Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

talk to you..



Haka Gimbiya Hakima ta tashi zata fita, yanda ta shigo cikin isa da takama, haka tazo fita ba ta yarda ta nuna taji haushi ba, tazo dai dai fita tace yace"lock at you, useless girl stupid kawai...



Wanna abun shi ya kara ba Gimbiya Hakima haushi na ta fito ta tsaya wani waje tana jiran fitowarshi dan sai ya gaya mata shi DAN GIDAN UBAN WAYE a cikin garin Zaria da zai ce mata useless, bayan duk korarta da yayi bai isheshi ba, ita shiyasa bata san harka cikin talakawa, dan talaka bai iya cin arziki ba dan ya samu yana lecturer shine yake san gaya mata maganar, "ina kamar ni GIMBIYA HAKIMA wani banzan talaka bai isa ya gaya man magana..


Haka Gimbiya Hakima ta kama magana tana jiran fitowar YARIMA HAKIM ta sauke mashi kwadon rashin mutunci🀣..


Muje zuwa my fan, Team Hakima kun dai ba Hakima shawara karta janyo maku August nidai babu ruwa na lol☺️😚.. .





_By Jameelah Jameey✍🏻_








Share and comments pls

πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»
*GIMBIYA HAKIMA*
πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈ

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey πŸ–‹_

*(Yar mutan kankiaπŸ‘ΈπŸ»)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```


15&16



Shi kuma Yarima Hakim, tunda ya kora Gimbiya Hakima waje, sai kowa ya kara shiga taitayinshi a class din, dan sun lura da alama baya daukar nonsense, dan haka sai ko wace mace mai shirin shigarmai rayuwa sai gwiwoyin su suka yi sanyi, Amman duk da haka wasu daga cikin su suna kan bakarsu..



Yana mamakin rashin tarbiya da kunya da Wannan yarinyar da ya kora, dan ga dunkan alamu yarinyar bata da kunya dan ya ga zahiri a cikin idanunta, aiko bamu shiryawa da ita, dan ko wacece ita ba zan dauke nonsense ba..



Haka Yarima Hakim yaita mamaki, sannnan ya cigaba da yi ma yan class darasi, bayan ya gama ya hada takardunshi ya fito yayi hanyar office din shi..



Tunda ya fito Gimbiya Hakima ke bin bayanshi, bai lura da ita ba dan shi har ya manta da ya kori wata yau a class din shi..


Yana bude office din shi ya shiga ya zauna, yana zama ko suit din shi bai cire ba, saboda anfara yin zafi shiyasa yake san ya rage suits din jikinshi..



Sai kawai ya ji an bankado door din office din shi, dagowar da zaiyi sai ya ga yarinyar da ya kora a class tana nuna shi da yatsa tana cewa..


"Kai dan gidan uban waye cikin garin zaria da zaka koreni a class har kana ceman useless?


Yarima Hakim tsayawa yayi kwallon Gimbiya Hakima yana mamakin furincinta, wai shi Hakim take mana question na shi dan gidan uban waye, cikin zafin nama Hakim yace.


"Indan baki barman office ba sai kinyi danasin shigowarki office din na, ke bama danasin shigowarki office dina ba, sai kinyi danasanin haihuwarki duniya, wawiya marar tarbiya..



"Kai harka isa kace man zanyi da na sani, ni Hakima ba wanda ya isa yace man zanyi da na sanin haihuwata duniya, balle Kai,ji baika dan Allah kamar wani almajiri, sannnan kaine baka da tarbiya ba dai ni ba..



Kafin Hakim ya tashi yayi ma Gimbiya Hakima wani abu, har tayi ficewarta, dan daman a tsorace take dashi tana kallon idonshi da ta shigo office din shi taji tsoranshi ya kamata, kawai dakewa tayi ta mayarmai da ansa, dan bata iya daukar bakin ciki ita daya kwara suyi two two, daga office din Hakim wata lecture din ta wuce, Allah ya sota lecturer din bai Kai da shigowa ba, ta samu waje ta zauna taci kunu.

