Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```





05&06



Wacece Gimbiya Hakima!!



Masarautar kano, Babbar masarautace wanda tana daya daga cikin masarautar da take babba a Nigeria..


Sarki Abdulsamad Abdulrazak shine mahaifin Sarki Abdulhadi Abdulsamad, sarki Abdulhadi Abdulsamad shine mahaifin Gimbiya Hakima Abdulhadi Abdulsamad...



Sarki Abdulhadi Abdulsamad adalin sarkine, yana mulki cikin Ilimi da adalci baya san yaga tallakawanshi cikin hukubar yunwa ko wani abu na wahalar rayuwa..


Wannan kyaukywan hali na sarki Abdulhadi Abdulsamad ya gajeshine a wajen mahaifin shi Sarki Abdulsamad Abdulrazak..



Mahaifin Abdulhadi su biyu ya haifa shida da kaninshi Yarima Annas, sun taso cikin kulawa ta sarauta, mahaifinsu ya koya masu yanda ake mulkin adalci ya tusa masu soyayyar tallakawa a cikin zuciyoyinsu..



Sunan Mahaifarsu Hakimatu, gimbiya Hakimatu ta ba yaranta da Allah ya bata guda biyu tarbiya iyakar bakin kokarinta, ta koya masu gwamawarar rayuwa ta bada gudun muwa wajen gani soyayya ta shiga tsakanin su da tallakawa domin ita macece mai tausayin na kasa da ita..


Abdulhadi yayi karatun addini dana boko, shida kanin shi Annas..

Annas yana final year yayi accident ya rasu, haka su Sarki Abdulhadi suka yi kukan rashin da sukayi suka barma Allah lamarinshi..


Mahaifiyarsu diyar sarkin katsina ce Gimbiya Hakimatu tana da faranfaran da mutane, ta zauna da sirikarta lafiya har mai rabawa tazo ta raba su..



Bayan Abdulhadi ya gama karatu ya auro yar'sarkin sukaja Gimbiya Yakumbo, Gimbiya Yakumbo Allah ya albarkace su da d'a daya Yarima Annas daga shi Allah bai sake ba Gimbiya Yakumbo haihuwa ba..



Bayan Sarki Abdulsamad yayi murabus ya maida mulki a hannun Yarima Abdulhadi da shekara hudu, sarki Abdulhadi ya auri yar'sarkin Adamawa Gimbiya Aisha ana kiranta da Gimbiya Fulani...


Gimbiya Fulani ita ta haifi Gimbiya Hakima Abdulhadi Abdulsamad..


Gimbiya Hakima ta taso cikin gata da kulawa a wajen Yakumbo, dan Gimbiya Hakima bata san Fulani ce mahaifiyarta ba sai da ta girma sanann ta san ita ce mahaifiyarta.


Fulani da Gimbiya Hakima ba wani shiri suke yi sosai ba, duk da mahaifiyarta ce, amman Fulani tace mundun bata chanza halinta ba, to basu taba zama inuwa daya.



Gimbiya Hakima ta tashi da wani kallar hali wanda ya girgiza iyayenta, domin Gimbiya Hakima bata san tallakawa ko kadan, tun tana yarinya indan su Inna Lantana suka dauke ta, to suna ajiyeta sai anyi mata wanka inba haka ba bata iya bacci a ranar..



Tun Yakumbo na ganin kamar Gimbiya Hakima tana da kyamane, sai daga baya ta lura baki daya Gimbiya Hakima bata san tallakawa ko kadan...



Sunyi mata fadi amman bataji saboda ita acewarta bai dace sun hundanya da tallakawa ba, domin su masu mulki da kudi ne, wannan shine dalilin da yasa Gimbiya Hakima bata san tallakawa ko kadan..


Bata jin komai ta wulakanta tallaka, ko waye duk tsufanshi kuma duk yarintarshi, haka suke ta hakuri da halin Gimbiya Hakima tun tana karama take haka har yanzun gashi ta girma ta mallaki hankalinta..



Gimbiya Hakima, tana bala'in san taje kasar turkey karatu, wannan yana daya daga cikin burinta na taje kasar turkey..


