Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jeroma Ubangiji da kalar ni.imar dayai mata.

Bata san iya lokacin data dauka a haka ba. Sam bataji shigowar jabir ba saida ya hawo kan gadon inda take ya sumbaci kuncinta.

"Honey j"

Ta furta a sanyaye tana bude idanuwanta kan fuskarshi. Murmushi tai mishi. Ya mayar mata.

"Naji kana kamshi. Ko ayna ta feso maka turaren angonci tun yanzun"

Tana kallon yanda sonta ke yawo cikin idanuwanshi. Mamakinta jabir yake sosai. Yana kuma jin tsoro can kasan zuciyarshi kar sai anyi auren ta birkice masa.

Sauke murya yai.

"Jana. Are you okay kuwa?"

Saida ta mintsinar mishi kunci sannan tace.

"Me yasa kake tambaya?"

Gyara zamanshi yayi kan gadon sosai ya kwanta rigingine kaman yanda take. Kanshi yaja ya hada da nata sannan ya soma magana cikin sanyin murya.

"Na kasa yarda cewar bakya bani matsala dan zan kara aure. Ina jin kaman kina boye komai ne a kasan ranki. Ina jin kaman zaki iya birkicemun in anyi auren nan"

Kanta ta juyo ta sa idanuwanta cikin nashi. Takai hannu ta kamo nashi hannun sosai take kallonshi.

"Honey j yau na sake ganin abinda ya kara karyamun zuciya. Yau naga abinda rayuwa take tattare dashi mai muni da kunci.

Ko kamun ingani kishi na dawainiya dani. Kuma har yanzun bai daina ba. Sai dai banida dalilin damuwa inhar ina ganin wannan soyayyar cikin idanuwanka.

Fatana daya kar wani abu ya canza ta"

Sauke numfashi yai.

"Ina sonki sosai jana. Nagode da kalar kaunar da kika nunamun. Allah yasa kece matata har a aljanna"

Sosai taji dadin addu.arshi. Itama tata takeyi musu. Allah ya basu zama na fahimta ya bashi zuciyar yi musu adalci.

Hannunta ta dora kan cikinshi sannan tace.

"Kaci abinci?"

Hannunshi ya dora kan nata.

"Ina zanci abinci naki yana jirana?"

Dariya tayi tana mikewa. Ta sauka daga kan gadon. Ta zagayo. Saida ta rankwafa sannan ta sumbaci gefen fuskarshi.

Hannu yasa ya kama kanta ya sumbace ta a labba sannan yai mata rada a cikin kunnenta. Dariya tai sosai tana girgiza kai.

"Ka tashi nikam muje muci abinci"

"Duk abinda uwargida take so"

Ya fadi da murmushi. Girgiza kai kawai tai ta wuce da wata kaunar shi mai nauyi a zuciyarta.......!

****

Ya rasa abinda yake masa dadi a zuciyarshi. Sam tunda ya koma gida ummie ma da tazo tana tambaya cayai mata ba komai.

Karantar datai baya son surutun yasa taba shi waje. Ya kuma ji dadin hakan ba kadan ba. Wayarshi ya dauko ya nemo number din pha.iza ya kira.

Ringing din farko ta daga hadi da yi mishi sallama ya amsa mata ta dora da fadin.

"Kowa lafiya dai ko yaya haneef?"

"Hmm pha.iza ya mukai dake?"

Ya bukata yana tuna maganar dayai mata tun jiya. Dan saida ya fara kiran abdulkadir mijinta ya roke shi daya barta tazo asibitin yau kamun ma yai mata magana.

Shiru ta danyi kamun ta ciki ciki ta amsa shi da.

"Kayi hakuri yaya haneef. In shaa Allah zan samu lokaci inzo. Kawai zuciyata ce ta kasa hakura wallahi"

Dafe kai haneef yai. Yau yaga rayuwa ba komai bace ba. Yar yarinya ma kenan da bata da wani zunubi mai yawa Allah ya dora mata wannan ina gasu.