(Gaskiya Gimbiya Hakima baki da sauki, ya kamata ki gyara fa, dan Yarima Hakim ba kyaleki zanyi ba! Nidai gaskiya na gaya maki nida yan Team HakimπŸ˜ŽπŸ™ƒ)..



"Hmm! Mai zanyi ma yarinyar nan naji dadi"


Yarima Hakim ya ke fadin haka yana ta zagaye cikin office din shi, dan tunda yake bai taba ganin wanda taci mashi mutunci ba kamar Hakima..



"Ni wanann yarinyar zata cema dan gidan uban waye cikin garin zaria, to ita waye ubanta? Ko waye ubanta cikin garin zaria sai na gyara mata zama, ta koyi yanda ake iya magana da mutunta na gaba da ita, dan na fahimci uwarta da manta da wannan aikin, tunda ta manta ni zan koya mata..


Haka Yarima Hakim ya gama tunanin wulakancin da zaiyi ma Gimbiya Hakima, sanann ya hada komai shin ya tafiyarshi gida..


Itako Gimbiya Hakima ranta tas, dan ta rama abunda Hakim yayi mata, shiyasa ta maida hankalinta wajen lecture din da akeyi..



Alhmdulh Gimbiya Hakima taba yan class din su mamaki, dan duk question din da malamin nan yayi Gimbiya tana daga farko wajen tashi ta bada amsa, Amman cikin isa da takama da kuma nuna mulki take bada amsa..



Ba yan class kawai ba harta malamin yana mamakin halin Gimbiya Hakima, dan ya lura yarinyar zatayi ji da kai sosai, sai dai inda ta burgeshi tana da ilimi dan ya ga alama ta san abunda takeyi..



Bayan ya fita wata tazo ta zauna kusa da Gimbiya Hakima, tace mata, "sannu fa, Gimbiya Hakima kallonta kawai tayi bata sake kallonta ba, sai da tayi kusan minti biyar sannan tace "Yauwa..



"Sunana Maryam Bello, Babana ne V. C din makarantar nan, sai da Gimbiya Hakima ta gama danna waya sannan ta juyo tace mata, "you are welcome, "thank You, kefa ya sunanki?



"Hakima Abdulhadi Abdulsamad,"wow nice name, kema yar nan zaria ce, "Aa kano, wani abu? "Aa bakomai kawai dai naga kinyi man shiyasa, ina san mu zama friend inba matsala...



Sai da Gimbiya Hakima ta gama yi ma Maryam kallon raini sannan tace, "ur wclme, "thank You Hakima..



Nan suka zauna ba wata magana sai ita Maryam take jan Hakima da labari, amsa daya ce take samu wajen Hakima daga Uhmm sai Aa.



Haka dai har sukayi exchange digits sannan suka yi Sallama, Maryam ta shiga motar ta, tana kallon yanda Bala drive yake budema Gimbiya Hakima mota, kamar zan duga mata da yanda take yi sai da tayi mamaki,amman ita dai Gimbiya Hakima tayi mata duk da taga ba halinsu daya ba, Amman zatayi hakurin zama da ita, har Allah yasa taga ta chanza mata hali, dan wannan ba hali bane mai kyau na wulakanta mutane..


Bayan Gimbiya Hakima sun koma gida wanka tayi sannan ta fito parlour ta zauna, su Lantana suka fara yi mata tausa(messaging), bayan sun gama ta ci abinci sannan suka fara bata labari...


_______________________________


"Sannu da hutawa, Ranki yadad'e, "yauwa Hakim, har andawo? "Eh Allah ya yarda, wallahi duk na gaji Fulani sosai...



"Ai dole ka gaji, tunda ka daukarma kanka aiki, "Fulani nidai kisa albarka, "ai Hakim kullun ita muke sawa..


