Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kyauta, na lura kifi son Hakima a kaina komai akayi nine banda gaskiya"...



"Yes of course! Nidai naga kai ka wurga mata ɓawon ayaba, maimakon ka bata hakuri sai MULKI DA SARAUTA suka hanaka dan gani kake ka fi karfin da zaka bata hakuri, ita kuma taga bata iya kyaleka har ta rama"..



"To na Hakima naji sai akayi ƙaƙa? Dan haka ba ruwanka faɗana da Hakima kasa ido kayi kyalo shine naga OK?! "..


"Ni kuma bani yin shiru mudin nagani sai nayi magana, kawai ina ganin gaskiya a hana ni magana gaskiya sai nayi"..


"To parrot! Ai sai kai tayi, tunda bakasan kaga bakinka yana shiru ni tashi ka ban waje zani gaida Fulani"...



"Ai bakai daya keda Fulanin ba, dan haka tashi mu tafi daga nan naga Sahibata"..


"Baka da kunya a gabana? Kayi addu'a Allah yasa Maimartaba indan ya tashi badasu ya sa sunanka"..



"Amin ya Allah! Nifa Hakim duk wanda aka bani inaso dan ai duk kamarsu ɗaya dan har yanzun bani gane Maryama balle Sadiya"...



"Hakane kake wahalar banza baka ganesu kenan? "Wallahi ko"to Allah ya kyauta niko dai ba gaya maka zanyi ba"...



"Naji tashi mu tafi! Nan gaba dole na ganesu insha Allah tunda ɗaya zata zama halak malak ɗina"..



Haka suka tafi shashen FULANI shidai Hakim yana mamakin yanda Aliyu yake kare Hakima bayan duk rashin kunyar da take yi mashi..


Shidai baya iya ƙyaleta yaga tana yi mashi rashin kunya dan ko su Maryama sun girmi Hakima da shekara ɗaya ko biyu shiko maganar gaskiya baya iya daukar rainin wayau Hakima..


"Fulani barka da hutawa, "Yauwa Aliyu! Yau kenan a gidan namu? "..


"Laaaa! Ina neman afuwa Fulani amman ina shigowa sosai"..



"Eh ba laifi, dan nasan kafi wancan ɗan neman, dan na lura baki ɗaya Hakim baya san zuminci"..


"Aa Fulani ki bar cewa haka, wallahi kullun sai naje na gaida Mama ko Aliyu? "..


"Eh gaskiya kana zuwa, nine dai bani shigowa sosai, ina neman afuwa kuma"...


"Ai Aliyu nasan ya zuwa shashen ku sosai, ina nufin baya zuwa shashen Su Gimbiya Zulaha da Kilishi kaga banjin daɗin haka gaskiya Hakim"...



"Allah ya taimakeki yar'sarki matar sarki kuma jikar sarki, amman ba uwar sarki ba dan ni bani san sarauta na barma Hamad yaje ya riƙe"..



"Aa Hakim inkai baka so mu mana so a baka ko Fulani? "..


"Kudai kuyi fatan Allah ya tabbatar maku da alkhari cikin rayuwarku, mu kullun shine fatan mu dan haka idan ba Mulkin bane alkharinka Hakim Allah ya taya Hamad riƙo, in kuma shine alkharinka Allah ya tayaka riƙo"..



"Kuma ba wannan ba Hakim! Ya kamata ka fiddo mata hakanan dan na gaji da ganinka haka babu mata, ina amfani ku dukanku babu aure bakai babban ba ba ƙannanka ba"...



"Insha Allah Fulani zanyi koƙari naga na fidda mata dan bansan Maimartaba ya fara yi man maganar fiddo mata"...



"Aiko yana hanya dan har ya fara yi man magana kawai dai kaine bai kai dayi mawa ba"..



"Ai Fulani kafin ma yayi ma Hakim zai fiddo mata, dan yana nan yana neman wata... "Dakata haka dan Allah parrot uban yan'surutu"..



"Ya ka buge mashi baki? Bangane yayi shiru ba Hakim? Bakasan ya gayaman inda sirikar tawa take dan daman nasan Aliyu yasan inkanada Budurwa ko ma baka da ita dan shine kawai abokinka"..



