Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma nasan Abba bai ƙara yi man aure tunda ga su Hamad nan, yanzun mu tafi shashen Fulani muyi breakfast kafin Yakumbo su iso ko."?.... "To shikenan masoyina ilove with all my heart.".... Love you too Jewel mu tafi karda muyi leting.".... "Ok let go."


Haka suka tafi shashen Fulani bayan sun gaidata suka fara yin breakfast.


_____________


"Gimbiya wai taron mai Abba zai yi kinga yanda akeyi ma wajen fada decoration kuwa."?

"Wallahi ko Hamad bansan taron mai zaiyi ba, ni ba wannan ne gabana ba har yanzun banji anfasa ihu ba Hakim ya mutu kuma yau shekara biyar take cika amman shiru nike ji Hamad."


"Wai daman yau shekara biyar take ciki? Kuma Hakim zai mutu Hakima ta zama tawa."?


"Haka kaji nace amman shiru ka kakeji kamar mai, amman ila zuwa anjima zai mutun ko."?


"Nima haka nike tunani Gimbiya, mu gama cin abincin muje wajen taron da nan naga manyan baƙin duk sun hallara harda sirikina ma Sarki Abdulhadi duk naga sun zo amman iyalanshi suna shashen Gimbiya Fulani."


Hmmm! "Daman nasan ba Yakumbo bazata shigo sheshena ba, balle Fulani Aisha, amman ai yau Hakim yake mutuwa kuma gobe ubanku shima zai mutu jibi kuma a baka sarkin masarautar Zaria, gata kuma zan maida Fulani Kubrah baiwata, sai Gimbiya Fulani Kubrah tayi kuka da idanunwanta, sai idanunwanta sun tsiyaye saboda da kuka daga karshe kuma bakin ciki ya kasheta tana ganin ka ɗauro Hakima ta zama taka."


Ikon Allah kunji Gimbiya Zulaha da wata magana, hmmm kudai muje zuwa muga wannan wani taro ne Sarki Abdulmalak ya haɗa wanda ba wanda ya san ni🤔.

__________________



"Hasiya."

"Naam Allah ya taimaki Gimbiya Kilishi, Allah ya huci zuciyar Gimbiya Kilishi lafiya naganki cikin wannan yanayin? Banga kina niyar fita ba ma gashi wajen taro ya cika da bul'adama."


"Hasiya ni wannan bai gabana, har yanzun baki ji kuka ya fito daga sheshen Fulani ko kuma Zulaha."?


"Allah ya taimakeki banji kukan komai ba, sai busar da sarkin busa suke busawa da kuma sautin kiɗin da sarkin makaɗa yake bugawa, dan gaskiya daga gani wannan babban taro ne za'ayi na musamn... Tas! Tas! Tas!, ji kake Gimbiya Kilishi ta wanke Hasiya da marika guda uku lafiyaiyu dan ko maganar ma kasa idata Hasiya tayi ta dafe kunci tana kallon Gimbiya Kilishi da mamaki dan ita bata san abunda tayi ma Kilishi ba.


"Ke har kin isa, ina tambayarki kina yiman wani shiruntunki na banza da wofi, na tambayeki busa ko kiɗi? Amman zaki isheni da wani busa ta kiɗi, maza tashi ki ban waje ko nayi ball dake sakarar banza sakarar wofi."


Haka Hasiya ta tafi tana sosa kunci dan mararin ya shige ta sosa.


*NIKO NACE ALLAH YA KARA DAMAN DUK WANI MUNAFIKI MAGANINSHI KENAN, HASIYA KAƊAN KIKA GANI🤪*


Tunda Hasiya ta tafi Kilishi take zagaya ɗaki tana mamakin yanda har yanzun bataji ankirata ba tazo Hakim da Hamad sun mutu, ba abun yana bata mamaki, amman sai tayi tunani ila da anjima zasu mutu wannan tunanin yasa taji sanyi ranta ta tashi ta tafi wajen taro kunyanganta suna take mata baya.

________________







Bacci take taji ya faska mata bugu a baya ana cewa, "mai zangani haka? Hikimatu baccin mai kike har haka baki tashi an barki sheshe ki ɗaya kina baccin asara."


