban Nana.

Zai iya daukar duk rashin kunyarta data koya yanzun. Banda gaban Nana. Karshen abinda zaiso shine tasa ma yarshi yi mishi wani kallo na daban.

Mikewa safiyya tayi ta fice ta na dan doko kofar da karfi. Yabita da kallo kamun ya mayar da kallonshi kan Nana datai murmushi tace.

"Karka damu. Na yarda dakai"

Ware idanuwa yayi. Kamun yai yar dariya. She is smart. Ya fadi cikin zuciyarshi. Kamun yace wani abu Nana tace.

"Zaka zauna damu?"

Dariya yayi.

"Kina son mumynki ta yankani ko?"

Dariya take sosai. Inda rayuwa zata tsaya a haka zai iya cewa farin cikin data miko mishi mai dorewa ne.

*

Dr. Jana na hango safiyya ta karasa wajenta hadi da fadin.

"Naso mu rike Nana sai zuwa gobe. Bazan iya masifar babanta ba"

Sauke ajiyar zuciya safiyya tayi.

"Dan Allah kiyi hakuri......."

Murmushi Doc jana tayi mata hadi da fadin.

"Karki damu. Ko zazzabi kikaji jikinta ku dawo. Abin na spreading da sauri fiye da yanda muke zato"

Wasu hawaye suka ciko idanuwan safiyya. Addu.a take Allah yasa fu.ad yazo dai dai da abinda ake bukata. Dafa mata kafada doc jana tayi sannan ta wuce.

Mayafinta ta janyo tana goge idanuwanta. Sannan ta wuce ta koma. Zaune ta same su fu.ad yana ba Nana labari.

Kallonsu take. Ta kasa nutsuwa dashi. Tana tsoron kar tarihi ya maimaita kanshi. Wata zuciyar tace koma menene yaxo ai. Kuma yana nan yana son taimakon Nana.

Zatai focusing akan wannan kawai. Zata danne son shake shin da ke taso mata. Zatai kokarin boye abinda ya faru tsakaninsu inda yake duk shekarun nan.

Gyara zama tayi tana kallonsu. Da yanda sukai kama ba yar kadan ba. Ko mintina goma ba.ayi ba ruwan dake jikin Nana ya karasa karewa.

Tasowa safiyya tayi ta kashe. A tsorace fu.ad ya kalleta.

"Me kikeyi? No kirawo doc suzo su cire mata"

Kallon da gaske kake? Safiyya tai mishi kamun ta koma kan abinda take kokarin yi.

Mikewa yai a dake yake fadin.

"Da gaske nake. Ba aikinki bane ba zaki tabamun yarinya ba...."

Wata dariyar takaici tadan kwace mata. Karfin hali take kallo kiri kiri. Yana son nuna mata yafita damuwa da Nana ne.

Riko hannunshi Nana tayi hadi da fadin.

"It's ok. Tana ciremun wani lokaci"

Girgiza ma Nana kai yayi idanuwanshi na kafe kan safiyya hadi da fadin.

"Lokacin bana nan ne......"

Bude baki tayi zata amsa shi. Doc jana ta shigo dakin. Hankalinshi fu.ad ya mayar kan ta da cewar.

"Wanne doka ya baku damar barin wanda ba doc ko nurse ba taba marar lafiya?"

Safiyya ta kalla. Dan batama gane kan tambayarshi ba.

"Ignore him. Yana jin dadin magana shi kadai wasu lokuttan"

"WTF sofi."

Idanuwanta ta ware mishi dake nuna a shirye take ta biye mishi su kwashi yan kallo gaban Nana. Mayar da maganar da yake shirin yi yayi.

Doc Jana ta wuce ta zare ma Nana ruwan. Ta cire abin daga hannunta tasa auduga tana danne wajen kamun ta sakarma Nana.

Da sauri fu.ad ya kamo hannun yana saka audugar ya danne mata.

"Sannu."

Murmushi Nana tayi. Tana kallon yanda yake dakuna fuska kaman abin a hannunshi yake. Hakan kuwa yakeji har ranshi.

Doc jana tace.

"Please ko ciwon kai take ji ku dawo da ita."

Kai suka jinjina mata su duka biyun ta kalli Nana tace.

"Allah ya kara sauki"

Da murmushina fuskarta ta amsa da.

"Amin anty jana. Meke damunki?"