"Wallahi Fulani banda ko kiyashi amman insha Allah zan fara neman budurwa verysoon insha Allah "...



"To Allah yasa! Inata addu'a dai Allah ya haɗaku da nagari, "Amin ya Allah "..


"Wai Fulani ina su Maryama suke? "Basunan sun tafi gidan su Maryam amman nasan suna hanya yanzun haka "..



"To Allah ya maidosu lafiya, "Amin, "Fulani maiyasa ake barin su Sadiya suna fita wai? "..


"taya zan hanasu zuwa gidan su Maryam bayan kasan wacece a wajensu"..


"Hakane mu zamu wuce Fulani mun barki lafiya, "uhmm"...

___________________________



"Gaskiya Maryama abunda Yaya Hakim yayi ma Hakima bai kyauta ba baki ɗaya"...



"Dan Allah mai yayi mata? ".


Nan Maryam ta gayama su Sadiya abunda Hakim yayi ma Hakima..



"Wallahi da kun ganta a lokacin sai ta baku tausayi dan kuka ta kama yi ni na kaita gida da kaina".


"Gaskiya Yaya Hakim bai kyauta ba, muda muke san su auri juna taya haka zata kasance yana yima ta kallar wannan cin mutuncin? "..


"Aa ai ko baya taɓa yuyuwa dan ko ni bani auren wanda ya tsaneni, to wani kallar rayuwa zasuyi bayan nasan baya sona ya tsaneni nida nike son nayi auren soyayya"...




"Kamar kin sani karkiso kiji yanda Gimbiya Hakima ta tsani Yaya Hakim, dan yau ta faɗi kalmar tsana bansan iyakaba"..


"Banga laifinta ba gaskiya ai abun yayi yawa, Fissabililah ai cin fuska baida dadi, sai kace ba yan'uwanjuna ba"..


"Yan'uwanjuna kuma? "..


"Ehman Sadiya yan'uwanjuna tunda su dukansu muslmai ne suna sallah kinga ko sun zaman yan'uwa"...



"Hakane kuma ai nasa mu yan'uwa ne, "Aa ko ɗaya kawai dai jininmu ne ya hadu da nata tun bamu ganta ba"...



"Wallahi ko! Jinike kamar naje na ganta amman ba dama, "aiko dai, dan Allah Maryam ki ƙara bata hakuri sosai please"..


"Ok insha Allah, "mu zamu wuce gida kinga dare ya fara karda mu kashema kanmu kasuwar gobe"..


"Gaskiya ku tashi ku tafi karda ma ku kashe harda ta jibi, "Byeee ki gaida Hakima, "ok zataji byee..






_By Jameelah Jameey✍🏻_






Share and comments pls


👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_


_Jameelah jameey 🖋_


*(Yar mutan kankia👸🏻)*


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```




35&36




Washe gari bayan Hakima ta gama yin breakfast ta shirya ta wuce school..


"Hakima! ina kwana?, "Yau kuma da wannan kika zo? "..


"Laifine dan na gaida kawata, kuma Gimbiya yar'sarkin Kano? "..


"Aa baki yi laifi ba, yasu Momy?, "suna lafiya Hakima, kawayena yan gidan sarki suna gaisheki"..


"Uhmmm, "haba Hakima ya zani ce maki friends ɗina suna gaisheki amman Uhmm kawai zaki ceman? "..


"Kedai baki gajiya da complain uwar yan complain imeans ina ansawa haba, dole sai kinsa mutun magana koda baiso"...


"Allah ya baki hakuri kenan yau yan mulkin suna bisa kai, Allah ya kyauta, "Uhmmm"..



Nan Maryam itama ta kama ƙanta tunda ta lura da Gimbiya Hakima batasan yin magana itama sai tayi shiru dan bata san suyi faɗa da ƙawar tata..



Nan suna zauna sai ga Hakim ya shigo lecture, ba ƙaramin kyau yayi ba daman abunka da farin mutun ya ɗauko wani bakin bowel mai bala'in kyau da tsada ya sanya sai ya fito jinin sarautar sak da shi dan yau shima sarautar ta mutso mai shiyasa class din basuga fuskar yin noise ba kowa ya kama girmanshi sun naba'a kamar anyi mutuwa..