Tashi tayi tana murtsuka idanu, tana kallon Gimbiya Binta dake gabanta tana mata wani kallo, tashi tayi tace, "laaa Mama yaushe kukazo."?


"Bansani ba, abunda na tambayeki kenan? Nace daman haka kike wanann sakarcin gidan mijinki, nazo bakowa sai ɗaya gashi kuma har ana ta taharamar fara taron mu munsa ma mun makara amman Allah yasa ba mu makaraba ke ko shirya wa ma baki yi ba."


"Haba Mama ni ai nasa bandamu ake wannan taron shiyasa ban tashi ba, kuma ko na tashi mak zanyi na gaya maki Hakim baya cin abincina daga na wacer munafikar matarshi sai kuma na uwarshi su kaɗai yake ci shiyasa yanzun na bar bama kaina wahalar tashi dafa mashi wani abinci, amman yanzun zan fito wanka Mama."


"Sai kiyi sauri ki fito wankan inasan nayi magana dake kafin a fara taron, "to ni na shga."


Tana shiga ta watsa ma jikinta ruwa ta fito, dan ni banzance tayi wanka ba tunda tana shiga tana fitowa, kuma ko sallahr asuba batayi ba amman kawai tana wanka ta fara shiryawa, bayan ta gama ta haɗa complex tasha sannan tace "Mama nagama ina sauraranki."


"Hikimt kikace har yanzun Hakim baicin abincinki."?


"Wallahi ko Mama, kona dafa bayaci."

"Kiceman duk asirin dani yi mashi baya tasiri kanshi."?


"Mama na fahimci Hakim asiri baya kamashi, saboda danaga baya cin abinci na sai nace ma boka yabar bani aikin da za'a samashi cikin abinci dan ba ci yake ba, amman duk da haka banga wani sauyi ba dan ko kusantata Hakim baisan yi sai na matsa mashi sannan."



Hahahahaha! "Karki damu Hikimatu yaro baisan wuta ba sai ya taka, damu Hakima take zance, ai daman boka yace man komai muke Hakima take asiri tana karyashi amman ga wannan maganin zakiyi. Matsi dashi duk sanda jinin haila yazo maki kinayi matsi komai ya wuce Haka boka yace."


"To shikenan Mama."


"Amman yace idan kuma ki ka yarda kikayi ma'amala da wata mace maganin zai kare dan haka sai ki hakura da neman mata, dan nasan halinki yana nan na bin mata, idan baki koshi da Hakim ki sawo wannan abun na zamani mana kiyi amfani dashi amman sai kin yi hakuri da bin mace."


"Amman... "Yi man shiru mutuniyar banza, tashi mu tafi karda mu makara."


Haka suka tafi amman Hikimatu ta aiyanama kanta bata hakura da Azizarta dan tanajin dadi ma'amala da Aziza.

________________



Suna cikin yin breakfast, su Gimbiya Yakumbo suka shigo bayan sun tarbesu suka zauna suka ida breakfast ɗin tare, sannan suka danyi firar yaushe gamo sannan suka ɗunguma suka tafi wajen taro.



Koda suka isa wajen taron sai da tsikar jikin Hakima ta tashi saboda mutanan da sukazo wajen baka ganin komai sai kwawuna, riƙe hannunta Hakim yayi sosai dan ya lura da Hakima ta tsorata da Mutanan wajen, yakan yi mamakin yanda Hakima take da tsoro har haka, dan shi a tunaninshi jarumace sosai.



Sarki Abdulmalak da Sarki Abdulhadi sai Sarki Abubakar sune bisa hight table ko wane matanshi a gefensu, daga ƙasa kuma Yarima Hakim ne dasu Gimbiya Hakima a gefensu, sai ƙasansu kuma Yarima Hamad ne da Yarima Humad sai Aliyu, suma daga ƙasansu Gimbiya Maryamace da Gimbiya Sadiya da Maryam, suma daga ƙasansu Wazirine da matanshi, sai sauran yan fada da kuma yan siyasa da manyan baƙi.



