Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fara ci tana kallo tashi tayi ta ɗauko remote ta sake tasha ta mai TELEVISTA TV tana kallon music, shima Hakim tashi yayi ya maida NTA NEW haka ta tashi ta chanza inda take haka sukai tayi ba wanda yayi ma wani magana, tashi taga yayi ya nufo ta ta shi da gudu ta shiga, ɗaki dariya ya kamayi yana cewa, "ga jan faɗa dai shigen tsoro."

______________


"Kilishi kinga Amaryar Hakim, kamar ita tayi kanta dan kyau."?

"Hmm, ni bansan mai ma zance ba Gimbiya kawai ace shi maimartaba baya san yaranmu sai dai Hakim, inba ba'ason yaranmu ba mai zai hana idan ya tashi neman auren ya nema masu lokaci guda, amman sai ya nema ma Hakim shi ɗaya dan yana ɗan so."


"Kilishi kin sosa man ida keman ƙaiƙayi, sai yanzun kika gane ba'ason yaranmu sai dai Hakim? Da yake abun harda ke ya shafa tunda Humad ya isa aure shima idan aka bashi mace tsab zaiyi mata ciki ta haihu, amman duk bai gani ba sai girman Hakim kawai yake gani shi da yake da kwain haihuwa , shi ya isa haihuwa banda namu."

"Yanzun ba wannan ba yaushe zamu wajen Turmurturs akan wannan yarinyar karfa mu tsaya sanya tazo ta samu ciki saduwar farko fa."

"Hakane fa Kilishi dan ni ban kawo wanann a ran nan ba dan haka tashi mu tafi yanzun dan zama bai ganmu ba, yau kwana uku da biki wallahi ko ta samu cikin sai an zubda shege dan bama ta yuyuwa Hakim ya haihu ai aikinmu zai dawo baya tashi mu tafi mana."


"Gimbiya ki fara fita mana sai na biyoki, karda mu fita tare mu janyo idonun mutane, "to naji nayi gaba sai kin fito, "to yanzun ko."


Haka Kilishi ta fito suka nufi wajen Turmurturs, tunda suka je suka gaya ma Turmurturs abunda yake tafe dasu wani baƙin magani ya basu yace su tabbatar da Hakima ta ci shi cikin abinci tana ci bazata ɗauki cikin Hakim ba sai dai na Hamad kuma ya ƙara ce masu suna nan suna aikinsu nan da wata tara Hakim zai mutu, haka suka taso cikin farinciki dan yau sunji dadin zuwa wajen Turmurturs, nan Gimbiya Kilishi tace, "Gimbiya kinga sannu bata hana zuwa *{sunan novel ɗin Bikinsu S FAri ya nan yana yawo a social media🤫karki sake a baki labari}*, "aiko dai Kilishi sai dai a daɗe ba'aje ba, amman Kilishi mai yasa kikace haka."?

"To da muna hangan shekara biyar tayi nisa yanzun gashi saura wata tara, "hakane gaskiya kuma Kilishi ni yau ina cikin farin ciki gobe da safe da kaina zanyi masu abincin safe kinga sai na sa mata maganin da taci shikenan bukata ta biya."

Haka suka kama magana har suka iso gida ko wace ta wuce shashen ta ta kwanta.


_____________


Bayan Hakima ta gama duk abunda take ta tashi ta wuce kitchen ta haɗo coffe tasha sannan ta yi hanyar room dinta, a haka suka hadu da Hakim shima zai shiga kitchen din ya haɗa tea tayi mashi kyau sosai dan kasa boye maitarshi yayi dan fili fuskarshi ta nuna hakan, wucewarta tayi dan tasan halin shi ba kunya ta isheshi ba yana iya rungumota, tana shiga ɗaki ta kulle ta bar key ɗin jikin door ɗin tayi addu'a ta kwanciyar ta.