"pha.iza kijini. Gabaki daya rayuwar nan bata da tsaho. Mu dukanmu munyi kuskure da muka zabi mu share fu.ad kaman yanda yai mana.

Daya mutu fa? Ban fada miki yarshi bata da lafiya ba? Yar karama ce. In kika ganta zaki sota sai dai cancer take fama da.

Allah baiyi rayuwarta zatai tsayi ba. Fu.ad na bukatar soyayyarmu ne ba fushin mu ba pha.iza.

Dan Allah ku yafe mishi yaji da abu daya"

Yana jin yanda ta amsa da

"In shaa Allah"

Dakyar sannan ta kashe wayar yasan kuka take. Sauke wayar yai yana tunanin yanda rayuwa zata iya birkice maka cikin kankanin lokaci.

****

Tunda Ansar yazo suke zaune su duka hudun a falon an rasa wanda zai fara magana.

Nufin safiyya su dukansu in Nana tana ganin su zasu iya comforting din ta. Amman abin ya gagara. Rashin iyayenta zafin shi dabanne a zuciyarta.

Bata san asalin ciwon da zuciya zata iya ji ba sai yanzun. Tasan babu wanda zai fahimce ta sai wadda tasan dadin haihuwa.

Sai wadda tasan me rayuwa da d'a yake. Dan daka raina har tsayin shekara goma sha daya. Ki jariri ne ka rasa hakan nada ciwo sosai balle wanda irin wannan shakuwar ta shiga tsakaninku.

Mikewa daga kan kujera nana tai inda take zaune kusa da fu.ad. Yana kallonta ta taka har ta karasa inda sofi ke zaune kan kafet tayi shiru.

Zama Nana tayi ta na matsawa sosai kusa da safiyya. Hannuwanta ta bude ta rungume ta. Sosai ta matse sofi a jikinta.

Wani irin kuka marar sauti ne ya kwace ma sofi. Ita ya kamata tai ma Nana wannan bawai ita ta lallashe ta ba.

Tissue din dake hannun ansar yasa yana goge idanuwanshi da yake jin sun kawo hawaye.

Bazai manta shekaru hudu Kenan da kaddara ta hadashi da safiyya. Taje neman aiki a company din da yake aiki.

Tun daga ranar ta shiga zuciyarshi. Hakan bai karu ba sai lokacin dayaga Nana. Itace sanadin shakuwar su da safiyya har yaji labarinta.

Nana ta hadasu. Bazai manta yarinyar ba da lafiyarta. Yarinyar da duk wanda zai ganta sau daya zai jima bai mantata ba.

Bazai manta shekaru biyu da sanin su dayai ba Nana ta fara wannan rashin lafiyar. Yana tare dasu a duk lokacin nan.

Duk da bai aure da wuri ba. Kuma matarshi har yanzun Allah bai azurta su da samun haihuwa ba tun bayan barin datai bai hana shi jin nana kamar yarshi ba.

Yana kaunar yarinyar har ranshi. Kuma ko shi yasa rai da samun lafiyarta. Sai yau din nan da safiyya ta fada mishi.

Sosai abin ya tabashi. Yanzun kam ganin yanda suke manne da juna da safiyya ya kara karyar mishi da zuciya sosai.

Fu.ad kallon su yake. Yana kokarin tarbe nashi hawayen. Zai zama strong for Nana. Ta roqi hakan daga wajen shi. Bai gaba ganin yarinya mai karancin shekaru irinta ba tunda yake.

Duk dai bawai yaga yara da yawa bane. Yana jin ita din ta dabance ba kuma dan tana jininshi ba. Ansar yake kallo yanda gabaki daya ya birkice.

Sai yanzun yaga tsantsar kaunar da yake ma Nana. Kuma zuciyarshi ba zata taba manta wannan ba. A hankali nana ta janye jikinta daga na safiyya.

