Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ο»ΏπŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»
*GIMBIYA HAKIMA*
πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈ

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey πŸ–‹_





*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```







01&02







"Ranki ya dade, gimbiya Hakima, Fulani tayi aike, tace tana son magana dake, "Lantana aje ace mata yau bani san yin magana da kowa....




"Maryamu, yau gimbiya Hakima tace bata son yin magana da kowa,"wai Allah kice yau an tabo jaraba a cikin gidan nan? "Aiko dai, "Lantana! Lantana!! Lantana, "na bani Maryamu, gimbiya na kirana, ni yau na shiga ukku, yau buguna ne Kawai baza tayi ba...



"Allah ya kara maki lafiya, rain Gimbiya ya dade, ina neman sausaci rain Gimbiya ya dade, "Lantana, mai kika tsaya yi waje ina ta kiranki kin gyaleni?

"Ina neman afuwarki ya uwargijiyata, "yi man shiru ba wanann na tambaye ki, "nace uban me kika tsaya yi a waje? "Eh naje nakai sakonki ne, "wani sako? "Na baki san yin magana da kowa yau..


"Shine kika yi ma wannan uwar tsayuwar, ke Bilki, "Naam Allah ya da rainki ya dade gambiya,"wuce maza ki kiran man Sarkin bulala, yanzun nan, "to Gimbiya, "dan Allah Gimbiya ki man rai, ki duba tsufa na, kiyi hakuri, kuskurene nayi ina neman afuwa..



Tas! Tas!! Tas!!! Gimbiya Hakima ta wanke Lantana da Mari tana cewa, "yi man shiru tsohuwar banza, tsohuwar wofi, ke har wani tsufa ne dake da za'a kalla aji tausayinki, to ni *GIMBIYA HAKIMA,* bani tausan Yaro balle tsoho...



Suna cikin wannan yanayi sai ga Sarkin bulala yazo, "Ran Gimbiya ya dade, gani na ansa kiranki, yake uwar Marayun masarautar kano...



"Sarkin bulala, ina son yanzun kayi ma Lantana bulala hamsin, indan ta sosa ta zube, ko kuma tayi kuka, itama ta zube, bayan ka gama, ka kai ta gida Maza, tayi sati biyu, ana yi mata horo mai tsanani....



"Angama uwargijiyata, Yanzun ko zani zartar da hukuncin da kika bani, nan Sarkin bulala ya fara zane Lantana, ko dogon tausayi babu a idonshi, sai da yayi ma Lantana tsinanan bugu, sannan aka dauke ta zuwa gidan Maza...



"Allah ya taimekike, "Maryamu, lafiya naga kin shigo haka, hankalinki tashe? "Allah ya taimakeki, Allah ya kara maki nisan kwana, da man Gimbiya Hakima ce tasa ake yi ma Lantana hukunci...



"Subuhanalillah, mai tayi mata? "Da man dan ta dade, da ta ce aso ace man nace maki yau bata son yin magana da kowa, shine tace ta dade, ta barta tana ta magana...



"Allah sarki, je ki kira man sarkin gida, "to Ranki ya dade, nan Maryamu ta wuce jiki na rawa ta taho da sarkin gida..



"An gaisheki, Amaryar sarki, daga ke ba kari, " Sarkin gida, kai dai baka rabuwa da zolaya, kaje kace ma Hakima nace ta soke wannan hukuncin da tasa ayi ma Lantana, in ba haka ranta zai mumunan baci, kuma kace tasan tayi maza tazo kiran da nayi mata...



"To Ranki ya dade, nan Sarkin gida ya tafi, yana zullumin yanda zai hadu da Gimbiya Hakima, dan ya san lamarin ta ba mai sauki bane...




Nan Sarkin gida yana zuwa, ya aika ayi mashi neman iso,"Gimbiya Sarkin gida, yana son ganin ki, "Bilki kice mashi na ya san ida dare yayi mashi kafin raina ya baci...



"Allah ya taimaki Sarkin gida, Gimbiya tace yau bata son yin magana da kowa, "kije kice mata Fulani ta aiko ni, "Gimbiya yace sakone daga wajen Fulani, "kije kice ya shigo, ya jira ni gani nan zuwa....