Da mamaki sosai Doc Jana ta kalli Nana. Sosai take jin mamakin tambayarta. Hakan yasa Nana fadin.

"Ko yaushe kina mun hira har ki gama dubani. Banda yau da safe da yanzun kuma.

Kina kawomun milkshake ko zuwa mukai ban kwana ba. So kawai wani abu na damunki"

Lumshe idanuwa doc jana tayi. Tana bude su kan safiyya. Allah ya bata yarinya mai tattare da baiwa kala kala.

Safiyya tace.

"Nana....."

Hannu doc jana ta daga mata alamar babu komai. Tsakaninsu ne. Hankalinta akan Nana tace.

"Yeah wani abu na damuna. Karki damu i will be ok. Sorry ban kawo miki milkshake din ba. Kina bina ok?"

Murmushi tai har hakoranta suka fito.

"Alright nagode anty jana. Kiyi addu.a komai mai wucewa ne tunda kina da lafiya"

Wannan karin fu.ad ne ya ware idanuwanshi kan safiyya da tambayar haka Nana take so smart ko kuma shi kadai ne ya kula.

Kai tadan rausayar gefe da nufin. Haka nake fama. Murmushi yai dayakai har zuciyarshi. Mouthing ma safiyya yai.

"She is my daughter"

Dake nuna dole ta zama smart. Wato ta biyoshi. Dariya safiyya tai data janyo hankalin nana da doc jana kanta. Ta dan hade fuska.

Mikewa doc jana tayo batace musu komai ba ya fice. Rankwafawa fu.ad yai ya kama Nana yana dorata kan kafadarshi.

Dariya ta kamayi tana fadin.

"Ka sauke ni zan iya tafiya da kaina fa......"

Girgiza mata kai yayi. Yana kara yara mata zama a kafadarshi.

"Princess basa tafiya da kafarsu"

Dariya take sosai. Safiyya yake kallo tana tattara kayyakinsu cikin wata jaka. Karasawa yai yana kokarin daukar jakar.

Ta janye hadi da watsa mishi wani kallo.

"Bana so"

Dan daga kafada yai alamar matsalarta ce. Ya wuce ya hude kofar ya fita da nana dake ta mishi surutunta.

Sauke ajiyar zuciya safiyya tayi. Lokaci daya ya shigo rayuwar Nana ya sace zuciyarta. Yanda yan uwanshi sukai mishi dazun bai bata mamaki ba.

Son shi baya bari aga laifinshi. Wannan a jininshi yake. Daukar jakar tayi da mukullin motarta daya ajiye gefen gadon nana tabi bayansu.

Tsaye ta same fu.ad nana nakan kafadarshi. Bude musu motar tayi. Baya ya bude ya saka Nana shima ya shiga.

Kallonshi tayi. Ya wani kauda ido. Ita zata tuqa. Inda yake zaune nan Nana zata zauna. In tsarin bai mata ba ta dawo baya su koma gaba.

Ta karance shi tsaf dan haka ta zagaya ta bude motar ta shiga ta tayar tana daukar titi.

****

Tana shiga cikin gidan taga motar nawaf. Lumshe idanuwanta tayi tana sauke ajiyar zuciya. Tsayawa tayi na wajen mintina biyar tana kokarin mayar da fuskarta dai-dai.

Ganin farhan ba karamun shock yazo mata dashi ba. Ta kuma san nawaf kaman yunwar cikinta. Yana karantar komai a fuskarta. A hankali ta taka zuwa cikin gidan ta tura kofar da sallama.

Yana jingine da bango a tsaye. Ya dago idanuwan nan ya sauke su akanta. Yanayin su tagani tai tsaye taki karasawa ciki.

Takowa nawaf yayi yazo daf da ita yana fitar da numfashi da sauri da sauri. Muryarshiba dakushe yace.

"Waye kuke tsaye dashi a bakin saloon?"

Wani irin dumm taji cikin kunnuwanta kamin zuciyarta ta dauki duka. Tambayarshi ta girgiza ta. Abinda ta tsaya tana kokarin boyewa ne.

A tsawace ya ce.

"Tambayarki nake nuri"

Ja tai da baya kadan. Ya damqo hannunta kaman zai karyata. Kokarin kwace hannunta takeyi ta kasa. Jijjigata yayi yana fadin.

"Dawa kike magana Nuri? Waye shi?"

Cikin kuka tace.

"Ka sakemun hannu....."

Mari ya dauketa dashi yana kara jijjigata.

