Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannann kidahumar baiwar bulala Hamsin, indan tayi kuka ta zube ko kuma ta sosa balle motsawa..


"Angama uwar marayu, godiya take, nan Sarkin bulala ya tashi ya fara zula ma wanann baiwa bulala sai da yayi mata bulala hamsin sannan ya tsaya, "ranki ya dade nagama cika umirninki..



"Akaita gidan horo, ayi mata horo na tsawon sati, angama uwar marayu..


Kai kai kai!!! Gimbiya Hakima ya kamata ki tausaya bayin nan fa😚, suna ce maki uwar marayu, Amman baki tausayinsu hukuncinki yayi tsanani faπŸ’πŸ»β€β™€οΈ, kudai muje zuwa my fanπŸ₯°


"Lantana!

"Naam Allah ya taimakeki, kije kice ma Barde a shirya man dawakai yau zani shakatawa da karfe biyun rana...


"Angama, Allah ya ja da tsawancin kwana..


Nan Inna Lantana ta tafi wajen Barde..



Nan Gimbiya Hakima ta shiga ciki, su Bilkisu suka fara yi mata tausa, azima tana karanta mata novel, kafin anjima su shirya mata zuwa shan iska...


______________________


"Lanto, "Naam Allah ya taimaki Gimbiya Zulaha, "ya kukayi da bokan Lawali?


"Cewa yayi ya zama dole sai ansa ma Yarima Hakim wannan maganin cikin abinci yaci yana ci zai mutu, amman sai in zai kwata bacci za'a bashi abincin yace, yanda ana wayar gari a tashi da gawarshi...



"Da kyau aikinki na kyau Lanto, Allah yasa wannan karan karda ya bata mana aiki, kinsan shi wani kalar mutun ne uwarshi ta batashi da rashin kunya..


"Gimbiya kibar komai a hannuna wannan aikin nawane, yanzun ma zan tashi naje na kai ma Mino kinsan tana daya daga cikin masu dafama Yarima Hakim abinci, na san zata yi aikin yanda muke bukata...



"Hakane Lanto, ni na manta da Mino bangaren Hakim take dafuwa, to tashi ki kai mata amman kice ta kiyaye dan Hakim wayau gareshi, sannan ta kula da idanun mutane..


"Angama ranki ya dade, na barki Lafiya..


Nan Lanto ta tafi shashen Yarima Hakim, wajen masu girki..


"Ranki yadade Gimbiya Zulaha, Yarima Hamid yana san magana dake, "ace mashi ya shigo..


"Allah ya taimakike, "Hamid sai yau ka gadamar dawowa cikin masarauta? "Haba Gimbiya to mai zan tsaya nayi cikin masarautarnan basu mata babu abun sha sai lemu da tufa..



"Wai Hamid sai yaushe zaka daina neman matan banza da wannan shaye-shayen da kake yi?


"Gimbiya very Soon na kusa daina, "haka kake san abaka sarauta kana wanann halin, ai kasan Maimartaba ba zai yarda da haka ba, shiyasa yafi san Hakim sama da kai..



"Shi Hakim din kunsan abunda yake aikatawa indan ya fita waje? Ai gwara ni na fito da halina kowa ya gani, kuma dole na zama SARKIN ZARIA ko suna so ko basu so..



"Kai dallah can matsa, muna yin abun mu cikin natsuwa da kwanciyar hankali zaka yi man hauka, waya gaya maka zakayi mulki mundun Hakim yana numfashi a doran kasa to baka ba mulkin kasar Zaria..



"To ni ki barni na wuka na tafiyar mashi da kai uban kowa ma ya huta...


"Rufaman asari Hamid, ba ruwanka kai dai kawai ka samana ido, ni nasan abunda nike yi, indai Mulkine sai kayi shi indai ina numfashi a doran kasa, dan haka kaje kayi hidimarka nima ka barni da tawa..



"To shikenan, na barki da hidimarki ni na wuce marace yayi zan hadu da wata baby yau ta shigo gari, kin san yan university sun fara dawowa..



"Wuce ka tafi, Amman Hamid ka kiyaye, saboda makiya, "na barki lafiya..



