Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

banzaye ajiyarsu.


Su kuma su Gimbiya Kilishi bakin ciki kamar ya kashesu, ba kamar yanda sukaga iyayen lafe su duk a tunaninsu Maimartaba Sarki Abdulmatalak shi ya bada kuɗin duka akayi wanann lafe ga kuma sunga dubai akaje aka haɗo su hakan ya ƙara tun zuramasu zuciya.



Gimbiya Kilishi abun ya isheta kasa zaune tayi hakan yasa ta ɗauki hanyar shashen Gimbiya Zulaha hankali tashe dan batada wata kwanciyar hankali gani take dukiyar Maimartaba ce duka Gimbiya Fulani ta ansa taje tayi ma Hakim wanann ƙarya injisu ba.


"Gimbiya wai kina ganin abunda ke faruwa cikin masarautar nan."?


Hmmm! "Ina gani Kilishi, daman tuni nasan Abdulmatalak yana nuna mana banbanci tsakaninmu da Kubrah, yafi sonta a kanmu kuma asirine kawai tayi mashi shiyasa baya saurarar kowa sai ita."



"Ina wallahi bazai saɓuba budunga a ruwa, ya zama dole muma idan su Hamad suka tashi aure ayi masu fin abunda akayi ma wance gawar, suna wahalar banza basu san saura shekara ɗaya ya mutu ba."




"Ai ni harda haka yasa na kwantar da hankali na su gama wahalar banza saura shekara ɗaya ya mutu kinga komai suka saya Hamad za'aba shi duka harda ita matar dasuke rawar ƙafa a kanta."


"Aiko dai hakane kawai mu samasu ido suka gama haukansu wawaye kawai dasu, ai gobe ne zamu kai lefe ko."?


"Eh gobe ne, "ok muna jiran goben tayi zamu kai lefe yanda take bukata mudai musan karshen lefen namu ne."


"Ehmana, kedai bari Kilishi ni kawai sama Kubrah ido nayi tagama bikinta da dariyarta nan da shekara ɗaya kuka zatayi sannan tanaji tana gani za'a ɗaura Hamad mulki na maida ta baiwa ta bikin ciki zaiyi ajalinta."


Uhmmmm! Abunsa Kilishi tace kenan ta tafiyarta dan ita kaɗai tasan abunda zatayi ma Gimbiya Zulaha, nan da shekara ɗaya itama zatayi kuka karshe bikin ciki zaiyi ajalinta itama, dan gaban idonta za'a ɗaura Humad mulki, haka tai ta tunaninta daga karshe ta kama dariya dan gani take komai ya kusa zuwan mata karshe tana haka bacci ya kwasheta ba tare da tayi addu'a ba, to ina ma zatayi addu'a matar da ko sallah batayi.



*{yan uwa muslmai wallahi muji tsoran Allah ita wannan duniyar ba matabbata bace, duka nawa duniyar take da zakiyi ma Yar'uwarki hassada da bakin ciki bayan kunsan cewa hassada ga mai rabo takice🤔😰, to maiye abun yi ma mutun hassada bayan Allahn da baya mutun shi zai baki idan kina da rabo wanda kike ma hassada karki manta bashi ya ba kanshi ba, Allah ya bashi dan haka nidai shawarace tawa sisters murage yi ma junanmu hassada kaima kayi addu'a Allah yabaka abunda zai zamaka Alkhari ka nema Alkharin Allah, Allah yasa mudace Amin}*







_By Jameelah Jameey✍🏻_






#JameelarhSadiq@wattpad
#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please



👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```



73&74

Washe gari bayan su Gimbiya Zulaha sun gama shiryawa suka ɗauki hanyar Kano dan zuwa kai lefen Gimbiya Hakima da Yarima Hakim.


"Kilishi yau dai zamuga wannan Hakimar da Hakim ke yi ma rawar kai".

"Aiko dai yayi ya gama dan shekara ɗaya zaiyi ita, ta zama ta Hamad baki ɗaya har abada kuma ta haifamana sarki".


