Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hakim.



"Hamad yaushe ka zamo wawa wanda baya aiki da tunani."?

"Amman Gimbiya, "Amman mai Hamad kasan bala'in da zaka ballo mana idan ka kashe Hakim".?

"To tsaya kaji ni, mudun ka kashe Hakim, to kaima kasa a ranka sai ankashe ka, kaga mulkin da muke jira ya koma hannu Kilishi kenan munyi wahalar banza."


"Amman idan kabi a hankali ba wanda yaji ba wanda ya gani zamu kashe Hakim cikin ruwan sanyi, ba wanda zaice kashe shi akayi, "taya haka zata kasance Gimbiya? Sannan sai yaushe zaku kashe Hakim."?



"Yanzun Hakim zai aure Hakima, amman boka Turmurturs yace zasu hana Hakima haihuwa da Hakim, suna kashe Hakim kuma sai a maida aurenka da Hakima kaga shikenan mun jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya."



"Amman ina kishin Hakim ya rigani sanin Hakima a matsayin mace, zanyi hakuri da shawararku Gimbiya ni zan koma aiki."


"To shikenan, karka kuskura na sake jin kalma sai ka kashe Hakim , kajini ko".? "Eh naji na barki lafiya.


Tunda Hakim ya tafi shashen Fulani ya kasa komai dan ko abinci kasa ci yayi shidai kagashi nan kamar ba shi ba haka yake jin kanshi.


"Hakim ko baka san zaɓin da Abbanku yayi maka."?

"Aa Fulani wallahi inaso, in ban bi umirnin iyayena ba umirnin wa zan bi, kawai ji nike kamar bani ba yau ɗina."


"Ka yawaita addu'a Allah yana tare dakai kaji yaron kirki."?

"Eh naji Fulani, ni gobe zan tafi kano ni ɗaya zani ko na tafi da Aliyu."?

"Aa ka tafi kai ɗaya ganin juna zakuyi kuma bikin saura wata ɗaya haka naji Abbanka yace.''


"To Allah ya kaimu, ni zan wuce massallaci na barki lafiya."

Bayan Hakim ya dawo daga sallah Tea ya sha sannan yayi addu'oi sannan ya kwanta dan ya gaji sosai ga washe gari zashi kano.

_______________________________


Tunda Hakima taji gobe Hakim zaizo bata zauna ba dan shiri take duk da tanajin ba dadi a zuciyata amman haka take ɗaurewa dan taba mutanan gidansu mamaki.


Bayan sun gama wani shirin dan Hakima ƙara komawa tayi wajen gyaran jiki aka sake yi mata su dilka sannan ta dawo gida, har yanzun bata samu lokacin waya da Maryam ba balle ta gaya mata ba, amman tana ranta tana san gaya mata, bayan ta dawo wanka kawai tayi sai bacci.



Washe gari tunda safe su Lantana suka tashi suka fara aikin tarar bako dan suke kamar mai abinci ake kala-kala dan har abun ya fara ba Gimbiya Hakima tsoro dan gani take kamar yau ce ranar bikin dan hidimar da bayin gidan keyi duk dan tarbar bakon da zatayi a yau kawai.



_Too My Fans wani kallar drama za'ayi idan Hakima da Hakim suka ga ashe junansu zasu aura? Am watting urs Answers🤣😎_


_BY Jameelah Jameey✍🏻_

#JameelarhSadiq
#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please





👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```






67&68




Bayan anfito daga sallar asuba, Hakim yaje wajen Maimartaba yake gaya mashi tunda safe zai ɗauki hanyar kano dan baisan yayi tafiyar dare, nan Maimartaba yasa mashi albarka da fatan zuwa lafiya da dawowa lafiya.



Daga wajen Maimartaba wajen Gimbiya Fulani Kubrah ya wuce nan itama tayi mashi fatan zuwa lafiya da dawowa lafiya, sannan ta bashi wata super aura da wani laces dan two million tace ya ba Hakima idan yaje haka ya ansa yana godiya ya fita.



