Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ina fatan haka daga gareku."


"Insha Allah Abba zamu zama mai biyaiya a gareka, zamuyi koyi da abunda Yaya Hakim yake da yarda Allah zamu zamo masu bin umirnin iyayenmu.".... Humad yace haka kanshi ɗuge, shi dai Hamad baice komai ba, kallon Humad Sarki Abdulmalak yake dan ba tun yau ba yake yaba hankalin Humad dan kusan halinsu ɗaya da Hakim, Hamad ne kawai yasha banban,cigaba da cewa yayi, "Alhmdulillah, Allah yayi maku albarka gaba ɗayanku, to dalilin kiran da nayi maku ba komai bane ila kai Hakim na sake shidamaka da nan da wata ɗaya zani ɗaura maka Aure da Gimbiya Hikimatu yar' sarkin Katsina."


Wani kallar faduwar gaba ya ziyarci Hakim da Hakima lokaci guda, dan Hakima ji take bata gani sosai ma dakewa tayi, Gimbiya Fulani Kubrah lura da yanayin da Hakima ta shiga yasa ta riƙe hannunta tana shafawa ba tare da kowa ya gani ba, amman kash sai dai Hakim yana ganinsu duk da tashin hankalin da yake ciki dan bai da niyar yi ma Hakima kishiya dan son da yake ma Hakima ya wuce ya haɗashi dana wata mace, amman bashi da zaɓi dole ya bi umirnin mahaifinshi dan faɗar Allah(SWT) ce duk wanda yayi ma mahaifinshi biyaiya yana tare da Allah, sannan kuma wanda ya bujirewa iyayenshi yana tare da fushin Allah, dan haka shi ko dole ya bi umirnin mahaifinshi mudun bai saɓama shara'ir musulunci ba, yana cikin wanann tunanin yace Gimbiya Zulaha na cewa, "ina wallahi sun wannan abun ba zai saɓuba, na gaji da rashin gaskiyar da kake nunawa cikin gidan, komai dai kace Hakim, mu bamu da ya'yan ne? Ko kuwa namu basu isa su zauna da mata ba? Ko kuma basu da kwain haihuwa? Shiyasa komai ka samo sai ka kaishi wajen ɗ'an so to wallahi wanann karan ba zan yarda ba , haka kazo kace zaka ɗaura ma Hakim auren Hakima, kuma yanzun kadawo kace zaka ɗaura ma Hakim wata Hikimatu to wallahi ban yarda sai dai maida auren a kan Hamad ko kuma yanzun Hakim ya saki Hakima, a ɗaura ma Hamad ku kuma a ba Hamad auren Hikimatu ba dai Hakim ba, ehe."


"Kingama."? Sarki Abdulmalak ya faɗa cikin ɓacin rai dan sai yau ya ƙara yarda da Zulaha bata da hankali... "Eh nagama, kuma dole ayi yanda nike bukata, dan shima Hamad ɗ'ane kamar kowa, idan shi Humad ka nuna bai isa ba to ai shi Hamad ya isa tunda duka duka wata biyar Hakim ya ba Hamad."


"Ashe ke Zulaha baki da hankali?, "ai ba rashin hankal... "Yi man shiru mutuniyar banza, kinci darajar ya'yan nan suna cikin wajen nan kikayi wannan maganar, da mu kaɗaine ni ɗaya nasan abunda zan maki dan haka ku duka ku tashi ku ban waje, kuma kai Hakim kasani aure na nan ba fashi nan da wata ɗaya insha Allah, sai ku fara shiryawa idan kuna bukatar kudi kuyi man magana, ai shi aure lokacine, to lokacin auren su Hamad ne baiyi ina nasan kin san da haka."


Zubewa Hakim yayi yana godiya da babbar kyauta da Sarki Abdulmalak yayi mashi sannan suka taso suka taho ko wane ya wuce shashen shi da abunda ke cikin zuciyarshi.