Koda Hakim ya gama duk abunda yake ɗakin Hakima ya nufi direct amman ya tadda kulle baiyi yunkurin budewa ba ya koma nashi ɗakin ya kwanta, amman da tunanin Hakima bacci ya kwasheshi.



Tun asuba suka tashi Hakim ya wuce massallaci ita kuma tayi sallah, koda ta gama sallah kitchen ta shiga tayi masu dankali da tea sai kosai dan angaya mata Hakim yana son kosai sosai, koda ta gama wanka ta shiga ta shirya cikin wasu riga da wando ba ƙaramin kyau tayi ba ta tunke gashinta ta ajiyeshi a chests ɗinta sannan ta fito direct room ɗinshi tayi, nocking tayi amman baiyi magana ba, shi yasa ta shiga lokacin da ta shiga dai dai time din ya fito daga wanka daga shi sai towel ƙara Hakima ta saki yana juya mashi baya dan bata taɓa ganin namiji haka ba daga shi sai towel, shi ko Hakim ko a jikinshi dan ma matsawa yayi kusa da ita tana tambayarta abunda ya kawo ta room ɗinshi, idonta rintse take ce mashi zuwa tayi ta ce mashi ya fito yaci abinci ta gama haɗawa, yaji dadi sosai shiyasa yayi huging ɗinta yana manna mata kiss a koshi daman tayi mashi kyau sosai ce mata yayi ta shirya mashi sai su fita tare, cewa tayi bata yarda ba sai dai ya shirya ya fito matsa mata yayi ba yanda ta iya ta fara shafa mashi mai tana yi mashi Allah ya isa cikin zuciya, komai take Hakim yana kallon ta ta mirror dan hakan ma da take kyau take ƙara yi mashi sosai, bayan ta gama shafa mashi mai ta ɗauko wani jean da T-shirt masu kyau tace yasa amman sai yace duka ita zata sanya mashi nan fa suka fara drama dan ko boxer bai sa ba wai duk ita zata sanya mashi ita ko tace bai isa, daman yasan bazata saba kawai dai shi yana son yaga tana magana dan ƙaramin bikin nan nata yana motsawa kamar anayi mata dole, sai da ya gama kallonta san ranshi sannan ya cire towel ɗin a gabanta dukewa tayi tana salati dan Hakim ya girmi tunaninta ko kunyarta baijinya tsaya a gabanta haihuwar uwarshi, bai damu da abunda take ba ya gama shiryawarshi yayi gaba abunda shi ya barta tsugune sai da ta tabarta da ya fita sannan ta bi bayanshi, bata yarda suka haɗa ido ba ta zuba mashi abincin ta tura mashi gabanshi sanan ta zuba nata nan suka fara ci, shi abun dariya yaso ya bashi wai Hakima ce batasan haɗa ido dashi duk tsiwar da rashin kunyar sun gudu dan ya cire towel a gabanta yana sane yayi haka dan ya dasa mata tsoranshi cikin zuciya.


*NIKO NACE MALAN HAKIM AI KO BUKATAR KA TA BIYA DAN NAGA ALAMA HAKIMA TA TSORATA SOSAI 😛*


Haka wunin ranar Hakima a tsorace take da Hakim dan bata yarda ta biye mashi sukayi faɗa ba duk da shi yana jan ta faɗan take kyaleshi.

_________


Gimbiya Zulaha ta shirya ma su Hakima abinci mai rai da lafiya wanda yasha magani dan da kanta ta ɗauki hanyar shashen Hakim dan kaima Hakima abinci.






