Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya haɗa ta cikin yaranshi, dan zumincin su ya ƙara ƙarko.



"Alhmdulillahi Wannan magana tayi daɗin ji sosai, ai Abokina ba sai ya nemi aure ba ni Abdulhadi Abdulsalam na ba ɗ'ana Hakim auren Hakima kawai yazo suga junansu sanann a ɗaura tunda daman ta gama karatunta."



"Aiko naji daɗin wannan kyautar da kayi mana ina godiya Abokina."


Nan suka gama maganarsu sannan suka fito, shi kuma Hamad yana can yana san magana da Gimbiya Hakima amman bai ga fuska ba, yana cikin haka sarki Abdulmatalak yace su wuto su wuce gida, haka suka ɗauki hanyar Zaria ba dan ya so ba.








*Wata sabuwa inji an ca_ca Sarki Abdulmatalak ya nema ma Hakim auren Hakima ba tare da sanin Hakim ba😱*



*Sarki Abdulhadi ya Amince da magana har ya bada ba tare da sanin Hakima ba😱*



*Yarima Hamad ya faɗa kogin son Gimbiya Hakima ba tare da shirya ba😱*




_Wai Allah wannna shine ɗaurin goron😝, kudai ku cigaba da biyoni_


*Shin Gimbiya Hakim zata amince da auren Yarima Hakim kuwa?*


*Yarima Hakim zai Amince da Auren Gimbiya Hakima shima?*




*Yarima Hamad zaiyi hakuri da soyayyar da yake yi ma Gimbiya Hakima ya barma Yarima Hakim tunda shi ance na bashi?*



*su Gimbiya Zulaha zasu yarda Hakim yayi aure nan, kuma zasu hakura da shekara biyar ta ida cika suka aikin boka Turmurturs yana yi?*




_Turkashi wanann ansoshin duk suna nan gaba cikin wannan labari mai albarka na Gimbiya Hakima ku cigaba da biyo kawai_



*#JameelarhSadiq*

#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```




61&62





Bayan tafiyar Sarki Abdulmatalak, Sarki Abdulhadi ya haɗa Gimbiya Fulani da Gimbiya Yakumbo cikin daren nan yace yana san yayi magana da su.


Bayan sun zauna suna jiran jin maganar da Maigidan nasu zai yi su cikin daren nan, bayan bai taɓa yi masu kallar wannan neman na gaugawa ba.




"Yakumbo! Fulani."

"Allah ya taimakeka, Allah ya sa lafiya dai? Dan tunda nike dakai baka taɓa taramu cikin dare ba, koda zaka auri Fulani ba cikin dare kayi man maganar auren ta ba."



"Yakumbo lafiya lau, wanann abun a faɗi ne da zafin-zafinshi ba sai ya huce ba shiyasa na tare ku."



"To Alhmdulh yanzun hankalina ya kwanta, muna sauraranka Mijinmu."




"Da man maganar Hakima ce."


"Hakima kuma Maimartaba sarki Abdulhadi."?


"Eh Yakumbo Hakima Allah yayi na fidda ma Gimbiya Hakima miji."?



"Miji? Hakima ka fidda ma Miji."?


"Eh miji, ya naga kamar hankalinki ya tashi wani abu? Ko tana da wanda take so."?



"Aa ko ɗaya, kawai ina mamakin Hakima da miji, naga duka duka yaushe ta gama karatun har kuma an fara maganar aure."



"Karki damu, daman ai nasha tambayarki nace Daughter ɗinki tanada wanda takw so kice babu, to ni Abdulhadi Abdulsalam na baka Yarima Hakim Abdulmatalak auren Gimbiya Hakima ko bayan raina ban yarda a ɗaura ma Hakima ko wa ba inba Hakim ba."



"Ai ba matsala naji dadi da Hakim ka ba auren Hakima, dan nasan Gimbiya Kubrah zata kula da Hakima sosai."




"To kunji abunda zan gaya maku, in Allah ya kaimu gobe ina san sake ganinku baki ɗaya harda su yaran, dan inasan gaya ma Hakima wannan albishir ɗin."



"To Allah ya kaimu goben lafiya."


