Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Azima tayi mani cake, amman zansa tayi mani cake ko dan saboda da kallar wanann bakar lecture din tashi na kamaka rabona da bacci wallahi tun karfe biyun dare Maryam..




"Gaskiya kina kokari Hakima, nan dai suka shiga restaurant suka samu abinci suka ci, bayan sun gama, Hakima tace aka wo mata chip exotic chivita na watermelon..


"Hakima mai zakiyi da chivita bayan nasan baki shan exotic ke kika fadamn da bakin ki kin fi san ayi maki juice nan take dan baki shan chemical?



"To yau ina bukatar sha, ji nayi kawai ya burgeni da naga wannan guy din yana sha, "to ai sai ki sha mu tashi mu tafi wata lecture din..



"Aa ba yanzun zan sha shi ba, kiyi gaba gani nan tafe zan biya wajen Bala na bashi kudi ya samu abunda zaici dan shima baiyi breakfast ba muka taho..



"Ok sai kin iso, ni na wuce amman dan Allah kiyi sauri kinsan bansan zama ni daya sai naji duk ba dadi..


"Ok yanzun ko zan taho ai ba wani ajima zanyi ba..



Nan Maryam ta wuce lecture hall, ita kuma Gimbiya Hakima ta kama hanyar office din Yarima Hakim, tana zuwa tayi nocking..


"Yes, ya cigaba da aikin papers din gabanshi dan yayi ma level 2 test, kuma yasa ma Aliyu ne..


Nan Gimbiya Hakima ta shiga office din cikin takama da nuna ita watace dan harda taunar chigum take, bata san shi Hakim baya san yaga mace na tauna chigum sai yaji ya shiga cikin wani hali mai wuyar fassara..



Tashi yayi ya nuna mata kofar dan ko magana kasawa yayi tunda yaga tana cin chigum take felling dinshi ya taso more felling ma, shiyasa ya kasa magana dan idan yace zaiyi magana numfashinshi na iya daukewa shidai kawai ya narka mata narkarkin idanunan nashi da suka tashi daga fari suka koma ja dan tsananin azaba...



Sai da tayi kusan three minutes tana mashi kallon tsana dan ji take kamar ta zunduma mashi wuka a ciki ya muti ta huta da ganinshi..



Kawai Hakim ji yayi an watsa mashi abu mai sanyi ai take ya dawo cikin natsuwarshi, tsaya wa yayi yana kallon abunda Hakima tayi mashi, new gizina shaddarshi da yafara cewa a yau itace tayi ma haka gata fara ce sosai amman ta watsa mashi Jan abu a jikinta..



"This is a last warnings din da zai sake yi maka Hakim, ka fita a rayuwa hakanan karka sake shigarman rayuwa ni na fi karfin a wulakantani cikin mutane, kuma nace maka da man duk wanda yaci tuwo da Hakima miya yasha useless kawai ta kai, mtssssss.


Nan Gimbiya Hakima tayi tafiyarta class bayan ta gama yin abunda tayi niya...



Yarima Hakim kasa komai yayi, "wannan idiot girl din wai yar gidan uban wa ce, waye ubanta cikin zaria bama zaria ba duka kaduna da kewayanta, da ko zanga ubanki a gaban idonki zansa a yanke mai yatsan hannu dan dole na hukuntasu saboda basu baki tarbiya ba Hakima..



Abunda Hakim yace kenan ya tuna da papers din students dinshi Allah ma yaso basu jike ba, nan ya tartarasu a jiye ya kira Aliyu waya yazo ya daukeshi ya taho mashi da wasu kaya...



"Hakima ina kika je? "Lafiya wanann question din ka bayan kinsan nace maki zan ba ma Bala kudin abinci..



"Hakima ba wajen Bala kika je ba, dan yanzun na ba Bala kudin abinci dan yazo neman ki bashi izini yana san ya koma gida yace abinci har ya kowa maki naki inkina bukata..



