Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zakiyi ma dan uwanki musulmi irin wanann tsanar? "


"Nidai!! I tell you, dan haka No Need to touch my friend, ok as with wish Hakima ..


"Ni zan wuce gida mangrid tayi, sai mu hadu test tomorrow by the graces of God, "ok byee thank for visit me, "don't wrong, thank uh too..


Nan Hakima ta wuce gida, wanka kawai tayi da sallah ta zauna ta cigaba da karatunta, dan yanzun bata da lokacin kowa sai na karatunta tayi missing din gida, amman tayi promise bata ko mawa wani weekend sai dai taje holiday..


Bayan ta gama karatu tayi alwallahr bacci da addu'a ta kwanta bacci da wuri dan eight suke da test din gobe ..

_______________________________


"Gaskiya Kilishi Ina mamakin yanda Hakim yake bata mana aikin mu, ko wane aiki mukayi mashi bai kamashi abun da Mamaki..


"Ni abunda nace Gimbiya mai zai hana mu sake boka, "mu sake boka fa Kilishi? "Eh mana, tunda shi yanka daya aikinshi yaki yi sai mu sake wani mu gamu, ba mu san ida za'a dace ba..



"Kin kawo shawara mai kyau kuwa Kilishi, amman wani hanzari ba gudu ba, "maikenan?


"Ni ina gani harta bayi wanda muke ba aiki sai mun sake wasu amman ya kika ce? "Eh to hakane mu fara chanza boka dai..



"To zanyi ma Lanto magana sai ta chanza mana sabon boka, dan Lanto ba bakon da bata sani ba..



"To hakan ma yayi, ni zan wuce na barki lafiya, "mun kwana lafiya..



"Kaga Aliyu nifa na fara jin bacci, tunda muka dawo duk ka bi ka damai ni da shututunka, har yanzun ban saurari mai amfani ba..



"Yanzun maganar Hakimar ce bata da amfani? Wallahi serious Hakim inasan naga ka auri Hakima dan kunyi marching..



"Kaga ai shiyasa nace maka baka da abun fadi mai amfani dan haka sai da safe, karda nasa ayi man waje da kai..



"Mai yayi zafi Allah ya tashe mu lafiya, "Uhmmm, Hakim yace sannan ya shiga toilet yayi alwallah ya fara sallolinshi da duk abunda ya saba yi kafin ya kwanta bacci...



Bayan ya dawo daga massallaci wanka yayi ya shirya cikin shampoo shadda brown ba Karamin kyau Hakim yayi ba, sannan ya dauki hanyar makaranta saboda test..


______________________________


"Gaskiya Hakima kin burgeni yau da kika shigo da wuri, "kinji ki da wata magana daman can da wuri nike zuwa school, wancan marar mutuncin ne shine yake ganin bani zuwa cikin lokaci...



"Hmmm!! Nidai Hakima kina bani Mamaki wallahi kedai Hakim bai yin dai dai a wajen ki, "Hmm..


Nan Hakim ya shigo yayi masu test sannan ya kama gabanshi...





_By Jameelah Jameey✍🏻_





share and comment pls

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_


_Jameelah jameey 🖋_


*(Yar mutan kankia👸🏻)*


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```



29&30



"Oyoyo! Oyoyo!! Oyoyo!!! Daughter sannu da dawowa"...


"Yauwa Momy, wallah Momy duk nayi missing dinku, "ai muma munyi missing dinki Daughter, "Amman shine ko ziyara baku kawo man ba?


"Ai Maimartaba yace karda aje, a barki kiyi karatu sosai, yanzun tashi kice abinci sai kije ku gaisa da Fulani..


"Uhmmm! Mai aka dafa man? "Sinasir mana shi nayi maki da kai na ma, "Yauwa thnk you Momy..

Nan Gimbiya Hakima taci Sinasir din sosai sannan ta nufi shashen Fulani....



"Fulani sannu da hutawa, "Yauwa Hakima ya karatun? "Alhmdulh, "Allah ya baki sa'a, "Amin ya Allah..