Tafiya kawai take amman ita batasan ya akayi ba sai dai kawai ta ganta a shashen Gimbiya Kilishi, Kilishi tana shafa mata ruwa, tashi tayi zauna tana cewa, "wallahi sai inda ƙarfina ya ƙare, dan ba zan zuba ibo na naga anayi man kallar wannan cin kashin cikin gidan nan ina ido to yau tazo karshe."



"Haba Gimbiya maiyasa kike haka wai? Ko kin manta sauran wata hudu Hakim ya matu."?.... "Duk da haka Kilishi ba zan bari Hakim ya auri Gimbiya Hikimatu ba, bayan ga Hamad yana numfashi, shima fa Hamad mutun ne kamar Hakim yana bukatar mace kusa dashi."


"Nasan da haka, amman ni kibarsu suyi auren su sai itama aje wajen Turmurturs ya bamu maganin da ya bada aka sama Hakima cikin abinci kinga shi kenan ba ita ba haihuwa idan Hakim ya mutun sai ta gama gabanta kinga daman bata haihu balle muga bakin ciki,amman kiyi tunani Gimbiya."?


"Shikenan Kilishi zan hakura na bi shawararki anayin auren zan je na anso maganin dan yanda na hana Hakima ɗaukar ciki cikin gidan nan haka zan hana Hikimatu ɗaukar ciki,ba dai sunga auren Hakim ba, to har su mutu basu ganin jinin Hakim."



Ohi nace Gimbiya Zulaha sudai suna mantawa da Allah, basu tunanin kafin wata hudun su su mutu🤔.

_______________


"Hakima Fulani nasan ganinki yanzun, "Maryama yanzun da safen nan."?


"Eh haka tace dai kizo yanzun, "to shikenan, amman ban dafa mana komai ba dan wallahi dan daɗe da tashi ba wanka kawai nayi, "karki damu Yaya Hakim ma yana shashen mu wajen Fulani tun safe daman yace baki tashi bacci ba da tuni nazo na kiraki, "to mu tafi Maryama."


Haka suka tafi tare shashen Gimbiya Fulani, amman da kaga Hakima kasan tana cikin damuwa ko bata faɗa ba , amman Hakima ta ɗaure dan tunda akace Hakim zaiyi aure bata yi ma kowa maganar ba sai Gimbiya Yakumbo kuma Gimbiya Yakumbo ta kwantar mata da hankali sosai tayi mata wa'azi mai shiga jiki, haka suka isa shashen Gimbiya Fulani, tunda ta shigo Hakim yake kallon ta dan damuwar ta sama kanta har tasa tayi rama dan ta faɗa ba laifi, samun waje tayi kusa da Fulani ta zauna sannan tace, "Fulani ina kwana."?

"Lafiya lau, Ɗiyata kin tashi lafiya."?... "Lafiya lau Alhmdulillah, gani kince kina san gani na."


"Eh Daughter inasan ganinki, tunda Abbanku yayi maganar ƙarin auren da Hakim zaiyi ban sake ganinki ba, Hakima nasan abunda kike ji gamai da wannan auren da Hakim zaiyi ko wace mace dole taji kishi idan za'ayi mata kishiya ko ya take balle ke da kika tashi baki san yanda ake zaman kishi ba tunda Alhmdulillah gidansu iyayanki sun zauna lafiya basu kishi irin na masarautar nan ba zamansu, gaskiya ina san kallar wannnan zaman."


"Dan haka Hakima umirnin zan baki amman idan kin ɗauki a matsayin da na ɗaukike wato ɗiyata,"Fulani keɗin mahaifiyatace bani da kowa a garin nan sai ke dasu Maryama na ɗauki a matsayin mahaifiyata ba sarakuwa ba, zan iya gaya maki ko wace matsala ta idan ta samaini dan haka yanda zaki ba su Maryama umirnin nima haka zaki bani dan keɗin uwatace banda kamarki a garin nan."