_By Jameelah Jameey ✍🏻_




#share
#comment
#vote
#like
#please



👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```



83&84

Zaune suke a parlourn suna kallo amman ba mai cema dan uwanshi komai wani indian series ne suke kallo, amman Hakima ita ta maida hankalinta wajen kallon shi Hakim marking ɗin pappers ɗinsu Hakima yake yi dan lokacin ma yake yin ta Hakima, yana mamakin yanda Hakima take da kokari domin komai nata burgeshi yake sosai, tsayawa yayi yana kallonta sai ta burgeshi dan ji yake kamar yaje ya rungumota ko yaji dadi dan yanzun yana bala'in son ya ganta cikin jikinshi zuciyarshi sanyi take bai son tayi mashi nisa koda na second ne dan ba zai iya jura ba, acewarshi idanunshi bazasu juraza rashin ganinta a kusa dashi ba kunnunwanshi ba su jura rashin jin amon muryarta ba shiyasa yake yawan tsokanarta faɗa dan kawai tayi magana yaji sanyi a zuciyarshi, kallo take cikin natsuwa dan ga dukan alamu film ɗin yana yi mata dadi sosai, ajiye pappers ɗin yayi waje guda sannan ya tashi ya chanza tasha ya maida nasu Manara Tv, kallon shi tayi ta tashi ta maida inda take kallo shima ya tashi ya chanza ya riƙe remote ɗin a hannunshi taso wa yayi tace, "ka bani remote bansan kana yi man haka gaskiya Hakim, kai dai na lura baka san bakin mutun yayi shiru.".... Kallon dan cute lips ɗinta yake daman sun sha pink jan baki, take yaji yana son ya tsotsa bakin, amman sai yayi kamar bai jita ba, sake cewa tayi, "wayyo Allah na dan Allah ka bani mana karfa su wuceni sosai.".... Cewa yayi, "idan kina da ƙarfi sai ki ansa tunda gashi a hannuna kina gani."... Cewa ta kuma yi, "nidai dan Allah ka bani."... Amman Hakim sai ce mata yayi, "banfa baki sai kin ansa da kanki."



Daman tayi shirin bacci dan wata yar ficiciyar amless rigace a jikinta dan ko ciyarta ba ta kulle ba, kuma boos ɗinta duk rabunsu waje suke ko motsi tayi mai ƙarfi to dukansu zasu fito waje, jumping ta fara yi ita a dole sai ta ansa remote a hannun Hakim, tunda ta fara jumping boos ɗinta suka fito waje suna kallon Hakim, mutuwar tsaye Hakim yayi dan Hakima ta wuce tunaninshi wajen kyau da sura, da ya fahimci tana niyar ansar remote ɗin sai ya ƙara sama da hannunshi sosai, ita ko tsalenta take bakin ƙarfinta dan tana san taga ayi paster da ita, har ta fara gajiya sosai da Hakim yaga ta gaji sai ya ɗauketa yayi sama da ita wule-wule take wai ita ya ajeta ya bata remote, amman ina dan ba inda Hakim ya direta sai bisa threesiter nan parlourn ta buɗe baki zata yi magana kenan ya haɗa bakinsu waje ɗaya nan ya fara aika mata da hotskiss, zamar da ita yayi ya kwantar da ita saman kujerar yana shafeta yana sauke numfashi ya sake mayar da bakinsa saman nata yana tsotsar harshenta da lips dinta zuwa kunnenta, a hankali ya dora hannunsa saman boos ɗinta sukaja numfashi yasa hannunsa cikin rigarta yana shafa kan breasts ɗinta ta rintse idonta da qarfi saboda numfashinta da taji yana barazanar daukewa.
Kama nipples dinta yayi yana mulmulawa yana kallon kyakkyawar fuskarta, numfashi kawai Hakima take dan batada ƙarfin da zata iya ture Hakim ko kuma tayi mashi wani abu suna cikin wannan yanayi Gimbiya Zulaha ta shigo dan ko neman iso bata aiko ba ta shigo dan a tunanin ta Hakim baya gida na wajen Fulani Kubrah shiyasa ta shigo ba tare da neman izini ba dan gani take ta isa har tayi yawa, tunda ta shigo take jin gurnanin Hakim dan Hakim baki ɗaya ya fita cikin tunanin dan so yake ya jishi wata duniya ta daban, jin ƙarar faduwar wani abu da kuma tsawar da Gimbiya Zulaha tayi ya fara maidoma da Hakim hankalinshi, ita ko Gimbiya Hakima tunda Gimbiya Zulaha tayi ƙara ta fara ture Hakim tana cewa, "na shiga ukuna Hakim ka jawoman abun kunya ai sai ka ɗagani ko."?... Ƙara janyota jikinshi yayi yana neman cigaba da abunda yake, tureshi tayi da karfin gaske sannna ya Fahimci da mutun cikin parlourn, dugewa Hakima tayi ta fara kuka dan bata ji dadin ganinsu da Gimbiya Zulaha tayi ba cikin wannan yanayin yanzun shikenan zata ɗauketa marar kunya, koda Hakim ya buɗe idonshi sosai yaga Gimbiya Zulaha ce ta shigo sai yaji dadin ganinshi tayi da Hakima a haka dan zata tabbatar da Hakima ta zama tashi har abada dan dun wani tugu da suke yana sane dasu, tashi yayi yana cewa, "Gimbiya sannu da zuwa, baki gaya mana zuwanki ba da mun shirya maki tarba ta musanman."