Tun da sarki Abdulhadi ya fahimci Gimbiya Hakima, tana san zuwa turkey karatu shi kuma yace indai tana san ya kai ta turkey to sai ta chanza hali domin baya san halinta baki daya..


Gimbiya Hakima, tayi iyakar kokarinta na ganin ta rake abunda take amman ta kasa, duk da a haka tayi sanyi sosai akan da..


Ba yanda batayi ba sarki ya fahimta shida Fulani ta chanza hali, amman sunce su dai basuga wani change ba, shiyasa Maimartaba Abdulhadi ya samar ma Gimbiya Hakima addimission a A. B. U zaria yanzun haka yasa ana yi mata registration jira yake ayi resume ya hada mata kayan ta ta wuce makaranta dan so yake ta san maiye rayuwa..


Shi kuma yarima Annas yanzun haka yana turkey karatu yana karata engineer..




Wannan kenan kunji wacece Gimbiya Hakima in Summary dan bani san mu bata time wajen bata labarin da gwara kawai muyi mai anfani.. 😎




Back to story πŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈ




"Lantana!

"Naam, Allah ya taimakeki Gimbiya Hakima uwar marayun masarautar Kano..


"Yau bani san fita parlour cin abincin rana, dan haka Ina san keda Bilkisu ku kwaso man abincin dasu ka dafa Yau a shigo man da shi ciki..


"To, angama yar'sarki jikar sarki, nan Inna Lantana ta tashi ta fita..


"Tashi bacci bai ganki ba, "na shiga uku ni Bilkisu wani abu muka sake yi ma Gimbiya Hakima, tunda naji ta kiraki hankali na yake a tashe?


"Kwantar da hankalinki, ba abunda mukayi sai dai yanzun muke san janyo ma kanmu bala'i, kin san dai Gimbiya Hakima bata san jira indan ta sa aiki, dan haka tashi mu shigar mata da abinci cikin uwar'daki, Yau bata san cin abincin a parlour sai cikin uwar'daki..


"Alhmdulh, wallahi Lantana har hankalina ya kwanta, bansan abunda zai hadani da Gimbiya Hakima dan ita bata gani tsufanka zata ci maka mutunci ba ruwanta...



"Yanzun zaki tashi mu kaimata ko har sai ta ne maimu? "To na tashi Allah ya fiddo mu lafiya, "Amin ya Allah Bilkisu..


Nan su Ba'ba Bilkisu suka kama kwasar abinci suna kaima Gimbiya Hakima a bedroom dinta sai da suka gama kai mata komai sanann suka zuba mata..



"Bilkisu! "Naam Allah ya taimakeki, "maza kije ki Kira man A'bu da Murya suzo ina bukatar ganinsu..


"Angama uwar marayu, Allah ya huci zuciyarki, nan Ba'ba Bilkisu ta wuce kiran su A'bu..


"Lantana! "Naam Gimbiya Allah ya da tsawancin kwana..


"Yau wa zai wanke wannan bayin?

"Allah ya taimakeki, ai mun wanke shi da kika tafi shashen su Gimbiya..


"A haka kuke nufin kun wanka bayin? "Muna neman Sausaucin Gimbiya Hakima mai farar Aniya..


"Tashi ki sake wanke shi, har sai nace ki barshi haka, "to Gimbiya angama, haka Lantana ta shiga toilet ta fara wanke shi, toilet din da sai ka kwanta kayi bacci cikinshi saboda wankuwa da yayi Amman Gimbiya Hakima tace bata ga wanki a nan baπŸ₯Ί..


"Sannunku! Madafa, "Aa Ba'ba Bilkisu kece da kanki da kafafunki, kice har yanzun Gimbiya Hakima bata fito waje ba?


"Waya gaya maku Murja? To Gimbiya Hakima ke san ganinku yanzun tace komai kuke ku ajiyeshi ku zo tana bukatar ganinku..



"Inalillahi wa'inna'alaihirajiun! Allah yasa dai lafiya Ba'ba Bilkisu Gimbiya Hakima ke neman mu?


"To nima wallahi ban sani ba A'bu kawai dai tace tana san ganinku, dan haka ni kunga tafiya sai kun iso...


