Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amman sai tayi tsaki tace ita ina ruwanta da kyaun da yayi bayan baida mutunci..


Haka Hakim ya gama yi masu lecture ya kama gabanshi dan ba ƙaramin kyau Hakima tayi mashi ba ko dan yau tasa hijab shiyasa yaga tafi kullun kyau haka ya kama tunaninshi har yana mamakin kanshi..



Haka rayuwa ta cigaba da tafiya wasa-wasa Hakima da Maryam sunyi kunsan wata ɗaya suna gaba, ba tare da sun fargaba dan yanzun sun shiga shirin fara exams hankalinsu baki daya ya koma wajen karatunsu...


*Wattpad JameelarhSadiq

*share
*Comment
*Vote
*please


👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

   *(Yar mutan kankia👸🏻)*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

*MAI HAKURI MAWA DACI WATARAN ZAI DAFA DUTSE, NA GA YANDA KUKA NUNA DAMUWA KUMA KUKA BANI HAKURI KUMA NA HAKURA KUMA ALLAH YASA KU GYARA KAMAR YANDA KUKA ƊAUKI ALKWARI☺️💯*

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

47&48

"Hakima sannu kinsha karatu kinga yanda kika koma."? 

"Momy ba dole ba wallahi karatun naija ba sauki shiyasa naso Baffah ya fidda ni turkey amman yaki yarda."

"Daughter ai zuwanki Zaria kin chanza sosai ba kamar da ba, tunda gashi yanzun bayinki suna samun sausauci."

"Uhmmm! Ni daman ko da Momy ba abunda nike yi masu kawai dai kuke ganin Ina matsa masu."

"To Daughter ki kara sabo dasu kinj."?

"Eh naji Momy, "Daughter yanzun har zaki shiga 300 level amman banji kin fara kula samari ba, komai yasa."?

"Haba Momy ai ni yarinya ce fa duka duka yanzun  nike da shekara sha tara fa, ni gaskiya ban isa aure ba."

"Aiko kice kika isa aure, ki fara kula samari in ba haka ba Maimartaba ya fidda maki da kanshi kinsan dai kina gama karatun nan aure zaiyi maki."

"Momy jibaini fa yarinya dani Baffah yayi man aure tun yanzun ina laifin na gama masters din sannan."

"Daughter waya gaya maki gidan sarauta ana karatu."?

"Momy amman.. "Da kata Hakima."

Yakumbo ta tsada Hakima cikin fushi dan ta lura Hakima batada ra'ayin kula samari kuma tana tsoran karda maimartaba yayi mata auren dole...

"Daughter gidan sarauta ba'a karatu sai dai mulki yanzun ne da zamani ya shigo mu masu sarauta muka dauki boko muka sama kanmu Amman mu da mulki aka sanmu."

"Kuma Ina laifin da ya barki kikayi degree, ki fidda master a zuciyarki kisa aure, Daughter ki fara kula samari kafin dare yayi maki shawarata kenan a matsayina na Wanda ta daukeki diya."

"To insha Allah Momy zan duba, ni zan wuce Momy na barki lafiya."

"To Daughter, kin gaida Fulani KO? "Aa yanzun zan wuce wajenta daman daga wajen Baffah na biyo wajenki sanann wajenta, "OK Daughter."

Haka Hakima ta dauke shashen Fulani tana tunani maganar da Yakumbo tayi mata ba kamar wannan maganar, "Daughter ki fara kula samari kafin dare yayi maki."

Haka Hakima ta Kama maimata wanann maganar har ta iso shashen Fulani, nan akayi mata iso ta shiga..

"Fulani ina wuni, "Lafiya Hakima ya karatun."?

"Lafiyalau Alhmdulh, "to Allah ya bada sa'a, "Amin ya Allah..."

"Na sa maiki Lafiya."?

"Lafiya lau, in kina bukata ki shirya gobe zamu adamawa bikin Yarima Bishir."?

"Ok daman Yaya Bishir aure zaiyi kenan? Shine babu ko gaiyata."

"Hakima taya Bishir zai gaiyaceki bikinshi bayan kin gujeshi? Wani irin sone Bishir baiyi maki ba."?