Kasa kallon idanunshi Gimbiya Zulaha tayi sai dai tace, "bakomai Hakim, ai ko yanzun ma naga tarbba ta musanman."... Ta wuceshi ta taso Hakima tana cewa, "maiye abun kuka amarya sai kace wanda akeyi ma dole ko kuma baki son mijin yake kusantarki dole."?... Wata sabuwar kunyace tasake baibayi Gimbiya Hakima dan bata shirya jin wannna maganar daga bakin Gimbiya Zulaha ba, sai ce mata tayi, "ai auren da ba'ayishi da soyayya ba shi ake kira da dole, amman ni da mukayi auren soyayya nida mijina ai komai yayi man cikin sone, kuma kukan dadi ne nike dan sai da abun ya ɗauko dadi kika shigo mana shashe."



Ba Gimbiya Zulaha kaɗa ba harta Hakim sai da maganar Hakima ta bashi mamaki amman yaji dadi yanda ta gaya ma Gimbiya Zulaha magana ta haka zata kiyaye ta, Gimbiya Zulaha cewa tayi, "ai yarinya ko auren da akayi shi da soyayya ana saduwar dole ba dan dadi ba."... Gimbiya Hakima tashi tayi ta matsa kusa da Hakim tana kallon idanunshi ta kuma haɗa hannunta da nashi waje ɗaya tana wasa da yatsanshin sannna tace, "mijina wai da gaskene masoya suna gajiya da junansu a aurataiya."?


Hakim ƙara rungumota yayi yana sakar mata wani killers smiles dan yau yaji yana bala'in son Hakima, dan zai iya yin komai ga wanda yake niyar rabashi da ita cewa yayi, "Habity ga wanda suke zaman da ba amana sune zasu iya gajiya da juna, amman banda *HAKIM DA HAKIMA* dan mu ko muna tare da juna mutu ka karaba dan insha Allah nan da dan watan ni zaki haifaman baby mai kama dake."


Gimbiya Zulaha bakin ciki ne ya kusa kashe she ta, amman sai ta ɗaure tace, "muna fata kuma muna jiran muga jininka Hakim, dan haka daman ni ba wani abu ya kawoni ba abinci ne naga ya dace nima ba dafa maku tunda kuka fara amarci ban kawo maku ba saboda ban lafiya ga shi can."......... Ta faɗa tana nuna masu abincin tana murmushi bakin ciki dan sanine bata yi fuskar tanuna bakin ciki fili, ɗauko abincin tayi ta ba Hakima sannan tace ta barsu lafiya, godiya sukayi mata sannan ta tafi.