"Tashi mu tafi Murja karda laifin ya kara nunkuwa, dan nasan Gimbiya Hakima bata kiran arziki, in dai Gimbiya Hakima ta kiraka to rashi mutunci da cin mutunci zata yi ma mutun..



"Hakane A'bu, Allah yasa dai Gimbiya Hakima ba wulakantamu zatayi kamar dazun da safe ba, kinga dai yanda taci mana zarafi gaban shashenta Yau din nan da safen nan..


Haka suka taho duk hankalinsu tashe, jiki duk a sanyaye dan sun san kiran Gimbiya Hakima ba alheri bane..

"Ranki ya dade, na isar da sakonki, ga sunan zuwa, "Bilkisu zo ki tausaman kafar naji ta ba yanda nike san ta..

"To Gimbiya, nan Ba'ba Bilkisu ta fara yin ma Gimbiya Hakima tausa..


Lantana sai wanke kewaye take, ta gaji sosai ga daman abunka da jikin tsufa, ga dukuwa ba dadi, ta wanke yafi sau goma sha hudu, amman Gimbiya Hakima tayi burus da ita, ta nuna bama ta san da ita cikin toilet din ba..


"Ranki ya dade, ga mutanan madafa nan sun iso, "je Bilkisu ki shigo da su, "to ranki yadade..


"Har kun iso Kenyan? "Wallahi ko Ba'ba Bilkisu mun iso, "to bissimilla ku shigo cikin, "har ciki zamu shiga? "Eh ko insha Allah, ku taho..



"Ranki ya dade gamu mun ansa kiranki cikin gaugaugawa..


"Bilkisu! "Naam Gimbiya Hakima, "sake zubo man sabon abinci ki kawo man..


"To Gimbiya, Nan ta sake zuba mata wani sabon abinci ta bata..


"Gashi Uwargijiyata, "ajiye shi nan, sake zubo wani, "to Yanzun ko Gimbiya, nan ta sake zuba mata wani sabon abinci, "gashi ranki yadade...



"Mika masu, "to angama Gimbiya yar'sarki jikar sarki, Nan ta mike masu abinci tana kallon ikon Allah..



"A'bu! Murja! "Naam ranki yadade, "kuci abincin nan yanzun gabana, "to..



Nan suka fara cin abinci, su dai basu ji abunda abincin yayi ba..

"Allah ya taimakeki munci, "ai na gani, ko kinga ana yi man jagora?


"Allah ya huci zuciyarki..

Nan itama Gimbiya Hakima ta fara cin abinci, tana ci ta ya mitse fuska ta furzar da abincin bakinta akan fuskar A'bu, sanann ji kake...


Tas!!! Ta wanke Murja da wani lafiyayen mari sannan ta fara magana.


"Ni zaku kashe?


"Ranki yadade muna neman agaji da Sausauci wajen Gimbiya Hakima uwar marayu.


"Bana maku bana san yaji yayi yawa a cikin abinci ba? Sannan kuma kun cika man mai cikin abinci, wato na mutu ko?


"Allah ya taimakeki, ai mu yau muka dawo madafa da girki, wallahi su Ladi basu gaya mana ba..


"Ku baku da hankalin da zakuyi aiki da kwakalwarku ehye? Maiyasa ku wasu kallar dabbobine ku baku aiki da hankali..



"Ayi hakuri ba zamu sake ba..

"Dallah can kuyi man shiru, wawayen banza wawayen wofi, ku tashi ku kwashi tsiyarku ku barman waje salan in kun tashi yin na dare ku juye buhun barkono a ciki..


"Tuba muke nema Gimbiya Hakima, godiya muke, nan suka kwashe kaya suka fita dasu waje...


"Lantana fito ya wanku, yanzun, "to godiya nike Gimbiya Hakima, uwar marayu da gajiyaryun Kano..


Nan Ba'ba Bilkisu ta kama yima Gimbiya Hakima tausa, ita kuma lnna Lantana ta na bata labari haka suka kama yi mata har bacci ya kwasheta sannan suka fita waje..


"Wai Lantana yau su A'bu sunga masifara Gimbiya Hakima, "kedai bari Bilkisu ai halin Gimbiya Hakima sai mu kawai zamu iya dashi, yanzun muje muci abincin da tace bata ci, "aiko dai..