"To uwata naji ba wajen Bala naje ba, shi kenan ko? "Wajen prof Hakim kika je ko Hakima? "Eh wajenshi naje wani abu?



"Haba Hakima maiyasa kika biyema zuciya eyeh? Hakima ya kamata ki sani ba komai ake biyema zuciya ba dan sai kazo kayi da na sani daga baya, kin ko san ki waye Hakim a garin nan ba ko?



"Da kata dallah Maryam bani bukatar nasan waye wani Hakim can, NI KINSAN KO WACECE HAKIMA A GARIN KANO?..



"Duk da haka ya kamata kiringa ragi ko yaya ne Hakima, ina san mutun mai sausauci da ragi Hakima, yanzun wanann Balan baki daya baki raga mashi ko kadan kuma shima mutun ne kamar ke yana bukatar hutu, haba Kawayata pls ki dan ringa rigi..



"Naji, amman indan Hakim yayi mani wallahi sai na rama, "to wai maikika yi ma Hakim din?



"Maifa zanyi mashi tunda ban iya dambe dashi? Kawai chivita naje na watsa mashi a jikin wannan tsunman shaddar tashi daya sa yau..



"Yanzun gizinarshi kika watsama chivita Hakima? "Kwarai kuwa Maryam take dubu dari shidda? Ni shadda inba ta kai million ba ban dauke ta shadda ba ke harda atamfa dasu laces dan haka take note..



"Uhmm gaskiya ne Hakima Allah yasa mudace, "Amin dai Maryam, ya naga har yanzun bai zo ba? "Eh ba wani abu yayi ba area of concentrate ya bada kawai..



"Ok shikenan, tashi mu tafi gida, dan nasa su Lantana sunyi maki dambu fa, "woow like uh Hakima gaskiya naji dadi sosai..




_By jameelah jameey ✍🏻_





Share and comment


πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»
*GIMBIYA HAKIMA*
πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈ

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_


_Jameelah jameey πŸ–‹_


*(Yar mutan kankiaπŸ‘ΈπŸ»)*


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```





21&22





"Hakim mai yasa mai kayan haka?

"Hmmm! Aliyu kaidai kawai ni banma ya san ya zance maka ba, amman wallahi Aliyu na tsaneta..


"Ka tsaneta? Wacece mai kuma ya hadaku? Kai da baka damu da mutane ba..


"Ban qaunarta I hate her wallahi, Hmmm Ammn, "gaya man wai wacece Hakim?



"Hakima wai ita sunan ta, bani san ta wallahi Aliyu, ko ganinta bani san yi..


Nan dai Hakim ya gaya ma Aliyu yanda sukayi da Hakima..


"Bala'i ko wacece wannan bata san ko kai waye ba shiya take yi maka haka, dan haka ka nuna mata kawace ajinta ta ko ina...


"Kyaleta Aliyu zanyi magana ninta ai tace duk wanda yaci tuwo da ita miya ya sha, to zata gane kurenta bani rigarnan nasa..


Nan Hakim ya sa rigar da Aliyu ya kawo mashi sannan suka wuce gida...


"Sannu da zuwa Maryam yau dai gaki temporary gidan Hakima..


"Gaskiya ko gani gidan Hakima, amman ita Hakima ko maganar zuwa namu gidan bata yi..



"Karki damu kisa a ranki Hakima tazo gidanku har angama, "to Allah yasa ita Hakima da gaske take, "da ma gaske take..


"Lantana! "Allah ya taimakeki gani gabanki ina jiran umirninki, "sai nace kuke wo ma bakuwata abin sha da abinci?


"Muna neman sausaucin uwargijiyarmu , "mtsss! Wai ku dan Allah wasu kalar jahilai ne mararsa gwalkwalwa baki daya har yanzun baku da lissafi, komai sai kunsa mutun magana..



