Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

so namiji yake to Hakim ɗinta yake har ya wuce wajen, riƙe hannunshi tayi tace, "Mijina abun sona ina alfahari dakai Angle, inasonka ina kaunarka, fatana Allah ya raya mana abun da muka haifa."..... Sai da tace haka ya tuna ashe ma baiga mai aka haifa ba cewa yayi, "Jewel fatan dai mace kika haifamana mai kama dake ko."?... Kallonshi tayi tana mamakin tambayar shi sannan tace, "kana nufin bakaga kyautar da Allah ya bamu ba."?


Shafa fuskarta yayi sannan yace, "hankalina baya jikina, yana wajenki lafiyarki itace lafiyata, kece rayuwata idan na rasaki bansan ina zan sa kaina ba Jewel, na safa'a na wutosu parlour na wuto nan domin naga lafiyarki,amman yanzun zan tafi na gano su."

"Ba sai ka taso ba gasu nan mun biyoka dasu.".... Gimbiya Zulaha take cewa haka fuskarta kunshe da farinciki dan ji take kamar Hamad ne aka haifarma yaran, dan yanda take jin Hamad a zuciyarta haka take jin Hakim da Humad suma, taso yayi yana kwantar da kanshi bisa ƙafaɗarta sannan yace, "wallahi Gimbiya na rudene shiyasa ban tambayesu ba."... "Eh ai dole ka rude, kai mai mata ko? To mu kuma masu jikoki."... "Wai kike cewa jikoki ni ɗaya na gani kuma gashi nan a hannunki bani na ganshi ma."... "Wa ya ce maka ɗaya ne? Maryama ku shigo."Gimbiya Zulaha tace tana dariya nan su Maryama suka shigo da yara guda biyu a hannunsu dan maryama ta ɗauki ɗaya Sadiya ma ta ɗauki ɗaya sai ɗaya a hannun Gimbiya Zulaha, ja da baya Hakim yayi, sujada kawai yayi yana godiya ga Allah da ya bashi wannan kyautar dan yasan ba wayaunshi ko dubararshi ba ta bashi wannan kyautar, hawaye ne sarkar a idanunwanshi Gimbiya Zulaha ta fara goge mashi hawayen tana cewa, "Hakim ba kuka zakayi addu'a zakayi masu kasa masu albarka, Allah rayaiyune masu taimakon al'umma kuma mahaddata quri'ani mai girma."


Kai kawai ya girza mata sannan ya anshe su ɗaya bayan ɗaya maza biyu sai mace ɗaya, hudiba yayi masu sannan ya sa masu albarka.


Ta haihu da kwana ɗaya suka dawo gida, sheshen Gimbiya Zulaha dai aka sauke ta ita ke mata wanka dan kula ta musanman Gimbiya Hakima take samu wajen Gimbiya Zulaha ita da yaranta, ranar suna yaran suka ci sunan *YARIMA JALALUNDEEN* shine Hassan sai *YARIMA JAMALDEEN* shine hussaini sai *GIMBIYA JALILA* itace Gambonsu ta ukkun kenan.


Bayan suna da sati ɗaya aka fidda Gimbiya Kilishi kasar saudia dan nema mata maganin haukan dake kanta, ita da Gimbiya Fulani Kubrah suka tafi aka bar Gimbiya Zulaha tana kula da gida ta kuma fara shirye shiryen bikin su Maryama.


Tunda su Gimbiya Kilishi suka tafi saudia aka fara shirin biki dan Gimbiya Zulaha zagewa tayi tana gyara amaran nata harda Hakima itama mai wanka dan duk abunda aka basu Maryama sai anba Hakima itama dan danan suka chanza saboda gyaran dasuke sha ba yau ba gobe, Hakima ta chanza ta zama babban mace dan jegon ya ansheta tayi kyau sosai komai nata ya ƙara fitowa kuma bata shan takurar Hakim saboda yana fada bai dawowa sai dare kuma yana zuwa Gimbiya Zulaha taga zai takura mata zata korashi a haka akai tayi har tayi arba'in, kamar yanda al'ada take haka Gimbiya Zulaha ta shirya ma Hakima komai ta sa harda su Maryama suka tafi kano yawon arba'in, taga kokarin Hakima tunda akayi bikinta ba ta sake zuwa gida ba, sai da zata yawon arba'in, aiko Hakima tayi murna sosai dan sai da sukayi faɗa da Hakim wai tana murna zata tafi ta barshi bata ko tausayinshi haka dai suka rabo wai yana fushi da ita, tafiyar su itama Gimbiya Zulaha ta shirya ta tafi Dubai dan haɗo ma su Humad lefe da kuma yin kayan ɗakin su Maryama.