"Kinje kin gaisa da Maimartaba ko? "A'a sai gobe zani, na dai aika am maman ison ganinshi..


"To Allah yayi maki albarka, "Amin ya Allah, ni zan wuce, "To Hakima dan Allah kiyi hakuri da wannan bayin Allah da suke a karkashinki"..


"To insha Allah zanyi iyakar kokarina Fulani, na barki lafiya"..


Bayan Hakima ta koma shashen ta, waya tayi da Maryam sun jima suna wayarsu sannan sukayi sallama..


"Bilkisu, "Allah ya taimaki Gimbiya Hakima gani gabanki ina jiran umirninki"..


"Ki dauko takalma nan akaima Barau ya gogeman su, dan inasan gobe naje gidan marayu"..


"Angama ranki yadad'e yanzun zani cika umirninki "..


"Uhmmm, abunda Gimbiya Hakima tace Kenan , sannan tace, "kice ma Azima ta ansoman dinkina gidan waziri, Lantana kuma ta gogeman kayan baki dayan su"..


''To angama yar'sarki jikar'sarki, "bayan nan ki gayama masu aiki nan shashen gobe da safe bayan kungama aiki ina san ganinku baki daya"...


"Insha Allah uwargijiyarmu na barki lafiya "...


Nan Bilkisu ta tafi ta gayama Barau sakon Gimbiya Hakima..


"Malan Barau sannu da hutu, "Yauwa Bilkisu yan zauzau ansha zauzau, "Aiko dai Malan Barau ya muka samaiku? "Alhmdulh "..


"Ai mu tunda kuka tafi , muka fara giba da kumari, dan rabon da aima wani bawa a masarautarnan ko yatsa tun tafiyarku ba'a nuna mana ba, daman Gimbiya Hakima itace marar tausayin da mutunci, to kuma tayi mana nisa"...


"Muma ai tunda muka tafi muke jindadinmu, da man kune kuke jamana, tunda bakusan halin Gimbiya Hakima ba shiyasa kuke bata mata rai"..



''Ai baku ganeba Bilkisu Amman.. "Da kata dan Allah, haba ya isa haka Malan Barau , ko baka san baki shi ke yanka wuya ba? Yanzun idan wani yazo wucewa ya jika kana ai banta Gimbiya Hakima kaga kashiga uku kenan, harda ma ni, dan haka ga wanann takalman nan na Gimbiya Hakima ka gogesu kafin gobe"...



"Yanzun duka uban takalman nan zan goge? Kuma kafin gobe? "Eh ashe ma tambayata kake? Kayi yanda ka gadama ni kaga tafiya ta"..



"Gaskiya sunyi yawa dan na Gimbiya Yakumbo nike gogewa tun jiya har yanzun ban gamaba, kuma ni Gimbiya Hakima daga gani sunfi na Gimbiya Yakumbo yawa"..


Nan Bilkisu ta tafi tabar Barau da salati, dan ya rasa yanda zaiyi ya gama kafin gobe da yaga tunanin ba mai fishewa bane ya tashi ya cigaba ya cigaba da aikinshi ya samu ya gama kafin gobe..


"Ku Gimbiya Hakima tace gobe bayan kungama aiki tana san ganinku"..


"Munbani Ba'ba Bilkisu mai mukayi ma Gimbiya? Daga dawowarta ko sati biyu batayi ba"...


"Taya zan sani Larai? Nima ai yar sakoce, ke kuma Azima tace kije gidan Waziri ki anso mata dinki, Lantana kuma ki goge mata su"...




"Mun shiga ukunmu Allah yasa dai ba wani abu mukayi mata ba, "Amin Ladi nima abunda nike tunani kenan, dan wallahi bansan kiran Gimbiya Hakima dan ba alheri bane"...




"To Ab'u ya zamuyi inba hakuri ba, dan ni wallahi ban so suka dawo hutu ba, muna zaman-zaman mu ta dawo zata matsa mana "...