"Yaya sannu da zuwa, "yauwa Maryama ina Sadiya take maiyasa bakuje school ba?


"Bamu da lectures yau sai gobe, "ok, Fulani ni zan wuce na gaida Maimartaba, "to adawo lafiya, ka dai ci abinci ko? "Eh naci, "karka kuskura kaci abincin gidan nan ina kara maimaita maka Hakim..



"To ina kokarin kiyaye wa Fulani, na barki lafiya..


Nan Yarima Hakim ya wuce Fada dan ya gaida Maimartaba yana cikin tafiya yaji an ingijeshi, waiga war da zaiyi sai yaga Yarima Hamad yana yi mashi wani kallo...



"Hamad ina wuni? "Ban ganshi ba, da ban wuni ba da ka ganni? "Uhmm, abunda Hakim yace ma Hamad kenan ya wuce ya barshi tsaye..


Aiko Hamad ya dunga masifa, dan ba haka yaso ba, ya so Hakim ya biye mashi..


Yarima Hakim zuwa fada, ya mike gaisawa wajen sarki, sannan fadawa suka mike mashi gaisuwa cikin mutuntawa, domin suna jin dadi huddarsu da sarkin nasu mai jiran gado..



"Gimbiya, wallahi raina ya baci, sai na kashe Hakim..


"Kai Hamad wai sai yaushe zaka gane kashe Hakim sai anbi a sannu, eye?



"Wani abi a sannu ni ki barni na dauke kanshi da wuka a gaban uban kowa..


"Kana san wahalar da mukayi a baya ta zama a banza? Ko kuma kana san na haukace?



"To Gimbiya ni na gaji da ganin Hakim cikin masarautarnan, wallahi na tsaneshi, yanzun haka yana fada fa..


"Duk da ka tsaneshi hakuri zakayi mu kasheshi a sannu,,dan idan ka kashe Hakim gaban mutane kai ma kashe ka za'ayi Hamad gaban kowa, kaga kenan mulki zai tashi daga hannunmu ya koma wajen Kilishi dan Humad kawai za'aba mulki, ina bani fatan ganin wannan bakar rana..



"Dan haka kabar komai a hannuna Hamad, wannan maganar ta zamu ta karshe tsakaninmu..


"To naji Gimbiya, ni na wuce, "ka biya shashen Kilishi ka gaidata, "to na barki lafiya..



Haka Yarima Hamad ya fito shashen Gimbiya Zulaha ranshi bace, dan yaso ta bashi goyan bayan kashe Hakim, Amman ya fidda hannu kamar yanda ta bukata shi dai yana jiran mulki...



Bayan ya gaida Gimbiya Kilishi ya wucewarshi hidimar gabanshi, dan su da sake ganinshi sai hali kuma..



"Ranki yadad'e Gimbiya Kilishi, Gimbiya Zulaha tana san magana da ke, tana bakin kofa, "Mariya je ki shigo da sakarai, "to angama Ranki yadad'e..


Nan Gimbiya Zulaha ta shigo bayan sun gama gaisawa su ka fara magana..


"Kin san mai ya kawo ni Kilishi? "Aa Gimbiya, "yauwa nazo nace maki ya aka tsaya wajen aikin Maimartaba tunda naga duk aikin da muke kanshi ba ta siri..



"Ai wannan aiki ne mai sauki, dan ban dauki kashe Maimartaba wani aiki ba..


"To shikenan, Amman duk da haka sai mun gyara shirin mu, "to Gimbiya insha Allah, "ni na wuce, sai sa safe..


To fa kunji wata sabuwa kuma, Ashe harda maimartaba ake shirin aikawa barzahu, Allah ya mare zuciyoyinmu daga aikata aikin da na sani ko wani kallar ne AminπŸ˜žπŸ™πŸ»




_By Jameelah Jameey✍🏻_





Share and comment pls

πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»
*GIMBIYA HAKIMA*
πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈ

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey πŸ–‹_

*(Yar mutan kankiaπŸ‘ΈπŸ»)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```



17&18




Yau karfe biyu Gimbiya Hakima take da lectures sai da su Lantana suka ji kamar su fasa ihu...