Nan Gimbiya Fulani ta fito tana murna dan taji dadin haɗin da mijin nata zaiyi ma ɗiyar tata, nan ta bar Gimbiya Yakumbo dan ita take da kwana a turakar mai Maimartaba.

____________________________


*×ZARIA×*



Bayan Sarki Abdulmatalak ya huta yake tara duka iyalanshi taron gaugawa a babban parlournshi.



Sai da kowa ya zauna sannan ya fara magana, "dalilin da yasa na tara ku ba komai bane ila maganar auren Hakim."



Ba su Gimbiya Zulaha ba, harda shi kanshi Hakim ɗin sai da hantar cikinshi ta motsa dan baiyi tunanin wanann ranar tana gan da zuwa ba, kawai kallon Maimartaba yake shi ba a mutun kuma ba mataitace ba.



''Aure kuma? Auren ma na Hakim ba na Hamad ba."?


"Haka kikaji nace Zulaha auren Hakim,na nema ma Hakim auren yar'sarkin Kano dan haka kai Hakim Umirni na baka ba shawara ba kaje ku gana da junanku."


Zubewa Hakim yayi yana kwasher godiya wajen mahaifin nashi, "godiya nike Abba Allah ya ƙara tsawancin kwana bani da zaɓi da ya wuce zaɓin iyayena, nasan kun fini sani abunda ya dace dani."



"Allah yayi maka albarka, daman abunda yasa na taraku kenan sai Ku tashi Allah ya yi maku albarka baki ɗayanku."



Haka suka fito ko wane da abunda yake cikin ranshi kallon kallon kawai ake yi ma juna.


Bayan su Yarima Hamad sun shiga shashen Gimbiya Zulaha ya fara magana, "Gimbiya wallahi mudun Abba ya ɗaura ma Hakim Gimbiya Hakima wallahi sai na kashe Hakim dan dani Hakima ta dace ba Hakim, dan akan Hakima ina iya kashe ko waye koda shi Abban ne wallahi."




"Wacece Hakima kuma?, "Gimbiya Hakima itace yarinyar da mukaje walimar gama karatun su ita da Yayanta Yarima Annas, Gimbiya inason Hakima ina kaunar Hakima akan Son Hakima zan iya kashe waye wallahi."



"Baka da hankali Hamad? Bani san kana faɗin wannan kalmar ta kashe mutun kai tsaye haba Hamad ka bari nayi tunani mana."



"Har sai yaushe zakiyi Tunani? bayan kin san Abba yace Hakim ya shirya yaje su ga juna, kuma Abba magana ɗaya yake baya chanzawa."



"Ba dai kana san Gimbiya Hakima ba."?

"Eh inasan Hakima, Gimbiya ki taimakeni wallahi Hakima ce rayuwata mudun ban samu hakima ba zan iya kashe kai na ko kuma a waye gari ki tadda gawata ciwon son Hakima yayi ajalina."



"Yau ɗin nan zani wajen Turmurturs ba sai gobe ba Hamad, dole ka auri Gimbiya Hakima ko ta wani hali ne nayi maka wanan alkwarin."



"Nagode Gimbiya, shiyasa nike sanki mahaifiya mai share hawayen ɗanta."


"Tafiyarka Hamad Gobe zani nemaika kaji yanda mukayi da Turmurturs , "na barki lafiya Gimbiya."


Haka Hamad ya tafi ya bar Gimbiya da tunani dan bata shirya rashin Hamad ba dan haka sai dai inda karfinta ya ƙare.



"Mariya ba zan bari ayi wannan aika-aikar ba, taya zan bari Hakim yayi aure muda muke san kasheshi."



"Uwargiyata, Gimbiya Kilishi mai zai hana mu koma ma boka Dashshe nasan ba'a rasa yanda za'ayi ba."



"Aa Mariya, bari kiga ba tafi wajen Gimbiya Zulaha mun san yanda za'ayi, "To adawo lafiya ranki ya daɗ'e."



Nan Gimbiya Kilishi ta tafi shashen Gimbiya Zulaha hankali tashe dan batada wata mafita hankalinta ya fita jikinta bayan ta shiga dan yau ko iso bata aika nema ba wajen Gimbiya Zulaha ba sai dai kawai Gimbiya Zulaha taga Gimbiya Kilishi tsaye gabanta.