Wannan maganar, da Hakima tayi ba Fulani kaɗai ba harta Hakim tayi mashi dadi dan daman yana fatan Allah ya bashi mata ta gari wanda zata ɗauki mahaifiyarshi kamar mahaifiyarta, ta maida ƙannanshi kamar nata kuma baida abunda zayi sai dai godiya ga Allah da kuma mahaifinshi daya haɗasu aure da Hakima tabbas ya yarda duk wanda yayi biyaiya ga iyayenshi bazai taɓa yin da yasani ba kuma gashi ta kasance a kan su shida Hakima insha Allah ba zaisa masoyiyarshi kuka ba.


"Allah yayi maku albarka gaba ɗayanku, "Amin ya Allah."suka ansa su dukansu, sannan ta numfasa tana kallon Hakima, babu shakka abu ne mai wuya zama da kishiya a wannan zamanin,abu ne da har yau yaqi dadi a cikin gidajen aurenmu,amma duk da haka ta sani ba duka aka taru aka zama daya ba,duk abinda zata gaya mata a yanzu shi zai zame mata madubin dubawarta.

Murmushi Fulani tayi sannan tace
"abinda nake son gaya miki kawai shine kada ki soma cewa zaki tada hankalinki ko ki daga hankalin mijinki,ki zauna da ita tsakani da Allah,ki sauke duk wani haqqi nata dake wuyanki,Hakima kada ki sake kice zaki cuceta,idan kika cuceta Allah yana nan bazai taɓa yafemaki ba, sannan karki sake kice zaki shiga neman bokaye da malamai saboda da neman duniya Hakima ki miƙe lamarinki ga Allah dan kuwa Allah yana tare da mai gaskiya kinji dai ko."?

Kai ta gyada tace"insha Allah Falani zanyi duk abinda kika ce,da ikon Allah bazan zama mai sabawa maganarki ba."



A hankali Fulani ta dinga kwantar mata da hankali haka har Sadiya ta kawo mata breakfast saukowa Hakim yayi suka ci tara dan shima bai samu yace komai ba dan tunda yaga Hakima ta shiga damuwa ya kasa cin komai dan baisan abunda zai tada hankalin Hakima ko ya yake, amman yanzun har hankalinshi ya kwanta tunda yaga har dariya take idan Fulani tayi wata magana, har yaji karfin jikinshi ya dawo da ta da walwalarta, bata san sun cinye abicin ba sai da tasa hannu zata ebo taji suna yi mata dariya wai abinci yayi dadi bata san ta cinye ba, "Fulani kinganshi ko yana yi man dariya bayan duk shi ya cinye abincin ba ni ba."... Ta ƙarashe maganar cin shagwaba, "rabu dashi Daughter ina ganinku ai yanda kukaci abincin duk shi ya cinyeshi."


"Ful... "Yi man shiru Hakim tashaa ka bamu waje, "to shikenan na zan wuce.".. Waigowar da zaiyi yaga Hakima tana yi mashi gwalo, nuni yayi mata da gira zasu haɗe anjima, duk abunda suke su Fulani na kallonsu sai sukayi kamar basu ganinsu, abun yana yi ma Fulani dadi yanda suke zamansu cikin soyayya abun burgewa, sai da la'asar ta koma shashensu ta ɗaura masu abincin dare, bayan ta gama wanka ta shiga ta shirya Hakim ba dawowa abincin sukaci sannan ko ya wuce room ɗinsu.



___________

Garin katsina......





_By Jameelah Jameey ✍🏻_



#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please


👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```


91&92


"Mama wai ya maganar auren na da Abbu yace, zaiyi man har yanzun ango bai zo ba kuma bikin saura sati haka za'a kaini gidan miji bai ɗoukin gani na."?