"Sannunku Murja, Allah ya baku hakuri, "Hmm! Ai yau Ba'ba Bilkisu munsha wulakanci baki ji kumatuna ba yanda suke yi mani zafi ba..


"Hmm! Ai Murja ki gode ma Allah da hukuncinku ya tsaya iyakar nan, ni daga ta kirani sau uku tasa Sarkin bulala yayi man bulala hamsin da kaini gidan horo..


"Hakane fa Inna Lantana, Allah yakara bamu hakuri, ga abincinku can kuma kuci tunda ita tace bata ci mun cika barkono da mai...


Nan suka ci abinci suna labari, sai da mangarid sanann kowace ta koma bakin aikinta, su kuma su Lantana sune basu bar shashen Gimbiya Hakima ba har sai da tayi bacci sanann suka dawo shashensu na bayi...




_By jameelah jameey_ ✍🏻



Share and comment pls

πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»
*GIMBIYA HAKIMA*
πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈ

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_
_Jameelah jameey πŸ–‹_





*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```



07&08



"Ni wallahi Hakim kina bani mamaki, "mamaki name kenan Aliyu?


"Kai dai rayuwarka haka kake ba ruwanka kamar ba dan sarki ba.


"Hmmm Aliyu kenan to muye dan ina dan Sarki? Ai duk daya muke a wurin Allah banbancinmu shine wanda yafi bauta mashi..


"Hakane amman duk da haka maganar gaskiya kana bani mamaki ace dan sarki kamar kai dan Sarkin ma na Zaria amman kana rayuwa cikin tallakawa gaskiya ina mamaki ko ni da nike dan waziri ai bani kallar wannan sai dawowarka nike shiga cikin su...



"Kenan da baka shiga cikin tallakawa? "Gaskiya bani shiga ai sai su renani..


"Kaga niko ina shiga cikin tallakawana dan nasan mai suke bukata, sanann nasan maiye rayuwa, kasan ko saboda mai nake yin lectured a A. B. U?



"Aa nidai nayi mamaki ace kamar ka kake wani lectured a wata A. B. U, da daman ina san nayi maka maganar kawai fuskace ban gani ba...


"To na zabe yin lectured saboda nasan wani hali al'ummar kasar Zaria ke ciki, san nasan wani hali tallakawa ke ciki, mai suke bukata ayi masu, mai ake yi masu wanda basu jin dadinshi, sai kuma ina kara yin expressed akan halin mutane..



"Kaji dalili, Alhmdulh naji ance ankusa koma wa hutun Season kaga za'a kawo new inters student kuma ni zan dauki yan Chemistry..




"Gaskiya kaji dadi halinka yana bugerni, wanda bai san halinka ba sai yace baka da tausayi balle imani..


"Amman Hakim maiyasa baka dariya cikin tallakawa? Kuma kana san shiga cikin su dan kaga matsalarsu..


"Dan ina shiga cikin su shine zai sa nayi masu dariya ko sakin fuska sosai, ko ka manta nidain Yarima ne?



"ai naga tunda kana ma'amula dasu sosai ya dace ka zama mai sakin fuska garesu sosai..



"Hmmm! Ai ni kai kasani haka Allah ya hallicine ban cika magana ba, ko da ko ina gaban Gimbiya Fulani, dan haka ba laifina bane yin Allah ne..



Hmmmm! YARIMA HAKIM kenan, dan sarkin Zaria matashi maiji da samartaka ga kuma haiba da kyau da jinin sarauta dake yawo jikinshi..



Yarima Hakim, missikiline na ajin karshe dan bada kowa yake magana ba, inka ga maganar shi to shida mutun uku ne, daga Fulani mahaifiyarshi kenan sai kuma Maimartaba sannan abokinshi tun na yarinta Aliyu haidar, da wannan mutanan biyu suke ganin maganar shi mai tsawo, ko kannanshi Gimbiya Maryama da Gimbiya Sadiya basu ganin maganar shi balle dariyarshi abunda ke hadasu shine kawai su gaisa, ba wai wulakanci ke sashi haka ba Aa halinshi daga Allah ne wannan kenan....