Tana tafiya Hakima ta ajiye abincin a dining table, sannan ta wuce bedroom ɗin ta, shidai Hakim tsayawa yayi kallon ikon Allah dan yana son gwada iliminta shin zataci abincin da Gimbiya Zulaha ta kawo masu, wanka tayi sannan ta sake shiryawa cikin wasu nightwears ɗin sannan ta fito direct kitchen ta wuce ta ɗauko plate da spoon sai freshmilk mai sanyi ta zauna ta fara zuba abinci.......




_To fa wata sabuwa shin Fans Hakima zata ci abincin ko Hakim zai hanata?😰_




_By Jameelah Jameey ✍🏻_


#Share
#Comment
#Vote
#Like
#please





👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```


87&88


Yau masarautar Zaria ta wayi gari da wani babban bako, dan tun safe Hakim take kitchen Maimartaba da kanshi ya aiko mata da sakon tayi ma bakonshi girki da kanta dan tunda yaci abincin ta yaji da dadi yace tayi ma abokinshi dan tare sukayi university tare shida Baffahn ta ,abinci mai rai da lafiya ta girka masu tasa aka kai shi fada bayan tagama ta shiga wanka ta shirya ta wuce shashen Gimbiya Fulani.

Bayan Sarki Abubakar ya gama cin abinci suka fara gaisawa da abokinshi sarki Abdulmalak, "abokina na samaiku lafiya."?

"Lafiya lau Alhmdulh, ya ka baro kasar Katsina."?

"Kasar katsina tana lafiya ita da mutunan cikin ta, "Alhmdulh haka akesan ji, Allah ya ƙara mana hakuri da talakawamu, "Amin ya Allah, ai abun dole sai da hakuri, dan shi daman zaman duniya ya gaji wannan abun guda biyu zo mu zauna zo mu saɓa, "Aiko dai hakane."..... Sai da Sarki Abubakar ya numfasa ya kurbai ruwan inibi sannan ya fara magana,"abokina da farko dai ina tayaka murnar auren da kayi ma Hakim shida ɗiyata Hakima, tunda mu uku tare mukayi karatu nida kai da babanta, agaskiya naji dadi sosai, sai dai kash lokacin da akayi bikin bani lafiya sosai shiyasa na turo wakili."

"Hakane ko, ai abokina nasan baka lafiya shiyasa baka hallaci ɗaurin auren ya'yanmu ba, kuma daga ni har Abdulhadi munyi maka uzuri babba, Allah dai ya baka lafiya, su kuma Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a ɗaiyaba."


"Amin ya Allah, sai magana ta biyu kuma, gani gaba abokina nazo da koƙan barata, wata alfarma nike so kayi man dan Allah ina fatan Allah yasa na samu."?


"Haba abokina, ai ba abunda bakafi ƙarfi ba a wajena komai shi ko, ka gaya man ko wace alfarma ce insha Allah zaiyi maki mudun inadashi."... Sarki Abubakar yaji dadi sosai duk da daman yasan yafi ƙarfin komai wajen Sarki Abdulmalak amman hakan kuma da ya nuna mashi ya ƙara mashi ƙarfin giwar gaya mashi bukatarshi.

"Masha Allah da man da wani abu bane illar na zauna nayi tunani inasan nima na haɗa zuri'a dakai, bi ma'ana inasan idan ba damu naba ɗana *YARIMA HAKIM* auren ɗiyata *GIMBIYA HIKIMAT* amman idan zai yuyu, duk nasan akwai su Hamad da Humad amman tarbiyar Hakim tafi kwantaman shiyasa nayi ma Hikimat shi'awar aurenshi.