"Mariya! "Naam Allah ya taimakeki Gimbiya Kilishi..


"Ya kukayi da boka, "eh yace Yarima Hakim abashi kwana biyu zai fara aiki kanshi saboda yana da rikon addini da wuya aljanu su je wajenshi, kuma bai zina balle ko wajen zina suzo su shigeshi suyi aikin domin dole aikin da za'a yi sai da aljanu za'a yi shi...



"Naji, to shi wannan sakaran fa shida sakaran uwarshi..


"Eh Yarima Hamad yace anbarshi da wannan halin na shaye-shaye da bin mata, ita kuma Gimbiya Zulaha yace abarta ta gama bin bokayen sannan zaiyi aikinsu ita da Hamid bayan ya gama mai wahala aikin Hakim..



"To shikenan Mariya gaskiya naji labari mai dadi da marar dadi , taya za'a yi mu hana Yarima Hakim yawan wannan ibadar da ya daukarma kanshi?


"Shine abun dubawa, ki kwantar da hankalinki uwargijiyata ko da masifa sai YARIMA HUMAD yayi sarautar masarautar Zaria, sai kin zama uwar sarki kema wannan alkwarin boka ne..



"Naji, tashi ki tafi bakin aikin ki, ki kula sosai da abunda fulani dake ciki ita da wannan banzan yaranya nata, "insha Allah ranki yadade..



"Allah ya taimakeki Gimbiya Kilishi na neman iso, "ace mata ta shigo..


"An wuni lafiya Gimbiya Zulaha, "lafiya Gimbiya Kilishi, "ya Lanto ta dawo daga wajen bokan? "eh tadawo harma anyi sa'a, "anyi sa'a fa kika ce Gimbiya Zulaha,"eh anti sa'a gobe da safe ki tashi da shirin zaman makokin YARIMA HAKIM, "taya haka ta kasance?


Nan Gimbiya Zulaha ta gaya ma Gimbiya Kilishi yanda akayi da boka yace masu, ba karamin farinciki tayi ba, dan tana ganin cikin sauki zata ida kauda Gimbiya Zulaha da YARIMA HAMAD cikin lokaci kadan tunda sun kauda mata Yarima Hakim, "dole sai Humad yayi mulki, Gimbiya Kilishi ta fada cikin zuciyarta tana murmushin farinciki tace, "gaskiya Gimbiya Zulaha aji tsoranki aikin ki yana kyau, "Hmm Kilishi kenan angaya maki ni ta wasa ce, sai dai ba sunana ZULAHA ba..



Haka suka gama maganarsu sai da dare ya fara sannan Gimbiya Kilishi ta wuce shashenta cikin farin ciki..


______________________________


"Allah ya taimakeki Gimbiya Hakima, Barde yace angama komai fitowarki yake jira..


"Uhmmm! Abunda Gimbiya Hakima tace kenan..


Gimbiya Hakima ta cigaba da abunda take saida ta sha iska tayi ma Lantana nuni da alkaibarta, nan Lantana ta tashi ta sanya mata sannna Azima ta dauki wayoyinta da post dinta suka fito, da yake lokacin sanyi ne Gimbiya Hakima rigar sanyi ta dogan wando ta sanya dan maganin sanyi, ga kuma alkaibarta da aka daura mata, Gimbiya Hakima ba karamin kyau tayi ba, sannan suka fito ta hau doki su Lantana suna kasa suna take mata baya har suka isa wajen shakatawar Gimbiya Hakima..


"Azima, "Naam Allah ya taimakeki, "miko man wayata wanda nike chatting da ita, "angama uwar marayu, nan Azima ta mika ma Gimbiya Hakima waya, nan Gimbiya ta cigaba da chatting sai da taji duk bakin cikin da Maimartaba ya cusa mata shida Fulani ya gushe sannan suka dawo gida....



Bayan sun dawo wanka tayi tasa kaya mararsa nauyi ta kwanta aka cigaba da yi mata tausa ita kuma tana chatting, sai da dare yayi sannan aka kawo mata Tea da chaps taci sannan ta kwanta aka cigaba da yi mata tausa Azima nayi mata karatu sai da tayi bacci sanann suka dawo suma suka kwanta dan su huta...