Shashen shi ya wuce ya ajiye kayan, sannan ya shiga wanka bayan ya fito daga wanka ya fara shiryawa cikin wani black bowel da kaga wanan bowel ɗin kasan kudi sunyi kuka a wajen sayanshi balle Allah kaɗai yasan nawa ya bada wajen ɗinkinshi, takalminshi dan campany oriflame shida watch ɗin da ya manna a hannunshi ita kanta watch din abun kalloce balle azo ga hular da yasa ita black and red Infact Hakim ba karamin kyau yayi ba.




Bayan ya gama shiryawa ya dauki hanyar Kano, yana mamakin yau shine zashi wajen mace da sunan zance, macen ma da yanzun sauran one mouth bikinshi da ita.


"Dole ni Hakim na koya ma kaina san wanan baiwar Allah da Abba ya hada ni da ita, sannan dole na cire tunanin wanna stupid girl din cikin zuciyata dan ba anfani na kama tunaninki Hakima, I hate you too Hakima ki fita daga rayuwata."


Abunda yace kenan ya cigaba da driving dinshi da yaga abun ba mai ƙarewa bane sai ya kunna ƙira'ar Ahmed Sulaiman yana sauraron, sanan ya fara dawowa dai-dai.


____________________________


*×KANO×*



Bayi aiki suke tukuru dan tun Hakima tana lisafa kalar abunda ake haɗama bakon nata har ta daina dan gani take abun ya wuce misali sai kace wanda za'ayi ma biki.



Ruwan wanka mai rai da lafiya Lantana ta haɗa mata dan har sun fara yi ma uwargijiyar tasu shiri na musaman saboda kowa yasan bikin saura wata ɗaya shiyasa suka tashi tsaye wajen ganin su shirya ta yanda dace.


Bayan ta gama haɗa mata ruwan wankan sannan Hakima ta shiga, ita kuma Azima ta fiddo mata kaya nagani na faɗa, dan already Azima taje ta ɗauko mai make-up Hakima kawai suke jira ta fito wanka su fara aikinsu.



Sai da Gimbiya Hakima tayi kusan minti talatin a toilet sanann ta fito ta zauna aka fara tsara mata kwaliya mai rai da lafiya, bayan angama tasa kaya aka ɗaura mata dan-kwali ɗaurin Zara Buhari akayi mata amman ya fidda shapes sosai.




Bayan Hakim ya iso Yarima Annas yayi mashi jagora shashen Maimartaba ya fara gaidashi sannan ya wuce shashen Gimbiya Yakumbo itama ya gaidata sanann shashen Fulani itama ya gaidata, tun anan Yarima Hakim yasan yazo gidan sarauta kuma gidan sarauta masu mutunta mutane suka jarajar dan adam nan take yaji dadi dan da alamu masarautar kano ba'a tungun da akeyi a masarautar su, bayan sun fito daga shashen Gimbiya Fulani bayi suka kama gaidashi suna yi mashi barka da zuwa masarauta mai albarka, kuma yaga alama, shashen Yarima Annas suka koma sannan Yarima Annas ya kira Gimbiya Hakima yace tazo shashen shi bakonta yana jiranta.



Abinci aka fara jerama Hakim gabanshi kala-kala dan har Hakim sai da yayi mamakin karanci irin na wanan masarauta gaskiya suna da karanci da sanin mutuncin mutane, dan yaga yanda bayinsu suke walwala kamar ba bayi ba bayan sun gama ajiye mashi abinci suka fita.



Yarima Annas ya matsama abokin nashi yaci abinci sosai dan sai da yaga yaci sosai sanann ya kyaleshi nan suka ƙara gaisawa ya tafiyarshi ya bar Hakim yana zaman jiran isowar Gimbiya Hakima.