Tashi Sarki Abdulmalak yayi ya fara magana kamar haka, "Assalama Alaikun, ina godiya ga manyan baƙi da duk wani wannan ya hallaci wannan taro mai albarka taron da rabon da ayi shi yau kimanin shekara 40 kenan sai yau Allah ya yarda shekara ta zayo."


Shiru kowa yayi yana jiran yaga ikon Allah tunda Gimbiya Zulaha taji Sarki Abdulmalak yace shekara 40 rabon da ayi kalar taron sai da gabanta ya faɗi amman sai ta dake tana kallon ikon Allah kamar yanda sauran keyi.


Cigaba da cewa yayi, " Alhmdulillah, Allah na gode maka da kanuna man wanann ranar da ni Abdulmalak Muhammad zani yi murabus daga wannan mulkin danike sama zan ba ɗ'ana Hakim ya cigaba daga ida na tsaya, wannan abun babban abun farin cikine daga gareni."


Hayaniya ce ta fara tashi wajen dan mutune sunga kokarin Sarki Abdulmalak suna jingina ma dantaku irin tashi, dan a wanann zamanin ba kowani sarki bane zaiyi murabus ya ba ɗanshi ba tare da yaji komai ba, tunda Gimbiya Zulaha taji Sarki yace yayi marabus ya ba Hakim mulki zufa ta jiƙeta sarkab haka ma Gimbiya Kilishi, shi ko Hakim tunda yaji wai yau shi a za'a ɗaura ma nauyi bisa kanshi ya fara kuka kamar ƙaramin yaro dan ji yake kamar ya tashi yace ma Abbanshi baya so wannan mulkin da yake niyar ɗauramai ya ba Hamad shi ko dai ya yafe, tunda Gimbiya Hakima da yanayin da mijinta ya shiga ta kama hannunta yana murzawa tana yi mashi nuni da yayi shiru, itako Gimbiya Hikimatu wata murnace ta kamata za'aba Hakim Mulki, Yanzun zata fara nuna wacece ita daman tana maganin da zatayi amfani dashi wanda Mamarta ta kawo mata bata damu da yanayin da mijin nata ya shiga ba, suna cikin wannan hali fadawa suka zo suka tafi da Hakim bisa munbari suna ta yi mashi kirari nan sarkin fada ya tashi ya fara naɗa Hakim mulki, ana naɗa mashi yana kuka dan yana tsoran masifar da ke cikin mulki, yana gama naɗashi kowa da kowa ya miƙe ya fara yi miƙa gaisuwa ga sabon sarkin su wato *SARKI HAKIM ABDULMALAK MUHAMMAD*, suna gamawa kowa ya tashi zai gama gabanshi ji mutane suke tum Gimbiya Zulaha ta yanke jiki ta faɗi sumaimiya, da gudu Hakim da Hamad sukayi kanta suna kiran "Gimbiya."... Abun ya ba kowa mamaki yanda Hakim yake gudu dan chito da ran Gimbiya Zulaha, ɗaukarta yayi nisa kafaɗarshi yayi hanyar shashenta da ita dan Hamad kasa komai yayi sai aikin kuka yake dan bai san ya zaiyi ba idan ya rasa mahaifiyarshi da mai zaiji da rasa mulki da yayi ko kuwa rasa Hakima da yayi ko kuma rasha mahaifiyarshi?, haka suka ɗunguma su dukansu suka nufa shashen Gimbiya Zulaha, ita kuma Gimbiya Kilishi bata damu da yanayin da Gimbiya Zulaha ta shiga ba ta wuce wajen Turmursturs ranta ɓace.




💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼Jama'a kunga yanda Shekara biyar ta yi dasu Gimbiya Zulaha🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣.



🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔
Komai Gimbiya Kilishi taje tayi ma Turmursturs 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼


Shin Gimbiya Hikimatu zata hakura da Aziza tayi aiki da maganin nan yanda ya dace🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔



Wai Allah na yau nagaji sosai wlh 😭😰


Much love my dear Fan❣️🔐

*Masoyana duk mai bukatar karanta IZZAH KO MULKI yayi ma wannan num mgna 08160508316*

_By Jameelah jameey ✍🏻_




#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please




👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```



99&100


Tana zuwa ta iske Turmusturs kwance rai hannu ga Allah cewa take, "kan bala'i nan wallahi ko mutuwa kayi sai ka tashi ka gaya man abun mai ya hana Hakik da Hamad mutuwa a yau ɗin nan sai dai naga na naɗa Hakim mulki bayan kace mutuwa zaiyi."?