"Ai Fulani ni yarinyace ban isa aure ba shiyasa ban yarda da soyayyarshi ba."

"Ai sai ki ta zama Hakima har sai randa kika isa auren sai kiyi, shidai Bishir jibine aurenshi yar'sarkin Yobe zai aure Gimbiya Zaituna."

"Allah ya basu zaman Lafiya, "Amin ya Allah."

"Ni zan wuce nasa a fara shiryaman kayana kafin goben."

"To mu kwana lafiya, "Allah yasa Fulani."

Haka Hakima ta dawo shashenta tasa Azima ta shirya masu kayansu ita da su Inna Lantana..

_____________________________

"Kilishi kinga wannan maganin shi za'a sama Maimartaba cikin abinci yana ci ya gama aiki."

"Ar'riri nanaye, Gimbiya wannan abun yayi man dadi sosai bani shi nan naje na sama shi tunda yau nike dashi."

"Daga ganin Sarkin Fawa sai Miya tayi zaki."?

"Ai Gimbiya zafi-zafi a kan buga karfe ko."?

Hmmm! "Ai duk saurin unguwar zoma dan ubanta ta bari a haihu sanann tazo ta yanke cibi."

"To Gimbiya gayaman ya za'ayi."?

"Ajiye maganin zamuyi sai nan da shekara biyar sanann."

"Maiyasa kikace haka Gimbiya."?

"Eh Kilishi yanzun muka bashi magani yasha ya mutun kafin shekara biyar kinga dole aba Hakim mulki."

"Kin kawo shawara kuma mai kyau."

"Wallahi na tsani naga Hakim yayi mulki kona kwana daya ne, dan uwarshi za'a kirata da uwar'sarki, na tsani naji ana kiranta da wanna sunan."

Haka suka kama tautaunawa sannan kowa ya kama gabanshi..

______________________________

"Ranki ya daɗ'e angama shirya komai."

"Azima kin tabbata komai da komai kika shirya."?

"Eh duk abunda nasan zaki bukata na shirya shi kawai umirnin ki nike jira uwar marayu."

''Ok zaki iya tafiya ki fiddo naku kayan sai mu wuce shashen Gimbiya Fulani."?

"Godiya muke uwar marayu, yar'sarki jikar'sarki uwar sar... "Dakata haka mana Azima kinsan bansan wannan surutun naku na banza tashi kije Kiyi abunda na saki kafin ranki ya ɓaci yanzun."

Hakima ta faɗi cikin ɓacin rai dan ba abunda ta tsana duniya bai wuci kace mata uwar'sarki ba dan ita bata shirya aure ba dan yanzun balle har ta zama wata uwar'sarki..

Haka Azima ta tashi tana mamakin Hakima ta lura duk yanda kake da Gimbiya Hakima mudun kace mata uwar'sarki sai ta nemi wulakanta mutum ko waye shi nan Azima ta cigaba da fiddo kayan su amman tunanin na cikin zuciyarta bata tace, "oni Azima ko maiyasa Gimbiya Hakima batasan ace mata uwar'sarki."?

Batasan maganar ta fito fili ba sai ji tayi Ba'ba Bilkisu nacewa, "ai abunda yasa Gimbiya Hakima bata san kiranta da uwar'sarki saboda bata shirya yin aure ba yanzun."

"Sannan bata gaji da mulkamu ba san ranta yanda take bukata duk da yanzun Alhmdulh komai yayi sauki ba kamar da ba."

Hmmmm! "Aiko idai hakane gaskiya muna da aiki nida nike murna ta kusa gama karatunta sai aure amman ace mutun bai san aure."

"Azima kisa a ranki ki ko gidan aure tare zaki da Gimbiya Hakima sai dai kawai mu samu muna shiga jikinta sosai yanda zata ji kunyar wulakanta mu cikin mutune."

"To shikenan kawai ku taso mu tafi kunsan bata san jira, "aiko dai."

Nan suka tafi suka ida shirya ma Gimbiya Hakima
Sannan suka wuce shashen Gimbiya Fulani...

Bayan Gimbiya Fulani ta gama shiryawa suka dauki hanyar Adamawa...

Bayan sun isa Adamawa aka tarbaisu tarba ta girmamawa aka saukesu shashen Gimbiya Fulani dake cikin gidansu nan tayi yan-matancinta..