"Murja wallahi ku iya ganinku, nidai gaskiya nagaya maku, nidai kunga kwanciyata sai da safenku dan yau da wuri zanyi bacci, "to Ba'ba Bilkisu mu kwana lafiya"...



__________________________________



"Gimbiya Zulaha nifa nafara gajiya gaskiya, "Kilishi kwantar da hankalinki dan boka yace nan da wata hudu Hakim ya zama labari, dan yace mutuwa zaiyi cikin ruwan sanyi irin mutuwar da ba wanda zaiyi zargin kashe shi akayi ba"...


"Yauwa Gimbiya Zulaha, gaskiya naji dadin wannan labari naki"..


"Au ai yanzun gashi kingani da naje da kafafuna, ansamu aiki maisauki da kyau, dan Million da'ya na ba boka yayi abunda ya kamata ayi "..



"Da yace na samo bakar Akuya da bakin Zakara da Kaza mai wake-wake da Bunsuru dan shekara goma sha biyar"..



"Dan shekara goma aha biyar fa Gimbiya? "



"Ki tayi gani Namiji da suna Hajara, shiyasa nace ni ina zan samu wannan abubuwan ina gidan sarauta fita sai kabi dare? "



"Gaskiya ko Gimbiya,"ai shiyasa na bashi million daya yayi duk abunda ya dace ayi, da man ni bani san aikin da za'abamu mu zuba ma Hakim a abinci ko abun sha"...



"Nima gaskiya bani san kallar wannan aiki, gwanma kaba da kudi suyi aikinsu da kansu, kai kuma kayi baccinka, ni zan wuce mu kwana lafiya muna zuba ido muga wata hudu yayi zamuyi shagali dan har rawa ma sai nayi "...


"Wai waya ga Kilishi da rawa, ai yana mutuwa zamuyi lokacin ubanshi dan shima na gaji da ganinshi a doran kasa"...



"Au hakane fa, amman ni ban dauki ubanshi matsala ba shiyasa nike mantawa dashi, amman zamuyi lokacinshi mu kwana lafiya"..




Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Gimbiya Zulaha da Gimbiya Kilishi sun kasa zaune sun kasa tsaye wajen neman Bokaye..



Basu wurin Boka basu wurin Malan Boka, dan ko wace so take ace nata ya zama Sarki, amman duk tungun da Gimbiya Kilishi take yima Yarima Hamad Gimbiya Zulaha bata gane ba...



Ita dai tasan bata da masoyiya kamar Gimbiya Kilishi, kuma bata da makiya kamar Gimbiya Fulani, dan gani take da Sarki bai aureta ba da Hamad ya zama Yarima mai jiran gado, amman Sarki yayi gajin hakuri yayo mata kishiya ga shinan tana haihuwa da wata biyar itama ta haifi Hamad, dan haka ta uzurtama kanta sai Hamad ya zama sarkin Zaria, dole ta zama uwar sarki dan haka sai inda karfinta ta kare...



Ita kuma Gimbiya Fulani baiwar Allah bata damu da hidimarsu ba, Ita dai tasan rai da lafiya suna wajen ubangiji mu dan haka idan Hakim ya rasu lokacinshi ne yayi, ba dai asiri ba.


Shiyasa bata tada hankalinta ba tasa hidimar gabanta a gaba tana kula da mijinta da yaranta..



Itako Gimbiya Kilishi tana ganin yanda take yar'sarki jikar sarki matar sarki dan haka ya zama dole ta zama uwar sarki bata damu da Humad ba shi bane Babba tunda nan da wata hudu Hakim zai mutu, sauran ta ida dasu Hamad shida uwarshi..


Dan haka sai inda karfinta ya kare, mundun tana da rai da lafiya sai Humad ya zama Sarkin Zaria, shiyasa ta bazama neman bokaye da Malan Boka...


________________________________



Bayan ko wace ta gama aikinta suka hadu a kofar shashen Gimbiya Hakima suna jiran fitowar ta..



Sai da Gimbiya Hakima ta gama shiryawarta sanann ta fito..