"Hikimatu ina sane da haka, karki damu Hikimatu dole Hakim ya soki ko ta wace hanyane, kedai ba gurinki ya cika ba, ko kin manta bakoye nawa muka bi kafin mu samu asiri ya hau Abbunki ya yarda da zaije ya nema maki auren Hakim."?

"Mama wallahi ina san Hakim kan Hakim ina iya kashe mutu, wallahi sai na raba Hakim da Hakima ai boka yace man Hakima ita ta ɗauke man hankali shiyasa baiyi ma ko wace mace kallon arziki, to wallahi Mama ina shiga gidan Hakim zani rabashi da matarshi ba ma matarshi ba harta uwarshi sai na rabasu, dan Hakim nawa ne ni ɗaya, dan haka ni *GIMBIYA HIKIMATU* na dauki alkwarin raba Hakim da kowa nashi nayi wannan alkwarin Mama."


"Tabbas Hikimatu kinsha Nonona, naji dadin maganarki ina san naga mutun mai zuciya dan haka karki kuskura ki ɗaga ma kowa, duk Wanda ya nuna mako yatsa kema Ki nuna mashi ban yarda Ki zauna lafiya da Gimbiya Hakima ba, Ki fidda ta a gidan wannan shawarace na baki ni *GIMBIYA BINTA*, karki manta Hikimatu ni nan baiwace a gidan nan, Amman bala'i na sai da na shiga na fita na zama matar Sarki Abubakar gashi har na haifeki, kuma na rabashi da kowa nashi dan haka inasan kema idan kika shiga masarautar zaria Ki raba Hakim da kowa nashi sannan ki haifamai magaji haka nike bukata daga gareki."


"Shiyasa nike sanki Mama, Ina alfahari da kika zamo mahaifiya a gareki, Mamana kwantar da hankali koda na taida Hakima tana ɗauke da cikin Hakim ni Gimbiya Hikimatu sai na zubda shi har lahira dan ni yafi dacewa da na haifama Hakim ɗ'a wanda nan gaba zai gaji masarautar zaria, nayi wannan alkwarin Mamana."


(Wata sabuwa 😳 ita kuma Gimbiya Hikimatu da da salon da zata shiga gidan Hakim kenan😰😭)

______________


"Maryam wallahi nagaji da magangunan da Fulani take bani, baki ji yanda nike jin kaina ba, wallahi jiya kasa bacci nayi wani magani da Fulani ta bani dan wallahi har sai da nasha kuka na kafin na samu bacci ya kwasheni."


Hahhahhha! "Hakima wallahi ki bada kai bori ya hau, dan wallahi idan baki ba Yaya Hakim hanya ba akayi komai aka wuce wajen amaryashi na shigowa za ta bashi abunda ke kika hanashi tunda ke baki so ai ita naso."


"Maryam kin san bani boye maki komai nawa, keɗin ƙawatace kin san nasa gaya maki a da bani son Hakim na tsaneshi ko."?... "Eh hakane Hakima bani ɗaya had ta su Maryama sun san baki san Yaya Hakim baki kaunarshi."


"Hakane ko gaskiya Maryam.".. Hakima tace tashi tayi tana zagaya bedroom ɗin ta ruwa ta ɗauka tasha sannan ta numfasa tace, "Maryam yanzun ina son Hakim ina kaunarshi, amman bansan ya zanyi ba duk da ina iyakar kokarina na ganin na shawo da hankalinshi a kaina."


"Alhmdulillah, Allah nagode maka Hakima da gaske kina son Yaya Hakim."?

"Wallahi Maryam inasan Hakim sosai maiye mafita Maryam."?


"Mafita ɗaya ce Hakima ai yanzun gobe ne za'a kawo Amarya ko."?

"Eh gobe ne ɗaurin aure Hakim, Maryam wallahi ji nike kamar nayi hauka."... "To shikenan idan kin yarda yau za'ayi komai a wuce wajen amman idan kin bani haɗin kai daman dare yayi."