Bayan sun huta Suka dunguma sai shashen tsohon sarki  Maimartaba Sarki Kabir mahaifin Fulani Aisha..

Nan suka gaisheshi sannnan suka wuce shashen Maimartaba Sarki Al-Khamis shine sarki mai mulki yanzun yayan Fulani Aisha ne uwa ɗaya uba ɗaya ɗanshi ake yima biki Yarima Bishir..

Bayan sun gama gaisawa ta wuce shashen Gimbiya Mabaruka wato mahaifiyarta sai da suka gama gaisawa sannan ta wuce shashen kowa suka gaisa ta dawo shashenta..

Washe gari aka fara hidimar biki ba karamin kudin ake zubda wa ba haka aka kama al-adu kala-kala sune basu je suka kwanta ba sai dare..

Haka ma wan shekare aka ɗaura daga inda aka tsaya bayan angama kowa yaje ya kwanta..

Washe gari aka daura Auren Yarima Bishir da Gimbiya Balaraba yar'Sarkin Yobe..

Nan Gimbiya Hakima taje yi ma Yarima Bishir Allah yasa alkhari..

Tafiya take cikin natsuwa da kwanciyar sai kace wanda take jin tausayin kasa bata san takata, wani irin lafoyaiyen lace ne black a jikinta ba ƙaramin kyau yayi ma Hakima ba abun ka da farar fata sai kace itace amaryarma..

Tunda ta doso wajen Yarima Bishir ya kafeta da ido yana ainama kanshi duk rintsi sai ya mallaki Hakima da sunan matar aurenshi dan ba ƙaramin so yake yi ma ƙanwartashi ba..

Sai da ta iso wajenshi ta fara magana sannan ya dawo cikin haiyacinshi, dan ƙaramin bakinta yake kallo tana motsashi kamar anayi mata dole..

"Ina tayaka murna Yaya Bishir Allah ya baku zaman lafiya"..

"Hakima maiye aibuna a wajenki?  Maiyasa baki sona? Nifa ɗan'uwanki ne Hakima kuma ina masifar sonki da kaunarki"...

"Haba Yarima Bishir taya zakayi wannan maganar bayan abun ya wuce tuni gashi yau aka daura maka aure"..

"Dakata haka Hakima nayi alwari komai nawa zai ƙare sai dai ya ƙare wajen neman auren ki dole ki aureni Hakima ko kina so ko baki so"..

Ya faɗa cikin fushi da ɓacin rai ya barta tsaye da mamaki..

*Tota Team Hakim gafa Yarima Bishir nan ya sake dawowa anya wannan abun zai yuyu kuwa?*

'''"""""Nidai question nayi maku ina jiran answers🤷🏻‍♀️'''''''''''



_By jameelah Jameey ✍🏻_

*Share*
*Comment*
*Vote*
*Like*
*please*



👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

    *(Yar mutan kankia👸🏻)* 

  


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''



49&50



Tunda Yarima Bishir ya tafi Hakima batayi motsi ba tana mamakin yanda Bishir yake yi mata gadara har haka, "sai mu gani Bishir ni kuma bani sonka, baka isa ka sani dole ba."

Haka Hakima ta ce sanann ta wuto warta shashen su ta cigaba da hidimarta hankali kwance dan tasa a ranta ko kasheta za'ayi baza ta iya auren Yarima Bishir ba...

Haka suka gama shagalin bikinsu sanann suka dawo gida..

"Lantana anjima ki shirya zani wankin kai da gyaran jiki dan haka  a gaya ma masu shirya fita cikin gari."

"Angama uwar marayu, Allah ya kaimu anjimar lafiya."

"Amin sanann kice ma su A'bu kar suyi abincin dare dan yau shashen Fulani zanci abincin dare."

"To Allah ya taimaki Gimbiya Hakima komai kika ce haka za'ayi zan isar da saƙonki yanzun nan na barki lafiya."

"Ki turoman da Azima tazo yanzun ba sai anjima ba ina san ganinta."

"Angama uwargijiyata, na barki lafiya."

