Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan karuwai ne fa"
Ji tayi jikinta yayi sanyi dan ya fada gaskiya kumawa tayi cikin motan ta zauna amma ta kasa magana shima beyi magana ba
Tunani take yanzin wata sani da zataje gidansu ta zauna dan a gaskiya se yanxin taji bazata iya zama a gida ita kadai ba kaman karuwa
"Naji kinyi shiru" ya katseta
"Uhmm, kasan pawa road koh" daga mata kai yayi
"Yawwa tou kaini can" abunda yazo mata kenan kawai taje gidansu Zulaihat dan babu wanda ze taba tunanin tana can kuma tanada tabbacin cewa key na gidan sannan tasan Umma bata zuwa gidan dan kullum tana gida sede wata rana ta leka bakery nata

Tafiya suke sunyi nisa amma wani gefe a zuciyanta yana hanata zuwa gidan batasan dalili ba
Wayanta ta ciro tana kalla a zuciyanta tace dama tanada wani a garin nan da gunta zata
Kawai se tularh ta fado mata Allah sarki tun rasuwan kakanta babansu ya kuma sama aiki a india basu sake dawowa ba
Suna isa tamai kwatancan gidan har kofan gidan yakaita ta bashi kudinshi tare damai godiya ya fito mata da kayanta sannan yaja motanshi ita kuma taja akwatin a bakin kofan ta tsaya ta kusan 20mins seta durkusa hannunta takai karkashin gate din danta taba ganin Umma na ajiyewa agun cikin ikon Allah seta sama wani dadi ne ya ziyarci zuciyanta bude gate din tayi taja akwatin tayi shigewanta

Parlon ta bude tana shiga ko'ina a gyare yake tsab kaman akwai mutum a gidan
Ajiye akwatin tayi seta kunna panka ta zauna akan couch dan kishingida tayi bata dade ba bacci yayi gaba da ita

_30mins later_
Ta mike wanka takeson yi amma wai ita bazata iya wanka a gidan ba ga kuma wani yunwa da take
Daga bayade indomie ta dafa tasha ruwa ta kuma ta zauna tana danne-dannen waya

Can gefansu Zulaihat kowa kowa yayi gungum-gungum barin ma Umma da ji take kaman ta kurma ihu
Mommy na zaune a parlo seta mike ta shiga dakin Umma ta tarar da ita tana hada kayanta
Da mamaki ta karasa gunta "Lafiya ina zaki??"
Kallonta tayi seta cigaba da hada kayan
"Gida zan koma. Dan wanda nazo saboda ita itama tabar gidan"
"Haba Umma Zulaihat dinfa? Do you want her to feel kaman kin dena damuwa da ita Dan Allah kiyi zamanki dan bema kamata ba ki zauna ke kadai a gida"
Lallaminta taketa yi dakyar ta yarda. Mommy tamaida mata da kayan
Zulaihat kowa tana can dakinta tasa tv a gaba amma ba kallo take ba she is feeling guilty dan tasan duk halinda Umma ke ciki yanxin is her fault da bata kula Fee_feey ba da tana gidan yanxin
Gani tayi zaman gidan ze haifar mata da wani abu seta shiga shiryawa tana gamawa ta wuce asibitin su dan ya fiye mata

_Two days later_
Kwanan fee_feey biyu kenan a gidan tana zaune daga indomie se drink take ci a gidan batama damu idan Umma ta dawo ba zata gane mutum ya zauna a gidan
Online ta hadu da wani yake mata tallan wani daki amma na yan makaranta ne dan haka tace bataso
A yau take shirin barin gidan ta gwanmace ta sama daki a hotel ya fiye mata

A kwana biyun da tayi saurayin nan ya kirata amma sau daya ta dauka suka gaisa daga nan idan ya kira bata dauka kuma ta sani sarai shine dan a lokaci daya kuma seya fara bata haushi dan haka bata dauka ma kuma batama san sunanshi ba dan randa sukayi waya yake tambayanta sunanta kawai se tayi hanging up dan iskanci irin nata ita bata san dalili ba abunda ta sani shine sanda ta ganshi yayi mata kyau kuma ya burgeta