"Kuna jina? "Eh Ranki yadad'e, "naji dadin yanda yanzun kuka maida hankali wajen aikinku, wannan ya nunaman kun fara sanin abunda ke maku ciwo, dan haka sai ku Kara maida hankali sosai, da mai magana? "...



"Aa babu, Allah yaja da tsawancin kwana, "Uhmmm! Kun iya tafiya ku bani waje"...


Nan suka tafi suna mamaki da jindadin chanjin da suke samu wajen Gimbiya Hakima dan tun dawowarta suke ganin chanjin sosai a wajen Gimbiya Hakima ..



"Lantana wuce kicema Bilkisu ta anso man takalman nan wajen Barau, sannan ku tabbatar da kun shirya dan fita zamuyi"...



"Angama ranki yadad'e, nan lantana ta gayama Bilkisu sakon Gimbiya Hakima, sannan suka fara shiryawa itada Azima..



Bayan sun gama shiryawa suka tafi shashen Gimbiya Hakima, ita ma Bilkisu ta anso takalmi har shiryawa tayi suna jiran fitowar Gimbiya Hakima su wuce gidan marayu..



Bayan ta fito suka wuce gidan marayu tayi masu abunda ta saba yi sanann suka wuce kasuwa nan tayi provision dan gobe take koma wa school sun gama hutu, zasu dasa second semester...



Washe gari Gimbiya Hakima ta shirya tayi bankwana da kowa sanann suka dauki hanya Zaria..




_ByJameelah jameey ✍🏻_





Share and comments pls


👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_


_Jameelah jameey 🖋_


*(Yar mutan kankia👸🏻)*


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```



31&32



Washe gari da wuri Gimbiya Hakima ta shirya ta wuce school dan ko breakfast bata tsaya tayi ba saboda tanada prpratical...



"Lantana!ki tabbarta da kungama komai dan bansan na ɓata maku rai"..

"Allah yataimakeki,Ranki yadad'e insha Allah zaki samaimu masu bin umirninki"..


"Uhmmm"..


Nan Gimbiya Hakima tafi tana sauri dan bata san ta makara dan ta lura lokacin gudu yake ga prof Hakim ne zai shigo masu..



"Bala"..

"Allah ya ji da tsawancin kwana, "idan ka kaini ka juyowarka gida zan kiraka indan mun tashi"..


"Godiya nike uwar marayu Allah ya ƙara maki lafiya da daukaka"..


"Uhmm! Yi sauri Bala bansan na makara lokaci na tafiya"...


Nan Bala ya ƙara bama mota wuta dan shima ya fahimci Gimbiya Hakima batasan tana makara dan taba bokonta Fahinmanci sosai...

Haka suka isa ta fita ta wuce class shi kuma ya wucewarshi gida yana murnar yanda Gimbiya Hakima ta barshi ya wuce gida ba tare da tace ya jira har sai ta gama lectures ba..



"Maryam kinga yanda kika ka ƙara kyau da haske ba kamar ba keba kinga yanda kika koma kuwa? "Hmm! Na kaiki Hakima baki ga yanda kimar Hakim ba"..


"Kinji matsalarki ko? Har zaki fara ɓata man rai ko? "..


"Hakuri Gimbiya yanzun dai ya kika baro su Fulani da Yakumbo? "..


"Lafiya lau wallahi suna gaisheki ma, "ina ansawa, mundawo kenan sai hutu kuma tunda second semester ba wani daɗawa akeyi ba"...



"Ni daman ba wani weekend din da zani sai hutu, yanzun dai muna zuba ido muga anfiddo mana da result''...


"Allah yasa dai muga alkhari"Amin ya Allah "..


Nan dai suka cigaba da maganarsu, nan sai ga Hakim ya shigo...


"Morning class,"morning sir, ba tare da ɓata lokaci ba Hakim ya cigaba da yi masu lecture, lecture ta dauko dadi dan class din yayi shiru ba kajin motsin komai sai maganar Hakim..