Tasa hannu tana goge mata fuska. Kamun ta mike. Wajen Ansar ta nufa da yake kan kujera a zaune. A tsayen da take ta bude hannuwanta shima tai hugging dinshi.

"I love you. I love you so much uncle Ansar"

Take fadi cikin Kunnuwanshi. Kai kawai yake dagawa yana riketa a jikinshi a hankali.

Saboda yanajin kalar ramar datayi ta cikin rigarta. Ji yake daya matse ta sosai zai iya karyata. Dagota yai ya sumbaci goshinta da kuncinta kamun ya sake riketa a jikinshi.

Magana tai mishi cikin kunne yanda shi kadai zaiji.

"Can you do me a favour?"

Muryarshi a dakushe shima cikin rada yace.

"Ko menene ki fada nana"

Sai da ta sauke ajiyar zuciya yana ji kamun tace.

"banida lokaci mai yawa. Ina son maida auren su mumy. Kana son mumy kaima ko?

Nasan ba zaka ji dadi ba"

Yar dariya ansar yayi. Tabbas Nana ta koyar dashi abubuwa da yawa. Ciki har da karfin hali. A hankali ya amsa ta da.

"Umm Nana bazan iya da dadynkin nan ba. Na bar mishi"

Dariya tai cikin kunnenshi daya sa shi dariya shima. Tun daga sanda yasan safiyya ya karanci wajen mutum daya take dashi a zuciyarta.

Koda yana sonta dole zai hakura. Kaunar dayake mata yana jinta kamar yar uwarshi ne. Nana ta katse mishi tunaninshi da fadin.

"You are the best uncle Ansar. I love you"

Lumshe idanuwanshi yai. Rashinta zai bar wani waje mai girma a zuciyarshi.

"I love you more princess din mumynta"

Fu.ad kam ji yake daman shi aka runguma haka. Kota ina bukatar lallashi yake. So yake wani ya lallashe shi har sai ya fitar da dukkan ciwon nan da yake cikin zuciyarshi.

Sai yanzun ya fahimci abin da Nana tace da ta fadi mishi tana tsoron mutuwa. Ba tsoro take ji wa kanta ba.

Tana tsoron abinda mutuwarta zatayiwa wanda take kauna. Zai iya rantsewa Nana ta dabance. Komai nata. Maganganunta da hankalinta ya girmi shekarunta nesa ba kusa ba.

Tana tsoron abinda mutuwarta zataiwa mamanta. She is the strongest girl daya taba gani a rayuwarshi.

Yana kallo tana takowa zuwa inda take. Saidai yasan ko zuciyar da take da kwari irin tata tana bukatar tallabi.

Kokarin saka kanshi yake a matsayinta ya kasa gane me zaiji ace yau yasan a hankali a hankali komai nashi na lalacewa.

A lokaci daya kuma yana jin ya kamata ya zama strong saboda halin da zai saka wanda yake kauna a ciki amman ya kasa fahimta.

Harta karaso kusa dashi kirjinshi kaman an kunna mishi wuta saboda zafin da yake masa. Goshinta ta hada dana shi tana tallabar fuskarshi da hannuwanta.

Yasan kwarin gwiwa take son samu daga wajen shi. Duk yanda yake jin kaman numfashin shi zai tsaya bai hana shi yin alkawarin zai zamar mata abinda take bukata ba.

Bashida wani abu dazai bata. Yana jin hucin numfashinta da take fitarwa akan fuskarshi ya ki yarda su hada idanuwa saboda baya son taga raunin da take dashi.

"Nagaji sosai. Bacci nakeji"

Ta fadi muryarta na wani irin sauka kasa sosai. Bashi bane a matsayinta amman a gajiye yake. Saida yasa hannuwanshi ya dorata kan kafadarshi sannan ya mike da ita.

Dakin dayakaita rannan ya nufa. Bai ajiyeta ko ina ba sai kan gadon a hankali. Ya gyara mata kwanciya. Ya zauna gefen gadon.