"Allah ya huci zuciyarki Gimbiya Hakima yar'sarkin kano jikar sarkin yola, muna neman sausaucin Gimbiya Hakima uwar adalci, uwar marayun kano baki dayan ta..


"Inba kuna banzaye ba... "Ya isa haka Hakima dan Allah, Maryam ta fada ta mai daga ma Hakima hannu ranta a bace dan taji haushin abunda Hakima tayi masu Lantana gasu sun fara manyanta..



"Mama tashi ki dauko mana abinci ki kawo mana cikin daki, "to godiya nike ranki yadad'e..



"Hakima mu shiga ciki mana, "maiyasa kika yi man haka a gaban bayi na?


"Shi ne nace mu shiga daga ciki magana zamuyi, "Uhmmm..


Nan su Lantana suka kawo ma Gimbiya Hakima abinci..


"Allah ya taimakeki, aci lafiya uwargijiyarmu Gimbiya Hakima uwar masu adalci..


"Dillah can tashi ki ban waje, zaki cika man kunne da surutun banza, kuma wa kika ajiye ya zuba abinci?


"Ina neman afuwarki, nan Lantana ta zuba masu abinci sannan ta wuce jiki ba dadi ..


"Hakima daman ke yar Sarki ce? Shiyasa kike yima prof Hakim abunda kika gadama, "Uhmmm! Ai ba sai na gaya maki ba Maryam, ni ban damu da ansa ko ni yar gidan waye ba..



"To shi Hakim din kin san ko waye? "Dakata Maryam indan muna tare ban san kina yi man maganar wannan useless boy din, dan na tsaneshi ban kaunarshi balle har na tsaya naji shi dan gidan uban waye bani bukatar wannnan..



"To shikenan Hakima, amman dan Allah ki daure ki ringa hakuri da wanann bayin Allah, wallahi Hakima su biyun sun haifi kamar har uku may be, gudarce dai bata isa haihuwar ki ba..



"Kinga bai kamata ba ace kina yi masu kallar wannan zagin ba, tunda iyayen wasu ne, kinga bai dace ba ina neman masu alfarma kawata..



"Ai laifin su ne Maryam, kinga ina yi ma Bala drive na haka? "Aa gaskiya ba kamar su ba, "yauwa kingansu nan baki daya basu da tunani balle hankali kuma, komai sai ance masu yi sannan zasu yi wallahi na gaji kawai zan ma Baffah magana a chanza man wasu bayin dan ni sukayi man sai nayi masu..


"Nidai bance kice a chanza maki wasu ba, a shawara ta amman kidai rage yi masu wani abun please mana..


"Tom naji, yanzun dai kici abinci, "tom mudai ci tare, "Uhmmmm..



Nan dai suka ci abinci, nan Maryam tayi ma Gimbiya Hakima wuni sannan ta wuce gida, itama tana jirin zuwan Hakima gidan su..


_______________________________

"Ranki yadad'e, Gimbiya Kilishi ga wannan maganin nan inji Boko yace a tabbatar da an barbadashi bisa gadon Yarima Hakim yana kwanciya zai samu ciwon mutuwar rabin jiki, kinga dole ya rage wanann bakar sallahr da yake yi har cikin dare sai a turo aljanu su ida nasu aikin...


Hahhahhahahaha"Mariya gaskiya aikin ki yana kyau sosai, yanzun wacece ki gyara shashen Hakim? Dan wanann aiki ne mai sauki boka ya bada...


"Eh Hasiya yace take gyara ma Hakim shashe, "Hasiya da kyau kice tamu mace take mashi, "eh ranki yadad'e..


"To Mariya yanzun aiki ya rage naki, "angama Amaryar Sarki kuma uwar sarkin gaba, na barki lafiya...


"Fulani sannu da hutawa, "yauwa Hakim har an dawo kenan? "Allah ya yarda, "Sadiya tashi ki dauko mashi abinci, "to Fulani..