________________________________



Washe gari tun da asuba Kuyangan Gimbiya Hakima suka fara aiki, kamar yanda ta bukata..


"Ladi, "Naam Larai..


"A gaskiya Ladi muna bautuwa a gidan nan, muna yi ma Gimbiya Hakima bauta amman bata gani, yanzun ji yanda muke ta wanann wahalar tun da asuba muke abu daya yanzun har bakwai tayi kuma tace kafin karfe takwas mun gama komai..


"To ya zamuyi Larai tunda munfito a bayi? Ai hakuri ya zama dolenmu, kuma ai daga wannan mopping din mugama sai mu jira fitowarta ta bamu umirnin mu tafiyarmu..


"Aiko dai Ladi, ai mu mungode Allah da ta fidda mu a madafa da Jiya mu zata wanka ma mari taci mana mutunci kamar yanda ta saba...


"Eh mana, da man su A'bu basu cika haduwa da itaba tunda gyaran gida kawai suke suna gamawa kuma inta gani zasu kama gabansu ba kamar muba dasu Inna Lantana da ba mu rabuwa sai dare, kinga ai munfisu shan wahalarta..


"Sosai ma, su daga Jiya kawai fa har sun fara koke-koke sun bani su ya zasuyi basu iyawa da aikin madafa, shine nace masu muma haka muka sha wuya har Allah yasa ta chanza mana aiki...


"Ku ina fatan kun gama ga maigirma Gimbiya Hakima nan fitowa, "mun gama yanzun muka gama, sai yanzun kenan Allah yayi zata fito yar-mulkin!


"Ke Larai ba ruwa, ki gyara kalamanki yanzun indan tajiki kiyi ya?

"Sai tasa a hukuntani, kuma hukunci na nawa ne bangani ba indai na Gimbiya Hakima ne..


"Nidai ba ruwana kunga tafiya wajen masu madafa naga har yanzun basu fara fito da abincin ba ga shi har Gimbiya Hakima ta tashi na niyar fitowa ma...



"To Ba'ba Bilkisu a dawo lafiya, "Allah yasa Ladi ni na barku lafiya..




"Ku yan madafa Ina fatan kungama dai ko?

"Eh mun gama yanzun muke shirin kai abincin wajen cin shi..


"To barkan ku, kutaso mu tafi kawo na taya ku dauka A'bu..


"To Ba'ba Bilkisu mungode, ni tunda dazun rabon da naga Inna Lantana, "kin san aikin Gimbiya Hakima ba karewa yake ba, tana can ta shafa mata mai..



"Allah sarki Inna Lantana, duk dai sannunmu da bauta, "yauwa kunga har mun iso, nan suka jera abinci a bisa dining table bayan duk kowace ta gama abunda take suka zauna zaman jiran fitowar Gimbiya Hakima...


Gimbiya Hakima itace bata fito ba sai karfe goma, bayan su kuma tun karfe takwas kowace ta gama aikinta...



"Takawarki lafiya yar'masu gida, Gimbiya Hakima uwar marayu, tar sarki jikar sarki..


"Bilkisu! "Naam Allah ya taimakeki Gimbiya Hakima anfito lafiya?


Gimbiya Hakima bata ansa ba sai da tayi kusan ten minutes sannan tace "Lau, Ina fatan kowa ya gama aikin shi?


"Eh Alhmdulh duk sungama umirnin Gimbiya kawai suke jira ta aiwatar a garesu..


Sai da ta mula tasha iska sannan ta tashi Bilkisu da Lantana suna biye da ita suka duba masu shara, sai dai suka gama zagaye sannan suka dawo ta zauna wajen abinci..


"Ace ma masu Shara su tafi su ban waje, "angama Uwargijiyata, nan Ba'ba Bilkisu ta fito main parlour inda suke tsugune tace..


"Ku su Larai, Gimbiya Hakima tace ku tashi ku tafi aikin ku yayi kyau, "godiya muke, nan suka tashi suka tafi suna Alhmdala cikin zuciyarsu sun rabu da Gimbiya Hakima lafiya ba tare da ta ci masu mutunci ba...