Nan Lantana ta tafi kai saƙon Gimbiya Hakima, ita kuma Gimbiya bayan ta fiyar Lantana kwanciya tayi tana waya da Maryam dan Maryam ta gaya mata gobe ake resuming school...

"Haba Maryam! Am tire wallahi ko,  wanann karatun ya fara fita raina sai mutun yana cikin hutu yana jindaɗinshi sai a wani koma school."

"Gaskiya ne Hakima dole kice haka tunda kina gida kina mulki, kuma mai ya rage tunda mun shiga 300 level saura one year fa."

"Haka mutane ke cewa saura one year, bakusan wata kalar kura ke cikin one year ɗin ba."

"Kuma kinsan karatun ba dadi sai dai hakuri kawai Hakima, "wallahi Maryam abun ba dadi sai addu'a nima this week zan dawo insha Allah."

"Allah ya kaimu lafiya, "Amin ya Allah byeee zana shirya zan tafi gyran kai da jiki."

"Ehyeeh! Gyaran kai da jiki kamar wata amarya, "wannan al'adata ne Maryam na saba gyaran jiki  duk mouth koda ina ƙauyenku."

"Kindai faɗi dan kiji dadi amman kinsan Zaria tafi ƙarfin a kirata da sunan ƙauye."

"Naji masu kishi, kowa kanshi ya sani byee."

Bayan ta gama waya da Maryam Azima ta shigo ta haɗa ma Gimbiya ruwan wanka.. 

"Ranki yadaɗ'e ga ruwan can yana jiran ki."

"Ok kisamu kaya mararsa nauyi ki fiddo man, dan naji ana zafi ba laifi."

"Angama uwargijiyata."

Nan Gimbiya ta shiga wanka Azima ta fiddo mata kaya, bayan ta fito Gimbiya ta shirya tayi kyau sosai sannan suka tafi gyaran jiki...

____________________________

"Kilishi nifa Ina lissafi saura shekara uku Hakim ya mutu."

Hahahhahhaha! "Haba Gimbiya ai nafiki lissafi dan har rubutawa nayi a litaffi, dan na gaji da ganin Hakim yana yawo bisa doran kasa."


"Na tsani Hakim, ban ƙaunar na bude ido naga Hakim yana numfashi baki yanda nike ji ba Kilishi."

"To ai hankalinki ya kwanta Gimbiya tunda Turmurturs yace shekara biyar nasan aikinshi ba wasa daga ganinshi."

"Tabbas ni zan cemaki aikin Turmurturs bana wasa bane, kawai musa ido muga ranar wasa-wasa ta kusa zuwa tunda har munyi shekara biyu da zuwa."

"Aiko kinga bayan ya mutu da kamar sati sai mu sama ubanshi maganin nan yasha kinga sai muce baƙin cikin matuwar Hakim yasa jininshi ya hau ya bishi tunda yana sonshi."

"Haka mana kinga ba mai sama mana alamar tambaya, hahahhaha! Wallahi Kilishi inacikin farin ciki na kusa zama uwar'sarki."

☺️☺️☺️☺️☺️ Niko nace GIMBIYA ZULAHA ko sakara tana ta dariya gaban makasarta bata sani ba, amman ita taba GIMBIYA KILISHI Amana, Allah ka tsaremu daga sharin zuciya😭😭😭..


Wani kallar kallo Gimbiya Kilishi tayi ma Gimbiya Zulaha da taji tace ta kusa zama uwar'sarki ji tayi kamar ta sheƙeta ta huta dan ita duniya ba wanda ta tsana kamar Gimbiya Zulaha itada ɗanta Yarima Hamad..

"Aiko dai munkusa zaman uwar'sarki nan da shekara uku masu zuwa."

"Daman Kilishi ni kaɗai nasan abunda zanyi ma Fulani Kubrah idan Hamad ya hau milki dan sai na wulakanta ta nasa Hamad yayi ma wanann yan-iskan yaran nata faɗe sanann mu koresu subar garin baki ɗaya nasan bata nisa zata mutu saboda bakin ciki."

"Kin kyauta ko Gimbiya ni zan wuce kinga dare yayi, "to mu kwana lafiya."

Bayan Gimbiya Kilishi ta fito shashen Gimbiya Zulaha ba inda ta wuce sai wajen Turmurturs..