"Lantana baki da hankali? Wai dan Allah har sai yaushe zakiyi hankali?ke duk yanda aka nuna maki baki gane sai kace mai kwakwalwar kifi..



"Allah ya huci zuciyarki, wallahi akasi ne aka samu..


"Akasi! Akasi kikace Lantana, to yau zan nuna maki ni Hakima ban yarda da wannan kalma mai suna akashi ba..


"Allah ya taimakeki, Ina neman sausauci, insha Allah banzan sa..... Tas!! Kake ji Gimbiya Hakima ta wanke Lantana da Mari tana nuna ta da yatsa sannan ta fara cewa, "ke wata kallar kidahuma ce? Inba kina kidahuma ba daga goge riga saboda sakarci irin naki kinbi ki toya, ni dallah can tashi kibani waje tsohuwar banza...


"Godiya nike Allah yaja da tsawanci kwana uwar marayu, nan Inna Lantana taja yan kafafunta ta tafi, tana hawaye saboda tunda take da Gimbiya Hakima bata taba yi mata wani abu da taji haushi kalar wanna, dan ko ba sau daya ba ba sau biyu ba tasha Mari a wajen Gimbiya Hakima Amman yau taji haushin abun sosai..



"Azima, "Naam Allah ya taimakeki, "tashi ki sake goge man takalmin nan, dan nasan wacer mahaukaciyar hauka kawai tayi man..



"Angama ranki yadad'e, nan Azima ta sake goge ma Gimbiya Hakima takalmi, duk ba abunda takalmin yayi, Amman haka ta sake goge mata shi..



Gimbiya Hakima ba ta tashi tafiya makaranta ba sai karfe daya dai-dai gashi tana da dan nisa tsaka ninta da makaranta gashi lecture din karfe biyu gareta..


"Bala kayi sauri bansan na makara, "angama Gimbiya, haka Gimbiya haka ta kama azalzalar Bala yayi sauri, haka suka samu suka isa, karfe biyu saura suka yi parking a bakin depertiment dinsu..




Sauri sauri Gimbiya Hakima take saboda hango Yarima Hakim da tayi yana tafiya cikin natsuwa yana shirin shiga lecture..



Duk tasan yana ganinta hakan bai yana Gimbiya Hakima sauri ba, ita acewarta sauri take, Amman Yarima Hakim gani yake kamar bata san taka kasa, dan danan ranshi ya baci sosai Amman zai barta ta shiga dan shi kad'a yasan abunda zaiyi mata..


Gimbiya Hakima na shiga taje wajen Maryam ta zauna, gaisawa kawai suka yi Yarima Hakim ya shigo..



Kowa ya natsu ya maida hankalinshi waje Hakim, dan suna jin dadin koyawarshi, dan prof Hakim ba daga baya ba wajen iya lesson, dan haka shiyasa kowa ya kama kanshi ya naba'a dan ya samu abunda ya samu..



Baki daya hankalin Gimbiya Hakima yana kan lesson din da Hakim yake dan harga Allah taji dadin koyawarshi dan ba karamin ganewa take ba..



"Hey stand up yayi pointing din Gimbiya Hakima, Amman sai tayi kamar ba da ita yake ba, dan ta lura malamin nan yana da san raini ita kuma ba daukar raini zata yi ba...



"Ke! Ke wata kallar kidahuma ce? KO baki jin turanci? Babanki yayi asarar kudin registration, dallah can stand up idiot nonsense stupid girl..



Haka Gimbiya Hakima ta mike ji take kamar ta tsiga kasa ta nitse dan kunya, dan ba karamin kunya taji ba ta yanda taga kowa a ajin ita yake kallo kamar wanda tati sata...