"Kilishi kenan daman nasan zaki zo shiyasa ban zo ba ni."

"Ba dole ba Gimbiya, kinji abunda wannan sakaran mijin namu yace wai aure zai yi ma Hakim mu da muke jiran ganin gawa nan da shekara biyu, salan ya ƙara aza mana wani aikin a kanmu."



''Hmmmm! Ni bansan ya zanyi ba, kuma yarinyar Hamad yace yana sonta amman san zuciya yasa akace Hakim zai aure ta."


Sai da Gimbiya Kilishi taji kamar fitsari zai kunce mata a wando dan batayi tunanin Hamad zaiyi yana san yarinyar ba , amman ita tasan yanda zatayi.



"Tashi mu tafi wajen Turmurturs ko ya share mana hawayenmu, dan nima abunda naso nace kenan ai Hamad shi ya dace ayi ma aure ba Hakim."



"Aiko dai amman ai mu ba'asan mu sai su an so ko?, "rabu dasu mudai mu tafi."



Haka suka ɗauki hanyar zuwa wajen Turmurturs dan ya share masu hawaye a cewarsu ba😰.




Bayan sun je wajen Turmurturs nan Gimbiya Zulaha ta fara bayani.


"Turmurturs ina san ka share mana hawayenmu, kamar yanda ka saba, wata sabuwa wai Abdulmatalak zaiyi ma Hakim auren da yar'sarkin kano."


"Hahhhha! Daman inasane da zuwan ku, ku dakata kuji aure ba fashi sai anyi shi sai dai ansa wata mafita bayan auren nasu, kuma Hamad hakuri zai yi ta aure Hakim har bayan mutuwar Hakim sai ya maida auren Hakima kanshi."



"Turmurturs. "Da kata Gimbiya Zulaha haka abun yake kuma haka zakuyi aure ya zama dole sai dai bayan bikin Turmurturs ya san yanda zaiyi ya hana Hakima ɗaukar cikin Hakim, amman duk wanda ta matsa tace sai ta hana bikin nan to nidai ba ruwana."



Haka suka ajiye mashi kudi suka taho biki sake, bayan sun koma gida Gimbiya Kilishi ta fara magana, "Gimbiya shawarar Turmurturs kawai za mu bi, indai zai hana Hakima haihuwa da Hakim lafiya lau suyi aurensu nan da shekara biyu sai shi Hamad ɗin ya auri Hakima kinga sai ta cigaba da haihuwarta."



"To nima abunda na gani kenan, dan haka zanyi ma Hamad bayani yanda hankalinshi zai kwanta, "yauwa ni na barki lafiya."



Bayan Gimbiya Kilishi ta koma shashen ta ta buga ma boka Turmurturs waya take ce mashi ya san yanda ya hanaa Hakima ɗaukar ciki yanda koda Hakim da Hamad sun mutu sai a ɗaura ma Humad Hakima.



Kunji wata sabuwa kuma my Fans, Allah yasa mufi ƙarfin zuciyarmu Amin🤝🏻



*#JameelarhSadiq*
#Share
#Comment
#Like
#Vote
#Please




👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```




63&64


*×KANO×*




Washe gari Gimbiya Hakima ta ɗauki hanyar shashen Maimartaba itada su Lantana suna take mata baya suna labari dan yanzun Gimbiya Hakima ta yarda da maganar Fulani da tace mata inma bata fiddo Lantana ba matsalarta, ta yarda da wanann maganar dan yanzun bata san abunda zai ɓatama su Lantana rai saboda suma basu san suga ɓacin ranta.



A bakin shashen Maimartaba suka haɗo da Yarima Annas na suka shiga tare su kuma Lantana suka tsaya suna gaisawa da dogarawan Annas.



"Yaya Annas wai neman mai Baffah yake yi mana."?


"Hakima nima ban sani ba, amman may be maganar Aure zai yi mana da man wannan ranar tana nan zuwa tunda mun gama karatu."



"Maganar Auren kuma Yaya Annas."?


"Eh, amman ai ce maki nayi may be ko."?