Duk Turmusturs baijin dadin jikinshi hakan bai hanashi tashi ba yayi ma Kilishi bayani daman yana jiran zuwansu ita ko Zulaha yaji dadi da Kilishi tazo dan yafi bukatar ganinta, dariya ya farayi, sannan yace, " Kilishi daman wannan ranar nike jira kuma ga tazo, hahahhahahah! Sakara kawai kinsa duk abunda ni Turmusturs nike gaya maku gaskiya ne."?


"Ikon haka ne kun zama wawaye keda Zulaha, bari na baka labari dani Turmusturs baban bokane, amman daga baya nadaina bokanci tuni ina dai nan zaune ina cin kudin jahilai irinku wanda basu dogara ga Allah ba suka dogara da wani wanda bai iya yi maku maganin komai inba ba Allah ba, ina sane nace ku bari sai shekara biyar ta cika nasan duk masifa kafin shekara biyar Hakim yayi aure harma ya haihu idan da rabon haihuwar wayau nai ta yi maku na hanaku zuwa wajen ko wani boka kuka dogara dani dan ceton rayuwar bawan Allahn nan Hakim, Hakim baiyi maku komai ba kun sashi gaba saboda da neman duniya bayan kun manta barin duniyar zakuyi baki ɗaya ku koma ga Allah, amman idanuwanku sun kulle Kilishi."



"Ina mai baki shawara kidaina duk abunda kike yi dan nima na daina harta zina duk na tuba na daina na koma ga Allah, to kema Kilishi ki koma dan shine tsaranki a gobe ƙiyama, kuma abu na biyu da zan gaya maki shine ki fara zuwa asibiti ansar maganin cutar ƙanjamau dan likitoci sun tabbatar man da ina ɗauke da ita sama da shekara 50 itace sillar kwantar dani dakika gan ni nan, ni dai abunda zan gaya maki kenan Kilishi, nima nan ƙarshe na nike jira kuma ban gajiya da neman yafiyar ubangijinmu Allah domin shi Allah gafurun rahim ne, dan haka bani da gurin komai sai na cikawa da imani kema ina maki fatan alkhari, kuma mu yafi... Gimbiya Kilishi ta cakama Turmusturs wuƙa a ciki, sake fiddo wukar tayi tfa sake caka mashi tana cewa, "Turmusturs Ni Gimbiya Kilishi ina iya kashe kowa a wanann lokacin duk munafintata da kayi har kake da bakin da zaka gaya man na tuba zuwa ga Allah, to na kasheka har lahira sai kayi tubar mai dalili, haka ta juyo ta bar gawar Turmusturs a dokar daji idan zakuna sun zo sunyi kalaci a cewarta daga wajen Turmusturs asibiti ta wuce nan aka gaya mata tana ɗauke da cutar H. I. V. AIDS, gaban Likitan ta fara ihu tana rawa tana cewa, "sai ni Kilishi, nice na kashe Ƙawata warda muke uwa ɗaya nazo na kashe boka Turmusturs sann... Likitan da sauri ya kulle mata baki yana kallonta dan ga dunkan alamu ta haukace, da yake babban asibiti ne direct wajen an gwajin ƙwakwalwa aka kaita bincike ya nuna Gimbiya Kilishi ta haukace, gashi basu san ko wacece ba, ana cikin Haka Aliyu ya shigo asibitin yana sauri dan wani abun awo yazo ɗauka a offices ɗinshi wanda zaiyi ma Gimbiya Zulaha gaji su gane abunda ke damunta, nan ya tadda an kulle Kilishi a bakin asibitin wai ko Allah zai jefo wanda ya santa, sai sub'batu take iri iri da har ya wuce yaji ana kiran "Shima Hakim ɗin sai na kasheshi.".... Waigawar da zaiyi yaga Gimbiya Kilishi kallo ɗaya yayi mata yagane ta haukace wasu kwala ne masu zafi suka zubo mashi dan tausayinta ya kamashi, sawa yayi aka sata cikin motarta wani likita yayi driving suka ɗauki hanyar masarauta.