Sai da Hakim yayi kusan minti ashirin sanan yayi time din Hakima...


Duk tayi laushi ta gaji, Amman ta daure dan bata san yan ajin suga gazawarta..


Questions masu wahala Hakim ya fara jefo ma Gimbiya Hakima, Amman ga mamakinshi yaga tana bashi amsa, sai kawai yayi mata wani question nan ta kasa bashi nan yace mata...


"Get out of my class, nan Hakima ta tashi ta wuce tazo dai dai fita Hakim yace meet me in my office, classrest ka anshin man matrix number dinta ka kawo man office dina.


"Ok sir, class captain yace, sannan ya cigaba da yi masu lecture, bayan ya gama ya Kama gabanshi..


Ita ko Gimbiya Hakima direct gida ta wuce ranta bace..


"Allah ya taimakeki, Allah yasa lafiya dan ban saba ganin uwargijiyata cikin s
Wannan yana yin ba?



"Azima so nike na san waye shi, waye ubanshi a cikin Nigeria, da har zai ci man mutunci a cikin mutane Azima?



"Tabbas ya tabka babban kuskure, dan bai san dawa yake magana ba shiyasa da baiyi maki abunda ya san ranki zai baci ba ranki ya dade....



"Kyale shi Azima, yanda yasa na zubda hawaye ta dalilin shi, shima sai na sashi zubda hawaye da idonshi, sai ya san ni GIMBIYA HAKIMA duk wanda yaci tuwo dani miya ya sha...



Haka dai su Lantana suka Kama fadanci sannan suka samu Gimbiya Hakima ta sauko daga dokin fushi, sannan suma hankalinshu ya kwanta haka har tayi bacci..


_________________________________



Hakim bayan ya koma gida wanka yayi yasa kayan shan iska ya tafi bayan gida domin shakatawa..


"Fulani,wai kinji abunda naji su Gimbiya Kilishi suna cewa, wai ko da bala'i sai sun kashe yaya Hakim...



"Laaa nima Maryama wallahi nima naje rannan suna maganar suna maganar randa na tafi shan iska ni daya banda ke Sadiya, har Mino tace man wancen satin har magani Lanto ta kawo asa mashi abinci, wai yana ci zai mutu, ke wani abunma bai faduwa makircin da asirin da suke yi ma yaya...



"Kunga duk kuyi man shuru da wannan surutun naku na banza, koma maiye mufi karfinsu da Ayar Allah dan haka ku cigaba da neman tsarin Allah ba na mutun ba..



"To shikenan Fulani Allah ya tsaremu, "Amin Maryama..



"Dan Allah Kilishi dubarshi sai kace wani sarki, wannan idan aka bashi sarki shida uwarshi banzaye zasu maidamu cikin gidan nan, tun yanzun yana wannan mulkin Ina ga ya zama sarkin..



"Kyaleshi Gimbiya lokaci kawai nike jira, wallahi indan har lokaci yayi Hakim jama'ar zaria baki daya mantawa zasuyi da anyi wani mutun Hakim, duk san da suke yi mashi ko, ke harta wanann munafukan yan biyun kannan nashi sai na shafe da babun su, balle uwar tasu...




"To wai yaushe wannan lokacin zaiyi Kilishi?


"Nan ba da dadewa ba, kedai kisa ido kiyi kallo, "shikenan Kilishi..



Nan suka gama meeting dinsu na kullun, sannan suka tafi..



Sudai su Gimbiya Kilishi basu da magana sai ta HakimπŸ’πŸ»β€β™€οΈ, laile ko suna da aiki wanann shi ake kira aikin burus inji tusaπŸ™…πŸ»β€β™€οΈ..



Sai da suka gama sannan suka tashi..


________________________


"Allah yaja da ran uwar marayu ga abinci nan yana jiranki...