Sai da suka gama sheƙe ayarsu sanann ta wuto gida, wanka kawai tayi ta kwanta bacci..

_________________________



Bayan Hakima sun dawo daga salon ta wuce shashen Fulani taci abincin dare sannan ta dawo ta kwanta...


Haka rayuwa  ta cigaba da tafiya dan yau Gimbiya Hakima take komawa school bayan ta gama shiryawa sukayi sallama dasu Gimbiya Yakumbo sannnan suka wuce school...

Bayan sun isa su Lantana suka gyara gida tas sannan suka haɗama Gimbiya ruwanka...

"Allah ya taimakeki ga ruwan wanka can yana jiranki."

"Bilkisu  Ki haɗoman Tea."

"Angama uwar marayu, amman asa sugar ko kar'asa."?

Wani kallar kallo Gimbiya Hakima tayi ma Bilkisu sannan ta wucewarta toilet, dan gani take raini ya fara shiga tsakaninta da Bilkisu...

Bilkisu take jikinta ya fara rawa tana mamakin yanda baki ɗaya Gimbiya Hakima ta chanza daga tambayar asa sugar, "oh ni Bilkisu mai hali dai baya chanza halinshi."

Abunda Bilkisu tace kenan sannan ta tashi taje ta haɗo ma Gimbiya Hakima Tea amman bata sa sugar ba sai dai ta ɗebo sugar ta shigo dashi baki ɗaya...

Bayan Gimbiya Hakima ta fito wanka Azima ta shafa mata mai ta tayata shiryawa sanann ta kalli Bilkisu tace, "idan kin tashi kijuyo buhun sugar kinji ni ko."?

"Ina neman sausaucin uwar marayu tuba nike bazan sake kallar wannan laifin ba."

Uhmmmm! Abunda tace kenan sannan ta anshi Tea ɗin tasa aka zuba mata sugar ta fara sha..

Kash! Itadai Gimbiya Hakima badai Mulki ba yanzun common imaging sugar ma baki sawa da hannunki sai anzuba maki🙄..


Tana shan Tea su Bilkisu nayi mata tausa ita kuma Azima tana karanta mata novel bayan ta gama shan Tea ta kwanta bacci sannan suma suka wuce suka kwanta..



_By Jameelah Jameey✍🏻_

*Share*
*Comment*
*Vote*
*Like*
*Please*



👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```





51&52







Washe gari bayan Gimbiya ta tashi daga bacci shiryawa tayi sannan ta fito yin breakfast..


Tafiya take kamar bata san taka kasa dan yau zata kaima bayin masarautar ziyara sannan ta wuce shashen wazari zata gano shi da jiki dan baiji daɗin jikinshi ba kwana biyu..



"Allah ya taimaki Gimbiya Hakima takawarki Lafiya yar'sarki jikar sarki gaba dai gaba dai Uwar Marayun kano baki ɗayanta."



"Lantana maza kije ki kiranta shugaban gidan horo inasan ganinshi yanzun kafin mu tafi ziyarar nan."



"Angama Uwargijiyata, muna neman sausaucin Uwar Marayu, na barki Lafiya."



"Bilkisu yi maza ki ɗauko kan wayata wanda nike waya da ita dan naga alamu baku fito da ita ba ko ni kuka bari na ɗauko maku wayar."?



"Allah ya ja da tsawancin kwana ina neman afuwar Gimbiya Hakima Uwar Marayu wallahi safa'a nayi nasa duka na ɗauko su."



"Ya isa haka Bilkisu ba abunda zanyi maki tashi kije ki ɗauko karki ɓatamana lokaci da wannna shurutun naki, kudai baki ɗayanku kun cika shurutun masifa wallahi haba."



Nan Bilkisu ta tashi ta ɗauko waya tana godema Allah da Gimbiya Hakima tace batayi mata komai dan ba ƙaramin tashi hankalinta yayi ba, dan taji ta aika a kira mata shugaban gidan horo baki ɗaya bama sarkin Bulala ba..




"Allah ya taimakeka, Gimbiya Hakima tace tana san ganinka yanzun -yanzun nan inma da hali mu taho tare ƙafata ƙafarka."