______________________________


"Kina jina ko Mino? "Eh Lanto ina sauraranki..


"Anshi wannan maganin ki tambatar kinsa ma Yarima Hakim abinci yanzun na dare nan ba sai gobe ba..



"Aiki mai sauki mana, yanzun a gabanki zan sanyashi ba sai kin matsa ba, "yauwa Mino shiyasa nike san aiki dake, "aiko bari ki gani, kinga na sa ko baki daya na juye shi ma..


"Na gani kinyi kokari, na na wuce, "to mu kwana lafiya..



Lanto na lafiya, Mino ta dauki abincin da tasa ma Yarima magani ta juye shi a shara ta zubdo shi ba Wanda ya sani, sannan tace ma wanda suke aiki tare ita daya ta kaima Yarima Hakim abinci yau ta hutar dasu, bayan sun tafi tayi sauri ta dafa mashi wani sabon abincin sanann ta kai mashi..



Su Lanto nacen suna jiran gobe da safe suyi zamab makoki🀣




Bayan Yarima Hakim ya dawo daga massallaci sai da ya biya yayi ma Fulani sai da safe sanann ya wuce shashenshi, bayan ya sha tea da yake hadawa da kanshi, dan da man shi baya cin abincin masu girki sai na Fulani, kuma bai cin abinci dare daman yana hada ruwan zafi da kanshi ya sha sanann ya cigaba da ibadodinshi yana neman tsari daga sharin makiya..





_By jameelah jameeyπŸ–‹_




Share and comment pls
πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»
*GIMBIYA HAKIMA*
πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈ

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey πŸ–‹_

*(Yar mutan kankiaπŸ‘ΈπŸ»)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```



11&12





Washe gari bayan Yarima Hakim ya tashi daga bacci yayi wanka sannan ya yayi addu'ar fita, ya fita sannan ya wuce shashen Fulani..



"Fulani ina kwana, "lafiya Lau Hakim ka tashi lafiya? "Lafiya lau Alhmdulh..


"Fulani ni zan wuce office,"to Hakim, Allah ya tsare ya baka sa'a, "Amin Fulani..


"Hakim ka biya shashen Gimbiya Zulaha da Gimbiya Bilkisu ka gaishesu kaji?



"Fulani kin san matan nan ba son mu suke ba, mai zanje nayi wajen su..


"Kaje ku gaisa Hakim ai kafi su har gun Allah,dan haka ka wuce ku gaisa..


"To shikenan ni na wuce dan yau inada lectures, "to Allah ya baku sa'a..


Nan Yarima Hakim ya fara shiga shashen Gimbiya Zulaha, nan yasa akayi mashi iso sannan ya shigo..


"Antashi lafiya? Lafiya, wani abu ka shigo man waje tunda safe? Dan nema..

Dan Gimbiya Zulaha Tayi mamakin ganin Yarima Hakim, ai ita ta tashi da niyar ganin gawar Hakim, to wai shi Hakim wani kalar mutun ne wannan, mutun yaci guba amman ya tashi lafiya lau kamar kowa, tana cikin maganar zuci taji yace...



"Kwantar da hankalinki matar sarki, kema kin san bin umarni ya kawo ni wajenki, ba dan haka ba ba abunda zani yi a wajenki..



Gimbiya Zulaha taji zafin maganar da Yarima Hakim yayi mata, amman sai ta daure bata nuna mashi komai ba tace.



"Ai daman ana san yaro mai biyaiya ga iyaye kayi kokari sosai Hakim..


Haka Yarima Hakim da Gimbiya Zulaha suka kama gaya ma juna magana a fakaice sannan ya taso ya wuce Shashen Gimbiya Kilishi..


"Antashi lafiya Aunty? "Lafiya lau Hakim, ana nan anata kokari ko?


"Alhmdulh Aunty ni zan wuce na barki lafiya,"to shikenan..