A na cikin lecture Gimbiya Hakima taji wani irin fitsari ya matso ta, dan tayi iya bakin kokarin ta na ta matsa fitsarin amman abun ya faskara dan ya ma kusa kufce mata...


"Excuss me Sir"...


Hakim yana jinta amman yayi banza da ita, dan tunda ya kalleta ya fahimcin fitsari ne ya kamata dan haka ya kudircin ma kanshi bai barinta fita sai dai tayi a wando, dan yanda ta cimai mutunci cikin mutu a join itama sai taga wulakanci yau din nan...


"Please Sir i beg Excuss me, "can you sit down or know? "...


"Sir i want to i.. "Shutup idiot i said sit down or cary your materials get out of my class"...


"Plea..se"...

Abunda Hakima tace kenan taji ruwan fitsari na bi mata kafafu, ba tasan lokacin da ta duƙe ba tana kukan bakin ciki dan tunda take ba'a taɓa ci mata mutunci ba kamar yau..



Ita dai Maryam da Yan class suna kallon ikon Allah, amman basu ji dadin abunda Hakim yayi ma Hakima ba dan cin fuskar yayi yawa ya wuce misali sosai...



Ko shi kanshi Hakim baiji dadin abunda yayi mata ba, dan tunda yake bai taɓa jin tausayinta ba kamar yau, amman dole ya rama abunda tayi mashi itama taji yanda yaji...



"Selient Class give me attension"..


Nan dai suka cigaba da lecture dinsu amman ba dadi dan gani suke yau cin mutunci Hakim yayi yawa dan ya cuce Hakima...



Itako Hakima tunda ta duƙe bata sake dago kanta ba, tana aikin kuka dan bata san wani kallar mataki zata ɗauka tsakaninta da Hakim, dan wata kallar wutar tsanarshi ke ruruwa a cikin zuciyarta...



Hakim bai fita ba sai da ya gama abunda ya kawo shi sannna fita amman duk jikinshi a sanyaye yake, da yake Hakim jarumine bai yarda aka gane mashi ba..


"Yi Hakuri Hakima tashi mu tafi ki chanza kaya dan Allah ma yaso na taho da wasu ɗinki da na anso wajen tarler na"..


"Na tsaneshi wallahi Maryam banda maƙiyi kamar Hakim insha Allah sai nayi mashi abunda bai mantawa dani"...


"Haba Hakima wai har sai yaushe zaku daina yar ramuwarnan? Nasan wallahi wani abu kika yi mashi shiyasa shima yayi maki haka"..



"Dan Allah kiyi hakuri ki ƙyaleshi ba dan ni ba, na roƙi wannan alfarma nidai yau a wajenki dan wallahi banjin dadin wanann faɗan da kuke yi, kudai baku taɓa haduwa waje ɗaya kamar annabi da kafiri? "



"Wallahi sai na rama Final na gama magana, ni gida zani muje kiƙa ni na chanza kaya kafin Dr Moha ya shigo"...


"Ok less go"..
_____________________________


Wanene Hakim..


Masarautar Zaria, Masarautace wanda tana ɗaya daga cikin Masarautun da ke babban a Nigeria..



Sarki Sulaiman Muhammd shine ya Haifi Sarki Muhammd Sulaiman, Sarki Muhammd Sulaiman shine ya Haifi Yarima Hakim, Yarima Hamad da Yarima Humad da Gimbiya Maryama da Gimbiya Sadiya su biyar ne Allah ya bashi a duniya...



Sarki Muhammd Sulaiman Gimbiya Zulaha ya fara aure ita yar'Sarkin Daura ce a kasar Katsina...



Allah ya daɗe bai ba Gimbiya Zulaha haihuwa ba, Gimbiya Zulaha ba karamin tashi hankalinta yayi ba, dan taga har sunyi shekara biyar da yin aure ita da Sarki Muhammd amman haihuwa shiru kake ji..