"Eh na yarda Maryam.".... Magana ta raɗama koni bansan mai tace ma Hakima ba naga kawai suna dariya sannan suka tashi su duga biyun suka shiga kitchen suka fara girki Hakima ita ke sauwa ita kuma Maryam tana haɗa juices, haka suka gama sannna suka fito, tare suka ci da Maryam sannan ta tafi gida ita kuma Hakima ta shiga wanka ta shirya cikin ƙananan kaya masu kyau doguwar rigace tasa iyakarta cinya sannan ta baza gashinta baya, ɗakin Hakim ta shiga ta haɗa mashi ruwan ka sannan ta fito, tana fitowa yana dawowa bata kyaleshi ba tadai ce mashi sannu da zuwa sannan ta shiga kitchen ta cigaba da fiddo abinci shi kuma Hakim ya shiga room ɗin shi wanka yayi ya shirya sannan ya fito cin abinci zuba mashi tayi sannan itama ta zuba suka fara ci bayan sun gama ta wuce room ɗin ta ta sake wanka dan wanka tayi na mutuncin ta fito ta fara shiryawa tana cikin shiryawa taga Hakim ya shigo room ɗinta direct wajenta ya nufo fisgota yayi yana manna mata kiss ta ko ina, cewa take "Hakim maiye haka baka laf.... Taji ya haɗa bakin su waje guda yana yi mata wani irin kiss wanda take ya mantar da Hakima duniyar da take ciki daman abunka da tana hannu sai ta fara biyema Hakim, murzata yake san ranshi itama baye mashi tayi suna ta murzar juna wani kallar numfashi suna fitar da sauti, tun suna tsaye har Hakim ya ɗauke ta ya sauketa bisa gado rumfa yayi mata da faɗanɗan girjinshi nan ya cigaba da murzata tun Hakima najin dadin abun har ta fara yi ma Hakim nisa dan Hakim yayi nisa bayajin kira ni Jameey da naga abun ya girmi tunani na kulle masu kofar na haɗo yan tarkacena na kama gabana nace masu asuba ta gari🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️.



Washe gari Hakim da kanshi ya taimaka ma Hakima tayi wanka ta gasa jikinta sosai yanda ya kamata dan bata sa san jiki ba ta gasa jikinta sosai sannan ta fito tayi sallah tana bisa abun sallah tana azkar Hakim ya shigo ji tayi anyi sama da ita cewa tayi, "wai maiye haka haba mana duk cin zalin ɗina da kayi bai isheka ba har sai ka dawo kasake cucata."


Tunda take maganar yake kallonta, dariya yake yi mata sai da ya gama dariyar shi sannan yace, "haba Jewel yanzun ni zaki cema naci zalin ɗinki bayan haƙina nazo na ansa."

"Ya isa haka."... Hakima ta faɗa cikin kukan wasa dan ita kaɗai tasan yanda take jin jikinta gashi kuma yazo yana niyar ɓatama rai, dariya ya cigaba da yi sannan yace, "wallahi Hakima ina sonki, ina kaunarki please i beg you Hakima ki soni ko da kadan ne, ki taimaki dan almajiri."... Yace yana langwabar mata dakai alamun ban tausayi, wani dadi ne ya ziyarci Hakima wai Hakim ne yake gaya mata kalmar so, Hakim ɗin da tasan baisan ta bai kaunarta amman yau ita yake roƙar ta soshi, Allah kenan tana cikin wannan tunanin taji yace, "Hakima gani gaban na duge ina neman soyayyarki Hakima please Hakima duk abunda ya faruna tsakani na dake a baya muyi fecing abunda zai faru gaba amman karki manta Hakima ina sonki kuma ba sai wannan abun ya faru a tsakaninmu ba a jiya naji ina sonki Aa na fara sonki tun randa idanuna sukayi gamo dake, amman na kasa gane hakan sai daga baya, baki ce komai ba."