Sai da sukayi sati ɗaya sannan suka dawo, gida kwana ɗaya tayi a shashen Gimbiya Zulaha ta haɗa komai nata aka maidata shashen ta dan Gimbiya Zulaha ta fahimci idan bata maida ma Hakim Hakima ba to ya kusa shima ya haɗo kayanshi ya dawo shashen ta shiyasa ta bashi mnatarshi can su gane tunda daman ta gama komai ya dace ayi ma Hakima, ranar da ta koma Hakim yasa doka a fada ko wani lokaci Sarki yana iya tashi yaje yaga lafiyar iyalanshin, sannan ba kullun zai ringa zuwa fada ba, randa bai samu damar zuwa ba Hamad ko Humad suna iya zama bisa kujerar suyi duk abunda ya dace ba dole sai shi ɗaya ba zai kama hawan kujera ba, kowa yayi na'am da dokar Hakim daman fadawan duk sa'in ninshi ne shiyasa.

Koda ya tashi daga fada yana dawowa gida ya tadda tana ba Jalalundeen nono shi kuma Jamaldeen yana kuka wai shi a dole sai ta dai na ba Jalalundeen ta bashi bayan bata daɗe da bashi ba amman da yake Jamaldeen yana da rigima shine yake yi mata kuka, ita ko Jalila wasanta take dan su duka sun fara rairafe ga wayou dasuke dashi masha Allah, yana shigowa ya ɗauki Jameldeen yana cilawa sama yana yi mai wasa, nan aka samu yayi shiru, Hakim ya tambayeta abunda tayi mashi har yake kuka, "Jewel kinsan bansan kukan Jamal ko."?... "Angle wallahi bansan ina Jamal ya kwaso wannan halin ba, ace yaro bai san gaskiya komai sai dai ace shi ɗaya za'ayi ma? Yanzun nagama bashi nono, daga yaga na fara ba Deen shine fa ake wanann kukan."... "Ai ba kyaleshi zakiyi ba Jewel lailashin shi zakiyi ai.".. "Nace yayi shiru fa.".. "Ko."? Abunda yace mata kenan ya cigaba da lailashen Jamal sai dai yayi shiru sanann ya sauke shi ya ɗauki Jalila da take wasanta ba ruwanta da rigima, wasa ya cigaba da yi mata tana dariya, bayan ta gama basu nonon suka shiga ya taya ta yi masu wanka sannan suka yi masu shirin bacci, suna gamawa Gimbiya Zulaha tayi aike a bata yaran dan wajenta zasu ringa kwana haka suka bada yaran aka tafi dasu shashen Gimbiya Zulaha, bayan tafiyar su ya ɗauke ta bai sauke ta ko ina ba sai toilet cikin kwamin wanka nan shima ya shiga zasuyi wanka, kissing ɗin juna suka fara sai da suka gama dan taɓai taɓainsu sanann sukayi wanka suka fito, Hakim da kanshi ya shirya ma Hakima sannan shima ya shirya ya ɗauke ta sau bisa gado yayi mata rumfa ya fara aika mata sakonninshi masuwuyar fassarawa wanda suke sa Hakima ta manta da wacece ita, koda naga abunda ya fi ƙarfina na haɗo yan kafafuna nace su Sarki Hakim asuba ta gari.



Yau biki saura sati, shiyasa masarautar zaria ta fara ansar baki daga kasa daban daban, haka suke ta ansar baki kullun ranar duniya, yau saura kwana uku biki dan ankawo laifen Maryama sannan itama Sadiya ankawo nata suma su Hamad ankai nasu, yau Yarima Annas ya sauka masarautar zaria domin ayi biki su koma da amaryarsu, anyi biki na gani na faɗa dan najeria baki ɗaya maganar bikin akeyi bayan angama aka kai ko wace amarya gidan mijinta sai dai muce Allah ya kawo daitin ɗaki😁.