"Ki fadamun waye kike tsaye dashi?"

Batasan lokacin da wani karfi yazo mata ba. Ture shi tai gefe tana sakin wani irin kuka.

"Farhan ne!!! Saika kyaleni yanzun ko?"

Ta karasa maganar tana goge fuskarta. Wani irin abu zuciyarshi takeyi. Duhun nan ya cika mishi kai. Janyota yai ya hadata da bangon dakin.

Yaci gaba da dukanta kunnuwanshi basa jin ihun da Nuri keyi. Maigadin gidan yaji ihun yai yawa daga inda yake ya shigo yaga ko lafiya.

Salati ya saka yana kokarin janye nawaf. Amman kaman ma sake tunzura shi yake. Tun Nuri na ihu harta daina saboda ta yi laushi ba kadan ba.

Dakyar maigadi ya janye nawaf daya fice daga gidan dan in yana ganin Nuri baisan abinda zai iya faruwa ba. Girgiza kai kawai maigadi yayi daya ga Nuri ta motsa ya fice.

Dan shigowar dayai ma ba huruminshi bane. Jiyai abin sai addu.a. Da bala.in karfin hali tana hawaye taja jiki ta janyo jakarta dake gefe.

Kuka take sosai. Ta tabbatar nan gaba nawaf kasheta zaiyi. Tana jure komai ne saboda bata da inda zata juya ma.

Mamanta ce. Ita kuma data koma gidan karuwai gara ta mutu a gidan nawaf. Ganin farhan. Ganin farhan yasa taji tana da zabi.

Rayuwa a gidan nawaf da yake tunanin zai jigeta a duk sanda yai niyya saboda ya mata alfarma ta aurenta.

Yanzun take ganin komai a saman farar takarda. Bakin rubutun kaddarar auren nawaf daro daro. Yanzun ta sake tabbatar da yan uwan nawaf sunsan dan uwansu mai lafiyane ba zasu taba bari ya auri yar gidan karuwa da ba asan asalinta ba irinta.

Koda kuwa liman ne rataye saman kanta saboda kamun kai. Hakan da karin bata da inda zata yasa take shanye duk dukan nawaf.

Yai mata alfarma mai girma. Amman itama ta mishi. Tana tare dashi a duk cutar shaye shayen dake damunshi. Tana tare dashi a duk wannan stage din.

Ita ta bashi kwarin gwiwa ta zame mishi mudubi a lokacin da bashida inda zai duba fuskarshi. Ita ta zame mishi titin daya hau yagane hanya lokacin daya bace.

Itace silar shi zuwa rehab. Har aka shawo matsalar shi ta shaye shaye sannan sukai aure. Sannan yan uwanshi suka kauda kai daga mugun gidan da ta fito domin sunsan in babu ita zai iya komawa inda babu wanda zai iya taro shi.

Dafa kasa tai da niyyar tashi wani irin ihun azaba ta saki jin wani zogi datai yana har cikin ranta. Hannunta ta rike da dayan tana juyi saboda azaba.

Kuka take sosai. Dayan hannun mai lafiyar ta dafa dashi ta mike zaune hawaye na zubo mata. Ko ina na jikinta ciwo yake.

Mayafinta dake gefe ta janyo ta goge bakinta inda ya fashe sannan ta mayar gefen fuskarta tana flinching saboda zogin da wajen yake.

Jakar ta janyo ta fito da wayarta. Number din da farhan ya bata tun a napep ta haddaceta ta yaga takardar. Hannunta na rawa take shigar da number din ta kira ta kara a kunne tana wani irin kuka.......!

****

Hamma yaga Nana nayi. Yace mata.

"Bacci ko?"

Ta daga mishi kai. Janta yai ya kwantar da kanta a cinyarshi yana jin wata irin kaunarta na shigarshi.

Can kasan zuciyarshi wani abu na daban yana tafasa. Abinda ya kamata ace yana yi ne shekaru sha daya. Sai yau ya samu dama kawai saboda safiyya ta zabi ta boye mishi ita.

*

Sanda suka karasa gida Nana har tayi bacci. A hankali fu.ad ya daukota daga motar. Safiyya ta karasa ta bude musu gidan.

Kan kujera ya kwantar da Nana. Harya mike da sauri yace ma safiyya.

"Ba zata fado ba?"

Bata kalle shi ba ta amsa da.

"Damuwata ce wannan"

A kufule fu.ad yake kallonta.