Kallonshi ta kama yi sai da tayi kusan 6min tana kallonshi sannan ta kwanciyar ta, ta kyaleshi ba ta ce mashi komai ba, cewa yayi, "please Jewel ibeg uh karki hukanta da laifin da nayi maki a baya na roƙeki zan jure ko wani hukunci daga gareki amman karki juya man baya karki kujeni domin kece rayuwata Jewel."


Sai da ta numfasa sanann tace, "naji Hakim ka tashi ka tafi please ina bukatar na huta, kuma ko ka manta yau ake kawo maka sabuwar amarya kaga ba abunda zanyi maka tunda yau za'a kawo maka sabuwar amarya dan haka dan Allah nima na roƙeka ka tashi ka fita ina bukatar hutu."


"Naji zan barki ki huta nima ai ina bukatar na huta dan haka tare zamu kwanta dake kuma kisani ina sonki ina kaunarki ba zan daina sonki ba har abada.".... Bude baki tayi zatayi magana yayi saurin haɗe bakinsu waje ɗaya yana aika mata da wasu hotskiss, nidai Jameey da naga lamarin yana neman ya wuce kiss na kulle masu kofa na nace dai Prof Hakim karda ka manta yau ake kawo maka sabuwar amarya 🤪.




______________


Yau aka ɗaura auren *HAKIM ABDULMALAK DA AMARYARSHI HIKIMATU ABUBAKAR*, akan sadaki naira dubu ɗari da hamsin, ango Hakim shi dai bai san wani yanayi zaice yake ciki ba, dan shi ba farin ciki ba kuma ba baƙin ciki ba, bayan angama ɗaura auren suka ɗauko amaryarsu sai gidan mijin ta, bayan angama komai kowa ya watsi ya kama gabanshi, kamar yanda al'adarsu take haka ta kasance sai da Hakim ya ɗauki Hikimatu suka je gaida kowa shashen sannan suka dawo gida.


Tunda Hakim ya fita Hakima take kwance bata lafiya dan bata fita ko da aka kawo Amarya kwance suka iske ta hakanan ta tashi ta anshi Amarya ita dasu Maryama, waya Maryama ta kirashi ta gaya mashi Hakima bata lafiya shiyasa hankalin shi yana kan Hakima kawai dai ganinshi suke, bayan sun dawo shashen su sakin hannun Hikimatu yayi ya wuce room ɗin Hakima bai ce mata komai ba, tsaye tayi tana kallonshi tsaki tayi sannan itama ta shige room ɗin ta itama.






_By Jameelah Jameey ✍🏻_




#Comment
#Share
#Like
#Vote
#Please


👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```



93&94

Yana shigowa ya isketa ɗaure da towel tana tsane ruwan jikinta da alamu fitowarta kenan daga wanka, ba taji shigowarshi ba sai dai ji tayi anyi hunging ɗinta ajiyar zuciya yai tayi dan ganin ta kawai da yayi yaji natsuwa ta samaishi hankalinshi ya kwanta yarda da ba tun yau ba yake son Hakima, yaa yarda duk abunda yake yi ma Hakima da take A. B. U duk sonta ne sanadi, yana sonta har bai san wani irin so ne yake yi mata dan haka shire yake da duk wanda yake shirin rabashi da rayuwarshi, raɗa ya hau yi mata cikin kunnanta harshenshi ya tura ciki yana cewa, "Jewel ya jikin naki, fatan kin samu lafiya? Dan bansan wajen ya daɗe bai samu sauki ba saboda shine rayuwar Hakim, Ilove with all my heart, kece bugun numfashi na Jewel, kice komai nawa dan Allah ki soni ko ya yake, ki furtaman kalma so yau ɗin nan ba sai gobe ba Jewel."..... Ya ƙarashe maganar cikin fuskar ban tausayi, dan ji yake kamar ha haɗiye ya huta saboda tsananin sonta da yake fusgishi.