*MY FAN'S KUNJI WATA SABUWA DA SARKI ABUBAKAR YAZO DA ITA😳*


Numfasawa Sarki Abdulmalak yayi, dan baiyi tunanin abunda Sarki Abubakar yazo dashi kenan da baiyi mashi alkwarin zai yi mashi alfarma ba, wani nauyin Sarki Abubakar ya kama Sarki Abdulmalak, bai san lokacin da yace, "Alhmdulh, gaskiya naji dadi sosai da wannan haɗin da zakayi Abokina hakan ma yayi, fatan dai Allah ya basu zaman lafiya baki ɗayansu, kuma da kake maganar su Hamad lokacin auren ne nasu Allah baiyi ba, Allah ya ƙaddara sai Hakim ya rigasu fara aure kafin su suyi dan haka Abokina karka damu nan da wata ɗaya insha Allah zamu zo abamu auren Gimbiya Hikimatu insha Allah."


"A gaskiya abokina bani da bakin da zani yi maka godiya sai dai nace Allah ya bar zuminci, insha Allah zamu shirya muma kafin nan da wata ɗaya."


"To Allah ya kaimu, fatanmu mudai, Allah ya haɗa kansu ya basu zaman lafiya da zuri'a ɗaiyaba wanda zasu taimaki al'umma nan gaba."


"Amin ya Allah.".... Nan suka cigaba da tautanawarsu ta abokai da kuma yaushe rabon da su haɗu.

_______________

"wai Hakima lafiya najiki sukuku? Kamar baki lafiya kodai yayanmu ya bada ajiyane mu fara tara kayan ɗaki."?.... Ta faɗa cikin wasa, "kedai kawai ki gani, amman wallahi yau gabana faduwa yake ji nike kamar wani abu ke damuna."


"Ayya kita addu'a insha Allah ba komai,"Allah yasa matar Yaya."

Dariya suka sa su duka ukun suka barke da labarin duniya, Hakima tana basu labarin makarantar, amman abun mamaki bata gaya masu kalar faɗan dasukayi da Hakim ba, suna cikin labarin Fulani ta shigo nan suka hadu su hudun suka cigaba da labarinsu dan Hakima kwantawa tayi bisa cinyar Fulani ta labarinsu, sai dariya suke dan Hakima ta ɗauki Fulani a matsayin uwa bata boye mata duk wata damuwarta haka suke rayuwarsu sun fahimci juna.


Tunda Hakim ya shigo yake tsaye yana kallonsu dan abun yana burgeshi sosai kuma yana jindadin yanda Hakima ta ɗauki mahaifiyarshi kamar mahaifiyarta, yakan godema Allah da ya bashi Hakima a matsayin matar aurenshi duk da ba wani zaman lafiya suke ba, amman tana daraja iyayenshi da yan uwanshi kuma hakan yana yi mashi dadi sosai da sosai, sai da ya gama kallonsu sannan ya shigo shima bisa cinyar Fulani ya ɗaura kanshi yana ture kan Hakima yana cewa, "wallahi ko Fulani yanzun kibar sona, tunda kika samu Hakima dan na fahimci baki damu yanzun ko na ci abinci ko ban ci ba."


"Hakim badai rigima ba, yanzun inba neman magana ba kai da kake da mata tambayar mai zan maka na kaci abinci?da dani ke tambayar ka ma dan baka da mata shiyasa amman yanzun nasan Hakima bata barinka da yunwa."


"Nidai duk da haka Fulani", "kaji dashi dai, ku tashi ku tafi shashenku","Aa ba yanzun ba dare baiyi ba","ni tashi zanyi naje wajen Abbanku, kaga bakonshi ya tafi tun ɗazun amman banje ba", "yauwa niko kamar naso na gane bakon Abba."

"Sarki Abubakar ne fa, shine sarkin katsina, ai ke Hakima kin sanshi ko."?


"Eh nasanshi, yaje walimar gama karatuna", "yauwa kai Hakim mantashi kayi dai, kuma dan badakai akaje walimar ba da kaganshi da Hamad akaje nasan shi Hamad zai shidashi idan ya ganshi."


"Hakane bari mu tashi mu tafi tunda wajen Abba zaki,mun barku lafiya, "to Allah ya kaimu."