Sai da Sarkin gida yayi awa daya zaune, yana jiran fitowar Gimbiya Hakima, amman shiru kake ji, ba bu alamunta..



"Bilkisu, dan Allah kije kice ma Gimbiya Hakima ina jiranta, "to sarkin gida, "gafara dai ran Gimbiya Hakima ya dade, nan Bilkisu tana shiga ta tadda Gimbiya Hakima tana chatting hankalinta kwace, "Ke lafiya kika yi man tsaya? "Allah ya huce zuciyarki yar sarki jikar sarki, da man sarkin gida yace yana jiranki, "je kice mashi ina zuwa, "to Gimbiya, sarkin gida tace tana zuwa...



Tafiya take cikin takama da jin kaika, tana tafiya tana harbin iska, tana busa hanci, "takawarki lafiya yar'masu gida, "yauwa sannunka Sarkin gida, lafiya kake nema, sai kace biyan bashi?



"Allah ya huci zuciyar Gimbiya da man Fulani ta bani sako, "wani kallar sako ne? Bana ce yau baniyin magana da kowa ba? "Allah ya huci zuciyarki, "naji mai tace maka? ka cika ni da surutun banza marar anfani, "da man tace ki maza ki soke hukuncin da kika yanke ma Lantana, tun ranku keda ita bai baci ba....



"Je kace mata naji, amman sai gobe zani sa a fiddo ta"godiya muke Gimbiya Hakima ikon Allah, nan gani nan bari, kinyi ma makiya nisa, "da kata sarkin gida, kana iya ta fiya dan ka matsa man da shirmainka



Nan sarkin gida ya tashi, jiki duk a sanyaye, yana mamakin yanda Gimbiya take gaya masu magana san yaranta, ko dan ta ganta ita yar sarki ce...



Ai a haife na haifi kamar Hakima sau ukku, amman dan ina karkashinta take zagina, baki daya bata biyo halin iyayenta ba, Allah dai ya shirya...



"Allah ya taimaki Fulani, "sarkin gida, ya kuka yi da ita? "Eh tace zata saketa amman sai gobe, kuma tana kan bakarta na yau bata son yin magana da kowa...



"Hmmm shikenan, sarkin gida, Allah ya shirya mana zuri'a, ka haifi da' baka haifi halinshi ba...



Nan dai Fulani ta kama fada tana mamakin halin diyar tata, ta rasa inda ta gado wannan bakin halin na wulakanta tallaka, tana mamakin yanda Hakima bata son tallakawa ko daya...




A rayuwa kenna, haka dai fulani ta gama sannan ta wuce shashen Yakumbo.....





"Ranki ya dade Gimbiya Yakumbo, Gimbiya Fulani, tana neman iso, "kuje kuce mata ta shigo,nan Gimbiya Fulani ta shigo ita da kuyunganta suna take mata baya...


"Sannu da hutawa Yaya, "yauwa sannu da zuwa Fulani, naji ance Hakima ta yanke ma baiwarta hukuncin sati biyu a gidan maza, "Hmmm hakane yaya, amman yanzun tace gobe zata sa a fiddo ta..



"Gaskiya Fulani, Hakima tana bukatar gyara, ban san ina ta samu wannan halin ba..


"Hmm wallahi nima Yaya wannan halin na Hakima yana da muna ban san ya zanyi da ita ba, kai haifi d'a baka haifi halinshi ba...



"To kuma naji ance tace yau bata san yin magana da kowa! "Eh hakane ai yanzun shashenta zan wuce dan ya zama dole ta tsaya ta saurare ni, tun kafin maimartaba yaji abunda tayi a yau..



"Gaskiya ya dace ai, "to ni na wuce Yaya...

"Nan Gimbiya Fulani ta tafi sheshen Gimbiya Hakima dan sunyi magana da ita..



"Ran ki ya dade ga mai girma Gimbiya Fulani a hanya, "to naji wace ki ban waje..

"Nan Bilkisu ta fita jiki duk a sanyaye, tana cewa haka dai zasu hakuri da uwargijiyar tasu..