Ban inda Gimbiya Zulaha bata shiga ba dan ta samu taga ta haihu amman ba wani bayani tun tana zuwa asibiti har ta fara biye-biyen Malamai da bokaye itada baiwarta Lanto amman duk inda suke je kudin su ake ci a banza ba, dan ba wani chanji da Gimbiya Zulaha take gani..



Ana cikin haka Sarki Muhammd Sulaiman yazo mata da zancen karin aure, zai auri yar'sarkin Adamawa..


Tunda Gimbiya Zulaha taji Sarki Muhammd yayi mata maganar zai kara aure nan ta kara tashin hankalinta dan ba asirin da batayi ba dan karda Sarki yayi mata kishiya amman ina Allah ya kaddara sai anyi wannan aure, bayan sarki ya gaya mata bikin da wata ɗaya aka ɗaura mashi aure da Gimbiya Kubrah, suna kiranta da Fulani..



Bayan auren ba wahalar da Fulani Kubrah bata sha ba wajen Gimbiya Zulaha, dan magungunan hana haihuwa aka kama sa mata cikin abinci amman bata yarda tasha koda ruwa ba da ya fito daga shashen Gimbiya Zulaha ba..



Ana cikin wanann hali tsakanin Fulani Kubrah da Gimbiya Zulaha sai ga ciki a jikin Fulani Kubrah, tunda Gimbiya Zulaha ta lura da Fulani Kubrah tana dauke da ƙaramin ciki ba ƙaramin shiga tashin hankali tayi ba..



Dan batasan iya adadin kudin da ta kashe ba, wajen neman Malamai da Bokaye amman a banza dan bakin duk Zakaran da Allah ya nufa da cera kona mazuru a na shaho sai yayi shi..



Gimbiya Zulaha tana cikin neman Malamai sai itama ga ciki ya fito a jikinta, ba ƙaramin murna tayi ba, dan harta Sarki Muhammd Sulaiman sai da yayi murna yana godema Allah da ya bashi kyauta biyu cikin shekara guda..



Haka suka cigaba da rainon cikin su, amman duk da haka Gimbiya Zulaha bata ƙyale Fulani Kubrah da cikin ta ba, dan tayi alwashin bata haihoshi duniya sai ta kaudasu..



Hak dai Fulani Kubrah tai ta hakuri tana neman tsarin Allah daga sharin Gimbiya Zulaha dan tunda take ko sau ɗaya bata taɓa gayama sarki irin zaman da suke da Gimbiya Zulaha ba..



Duk da yana sane da duk abunda ke faruwa tsakanin iyalinshi amman ya samusu ido, dan yasan gidan sarauta ya gaji haka...



Cikin Fulani Kubrah ya isa haihuwa dan ta haiho santalelen ɗanta Namiji mai kama da ubanshi aka sama yaro suna HAKIM..


Da Gimbiya Zulaha taji labarin haihuwar Fulani Kubrah kuma ɗa Namiji ta haifa ba dan ƙaramin yaki tayi cikin ɗakinta ba ita ɗaya, haka ta baza amintatun bayin ta bin Bokaye dan ganin mutuwar ɗan da Fulani Kubrah ta haifa amman asiri bai tashiri kanshi tunda Allah ya tsareshi..



Bayan haihuwar Fulani Kubrah da wata biyar itama Gimbiya Zulaha ta haifi ɗanta Namiji shima yana kama da ubanshi dan shi yana da duhu ba kamar Hakim ba...


Ranar suna yaro yaci suna HAMAD, bayan Gimbiya Zulaha ta gama wanka ta cigaba da neman sa'a dan taci alwashin sai Hamad ya zama sarkin zauzau, ko ta wani hali..


Tare suke yin komai shida Hakim, ba ƙaramin kaunar juna suke ba haka suka taso komai nasu iri daya ne...

Suna da shekara biyar Sarki Muhammd ya auro Gimbiya Kilishi yar'Sarkin Suleja..


Ba yand Gimbiya Zulaha batayi ba dan karda Sarki yayi mata kishiya ta biyu amman ba yanda ta iya sai dai tasa ido yayi aurenshi..