Kallon Bilkisu kawai tayi, sai ta shiga toilet ta zubo ruwa a roba ta kawo mata ta wanke hannunta..


Hakan na nufin yau bata san zuw parlour yin dinner dan haka shiyasa ta wanke hannunta, bayan ta gama wanke hannu, suka hada kayan suka kawo mata..



Ana cikin zuba mata ta Azima taji tace, "tsaya! Azima waya ce ku dafa man kus-kus?


"Allah ya ja da ra'n Gimbiya Hakima ai ba kus-kus kawai muka dafa maki ba, harda macaroni, sannan kuma ga coffee nan duk munyi maki..



"Uhmmm!


Nan Azima ta zuba ma Gimbiya Hakima macaroni, nan suka zauna suna bata labari taci har ta gama ci, sanan suka kwashe kayan suka je suka wanke, sannan suka dawo Lantana da Bilkisu suna tausa, ita kuma Azima tana karanta mata novel har tayi bacci sannan suka wuce suma suka kwanta..




_By Jameelah Jameey✍🏻_




Share and comment pls


πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»
*GIMBIYA HAKIMA*
πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈ

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_


_Jameelah jameey πŸ–‹_


*(Yar mutan kankiaπŸ‘ΈπŸ»)*


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```



19&20



Washe gari bayan Lantana ta gama shiryawa Hakima littafan ta, saboda karatun da Gimbiyar ta fara na dare dan cikin week din nan zasu fara tests din su dan haka shiyasa ta fara karatun ta..




"Lantana! "Allah ya taimakeki gani gabanki ina jiran umirninki..


"Maza kije kice ma Bala, ya fiddo mota yanzun dan ayi fixing din lecture yanzun nan, dan haka yayi maza ya fiddo mota, gani nan fitowa...



"Allah ya kara maki jaraja angama, "Amin, nan Lantana ta tafi wajen Bala...



"Malam Bala, ka tashi lafiya? "Lafiya lau Lantana, ya aiki? ''Aiki da godiya, "To Allah ya bamu ladar, "amin..



"Sako daga Gimbiya Hakima, "mai kuma nayi Lantana?

"Kwantar da hankalinka, ba abunda kayi, "Alhmdulh, kin san wallahi Lantana ban san abunda zai hadani da Gimbiya Hakima da girmanka da mutuncinka, amman Gimbiya Hakima sai ta taci maka mutunci cikin mutane..



"Hakane gaskiya, Allah ya kara tsaremu daga cin mutuncin ta, "Amin Lantana, mai ita Gimbiya Hakima tace maki?



"Cewa tayi ka fiddo mota yanzun dan an maido masu da koyarwa yanzun da safen nan, shine tace ki fiddo mota ga tanan fitowa..



"To shikenan, ai yanzun kuwa zan fiddo ta, "ni na wuce Bala na barma lafiya..



Nan Lantana taje tagayama Gimbiya Hakima an fiddo mota..


"To ni zan wuce Bilkisu yau ki san kuyi man dambun masara, ku samu zagole kusa a cikin dan yau da bakuwa zamu dawo kuma tana san dambu...



"Angama uwargijiyarmu, Allah yabada sa'a, "Uhmmm, sannan ta gama gaban tana saurin dan yanzun seven thirty tayi gashi lecture din eight yayi fixed dinta, bayan basu da wata lecture sai two amman dan mugunta ya maidota eight...



"Bala kayi sauri, ban san na makara ka sani, dan haka kasan yanda zakayi kafin eight na ganin acikin lecture hall..


"To Gimbiya uwar marayu, Gimbiya diyar sarki uwar sarki insha Allah..