"Fulani nifa a koshe nike, "ai nasani Hakim, ai kai kullun a koshe kake, kai dai har yanzun baka san cin abinci ko Hakim?


"Aa Fulani ina cin abinci sosai ma, "Allah yasa da gaske kake, "yaya Hakim ga abincin nan..


Kallonta kawai Hakim yayi Gimbiya Sadiya ta tashi ta barma masu waje, dan daman ita Gimbiya Maryama bata fito ba tana dakin ta..



"Kace abincin ko, "to Fulani, nidai Fulani ina mamakin ina Hamad ya koya wanann hali..


"Mai kuma Hamad din ya sake yi? "Wallahi ina hanyar dawowa naganshi shida wata yarinya cikin mota sun shiga wani hotel..


"Allah ya shirya shi, sai ka cigaba da neman ma dan'uwanka shiryar Allah, kuma ina sake maimai ta maka dole sai kayi hakuri dan kaine Babba, duk da dan watan nine tsakaninku ya zam dole kayi hakuri da yan'uwanka tunda jininka ne..


"Insha Allah Fulani, nan Hakim ya cigaba da cin abincin shi yana mamakin halin kanin nashi, dan daman tuni ya lura da Hamad yana neman mata...



"Allah ya taimakeki Gimbiya Zulaha, "Lanto da magana a bikin ki, gaya man ko Hakim ya mutune?


"Ko daya Gimbiya,Hakim ba mutuwa yayi ba, amman kinga wanann magani to shine ajalin Hakim, dan yanzun daga Niger nike wajen boka yanka daya..


"Maiyace ayi dashi maganin? "Eh cewa yayi kisa ma Hakim shi cikin shayi da hannunki sannan sai kije ki bashi yasha to yana sha zai mutu...



"Taya haka zata faru Lanto, bayan kinsan Hakim bai yarda dani ba, balle na bashi abu ya sha?


"Abu mai sauki ne Gimbiya, sai ki hada mashi ki kai mai, kice kinji ance bai lafiya kwana biyu, daman kinga ya bar zuwa gaisheki, kinga ba yanda za'ayi yake shan shayin da kika kawo mashi da hannunki...



"Hakane fa Lanto bari na tashi naje na hada mashi kinga dare nayi..


"Na manta yace sai kin baryin sallahr asuba kuma, "na baryin sallahr asuba Lanto, bayan ya hanani yin sallahr la'asar yanzun ya dawo yace ta asuba...


"To ranki yadad'e duka na sati nawane, ai kedai ba bukatarki kike san biya ba, ai nasa komai zaki iya yi Allah ya taimakeki Gimbiya Zulaha..


"Hakane Lanto, tashi muje muyi mashi sanyin nan, dan da zafi-zafi kan buga karfe...



"Kina jina ko Hasiya? "Eh Mariya, "anshi wannan maganin inji Gimbiya Kilishi ki tabbarta da kin barba ba dashi a bisa gadon Yarima Hakim..



"Wanann ai kinsan aiki ne mai sauki a wajena, "ai shiyasa Gimbiya Kilishi tace ke take so kiyi mata wannan aikin dan tasan baki da wasa wajen kallar wanann aikin..


"To kije kice mata ni Hasiya nace aikin ta anyi angama, to ni na wuce ki huta lafiya..



Nan take Hasiya ta barbadema Yarima Hakim magani nisa gado sannan ta cigaba da hidimar gabanta..


Gimbiya Zulaha ta gama hada ma Hakim shayi ta juya magani, sannan itama ta dauki hanyar shashen Yarima Hakim..




_By jameelah jameey ✍🏻_





Share and comment pls


πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»
*GIMBIYA HAKIMA*
πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈ

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_


_Jameelah jameey πŸ–‹_


*(Yar mutan kankiaπŸ‘ΈπŸ»)*


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```



23&24



"Ranka yadad'e, Gimbiya Zulaha ta kawo maka ziyara, "ziyara yanzun cikin daren nan? "Eh tana bakin kofa ma tana jiran ayi mata iso, "je kice mata ta shigo...