Idanuwanta ta lumshe ta dora hannunta kan cinyarshi hadi da fadin.

"Dady!!!"

Saida kalmar ta amsa yafi a kirga cikin kunnuwanshi sannan ta samu wajen zama a zuciyarshi. Wani irin abu yake ji da bazai fadu ba.

Sai maimaita kalmar yake yi. Cikin kanshi yana jin tana zama wajaje da yawa. Baisan yana bukatar jin ta kira shi haka ba sai yanzun.

Da sauri yasa hannu yana goge hawayen da yake jin kaman su fito mishi dan baya son ta bude ido tagani. Jin yai shiru yasa ta fadin.

"Zan iya kiranka dady?"

Da sauri yace.

"zan fi kowa sa.a in kika kirani haka princess"

Murmushi tai hadi dayin hamma. Tai shiru yana kallon yanda numfashinta ya canza alamar bacci ya dauketa. Gyara mata hannunta yayi.

Ya mike ya zuba mata idanuwa na wani lokaci. Baya son fita daga dakin yana son ya kalleta sosai. Yaita kallonta kamun tabarshi.

Saidai a yanzun yana bukatar yadan jinyaci ciwukan dake kirjinshi ko dana yan awanni ne. A hankali ya fice daga dakin yana ja mata kofar.

Baisan yana rike da wani numfashi ba sai yanzun ya sauke shi. Inda yabarsu safiyya nan ya same su. Kanshi a kasa ya nufi kofa sannan yace musu.

"Tayi bacci"

Bai jira amsar da zasu bashi ba ya fice daga dakin........!

*#TeamAs*
[7/9, 1:21 PM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: *_POST BY GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100_ πŸ“šπŸ“š_*
[7/9, 1:22 PM] πŸ…° "πŸ…° " D'πŸ…±β­•YπŸ”›πŸ”: AKAN SO 39
*πŸ’˜πŸ’–AKAN SOπŸ’–πŸ’˜*

~Written by~ :Luβπα SufyΞ±Ο€

39

*Mutane da yawa na fadin sunyi sa.a a rayuwarsu. Nagane hakan lokacin da rayuwa taimun kyautar kanwar da Allah baisa mahaifiya zata bani ba*

*ZAPHIRA ke kyauta ce a gareni daga Allah. Ina miki fatan alkhairi a komai na rayuwarki. Ba saina fadi yanda nake kaunarki ba. Kema kinsani*

*Sorry saboda rashin jina kwaba biyu. Ina busy ne sosai bana samun damar typing sosai. Godiya da kaunarku. ILYA*

*#AnaTare*

Sosai ya riko zee jikinshi.

"Nagode sweetheart. Ban taba zaton zaki fahimce ni ba"

Hawayen daya taru a idanuwanta taji ya zubo. Tasa hannu ta goge su. Muryarta can kasa tace.

"Haba dee. Da zuciya a kirjina fa. Waye zaiki fahimtarka"

Har cikin ranshi lukman yake jinta. Baisan wanne kalar so zainab ke masa ba. Zai iya cewa yafi kowa dace da mata irinta.

****

Zaune yake ya hada kanshi da gwiwa. Bazai ce ga iya abinda yake damun shi ba. Komai ciwo yake mishi.

Tun daga zuciyarshi. Kanshi da koma ina na jikinshi. Yanajin kaman mota tabi takanshi sai dai babu wani ciwo a jikinshi daga waje.

Daga ciki yake jin ciwon. Mikewa yayi. Zaman nan bazai mishi ba. Zaman nan bashi Nana take bukata ba. Tana bukatar yayi setting komai.

Ya roki yafiyar zunubansa datake biya. Dan haka ya mike ya ja iska ya fitar da ita ta bakinshi hadi da ficewa ya kulle dakin yasa key din a aljihun shi.

*

Tun da taxi ta ajiye shi bakin kofar gidansu abinda yai saura daga zuciyarshi yake wani irin dokawa.