"Lantana! "Naam uwar marayu, "Uhmm, abunda Gimbiya Hakima tace kenan Amman har Inna Lantana ta gane abunda take nufi🧐


Wai ashe tace nufin ta tashi ta zuba abinci ta fara ba su A'bu suci sannan ta ci itama wai Gimbiya Hakima ba dai masifa ba😁


"Ranki yadade angama zubawa, kallonta kawai Gimbiya tayi, nan take Inna Lantana ta shiga taitayinta..



"Murja bissimilla ga abinci, "to Inna Lantana, nan suka ansa suka ci sai da kowace tayi three spoon sannan suka ajiye..


Sai dai Gimbiya Hakima ta mula tasha iska sannan ta yi ma Lantana nuni da hannu..


"Gashi ranki yadade, nan Gimbiya ta fara cin abinci cikin natsuwa da kwanciyar hankali, sai da tayi two spoon sannan tace, "ku tashi ku tafi ku bani waje, "godiya muke Gimbiya Hakima...


Bayan Gimbiya Hakima ta gama cin abinci ta aika sako wajen jakkadiya tana san yin magana da Maimartaba..


________________________

"Hakim! "Naam Ranki yadade, "nifa Hakim ina mamakin yanda ka makale sai kayi wannan koyawar a jami'a..


"Fulani ya kamata ace yanzun kinyi hakura da wanann maganar dan Allah ki saman albarka cikin lamarin..


"Shikenan naji Allah yayi albarka, "Amin Fulani godiya nike, ni zan wuce massalaci, "to adawo lafiya...



Nan ya fitowa shashen Gimbiya Fulani dogarawa suka goya mashi baya sunata yi mashi kirari nan suka shiga massalaci sukayi sallah bayan sun fito yaga sun kara biyo shi nan ya tsaya.


"Wai dan Allah bana ce maku kubar yi man wannan abun kamar wani abu..


"Allah yaja da ran Yarima dan sarki jikan sarki, ka hanamu binka cikin gari nan ma kana cewa mubar binka, ai wannan shine aikinmu kare lafiyar Yarima sarkin gaba..


"To naji, amman ai ni nace na hutar daku ko? "Eh ranka dade, "to dan haka ku wucewarku nagode.


Haka suka tafi suna mamakin saukin hali irin na Yarima Hakim shi dai bai damu da mulki ba..


"Wai Kilishi ya ina maki magana kinyi shuru, tunanin mai kike?


"Hmmm! Kedai bari Zulaha, ina tunanin yanda zamu kauda wanann dan iskan yaron kullun da abun nike Kwana muke tashi, duk hanyar da muka bi bata bulewa, kullun sai fi yaran mu yake..


"Wannan abun nima yana damuna Kilishi, ban ki na bude idona naga Hakim baya numfashi a doran kasa...


"Baki daya Yaro shida uwarshi kallon banza suke ma kowa cikin gida, wato dan sun samu boka wanda yafi namu aiki shiyasa, sun mallake gida kina ga Maimartaba baya jin maganar kowa cikin gidan nan sai ta uwarshi..


"Kuma muma mun haifa cikin gidan nan fa, kuma nice babba cikin gidan nan, dan kawai an rigani haihuwa sai a daukeni sakara cikin gida ko magana ta ba'atsayawa a saurara..



"Karki damu Gimbiya Zulaha zan san abun yi, dole YARIMA HAMID zai gaji mulkin Maimartaba ba YARIMA HAKIM ba, dan Yarima Hakim da wata hudu ya girma Yarima Hamid kinga ko ya zama dole mulki ya fito dakin matar farko ba ta biyu ba..



"Aiko dai Gimbiya Kilishi, shiyasa nike sonki, dan kina gane gaskiya..


Haka sukai ta tautaunawa yanda zasu samu su kawarda Yarima Hakim a duniya duk saboda mulki..


______________________________


"Ranki yadade Jakadiya ta aiko da sako, "mai tace Bilkisu?


"Cewa tayi Maimartaba yana san ganinki..


"To ace mata gani nan zuwa, "angama Uwargijiyata..


"Uwani kije kice tace gata nan zuwa, "to shikenan Lantana..