"Hhhhhh! Kilishi kina sani farinciki wallahi shiyasa nike sonki, insha Allah zuri'ata ta dunga zama sarki kenan har abada Kilishi ".


Wani kallon banza Kilishi tayi tana aiyanawa cikin zuciyar ta itace zata kama ganin sarki a cikin zuri'atar , dan wannan komai da komai da Humad ya dace basu Hamad ba.


*Niko nace bawan Allah Humad shi baima san Gimbiya Kilishi na wanan wahalar ba dan bai damu da mulki ba🤣*

Haka dai suka kama yan maganganun su har suka iso masarautar Kano.

Baki sake su Gimbiya Kilishi dan sunga tarba ta girma, sunga idan akeyin abun girma da nuna arziki duk da Gimbiya Zulaha tasan masarautar Kano amman rabonta da masarautar Kano tunda da Sarki Abdulhadi zai auri Fulani bata sake zuwa ba ita acewarta ba halinta ɗaya da Gimbiya Yakumbo ba shiyasa suka rabu.


Bayan angama ansar lefe suka wuce shashen Gimbiya Yakumbo, da yake a shashen Maimartaba Sarki Abdulhadi aka anshi lefen, zasuje suci abinci sannan su wuce gida.


"Sannunku da zuwa Gimbiya Zulaha, ashe rai kanga rai".?

"Gimbiya Yakumbo gashi kuwa, ya na samaiki keda ɗana Yarima Annas ".?

"Lafiya lau kika samaimu, harda ma ɗiyarku Hakima ita da mahaifiyarta duk muna lafiya".

"Haka nike san ji, yau dai saura yan kwanaki akawo mana Amaryar mu, "eh daga gobe zamu fara aladar bikukuwan sarauta insha Allah ".


"Da kyau, ina ita Amaryar take bata zuwa ta gaidamu".?

''Aa fa Zulaha kin taɓa ganin ida Amarya ta fito ranar da ake kawo lefenta".?

"Ai nasa zaki kirata tazo mu gaisa ba wanda yaji ba wanda ya gani".

"Aa ni ba haka nike ba, kuma Hakima bata gidan ma baki ɗaya kuyi hakuri ta kusa dawowa masarautarku baki ɗaya ma".


"Shikenan muna maraba lale da zuwan ta Amarya Gimbiya Hakima ".

"Yauwa haka nike san ji daga gareku, kuci abincin mana, "to yanzun ko zamuci".


Bayan sun gama cin abinci suka ɗauki hanyar komawa gida, bayan sun koma gida basu ce ma kowa komai ba ita dai Fulani Kubrah bata damu da rashin gaya mata yanda komai ya kasance ba daman bata ran za'a gayamata ba.

Yau ake fara hidimar biki dan yau ake sa Amarya laile hidima ake kamar kama hannun yaro tun safe aka tafi da Hakima shashen Gimbiya Yakumbo aka fara shafama amarya laile, wanann yana farkon al'adar masarautar Kano kafin a fara biki za'a fara sama amarya laile sannan zasu cigaba da yin sauran al'adun.


Tunda aka fara shafama Hakima laile take bakin ciki dan ba haka ta so ba, ita da ba san Hakim take ba amman sai wani gyara ake yi mata sai kace gidan wanda take so da kauna za'a kaita.


"Momy dan Allah ki barni haka ko ina fa naga kun shafaman".

"Gidanku Daughter, idan bamu gyaraki ba mai kike san ayi maki".?

"Amman Momy tunda akayi baiko kuke duraman abubuwa cikin cikina,sannan kuma kuke man shafe-shafe Momy".


"Wannan shine gatan, nidai Daughter dan Allah karki bamu kunya ku zauna lafiya keda wannan baiwan Allahn, kinga dai yanda Hakim yake da hakuri kema banjinki Daughter fatana ku zauna lafiya kuba mariƙa kunya".


"Insha Allah Momy ba zan baki kunya ba zani kasance mai yi maku biyaiya har tsawan rayuwa nayi maki wanan alkwarin".