Bayan biki da sati biyu, yau su Gimbiya Kilishi suke dawowa daga kasar saudia, Alhmdullahi ta samu saukin haukan kuma an haɗo mata maganin H. I. V ɗin dake damunta dan idan ka kalleta ba zakace tayi ciwon hauka ko kuma tana ɗauke da cutar H. I. V ta kwantar da hankalinta tana shan magani kuma tayi nadamar abunda ta aika ta kanyin kuka idan ta tuna aika aikar da tayi a duniya dan tasan ita mai lefice da hannunta ta kashe ƙanwarta saboda soyayyar Sarki Abdulmalak ana sauran sati bikinsu aka wayi gari aka tadda gawarta aka maida biki da Gimbiya Kilishi, dan hannunta ta kashe boka Turmurtus kuma da kanta tayi ma Hamad asiri saboda da son duniya da bin zuciya gashi ta kaita ta baro ta, bayan sun huta suka haɗu a parlourn Sarki Abdulmalak bayan kowa ya zauna Sarki ya tashi ta fara magana yana cewa, "Alhmdullahi Ala'kulli hailin, Allah na gode maka da ka cika man gurina ka haɗa man kan iyalana, tabbas wannan yin Allah ne kuma ina ƙara gode maka ya Allah, kamar yanda kuka sani komai ya faru cikin masarautarnan mai dadi da marar dadi, wanda ba sai an tsaya gayashi ba kowa ya sani, tabbas Gimbiya Kilishi yana tayaki murnar dawowarki cikin hankalinki, sai wanann abun ya zama izina a gareki, ke bama ke ɗaya wannan abun zai ma izina ga duk wani mai kallar halinku keda Zulaha, domin ba hanya bace mai bullewa ba, Allah yasa mudace.".. "Amin."baki ɗayansu suka ansa, sannan ya cigaba da cewa, "Kilishi kinsan dacewa kina ɗauke da cutar H. I. V wanda kika kwasoma kanki saboda neman abun duniya, Allah cikin ikonsa mu nan ba mai ita dan haka idan kinji baki iya zama dani zakije ki nemo mai irin cutarki ki aura lafiya lau, idan kuma zaki zauna a haka shima lafiya lau, zaɓi ya zama naki."



Shiru Gimbiya Kilishi tayi tana kuka tabbas Mijinta mutun ne mai adalci duk abunda ta yi mashi amman ita yake tambaya zabi, bayan ta cancanci ko wane irin hukunci, amman bayin Allahn nan basu yi mata ba, basu nuna ƙyama ko wani abu daga gareta ba sai ma janyo ta a jiki da suke, kallonsu tayi sannan tace, "ina godiya da hallacinku da kukayi man, sannan ina ƙara neman yafiyarku, ba kamar Maimartaba da Hamad ina neman afuwa ku ƙara ya feman, sannan na zaɓi zama dakai har mai rabawa tazo ta raba."


Su duka wajen "Alhmdullahi." suka ce dan sunji dadi da Gimbiya Kilishi ta zaɓi zama cikinsu, sannan suka ƙara cewa duk sun yafe mata sannan kowa ya wuce shashenshi cikin farinciki, Humad rungume mahaifiyar tashi yayi yana murnar samun saukin ta sanann suka wuce shashenta shida Amaryarshi Maryam ranar nan suka wuni sannan suka koma nasu shashen.


*Bayan shekara uku*


Abubuwa da dama sun faru ciki harda rasuwar Gimbiya Kilishi, sai dai muce Allah yayi mata rahma ya yafe mata zunubanta😭, dan ko masarautar zaria sunyi babban rashi sosai, Allah ya ba Humad hakurin rashin mahaifiyarshi😰.


Bayan rasuwar da sati biyu Maryam ta haihu ta yan biyu duk mace ranar suna yara suka ci suna *KILISHI* suna kiranta da *MA'MA* itace Hassana sai kuma *HALIMATU* suna kiranta da *LEEMA* sunan maman Maryam ce, su Humad anzama Daddy da Momy😁.


Bayan sunan Maryam da wata ɗaya Gimbiya Maryama ta haihu itama ta haifi yan biyu duk maza, yara sukaci suna, *ABDULHADI* shine Hassan, sai kuma *ABDULMALAK* shine Husaini, ranar masarautar Kano ba ƙaramin shagali akayi ba, Gimbiya Maryama ta koma sheshen Gimbiya Fulani Aisha tana yi mata wankan jego, Sai dai muce Allah ya raya ma yan biyu, su Yarima Annas an zama Daddy ita kuma Maryama Momy😁.


Bayan sunan Maryama itama da wata ɗaya Gimbiya Sadiya ta haifi yan biyu duk mata, aka sama su suna, *ZULAHA* ana kiranta da *ANISY* sai kuma *ZAINAB* suna kiranta da *ZEE* sunan maman Aliyu, su Aliyu sun zama Momy da Daddy 😁.



Bayan sunan Sadiya da sati ɗaya Nana Aishatu ta haifi yan biyu mace da namiji ranar suna yara suka ci sunan *MUHAMMAD* suna kiranshi da *MAN* sai kuma *KUBRAH* suna kiranda da *I'RA* su Hamad an zama Daddy da Momy😁.