"Me kike nufi?"

"Duk abinda ka fassara"

Motsi yaga Nana tayi. Da sauri yakai hannu ya dan tallabeta.

"Damn it sofi. Karta fado fa"

Sauke numfashi tayi. Ya soma isarta kuma.

"Kana ina shekara goma sha daya. Sai yaune zaka damu da fadowarta?

Kana ina ka tallabeta lokacin data fado duniya?

So please baka da wajenta a rayuwarka. Baka da lokacin asara a sonta. Karka dame ni"

Tafasa zuciyarshi take yi.

"Karki fara. Karki fara dora lefin akaina. Bana nan saboda baki neme ni ba.

Bana nan saboda kin zabi ki boyemun ita......."

Dakatar dashi tayi tana jin yanda yake taso mata da bacin ran data jima tana binnewa. Cikin idanuwan ta kalle shi.

"Ba kama ka nai na turaka waje ba. Kafafuwanka ka dauka ka fice.

Me kake tunani? Duk abinda nai *Akan so*nka bai isheka ba? Ko a lokacin inada sauran abinda ya rage in baka?

Na baka zuciyata fu.ad. Nabar duniyata na shigo taka. Nabar kowa nawa sabo dakai......"

Tana jin wasu hawaye masu dumi na zubo mata. Kallonta yake yana jin zuciyarshi na auna nauyin maganganunta.

Wani murmushi yai da baikai zuciyarshi ba.

"Sofi ba sai kin jefomun abinda kikai akaina a fuska ba. Ina sane dashi.

Saboda me ni ba zaki duba abinda nai akanki ba? Ba zaki duba girman abinda nai miki ba?"

Bata son ganin shi sam. Saboda yanda take tunanin dazun tsanarshi na gogewa daga zuciyarta shirme ne. Tana nan daram.

"Ka fitarmun daga gida please. Dan Allah ka tafi"

Nana ya kalla. Sannan ya sake kallon safiyya. Bai sake ce mata komai ba ya fice daga dakin. Son kai. Son kan sofi yayi yawa.

Da wannan tunanin a zuciyarshi har yakai titi ya tari taxi zuwa hotel din daya sauka.

****
Kwance yake kan kujera cikin falon gidan nashi. Kallon ko ina na dakin yake da irin kayan kawa na duniya dake ciki.

Wanda sam basuda amfani a wajenshi. Kirjinshi zafi yake mishi sosai. Tunda ya dawo numfashi yake yana tafiyar da komai yanda ya kamata ayi bawai dan yana jin dadin shi ba.

Dadin me zakaji na duniya in babu kowa daya rage maka wanda ka damu dashi? Nuriyya ce last hope dinshi na jin dadin rayuwa.

Ita kadai take ragemishi dayake jinta kamar family. Komai ya tarwatse mishi dayaji tayi aure. Yai yunkurin nemanta ya fasa saboda yana gudun kar ganinshi ya ja mata matsala.

Yasan ba kowane zai iya auren Nuriyya ba duba da inda ta fito. Wanda duk ya aureta dole yana sonta. Soboda yasan *Akan so*nta dole yai rikici da yan uwanshi akan asalinta.

Wannan dalilan su ya rike. Su suke tare shi daga neman nuriyya sai yau. Daya ganta inda bai taba zato ba. Ya kasa jurewa saida yai mata magana.

Saidai ga mamakinshi duk abinda ya hanashi nemota karya ne. Ba haka abin yake ba. Daga yanayinta kawai yasan meke faruwa a rayuwarta.

Saboda ba bakon abu bane a tashi rayuwar. Cikinshi ya taso tun wayanshi har ya zuwa yanzun. Ya kuma jima da sanin matan da suke cikin irin halin da nuriyya take ba karamar matsala bane.

Baka da yanda zakai ka taimaka musu inhar basu suka baka dama ba. Yagani akan mahaifiyarshi har rasuwa ta risketa.

Wayarshi datai ringing ba karamun taimaka mishi tai ba don harya soma saka wuka yana tona ciwukanshi. Wayar ya dauka da take ajiye kusa da kanshi. Bakuwar number ce.

Dagawa yai hadi da fadin.

"Hello?"

Murya a sarqe yaji ance.

"Yaya farhan....."

Da sauri ya mike daga kwanciyar da yake yana tattara dukkan hankalin shi kan wayar. Yasa hannu biyu ya riketa.