"Fulani sannu da zuwa.

"Yauwa Hakima, ai ke keda sannu tunda kin nuna ban isa da ke ba, to ni gani na taso da kaina..


"Fulani zan fiddo Lantana gobe dan har umarni na bada na fiddo ta a gobe..


"Ni ba wannan ya kawo ni ba, inkin fiddo ta kanki inma baki fiddo ta ba shima kanki, tunda kinfi kowa anfana da Lantana..


"Nazo ne nayi maki bayanin addimission dinku a fito, dan haka Maimartaba yace ki fara shiri ko wani lokaci kina iya ta fiya makaranta..


"Haba Fulani, taya za'ayi Baffah yayi man haka?


"Yanzun kamar ni HAKIMA ace a rasa inda zani university sai a Nigeria, Nigeriar ma wai wata A. B. U. Zaria, salon tallkawa su rai nani su dauka matsayin mu daya dasu Fulani..


"Ke wacece inda mutun ba kamar su? Wai Hakima maiyasa baki san tallakawa? Basan ina kika dauki wannan mugun halin ba, shi tallaka ba mutun bane?


"Ke ba kowa bace face Gimbiya Hakima, daga nan baki wuce komai ba, kuma ya zamai maki dole kije karatu kasar zauzau, ni naji dadi da Maimartaba yace baki fita kasar waje..


"Ya zama dole ki koyi huda da tallakawa , dan baku da banbanci a wajen Allah nidai ina gaya maki gaskiya Hakima..


"Amman gaskiya Fulani ni bani zama hostel, "wanna kuma, ni na wuce, "to a huta lafiya..



Haka Fulani ta baro Gimbiya cikin bakin ciki da bacin rai dan Gimbiya tasa Maimartaba wasa yake da yace bai fidda data kasar waje karatu..


"Kash ni Hakima wai maiyasa Maimartaba yake san yana hadani da tallakawa, bayan ni ya san na tsani tallaka amman yanzun wai a rasa school din da ni *GIMBIYA HAKIMA* zani sai wai *ABU ZARIA* , amman shikenan..


Haka dai Gimbiya Hakima ta kama yan maganganun ta..



"Bilkisu!

"Naam Allah yaja da ran uwargijiyata, gani ina jiran umirninki na aiwatar..


Sai da Bilkisu tayi kusan minti goma tsugune tana jiran umirnin Gimbiya Hakima sannan tace..


"Ni kike jira naje na hada ruwan wankan da kaina kena?


"Tuba nike ranki ya dade..



"Yi man shiru duk baku da wani anfani a wajen, da zaran na hukuntaku ace ban yi maku adalci ba, bayan duk baku san aikin ku ba..



"Allah ya huci zuciyarki, ina neman sausaci rainki ya dade, anyi man afuwa insha Allah haka ba zai sake faruwa ba..


"Yi man shiru wawiya kawai dake, ku baku kama girmanku kurkure har na nawa kuke yi man cikin gidan nan, dan haka tashi kiyi aikinki kice ma yan uwanki gobe ina san ganinku dan tashi ki bani waje..



Nan Bilkisu ta tashi jikinta na rawa tana godema Allah da hukuncin Gimbiya Hakima ya tsaya iyakar zagi da bata yi mata hukuci irin na Lantana ba..


Haka ta shiga toilet ta hada mata ruwan wanka..


"Ranki ya dade, na gama hada ruwan, haka Bilkisu tayi tsaye tana jiran tashin Gimbiya, tana jin ina ace tana cikin masu yi ma Gimbiya girki ko gyaran gida da yanzun ta can ta na hutawa, amman yanzun su ke hadama Gimbiya ruwan wanka da kuma bata labari har sai tayi bacci ita da Lantana, sai da Gimbiya ta gadama sannan ta tashi ya shiga wanka, kafin ta fito Bilkisu ta gyara gado ya fiddo mata kayan sawa.



"Je ki hado mani tea ki taho man da tufa..