Ga wata zufa har cikin tafin hannun shi. Koda maigadi ya bude masa yake tambayarshi wa yake nema.

Kallonshi kawai yai. Ya rasa me zaice. Yau shi ake tambaya wayake nema cikin gidansu. Kalle kalle yake kaman yaune rana ta farko daya taba shigowa gidan.

Komai na nan yanda yasan shi. Wata irin ajiyar zuciya ya sauke yabar maigadin nan tsaye yana binshi da kallo. Da Alama ya mishi kama da yan gidan shisa ya kyale shi.

Da wani nauyi kafafuwanshi ke takawa har suka kaishi cikin gidan. Kaman a lokacin ranar daya bar gidan ya faru haka abin ke masa yawo cikin idanuwa.

Komai na dakin shine banda furnitures. Zai iya rantsewa yana kallon su wani lokaci can baya su duka zaune suna hira.

Wata irin kewar hakan ta saukar mishi. Cikin muryar dabai gane tashi bace yai sallama. Jin shiru ya sake sashi daga murya da sake yin
sallamar.

****

Tunda ta dawo gida ta kasa daina zubda kwalla. Nana ta tsaya mata a rai ba kadan ba. Dakyar ta iya samu ta watsa ruwa.

Haka abbah ya dawo ya sameta. Shima ruwan ya watsa yaci abinci suka zauna falonsu yana kallon tashar Nat geo. Yana kallon abubuwan al.ajabi.

Remote control din dake hannunshi ya ajiye gefe ya fuskanci momma datai nisa cikin tunani. Saida yai magana sau uku bata ji ba ya tabata.

"Meke damunki?"

Cikin sanyin murya tace.

"Baka son jin wannan matsalar nasani"

Da mamaki ya ce.

"Wanne irin magana ne wannan. Abinda yake damunki ai yana damuna ne"

Sauke ajiyar zuciya momma tayi. Cikin nutsuwa ta fada mishi duk abinda yake faruwa. Lumshe idanuwanshi yai yana jin wani irin abu na mishi yawo a zuciya.

Tun ran da fu.ad yasa kafa yabar gidan abin yake manne da zuciyar shi. Bai ya nunawa ne kawai bawai dan baya damun shi ba.

Bacin rai yasa shi yai furucin dayai ba wani abu ba. Bai taba dauka fu.ad zai tafi yaki waiwayarsu ba. Ya dauka abune na karamun lokaci.

Zai gane yayi laifi yazo ya roqi gafararsu komai ya wuce. Ya kasa ko da furta ma momma cewar yana kewar dan nashi kaman yanda take yi.

Yana son sake ganin shi ko sau dayane domin mutuwa ba sallama take ba. Bacin rai duk shi ya hana. Yanzun da take fada mishi maganar Nana har ranshi yake jin dacin abin.

Yasan bakinshi ne ke dawainiya da fu.ad. Fushin daya dauka ne. Hakika fushin iyaye babbar musifa ce ga yayansu.

"Baka ce komai ba"

Momma ta fadi muryarta na rawa. Ya kasa kallonta. Idanuwanshi a kasa yace.

"Ina fu.ad din yanzun?"

Girgiza mishi kai tayi.

"Haneef yace ya sauka a hotel ne. Ban san kowanne ba"

Bude baki abbah yayi zai sake magana suka ji sallama. Saurarawa suka yi. Sallamar suka sake ji wannan karin da dan karfi.

*

Fitowa su momma sukayi tare ita da Abbah dan su dukansu sunji kaman muryar fu.ad din.

In da ya dauka zuciyarshi dokawa take ba komai bane akan yanda yake jinta yanzun. Zai iya cewa su momma dake tsaye suna ganin hakan ta cikin rigarshi.

Hannu yakai wajen ya danna yana kokarin saita zuxiyarshi daga dokawar da take yi. Bakin shi na rawa idanuwanshi kafe kan abbah yace.