Koyawa yake cikin natsuwa da jan-class dan ko shi kanshi yana mamakin yanda yake jin bayasan magana, duk da haka halin shi yake amman yasan na yau yafi na kullun..


```Niko Jameey nace jinin sarautar kenan🤣☺️```


Suna cikin yin lecture nan Hakim yayi pointing ɗin Hakima ta fito ta zana mashi wani compoud aiko ba karamin dadi Hakima tayi ba dan har ta shirya irin abunda zata yi ma Hakim, balle da ta lura yau wani mulki yake ji sai kace ɗan sarkin zaria..


```Hahahahaha! TEAM Hakim kunji Hakima da wata magana wai Hakim take cema sai kace wani ɗan sarki kuji fa, koda yake tace shi ɗan gidan uban waye😚```




Tafiya take cikin isa da nuna ita ɗin watace, dan tafiya take amman kamar mai tausayin ƙasa dan bata san taka ƙasar sosai...



Ba Hakim ba harda yan class suna mamakin yanda Hakima take tafiya duk da sun saba da halin Hakima ba sabo bane a wajensu amman suna mamakin izzarta, kamar wata yar'sarki...



```Tofa! Team Hakima kunji fa abunda yan class da Hakim suke cema Hakima wai kamar wata yar'sarki☹️🙃```



Tana zuwa gaban Hakim ta miƙe hannu ta amshi maker ɗin da zatayi using da ita, daman takalmin Hakima ba flat bane, masu tsinine dan haka tana sane ta takema Hakim ƙafa, dan sai da yace..


"wash!.


Amman Hakima ko a jikinta dan nunawa tayi kamar bata taka komai ba, ta cigaba da abunda ya sata, baki ɗaya class din sai da suka tsorata...




Hakim ba ƙaramin zafi yake ji ba, dan yana ma tunanin yatsan ƙafarshi ya cire yanda Hakima ta take mashi su, kuma ta saki ƙarfinta baki ɗaya bisa ƙafar...



Amman da yake Hakim jarumin Namijine sai ya dake bai nuna yasan da wani hallita a ƙafarshi ba, duk da jinin da yaga ya fara fitarmai a ƙafa amman ya dake yanuna ma students dinshi bai damuba..


Hakima bata gamaba sai da ta tabbatar da Hakim yaji jiki sanann ta juyo ta miƙe mashi maker, suna haɗa ido ta kashe mashi ido ɗaya tayi mashi nuni da ita Hakima tafi ƙarfinshi dan ta wuce duk wani tunaninshi..


Hakim bai nuna ya ganta ba, haka ya cigaba da lecture ɗinshi har ya samu ya gama sanann ya fita..



Tafiya yake yana mamakin yanda Hakima ta raina mashi wayau, ta maidashi wani abokinta..



"Tabbas indan na biyeta Hakima ina iya lahantata, harni Hakim Hakima zata fiddama jini? Tabbas nayi sake da na bari Hakima ta rainani har haka"..


Hakim ne ke wannan maganar yana ɗaukar hanyar komawa gida yana mamakin rainin da ke tsakaninshi da Hakima...



"Haba Hakima wai bakiga abunda kikayi ma prof Hakim ba? "..


"Maryam na fahimci baki san Allah, ni bakiga abunda yayi man jiya ba? Dan na rama sai ya zama laifi? "...



"Ya kamata kubar yar'ramuwarnan keda prof Hakim, sai kace ƙananun yara, sai kace ba jinin sarauta ba"...


"Wannan matsalarkice, dan ina jinin sarauta sai akace karna rama abunda akayi man ko? "..


"Baki fahimceni ba, bake ɗaya bace jinin,"enough please Maryam ni kinga tafiyata gida dan inada abun yi, kuma wallahi Maryam ki kiyaye ni na gaya maki gaskiya ki zaɓi cikin biyu ni ko Hakim byee"...


"Allah ya baki hakuri ke na zaɓe ma ba sai gobe ba, byee"..

______________________________

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya rashin ganin mutuncin juna sai karuwa yake tsakanin Hakim da Hakima..



Dan ba wata jutuwa suke ba har yanzun, Hakima bata da wanda ta tsana kamar Hakim..


Haka shima Hakim bayan kaunar Hakima, dan baya san mutun marar kunya da ganin girman na gaba da shi..


Kuma ya fahimci baki ɗaya Hakima yarinya ce wanda batasan ta girmama na gaba da ita ba..