"Wai har naji hankalina ya kwanta, insha Allah ba maganar auren zai yi mana ba dan miko ban shirya aure yanzun ba."


"Allah ko Hakima."?

"Sosai ma Yaya Annas, "Ok Hakima Allah ya bamu sa'a dai, "Amin ya Allah Yayana."



Haka suka shiga parlourn Maimartaba amman Annas yana mamakin yanda Hakima take furta bata shirya aure yanzun ba bayan tasan Maimartaba ba ƙyaleta zaiyi ba, ko shi Maimartaba ya ƙyaleta to shi ba zai ƙyaleta ba haka suka shiga suka samu waje a kasa suka zauna shi kuma Maimartaba shida su Yakumbo suna bisa three siter suna kallon yaran nasu yanda suka haɗa kansu hakan yana yi masu dadi, bayan sun gama gaidasu sannan Maimartaba ya fara magana.



"Mamana."


Sai da gaban Gimbiya Hakima ya tashi da taji da sunan ta Baffah ya fara kira bana Yarima Annas ba, kasa magana tayi sai dai ɗago kanta da tayi tana kallon Baffah jira take kawai taji abunda zai gaya mata, koda Maimartaba ya fahimci sarautar har ta hau kanta ba ansawa zatayi ba amman hankalinta baki ɗaya yana wajen shi sai ya cigaba da maganar shi.



"Hakima na fidda maki mijin aure nan da kwana biyu zai zo kuga juna sai ayi biki ɗan sarkin Zaria ne."


"Nagode Baffah, Allah ya saka da Alkhari, nasan ba zaka zaɓe man abunda zai cutar dani kuma ya zama dole na bi Umirninka dan kaine mahaifina kafi kowa iko da ni, ina godiya Baffah Allah ya ƙara girma da ɗaukaka."



"Allah yayi maki albarka Mamana,nasan bazakiyi kuka ba akan zaɓin da nayi maki Allah ya baku zaman lafiya ya baku zuri'a ɗaiyaba wanda zasu taimaki al'umma baki ɗaya."


"Amin."

Baki ɗaya parlourn suka ansa banda Hakima ta da duƙe kanta kasa tana wasa da zoben zinarin dake maƙale a hannunta bata damu ba dan Baffah ya fidda mata miji ba ita dai fatanta Allah ya basu zaman lafiya.


"Allah yayi maki albarka Daughter, nasan Baffahnki ba zai zaɓa maki abunda zakiyi kuka ba."



Ita dai Gimbiya Hakima ba tace komai ba, amman tana mamakin wai ita za'ayi ma aure yarinya da ita.


*{hahahha! Team Hakim kunji wai Hakima bata isa aure ba😉}*


"Sai kuma kai Annas kaima ka zama cikin shiri dan aurer da kai zanyi ina nema maka mata dai-dai dakai, dan haka ka zama cikin shiri."



"To Baffah godiya muke, Allah yaja da tsawancin kwana, "Amin zaku iya tafiya Mamana ki fara shirin zuwan baƙon naki, "To Baffah insha Allah mun barka lafiya."



Bayan sun fito suka wuce shashen Gimbiya Yakumbo baki ɗayansu, bayan sun zauna Yakumbo ta fara magana."



"Daughter Allah yayi maki albarka, gaskiya kin burgeni Daughter kuma nasan Hakim yaron ƙirkine bazai cuceki ba, sannan mahaifiyarshi mutuniyar ƙirkice sai dai kun kula dan masarautar zaria ana tungu da surkule dan haka sai kin kula da hannunki."



"Momy da man Yarima Hakim Baffah zai ba auren Hakima."?


"Ehmana Yarima Hakim ne, da man kasanshi? Dan nasan rabonsu da nan masarautar tun haihuwar Hakima dasuzo sunan Hakima."


"Eh nasanshi sosai muna mutunci sosai da shi muyi zama dashi a dubai."



Ita dai Gimbiya Hakima batace komai ba, kuma bata kowa komai a ranta ba duk taji sunce Hakim amman bata kowa prof Hakim ba dan ta manta dashi ma.