"Allah yayi maki albarka Daughter, sannna ban yarda ki sake da kowa ba inba uwarmijinkina ba da ƙannansa, amman ban yarda ki yarda dasu Gimbiya Zulaha ba".

"To Momy, wai jiya su suka kawo lefe ko".?

"Eh sune sunso su ganki ni na hanasu, so suka yi su ganki abun ya zama gori nan gaba suna cewa baki da kunya dake aka anshi lefenki, shiyasa na hanasu basu san ƙar nake kallonsu ba, kuma halin Gimbiya Zulaha ba wanda ban sani ba tana iya aikata komai saboda kishi da hassada".


"Allah ya kiyaye dai Momy, "Amin ya Allah Daughter.


Ana sama ta laile Gimbiya Yakumbo tana bata shawara dani shirin zama da miji, kuma Hakima tana ɗauka duk da ba wani san Hakim take ba amman duk abunda Yakumbo ta gaya mata suna cikin kanta dan ta rigeshi sosai.

Bayan ta wanke lailen kuma ta fara zuwa shashe tana kai gaisuwa duk inda taje sai anbata tukunci haka ta gama yi har dare yayi sannan ta wuce shashen ta duk ta gaji sosai.


Wanka kawai ta shiga, shi kanshi ruwan wanka ba ƙaramin kayan haɗi ya sha ba ruwan sai kamshi yake kamar anyi ɓarin turere cikin ruwan, saboda da kanshi da ruwan yake ga kuma zafin da yake dashi shi yaba Gimbiya Hakima dama daɗewa sosai tana gasa jikinta sai da taji ta dawo dai dai sannan ta fito.


Mai kawai ta shafa ta kwanta, da Azima ta lura da uwargijiyar tasu ta gaji sai suka kama yi mata tausa suna bata labarin mai dadi har bacci ya kwasheta ba tare da ta sani ba, sai da suka tabbatar da tayi nisa cikin baccin sannan suka tashi suka tafi shashen su dan gobe za'ayi hawan daba.


_____________________________

"Hakim ya maganar biki damai damai ya zamuyi naga har yanzun baka gaiyaci friends ɗinmu ba".?


"Aliyu ni ba wanda zan gaiyata kuma ba abunda zaiyi ai hidimar biki tana wajen Hakima tunda itace Amarya".


"Duk da haka Hakim, ya kukayi da Hakima mai take bukata kudi ko wani abu".?


"Kash ni ko number ɗinta bani da ita, amman nasan bata bukatar komai".


"What".?

"Eh Aliyu bani da number ɗinta, ko laifi nayi naga ka tsareni da idanu sai kace wanda yayi laifi".?


"Baka kyauta ba gaskiya Hakim, ai at list ko wayace kun ringa yi haka zai kawo maku shakuwa kafin bikin".


"Ni ban damu da na shaku da Hakima ba Infact nasan ba sonta nike ba itama ba sona take ba zaman biyaiya kawai zamuyi kaga ba amfani kenan".?


"Kace ba Hakim ina gaya maka gaskiya amman bakaji ko".?

"Wata gaskiya kake gayaman wanda ban ji ba Aliyu ".?


"Ehmana gashinan Hakim, wai har sai yaushe zaka gane ka yaudarar kanka, Hakim ka fidda girman kai ka rungumi matarka hannu biyu ka nunamata kallar soyayyar dakake yi mata hakan zaisa itama taji tana sonka tana nuna maka irin nata son da take yi maka".


"Naji Aliyu zanyi yanda kake bukatar ni zan shiga wanka, "ok shikenan Hakim nima bacci nike ji na wuce mu kwana lafiya angon gata".


"To goron gata, kaima ka yi fushi ka shigo layinmu a daina ce maka goro".


"Gaskiya ne Hakim tun kafin akawo Hakimar har ka fara kirana da goro ina da ka shiga daga ciki".?