```Ni kuma nace kuji man Hakim yasan da haka yake biyema Hakima suna kallar wannan bed habib ɗin☹️ kash Allah dai ya shiryasu baki ɗayansu```


Hakima tasa karatunta gaba dan har sun fara exams ɗin second semester kuma daman an fiddo mashi result itace over rolla, tayi mamaki da Hakim bai kadata ba a course din shi..



Haka dai suka gama yin exmas dinsu har Gimbiya Hakima ta koma gida hutun season...



Su Gimbiya Zulaha kuwa suna nan sun zuba ido suna jiran wata hudu yayi suga gawar Hakim.. (Lol😜)





```My guys kudai ku cigaba da biyoni kuga kallar cakwakwakiyar da za'ayi tsakanin wannan mutunan guda hudu☺️💞```



*Gimbiya Hakima da Yarima Hakim*

*Gimbiya Zulaha da Yarima Hakim*


*Gimbiya Kilishi da Yarima Hakim*


*Yarima Hamad da Yarima Hakim*



_Wai Allah na kai dai Hakim kaga ikon Allah kowa da akai yake faɗa ayya Hakim bakai ne baka da gaskiya ba🤔_



*Team Hakim ina jiran Answers ɗinku wai shi Hakim ba shi bane baida gaskiya ba☺️*




_By Jameelah Jameey✍🏻_



Share and comments pls



👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_


_Jameelah jameey 🖋_


*(Yar mutan kankia👸🏻)*


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```



37&38




"Gimbiya Hakima! Uwargijiyarmu barka da dawowa wanann masarauta mai albarka"..


"Uhmmm! Ladi ina fatan kuna aiki yanda ya kamata? "..


"Eh Uwargijiyarmu muna yi, muna farin cikin dawowarki uwar marayu"...


"Zaki iya tafiya, ki gayama yan'uwanki da su tabarta da suna aiki akan lokaci"...



"Angama ƴar'sarki jikar sarki, na barki lafiya, "Uhmm"...


"Larai! Mu godema Allah wanan karatun yasa Gimbiya Hakima ta chanza baki ɗayanta"...


"Aiko dai Larai, karki so kiga kallar farin cikin da nike, domin koni jiya da naje yi mata barka da dawowa fuskar sake ba kamar da ba "...



"Alhmdulh! Hakan ma mungode, indai babu wanann zagin dake yi mana ai ba komai "..


"Zaman lafiyarku da Gimbiya Hakima shine ku ringa yin aiki kan lokaci, dan ita Gimbiya Hakima batasan taga mutun bai san abunda yake ba"..



"Hakane kuma Inna Lantana insha Allah zamu kiyaye duk abunda Gimbiya Hakima bata so, insha Allah zamu kiyaye"..



"Allah yasa, ni na wuce wajen Gimbiya tana jirana, "a fito lafiya"..


"Hutawarki lafiya ƴar'sarki matar sarki".


"Lantana na fahimci bakisan ki dunga ganina cikin gidan nan ko? "..


"Allah ya huci zuciyarki, ai idan baki gidan nan muma ai barinshi zamuyi, dan kice gidan baki ɗaya zaman ki muke Allah ya taimakeki"..



"To maiyasa kike ceman matar sarki? "..


"Allah ya taimakeki, ai aure dole ne Gimbiya Hakima uwar marayu, muna fatan muga jininki a hannunmu"...