"Angama ranki ya dade, Bilkisu ta tafi jikin na bari ta hado ma Gimbiya Tea mai kyau da dauko mata tufa harda ayaba ta kawo mata, nan ta bare mata ayaba ta miko mata, sannan ta zuba mata Tea din a cup ta mika mata..


Kawai sai Bilkisu taji an watsa mata ruwan zafi a fuska cikin bacin rai Gimbiya ta fara magana..


"Dan mai zaki hado man Tea ki sa man sugar?

"Allah ya huci zuciyarki, naga haka kika ce adinga samaki sugar in za'a hado maki shayi..


Tas! Tas!! Tas!!! Gimbiya Hakima ta wankama Bilkisu mari tana wurga nata ayaba a jiki da sauran Tea din da ya rage tana ce mata..


"Dan nace ku ringa sa man sugar sai nace maku kullun ko?


"Aa Allah ya huci zuciyarki, ina neman sausacin hukunci gurin uwargijiyata uwar Marayun masarautar Kano..


"To ubanwa zai gyara maki wajen? "Ina neman afuwarki yar masu gida, yanzun nike jiran umirnin tashi Gimbiya..


"Tashi maza ki goge wajen ki ban waje ki sheda ma shashasun masu Aiki bangareni irinki gobe karfe shiddan safe ina bukatar ganinku kafin kowace ta fara Aiki..


"To insha Allah, godiya muke Gimbiya uwar-adalci ga tallakawanta, nan ta tashi tayi mopping din wajen sannan ta wuce tana godema Allah da ya kubutar da ita daga mumunan hukunci Gimbiya Hakima..













_By jameelah jameey πŸ–‹__









Share and comment pls

πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»
*GIMBIYA HAKIMA*
πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈ

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey πŸ–‹_





*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```





03&04




Tunda Asuba su Bilkisu suke tsaye jiran Gimbiya Hakima, hankalinsu duk a tashe yake baki dayan su suna tsoron hukuncin da zata zartar a kansu..


"Wai Ba'ba Bilkisu mai mukayi ma Gimbiya Hakima?


"Wallahi A'bu nima bansan mai mukayi ma Gimbiya Hakima ba, amman karki so kiga yanda jiya ranta ya baci, ko nima nan dakal nasha dan harda mari sai da na sha cikin daren nan..


"Yanzun Ba'ba Bilkisu ke din Gimbiya Hakima ta mara? "Yo sau nawa akayi Murja ai sai dai kar'asake indai marine munsha shi wurin Gimbiya Hakima nida Lantana yunzun kinga Lantana tana gidan hukunci dan ma Allah yaso ta yau za'a fiddo ta, da sati biyu ta yanke mata..



"Wai dan Allah maiyasa Gimbiya Hakima bata biyo halin iyayenta ba, baki daya Gimbiya Hakima bata da tausayi balle imani, da tana da tausayi da bata mari kamar su Ba'ba Bilkisu ba..



"Hakane gaskiya Ladi, shiyasa na godema Allah da nike wajen dahuwa kawai, shiyasa kullun nike kiyaye wulakancin Gimbiya Hakima, domin bata gani girman kowa cikin masarautar nan..


"Aiko Larai, kinga yanzun har karfe goma na safiya yayi amman har yanzun bata yi lokacin mu, itada tace tun shiddan safe take san ganinmu, amman shiru kuke jinta..



"To ya zamuyi Ba'ba Bilkisu, ai hakuri zamuyi tunda haka Allah ya kaddari rayuwarmu, "aiko dai ai hakuri ya zama dole Larai..


Su Ba'ba Bilkisu suna can tsaye tun asuba, amman Gimbiya ta gyalesu kuma sarai ta san da tsayuwarsu a bakin shashenta saboda tun takwas din safe take ido biyu tanata chatting dinta sai da goma tayi sannan ta shiga wanka, bayan ta fito wanka ta shirya cikin wata purple din doguwar riga sannan ta fito tana tafiya cikin isa da mulki irin na sarauta..


"Sai yanzun kuka gadamar zuwa kenan?

"Muna neman afuwar Gimbiya, uwar Marayu, tun dazun muke nan muna jiran isowarki..