Bayan duk angama wanann shegali wanda tsayawa na gaya maku zai cinye mana time sosai amman fa ankashe kudi, dan kudi sunyi kuka.





Bayan suna da shekara ɗaya Gimbiya Hakima ta haifi yan biyu mace da namiji lokacin su Jamel suna da sunada shekara Hudu a duniya, murna a wajen su Sarki Hakim abun ba'a maganar ranar suna yara sukaci sunan *AMATALLAH* da *AMATAL RAHIR* ranar sunan ne naga mutane dan can na hango GIMBIYA HAKIMA FAN'S 1&3 suna kwasar gara dan sune yan gaban goshin Gimbiya Hakima wurin suna🤣, waigawar da zanyi na hango yan MANAZARTA WRITER'S suda yan ZEE ABU group suna kwasher rahoto dan su barbaɗama duniya kallar farincikin da keyi wajen sunan nan.



Bayan kowa ya watsa dare Hakim yake cema Jewel ɗinsa, "gaskiya Jewel yau yan Gimbiya Hakima fan's 2 sun bani dariya, kinga yanda na hangosu suna taka rawa dan anko ɗin da suka fidda wajen sunan nan yayi masu kyau sosai."



"Hakane Jewel kaga yanda Bilkisu abukur da adije da Bilkisu d da Zulfa,da Sakina fago, da da da da da da duk wanda suke Gimbiya Hakima Fans 2 take taka rawa gaskiya abun yayi man dadi."



"Nima haka Jewel dan sun nuna mana kara, ilove you more Jewel."


"Ilove uh more my especially one."..... Nan suka haɗa bakinsu wajen ɗaya suna kissing ɗin juna, kamar ba gobe, nan na haɗo yan ƙafafuna ina cewa Allah ya ƙara kawo yan hudu masoyan juna *HAKIM DA HAKIMA* 🔐❤️




































*ALHMDULILLAH, ALLAH ABUN GODIYA, ALLAH NA GODEMAKA DA KABANI DAMAR KAMMALA WANNAN LABARIN NAWA MAI TAKAN GIMBIYA HAKIMA, KURA KURAN DA NA AIKATA A CIKI ALLAH KA YAFEMAN, ABUNDA YAKE MAI ANFANI A CIKI ALLAH KA BANI LADARSHI AMIN YA ALLAH 🙏🏻*




*SAI MUN HADU A SABON BUK ƊIN NA MAI TAKEN SANADIN LINK GA KAƊAN DAGA CIKIN LABARIN👇*


Kwance take bisa makeken gadonta, tana sanye da ash colour night wear, earpiece ne manne a cikin kunnanta tana jin wakarasu *DJ-AB* mai taken *DA* *SO SAMU NE,* hankalin ta kwance babu abunda yake damunta a rayuwa,chatting take yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da alamu chatting din yayi mata dadi shiyasa hankalinta baki daya ya karkata agun chatting din, Allah sarki Safiya kenan...


"Sofy! Sofy!! Sofy!!!, oho ni Fiddausi wannan wata kalar rayuwace yarinyar nan ta daukarma kanta, ace shi mutun baida aikin da ya wuce jin wakokin sai kuma rige waya aikin kenan ba dare ba rana, ke Sofy wai baki jinane, ta buganmata baya sanna ta juyo cikin firgice da tsoro,"Mami, wallahi Mami kin bani tsoro sosai, bansan kin shigo ba sai kawai naji kin bigeni, "ai dole kice haka Sofy, yanzun sofy abunda kika daukarma kanki kena sabo da Allah, wannan ba hali bane mai kyau,"haba Mami, yanzun ke kullun saboda Allah ni mai laifi ce, baki san ki ganni cikin farin ciki, yanzun Mami maiye aibun chatting? Kuma ni yanzun ba yarinya bace tunda har degree nagama, haba Mami ai ya dace ki duba man mana..."



"Sofy, yanzun ni kike gayama haka, to nidai a matsayina na mahaifiyarki ba zan fasa gaya maki gaskiya ba, kuma tun wuri ki dawo cikin haiyacenki wallahi Sofy, haka za'ayi maki auren kina wanann *MUMMUNAR DABI'AR* , ai in ba shi Aliyun ba, ba wanda zai iya rayuwa da ke, dan haka ki tashi daga wannan dogon baccin naki, ina ma fatan kinyi sallahr isha'i? "Aah daman yanzun nike da niyar tashi nayi sallahr kike shigo, "Innalillahi yau naga ikon Allah ni Fiddausi yar-malan, yanzun Sofy har sai yaushe zaki ringa yin sallah kan lokaci? Ke kullun baki sallah sai nace maki kiyi, kinsan ko karfe nawa yanzun? "Eh duka yanzun karfe 10 fa Mami, kuma ai isha'i har gabannin asuba duk cikin lokacinta ne, "To shikenan tunda haka kika ce, tashi kiyi sallah, salan kuma inkin gama sallahr k ikoma bisa network din...