Hmmmm! Abunda Hakim yace ma Aliyu kenan ya shigewarshi wanka yana murmushi, shi dai baisan dalilin dayasa yake san Aliyu yana yi mashi maganar Hakima sai yaji wani dadi wanda bai iya musulta irinshi.


Bayan ya fito wanka sallah yayi sannan yayi addu'oin bacci ya kwanta yana nishaɗa dan yana son a anbaci sunan Hakima gabanshi hakan na yi mashi dadi.








_By Jameelah Jameey✍🏻_



#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please


👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻



*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________



_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*






*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*


_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

```NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍```




75&76




_______________

Tunda Hakim ya tashi ya ansa kiran da Maimartaba Abdulmalak yake yi mashi, duk da yaji dadin yanda ya bashi umirnin ya shirya yaje Kano ayi duk wata al'ada da akeyi dashi amman kuma sai yaji ba dadi tunda Hakima ba sonshi take ba kuma bata ɗaukin zuwan nashi tunda ya dawo daga gidansu Hakima bata kirashi waya ba duk da yasan bata da numbers ɗinshi, amman ai ba zasu yi mata wahalar samuba tunda Maryam ƙawartace kuma Maryam tanada numbers ɗinshi kamar yanda su Maryama suke da duka numbers dinshi.


Bayan ya koma shashen shi ya ɗauki waya ya kira Aliyu yake gaya mashi ya shirya zasu biki, dan basu dawowa sai da Amarya, bai damu da duk saigantakar da Aliyu yake yi mashi ba ya tsinke wayarshi ya kira Maryam yace ta turo mashi number ɗin Hakima, Maryam taji dadi sosai da Hakim ya tambaye ta number ɗin Hakima,tasan cewa ko sunyi aure Hakim ba zai biye ma Hakima ba suyi ƙarantar da sukayi ba a school.


Tura mashi number din tayi sannan yace ta shirya zasu kano biki itada su Maryama amman kar ta kuskura tace dasu Maryama zatazo balle shi, haka ko akayi Maryam tace mata zasuzo biki amman itada wasu course mate ɗinsu zasuzo, tunda maryam ta gaya ma Hakima take murna dan itaji dadi sosai ta samu kawar shawara da ita ɗaya da Azima kawai take shirinta tunda babu age mate ɗinta a masarautar baki ɗaya.


Haka suka gama shiri suka ɗauko hanyar kano shida su Maryam.

___________


Yau tun safe bayi ke aiki tukuru saboda yau ake hawan daba, shiyasa kowa da yake masarautar ba zaune yake ba yana aikin da shuwagabannin bayi suka bashi.


Harta Hakima bata gida tana wajen make_up, kwaliya ake yi mata tana gani ta faɗa dan da ka ganka sai kasan kudi sunyi kuka bisa fuskar nan tata, yau su Maryam da wasu friends ɗinsu zasujo bikin, shiyasa tun safe bakin Hakima yake bude ta kasa kulleshi dan batayi tunanin Maryam zatazo mata biki ba, amman abun yayi mata dadi sosai.


bayan angama shiryata ta fito Amaryarta sak,marron material aka sa mata sai alkalbarta itama marron takalminta marron color ne dan kyai ko Hakima tayi shi dan ɓata lokacine wajen tsayawa na gaya maku kallar kyaun da Hakima tayi sai dai kuyi imaging da kanku 😛.