Tana gama shirinta ta fito daga gidan haka tabarshi kacha-kacha ko wanke plate dinda tayi using batayi
Tana kulle gidan ta maida keys din inda ta gansu ta fito ta dade a tsaye a bakin gate din ko zataga abun hawa amma bata sama ba dan haka seta gangaro saboda ta fita titi haka ta ringa tafiya tana jan akwatin nan duk ta gaji
Harta iso titin napep kawai take gani babu taxi kwata-kwata badan taso ba ta tara
"Mallam dan saka min kayan a trunk"
"Trunk" ya maimaita
"A boat din idan bakasan trunk ba!!"
"Ranki ya dade ae babu boat a masin din sede na saka maki a bayan sit din"
Kallonshi tayi alaman tana jira ya fito ya saka mata shi kuma daya gane shiya fito ya tura mata sannan ta shiga
Yanayin shigan da tayi ma kowa yasan bata taba shiga ba
"Mallama ina zankaiki?"
"Ka dena cemin mallama kaman ka ganni da hijab"
"Yi hakuri ranki ya dade"
"Lawiza hotel zakakaini"
"Toh an gama" seya tada masin din suka fara tafiya ita kowa rike karfan gaban tayi gagam dan ji take kaman zata fada waje

Suna isa ta fito shima ya ciro mata akwatin ta bude wallet dinta yan dari biyar-biyar ne kawai a ciki sababbi ta zaro daya ta mika mai seta ja akwatin zata wuce
"Ranki ya dade!!" Me napep din ya kira da sauri juyowa tayi a hankali fuskanta a daure
"Lafiya?"
"Aa daman chanji ne baki amsa ba"
"Msteww. Toh rike" ta cigaba da tafiya
Seda yaga tayi nisa "Mstewww kede kika sani mutum se fada ae idan kikayi kwantai zaki ringa ma mutane fara'a yaja napep dinshi ya tafi
(Nace ji bawan Allah ina ruwanka)

Tana shiga gun receiptionist din ta nufa ta fadan mata tana son daki daya for one month
Matan tayi mata lissafin kudin nan take ta lalo ta bata sannan ta mika mata keys din ta wuce

Tana shiga dakin its already prepared a bakin kofan tabar akwatin ta tube tsindir seda ta shiga toilet sannan ta saka towel ta shiga wanka
Ta dade sosai tana gamawa ta fito kayanta ta bude ta ciro wani top irin dugan nan me zuwa har gwiwa ta fito dashi
Shafa mai tayi sannan ta ta saka inner wears ta fashe jikinta da turare kaman zata fita ita yarinyan akwai tsabta ne
Tana gamawa ta saka top din sannan ta haye gado ko tunanin sallah batayi ba baccinta ta shigayi hankali kwance
***

Hydar ne keta faman shiri wai zashi gidansu fee_feey ganin Zulaihat
Cikin wani white kaftan da black hola yayi kyau ya fito se kamshi yakeyi
A parlo ya tarar da Mommy yayi pecking nata yace mata zashi ganin Zulaihat tamai Allah kiyaye sannan ya fiti da wani jaka irin na kwalin nan a hannunshi tsaraban Umma ne da Mommy dan yasan yanzin Zulaihat tayi fushi dashi dukda laifinta yake gani saboda tun randa ya gayan mata he have fallings for her da tayi hanging up on him basu sake waya ba
Bude motan yayi sit din baya ya saka seya shiga gaba ya tada motan
Fitowa yayi daga gidan ya kama hanyan gidansu Zulaihat (as in gidansu fee_feey kenan)

Zulaihat kowa tana tashi tun karfe 6:00am ta bar gidan hospital dinda take aiki ta nufa dan abokiyar aikinta wato Safieyarh tanata kiranta

Tana isa wata mata aka kawo masu hospital din zata haihu kuma gashi duk doctors din basuzo lokacin dan haka dole sesu biyu zasu amsa haihuwan gara ma Safieyarh ta taba amsan haihuwa amma Zulaihat bata taba bah

Sun dade akan matan amma ta kasa haihuwa dakanta saboda haka Zulaihat tace ayi _inducing_ nata basu wani dade ba baby ta fito kyakkyawa abunta
Zulaihat tana ganinta tace
"Awwn she's so cute" ta riketa tana murmushi bata damuda jinin dake jikinta ba dan ita tanson babys sosai