*{gaskiya Hakima bata kaunar Hakim tunda ta iya mantawa dashi, salan naji Team Hakim kunce ba haka bane😎}*


Bayan sun gama maganarsu dan Gimbiya Yakumbo taba Hakima shawara sosai yanda zata zauna masarautar su Hakim ta gaya mata shirin masarautar sosai har suna mamakin yanda Yakumbo ta san masarautar har haka.



"Momy ni wallahi har na fara tsorata taya zan iya da halin su Gimbiya Zulaha? Bayan ni ban taso naga gidan mu ana haka ba."?



"Zaki iya Hakima sosai ma, abunda zakiyi shine karki yarda kice wani abu da ya fito daga hannu baiwar gida ko kuma hannun su Zulaha da Kilishi, karki yarda da ko wace baiwa sai wanda zaki tafi dasu daga nan masarautar suma da mutun uku zaki Lantana da Bilkisu sai Azima suma dan na yarda dasu amintaitun bayine nasan basu yarda a haɗa baki dasu a cuceki ba."




"Sannan karki shiga sabgar kowa, kuma nace maki Gimbiya Kubrah bata da matsala dan matace mai kawaici da mutunta mutane dan haka sai ki yaye Hakima, nasan ki baki ɗaukar rainin bayi to karki yarda wata baiwa daga cikin masarautar ta ringa shigarmaki shashen har zuwa cikin ɗakuna dan haka su azima su zasu gyara ɗaki da girki kinjini ko."?



"Eh Momy, naji kuma insha Allah zanyi abunda kikace man, dan ba zan yarda ba su Gimbiya Kilishi su raina ni nafi karfinsu da ayar Allah, amman Momy taya kikasan sirin masarautarsu har haka."?




"Nasan sirinsu wajen Gimbiya Zulaha, da aminatace sosai saboda amintakar da ke tsakanin mijina da mijinta, lokacin daga ni har ita bamu samu haihuwa ba taso taja ra'ayina wajen bin bokaye da malamai nice ban bata fuska ba muna cikin haka sai Sarki Abdulmatalak ya bujuro da auren Gimbiya Fulani Kubrah, hankalin Gimbiya Zulaha ba ƙaramin tashi yayi ba dan ba wajen bokon da bataje ba amman bakinsu ɗaya aure sai anyi ba, bayan anyi aure Allah mai iko yaba Fulani Kubrah ciki daga zuwanta nan ma Gimbiya Zulaha ta fita ta shiga taga cikin zube amman babu nasara har aka haifi Yarima Hakim, bayan haihuwar Yarima Hakim Gimbiya Zulaha itama ashe tana ɗauke da ciki, Hakim yana da wata biyar a duniya Gimbiya Zulaha ta haifi yaronta namiji shine akazo dashi wajen walimarku Sunanshi Hamad, Hamad yana da wata biyu na haifi Annas tunda Gimbiya Zulaha taga Hakim shine magajin sarki Abdulmatalak ta tada hankalinta shine take bin bakoye dan har yanzun tana kan bakarta na Hamad sai yayi mulkin Zaria ba sirihin da bata yi ma Hakim amman Allah ya kareshi daga sharinta, Gimbiya Kilishi kuma su Hakim nada shekara biyu a duniya sarki Abdulmatalak ya aureta da basu yar ga maciji tsakaninta da Zulaha daga baya da suka fahimci halin su ɗaya suka zama Aminan juna dan tare suke komai nasu ita kuma Kilishi ita ta haifi Yarima Humad kinji taƙaitacen labarin gidan surukanki Hakima zaki shiga gidan sarauta mai rikici dan haka sai kin iya takunki karki kuskura ki nemi bokaye dan haka ki riƙe Allah da ibadodi sune gatanki dan ita addu'a takobin mumunice."




"To Momy insha Allah, amman Momy taya kuka bar Abokantaka keda Gimbiya Zulaha."?


"Lokacin da Baffahnki zai auri mahaifiyarki, dana gaya mata shine ta nunaman naje wajen boka a hana bikin, ni kuma nace ban ƙaucema Allah saboda ɗ'a Namiji naje nayi saɓon Allah dan haka ban hana Abdulhadi aure koda mata uku zai aure nidai fatana muyi zaman lafiya, shine tace ba ita bani tunda ba halinmu ɗaya ba,daga ranar bata ƙara zuwa wajena ba sanan ku za'azo wannan masarautar bata zuwa ko sunanki ba ita tazo ba Gimbiya Fulani Kubrah tazo sunanki ita da Yarima Hakim kawai sukazo suna kinji abunda ya rabamu."