"To maiyasa bakuje kuka yi man magana ba?


"Allah ya huci zuciyarki, ai bamu da ikon zuwa turakarki batare da wani dalili ba, kuma ai kina bacci shiyasa..



"Matsalarku ce wannan, kuna jina?

"Eh muna ji uwargijiyarmu, muna jiran umarni daga gareki..


"Mtssss, wai ku wasu kallar jahilai ne dabobi wanda basu da gwakwalwa basu da lisafi da basu san inda yake yi masu ciwo ba...



"Allah ya huci zuciyarki, suka fada kansu a duge suna tsugune a kasa suna sauraren cin fuska da wulakancin da Gimbiya Hakima take yi masu..


"In ba kuna wawaye ba mararsa Ilimi ba, Wanda basu san daidai ba, yo ina anfanin zama da wanda basu da Ilimi, taya zakusan ya kamata bayan bakuda Ilimi..


"Afuwan uwar Marayu, Gimbiya Hakima diyar sarki jikar sarki uwar sarki insha Allah, muna neman sausaci ran Gimbiya Hakima, matar sarki insha Allah..



"Maiyasa baku san aikinku ba? Ku fi san kullun na kama yi maku magana daya sai kace wasu dokuna?


Su dai basu ce komai ba, dan yanzun su sunbar Mamakin halin Gimbiya Hakima, dan inda sabo sun saba da zagin wulakancin da Gimbiya Hakima take yi masu..



"Dan haka ku bude kunnuwanku da kyau zan sake maimaita maku ka'idojina, dan na lura ku jaikaine da man jaiki shi ake maimaitama magana..


"Daga yau karku kuskura na sake taraku akan magana daya, kunajina ko?

"Eh muna ji uwargijiyarmu, Allah ya kara tsawaucin kwana..


A'bu ke da Murja daga yau ku zaku ringa yi man sauwar abinci , karfe bakwai na safe na tadda kun gama hada man abinci, karfe biyu na rana kungama na rana, karfe bakwai na dare kungama na dare, kunji ni ko?



"Eh muna ji, insha Allah, bazamu sake mu sake karya umurnin Gimbiya ba..


"Dan haka ku tashi ku bani waje, salan na kama maku da laifi, kusan hukuncin da zan yi maku, "insha Allah zamu kiyaye..


"Ladi da Larai ku kuma daga yau aikin gida ya dawo kanku, dan na gaji da cin jagwalgwalon abincin ku da kullun sai kun cika mashi gishiri sai kace ba yan-mata ba..


"To godiya muke Gimbiya yar'masu gida..


"Ku tabbatar kafin na tashi bacci kun gama gyara ko ina cikin gidan nan banda dakin da nike bacci shi daya ne ban yarjemaku da ku shiganman daki ba, dan ba daukar kazantarku banzaye kazaman banza kazaman wofi, ku tashi ku bani waje..


"Godiya muke Gimbiya Hakima..


"Bilkisu ke kin san aikinku ai ke da Lantana, dan haka sai ku kara hinma, dan na lura yanzun kuma kuna san ku sa lalaci cikin aikinku, idan kuma ku ka bari raina ya baci bansan abunda zan yi maku ba, dan haka wuce ki karaman Sarkin bulala..


"To Gimbiya, nan Ba'ba Bilkisu ta tashi ta tafi kiran sarkin bulala..



"Sarkin bulala, Gimbiya Hakima tana san ganinka..


"Lafiya dai ko? "Eh lafiya lau tana san ganinka dai, "to gani nan zuwa, nan Ba'ba Bilkisu ta taho gaya ma Gimbiya sako..


"Ranki ya dade gashi nan zuwa, "naji tashi ki ban waje kika yi man wani tsugune gabana...


"Gimbiya Hakima, uwar Marayun masarautar kano, gani na ansa kiranki, ina mai jiran umarninki na zartas..


"Sarkin bulala, ina san kayi ma Lantana bulala goma, yanzun in dan ta motsa ko tayi kuka bulalar ta zube a sake wata daga farko, in dan ka gama hukunta ta a sako ta ta dawo bakin aikinta..