"Allah ya taimakeki Gimbiya Zulaha, Yarima Hakim yace ki shigo..


Nan Gimbiya Zulaha ta shigo, Lanto na biye da butun shayi a bayanta..


"Allah ya kara maki lafiya yau kice da kanki wajen da'nki? "Ba dole ba Hakim nayi kusan sati uku ban saka a idona ba, ko gaisuwarma mu bar cin arzikinta..


"Ba haka bane Gimbiya, aiki ne yayi man yawa, kin san zaman banza ba aikin yi sai sakaran namiji, shine zai kwanta yace komai sai dai ayi mashi, dan yana dan wani, shi kiga basu komai sai bin matan banza da sheye sheye...


Gimbiya Zulaha taji haushin maganar da Hakim ya gaya mata, dan tasan da Hamad Hakim yake, magana ce ya gaya mata a takaice, Amman sai ta nuna bata gane da ita yake ba, ita dai burin ta yasha tea, dan yana sha ya gama aiki..


"Aiko dai Hakim ai kasan babu maraya sai raigo, Allah dai yayi maku albarka baki dayanku kai da kannanka..


"Amin Gimbiya...


"Da man Hakim jina nayi ance baka ji dadi ba kwana biyu shiyasa nace bari dai nima nazo duba lafiyar sarki mai jiran gado..


"Godiya nike Gimbiya, Amman ni lafiya ta lau gaskiya, Wanda suka gaya maki basu fadi maki dai-dai ba..


"Tabbas, dan gashi na gani da idona, ga shayi nan nayi maka da hannuna dan nasan kana san shayi sosai..


"Nagode, nan Hakim ya ansa shayi ya aje gefe, ya cigaba da marking din papers dinshi, Gimbiya Zulaha na san tace mashi ya zuba yasha Amman bataga fuskar haka ba sai da tayi ta maza sannan tace..


"Hakim ai ya kamata kasha ka jike makoshinka, da man naga duk gaji da alamu..


"Zansha Gimbiya amman sai zan kwanta bacci, dan bani shan wani Abu in ina aiki..


"To shikenan na barka lafiya Hakim, "toh Gimbiya nagode sosai sai da safe..


Haka Gimbiya Zulaha ta fito wajen Hakim ranta bace dan ya bata mata aiki, tunda boka cewa yayi ya sha gabanta sannan maganin zaiyi aiki..


Shiko Hakim Gimbiya Zulaha na fita ya tashi yayi wanka yasa aka fitar mashi da Tea din da Gimbiya Zulaha ta kawo mashi,sannan yasa aka chanza mashi new bedsheet yayi addu'a ya kwantaciyarshi, cikin dare zai tashi yayi sallahr shi..

Washe gari da wuri Hakim ya shirya ya wucewarshi fada, dan yau weekend...


''Allah ya ja da ran maimartaba..



"maimartaba sarki ina ansawa Yarima mai jiran gado..


"Allah ya karamaka lafiya na samaika lafiya? "Lafiya lau Hakim ya aiki? "Alhmdulh, "Allah yayi maku albarka baki daya "Amin ya haiyu..


Nan ya zauna, su kuma fadawa suka cigaba da fadancinsu, Hakim bai bar fada ba sai karfe hudu, dan zasu dan fita shida Aliyu...


Nan ya shirya suka wuce warsu wani join inda ake sha iska..



__________________________________


Masha Allah wata fine girl ce nagani tana shiryawa, fara ce tas masha Allah, ga dara-daren idanunta wanda lashes tayi lub bisa rufar idanun sai kayi tunani fixed dinsu tayi, girarta tasha gyara kamar anzanata saboda yawanta ga kuma shape da tayi ga kuma uwa uba brownrish ne a girar ita ba baki kiranba ita ba brown ba, shiyasa indan ka kyaleta sai kayi tunani jagira tayi, hancinta yana da tsawo amman ba sosai ba sai dai ace medium shi ba karami ba kuma shi ba mai tsawo da yawa ba, bakin dai dai dashi shine Wanda ake kira round mouth ga pinklips dinta masha Allah dai-dai kiss, fuskarta round face ce Amman ba sosai ba round din..