Wooow! Masha Allah tafiya take cikin natsuwa da ɗaukar hankalin duk wani ɗ'a Namiji mai lafiya, lace ne purple a jikinta ɗinkin riga da siket ba karamin kyau kayan sukayi mata ba alkalbarta black ce sanan takalminta ma black ne agogonta yar company Gucci itama black ce, ba wata kwaliyar hauka akayi mata ba dab sai ka rantse kace ba a shafama Hakima poder a fuska ba dan pure skin Hakima ke gareta, take mata baya bayinta ke take mata baya sun ɗagemata alkalbarta dan karta share kasa, sai ka rantse kace yau ake ɗaura ma Hakima aure zabar kyaun da tayi.



Har cikin parlourn Yarima Annas bayinta suka rakota sune ɗage da alkalbarta daga ita har Hakim ɗin basu gane juna ba dan shi Hakim ba ita yake kyalo ba yana mamakin kalar mulki na amaryar tashi ne dan tafiyar ta kawai zai shedda maka da tanada mulki, bayan su Lantana sun gama gaisheshi hannu kawai ta ɗaga masu sannan suka tashi suka fita baki ɗayansu.


Ɗagowar da Hakima zatayi suka haɗa ido da Hakim, su duka suka miƙe lokaci guda suna nuna junansu da hannu nan Hakima ta fara magana tana nuna nashi da yatsa tana cewa...



"Waya ka woka gidanmu, ubanme kazo yi mana.. "Hakima enough ya isa haka."... Yana dakatar da ita ranshi ɓace.


Hakim ya faɗa kamar zai ɗauke Hakima da mari, ita kanta Hakima sai da ta tsorata dan tunda take da Hakim bata taɓa ganin ɓacin ranshi ba irin wanann.



"Lock at you, ni nafi karfin nazo nace inasanki dan kawai biyaiya zanyi ga mahaifina da ba abunda zanyi dake sann... "Hakim karya kake wallahi baka isa kace man haka ba, kayi yanda kayi ka iko mahaifinka wajen Baffah dan a ɗaura maka aurena ko? To tsaya kaji kayi maza-maza kace ma Babanka ka fasa aure na dan wallahi Hakim da ka aureni gwara karkayi aure a rayuwarka har ka mutu dan ni *GIMBIYA HAKIMA* na tsaneka bani kaunar dan haka bala'i da masifa zaka auro ma kanka gwara tun wuri kaje kace ka fasa Auren nan tun kafin dare yayi maka."




"Ke ɗin banza, ke har kin isa kice naje nace ma Abba na fasa aurenki to bari kije na gaya maki ni *YARIMA HAKIM* yanzun nayi niyar aurenki Hakima, zan aureki ba dan inasanki ba, zan aureki dan na koya maki hankali da tarbiya dan yanzun muka fara wasan nida ke Hakima useless girl."



"Aiko zaka ɗauro ma kanka wutar dafa kanka Hakim, "as we wish kina iya gaya ma mahaifinki bazaki aureni ba tunda daman ke ba kunya gareki ba, amman ni Hakim ba zan iya yin jayaiya da mahinfina ba dan nasan darajar iyaye, amm.." Dallah shut up ur darting mouse, har kai kake cema wani baiyin bayaiya ga iyayenshi, kamar yanda kayi biyaiya nima ita zanyi amman kasani bakai ba zaman lafiya a gidanka dan ni dai Hakima ba kaunar ka nike ba idiot wanda baisan mutuncin matune ba, ka godema Hakim haduwarmu tayi kyau amman haduwarmu ta gaba sorry to said."



Nan Hakima ta tafi tabar Hakim tsaye da mamaki baiyi mamakin rashin kunyar da tayi mashi ba dan ya san da man ba Kunya ke gareta ba, mamakinshi ɗayane daman ashe yar'sarkice? Shine yake mamaki ba rashin kunyar ba, bayan ya fito sukayi Sallama da Yarima Annas sannan ya wuto gida dan sakon Gimbiya Fulani daman already yaba Gimbiya Yakumbo ta ba Hakima.





_By Jameelah Jameey✍🏻_




#JameelarhSadiq@wattpad
#Share
#Comments
#Vote
#Like
#Please




👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```



69&70


Hakima direct shashenta ta wuce ta ɗauki waya ta kira Maryam, "Hello Maryam kina jina."?