"Lantana Allah yasa ba wani abu kuka yi mata ba."?


"Ba abunda mukayi kawai dai tana san ganinka , amman ba abunda akayi mata."



"To shikenan, mu tafi daman bansan naji ance wata baiwa tayi laifi a shashen Gimbiya Hakima dan bansan naga a na hukunta mata dama maza lafiya lau."



"Aiko dai Allah ya ƙara mana hakurin zama da ita, "Amin ya Allah Lantana."


Nan suka tare da Lantana su tautaunawa yanda lokaci guda Gimbiya Hakima ta chanza halinta baki ɗaya bayan sun isa Lantana tayi mashi iso wajen Gimbiya Hakima sannan suka shigo tare..



"Allah ya taimakeki Allah ya ƙarama Gimbiya Hakima tsawon rai, gani na ansa kiranki cikin gaugawa ina jiran umirninki."




"Mudi kana jina."?


"Eh Uwar Marayu ina sauraranki."


"Duk wanda yake cikin gidan horo a sallameshi ya koma bakin aikinshi, na yafema kowa koda bani yayi ma laifi ba balle nasan duk wanda yake cikin gidan nace sillar Shigarshi ciki."




"Godiya suke Uwar Marayu yanzun nan zai zartar da umirninki, na barki Lafiya."



Nan Mudi ya tafi fiddo bayin dake kulle gidan horo, ita kuma Gimbiya Hakima ta tafi ziyara gidan bayi ba ƙaramin kyauta tayi ma bayi ba daga nan ta wuce gidan waziri ta duba jikinshi sannan ta wuto shashen ta..




Masauratar kano a ranar ba ƙaramin murna sukayi ba dan har sai da bayi suka haɗama Gimbiya Hakima walima gobe za'ayi ta..



"Uwar Marayu gobe insha Allah baki ɗaya bayin gidan nan suna gaiyatarki walima bakin ruwa, zamu nuna maki godiya da jindaɗin abunda kikayi a jiya."



"Bilkisu Allah ya kaimu goben, yanzun bacci zanyi sannan kuma ku fara shiryawa jibi zamu koma makaranta."



Washe gari bayan Gimbiya Hakima ta gama shiryawa direct shashen Gimbiya Yakumbo ta wuce kafin dare yayi taje walimar da bayi suka shirya mata..



"Momy kin tashi lafiya."?



"Lafiya lau Hakima ya koƙari?, "Alhmdulillah Momy, Momy gobe zan koma school fa."



"Ai ya dace a koma tunda ankusa gamawa insha Allah."


"Aiko dai Momy sauran Shekara ɗaya insha Allah, "Allah ya kaimu Hakima, "Amin Momy Yaya Annas shima da mukayi yawa yace next year ɗin nan zai dawo ya gama shima baki ɗaya."



"Eh kinga tare zaku gama keda shi, "Aa Momy shi harda masters yayi fa nikuma degree kinga ai da banbanci sosai."


"To Allah ya baku Nasara baki ɗayanku, "Amin ya Allah ni barki lafiya Momy zan biya na gaise da Fulani."


"To Daugter Allah yayi maki al'barka, "Amin Momy."


Bayan ta wuce shashen Gimbiya Fulani suka gaisa sosai, "Fulani zanyi missing ɗinki gobe ne zan koma school."


"Nima zanyi missing ɗinki Hakima, dan Allah ki kula da mutuncin kanki kiyi abunda ya kaiki wannan gari."



"Insha Allah zan kiyaya, "idan mu iyayenki bamu ganinki to Allahn da ya halliceki yana kallonki kuma duniya duk abunda ka suka shi zaka girba dan haka kiji tsoran Allah sannan ki guji abunda zai ɓatama iyayenki rai har ya sasu hawaye."



"Insha Allah Fulani, bayan Fulani ta gama yi ma Hakima wa'azi sanann ta fito ta wuce shashen ta, shiryawa tayu sannan suka wuce walima.



Ba ƙaramin dadi Gimbiya Hakima tayi dan bayi sunyi koƙari sosai wajen ganin sun faranta ma Gimbiya Hakima rai, kuma Alhmdulillah suma sunji dadi dan a fuskar kawai zasu gane Gimbiya Hakima taji dadin abunda suka yi mata dan sai murmurshi take, bayan anci ansha sanann kowa ya tafi makwancinshi..