"Nuri. Nuriyya kina lafiya?"

Yana jin yanda kuka ke sarqeta ta cikin wayar dayake kona mishi rai.

"Nuri kimun magana. Dukanki yai ko?"

Dakyar ta iya cewa.

"Eh"

Wani abu dayaji ya taso mishi tun daga dan yatsan kafarshi yai tsaye a kirjinshi yana tafasa. In aka bashi bindiga maza masu dukan matansu zai fara harbewa.

Saboda babu zalincin dayakai wannan. Har wani huci yake. Muryarshi a dake yace.

"Calm down nuri. Bake kadai bace. I am here. Fadamun address din gidan"

Dakyar ta iya karanto mishi. Mikewa ya da wayar a kunnenshi ya dauki mukullin mota. Ko gidan bai ja ba. Ya karasa wajen motarshi yana fadin..

"Zanzo yanzun kinajina. Ki kulle dakinki. Karki bude mishi sai kinji na kiraki"

Bata amsa ba ta kashe wayar. Ya shiga mota yai baya da ita. Maigadi ya bude mishi ya fice daga gidan yana addu.a ya samu sanyi ko ya yake a zuciyarshi kamun ya karasa.

****
Yana zuwa alwala kawai yayi. Anan yai sallar azahar. Dan kamun ya fito ya nemi masallaci lokacin sallar yaja sosai.

Tunawa yai ya kamata yasa ma cikinshi wani abu duk da bakinshi baya so. Ordering fried rice yayi da farfesu. Dakyar ya iya cin rabi. Ya kira room services suka fita da kayan.

Wanka ya sake yi ya fito ya kwanta. Idanuwanshi ya rufe babu komai a cikinsu banda Nana. Dariyarta. Murmushinta zai iya rantsewa sautin muryarta har cikin zuciyarshi yake jinta.

Bacci ya dauke shi cike da mafarkin Nana.

*

Sanda ya tashi har anyi Asr. Dan haka sallah yayi. Yana zaune a inda yai sallah wayarshi ta hau ringing. Dagawa yayi yaga num din lukman.

Ya amsa da fadin.

"Hello......"

"Kuna asibitin ne har yanzun?"

A sanyaye yace.

"Aa an sallame su. Suna gida. Ni ina hotel din dana sauka"

Tambaya lukman yai ko a ina ne. Ya fada mishi yace ya jira shi gashi nan zuwa.

Ko mintina talatin ba aiba ya sake kiran fu.ad cewar yana wajen hotel din. Wayarshi ya dauka da mukullan dakin ya fito.

*

A mota ya samu lukman zaune. Ya bude ya shiga. Shiru sukai su duka kowa ya rasa me zaice ma kowa kamin fu.ad yace.

"This is awkward"

Dariya lukman yayi.

"Bansan ta inda zan fara ba"

Murmushi fu.ad yayi hadi da fadin.

"Banda abin fada. Daga lokacin dana tafi babu komai a rayuwata banda ball. So banda abin fadi"

Nisawa lukman yayi.

"Ina da zainab. Da junior da wani yana hanya mace ko namiji"

Da mamaki fu.ad ya kalle shi.

"Kana da mata da yaro lukman?"

Kai ya daga mishi. Wani nauyi zuciyarshi tayi. Baisan ta inda zqi fara kamo abubuwan daya saki ba.

"Ina jin nauyin ince ka kaini in gansu lukman"

Shi kanshi wani iri yake ji. Sun rasa abubuwa da yawa a tsakaninsu. Da wani yanayi a muryarshi yace.

"Kiran da zakayi shegen taurin kai ya hanaka"

Dariya fu.ad yayi.

"Irin wanda ya hanaka kirana ko?"

"Shut up"

Lukman ya fadi yana tayar da motar. Fu.ad baice komai ba har suka nufi hanyar dayake tunanin gidan lukman ne.

Yanda rayuwa ta tafi da sauri haka yake mamaki. Bashida komai da yake kallo balle yaga gudunta.........!

*#TeamAS*
[7/9, 1:18 PM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[7/9, 1:18 PM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: AKAN SO 35
*πŸ’˜πŸ’–AKAN SOπŸ’–πŸ’˜*

~Written by~ :Luβπα SufyΞ±Ο€

35

*Haka Allah yake ikon shi. Lokaci daya sai ya aiko maka da mutanen da zakaji kaman ka sansu tun farkon halittarka. You are not only a friend but a sister. I don't have to mention her name. ALLAH YA SADAKI DA DUKKAN ALKHAIRI SIS YAF*

*Saqon addu.o.inku ya sameni. Nagode. Tabbas #AnaTare*

Kuka take sosai. Can kasan ranta wani abu na fada mata babban kuskure tayi na kiran farhan. Idan kuma haukan nawaf ya hada dashi fa?