"Eh ina jinki Hakima, lafiya maike mafaruwa naji kamar baki cikin hankalinki."?

"Na shiga ukuna Maryam, bansan ya zanyi ba Baffah zaiyi man aure cikin watan nan."


"Aure kuma Hakima."?

"Eh aure kinsan ma da wa zai haɗani Maryam."?

"Aa ina saurarenki dai Hakima, da wa Baffah zai haɗa ki."?


"Wai prof Hakim, "Alhmdulh Allah na gode maka wallahi bakiji yanda hankali na ya tashi ba amman yanzun Alhmdulh komai namu wanan shine tuwo.. " shut up, haba Maryam ya ina gaya maki problem ɗin na amman kina wata maganar daban."?



"Cool down mana ƙawata, wallahi kasa boye farincikina nayi domin maganar gaskiya Hakima Allah ne ya cika mana burinmu nida su Maryama to taya zaƙi yin farinciki."?


"Ok thank you ni zan kashe waya ta da man na kiraki ne ki kagayaman yanda zanyi amman kin ƙara ɓataman rai kin kyaunta Maryam."


"Wait Hakima karki kashe wayar zan gaya maki iyakar gaskiya a matsayina na aminiyarki Hakima, "Uhmmm! Am watting ina jinki."

"Maganar farko Hakima yin biyaiya ga iyaye yanada mahinmanci ga rayuwa dan Baffah yasan waye Yaya Hakim shiyasa ya bashi aurenki."


"Amman Maryam tsakani da Allah kin san bansan Hakim shima baya sona dan bakiji kallar maganganun da ya gayaman ba yau da sai na baki tausayi, NO Maryam Impossible ba banzan iya zama da Hakim ba please help me."



"Keko zaki iya zama da Hakim, Hakima sai kace ba mace ba? Ke fa mace ce kinsan yanda zakiyi ki shawo kan Namiji ko waye shi wallahi, dan ba abunda Allah ya rageki dashi duk da ance mutun tara yake bai cika goma ba amman ke daban ce cikin mata."



"Allah yayi maki kyau ga Ilimi, ke ɓata lokacine tsawa baiyana maki kallar baiwar da Allah yayi maki, kuma wallahi daga ke har Yaya Hakim ɗin kuna san junanku kawai san zuciya ya hanaku ku fahimci haka, amman very soon nan gaba zaku gane."


"Gashi ance masarautar su bata da daɗin zama saboda maƙirci yayi yawa a cikinta Maryam."


"Hakima ina wasu wanda muka taɓa gaisawa dasu su biyu lokacin da muna 300lvl."?


"Wasu yan-biyu ko."?

"Yauwa su, Maryama da Sadiya ko."?


"Hakane na tunasu, maiya samaisu."?

"Ai ƙannan Yaya Hakim ne, ta dalilinsu muke zuminci da Fulani Kubrah itace mamansu ni kuma makaranta ɗaya mukayi dasu tun nusery har university shiyasa nike cewa Yaya Hakim gunsu na sanshi, Yaya Hakim mutune mai mutunci da sauƙin hali ba zan tsaya gaya maki ba amman nasan nan gaba da ƙanki zaki gayaman halayen Yaya Hakim masu kyau ne shima da ƙanshi zai gane Gimbiya Hakima tana da hali mai kyau."


"Kena nufin yan-matan nan ƙannan shi ne wanda mukaita labari randa n a rakaki wajensu."?


"Kwarai kuwa uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, labarin faɗanki dashi nike basu shiyasa suka ce suna san watarana su ganki shiyasa na janyo ki suka ganki."



"Har naji sanyi wallahi Maryam ko ba komai na samu ƙawaye nadan ji sauki watarana."


"Aiko kedai kiyi biyaiya Hakima watarana zaki san iyayenki sun maki zaɓin kwarai, "nagode Maryam wallahi ba ƙaramin kyautarman da hankali kikayi ba, ni zani shashen Gimbiya Yakumbo sai mun haɗu a Jameey Novel Fans anjima."