Hakima ita bata san wani kallar farin ciki take ciki ba, ita kanta tasan tana son mijinta kuma tana kishinshi sannan zata gaya mashi kalmar so kafin a rigita dan ta lura Amaryar tashi da rawar kai ta shigo cikin gidan nasu, tana son mijinta kamar ranta bata iya jure rabuwa dashi kona minti ɗaya ne amman ba yanda zatayi dole ta koyi hakuri da juriya na wasu lokaci kafin ya dawo gare ta, shi dai Hakim yana riƙe da yatsan hannunta yana murzasu cikin sauƙin so da kaunarta kana kallonsu a lokacin kasan masoya ne masu shirin sadaukar da rayuwar su a kan ɗayansu, ji yayi ta rungumeshi tana kuka, shima ƙara rungumota yayi yana aikin lailashi sai da tayi kuka mai isarta sannan tace, "nima inasonka mijina ina kaunar ina yi maka so na Amana da babu algunshin a cikinshi kaine rayuwata, masoyina dan Allah inasan kayi mana adalci a zaman nan da zamuyi da wannan baiwar Allah kayi iyakar yinka sai Allah ya dafa mana baki ɗaya."


Kiss ya fara yi mata yana sama mata albarka sai da ta hanashi dan taga yana san ja mata matsala wajen amarya dan har sha ɗayan dare yayi bai fito ba kuma tun goma ya shigo room ɗinta, ce mashi tayi, "tashi ka shiga wanka masoyina daman na haɗa maka karma ya huce ni kuma na samu na shirya sai in kai ka wajen Amarya nasan tana can tana jiranka."



Ɓata fuska yayi dan shi ya manta da wata Amarya dan so samu ne da zuwa zaiyi yace ta saida ma Hakima kwanta dan wallahi shi gani ɗaya yayi mata yaji bata yi mashi ba, dire-dire ta fara yi mashi tana cewa, "ni wallahi ka tashi ka shiga wanka kana ɓata lokaci kuma kasan akwai mai jiranka ko."?.... Ta ƙarasa maganar ta kama hannunshi wai ita a dole tada shi zatayi, fisgota yayi ta faɗo jikinshi kallon juna suke ido cikin ido kamar zasu cinye junansu, sun kusa 6min a haka sannan Hakima tayi janye fuskarta dan bata iya jurar kallon nashi ce mata yayi, "Jewel korata ma kike ko."?


"My Angle kasan kaine rayuwata ican't live with out you, but ina san itama ka bata haƙinta dan haka please ka tashi ka shiga wanka nima na shirya kafin ka fito."


"Naji amman ke dai zakiyi man wankan inba haka ba ba idan zani nan zan kwana muyin amarcinmu wanda bamuyi ba."



"Tare fa kace Angle? Kuma ni zan maka wanka."?


"Uhm, idan bakiyi kisa a ranki nan zan kwana."yana faɗin haka ya yi hanyar bathroom kasancewar zamanan da sukayi da shi tasan halinshi ta bi bayan shi suka shiga bathroom , koda ta shiga kulle idonta tayi wai ita bazata kalleshi a haka ba ba kaya daman ai haka ya taɓa yi mata ya cire towel ɗin shi a gabanta yanzu kuma rashin Kunyar tayi gaba wai ita zatayi ma Hakim wanka, ji tayi an saka ta cikin bahun wanka daga ita har towel ɗin shima ya shiga cikin firgigi tayi ta bude idonta tana ganin ikon Allah, saurin rungumeshi tayi ita wai karda ya kallan mata boos, bai damu ba ya fara yi mata wanka ƙyaleshi tayi ya gama yi mata sannan itama ya matsa mata sai da ta yi mashi dan yace bai sake wanka shi ɗaya mudun yana ɗakinta bayan sun fito suka shirya a gurguje sannan ta suka fito parlour Hakim ya zauna sannan Hakima ta wuce ɗakin Hikimatu zatayi mata

Please Login or Register in order to submit comment