Wanka kawai Gimbiya Hakima tayi sannan ta kwanta bacci, washe gari karfe biyun rana suka ɗauki hanyar Zaria..




*Oooooooo🥺wallahi nagaji sosai typing is no essay guy kuyi manage da wanannna pls inayinku ovver and over💃🏼❤️🖤💯*

*ANJIMA ZANYI MAKU WANI UPDATE INSHA ALLAH*

_By Jameelah Jameey✍🏻_




*Share*
*COMMENT*
*Vote*
*Like*
*Please*





👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```




53&54






"Boka Turmurturs na kawo kukana wajenka ina san ka shareman hawayena."



"Ina san haka, Gimbiya Kilishi ai ke ta daban ce wata matsala ce kuma ta kunno kai kuma."?


"Turmurturs kwana biyu maimartaba baya kulani ba kamar da ba shine nace anya ba shiga tsakaninmu akayi dashi ba."?


"Tabbas Gimbiya Kubrah ta shiga tsakanin ki da mai gidanki, dan haka idan muka cigaba da yin wanka lafiya lau kin fi karfin duk wani makirci."?



"Ni Kubrah zata haɗa da maimartaba shikenan Turmurturs kabarta tayi lokacine nan da shekara biyu sai Kubrah ta zama baiwata."



"Au to dan aiki yana nan yanda ya kamata dan Turmurturs yace ankusa gamawa da Hakim harda Hamad ɗin da kikace a kashe maki."



"Yauwa ina godiya Turmurturs."



Nan Turmurturs yayi mata wanka da abunda suka saba duk sati sanann ta wuce gida hankalinta kwance..


Bayan ta dawo gida wanka kawai tayi ta kwanta cikin farin ciki, dan gani take Humad ya gama Mulkin zaria, dan bata ɗauki shekara biyu wani abu ba tunda har tayi hakurin shekaru tana bin bokaye amman ba biyan bukata sai yanzun ta Zulaha ta haɗata da Turmurturs tasan bukatar ta tabiya, haka dai har bacci ya kwasheta..

_____________________________


Bayan Gimbiya Hakima sun iso gida, gyara gidan akayi sannan ta shirya ta wuce school dan suna da lecture three dan haka hutawa kawai tayi sannan ta wuce school..


"Hakima kinga yanda kika koma kamar wata sarauniya matar Sarki."


"Kinji ki wallahi Maryam kin cika surutu har wani abu na ƙara kenan? Ke bance kin ƙara wani abu ba sai ke."?


"Ai ni ba abunda na ƙara, amman ke baki ganki ba masha Allah kamar yar India, anya Hakima bakida dangi a Indiyawa ko kuma larabawa."?



"Ke dai akeji Maryam, wani lecturer ne zan ɗaukemu 300lvel wai."?


"Prof Hakim da Dr Moha sai wasu ni ban riƙe sunansu ba dan vistors lecturers ne."


"Ok Allah ya bamu sa'a, "Amin ya Allah result ya fito naga kece over'roll ma, gaskiya Hakima kinyi koƙari sosai Allah yasa ki gama da First class ɗinki."



"Kedai Allah ya bamu sa'a baki ɗayanmu ,"Amin ya Allah ga Dr Moha nan, "na ganshi daga shi sai gida kenan."?


"Eh ai last week Prof Hakim yayi attendance wai mune serious students tunda mun dawo kan lokaci, shine muka ce ai duk ku ba garin kuke ba shiyasa amman ya nuna I don't care a kan reason din da aka bashi."



Mtsssss"matsalarshi nasan saboda dani yayi attendance dan yaga ban dawo ba kuma bani da damuwa da wannan."



"Aa Hakima kije ki bashi hakuri, dan naji yace shine a matsayin first C. A din shi kinga dole kije office ki bashi hakuri dan mutane sai zuwa suke kuma yana yi masu favor kinga ai kema sai kije daman kamar kece karshen dawowa."



"Ba zuwan ba, wallahi wulakancin shine bani ɗauka kin sani kawai na hakura mun

Please Login or Register in order to submit comment