________________


Tunda Hakim ya kai Gimbiya Zulaha shashenta ya kira Aliyu akan yazo ya muba masu lafiyarta, dafa Hamad yayi yana bashi hakuri dan sosai Hamad ya bashi tausayi dan ko shi ya san uwa daban take, bayan Aliyu yazo ya duba ta yayi mata duk abunda ya dace har ta farfaɗado nan yake shidamasu ta samu mutuwar rabin jiki(paralasis) sosai Hamad yake kuka dan ji yake kamar yayi hauka wai yau Gimbiya mafi soyuwa a zuciyarshi itace keda wanann cutata, sosai Hakim yake ba Hamad Hakuri dan shima abun ya girgizashi, suna haka Aliyu yace zashi ya ɗauko wata na'ura a hospital ɗinshi zai yi mata wani test anan ne yaga Gimbiya Kilishi.



Bayan tafiyar Aliyu Yarima Hamad ya kama hannun Gimbiya Zulaha sai kuka yake itama kukan take tana girgiza mashi kai alamar yayi shiru, kunyar haɗa ido take Hakim dan tasan komai ya samaita alhakin Hakim ne amman sai gashi ya damu da lalurarta anbashi sarki amman bai damu da yaje fada ba ya tsaya na jinyarta, lokacin sallah yayi yace ma su Hamad su taso suje sallah sai su Hakima su cigaba da kula da ita kafin su dawo suma sai suyi tasu sallahr haka akayi kuwa dan su dukansu suka tafi harda Hamad.


*(🤔🤔🤔Hamad yau zaiyi alwallah yayi sallah jama'a karku manta fa tun tuni na gaya maku Hamad na shiga massalaci da sunan sallah asirin da Kilishi tayi mashi zai ƙarye domin daman duk tsanar da Hamad yayi ma Hakim da san sarautar da yake ba yin kanshi bane duk aikin Gimbiya Kilishi ne har shaye shayen da yake duk yin Gimbiya Kilishi ne to yau dai Hamad ya shiga massallaci💃🏼💃🏼)*


Suna shiga aka fara kiran sallah yaji kasanshi yana juya mashi yace yayi, "INNALILLAHI WA'INNA'ALAI HIRAJIUN."... Yana faɗan haka da ƙarfin tsaya yana faduwa ƙasa, nan wani abu kamar hayaƙi ya kama fita daga cikin hancinshi, Sarki Abdulmalak da Sarki Abdulhadi da Sarki Abubakar sai Hakim da Annas da Humad sai Liman suka ɗauki Hamad suka kanshi fada, har suka kanshi fada hayaƙin nan bai bar fita daga hancinshi ba, hankalin Sarki Abdulmalak ne ya tashi ya sa aka kira mashi wani babban malami a garin zaria nan fa ya fara yi mashi rukiya Aliyu ya shigo da Gimbiya Kilishi a ɗaure kamar an kama biri nan kallo ya koma wajensu dan sai da Hakim ya kama Humad, dan Humad kuka ya fashe dashi da yaga mahaifiyarshi cikin wannan hali daman wannan ranar yake kujemata amman bata jin maganarshi gashi wa gari ya waya, gaban Malan aka ajiye Gimbiya Kilishi sai surutu take kala kala, nan shi dai Malan sai yi ma Hamad rukiya yake nan ya samu suka fara magana aljanun suka gaya masu Gimbiya Kilishi ta turosu jikin Hamad sama da shekara 20 domin su ɓata mashi rayuwa yana bin mata da shaye shaye sannann su dasa mashi son sarauta a cikin zuciyarshi kuma su dasa mashi tsanar Hakim a zuciyarshi dan haka komai suka ga Hamad nayi duk bai san yana yi ba sune suke tashi, nan fada tahau salati kowa yana mamakin bakin hali irin na Kilishi, nan Malan ya ya fidda ma Hamad wannan baƙaƙan aljanun, yanan Hamad ya tashi yana cewa, "AUZUBILLAHI MINAI SHEƊANIN RAJIN."... Nan kowa yace, "ALLAHU AKBAR KABARIN."