Tana da breast sosai dan idan kaga breast dinta bazakayi tunanin na yar 'shekara 19 bace, ga uwa uba hips dinta ga shape coca-cola shape gareta, masha Allah gaskiya GIMBIYA HAKIMA ba daga baya ba wajen kyau ba..



Bayan Gimbiya Hakima ta gama shiryawa, ta dauke post dinta da wayarta kirar IPHONE, iphone 11 pro ce, nan ta dauko agogonta ta manna a hannu, yau Gimbiya wane dan bala'in lace tasa black color ba karamin kyau yayi mata ba, sannan ta dauko gyale da takalmi purpura colar ta daurama laces din, sannan ta jefa sweet a bakinta ta sannan ta fito parlour...


"Allah ya kiyaye hanya uwargijiyarmu, hannu kawai Gimbiya Hakima ta daga masu sannan ta fita waje wajen Bala ta amshi key din mota da hannunta dan yau Gimbiya Hakima da kanta dake bukatar yin drive dan sha'katawa zataje..



Nan ta dauki hanyar join itama..


______________________________


"Hakim kasan abunda ke ban mamaki a cikin gida?

"Aa Aliyu sai ka fada, "Hmm! Lamarin Hamad wallahi Hakim ya fara bani tsoro wallahi baki daya Hamad ya bata rayuwarshi da kanshi...


"Kaga shine neman mata, shine shaye-shaye, baki daya yanzun baida aiki sai na neman mata..


"Uhmm, Aliyu ya zanyi mashi? Nace ya daina yaron da baki daya baya matuntani, how comes zani cema shi ya daina ya daina Aliyu?


"No way gaskiya Hakim ni shiyasa na fi shiri da Humad shi ba ruwanshi, bai yarda ya baiyema Gimbiya Kilishi ba..


"Eh ai daman Humad da Hamad ba halinsu daya ba, shi Hamad baida hankali shiyasa nike yi mashi uzuri, kuma ina guje mashi ranar da Maimartaba zai gane yana wanna harka wallahi daga shi har Gimbiya Zulaha tausayi suke ba, Allah dai ya kauda tsotsayi, "Amin ya Allah...



"Masha Allah, Hakim kalli wata beb nan na tana tahowa wallahi ta hadu, "kai dai ka bani da kallon matan tsiya, dan haka kyaleni bata wata macen da zani kalla, yana fada yana yarda bawon ayaba, nan ko Gimbiya Hakima ta taka bawon bananar nan take sintsi ya kwashe ta ta fadi kasa...



"Inalillahi na boni, "sannu baiwar Allah inji Aliyu, dan shi Hakim tun faduwarta tana juyowa da shirin bata hakuri yaga Hakima ce ya kyale ta ya cigaba da cin ayabarshi hankali kwance..



"Sannu yi hakuri, "dallah can malan matsa kabani guri tunda ba kai kayi man ba, zaka tsaya yi man wata maganar gulma..


"Aa Allah ya huci zuciyarki, dole mu baki hakuri tunda mumaka yi maki laifi..


Tun ihun da Hakima tayi ma Aliyu ta zanyo attention din mutanan wajen sun tsaya suna kallon ikon mai sama Allah...



"Kai har ka isa ka jefoman banana ka kadani cikin mutune how dare you? Ko dan kace kana sona last week nace nafi karfinka shiyasa kace bari kazo nan tunda kasan nan ne wajen zuwa ka bani kunya cikin mutane to karya ne, ka sani dai Hakima na fi karfenka banza stupid man kawai dakai...