"A.... Abbah....."

Kallon shi abbah yake. Ya girma sosai kaman ba fu.ad din shin nan ba. Dan shi daya fi so fiye da kowanne cikin yayanshi ko da baya nunawa.

Yana kallon fu.ad din na takowa zuwa inda yake. Ya kasa cewa komai. Kallon shi yake yana tuna tsahon shekarun da suka wuce bai neme su ba.

Baisan yanda akai kafafuwanshi ke kaishi wajen abbah ba. Zai iya cewa tsantsar kaunar shi da yake yine a zuciyarshi ke janshi.

Saboda a shekarun nan yaki barin zuciyarshi ta fada mishi yanda yai kewar abbah. Yana amfani da fushin da yake yi dashi ne yana danne komai.

Inda Abba yake ya karasa. Hannuwan abbah ya fara kamawa ya sumbata duka biyun. Wani irin abu yake ji yana masa yawo.

Baisan lokacin da kafafuwanshi suka kasa daukar shi ba. Tsugunnawa yai yana sakin hannun abbah. Da duk hannayenshi ya rike kafafuwan abbah.

Duk abinda yake daurewa tun dazun ne yake dawo mishi. Ciwon da yake ji. Dacin da yake ji. Rashin adalcin da rayuwa ke mishi ta kowanne fanni.

Baisan lokacin da hawaye suka fara zubar mishi ba. Kan gwiwoyin shi ya koma ya sake rike kafafuwan abbah dam yana wani irin kuka marar sauti.

Gabaki daya jikinshi rawa yake. Ko ina na jikinshi bari yake. So yake yace abbah ya yafe mishi kalma ko daya taqi fitowa daga bakinshi.

So yake ya fada ma abbah yau yaga wautar daya aikata. So yake ya fada mishi yau yagane amfanin neman shawara. Yagane irin kaunar da suke mishi. Ya gane ba takura mishi suke yi ba.

Ya gane irin wannan ranar suke guje mishi. Yana jin abbah ya tsugunno yana riko shi da nufin ya dago shi daga jikinshi.

Girgiza mishi kai yake. Hawayen harda wanda yaki bari ya zubar lokacin daya tafi yau sun samu hanya.

Dole sai abbah ya tsugunna hannuwan fu.ad ya riko muryarshi dauke da yanayi na tausayawa da kaunar dan nashi yace.

"Fu.ad kai controlling kanka. Saika ce mace. Da karfin hali aka san namiji"

Girgiza kai fu.ad yai. Yana kamo hannuwan abbah yasa fuskar shi a cikin su. Yau lallashi yake bukata. Mahaifin shi yake bukata.

Cikin kuka muryarshi na wani irin sarqewa yake fadin.

"Abbah nagane soyayyarku mai girma ce a gareni. Wallahi nagane duk wata soyayya kasa take data iyaye.

Abbah ka yafemun. Ka yafemun ko zan samu inga dai daina rayuwata......."

Hawaye yaci gaba da zubdawa yana damtse hannayen abbah kaman karamin yaro. Momma dake tsaye itama ta kasa tarbe nata hawayen.

Kallonta fu.ad yai da fuskar shi da harta kumbura.

"Ku yafemun. Dan Allah ku yafemun....."

Muryar abbah na rawa yace.

"Na yafe maka fu.ad. Na yafe maka duniya da lahira"

Wani irin sanyi yake ji yana ratsa shi na daban. Momma ya kalla. Kai kawai take iya daga mishi alamar itama ta yafe mishi. Ta dade da yafe mishi.

Kallon abbah yai sosai. Idanuwanshi na sake cika da da wasu hawayen.

"Abbah mutuwa zatai. Nana zata mutu. Abbah ku taimakamun ita kadai nake da a duniya.

Nayi wautar da in ta tafi bazan sake sanin meye dadin da ya kalleka cike da kauna a idanuwanshi ba.