"Hmmmm! Naji yanzun dauko wannan tsarabar da mukayi ma bayin shashena ku raba kuba kowa kosan shi, sannnan ace ma su Ab'u yau su haɗa Liyafa mai kyau anjima zani ci abincin dare da kowace ma'aikaciyar shashen ni Hakima a babban parlour na"..



"Angama Gimbiya Hakima, Allah ya ƙara lafiya ya rabaki da murmushin mahassada"..


"Yanzun kinji matsalarki, kedai baki gajiya da fadanci tashi ku fara aikin da na saku, ke kuma Azima shiga toilet ki haɗa man ruwan wanka"...



"To Uwargijiyarmu, Allah ya ƙara girma"..


Nan Azima ta shiga toilet ta fara haɗama Gimbiya Hakima ruwan wanka, su kuma su Bilkisu suka fara rabon tsarabar da Gimbiya Hakima tayi masu..


"Allah ya taimakeki, nagama haɗa ruwan yana jiranki a bayi"..


"Ok! Nasan kinfisu sanin kaya masu kyau, dan su sun tsufa basu san zamani ba dan haka ki fiddo man kaya wanda ina gani zan yaba, inkin fiddo ku wucewarku kuma ku fara shiryawa kafin lokacin Liyafa"..



"Ranki yadaɗ'e angma, a fito lafiya uwar marayu, ", Allah yasa"..


Nan Azima ta fiddo ma Hakima kaya sannan suka kwashe tsarabar su suka wucewarsu..



"Sannunku mutanan madafa, "yauwa Aa ya mukaga iyayyen kaya a hannunku haka? "..


"Ga naku tsarabar Gimbiya Hakima ce tace a kawo maku, sannan kuyi abinci mai rai da lafiya tare da ita yau za'ayi Liyafa a babban parlour dinta anjima da dare dan haka sai kuyi sauri ku gama kuje ku shirya muma shiryawa zamuyi"...



"Alhmdulh! Alhmdulh!! Alhmdulh!!! "..


"Allah mun godema ka da ka anshi addu'armu da ka shiryar da wanann baiwa take Gimbiya Hakima "..



"Jama'a wai da gaske ne yau ɗin nan Gimbiya Hakima zatayi Liyafa damu? Bayan mu bayi ne wanda ta tsana take ƙama mune abun wulakantawarta a kullun"...



"Ai Allah kenan, kinga Gimbiya Hakima zatayi abunda ba'a taɓe yi ba a masarautar kano, dan shekarata asherin (twenty) ba wani ɗan Sarautar da ya taɓe cin abinci cikin bayin shi sai Gimbiya Hakima da zata fara a yau ɗin nan"..


"Gaskiya hakane Inna Lantana Allah yasa ta ɗaure a haka, "Amin mu mun wuce mukai ma sauran tsarabar su, kuma kuyi sauri ku gama dan Allah kafin lokaci yayi"..


"Insha Allah Ba'ba Bilkisu, daman mun kusa gamawa da yardar Allah"...



Nan su Bilkisu suka cigaba da rabama bayi tsaraba suna gaya masu su shirya zuwa anjima zasuyi Liyafa da Gimbiya Hakima cikin babban parlourn ta..



Nan take maganar ta gauraye masarautar baki ɗayanta kowa yana mamakin wai Gimbiya Hakima itace da ba bayinta tsaraba harda Liyafa zasuyi anjima..


"Ranki yadaɗ'e Gimbiya Fulani, yau nazo maki da labari mai daɗin saurare"..


"Ina saurarenki Zainabu Allah yasa naji daɗin da kike faɗi "..


"Zama kiji Uwargijiyata! Daman yau Gimbiya Hakima ta raba ma bayin ta tsarabar dawowa, sannan tace anjima su shirya zasuyi Liyafa tare a bangarenta da daren nan na yau"..