"Mutane saboda san duniya da san zuciya sai suyi abunda zasuyi da nasi nan gaba, Allah yasa mu dace, "Amin Hakima."




Nan dai suka gama maganganunsu sannna kowa ya wuce shashen shi.



_______________________________


*×ZARIA×*






💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼
*YAR UWA KADA KI WUCE BAKI KARANTA BA DOMIN KUWA AKWAI ƘARUWA A CIKI*


*_🗣️ALBISHIRIN KU🗣️_*


*JAMA'A KO KUSAN MATASHIYAR MARUBUCIYAR NAN WATO JAMEELAH JAMEEY WANDA AKA FI SANI DA YAR'MUTAN KANKIA TAYI SHIRI TSAF DOMIN FITO MAKU DA SABBABIN LITTATAFANTA GUDA BIYU.*

*SANADIN LINK*


*_HAHAHA YAR UWA DAGA JIN SUNAN WANI BOOK BASAI NA FAƊA BA KINSAN ZA'A SHA SOYAYYA. _*



*IZZA KO MULKI*


*WAI WANNAN KO BANSAN MAI ZANCE BA KUNSAN DAI YANDA LABARIN GIMBIYA HAKIMA YA KASANCE TO GA WANI NAN KUMA DAN SHI DABAN YAKE DA SAURAN☺️*



*TAKU CE JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA MARUBUCIYAR👇*

*NANA JAWAHEER*
*GIMBIYA HAKIMA*
*A HAKA NIKE SONTA*
*YAN MATAN ZAMANI*
_SAI KUMA_

*SANADIN LINK*
_DA_
*IZZA KO MULKI*

*MASOYANA KUDAI KU CIGABA DA BIYONI DOMIN SUNA KAN HANYA, 🤫KARKI BARI A BARKI A BAYA😁*




#JameelarhSadiq@wattpad
#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please



👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻


*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________


  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

    *(Yar mutan kankia👸🏻)* 

  



*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```



65&66



*×ZARIA×*


Tunda su Gimbiya Zulaha suka dawo daga wajen Turmurturs, Gimbiya Zulaha ta kasa zaune ta kasa tsaye dan gani take kamar boka yana yi mata yawo da hankali amman da ta tuna Turmurturs ne sai taji hankalinta ya kwanta dan boka Turmurturs ta amince yana share hawaye waya ta ɗauka ta kira Hamad akan komai yake ya ajiyeshi yazo tana san ganinshi.



"Hakim ya na ganka cikin damuwa Allah yasa lafiya."?

"Aliyu ina fa lafiya Abba zaiyi man aure."

"Aure kuma Hakim.''?

"Wallahi aure zaiyi man wai yar'sarkin kano, maganar da nike yi maka Fulani tace gobe zani je wajen yarinyar.''

"Innalillahi wa'inna'alaihirajiun, Hakim abunda nayi maka gudu kenan shiyasa naso kanemi yarinyar nan Hakima dan wallahi ba ƙaramin marching kukayi ba, amman girman kai yana hanaka wai kai cewa ma kake ka tsaneta bayan ga sonta nan cikin idanunka ina gani."


"Allah ya tsareni Aliyu, ai gwara da Abba ya fidda man mata, ni natsi Hakima bansan Hakima ban ƙaunar Hakima kai mai ma irin sunan Hakima bani santa da wall... "Da kata haka Hakim, wallahi karya kake ni Aliyu nace karya kake kana san Hakima kuma nan gaba zakace na gaya maka."