Ba zata taba yafe ma kanta ba in wani abu ya same shi ta sanadinta. Daga wani bangaren kuma yana gaya mata kome nawaf yai mata bai kamata ace tabarshi ba.

Yana tare da ita lokacin da take da bukatar taimako itama. Kamun ta karasa tunanin wayarta ta katse ta.

Tana dubawa taga number din farhan ne gabanta ya fadi. Salati ta shiga jerowa hadi da mikewa dakyar.

Wata azaba ta ratsata har tsakiyar kanta saboda zafin da taji a hannunta. Tallabe shi tai sabbin hawaye na zubo mata.

Dakyar ta iya daukar mayafinta ta dan yafashi. Ta riqe wayarta hadi da hannunta da take jinshi ba daidai ba. Tai waje.

Kallo maigadi yabita dashi. Tana fita kofar gida taga motar farhan yana ciki a zaune. Karasawa tayi ya miqo hannu ya bude mata murfin.

Tana shiga farhan ya kalli fuskarta yace.

"Ya Ilahi. Nuri......."

Yama rasa me zaice. Kowaye nuri ta aura zai iya cewa rashin tausayinsu in baizo daya da babanshi ba kadan ya hana.

Inba rashin imani da dabbanci ba. Baiga abinda zaisa ka ware karfi kana ma mace wannan dukan ba. Duk ya fasa mata fuska.

Yanda ta runtsa idanuwa ta sake dafa hannu yasa shi saurin kai idanshi wajen. A tsorace yace.

"Nuri saki hannun nan mugani"

Batai musu ba ta saki hannu. Wani zogi da radadi yasa idanuwanta suka kawo hawaye. Girgiza kai farhan yayi.

Ji yake kaman a bashi bindiga a ajiye mishi nawaf yaita harbi sai yaga babu sauran rai a jikinshi. Ya karyata. Hanunta a karye yake.

Wani daci yake ji a ranshi. Zuciyarshi na hango mishi mamanshi a kwance jini na binta. Yana hango abubuwa da dama na rayuwar shi.

Tayar da motar yayi suka nufi amini kano. Bai tsaya bata lokaci ba ya nemi wani abokinshi dake aiki a wajen. Dan yasan yanayin Nuri ba zasu kula su ba babu yan' sanda.

Shiya tsaya musu aka karbi Nuri farhan ya samu waje ya zauna da wani irin nauyi a zuciyarshi. Abu dayane yake gani.

Ko garin kano zata hade sai ya raba Nuri da wannan azzalumin. Koda zai mutu yana kokari kuwa. Daga kan mamanshi yai rantsuwa sai inda karfin shi ya kare akan masu irin wannan halin.

*

Bai san inda yake ba. Tunda ya dauki mota kawai tuqi yake. Harya samu waje yai parking. Kanshi ya hade da sitiyarin motar.

Zuciyarshi kuna take kaman ana zuba mata garwashi. Da ace yana da tabin hankali sai aima haukan daya sauke kan Nuri uzuri.

Runtse idanuwanshi yayi yana hango yanda ya taka mata fuska. Wani irin ihu ya saki daya fito daga maqoshin shi.

Kanshi ya daga ya doka kan sitiyarin motar. Yana maraba da zogin daya ziyarce shi. Kuka yake saboda komai ya masa zafi.

Gabaki daya duniyar ta hade mishi. Halin dayabar Nuri yake tunawa. Tayar da motar yayi yaja ta da karfin gaske yana hawan titi.

Gida ya wuce kanshi tsaye. Yana parking ko kashe motar bai tsaya yi ba ya wuce cikin gida da gudu.

Jini ne a falon kan tiles din. Bango ya dafa yana jin yanda kafafuwanshi ke son kasa daukar shi. Baisan ya mata wannan dukan ba.

Baisan inda hankalinshi yake ba.

"Nuri!!!....."

Ya kira da wata irin murya. Da bin bango idanuwanshi kafe kan jinin dake kwance kasa kaman wanda zai taso ya kama shi yake tafiya.