"Alhmdulh! Gaskiya ko Zainabu kin kowaman da labari mafi dadi cikin labarin da kike kawoman, dan haka kije na baki kyautar gold da murjani"...


"Godiya nike, uwar masu adalci Allah yasa Gimbiya Hakima ƴar'sarki ta ƙara koyi da ƙyaukwan hali irin naki".



"Uhmmm! Abunda Gimbiya Fulani tace ma Zainabu sannan ta bata kyautar da tayi mata..



Rasa inda zata sa kanta tayi dan murna, dan ba ƙaramin dadi taji ba Hakima ta fara janyo bayinta a jiki ba, bata san sanda ta tashi ta dauki hanyar shashen Maimartaba dan tasan Gimbiya Yakumbo tana can shiyasa batasan abunda daughter dinta tayi ba...



"Ranki yadaɗ'e Gimbiya Yakumbo! Gimbiya Fulani tana neman ki bata iso tana san kuyi magana"..



"Maza kije kice mata ya shigo, "angama Allah ya ja da tsawancin kwana, Allah ya taimakeki Gimbiya Fulani! Gimbiya Yakumbo tace ki shigo, a fito lafiya"...


"Assalama Alaikum"..


"Amin wa'alaikumus Sallam"


"Fulani naji kince kina san magana dani?, "eh Yaya! Ina Maimartaba yake? "..



"Yana ciki yanzun zai fito, ga dunkan alamu yau kina cikin farin ciki Fulani, dan ga shi nan fuskarki ta nuna"...



"Sosai ma Yaya, sannu da fitowa Maimartaba, "yauwa Amaryata Fulanita, fatan lafiya dai ko? Ko kuma Yayartaki kika biyo? "..



"Aiko dai, kasan ban iya kwana banga Yaya ba, daman zuwa nayi nagaya maku yau Hakima tayi abunda ba'a taɓe yinshi ba amasarautarnan "..



"A'aa mai tayi kuma Hakimar?, "yau taba bayinta tsaraba sannan tace anjima su shiryasa tare zasuci abincin dare"..


"Alhmdulh! Kunga abunda nike nuna maku ko? Da kun kun nace a dole sai na fidda Hakima kasar waje karatu, ba kamar ke Yakumbota "..


"Hakane gaskiya mijinmu! Munga amfanin karatu cikin talkawa ko, dan tuni na fahimci Hakima ta chanza hali tun dawowarta ta farko"..



"Ai daman nace maku zaman da zatayi cikin talkawa tana ganin yanda suke rayuwa dole itama watarana ta chanza, balle nasan duk mulkin Hakima sai tayi ƙawa, shiyasa ban ajiyeta a nan BUK ba na kaita kasar zaria"..


"Gaskiya ko! Godiya muke sarki mai adalci, "Allah ya ƙara shige mana gaba, "Amin ya Allah ni na barku lafiya"..


"Fulanita gobe ki turoman Hakima dole nayi mata kyauta da wannnan halin da nuna mai kyau cikin masarautar nan"..



"Insha Allah, mu kwana lafiya, "Allah yasa"..


Nan Fulani ta koma shashenta tana jin daɗin yanda suke zaman lafiya itada Yakumbo kamar ba gidan sarauta ba..



"Zainabu kije kice ma Hakima gobe inasan ganinta, "angama ranki yadaɗ'e yanzun ancika umirninki..


Nan Zainabu ta tafi shashen Gimbiya Hakima ta gaya mata sakon Fulani sanann ta koma, ta gayama Fulani tace to..



Masha Allah laƙuwata ilabillah! Tafiya take cikin isa da mulki ga kuma uwa uba aji da kyau dasu ƙara sata jin tafi kowa a kano state baki ɗaya gata kuma ƴar'sarki kuma matar sarki..