"Ok shikenan, kin san ko yau akwai chapter sosai, "aikuwa sai mu haɗu dai dan yau ban kunna data ba nasan tayi posting ɗin *A HAKA NIKE SONTA* da *YAN MATAN ZAMANI* nasan yau za'a sha comment."


"Idan kin dawo daga shashen Gimbiya Yakumbo kin karanta dan yau Fatima ba ƙaramin tausayi ta banta hmm gaskiya *A HAKA NIKE SONTA* ba ƙaramin dadi yayi ba Fatima tana ban tausayi."



"Gaskiya nima Fatima tana bani tausayi, sanan Hafsat tana burgeni sosai dan tafi Zainab da Sadiya hankali wallahi, "nima Hafsat tafi burgeni a *YAN MATAN ZAMANI* dan ita tafisu sanin abunda take, amman su kawai sunce burinsu sai ya cika ta kowace hanya, "aiko kinsan ko haka yan matan zamanin nan suke, Allah yasa mu dace dai ni zan tafi sai mun haɗa a Jameey Novel fans ɗin."


Sister idan baki karanta wannan litaitafin ki nemaisu dan karda a barki a baya *A HAKA NIKE SONTA* & *YAN MATAN ZAMANI* Hmmm ni ba zan ce komai ba sai dai indan kin karanta ke/kai zakuce komai😎.



Bayan Hakima ta gama waya da Maryam ta tafi shashen Gimbiya Yakumbo.


_*YAN MATAN ZAMANI YANA HANYA MASOYAN MU, MUNAJIN KORAFE KORAFENKU NA HAR YANZUN MUNBAR YI MAKU POSTING TO ALBISHIRINKU YAN MATAN ZAMANI YANA HANYA DAN BAMU MANCE DA KU BA MASOYAN MU💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼*_



_*A HAKA NIKE SONTA KUMA MUNA SANE DAKU ZAMU CIGABA DA YI MAKU POSTING AMMAN SAI KUN GYARA KUNA YI MANA COMMENTS YANDA YA DACE WANANN ALBISHIRNE NA BAKU MASOYAN BUK ƊIN A HAKA NIKE SONTA KARKU MANTA DR MUBARAK YANA SO DEEN MA YANA SO TO CIKIN WA FATIMA ZATA SO🤔🤪*_
______________________________


*×ZARIA×*



Tunda Hakim ya koma gida yake mamakin yanda Hakima take furta bata Sonshi bata kaunar shi wannan kalma tana yi mashi ciwo bayan shi yasan idanuwanshi da kunnuwanshi ba abunda suke san ji da gani inba Hakima ba, amman zuciyarshi bata san Hakima, amman ita Hakima baiga haka tartare da itaba inba tsanarshi da yagani zallah a cikin kwayar idanunta taya zai zauna da Hakima bayan bata sanshi ta tsaneshi? *{wannan answer team Hakima ku zaku ba Hakim ita ba dai ni ba😉}*


Da yaga abun bamai ƙarewa bane sai ya kira Aliyu yazo ya dawo amman su haɗu a shashen Gimbiya Fulani Kubrah sai su wuce Lambu."



Bayan yaje wajen Gimbiya Fulani Kubrah nan yake gaya mata yaje yaga Hakima kuma tayi mashi ɗari bisa ɗari, Gimbiya Fulani Kubrah tayi farin ciki sosai dan daman bata da gurin da ya wuce da taga auren Hakim kuma gashi cikin ikon Allah lokaci ya kusa.


Bayan sun gama magana da Gimbiya Fulani, ya tafi Lambu shida Aliyu su kuma su Gimbiya Maryama da Sadiya suka hau Murna dasukaji yace tayi mashi dan daman sun san Gimbiya Hakima ce Abba ya nema mashi aure tunda sun santa kuma gidansu su biyune ita da Yayanta Yarima Annas.