Nan Bala ya kama bankama mota wuta, Gimbiya Hakima sai da taji tsoron kalar gudun da Bala yake da ita cikin mota, to amman bata da choice din hana shi, dan idan sukayi wasa kan titin to zatayi late ne, kuma bata san wani abu yake hadata da Yarima Hakim, shiyasa tayi hakuri tana ganin rayuwa a iska.. (Lol sun Gimbiya Hakima ashe dai ana tsoro, kike iskanciπŸ™ƒ)



Cikin ikon Allah, karfe eight dai dai tayi ma Gimbiya Hakima cikin makaranta tana hango Yarima Hakim shima lokacin ya fito office din shi, dan haka tayi sauri ta shige warta ta zauna nan Maryam itama lokacin ta shigo ta zauna kusa da kawarta...



"Morning class,"Morning sir, "ok class listings attention, keep quite everbody, and get of a sit and sitdown pls, I said all of you keep quite...


Yarima Hakim ya fada cikin fada, sakamokon hango Hakima da Maryam da yayi suna ta surutu hankalinsu kwace..


Ba su san da shigowarshi ba sai da suka ji yayi tsawa sannan suka juyo lokaci guda, nan take Gimbiya Hakima taji bata dadi ba, dan tasan yanzun zai wulakantasu..


"Maryam, wannana idiot din kin san yanzun zai fidda mu waje, baki ga irin kallon da yake mana ba? Ta fada ma Maryam a hankali dan bata yarda lips dinta suka matsaba ma ba, balle yace tayi laifi dan Hakima tana san chemistry bata san ta ringa losing din lecture din shi, gashi ya iya koyarwa tana gane wa sosai..



"Mu boni Hakima gashi nan ya taho, "Uhmmm, abinda tace ma Maryam kenan, Ni kuwa nace yan mulkin sun taso kenan tun kan ya isoπŸ₯Ί.


"Hey you again? And you also? Kin biye ma wanann yarinyar zaki fara wasa da karatunki ko? Yace ma Maryam daya ke ba anan ba ya santa, ya santa kawarsu Gimbiya Maryama ce..



"Yaya Hakim dan Allah kayi hakuri, wallahi bamuji shigowarka ba..


"Saboda an koya maki jikkanci shiyasa baki shigowata ba, ita dai Hakima inda suke bata kalla ba dai da tana jin cin kashin da Hakim yake yi mata cikin class kowa na jinsu amman bata kyalesu har ya fidda Maryam waje sai ji tayi yace, "lock at you, stupid girl kawai, kina jiran nace maki get out ne? Oyaaa get out of my class idiot..



Gimbiya Hakima tsayawa tayi kallonshi, tana mamakin yanda yake san wulakanta ta cikin mutane, amman daga yau ba zai sake ba tace cikin zuciyarta, ta hada bag dinta ta fita ta baimar class dinshi, ga shi harda Maryam yau ya kora balle tayi mata tutorials din abinda ya kowa ya...



Bayan ya yi waje dasu Hakima ya cigaba da lecture din shi hankali kwance, dan shi ma kanshi yana mamakin yanda ya tsani yarinyar ce sosai, tunda yake bai taba tsanar wani mutun ba kamar ta, dan baya santa baya kaunarta ya tsaneta sosai...



"Hakima kin fito kenan? "Eh Maryam ba dole ba na fito, wallahi na tsani Hakim bani kaunar mai kaunarshi, ya gode ma Allah ni dalibarshi ce, shiyasa nike jure duk wani wulakancinshi amman wallahi Maryam banda na yau sai na rama..



"Haba Hakima sau nawa zan gaya maki mai hakuri yana da riba? Kuma malaminkine duk kowa yasan yana wulakantaki amman hakuri zaki yi tunda keke nema wajenshi kinga dole mu ringa hakuri da malamanmu komai ko suka yi mana..



"Maryam kinga ina sauraran wa'azinki ko? "Eh gaskiya kuma ina jin dadin ka, "to dan haka tashi mu tafi samu abunda zamuci dan ni ko breakfast banyi ba na fito..



"Ok mu tafi nadai naci cake cikin mota, kafin na iso, "ai ni banyi wanna hausar ba ai da nasa

Please Login or Register in order to submit comment