Kallonsu yake ɗaya bayan ɗaya yana mamakin abunda ya kawoshi fada, Hakim da Humad suka rungumeshi suna kuka dan ba ƙaramin tausayi Hamad ya basu ba, ace mutun sama da shekara 20 baya cikin yaiyacinshi komai yayi baisan yayi, Hakim godema Allah yayi cikin zuciya da bai taɓa sa yaji haushin Hamad ko dai dai da kwana ɗaya ne, Sarki Abdulmalak ta tashi yayi godiya da Allah da nuna mashi wanann ranar sannan yayi tir da mai hali irin nasu Gimbiya Kilishi da Zulaha, sannan ya tambayi Malan haukan Kilishi mai warkewa ne ko? Nan malamin yace ba mai warkewa bane sai dai shi Hamad ya yaye mata abunda tayi mashi nan Hamad yace ya yafe mata, nan Aliyu yake gaya ma Sarki Abdulmalak Doctor yace Gimbiya Kilishi tana ɗauke da cutar ƙanjamau nan hankalin kowa ya tashi, Sarki da Gimbiya Zulaha da Gimbiya Fulani Aliyu ya ibi jininsu ya wuce hospital dashi test yasa akayi masu Allah ya sosu ba mai ɗauke da ita dan rabon da Sarki Abdulmalak ya kusanci Gimbiya Kilishi har mantuwarshi ta manta, nan aka ɗauki Gimbiya Kilishi aka kaita shashenta aka cigaba da kula da ita ana bata maganin H. I. V, ita kuma Gimbiya Zulaha taji duk abunda Kilishi tayi ma Hamad tayi kuka sosai ta nemi tuba wajen Allah tayi mamaki yanda Kilishi taci amanarta har haka, itama kullun sai Aliyu yazo yayi mata gashin ƙashi yana bata magani Alhmdulh dan jiki da sauki tunda ta fara magana tana ɗaga hannunta Kuma tana zama tafiya ce kawai ta rage a fara koya mata.

_______________


Some days letter


Abubuwa da dama sun faru har da ta samun saukin Gimbiya Zulaha dan yanzun ba abunda batayi da kanta kamar take da, komai ya wuce dan sun yafi juna ita da Gimbiya Fulani suna zaman lafiyarsu kamar wani abu bai taɓa haɗasu ba, Hakim ya ba Hamad waziri shi kuma Aliyu shine sarkin fada, Humad da kanshi yace yana san a bashi Galadima kuma aka bashi, ansa ranar bikinsu su dukansu, *WAZIRI HAMAD* shida wata ƙawar su Hakima *NANA AISHA* sai *GALADIMA HUMAD* shida *MARYAM* sai *SARKIN FADA ALIYU* shida *GIMBIYA SADIYA* sai *GIMBIYA MARYAMA* ita da *YARIMA ANNAS*, rayuwarsu suke cikin aminci da yarda juna dan soyayya suke nuna ma junansu, Gimbiya Kilishi tana nan ana kula da ita yanda ya kamata dan baka cewa tana da matsalar hauka ma idan ba gaya maka akayi ba.


____________



Yau tun safe Sarki Hakim ya tafi fada ita ko Gimbiya Hakima ta koma da zama shashen Gimbiya Zulaha saboda tsufan da cikin ta yayi haihuwa ko yau ko gobe gashi lokaci guda cikin nata yayi wani irin girma abun har tsoro yake ba Hakima.



Tunda Gimbiya Hikimatu taga ba ba kowa shashen nata ta kira Aziza tazo su dan huta ta rage mata zafi, aiko haka akayi dan tinda Aziza ta zo suke abu ɗaya ko gajiya ba suyi, suna cikin wannan aika aika Hakim ya shigo shida Gimbiya Zulaha da Gimbiya Fulani da Sarki Abdulmalak zasu bashi shawara akan a fidda Gimbiya Kilishi waje a samarmata magani domin ba cutarda bata da magani in ba ikon Allah.