Bazan sake sanin.......abbah"

Kasa karasawa yai yanda yakejin numfashin shi har wani sama sama yake yi. Dakyar abbah ya kamashi yaja shi kan kujera ya zaunar dashi.

Nasiha ya shiga yi mishi da nuna mishi girman yadda da kaddara a musulunce. Jikin fu.ad ya kara yin sanyi.

Momma ta kawo mishi ruwa ya sha. Suna nan zaune aka kira magrib. Bangaren abbah fu.ad din yabi shi sukai alwala suka fita masallaci tare.

*

Tare suka ci abinci a plate daya. Sai dai duk wani motsi da fu.ad zai saiya sake kallon abbah yace.

"Abbah ka yafemun"

Saida ya gaji yace mishi.

"Fu.ad komai ya wuce. Anan zaka kwana yau. Gobe kaje ka kwaso kayanka ka dawo gida...."

Kai ya jinjina ma abbah alamar yaji. Wata irin girmamawa ta daban yake jin yana musu. Wata irin kauna daya san ko rabin wadda suke mishi bata kai ba.

Wanda ya haihu yasan meye dane kawai zai iya sanin girman kauna har haka.

Har sukaje sallar isha.i da abbah suka dawo. Dakin shi tun nada momma ta bashi mukullin ya wuce.

Yai mamakin ganin dakin fes. Komai na nan babu abinda aka canza. Wani irin abu yaji na daban na masa yawo.

Duk wanda ya dauki soyayyar iyaye abin wasa hakika yana daya daga cikin marassa rabo.

Kwanciya yai yanajin sanannen yanayin dake cikin dakin na nutsar dashi. Yau zai huta. Yau zaiyi jinyar ciwukanshi. Zai tattara duk wani strength daya san Nana na bukata daga wajen shi.

****

Tunda ta tashi ta zabi kayan Nana data san tafi so. Wata doguwar riga ce ta atamfa purple.

Ta dauko mata takalmanta da hijab purple. Dan sunyi da yusra zata zo karfe goma na safiyar ranar dan suyi magana da Nana.

Kitchen take tana soya kwai nana ta shigo. Sanye take da riga da wanda kanta da hula. Duk ramar datai bai hana safiyya ganin tayi mata wani irin kyau daya taba mata zuciya ba.

Kujera ta janyo ta hau sama. Safiyya ta lumshe idanuwa.

"Nana na hanaki tsayuwa kan kujerar nan. Sai kin fado ko?"

Dariya tai tana leqa frying pan din da safiyyar ke soya kwai hadi da fadin.

"Na tsaya da kyau bazan fado ba. Mumy in tambayeki?"

Saida ta juya wainar kwan dake ciki sannan ta amsa da.

"Uhum ina jinki"

Shiru tadanyi na wani lokaci.

"Kinyi alkawari ba zakiyi kuka ba in na tambaya?"

Wani miyau safiyya ta hadiye dan tun kamun ma ta tambaya din taji hawaye na taruwa a idanuwanta. Muryarta a sarqe tace.

"Ina jinki"

"Menene soyayya? Ya ake ji in ana soyayya?"

Cike da mamaki safiyya tace.

"Me yasa kike tambaya?"

"Oh oh mumy. Karki yi kuka please idan na fada miki"

Jinjina mata kai tayi. Idanuwa nana ta ware kan fuskarta hadi da fadin.

"Saboda nasan bazan girman da zansan ya akeji ba shisa nake so ki fadamun"

Abun dake tsaye wuyanta take ta so ta hadiye ta kasa. Dan gyaran murya tai tana kifta idanuwanta cikin son maida hawayen dake son zubo mata.

Kettle ta dauko ta dora musu ruwan zafi sannan ta fuskanci Nana tace.

"Soyayya wani abune mai girma Nana. Babu kalaman da zaka dora girmanta akai. Wani irin yanayi ne na daban"

A nutse Nana ke kallonta tana son fahimtar me take fada. Kamun taci gaba da cewa.