Nan Gimbiya Hakima ta shirya ta dauki hanyar shashen Maimartaba Sarki Abdulhadi..




_By jameelah Jameey πŸ–‹_




Share and comment pls

πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»
*GIMBIYA HAKIMA*
πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈ

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey πŸ–‹_

*(Yar mutan kankiaπŸ‘ΈπŸ»)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```



09&10



Nan Gimbiya Hakima ta shirya ta dauki hanyar shashen Maimartaba ita da kuyanganta...



Bayan sun iso Jakkaddiya tayi mata iso har gaban sarki..


"Ranka yadade Allah ya ja da tsawancin kwana, na barku lafiya, "Uhmmm, abunda yayi mata kenan Jakkaddiya ta kama gabanta, ta koma bakin aikinta..



"Baffah ina kwana, "lafiya Lau Mamana,"Baffah da man nazo ne akan maganar makaranta, "to inajinki Mamana, mai kike so ayi maki?



"Da man ina neman Sausaci wajen Sarki mai adalci akan hukuncin da ya yanke man na yin karatu nan kasar Nigeria..



"Kin gama Hakima, sai da gaban Gimbiya Hakima ya tashi da taji yau Maimartaba ya kira sunanta ba tare da yace Mamana ba..


"Eh Baffah na gama!

"To daga yau karna sake jin kin zoman da maganar baki san karatu nan kasar, ya zamai maki dole kiyi karatu a kasar Zaria, can nike bukatar kiyi karatu, ko kuma na maidoki nan Kano kiyi karatun..


"Allah ya huci zuciyarka, Amman, "ya isa haka Hakima kinsan bani magana biyu, dan haka ki shirya nan da kwana biyu zaki wuce makaranta dan naji da zamanki gidan masarautarnan kina shiga hakin bayin Allah..



"Godiya nike Baffah, Amman ina neman alfarma ta biyu, "Uhmmm ina jinki, "da man nace ayi man adalci, adalin sarki, kar a barni na zauna hostel..


"Da man ba hostel zaki zauna ba, na sa ankama maki gida, dan ba zaki zauna gidan Sarkin Zaria ba, ki zunda man mutunci kina wulakanta masu bayi...



"Dan haka ina mai maimaita maki Hakima nan da kwana biyu zaki tafi makaranta, kije kiyi karatu nasan tarbiyar da muka baki, tashi ki tafi Allah yayi maki albarka..


"Amin, godiya nike Baffah, ni na wuce..


Haka Gimbiya Hakima ta fito turakar Maimartaba ranta bace tana mamakin yanda Fulani da Maimartaba basu ansar uzurinta a rayuwa su dai sunfi bayin gidan nan akanta...

Tana cikin tafiya wata baiwa daga shashen bayi tafito bata bata lura da Gimbiya Hakima ba ta shafen mata gefen alkelba..



Tas! Tas!! Tas!!! "Ke wata kalar kidahuma ce da zaki taho kamar wani doki kike san bankadeni?



"Inalillahi! Ranki yadade kiman rai, wallahi banga tahowarku ba uwar marayu..


"Ke Azima, "Naam Allah ya taimakike, "maza kije ki kira man Sarkin bulala, "ke kuma in samaiki bakin shashena, "to Allah ya taimaki Gimbiya Hakima..


Haka wannan baiwar take gudu-gudu sauri-sauri, jiki na rawa haka ta isa shashen Gimbiya Hakima, ita ko Gimbiya Hakima tafiya take cikin kwaciyar hankali har dai tayi kusan awa sannan ta iso shashenta dayake da dan nisa tsakaninta da shashen su Maimartaba..


"Sarkin bulala, Gimbiya Hakima na bukatar ganinka, "To Allah sa dai lafiya? "To kawai za'ace kaima kasan indan Gimbiya Hakima tayi kiranka ai hukunci zata yanke kaima kasani, "to ai laifinkune, tunda kunsan halinta ba tausayine da ita balle imani, to dan mai zaku kama yi mata laifi, nidai indan ta ban umirni dole na bi, dan haka mu tafi...


"Allah ya ja da ran Gimbiya Hakima, gani na ansa kiranki, "sarkin bulala, ina san kayi ma

Please Login or Register in order to submit comment