Angama haɗa komai yanda ya dace dan su Hakim su iso har abinci sunci a shashen Yarima Annas Hakim da Aliyu suka sauka dan nan zasu zauna har agama hidimar bikin baki ɗaya sanann, Yarima Annas da kanshi ya kai su Maryam Shashen Hakima sunce abinci sanan sukayi wanka suka hau kwaliya suna cikin yin kwaliya Hakima ta shigo hauka ne kawai batayi ba san murnar ganinsu da tayi, bayan sun gama kwaliya suka jera suka fito da amarya dan kowa ya hallara banda Amarya.


Tun daga nisa Hakim yake kallon Hakima yana gaya ma Allah, dan tunda yake a duniya bai taɓa ganin mace mai kyau ba kamar Hakima, dan komai nata daban yake dana sauran, haka dai har suka iso wajen da zasu hau dokuna ita da Hakim suyi yar rere.


Hakima keda farin doki Hakim yanada bakin doki, kasa hawan dokin Hakima tayi, tayi kokarin taga ta hau amman ta kasa, Koda Hakim yaga ta kasa hawa sai ya sauko daga bisan nashi dokin ya je wajen Hakima dai dai setin kunnanta yace mata, "Idan kinsan baki iya hawa ba ai sai kice a taimakamaki yan mata, ba sai kinyi nukunuku ba."yace yana kashe mata ido ɗaya.

Bata ankara ba taji mutun ya ɗagata sama ya ɗaurata bisa dokin yana ɗage mata gira ɗaya yana mata nuni da shine boss, wata kunya da takaici ya turnike Hakima wai ita Hakim zai ɗauka, sai kace wata ƙawarshi da zai ɗauketa kuma gaban su Yarima Annas da Maryam dan ya kama rainata, ita bama ɗaukarma dariyar da suke yi tafi bata haushi dan suka ƙara koɗa mashi kai, bayan ya ɗaurata shima ya sake hawan nashi sannan akayi masu counting one-three sannan suka ba dawakansu wuta.


Hakim abun mamaki ya bashi yanda Hakima ta zage tana san ta wuce ita a dole ta yo na ɗaya ba Hakim ba, shikuma Hakim daya ga haka sai ya ƙara ma dokinshi wuta in munite ya taddo Hakima kallon-kallon suke ma junanshi na Hakim yace mata, "Yarinya ke nemi alfarma a ɗaga maki ki wuce dan wannan wasan na jarumaine ba na ƙanannan kiyashi ba."gwallo yayi mata sannan ya rage gudun nan Hakima ta wuce tayi na ɗaya, nan fa ƙawayen Hakima suka hau murna sunyi na ɗaya, bayan sun gama hawan dawakan akaci abinci kowa ya wuce masaukinshi.



Bayan Hakim ya huta ya ɗauko wayarshi ya lalubo number ɗin Hakima, ya daɗe yana kallon number sanann daga baya ya fara tura mata textmassege kamar haka👇.

_"Yarinya ki fara shirya zama da maƙiyinki, dan kinsan Yarima Hakim ba sonki nike ba kuma kinsan ke ba zaɓi na bace, nan gaba zaɓi na zata shigo ku zauna da ita dan haka take note."_

Tunda shigowar massege ɗin a wayar Hakima ta ɗauka ta karanta bada damu da abunda Hakim yace mata ba dan daman tasan ba son juna suke ba, dan haka itama ta mayar mashi da answer ɗinshi dan bata iya ɗaukar gaya magana marar dadi.

_"mtssssss, daman wa ya gaya maka ana sonka, kaima ka shirya zama da maƙiyarka wanda bata sonka bata kaunarka kawai biyaiya zatayi ta aurenka, kuma in katashi ba ɗaya ba ka kawo uku bayan ni duk matsalar ko baka san sai ana son mutun akeyin kishinshi ba to ni bani sonka balle nayi kishinka take note, sannan kuma kayi gaugawar goge number ta cikin wayarka."_

Shigiwar massege ɗin Hakim ya karanta take yaji baiji dadi ba ,da man shi yasan Hakima bata taba sonshi, daman yayi message ne yaga ko zata damu amman ga abinda ta mayarmai da answer, shi dai Hakim gashi nan dai dan baiji dadin jikinshi tunda Hakima ta turo mashi answer, kwaciya yayi yana juye juye dan da ya kulle idonshi sai ya hango daukar da yayi ma Hakima ya daura ta kan doki, ko kuma da ya kulle idonshi sai ya tuno fadan da sukeyi a school, murmushi kawai yake dan abun yana yi mashi dadi sosai haka dai bacci ya daukeshi.