Aliyu ya ƙarashe maganar cikin fushi dan bala'in haushi yake ji idan Hakim yace baya san Hakima bayan ga sonta yake ta ɗawainiya dashi wannan abun na bashi haushi gashi har za'ayi mashi auren dole.


```🤣 niko nace Aliyu kwanatar da hankalinka burinka ya kusa cika```

"Ya isa haka Aliyu enough, taya zaka zo kasani gaba kana gaya man maganganu saboda wata useless girl zaka sani gaba kana yi man tsawa, ka wuce ka ban waje kabarni da abunda ke damuna please."


"Ba inda zani kuma dole nayi maka tsawa Hakim dan wallahi banji dadin auren da Abba yake niyar yayi maka ba, gashi bamu san garin da Hakima take ba da nabita na nemo maka aurenta."



"What are you said?Aliyu kana cikin hankalinka kuwa? To bari kaji zanyi biyaiya na auri wanda Abba ya bani kuma zan koya ma kaina sonta after that kasan bani da budurwa to tada hankali name? Karka kuskura ka sake haɗani da wannna idiot gril ɗin take note".


"Hakim wallahi kana yaudarar zuciyarka, kayi kokari ko bayan aurenka ne kaje ka nemo garin da Hakima take ka aure ta dan nasan tuni kadaɗe da kamuwa da soyayyar Hakima itama haka Hakimar dan haka is ur on choice ni kaga tafiya ta office kayi tunani."


Haka Aliyu ya tafi yabar Hakim dan tunani, "Tabbas Aliyu bai ƙarya ba idanuwana sun kamu da soyayyar Hakima amman zuciyata ba abunda ta tsana kamar haka, how comes taya haka zata kasance? No impossible i hate you Hakima."


Abunda Hakim yace kenan ya tashi ya wuce shashen Fulani ko yaji saukin abunda yake ji a cikin zuciyarshi.


Tunda Gimbiya Zulaha ta kira Hamad waya ya ɗauko hanyar zuwa dan ji yanda zasuyi Hakima ta zama tashi dan abun bata samu mafita ba yana aikata komai mudun Hakima zata zamo tashi, dan ya ɗaukarma kanshi zai iya kashe koda Sarki Abdulmalak ne mudun ya hanashi auren Hakima.


*(Wai Allah na wata sabuwa anya Hamad yana da hankali kuwa🤔, taya zai kashe ubanda ya haifeka saboda mace, macen da bata san da zamanshi ba, Allah yasa mudace ya bamu zuri'a ɗaiyaba🙏🏻).*

Bayan ya shigo royal house ɗinsu direct shashen Gimbiya Zulaha ya wuce dan yaji abunda zata ce mashi, bayan anyi mashi iso ya shiga ya samu waje ya zauna yana saurarenta dan baki ɗaya hankalinshi wajen mahaifiyar tashi ya maida shi.


"Hamad kanaji na ko."?

"Eh ina saurarenki Gimbiya, "yauwa munje wajen Turmurturs amman yace aure dole ya ɗauru ba yanda zaiyi ya hana auren."



"To naji kinga tunda shi Turmurturs ya kasa, ni bari yanzun naje na sarema Hakim kai da man naga yana gida tunda naga motarshi"yana tashi tsaye yake maganganun dan da gaske yake zuwa zaiyi ya sarema Hakim kai tunda shi Turmurturs ya kasa.


"Na  shiga ukuna ni Zulaha, Hamad baka da hankali? Ko dai kayi shaye-shaye ne kafin ka shigo gidan nan".?


"Ba abunda na sha da hankali na wallahi kashe Hakim zaiyi ba zan bari ba ya auri Gimbiya Hakima ba, wallahi zan iya kashe koda ubantane balle Hakim da daman na tsaneshi komai za'ayi cikin gidanan shi Abba yake sawa saboda shine ɗan so, to idan na kasheshi uban kowa sai ya huta."


Tas! Tas! Tas!, Gimbiya Zulaha ta wanke Hamad da zafafan marika har guda uku dan gani tayi sai ta mareshi zai dawo cikin haiyacinshi.


"Gimbiya ni.. "Yi man shiru ko na ƙara wankeka da  mari wallahi sakaran banza sakaran wofi, zaka zauna ko sai raina ya ɓaci."?


Haka Hamad ya zauna yana dafe da kuncinshi da ya sha mari, wata sabuwar tsana yaji yana yi ma Hakim dan saboda shi Gimbiya Zulaha ta mareshi abunda Gimbiya ba ta taɓa koda dungurinshi ba amman yau shine tasa hannu ta mara becouse of

Please Login or Register in order to submit comment