Haka ya fita yana mamakin halin Gimbiya Kilishi, ita bata nuna ma mutun tana jin haushin shi ba kamar Gimbiya Zulaha ba da bata iya boye kishinta ba, bayan tare suke duk wani tungu acikin gidan..



Haka Yarima Hakim ya tafiyarshi gun aiki yana mamakin halin mutanan gidan su, na bala'in son mulki su dai su gaji sarauta..


"Ranki yadade Gimbiya Kilishi tana san shigowa, "je kice mata ta shigo, nan Gimbiya Kilishi ta shigo tace..


"Gimbiya Zulaha ya naga haka? "Hmm! Abun ya bani mamaki Kilishi, wait shi Hakim wani kalar mutun ne?



"Nima abunda nike tunani kenna, Amman anya da gaske Mino tasa ma Hakim magani? anya dan gaskiya ina kokonto Gimbiya Zulaha..



"Wallahi Kilishi a gaban idon Lanto Mino tasa maganin, Kawai dai ina tunanin shi Hakim din wani kalar Mutun ne?



"To rabu dasu, in sun san wata ai basu san wata ba, wannan aikin kawai ki barshi a hannuna Gimbiya Zulaha..



"Aa Kilashi wannan aikin dole mu duka biyu zamuyi wannan aikin dan naga alama ba aikin mutun daya bane..



"Gaskiya hakane kin kawo shawara mai kyau kema Zulaha, to ni zan wuce Humad na can yana jirana zamuyi magana da shi...



"To shikenan, ai da safe shi Humad din ya shigo gaidani, "ni kwana biyu kenan banga Hamid ba..


"Eh jiya ai gida ya wuni, kenan baije ya gaidaki ba? "Eh banganshi ba, "to wani uzurin ne ya hana shi zuwa wajenki na sani, "hakane ni na wuce..



"Humad, "Naam Ma'ma barka da shigowa, "yauwa Humad sannu da hutawa sarki mai jiran gado...



"Haba Ma'ma sau nawa zani gaya maki akan ni bani san wanann mulkin da kike neman tusaman, kuma ga sarki can mai jiran gado Yaya Hakim, Amman sai zaki cema wa..




"Humad anya kuwa kasha Nono na? Anya Humad kaine Humad nifa na haifeka, Amman ace baka biyo halina ba, Ina bata yuyuwa..



"Nidai gaskiya Ma'ma ya kamata ki duba wannan maganar da wannan kudin da kike kashewa a banza wajen sabon Allah ai gwara ki gina massallaci da kudin duk wanda yayi sallah zaa baki Lada..


"Yi man shiru, Humad na gaji da sauraran bakin ciki, to tsaya kaji ko kana so ko baka so dole sai kayi sarkin Zaria, kafi kowa cancanta kayi sarki ba Hamid da Hakim ba, dan haka tashi kaban waje shashasha marar zuciya, wanda yayi Amai kare ya lashe..



"Allah ya huci zuciyarki, na barki lafiya, nan Yarima Humad ya tafi ya bar mahaifiyarshi da bakin ciki, tana bakin cikin yanda Humad baki daya baya kwadayin Mulki ko kadan, "anya Humad ba asiri aka yi mashi ba, Gimbiya Kilishi ta fada tana mamakin wannan abun...

________________________________


Bayan Gimbiya Hakima ta tashi bacci, su Lantana suka shirya yata yanda take bukata, sannan ta fito ta zagaya cikin gida sanann ta dawo taci abinci..


"Lantana!


"Allah ya taimaki Gimbiya, "dauko man alkarbata zamu shiga kasuwa zamuyi sayaiyar makaranta..


"An gama ranki ya dade, nan Lantana ta dauko ma Gimbiya alkaiba, sanann suka wuce kasuwa..



Gimbiya sayaiyar Makaranta tayi a kasuwa sai da ta saya komai sannan suka wuce gida bayan sun dawo gida, nan Lantana ta shiryama Gimbiya kayan ta dan gobe zata wuce...


Bayan Lantana ta gama shirya ma Gimbiya kaya, sannan ta wuce itama ta hada kayanta ita da Bilkisu da Azima dan dasu za'ayi tafiya Sai da suka gama hada kayan su sannan suka kwanta bacci...

Washe gari da wuri su Lantana suka tashi suka ida hada duk abunda basu hada ba, sannan kuta hada ma Gimbiya Hakima ruwan wanka, sannan suka fita suna jiran ta tashi daga bacci sai ta shiga wankan...



"Ba'ba Bilkisu, "Naam Azima, wani abu naga kamar kina cikin damuwa?


"Wallahi tsoro nike ji sosai, da Ina murna Gimbiya Hakima Zata tafi makaranta zamu hutu har sai ta dawo sannan zamu cigaba da bauta, amman ina cikin wanda Gimbiya Hakima ta zaba zata tafi dasu karatu..


"To ya zakiyi Azima, ai ni daman nasan dani Gimbiya Hakima zata tafi zaria wannan karatun nida Lantana, dan baki bani bashin rantsuwa ko gidan miji damu Gimbiya Hakima zata tafi saboda ta saba da aikinmu Azima..


"Niko gaskiya banji dadin wannan abu ba, na gaji da wannan bautar dan kawai ba yanda zaniyi..


"Aiko kima saba, keda kika fara yima Gimbiya Hakima hidima daga baya, ni nan nida Lantana tun Hakima tana yar'shekara biyar muke yi mata hidima har yanzun maganar da nike yi maki..



"Wai gaskiya sannun ku, kunyi kokari amman duk da haka Gimbiya Hakima bata raga maku, balle mu..



"Ai haka halin Gimbiya Hakima yake sai dai hakuri, "to Allah ya bamu hakurin zama daita tunda mudai yanzun muka fara, ko taya zamuyi zama da ita a Zaria? "Wannan ansar sai munje zaria zamu ganta.


"Ku taso ga Gimbiya Hakima nan ta fito ku, nan suka tashi suka marama Gimbiya Hakima baya zuwa shashen Maimartaba, suna zuwa nan ta tadda Fulani da Yakumbo...



"Barkanku da hutawa, "barka Daughter har kin shirya ko? "Eh na shirya Momy...



"To Daughter kiji tsoran Allah, indan mu bamu ganinki, to kisani Allahn da ya halliceki yana nan yana kallonki ko da karkashen kasa kika shige kika boye...


"Sannan kiji tsoran Allah kiji tausayin bayin da zaki tafi dasu Daughter, dan Allah karki cucesu kamar yanda kike yi masu, kinga yanzun karatu zaki tafi..



"Insha Allah Momy, zan kiyaye, "yauwa Allah ya yi maki albarka, "Amin Momy...



Bayan Yakumbo ta gama yi ma Gimbiya Hakima wa'azi nan Fulani da Maimartaba suka yi mata fatan alkhari, sannna maimartaba yace...


"Na baki direba, sannan kin zabe kungangai gudu uku, na baki masu gadi guda hudu, dan haka Mamana akiyaye, in kinje kiyi abunda ya kawoki..



"To shikenan insha Allah Baffah, nan dai suka gama yi mata wa'azi sannan aka sa kayan Gimbiya Hakima cikin mota nan suka dauki hanyar Zaria, da mota hudu akayi ma Gimbiya Hakima rakiya dan harda Gimbiya Yakumbo sai da ta raka Gimbiya Hakima makaranta...



Bayan sun sunka gidan da aka kama mata, sannan suka dawo gida..


Gidane flat house, babban parlour ne da bedroom guda uku, sannan boys coters, nan masu gadi da direba zasu ringa kwana, Gimbiya Hakima da su Lantana kuma zasu ringa kwana cikin gida, amman bedroom din Gimbiya Hakima daban...



_By jameelah JameeyπŸ–‹_





Share and comment pls

πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»
*GIMBIYA HAKIMA*
πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈ

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey πŸ–‹_

*(Yar mutan kankiaπŸ‘ΈπŸ»)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```



13&14



Washe gari tun da asuba Inna Lantana ta tashi ta hadawa Gimbiya Hakima ruwan wanka..


"Allah ya da tsawancin kwanan Gimbiya Hakima uwar marayu, ga ruwan wanka nan ya jiranki..



"Ina Bilkisu take? "Ranki ya dad'e ai Bilkisu suna madafa suna nema maki abunda zaki karya kummallo kafin ki wuce bokon..



"Maza kije kice mata, ta sallami Azima ta taho ta taya ki fiddo man kayan sawa, dan ita Azima tafi ku sanann kyau...



"Angama yar'sarki, matar Sarki da yardar mai duka, "zaki tashi kije ki ban waje ko tsayawa zakiyi ki isheni da wannan maganganun naki, wanda basu da dadin sauraro?




"Tuba nike uwargijiyata, "maza tashi ki ban waje kije ki kirata ko kun dawo...


Nan Gimbiya Hakima ta shiga wanka da suna da eight, Lantana tayi mamakin yanda Gimbiya Hakima tayi mata yau, wai yau Gimbiya Hakima bata zageta ba da tace mata matar Sarki, bayan Gimbiya Hakima bata san ace mata haka tunda ita bata da niyar yin aure, tafi san ta zauna gida tana zuba mulkinta yanda ta gadama, Gimbiya Hakima kenan..



"Harma kun gama kenan? "Wallahi kin san halin Gimbiya Hakima, bata cin abu mai nauyi da safe shiyasa muka soya mata biredi sai dankali da Tea..



"Sannun ku to, ke Azima taso muje fidda mata kayan sawa har ta shiga wanka..



"Wai Inna Lantana kina nufin Gimbiya Hakima ce ta tashi tun karfe bakwai saura?



"Nima nayi mamaki, dan tun ina gyara cikin dakin baccinta naga ashema idonta biyu, kawai dai tana wasa da waya sai da na gama hada mata ruwan wanka sannnan nayi mata magana..



"Ku har mamaki kuke kenan?

"Ai abun mamaki ne Ba'ba Bilkisu,"to ku daina Mamaki ke Lantana kin manta yanda Gimbiya Hakima ke da san karatu? "Aah nasan tana da san karatu mana ban manta ba..



"To Azima bari na gaya maki wani hali mai kyau na Gimbiya Hakima, "to Ba'ba Bilkisu ina sauraranki, Amman bari muje my m fiddo mata kayan sawa kafin ta fito...



"To shikenan nima kafin ku gama na gama jera mata abinci, "to mun tafi, nan su Lantana suka tafi fiddo ma Gimbiya Hakima kaya, ita kuma Bilkisu ta jera mata abinci, bayan sun fiddo sanann suka dawo...


"Ba'ba Bilkisu na dawo ina sauraranki wallahi ni kasa fiddo kayan nayi sabo da zumidin naji kyan halin da Gimbiya Hakima take shi, matar da nasan bata da kirki da tausayi..



"Tabbas Azima maganarki dutsi, Gimbiya Hakima bata da tausayi Amman tana da hali mai kyau, kin san maiyasa nace maki haka?



"Aah Ba'ba Bilkisu sai kin fadi, "To bari kiji, Gimbiya Hakima tana san karatu quri'ani dan hadda ma gareta, idan dare yayi lokacin da ina kwana wajenta kafin ta ida girma, wallahi karfe biyun dare take tashi sallahr dare bata kwanta sai bayan ta gama azkar din safiya sannaan take kwantawa bacci...



"Wai Gimbiya Hakima jiya kenan sallahr dare ta tashi da naga haske a dakinta..



"Kwarai kuwa, ai duk daren duniya Gimbiya Hakima bata bacci, shiyasa zakiga karfe taran dare ta kwanta bacci..



"Ni sai nai ta mamaki, nace ita ta riga kowa kwanta bacci, Amman itace karshen tashi bacci, Ashe saboda da sallahr dare take kwantawa tun tara?



"Eh, sannan kinsan maiyasa aka bata uwar marayu? "Aa nidai ina mamaki ace Gimbiya Hakima itace uwar marayun kano..



"Tana bala'in tausayin marayu, dan Gimbiya Hakima tana da gidan Marayu ko ni kaina ban san adadinsu ba a cikin garin Kano, kuma ita take ciyar dasu, ta kuma yi masu dinkin sallah, sannan kuma ta sasu makarantar arabi da boko..



"Allah ya saka mata da alkhari, Amman maiyasa bata tausayin mu bayinta?


"Wannan kuma a jininta yake, haka Allah ya hallinceta da iszar mulki, jinin sarautar kenan, dan ma iyayenta suna yi mata wa'azi, nan ai haka Gimbiya tayi sauki tunda har take bude baki tace yi kaza..




"Wai kina nufin Gimbiya Hakima da bata yin magana?


"Eh haka nike nufi, da in zata saki aiki da ido take kallonki kin san abunda take nufi, kuma indan zata sa ayi horo sai anwatsa maka ruwanzafi ko na sanyi sannan ake yi maka bulala, bayan angama yi maka bulala tasa a daureka jikin wani abu sai kawuni sannan a kanka gida ladabi har na tsawon wata, sai da Maimartaba yayi tsaye sannan ta chanza hali.


"Wai Allah mun gode maka, "ku ga Gimbiya Hakima nan fitowa..



"Takawarki lafiya uwar marayu, "Bilkisu mai kuka dafa?

"Soyayyan biredi sai dankali da tea..


"Uhmm, nan Gimbiya ta zauna tayi breakfast, sannan suka rakota ta shiga mota sai A. B. U. ZARIA..



"Ranki yadad'e antashi lafiya?


"Lafiya da man kaine driver din da Baffah ya bani?


"Eh nine uwargijiyata, "ok Uhmm, nan ya bude mata back sit ta zauna, sannan ya zaga ya mazaunin drive ya tada motar, nan yayi horn masu gadi daman already sun wangale gate nan GIMBIYA HAKIMA suka dauki hanyar makaranta...

"Kana jina Bala? "Allah ya taimakeki ina jinki..


"Bance ka tafi ba indan ka ajine, ka tsaya har sai nagama lectures sanann zani mutafi gida tare..



"Angama Ranki yadad'e, Allah ya baku sa'ar karatu..


"Uhmmm! Abunda Gimbiya Hakima tace kenan ta cigaba da chatting dinta, gashi ta makara dan yanzun har takwais da minti talatin, Amman hankalinta kwance..


______________________________


Woow wani santalelen handsome guy ne wadda Aqqalah ba zai wuce shekara 26 ba, dugone Amman ba irin sosai ba, farine ba,mai matsakaitan idanu Samanshi dauke yake da dogayen gashin idanu, girarshi a ciki take ta kwanta lufff, fuskarshi dauke take da dogon Hanci yayin da pink din bakinshi ya kasance karami dashi, Fuskarshi manne take da glass Amman class din na kara lafiyar idanu wato medical glass..



Lecture yake cikin natsuwa da kwaciyar hankali, Wanda duk rashin ganewar mutun idan prof HAKIM ABDULMATALAK ya koya maka sai ka gane saboda yana da method of teaching...



Ajin shiru kake jinshi kowa ya na ba'a ya baida hankalinshi waje prof Hakim, ana sauraran lecture ga shi kuma lecture din ta dauki dadi, har ma wasu daga cikin student din basu san lokaci yayi ace ya gama, wasu daga cikinsu yan matane, wasu kuma serious student ne wanda suka abunda ya barosu daga gidan iyayensu gaba...




Ji suke tashi kas! Kas!! Kas!!! Na tashi baki daya aji kowa waiga yayi yaga wace yar hutuce Wanan da take shigowa lecture yanzun anyi awa daya da fara lecture Amman ita sai yanzun take shigowa, kuma hankalinta kwace tana tafiya kamar bata makara ba, ta nuna bata san da akwai malami a cikin ajinba balle ya samu alfarma tambayar excuse..




Tafiya take cikin mulki da isa, sai busar iska take tana bada fadi, har ta isa wajen wani sit zata zauna sai kawai taji ance"Hey get out of my class, Gimbiya Hakima yi tayi kamar ba da ita yake ba, sai ji tayi ya sake cewa"I said get out of my class, you am

Please Login or Register in order to submit comment