```Amman bani Jameey nace matar sarki ba, Inna Lantana ce babu ruwana ba'ajin mutuwar sarki bakina🤭```



Wani Arnan black material ne jikinta, dinki doguwar riga akayi mata, dinki yabi jikinta yayi bala'in ya mata kyau, ga wata alkyaiba da ɗaura a bisa rigar sai ta ƙare fitowa *GIMBIYA HAKIMA* dan ko tafiya dakyal take yinta kamar tana tausayin taka kasa kawai mulki ne yake sa Gimbiya Hakima wanann tafiyar..



"Sannunki da fitowa Uwargijiyarmu "..


Bata kyalesu ba balle su sa ran ansawa, sai da ta zauna ta huta sannan ta kyalesu ɗaya bayan ɗaya sai tace, "yauwa sannunku kuma"...



"Fatan duk kuna lafiya ba mai bukatar wani abu kuma? "..


"Eh Alhmdulh Gimbiya bamu bukatar komai sai farincikinki uwar marayu"..


Kallon su Bilkisu kawai tayi suka tashi suka fara saving ɗinta, sanann sukayi na sauran baki ɗaya bayan sungama suma sukayi nasu suka zauna...


Gimbiya Hakima ta tashi tayi masu addu'ar cin abinci sannan kowa yayi bissimilla suka fara cin abinci..


Wajen shiru baka jin motsin komai sai na cokali, duk da Gimbiya Hakima ba cin abincin take sosai ba dan bata jin yunwa, amman taci yanda ya kamata suma bayin sunci dan harda masu ƙarawa sai da kowa ya koshi sannan suka kama gabansu, bayan sun gyara wajen..


Koda Gimbiya Hakima ta koma ɗaki wanka tayi sanann ta kwanata ta fara waya da Maryam bayan sun gama waya ta kwanata bacci dan zata tashi sallahr dare...



Washe gari bayan Gimbiya Hakima ta gama duk abunda take ta wuce shashen Gimbiya Fulani, bayan anyi mata iso ta shiga..


"Fulani ina kwana?, "lafiya lau Hakima ya kika tashi?, "Alhmdulh "...


"Daman kiran da nayi maki shine kyauta zan baki dan naji dadin abunda kika yi ma bayinki jiya, dan haka na baki kyautar zinari da azurfa sai kudi million ɗaya"..



"Fulani basuyi yawa ba?, "basuyi ba Hakima dan jiya ƙin farantaman sosai, "nagode Fulani"..


Sanann kije shashen Baffahn ki shima yana neman ki, anjima zakiji kuɗin sun shigo a asusunki, ga zinarin da azufarnan wuce dasu Allah yayi maki albarka"..


"Amin ya Allah Fulani, na barki lafiya "..


Nan Gimbiya Hakima ta wuce Shashen maimartaba bayan anyi mata iso ta shiga..


"Momy ina kwana?, "lafiya lau Daughter, ya kika tashi?, "Lafia lau, Baffah ina kwana?, "lafiya lau Mamana"..


"Naji dadin abunda kikayi jiya Allah yasa ki ɗaure haka, sanann anshi wannan makulin motane ki dauka na baki"..


"Baffah! TOYATA A M G MERCEDES 2020 ka bani fa?, "eh Hakima na sani, "wow! Nagode sosai Baffah Allah yaƙara girma, "Amin Hakima".. pls



"Ni Hakima zan turo maki million ɗaya ta account ɗinki anjima, "nagode Momy, ina sonku sosai iyayena, na barku lafiya..


Nan Hakima ta tafi tana farin cikin kyautar da iyayenta suka yi mata, tana zuwa shashenta ta kira Maryam waya ta gaya mata..





_By Jameelah Jameey ✍🏻_




Share and comment pls



👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_


_Jameelah jameey 🖋_


*(Yar mutan kankia👸🏻)*


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```




39&40




"Kilishi ya kamata ki tashi mu tafi wajen Bokan nan tunda ƙafafu sun ɗaga"..


"To Gimbiya yanzun daman nike shirin aiko maki Mariya naji ko kin shirya"..


"Amman kifara fita sanann na biyo bayanki duk da munyi ɓata kama amman mu kiyaye"..


"To mu hadu ta baya, dan yau sai naji abunda yasa Hakim bai mutu ba har wata hudun yayi"..


```Niko nace da alamu Gimbiya Zulaha ta manta da Allah, dan naga kominta a boka ta miƙa shi ba ga Allah ba ☹️😡```


"To shikenan! Nima yanzun zan biyo bayanki, "kidai yi sauri dan nasanki da nawa sosai"..


Bayan fitar Gimbiya Zulaha, Gimbiya Kilishi ta fara magana kamar haka.


"Sakara ai ko bakice ba dole na biki wajen bokan nan naga idan yake nima na ringa zuwa dan da alamu aikinshi yana aiki"..



"Dole naga bayan Hamad, ke kuma Zulaha zan barki kiga bakin ciki, kina kallo Humad zai mulka masarautar Zaria, kina ji kina gani zan zama uwar sarki, shashasha kawai marar wayau kin ɗauki yarda kin ɗauraman"...



Haka Gimbiya Kilishi ta kama surutunta har ta gama shiryawa suka ɗauki hanyar zuwa wajen

Please Login or Register in order to submit comment