Itama Hakima bayan ta turama Hakim da answer suka cigaba da labarin duniya ita dasu Maryama dan daman can sun san juna shiyasa, sune basu kwanta ba sai wajen biyun dare sanan ko wancansu ta kwanta bacci.



Yau za'ayi wanki, wani program ne da ake gidan sarauta mai suna *WANKI*, wanki dai suna nufin wankin lailen da akayi ma Amarya, dan haka da wuri suka tashi suka shirya ba ƙaramin kyau Hakima da ƙawayenta sukayi ba, karfe hudun rana aka fara gudanar da wanki, gaskia ko Hakima taga gata wajen wanki dan ba ƙaramin kudi a zubda mata ba sai mangrid sannan a ka tashi.

Wanka kawai Hakima tayi ta kwanciyarta bacci, duk da ba baccin take ba tunanin zaman da zasuyi da Hakim Yanzun yake neman hanata bacci gashi gobe ne ɗaurin aurensu, tuna message ɗin da Hakim yayi mata ya tada ma hankali batasan sanda hawaye suka fara zuba a idonta ba, dan tasan zata sha wuya wajen Hakim dan ma saukinta gasu Maryama nan da Sadiya tana da abokan ɗebe kewa, gashi yan jere sunjr sunce a shashe ɗaya zasu zauna da Hakim, harda haka yake ƙara tada ma Hakima hankali, parlour ɗaya ne babba sai bedrooms da suka zagaye da parlourn kitchen kuma ɗayane toilet ne kawai basu haduwa da Hakim sai bedroom dan suma ance suna da yawa a shashen nasu, haka dai ta kama juyi tanajin su Maryam suna lissafa kudin da suka samu yau wajen Wanki, har suka gama laissafi suka kwanta bacci amman ita idonta biyu tana tunanin rayuwar da zata shiga daga gobe.


Shima haka takasance Hakim, tunda suka dawo kasa cin abinci yayi yana mamakin yanda Hakima ta tsaneshi da yawa har haka, yana san kasancewa da Hakima inuwa ɗaya koda ko zasuyi faɗan dasuka saba, duk da yasan cewa ba sonta yake ba amman yana san yaganta kusa dashi, sai yanzun ya ƙara amincewa da kunnunwanshi da idanuwanshi suna son Hakima, amman zuciyarshi bata son Hakima, yana taƙaicin yanda ita Hakimar batajin haka a taitare dashi, da tana jin haka da tayi kishi jiya da ya tura mata message zai mata kishiya amman a banza ko a jikinta, daɗinshi ɗaya ma shashe ɗaya zasu zauna ma dole ne zasu ringa ganin juna ko wani lokaci bacci kawai zai rabasu ko wane zaitafi ɗakin baccinshi, a haka dai ya kama tunaninshi yana hangon kyaun da Hakima tayi wajen al'adar bikin nasu, duk da yasan cewa Hakima kyaukyawace amman tayi mashi kyau sosoi haka har bacci ɓarawo ya kwasheshi.


Yau masarautar kano ta fara sanin zatayi hidimar biki, dan sarakuna da yan siyasa yan kasuwa da duk wani mai faɗa a ji a nigeria sai da ya hallaci kano dan kawai ɗaurin auren Gimbiya Hakima da Yarima Hakim, da yake ɗaurin auren 1pm za'ayi shiyasa jama'a suke samun damar zuwa ayi dasu tunda ɗaya ne za'a ɗaura auren.


"Haba Hakima dan Allah ki tashi ayi maki make-up ɗin nan kinsan one za'a ɗaura wannan auren naku kuma gashi yanzun 12 tayi amman kinƙi tashi ayi maki make-up haba please."


Itadai Hakima bata ce ma Maryam komai ba, sai dai ido ta tabita dashi, kuma bata tashi ba, ji tayi an bugar mata cinya sannan tayi ajiyar zuciya tana cewa, "Maryam wallahi banson auren nan, banson Hakim kinfi kowa sani bansan ya zanyi ba."