Bayan sunje Lambu Hakim ya fara magana yana cewa, "Aliyu Hakima ce."


"Bangane Hakima ce ba? Kodai kafara sub'batu Hakim."?


Hmmm! "Ba sub'batun da nake Aliyu,Hakima ashe y'ar Sarki ce Aliyu."


"Kana nufi Hakima itace wanda Abba ya nema maka auren ta."?


"Tabbas Aliyu, Hakima itace wanda za'ayi mana aure wannan watan amman matsalar ɗaya Hakima ta tsaneni bata sona ko kaɗan, ni kuma zuciyata bata san Hakima amman kunuwana idanuwana suna san ganin Hakima da jin amon muryar Hakima."



"Kaima karya kake wallahi zuciyar ka tana san Hakima yaudarar kanka kake Hakim, itama Hakimar tana sanka duk kuna yaudarar kanku nan gaba zakace na gaya maka amman shashen za'abudema Hakima sabo ko kuma shashenka zata zauna."?



"Mun ma gama wannan maganar da Abba, shashena zata zauna tunda babba ne part ukune a cikin shashena to ba idan zata tana shashena ina lura da duk wani motsin ta, kuma banda matsala wajen mutanan gidanan dan Hakima bata kyale ta kwana nasan bazata shirya dasu Gimbiya Zulaha ba."



"Nima harda haka na matsa ka auri Gimbiya Hakima dan nasan su Gimbiya Zulaha ba zasu samu fuskar da suce zasuyi wani aminci da ita dan ita Hakima kallo ɗaya zakayi mata sai kaji shaskarta ta shigeka haka Allah yayi ta."



"Hakane Allah dai yasa mu dace, amman idan Hakima tace muyi zaman lafiya zamuyi mudun tace zaman rashin mutunci zamuyi wallahi zan biye mata daga baya mun sasanta, "Aa ban goyi bayanka ba Hakim, "saboda mai."?


"Saboda nasan ka baka iya hakuri, "ko? Da da babu Hakima na mutu."?


"Ai lokacin baka sama ranka ba, sanan ba ka ganin mace sai ka fita waje amman yanzun shashenka fa zaku zauna tare ai kai ba Sahabi bane da zakace bazakaji kana san ta baka haƙinka ba."


Uhmmm! "Zanko baka mamaki, "Allah yasa tashi mu tafi sallah lokaci yayi, "ok."


Bayan sum dawo daga sallah tea kawai Hakim yasha ya kwanta bayan ya tofe jikin da ayatul-kurshiyu da dai-dai addu'oi kala-kala sannan ya kwanta, kafin uku tayi ya tashi ya fara sallahr dare kuma sai asuba.






_By Jameelah Jameey✍🏻_




#JameelarhSadiq@wattpad
#Share
#Comments
#Vote
#Like
#Please



👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```





71&72



Tunda Hakima ta tafi shashen Gimbiya Yakumbo nan suka zauna suka fara magana.

"Daughter kinga Hakim ko."?

"Eh naganshi Momy kuma yayi Allah dai ya albarkaci Aurenmu."

"Amin ya Allah, daman nasan kuna ganin juna zaka amince da juna saboda ba ƙaramin dacewa kukayi da juna ba."


"Gaskiya ne Momy, yana da hankali ga dukan alamu dan jiya kawai muka fara ganin juna amman naga hankali a taitare da shi."


*{kunji Hakima da wata sharaton wai jiya suka fara ganin juna 🤣🤣}*

"Ai haka yake kuma gado yayi waje biyu daga uban har uwar, nidai Daughter dan Allah karki bamu kunya ku zauna lafiya keda wannan baiwan Allahn, Allah yayi maku albarka."


"Amin Momy, insha Allah ba zan baku kunya ba, "haka nike san ji ai ga wannan ya kawo da kudi dubu ɗari biyar."


"Wooow! Momy gaskiya nagode, amman ban ansar kudin nan sunyi man yawa ina da kudi sosai."