Kamun ya juya ya shiga dakin su. Bata ciki. Da karfi ya shiga kwala mata kira. Babu inda bai duba ba na gidan amman bata nan

Da gudu ya fito ya tambayi maigadi ko yaga Nuri yace mishi ta fice. Dafe kai yayi da hannayenshi biyu. Shikenan ya rasata.

Motarshi ya shiga. Ya jata. Yanda ya figi motar har maigadi saida ya tsorata. Yana hanya ya lalubo wayarshi ya kira yayanshi.

Bugu daya ya daga. Yana wani irin kokawa da numfashin shi yake fadin.

"Yaya nuri. Nuriyya ta tafi........"

Magana yayan nashi yake amman bayajin komai cikin kunnuwanshi da kanshi sai kalma daya. Sakin wayar yayi yana jin wani luuu.

Kamun ya saki motar gabaki daya ya dafe kanshi dake wani juya mishi. Hakan yasa motar ta kwace daga hannunshi ji kake wani quuuuuuuu.

Sama nawaf yaji motar tayi. Yana jinta ta dawo kasa dashi. Tana jujjuyawa kamun ya daina jin sautin komai cikin kunnuwanshi.

Wani abu yaji yana bin fuskarshi kamun wani irin duhu mai tsanani ya lillibe komai na duniyarshi...........!

****

Suna parking din motar hassan na fitowa daga gidan dauke da junior saman wuyanshi suna hira. Kallon shi fu.ad yake yi.

Lokaci daya ya hango hassan din daya bari. Ya kalli wannan saurayin dake tahowa. Baxai iya fassara abinda yake ji a zuciyarshi ba saboda baisan komenene ba.

Idanuwa ya dago ya fara sauke su kan lukman da yace mishi.

"Hassan ana ganinka daman"

Sam bai kula da fu.ad ba. Yar dariya yai ya amsa da.

"Ina wuni. Wallahi aiki babu lokaci sosai. Yanzun ma naje gidan yaya haneef nace bara na biyo........"

Kasa karasa maganar yai ganin fu.ad. A hankali duk fara.ar dake fuskarshi ta soma dakushewa har ya zamana babu ita ko kadan.

Junior ya sakko daga kan wuyanshi zuwa kasa. Da gudu ya ruga wajen lukman ya rike hannunshi.

A dakile hassan ya dauke idanuwanshi daga kan fu.ad ya mayar kan lukman.

"Zan wuce. Sai anjima....."

"Hassan......."

Fu.ad ya kira. Banza yai ya kyale shi. Yana karasawa inda machine dinshi yake ajiye ya hau. Kallon lukman fu.ad yayi. Yadan ware mishi idanuwa dake fassara babu ruwana.

Da hanzari fu.ad ya karasa inda hassan yake yana kokarin tayar da machine dinshi. Hannu yasa kan handle din machine din ya riqe dam.

Gefe hassan ya kalla dan baya son sake ganin fuskar fu.ad dinma kwata kwata. Zagayawa fu.ad yayi muryarshi a sauke yace.

"Hassan"

Batare da nuna alamar sanayya ba yace.

"Sannun ka fa"

Yaji yanayin muryarshi sarai. Ya share da fadin.

"Hassan please mana. Ka daina mun magana kaman yau ka fara ganina"

Sai lokacin ya ware idanuwanshi kan fuskar fu.ad din. Ranshi a bace yace.

"Nasanka ne?"

Dan runtsa idanuwa fu.ad yayi ya budesu.

"Harshenka bazai canza matsayina a wajenka ba"

Kallon mamaki hassan ke mishi kamun yace.

"Wanne matsayi kenan?"

Ya wani kankance idanuwa. Fu.ad ya amsa shi da.

"Yayanka"

Wata irin dariya hassan yai. Kamun lokaci daya ya hade rai. Ya hanga mishi lukman dake tsaye rike da junior.

"Kaga wancen shine yayana. Yaya haneef. Babban yaya. Banda su banda wani yaya.

Oh na manta da wanda ya yarda mu kaman bamu taba hada alaqa dashi ba. Now if you will excuse me inada abin da zanyi....."

Kokarin jan machine din yake fu.ad ya riqe dam.

"Saboda me yasa baka kirani ba? Ko da yake ba wannan ba. Kawai zanji ya kake"

Cikin idanuwa ya kalli fu.ad. Da gaske yake tambayar dayai. Yaga

Please Login or Register in order to submit comment