Ta sowa Maryam tayi ta zauna kusa da Hakima, tana zama su Maryama na shigowa suma direct wajen suka zauna dan sun san komai suma, dafa ƙafarta sukayi su duka ukkun sannan Sadiya ta fara magana, "Hakima munsan cewa baki san Yaya Hakim, amman kisani Yaya Hakim yana sonki yana kaunarki, Yaya Hakim yana yi maki so wanda har yanzun baisan adadinshi ba a cikin birnin zuciyarshi ba."


"Ta..., "dakata Hakima mu gama gaya maki waye Hakim, da mai-da mai Hakim yake so da wanda bai so, koda baison ki idan kina yi mashi abubuwan da muka gaya maki wallahi zaki juya Yaya Hakim kamar ranwa, Hakim zai zama mijintane daki juyashi yanda kike bukata, domin zai soki kamar ranshi, amman idan kinbi shawarar da muka baki."


"Yaya Hakim mutun ne maison a girmamashi, yana son kwaliya more expecially yaga kinsa jan baki, yana son yaga mace yar'kwaliya da kisisina da shagwaɓa, baya cin abincin bayi dan haka ki shiga da niyar ke zaki ringa yi ma mijinki sauwa , ki tabbbatar da ke gwanace wajen iya girki da kwaliya, Hakima tsafta tana gaba wajen sace zuciyar ɗ'a namiji yanga da jan aji ko yayake ko, dan kitson nan da kunshi zu zama abokanarki Hakima suma suna ƙarama mace martaba a wajen mijinta, ki rige Ibada da neman tsarin wajen ubangijinmu Allah, wallahi Hakima idan kika rige abubuwan da muka gaya maki sai kinzama zara a wajen Yaya Hakim, sannan naji watarana a lambu yana gaya ma Yaya Aliyu idan mace na cin chingum tana taso mashi da shi'awarshi dan haka sai ki tafi da kwalin chigum, wannan zaman da zakuyi ki kasance mai yawan cin chigum amman a gabanshi kina sa ƙananan kaya masu masifar ɗaukar hankalin ɗ'a namiji zaki sha mamakin yanda Yaya Hakim zai nemi ku sasanta kanku ku zauna lafiya mudai muna maraba dake muna kaunarki a matsayinmu na ƙannan Hakim."


"Nagode sosai Sadiya, kuma insha Allah zanyi duk abunda kuka gaya man, amman mai Hakim yafi so wajen abinci."?


"Yafi son tuwon shinkafa miyar kuka, sannan kuma yanason dambu sosai, "nagode Allah ya bar zuminci, "Amin ya Allah Hakima, ku taho ayi make-up ɗin sha-biyu da rabi har tayi fa."

Nan aka yi ma Hakima kwaliya, wata atamfa tasa mai ratsin ja da baƙi atamfar tayi mata kyau sosai, sannan ta ɗaura alkarba sama ana ɗaura aure za'a tafi da amarya gidan mijinta, shiyasa ta shirya.


Kutsawa nike cikin mutune dan na kwaso maku rahota wata kallar kwaliya ango Hakim yayi, wai na samu na ganoshi shida friends ɗinshi, farar shidda yasa tasha aiki masha Allah ga babbar riga duk ya ɗaura a bisa rigar aikin ɓakin zare aka yima atamfar abundai masha Allah kawai zamuce.


Da kaga Hakim kaga ango dan bakinshi yaƙe kullewa dan murna, dan koshi kanshi yana mamakin yanda yake farin ciki har haka sai kace wanda zaiyi auren soyayya, amman shi yasan yau babbar ranace a wajenshi, ya rasa yanda zaisa kanshi dan murna duk da tsokanarshi da Aliyu yake amman bai damu ba shidai ya kosa ma a ɗaura auren bak ɗaya, dan ji yake inama ya matso da time ɗin.




Hausawa sunce rana bata karya sai dai uwar ɗiya taji kunya,

Please Login or Register in order to submit comment