Ita ko Gimbiya Fulani bata wani damuba ita dai tasa Allah gaba tana neman tsari daga masu sheri dan ba dare ba rana haka take wuni ibada da roƙan Allah..


Gimbiya Kilishi daga auren ta da shekara ɗaya itama ta haiho ɗanta Namiji mai bala'in kyau dashi masha Allah, yaro yaci sunan HUMAD..


Tunda Gimbiya Zulaha ta lura da Gimbiya Kilishi itama ba daga baya ba wajen bin Bokaye da Malamai dan sau biyu suna haduwa wajen Boka daban-daban shiyasa suka kulla Aminta ba dan ransu yaso ba..


Gimbiya Kilishi ta sama ranta ko ta halin ƙaƙa sai Humad yayi sarkin zaria, shiyasa itama ta hana kanta bacci take bin Bokaye..


Amman a gaban Gimbiya Zulaha nunawa take Humad bai isa ya riƙe mulkin zauzau ba tunda ga Hamad..


Soyayya sosai ke tsakanin Hakim da Hamad da kuma ƙaninsu Humad dan basu yarda ko ƙuda ya taɓa shi ba..


Tunda su Gimbiya Zulaha suka lura da shakuwa na shiga tsakanin yaransu sai suka kama hure ma yaransu ƙunne..


Haka Gimbiya Zulaha ta kama cusa ma Hamad san mulki, a hankali Hamad shima yaji yana san mulki tun yana yaro dan shekara goma.



Shi ko Yarima Humad bai yarda ya biye ma hudubar Mamanshi ba dan bai yarda ya hudɗa da Yarima Hakim ba..


Humad yana da shekara goma a duniya Fulani Kubrah ta haifi yaranta yan biyu duka mata, ranar suna yara sukaci sunan Maryama da Sadiya , lokacin Hakim yana da shekara goma sha biyar a duniya..


Gimbiya Kilishi da ta lura Hamad yana san mulki sai tayi mashi asiri tasa aka tusa mashi ƙiyaiyar Hakim cikin zuciyarshi sannan aka sa mashi shiririta da rashin san yin ibada..


Amman Bokan yace duk randa Hamad ya ɗauki buta da sunan zaiyi alwallah yayi sallah wannan sihirin ya kare..


Wanann shine dalilin da baki ɗaya Hamad baya san Hakim dan ko ganinshi bai san yi..



Aliyu shi dan gidan Waziri ne dan sa'annin junane shida Hakim, Hakim wata biyu ya ba Aliyu a duniya duk tare suka taso..



Wannam kenan ☺️



Back to the story kundai summary din kabarin Hakim shida yan uwanshi..




_By Jameelah Jameey✍🏻_



Share and comment pls

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_


_Jameelah jameey 🖋_


*(Yar mutan kankia👸🏻)*


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```





33&34





"Hakim lafiya naga duk ka wani zama silent maike damunka? "..



"Hmmm! Aliyu kai dai bari wallahi yau nayi ma Hakima abunda banji dadi ba ko da sau daya ne"..



"Mai kuma ya sake haɗaku da ita? "..


"Kawai dai kasan abunda tayi man a join, to shine nima na rama amman at the end banji dadin abunda nayi mata ba wallahi totaly"...


"Wata sabuwa inji yan-caca, mai kuma kayi mata? "..


"Kawai dai ta tambaye ni zata fita na hanata daman already na fahimceta fitsari xatayi, wallahi banyi tunanin fitsarin ya matseta sosai ba kawai naga yarinya na fitsari a tsaye, baka ji yanda nike ji ba kamar mai"...



"Ayya! Maganar gaskiya Hakim baka kyauta ba, ai koda zaka rama abunda Hakima tayi maka bai kamata kayi mata haka ba"...


"Ko baka san ba'asan mata na tara fitsari ba? Balle ita ta tambaye ka ka hanata gaskiya baka kyauta ba"..


"Uhmmm! Naje nayi ita bata ga abunda tayi man ba, dan haka ni nama

Please Login or Register in order to submit comment