"Lokacin da kake son wani zakaji zuciyarka ta cika. Bata gane komai sai wannan yanayin.

Zakaji kaman daman can an halitta maka zuciyarka ne domin mutum dayan nan"

Tunawa take. Tana tuna yanda taji son fu.ad. Yanayin soyayyar shi a zuciyarta. Komai dawo mata yake da wani irin bazata.

"Haka kikaji da dady?"

Nana ta tambaya muryarta da murmushi. Hararta safiyya tayi. Shagwabe fuska nana tayi.

"Mumy please. Waye zai fadamun in bake ba?"

Yar dariya safiyya tayi. Karya itace karshen abinda zata so taima Nana a wannan lokacin. Dan haka ta zabi ta gaya mata gaskiya.

"Ya girmi hakan da dad dinki"

Cike da jin dadi Nana tace.

"Har yanzun?"

Wannan tambaya ce da bata son amsa ma kanta ita. Bata son ta fara wannan tunanin ko da wasa. Da wani rauni ta kalli Nana hakan yasata fadin.

"I'm sorry"

Murmushi tayi.

"Daukar mana wannan kikai mana falo gani nan zuwa"

Ba musu Nana ta dauki plate din dankali da na wainar kwan ta wuce. Sauke numfashin da take rike dashi tayi.

*

Suna gama breakfast din Nana tace zataje ta kara yin wanka. Itama safiyyar wankan taje tayi.

Tana fitowa yusra ta kirata suka gaisa. Tace mata zata iya tahowa a shirye suke. Atamfa ta saka daviva ruwan hoda ta matukar amsar jikinta.

Duk da babu wata kwalliya a fuskarta. Tana zuwa falo ta zauna Nana ta fito sanye da doguwar rigar daya fito mata da ita da er hijab.

Kallonta safiyya take. Harda jan baki pink a lebenta. Dan murmushi tayi.

"Bana so inyi kama da marassa lafiya. Bana son mutane su kalle ni da irin abinda nake gani cikin idanuwanku bayan basu sanni ba"

Sauke idanuwanta tai daga kallon da take ma Nana a sanyaye tace

"Wanne irin kallo ne muke miki Nana?"

Karasowa tai kusa da safiyya ta zauna.

"Tausayi. Sona duka a tare. Inkun mun bana jin kaman banida lafiya. Amman in anty jana tamun banajin dadi.

Bana son ganin shi a idon kowa sai naku"

Sauke ajiyar zuciya safiyya tayi tai shiru saboda bata san me zata ce ba. Wasu maganganun idan Nana tayi sai su saka rasa naka kalaman.

****

Da motar abbah yaje hotel din ya dauko komai nashi yai Check out ya dawo. A gida yai wanka sukai breakfast gabaki daya.

Wata irin kewar Nana yake ji. So yake kawai yaje ya ganta. Shiya fara mikewa daga kan dining din hadi da fadin.

"Momma aramun motarki"

Kamun ta amsa Abbah yace.

"Ka dauki mota daya cikin nawa kawai"

Saida ya kalli abbah sosai sannan yace.

"Nagode abbah. Allah ya kara girma"

"Amin. Kaje daki mukullan suna nan gefen gadona"

Kai yadan daga alamar to. Haryazo wucewa abbah yace.

"Fu.ad......"

Dawowa yai ya zauna. Yana bama abbah dukkan hankalin shi.

"Ka kawomun ita anjima inganta"

Cike da kaunar abbah cikin idanuwanshi yace.

"In shaa Allah"

Sannan ya mike. 406 ya dauka dan shi yanzun duk wani kyale kyalen duniya ya fice mishi a rai.

Daya shiga ciki yaja motar wani murmushi ya kwace mishi. Rayuwa ba komai bace ba. Wai yau shine kwata kwata bai damu da mota ba.

Ta zame mishi wani abu dazai hau ya biya bukatarshi. Bai

Please Login or Register in order to submit comment