Shigarsu suka wannan ikon Allah koda Gimbiya Hikimatu taga Hakim harda su Sarki nan ta tafasa ihu, tana neman abunda da zata boye jikinta dan a parlour suka taddatasu suna wanann abun, shi Hakim dafe kanshi yayi baice mata komai ba Sarki Abdulmalak da kanshi ya ba Hakim umirnin ya saki Gimbiya Hikimatu, kuma ya kira Sarki Abubakar ya gaya mashi duk abunda ya faru, haka Hikimatu ta haɗa kayan ta sai gida, koda taje gida kashe tane kawai Sarki Abubakar bai yi kuma a ranar ya saki uwarta Gimbiya Binta, daman baiwace bata da kowa Allah ma ya sota tana da wani gida a cikin gari nan ta koma da zama.




Bayan Sakin Hikimatu da sati ɗaya Hakima ta tashi ta nakuɗa.....






_By Jameelah Jameey✍🏻_




#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please


👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```

*ALHMDULILLAH ALLAH NAGODE MAKA DA KABANI LAFIYA HAR NA KAMMALA WANNAN LABARI MAI TAKEN GIMBIYA HAKIMA*

*TO JAMA'A ANCE LAIFIN DADI ƘAREWA TO GASHI TA KASANCE DAMU, YAU NA KAWO MAKU KARSHEN GIMBIYA HAKIMA, WANDA NA ƁATA MA RAI TA SANADIN WANANN LABARIN DAN ALLAH YA YAFEMAN NIMA NA YA FE MAKU 😁*

*NAGA MASOYA SOSAI KUMA INA YI MAKU GODIYA DA WANDA NA SANI DA MA WANDA BAN SANI BA DUK INA GODIYA ALLAH YA BAR KAUNA DAN INAYIN DADIN KASANCEWARKU DANI INA GODIYA SOSAI😁*

*LOKACINE, TABBAS KOMAI LOKACINE GASHI LOKACIN YAYI MUN GAMA GIMBIYA HAKIMA SAI KU TARENI A SABON BOOKS ƊIN NA WANDA ZASU ZO INSHA ALLAH NGD😁*


101&110🔚


Ruɗewa sosai Gimbiya Zulaha tayi, waya ta ɗauko ta kira Hakim ta gaya mashi Gimbiya haihuwa ta zo, Hakim kiran Aliyu yayi suka zo suka ɗauketa sai asibiti, domin ganin anceto rayuwarta ita da abunda ke cikin cikinta.


Bayan sun kai ta asibitin, shidai Hakim kasa tsaye yayi ya kasa zaune dan yana cikin tashin hankali balle da yaga sun kusa aya babu labarin komai tashi yayi kawai yayi alwallah ya shiga massalacin da ke asibitin ya sallah yana rokan Allah ya tada ƙafadun matarshi lafiya, cikin ikon Allah Hakim yana cikin sallah sai ga Hamad yazo yana sanar dashi haihuwar Hakima, duk farincikin da yake cikin sai da ya gama sallah ya ƙara godema Allah sannnan ya tashi ya bi bayan Hamad suna zuwa suka shiga direct wajen Hakima ya wuce bai tsaya tambayar abunda aka haifa ba shidai so yake yaga Jewel ɗinshi wani hali take ciki, yana zuwa ya kama hannunta yana mata sannu, kallonshi tayi sai tayi murmurshi kawai dan har lokacin bata ida jin ta dai dai ba, tsugun nawa yayi yai mata kiss a goshi sannan yace, "Allah yayi maki albarka Jewel, Allah ya saka maki da mafificin alkhari, Allah nagode maka da ka sauki matata lafiya, tabbas yau ranace ta farinciki a gareni Jewel da ba abunda ya samaiki ina godiya ga Allah(SWT)."


Kallonshi take wani sonshi ke fisgarta tabbas tayi dacen miji da kowace mace take da burin samu a duniya, duk wani qualities da ake

Please Login or Register in order to submit comment