*Hmmmmm wanan kenan Kadan daga litafin sanadin link yana hanya💃🏼*



*Sai kuma IZZAH KO MULKI 👇*

```Wannan labarin ba true life story bane,kirkirarran labarine,Amman yabambanta da sauran labaran da akasaba ji.....```


*IZZAH* *KO* *MULKI* ```labarine mai cike da tuggu na sarauta ga kuma tsabagen mulki Mai cike da izza da kasaita sannnan kuma wannnan labari bana zamanin nambane labarine na DA,saboda baikunshi kayan zamaniba kamarsu,waya mota jirgi dasauransu.```


```Inafatan wannnan labari na izzah da mulki zaikayatar nishadantar da waazantar da alumma baki daya, dafatan Allah yasadamu da mafificin alkhairyn da ke cikin wannan littafi yarabamu da sharrin dake ciki.```

*Masoyana kubiyoni acikin wannan kayataccen littafi mai taken *IZZAH* *KO* *MULKI...* *muje zuwa masoyah fatan alkhairi inayinku..........*



Tafe yake cikin takama da *IZZAH* ga kasaita kamar bayasan taka kasa ga bayinsa dake takemasa baya sunata kirarashi...


"Takawarka lfy Dan sarki jikan sarki taka a sannu Allah ya tsareka daga murmushin makiya,gaba sumul baya lafiya Allah yakara maka yawan rai."



Amman dik wannan
kirari Kai kace ba dashi suke ba,duk inda suka wuce sai bayi sun zube sun kai gaisuwa ko kallon Inda suke bayayi a haka sukaci gaba da takemasa baya....




Da ya doso waje san yayyan kamshin tirarensa ke sanar da zuwansa.....



Babu inda suka tinkara sai wani hadaddan lambu,masu kula da lambun tin daga nesa suka ruga suna masa sannu da zuwa,nan yashiga cikin lambun....




Tin kafin ya isa wajen hutawarsa har an kayata wajen yasha kilissai ga kayan marmari Kala-Kala abun ba'acewa komai,Amman duk irin nau'in kayan itatuwan nan ko kalansu baiyi ba,saboda a wannan lokacin ba, abinda ya kawoshi kenan ba......




Kafin ma ya zauna wani aikin, kai kace bashi aka gyarawa wajenba,sai da ya ɗauki wajen kusan minti ukku sannan yayi yun kurin zama,nan fa bayi suka,fara cewa .


"Zaman ka lafiya magajin gobe Allah "Allah ya taimakeka...... "



Bayan ya zauna da minti biy, ya daga musu hannu atake kowa yawatse,
yabar wajen domin kobai magana ba sun gane abinda yake nufi.



Hakadai ya zauna yana ta yan'tinane tinane ba abinda yake tinawa sai irin kalubalen da yake fuskanta akan yanda kowa idonsa na kanshi kuma shi ba ma'abocin san mulki bane,duk da cewa mahaifinsa yana samasa ra'ayin hakan.....




Dan yasan masarautar su cike take da kalubale ga tuggu da makirci kala-kala......



Yana zaune yana wannan nazari sai ga babban bawansa na hannun damarsa,saminu yazo yasanar masa maga takarda nasan ganinshi.




Sai da yadauki yan dakikai sannan ya kalleshi hakan yabasa daman komawa yai masa iso har wajen hutawarsa.....




"Hutawarka lfy bango majinginar marayu magajin gobe, mai martaba yace in kawo maka wannan sakon.... "



Ya dago, ya daura masa wannan sexy eyes din nasa,sai yayi zaton kamar harararsa yayi take gabansa yafadi.....



"Tuba nake ranka shidaɗe Allah ya huce zuciyarka.".. Nan ya kalli saminu,ya anshi takardar yamika masa,Kai kace bashi akamiko mawaba



"Allah yataimakeka gashi sannan yasa hannu ya'ansa....."




Kamar bai san budawa yabuda yana tinanin me mahaifin nasa zaice a takarda yabude ta kamar haka....



_"Assalamu-alaikum,

_dafatan ka riski sakona inasan ganinka yanzun a fada,bissalam".__



*IZZAH KO MULKI KENAN, KUDAI KU CIGABA DA BIYOMI DOMIN SANIN YANDA WANNAN ABU DRAMAR ZATA KASANCE💃🏼*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment