Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

magana ta fito Hakim yana san magana dasu.


Da Sallama Hakima ta shiga duk da Hikimat bata ansa mata sallamar ba, cewa tayi, "sannu Amaryarmu, na samaiki lafiya."?


Wani kallon banza Hikimatu tayi ma Hakima sannan ta matsar dan daman cike take fam fashewa ne kawai bata kai dayi ba🤣, sannna tace ma Hakima, "da ban lafiya ai a gadon asibiti zaki iskeni ko kuma ina kwance ina saman ruwa, kuma kice ma shi mijin naki bani fitowa, dan haka ina mai ja maki kunne daga yau karki sake ki sake shigo man room banza maiyar miji."


Duk da Hakima taji haushin kalman da Hikimatu ta gaya mata amman sai ta ɗaure kuma suke da laifi dan Hakim ya daɗe a room ɗin ta, bayan yasan Amarya na jiranshi cewa tayi, "Allah ya baki hakuri Amaryarmu ni zan wuce."


"A gayas dagin tsiya."... Waigowa Hakima tayi ta kalleta sai ta girgiza kai tayi murmushin ta wuce, wai ita ce dagin tsiya tayi mamakin yanda ta kyale Hikimatu har haka amman ita tasan da da yanzun ba ɗaya ba da dane Hikimatu ta gaya mata wannan maganar da basu kwashi yan kallo da ita ba, amman ita yanzun bata iya kallar rayuwar dan ta fahimci duk masu kallar rayuwar ganewa ne kawai basuyi ba amman rayuwar dabbobi suke bata mutane ba, dan haka ita yanzun bata iya faɗa dab faɗa karnuka ke yinshi ba dai mutane ba.



Haka Hakima ta shi iso parlour ta samu waje ta zauna tana kallon shihabin nata, ce mata yayi, "ina ita Hikimatun na ganki ke ɗaya Jewel."?


Shagwaɓe mashi fuskar tayi tana kisisina sannan ta bude baki tace, "tace gata nan zuwa Angle."ta ƙarashe cikin yanga, ai oga Hakim shagala yayi da kallonta dan sai da yayi suma ta wucen gadi sannan ya dawo, tashi yayi daga kujerar da yake ya koma wanda ta zauna ka mota yayi yana wasa da yatsanta sannnan yace, "idan kina yi man kallar wannnan salon naki mantawa nike dani waye Jewel ba tun yau ba, Jewel keɗin ta daban ce, kuma ke ɗin tawace bata kowa ba, mutuwace kawai zata rabamu, kuma ina fatan mu mutu tare Jewel idan ba hali ina rokan Allah na rigaki mutuwa, Allah na tuba karnayi sabo da nace ban iya jurar ganin gawarki a shinfiɗe kasa baki numfashi Jewel nasan nima binki zanyi a ranar, shiyasa nike rokan Allah yasa mu mutu tare masoyiyata."



Kamo kanshi tayi suka haɗa goshi wajen ɗaya suna shakwar numfashin juna sannan tace, "Angle ban taman ka mutu kabarni idan ka mutu kabarni ya zanyi da rayuwata? Nidai Allah yasa sai mun haihu munga jikokinmu sanann mu mutu, amman dan Allah daga yau kabar yi man kallar wannan maganar."... Ta ƙarasa maganar tana hawaye, lashe hawayen yayi duka a bisa fuskarta sannan yace, "Sorry Jewel na daina, amman kisani mutuwa ta zama dole sai dai muyi fatan cika da kyau da imani."


"Amin."tace sannan tace, "Angle dare keyi fa ka wuce wajen Amarya basai mun zauna ba insha Allah gobe sai mu zauna ko."?


"Aa bari na tashi dai na kirata."... Abunda su Hakim basu sani ba duk abunda sukayi a parlour a kan idon Hikimatu sukayi shi, tana ganin Hakim ya tashi tayi sauri ta koma room ɗin ta tana goge hawaye tana guɗirinma kanta ko ta wani hali sai ta raba Hakim da Hakima dan ta lura idan Hakima nanan to Hakim ba wani rawar kai zaiyi kanta ba, shigowa yayi yace, "wai mai kika tsaya yi ne Hikimatu muna jiranki fa dare yayi."?


"Yi hakuri mijina yanzun nike shirin fitowa, "ok let go."tare suka fito parlourn suka zauna a kujera ɗaya sai wani shige ma Hakim take a jiki shi kuma yana dan ja baya dan wani bashi bashi yaji ta nayi duk abunda suke Hakima tana kallonsu sai ta nuna bata san anayi ba, dan take mulkin da sarautar ya taso mata, addu'a Hakim ya bude taron sanann ya fara magana, "Alhmdulillahi Allah abun godiya da ya bamu rai da lafiya har mukaga wannan ranar, ke Hakima kece babba dan haka inason ki rige girmanki ki zauna lafiya ke da ƙanwarki, ke kuma Hikimatu kice ƙarama inasan kiyi mata biyaiya ku had'a kanku ku zauna lafiya karku biye ma yan tashi zaune, ina fatan zaku zamo masu biyaiya a gareni."



"Insha Allah zaka samaimu masu bin umirnin ka a kowani lokaci."cewar Hakima, itadai Hikimatu bata ce komai ba sai fusgar iska dakeyi, cewa yayi, "masha Allah , sannan maganar raba kwana uwar'gida ya kika ga za'ayi."?


"Aa Amarya ta faɗi yanda tace haka za'ayi.".... Koda Hikimatu taji ance ta faɗi sai taji farin ciki dan ta lura ji suke kamar su cinye junansu, dan haka tasan abunda zatayi masu dan daman da shirin ta tazo dan haka sai tace, "nidai a gani nina kwana ɗaya yayi ko Yaya."?... Ta jefama Hakima question ɗin tana kashe mata ido, Hakima tasan san zuciya yasa Hikimatu sa masu kwana ɗaya bayan tasan ko wani gida idan akwai kishiya kwana biyu akeyi ma ko wace idan kwananta ya zagayo amman su naso daban yake da na kingin, Hakim addu'a yake Allah yasa Hakima tace yayi kaɗan dan ba zai iya juran kwana ɗaya kawai zaiji dumin Jewel ɗin shi , amman sai yaji Hakima tace, "eh haka yayi kanwata, Allah ya bamu ikon yin biyaiya ga mijin mu, "Amin tace tana shi'umin murmushi dan gani take tana gama amarci ya koma ɗakin Hakima zai dai dawo nata tunda kwana ɗaya ne ba biyu ba ko hudu, bayan sun gama Hakima ta rakasu har room ɗin shi sannan ta dawo nata duk da Hakim yaso ya rakota amman tace ya barshi itako ta hutar dashi.


Haka ta kwanta ta gama juyi danji take kamar ta fasa ihu, tashi tayi ta ɗauro alwallah ta fara sallah, bayan ta gama sallah ta fara karatun al'quri'ani mai girma.


Bangaren Amarya Hikimatu ko taji maza dan Hakim ba tausaya mata yayi ba balle daman yanajin haushinta ta sa masu kwana ɗaya ko wani ɗaki shiyasa ya fidda tausayinta jiya ya murjeta sosai yanda zataji abun ya fita ranta, kawai dan haka yayi ma'amila da ita ba dan dadi ba dan wani wari ma take wanda shi baisan ina ta samo shi ba, duk da sau daya yayi sex da Hakima amman Hakima tafi Hikimatu komai harda dadi ma dan duk wani abu da ake bukata a jikin mace, kuma Hakima tafi Hikimatu budurci dan cikarkar budurwa ya samu Hakima, amman ita Hikimatu bai san wani layi zai saba wanda ta kawo budurci ko akasin haka shi dai bai sani ba, bayan ya gama yi mata abunda ya gadama ya sauka samanta ya shiga wanka, wankan tsarki yayi sannan ya ɗauro alwallah ta fara sallah shima.




_By Jameelah Jameey ✍🏻_



#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please


👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```


95&96


Tana zaune tana lazimi gama raka'atul fijir inta kenan tana lazimi Hakim ya shigo, zauna nawa yayi suka shafa tare sannan yace tunda ta tashi shi zai tafi sallah, bayan ta gama sallahr asuba wanka tayi ta shirya cikin wata atamfa yellow mai ratsin green sannan ta fito kichent ta shiga ta fara haɗa masu breakfast na gani ba faɗa, dan zagewa tayi tana tsara masu break mai kyau da dadi, su kuma su Azima daman su ke gyara shashen su uku haka suka fito suna aikinsu, Hakim ya gama azkar ɗin shi sanann ya taho sheshen shi gaisawa yayi dasu Azima dan yana ganin girmansu, balle ma da yake ganin kaunar Jewel ɗin shi a kwayar idanunwansu shiyasa yake basu girma dan duk mai san Hakima yace shi yake so, kuma duk wanda bai san Hakima tabbas bai sonshi shima tunda Hakima itace rayuwarshi, bayan sun gama gaisawa ya shiga cikin parlour kamshin girkin Hakima ya doki hancin Hakim, lunshe idanun shi yayi yana godiya ga Allah da ya bashi Hakima dan yasan ba wayaun shi bane ya bashi ko dibararshi Hakima kyautace Allah ya bashi, kuma ya ansa hannu biyu yana yi mashi godiya.



Ji tayi an ɗagata sama ana juyi da ita,dariya ta fara yi mashi tana cewa, "please Angle ka sauke ni pls mana."...... Ta ƙarasa maganar tana tusa hannunta cikin laulausar sumar kanshi da taji kudi wajen gyara, bai sauke ta ba sai da ya gaji dan kanshi sannan yace, "Good morng Rayuwata, yana yi mata wani hots romatic kiss, "itama cewa tayi, "Morg too bugun numfashi na.".... Dariya sukayi su dukansu yana jan hancinshi cewa yayi, "Jewel mai like dafa mana har haka ya cika gida da kamshi haka."


"Gasarsaiyar gurasa sai kosai, "wow Jewel bari na taya ki ko."? .... "Aa ai na gama Angel ka gani ma."?.... "Eh nagani Jewel sannu da aiki.".... "Yauwa yanzun dai kaje ka shirya sai ku fito kai da Amarya muyi breakfast."..... "To shikenan yanda kakece haka za'ayi uwar gida sarautar mata."

Haka suka fito tare shi ya shiga room ɗin shi itama ta shiga nata wanka ta shiga, tunda Hakim ya shigo room ya tarda Hikimatu tana bacci lokaci ya duba yaga 10am, amman ga dukan alamu bata tashi tayi sallah ba balle ta shirya, ranshi ɓace ya tadda, "wai shin bazaki tashi kiyi wanka kiyi sallah ba? Tun ɗazun nike tadaki harna fito wanka amman baki tashi ba? To kinga tafiya dan Jewel nacen tana jiranmu mu fito cin abinci bansan bata mata lokaci."


Wani irin kallo tayi mashi, wai duk abunda Hakim yayi mata amman da maganganun da zai saka mata dasu kenan "wallahi dole na fidda Hakima a zuciyar Hakim."... Ta faɗa cikin fushi tashi tayi ta haɗa ruwa tayi wanka tana fitowa tayi sallah sannan ta shirya ta fito, zaune ta iskesu bisa dining sun ajiran isowarta, tana zuwa ta samu waje ta zauna sai cin magani take, Hakima tace mata, "ina kwana Amaryarmu fatan kin tashi lafiya."?.... Wani kallo tayi mata sannan tace, "lafiya."?


Murmurshi Hakima sannan ta tashi ta fara zuba ma Hakim abinci itama ta zuba nata ta turama Hikimatu cooler ɗin abincin duka a gabanta, zubawa tayi sai da Hakim ya ɗaga kai ya kalleta dan sai da ta cika plate tas sannan ta tura cooler ta fara ci ba ko bissimilla babu ta fara cin abincin ta, bissimilla Hakima tayi ta fara cin abincin itama, shima haka Hakim, basu wani jima da fara cin abincin ba Hakima ta tashi ta koshi ko rabin wanda ta sa bata ci ba, kallonta Hakim yayi yace, "ya naga kin tashi Jewel."?..... "Uhm, ni na koshi Angle cikina cike yake kamar zai fashe."?..... "Oya, maza zauna ki ƙara cin abinci kar raina ya ɓaci mai yasa baki san cin abinci Jewel."?


"Ina fa ci kawai dai na koshi, kuma ai nace da yawa."... "Eh nagani."... Abunda yace kenan ya cigaba da cin abincinshi dan abincin yayi mashi dadi sosai, koda taga Hakim ya kyaleta sai ta wuce ta barmasu parlourn dan su huta susha amarcin su, koda ta shiga ɗakin Waya sukayi dasu Fulani da Yakumbo sannan ta hau online ta fara chatting da su Maryam.

____________________________



"Boka kaji wata sabuwa kuma fa, wai Hakim ya ƙara aure wata Hikimatu boka so nike a kashe man ita."

Hahhahahaha, "ina san haka, ai itama ba kashe ta zamuyi ba anshi wannan maganin shi zaki bata taci cikin abinci itama ba maganar ciki dan haka sauran sati biyu Hakim ya mutu to maiye abun tada hankali."?... "To Turmurturs yanda kace haka za'ayi mun barka lafiya."


Haka suka taho cikin farinciki, koda dare yayi sai da Kilishi ta koma boka yayi mata wanka sannan ta dawo gida ta kwanta.


_______________


Soyayya ake mai ƙarfi tsakanin Yarima Annas da Gimbiya Maryama, Aliyu da Gimbiya Sadiya, Maryam kuma da Yarima Humad, dan su duka sunyi nisa cikin soyayar junansu har iyaye sun shiga dan har an aiko da kudin neman auren Gimbiya Maryama da Yarima Annas, shima Aliyu sun kawo nasu dan har an tsada ranar bikin.

____________



Yau Hakima take ansar kwana dan haka breakfast ɗin yau daban yake da na kullun, bayan sun gama breakfast ɗin tashi sukayi suka shiga ciki shi Hakim shashen Gimbiya Fulani ya wuce, Gimbiya Hikimatu na ganin Hakim ya fita ta ɗauko waya ta kira Mamarta suka fara magana, "wallahi Mama Hakim bai sona bai damu dani ba sai matarshi dan gabana suke soyayya ko kunya basu ji.".... Mtssssss! "Aikin banza aikin wofi, anya Hikimatu kinsha Nonona kuwa? Ina maganin da na baki kiyi amfani dasu."?


"Wallahi Mama nayi anfanin dasu ammman banga wani aiki ba, amman ai yau nike fita kwana dan haka ina da wata ƙawa zata rakani wajen wani boka wallahi sai nayi maganinsu Mama."


"Yauwa yar'halak, yanzun naji batu dan haka bance kiyi sanya ba, "daman ai ba sanya zanyi ba sai na rabasu."



Haka suka gama wayarsu sannan ta kwanciyarta ta fara bacci, ita ko Hakima gyaran kai da jiki tayi dan ta iya an koya mata yanda zatayi dilka ta gyara jikinta bayan ta gama taje Maryama tayi mata kitso Sadiya kuma tayi mata kunshi ta dawo ta ɗaura sauwa, shiri tayi na musan man, koda Hakim ya dawo lokacin tasha kwaliya suna zaune parlour su duka biyun amman ba mai yi ma wani magana sai da Hakim ya dawo ta taso ta tarboshi ta anshi bag ɗin hannunshi suka shiga cikin ko kallon arziki bai isa Hikimatu ba balle ya samu damar ko sannu da zuwa, wanka suka shiga sukayi tare sai da suka gama wasansu cikin toilet ɗin sannan suka yi wanka suka shirya sannan suka fito a tare sukayi dinner sannan sukayi mata sai da safe suka shige ciki, koda taga sun shiga ciki ta samu ta fita sai gidan su Aziza, tana zuwa suka rungume juna ita da Hikimatu suka fara kissing ɗin juna kamar sunci kansu, nan suka zube bisa gado suna abunda suka gadama sai da suka gama watsawarsu sannan su kayi wanka suka wuce gidan boka, nan ma sai da boka yayi lalata dasu su duka biyun sannan ya bata wani magani ta yace tasa shi a abinci Hakim naci zai saki Hakima, sannan suka taho nan suka rabu da Aziza akan zata shigo itama taga gida, bayan ta koma wanka tayi suka cigaba da waya da Aziza suna batsa wai dan su kwantarma juna da shi'awa dai da suka gama sannan suka kashe wayar Hikimatu ta kwanta.


Hakim ko yau ya sheda ya dawo dakin Hakima, dan yau Hakima ta sashi farin ciki sosai, bayan sun gama suka tashi sukayo wanka suka fara sallahr dare sai sukayi raka'atul fijir sannan Hakim yayi shirin massallaci ya biya room ɗin Hikimatu ya tada ta shima ya wuce sallah, bayan ya dawo sai da ya ƙara neman Hakima sannan yayi bacci koda gari ya fara haske tashi ta samu tayi wanka tayi ta shirya sannan ta wuce kitchen ta ɗaura sauwa, bayan ta gama sauwa ta dawo ta tada Hakim bacci yake yaji harshe yana yi mashi yawo cikin kunne tana fura mashi iskan bakinta tana cewa, "Angle wakeup tashi muyi wanka muje muyi breakfast."


Janyo yayi yana mata kallon so dan ji yake kamar ya cinye ya huta, tashi yayi sukayi wanka suka shirya suka fito, lokacin da suka fito Hikimatu ma tana fitowa kamar buzurwar kura dan ko poder bata shafa ba ta fito haka ita ba wani kyaun kirki ba amman ta fito haka kamar wanda akayi ma baki, dan Hikimatu ƙazamaci sosai Hakim ma ya lura da haka, shiyasa yasama kanshi bai iya cin abin hannun Hikimatu, shi dan ba yanda zaiyi yake kusantar Hikimatu dan wani wari take marar dadin shaƙa.


*(Hattara yan lesbians wallahi ku tuba ku koma ga Allah, wallahi duk mai lesbians idan ta zauna kusa dake sai kinji tana wari, to maiye amfanin neman jinshinki? Bayan kin san yin hakan babban zunubi ne, Allah yasa mudace Amin)*

Bayan sun gama breakfast ɗin suka tashi, shi dai Hakim wajen aiki ya wuce, ita kuma Hakima shashen Gimbiya Fulani ta wuce dan ba ita zatayi abincin rana da dare ba Hikimatu zatayi shi, koda Hikimatu taga ba kowa gidan sai ita daya ta samu damar shiga kitchen tayi masu wata yagwalerlen taliya marar dadi ta zuba wannan maganin ta jera a dining tana gama jerawa Gimbiya Zulaha na shigowa da cooler din Abinci wai ta kawo mata abunka da kura uwar haɗama ga abincin da ta dafa amman sai da ta amshi na Gimbiya Zulaha, a gaban Gimbiya Zulaha ta zuba abincin taci mai isarsa dan sai da taji ba waje sannan ta tashi aiko Gimbiya Zulaha ta tafi tana farinciki da bukatar ta biya, Hakim na dawo shashen Fulani ya wuce bai san Hakima na can ba haɗawa sukayi abinci sukaci tare sannan suka dawo koda suka dawo suka wuto dining suna duba abincin da Hikimatu tayi sukace sun koshi dan ko sunci abinci sai dai aka ba bayi suka zubda dan ba mai iya cin abincin nan saboda rashin kyaun shi.


Raka Hakima yayi har room ɗin ta addu'a ya tofa mata sannan ya fita yana jin kamar ya dawo.


Koda yaje room ɗin shi ya tadda, Hikimatu har taje tana jiranshi wanka ya shiga ya fito ya kwanta, amman saboda da rashin class ɗin Hikimatu sai da ta nemaishi yace mata yau bai iya yi mata komai dan baida lafiya duk nacinta sai dai kyaleshi tayi ta kwanta tana tunanin Aziza dan ji take kamar tayi hauka dan tana bukatar ma taimaki,lura da yanayin da take ciki sai taba Hakim tausayi nan ya kusanceta ba dan dadi ba sai dan kawai ya fita hakinta, shi yanzun ma yake jin dadi ta dace kwana ɗaya dan bai iya yin kwanaki ba tare da yaji dumin Jewel ɗin shi ba.


Some days letter


Abubuwa da ma sun faru tsakanin Gimbiya Hakima da Gimbiya Hikimatu da kuma Yarima Hakim dan wani kallar kishi suke wanda wata rana yana ba Hakima tsoro tash kama Hikimatu tana yi masu barbaɗe cikin abinci daman saukinta Hakim baya cin abincin Hikimatu, taraiyar Hikimatu da Aziza abun gaba yake dan Aziza yanzun har gida take biyo Hikimatu suna shige ayarsu.


Bangaren su Gimbiya Zulaha kuwa suna ta zuba ido dan sauran sati shekara biyar ta cika su ga gawar Hakim, dan ko Gimbiya Zulaha ta fara shirin yanda zasu yi shagalin mutuwar Hakim da Sarki Abdulmalak.


Bangaren Gimbiya Kilishi itama tana nan tana bin boka yana yi mata wanka tana jiran sati ya cika taga gawar Hakim da Hamad..... Ita kuwa Gimbiya Fulani Kubrah bata damu da abunda akeyi ba duk da ta lura da Gimbiya Hikimatu halinsu ɗaya dasu Gimbiya Zulaha, shiyasa tasa ido akan Hakima tana bata kula ta musanman tana bata addu'oi tana sha tana wanka dasu sannan kuma tana ƙara ja mata kunne akan ta riƙe Allah, dan Allah yana tare da mai gaskiya.



Yau tunda Hakima ta tashi bata lafiya gashi Hakim ba ɗakinta ya kwana ba, koda yazo wajenta da safe bata nuna mashi bata lafiya ba dan tasan tana gaya mashi zaice baya zuwa aiki dan haka bata gaya mashi ba, sai bayan Tafiyarshi ciwon ya tashi sosai sanyi takeji duk da ta kashe duk wata na'auran sanyaya ɗaki, amman hakan baisa tta daina jin sanyi ba, koda Hakim ya dawo ya tadda bata lafiya ɗaukarta yayi ya kaita hospital ɗin Aliyu test Aliyu yayi mata koda result ya fito sai ga Hakima tana ɗauke da ƙaramin ciki dan wata hudu, murna wajen Hakim ba'a magana koda suka dawo gida shashen Fulani suka wuce suka gaya mata, nan Fulani tace bata ci su gaya ma kowa ba koda Hikimatu ce, haka ko akayi ba wanda suka gaya mawa suka cigaba da rainon cikinsu cikin sirin.



Yau tunda suka tashi sukaji Sarki Abdulmalak yana shela gidajen redio da television da masu shele yana gaiyatar ko wa gobe a fada zaiyi wani babban taro, ba wanda yasan da taron sai dai sukaji ana shele a cikin masarauta haka kuma a gidajen radio, koda Gimbiya Zulaha ta tambayeshi ce mata yayi idan gobe tayi sun gani,Rana bata karya sai dai uwar ɗiya taji kunya gobe shekara biyar take cika, gobe su Gimbiya Zulaha zasuga gawar Hakim.....




To FAN'S gobe ne fa😁.... Shin gobe su Gimbiya Zulaha zasuga gawar Hakim kamar yanda suke faɗi.🤔


...... Gashi gobe kuma Sarki Abdulmalak yana neman duk wani bawa da hakimai da kuma iyalanshi a fada zaiyi wani abu wanda ba wanda ya sanshi sai dai gobe zasu gani🤪.


......... Komai ye wannan abun🤔





Wannan ansar ku jirata a page ɗin gobe💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼




_By Jameelah Jameey ✍🏻_




#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please


👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```


97&98




Tunda safe Hakima ta tashi ta fara hidimar gabanta tunda ba ita zatayi break ba Hikimatu ce tunda room ɗinta Hakim ya kwana, daman ita ba komai take ci ba yanzun duk da cikin nata ya kai wata biyar yanzun bata da girman ciki shiyasa har yanzun ba wanda ya gane tana da ciki kuma bata shiga sabgar kowa, duk da fitinar da Hikimatu take janta, amman bata da lokacinta kuma komai Hikimatu zatayi mata bata taɓai gaya ma Hakim ba, amman ita Hikimatu komai Hakima tayi mata sai ta gaya ma Hakim, Hakim har mamaki yake dan baki ɗaya halin Hikimatu da Hakima ba ɗaya bane.


Bayan Hakim ya tashi daga bisa abin sallah azkar yayi dan yau tunda ya dawo sallahr asuba yaji bai iya komawa bacci ya cigaba da azkar ɗinshi yana gamawa yayi wanka ya shirya ya fita ya bar Hikimatu tana baccin asara, bacci take bata damu da ta tashi tayi masu break ba, daman shi tunda yake da Hikimatu bai taɓa shan koda ruwan hannun Hikimatu ba dan shi harga Allah ƙyamarta yake, bayan ya gama shiryawa ya tafi yaga ya sanyin idanuyanshi ta tashi ita da Babynshi, yana zuwa room ɗin Hakima suka cin karo da juna, ja da baya tayi sannan tayi hug ɗinshi tana cewa, "ina kwana mijina."?


Ƙara rungume ta yayi sannan yace, "lafiya lau My Jewel ya kuka kwana keda Babyn na."?..... "Uhmm, abunda jiya Babyn ma hanani bacci yayi, sai dai na tashi nai ta sallah fa.".... Ta ƙarasa maganar cikin yanga da shagwaɓa rungumeta ya ƙarayi sannan yace, "sorry Jewel ban sani ba ai da nazo munyi sallar tare ko."?... "Aa ai inasan kayi bacci ka huta, kuma Hikimatu ba bari zatayi ba, ni yanzun bansan tashin hankali."... "Ai ko da na sani da sai nazo munyi sallahr tare, amman ai yau zamuyi ko."?.... "Eh insha Allah, Angle nifa hankalina tashe yake, bansan taron mai Abba zaiyi ba yau naji Baffah yace zasuzo dan suna hanya ma, Allah yasa ba wata matar zai sake baka ba.".... Lakusar mata hanci yayi sannan yace, "Jewel bai dai tsoron kishiya kike ba."?.... "Aa Angle ban tsoron kishiya amman kasani ina sonka ina kishinka."..... "Nima ina sonki ina kishinki, insha Allah daga Hikimatu ba zan sake aure ba,

Please Login or Register in order to submit comment