"Angama ranki yadade, yanzun zani zartas da umirninki, nan sarkin bulala yaje, ya fiddo Lantana yayi mata hukuncin da Gimbiya Hakima ta bashi umirni sannan yace tace ta wuce ta koma bakin aikinta..


Haka Inna Lantana ta taho, tana mamakin halin Gimbiya Hakima yanzun ace wai bakin aiki zata koma, bayan duk wahalar da tasha, haka ta koma shashen Gimbiya Hakima..


"Godiya nike Gimbiya nagode da sausaucin hukuncin da na samu daga gareki..


"Lantana daga yau ki kiyaye duk abunda zai bata man rai, tashi ki ban waje..



Nan Gimbiya Hakima ta shirya, ta dauki hanyar Shashen Gimbiya Yakumbo daga nan ta wuce Shashen Gimbiya Fulani dan ta gaidasu,da kuyangirta Aisha tana biye da ita a baya..


Bayan Gimbiya Hakima sun isa bakin turakar Gimbiya Yakumbo, nan aka yi masu iso wajen Gimbiya Yakumbo sannan Gimbiya Hakima ta shiga..


"An tashi lafiya Momy? "Lafiya lau Daughter, fatan ki tashi lafiya?


"Lafiya lau Momy, wai Momy yanzun tsakani da Allah Baffah yayi man adalci?


"Daughter ba yanda banyi da Maimartaba ba akan ya kaiki Turkey karatu, amman yace shi a dole nan kasar zakiyi karatu to ya zanyi dole sai dai muyi hakuri, kawai in kinje ki maida hankali kayi karatu da man ban jinki a famnin karatu, dan haka ki fidda komai a ranki Hakima ki maida hankali kiyi karatu..


"Nidai gaskiya ba'ayi man adalci ba, ace ni Hakima zani university a Nigeria, duka karatu a nan kasar nayi shi, shi ko Yaya Annas yana can yana karatun shi Dubai, niko za'a hadani da tallakawa su gogeman zufar tallauci..


"Daughter ki tuna tallaka da mai kudi da mai sarauta duk Ubangiji Allah ya hallicemu, bamu da banbanci a gurin Allah sai wanda yafi bauta mashi, dan haka ina bukatar ki gyara kalamanki..


"Afuwa nike nema Momy, "shikenan akiyaye gaba, kinje kin gaida Fulani?


"Aa daga nan zan wuce wajenta, "to yi maza ki tashi kije ki gaidasu dan Baffanki yana shashenta, "to ni zan wuce a huta lafiya, "Uhmm..



Nan Gimbiya Hakima ta wuto Shashen Gimbiya Fulani dan gaidata itama, suna zuwa aka yi mata iso nan ta shiga ta samu waje ta zauna..


"ina kwana Fulani? "Lafiya..


"Fulani ko na yi maki laifi?


"Ko daya mai kika gani Hakima?


"Naga duk kin chanza mani baki daya, wallahi Fulani baki sona kamar bake kika haifeni ba, Yakumbo tafi sona..


"Hakima tashi ki bani waje tunda mun gaisa, haka kike so na soki baki jin tausayin bayin dake cikin gidan nan balle tallakawan waje?


"Haba Fulani, ni kullun sai kunce man naji tausayin tallakawa da bayin gidan nan, to ya kuke so nayi bayan ina iyakar bakin kokarina..


"Naji Hakima, tashi ki ban waje, karki manta ki fara shiri kafin Maimartaba ya ce ki fito...



"To shikenan Fulani, amman ina Maimartaba na gaidashi Yakumbo tace yana na?


"Eh! Yau bai san yin magana da kowa, yau ko fada baya fita, "to an gaidashi ni na tafi...


Nan Gimbiya Hakima ta koma shashenta, tace ma su Lantana yau bata san ganin kowa, sannan ta shiga bedroom dinta tayi wanka ta kwanciyarta...






_By jameelah jameey πŸ–‹_




Share and comment pls

πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»
*GIMBIYA HAKIMA*
πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈ

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey πŸ–‹_





*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk

Please Login or Register in order to submit comment