Haka suka jero suka taho bayi sai gaidasu suke suna yaba kyau da kyaun hali irin na Hakima da Hakim, suna shiga shashensu ko wane ya wuce room ɗinshi ya cigaba da hidimominshi.

______________


"Gimbiya lafiya naga kina rawa ke ɗaya cikin ɗaki."?

"Kilishi ai bansan kin shigo ba sai dai kawai naji maganarki."


"To taya zakiji shigowata bayan kina da taka rawa kece ta samu amman ba a nemaimu ba, to gani gaya man lafiya."


"Ai maganar gizo bata wuce ta koƙi inji hausawa, kawai ina farincikin saura wata hudu mutuwar Hakim, kuma har yanzun wannan yar'neman bata ɗauki ciki ba, shiyasa kikaga inata murna."


"Hakane fa, amman baki san maimartaba yana neman kowa da kowa a shashenshi bayan sallahr isha'i."?

"Aa ban sani ba gaskiya, bari na kira Hamad yazo ayi dashi wa ya sani ko aure ya nema mashi shima."


"Hmmmm, ni ko na tafi sai mun haɗa a taron."


"To shikenan."

__________________


"Ki shirya anjima zamu shashen Abba yana san magana da damu."


"To shikenan, Allah ya kaimu lafiya Amin."



Bayan sallahr isha'a kowa da kowa iyalen sarki Abdulmalak sun hadu a babban parlournshi suna jiran isowarshi suji kiran mai yake yi masu.............




```MY FAN'S YA KUKE GANIN NEXT PAGE ZAI KASANCE, KUDAI KU BIYONI DANJIN YANDA ZATA KASANCE😛```




_By Jameelah Jameey✍🏻_




#Share
#Comment
#Vote
#LIke
#Please


👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```


*🤣🤣🤣🤣Wallahi ko yau kun bani dariya sosai TEAM HAKIMA, haka kuke da kishi daman🤪*



89&90


Shigowa yayi ya samu waje ya zauna, kallonsu kawai yake ɗaya bayan ɗaya dan bai san ta ina zai fara ba, dakewa yayi sannan ya fara magana yana cewa, "fatan kowa yana lafiya."?.... "Lafiya lau, Alhmdulillah." ..... Sukace gaba ɗayansu, dan kowa mamaki yake wannan taron gaugawar da Maimartaba ya tara, numfasawa yayi sai da yayi kusan 6min sannan kuma ya fara magana,"kamar yanda kuka sani ni na bukaci ganinku wajen nan."


Ba wanda yace komai sai dai kallonshi da wasun su suke wasu kuma ƙansu ɗuke yake suna sauraran Sarki Abdulmalak, numfasa yayi sannan ya kira sunan Hakim, "Hakim."... Ɗago kanshi yayi yana kallonshi, gabanshi faɗuwa yake sosai dakal ya samu bakinshi ya buɗe yace, "Naam Allah ya taimakeka."... Cigaba da cewa yayi, "Hakim nasan waye kai, bance kafi kowa cikin yaran da na haifaba, Aa amman ina da yaƙinin ko bayan raina yazaka kula da yan'uwanka, kaine babba kunsan Hausawa sunce Babban wa uba, haka ne."?..

Yayi tambayar yana kallon Gimbiya Zulaha, ɗaga mashi kai tayi tana murmurshi, amman ji take kamar tayi kuka dan yace Hakim shine babba, shidai Hakim baice komai ba,dan tunda yaji Abbanshi ya kira sunanshi yake addu'ar Allah yasa ba wani laifi yayi ba , yana cikin tunanin yaji yana cewa, "to saboda Haka, kai Hakim yau ma ga wani umirnin zan baka kamar yanda na baka umirnin auren Hakima kuma kayi man biyaiya naji dadin haka, kuma su Hamad

Please Login or Register in order to submit comment