Aiko nan mutane Suka kama yan maganganu suna mamaki kamar yarima Hakim wanann yarinyar take yi ma wanna abun cikin mutane..


Yarima Hakim rasa abunda zai cema Hakima yayi, dan haka ya mike ya wucewarshi rashi bace, nan fa yakara sama mutane confused dan wasu sun yarda wasu ko suna confused sosai..


Nan itama Hakima ta juya warta ta koma gida...



_By jameelah jameey✍🏻_




Share and comment pls


πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»
*GIMBIYA HAKIMA*
πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»πŸ‘ΈπŸ»



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈ

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. πŸ€™πŸ»```
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_


_Jameelah jameey πŸ–‹_


*(Yar mutan kankiaπŸ‘ΈπŸ»)*


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```





25&26



"Hakim gaskiya wannan wannan Yarinya ta cika cika marar kunya, amman abun Mamaki shine baka yi mata komai ba"..


"Uhmmm! Aliyu itace wanda na gaya maka ta watsaman chivita a office"..


"Da man wannan yarinyar kake gaya man? Gaskiya batada mutunci ko daya bata san rajarar mutane ba".


"Hakima kenan, Aliyu wallahi yarinyar na tsane ta sosai, "Aa Hakim ka daina cewa ka tsane ta, domin karda tsanar ta juya soyayya"..


"What? Aliyu maikake cewa? Kana nufin ni Hakim zani so Hakima? To har abada wallahi ko bcox I hate her, baki daya behavior and character dinta bai yi ma ni ba, kai idan zanga wani yace yana son Hakima sai nayi iyakar kokarina na gaya man bata da halo"..


"Haba Hakim! Ya kake yin haka ne dan baka santa sai ka hana kowa aurenta? "Eh domin ban san tayi farin ciki a rayuwarta..



"That Mean! Kaine kenan zaka zama mijin kenan? "Wallahi Aliyu da dan kai bane da bansan abun zanyi maka ba, taya zanso Hakima?


"Amman Hakim! "Dallah Aliyu, please! can't uh keep quite or No?



"Shikenan nayi shiru kamar yanda ka bukata, Allah ya bamu sa'a Hakim, amman wallahi ka rage tsanar Hakima a zuciyarka, in my advance kenan, "


"ok i'll try my best "

_____________________________



Tunda Hakima ta fito daga Join bata tsaya ko ina ba sai gidan su Maryam nan take gaya mata yanda su kayi da Hakim..


"Wai Hakima gaskiya baki da sauki, amman kiyayi prof Hakim fa, kinga gobe zamuyi test din shi, ga kuma next week exams dan haka ki ajiye makamanki Gimbiya Hakima yar sarkin Kano, ai haka naji bayinki suna cewa ko?



"Mtssssssss!!! Wallahi keki ka damu da test dinshi nidai iyaka mutun ya kadani indai nasan nace banyi failure ba, wallahi sai na shiga na fita cikin ABU Zaria an fiddo man hakina...



"Hakane kuma, balle ma nasan baya kadaki, saboda yanada kirki..


"Wai ke Maryam mai yasa kullun maganarki bata wuce, Hakim yana da mutunci? "To dan yana dashi ai shiyasa na fadi, dan wallahi ya fiki mutunci da tausayi ma, nan ne kawai bamuyi marching ba wallahi Hakima"..



"Godema Allah a cikin gidan ku kika yi man wanann maganar, "inba cikin gidan mu nayi maki ba mai zaki yi man?


"Wallahi sai nasa anyi maki hukunci mai tsanani, sai kinyi wata goma gidan horo horon ma mai tsanani, dan naga baki d'aya baki sona, Hakim kike so ai sai kije ki gaya mashi bai sai kin dunga man haka ba..


"Hmm! Shikenan nayi shiru, wannan tsanar is too much gaskiya Hakima very much ma, taya

Please Login or Register in order to submit comment