"Kinga a haka akayi ma kowace mace indai gidan sarauta ta fito sai uwar miji ta bada tukuncinta na fara zuwa neman aure kuma kw zakiyi amfani da komai da aka kawo wanan ne zaki nuna kin gode."


"To Momy nagode, na zan wuce na fara jin bacci, "to Daughter Allah ya kaimu, "Amin ya Allah."


Azima ta anshi kayan hannun Gimbiya Hakima sanann ta wuce dasu su kuma su Bilkisu suka take mata baya zuwa shashen ta, tunda Azima ta anshi kaya sai da ta kaisu kowane shashen dake cikin masarautar baki ɗaya sanann ta dawo wajen Gimbiya Hakima.


"Allah ya taimakeki, gaskiya Yarima Hakim yayi koƙari dan tunda nike ban taɓa ganin irin wanan kyautar ta ganin farko ba sai gunku."


"Uhmmm! Azima ku riba kuɗin ga duk wani bawa dake shashena sai kuyi hakuri ba yawa, sai ku fara shirin bikin kafin na baku abunda zaku bukata su kuma wanann super aura da wanann laces ɗin akai ma ɗikin fatan kinjini."?


"Allah ya taimakeki yanzun zani cika Umirninki, muna godiya Gimbiya Hakima Allah ya ƙara tsawancin kwana ya raba ki daga shirin maƙiya."


"Amin, ku wuce ku ban waje ina bukatar na huta, "to mun barki lafiya."


Haka suka tafi suna murna, ranar bayin shashen Gimbiya Hakima sunyi murna daman basu wuce su bakwai ba aiko sunsha kudi, Gimbiya Hakima ko tasha addu'oi kala-kala.


Bayan tafiyar su Lantana, Hakima online ta hau direct *JAMEEY NOVEL FAN* ta shiga nan suka fara comment da shirhi na novels ɗin Jameey dan suna gani koƙarinta wajen yanda take baje basira take Nishad'antar da masoyan ta, bayan sun gama sannan ta sauka online ta kwanta bacci.


*SOME DAYS LATTER*

Tunda Hakim yazo bai ƙara waiwayar Hakima ba itama bata damuba dan daman ita ba jiran wayarshi take ba balle zuwanshi, hidimar gabanta take balle biki yanzun saura sati ɗaya dilkar da halawar da ake yi mata sun ma isheta dan jike kamar ta kurma ihu da gyaran jikin da ake yi mata.



Gimbiya Yakumbo yanzun bata da lokacin zama dan gyara Hakima take ciki da waje, dan tace idan kana da kyau to ka ƙara da wanka shiyasa ta ko ina gyara Hakima take dan yanzun Hakima ta dawo shashenta da zama baki ɗaya.


Daga can bangaren kuma Gimbiya Yakumbo tsaye take tana ba Hakima maganin kariya daga shirin shidanu sannan kuma tana ƙara janjamata ta riƙe Allah dan shine gatan ko wani bawa.



Shiri suke ba kama hannun yaro, cikin lokaci ƙalilan Hakima ta koma kamar balarabiya dan baka gane ta sai tayi magana, maganar ma idan tayi sai ka kyaleta sosai zaka gane Gimbiya Hakima ce saboda ta chanza baki ɗayan ta.


_____________________________


*×ZARIA×*

Itama Gimbiya Fulani Kubrah ba abarta a baya ba dan ta zage tayi ma Gimbiya Hakima lefe nagani da buɗe, duk da Maimartaba Sarki Abdulmatalak ya bada kuɗi amman itama ta ƙara da kuɗinta banda kuɗin da Hakim shima ya bada, dubai taje itadasu Maryama suka haɗo ma Gimbiya Hakima Lefa set 42 akayi mata banda gana most go guda shidda ba abunda ke cikinta sai bags da dai sauransu.


Bata damu da fidda hannu da su Gimbiya Zulaha suka yi ba, daman tasan haka zai faru shiyasa taita hidimar gabanta badamu da abunda suke ba, ta ba

Please Login or Register in order to submit comment