_Some minutes later_
Aka gyara baby da mamanta sannan aka barsu dansu huta
Itama taje ta gyara jikinta ta fito tana kallon wani file alaman sauri take ta shiga wani daki wani karamin yaro ne patient dinta ne yau kwananshi biyu da kawoshi asibitin ya sama infection ne a kidney nashi

Tanason yaron ji take like the brother she never had so tana kula dashi sosai danshi ma take yini a asibitin yanxin
*****

Yana isa yayi horn gateman ya bude mai seya shigo yayi parking fitowa yayi yana cire shades din idonshi seya kama hanyan shiga cikin gidan
Wani kofa ya gani alaman shine hanyan shiga gidan dan haka ya shiga da sallama

Sallama daya biyu yaji an amsa dan haka ya shiga ciki sosai wata mata ya gani tana zaune wanda ya tabbata itace Mommy fee_feey idan be manta fuskan ba
"Bismillah" ta fadan mai dan haka seya shiga parlon ya zauna kan couch se kuma ya sauko yadan rage tsayi ya gaidata fara'a sosai a fuskanta ta amsa sannan ta bashi izinin ya zauna
"Sede ban gane fuskan ba"
Murmushi yayi "Hydar ne classmate din Zulaihat da fee_feey"
"Ohhh Allah sarki se yanxin na gane ya kuke? Ya kuma karatu? Da fatan yanxin an gama?"
"A na gama yanxin ma na fara aiki"
"Toh Allah sanya alkairi ya bada sa'a"
"Amiin"

Se sukayi shiru can tace "gashi kuma duk basa nan Zulaibat tana gun aiki"
"Daman gun Umma nazo" yana magana yana susa keya kuma karya yayi yazo ganin angel nashi ne

"Toh shikenan barin kirata" ta mike tasan definately gun Zulaihat yazo but abunda yayi ya burgeta dabe nuna gun nata yazo ba



☆☆☆★★★
[18:30, 4/18/2017] Tyetyelorh-❣: Tana shiga dakin Umma ta tarar da ita as usual tana kwance tana kallon celin dan tun barin Fee_feey gida haka ta kuma ko dan hiran da takeyi ta dena ta kuma so quite
"Umma kizo kinyi baku" shiru taji dan haka ta matsa kusa da ita ta dafata se alokacin tasan mutum ya shigo cus furgitan da tayi

"Habah Umma dan Allah ki rage wannan tunanin da kikeyi kinsan fa kinada nalura kuma duk inda fee_feey take insha Allah tana lafiya kuma Allah na kare mana ita so please ki rage kinji"
Nodding tayi
"Yawwa tou kinada baku dan Allah ki fito" sake nodding tayi sannan Mommy ta fito ta shiga dakinta

Se bayan like 5mins sannan Umma ta mike ta saka hijab ta fito
Tun daga nesa ta hango wani saurayi amma ta baya ta ganshi
Shiga parlon tayi sosai ta zauna shi kuma ya sauko daga kujeran ya gaidata
Amsawa tayi fuskanta ba yabo ba fassala dan bata gane wayeshi ba
Kumawa yayi ya zauna can yace

"Umma, Hydar nefa"
A lokaci daya seta saki murmushi
"Laa Hydar ashe rai kanga rai ya karatu ya hidima?"
"Lafiya klw wlh"
"Hydar!!" Ta sake kiran sunanashi "kai naji dadin ganinka yaushe ka dawo? Bade se yanxin ba tun tafiyanka?"
"Wlh Umma se yanxin"
"Gaiskiya ka dade ba kadan ba gara ma su Zulaihat suna zuwa amma kai se yanxin. Ina fatan yanxin an gama komai?"

"A na gama yanxun na dawo nan ne a Nigeria nakeson bude company na shiyasa"
"Aa abu fa yayi nisa. Allah ya bada sa'a ya hadaka da employees na gari"
"Amiin Umma"

"Umma ashe haka abun ya faru"
"Hmmm Hydra ashe kaji labar.......-" kawai seta fashe da kuka daman kadan take jira
"Subhanallah Umma meyafaru did i say something wrong am very sorry"
"Hydar ba kaibane. Wlh duk wanda yamin abun nan ban yafe mai ba i really love her but she is still not ready to accept me as her mother Whats wrong with me?" Seta sake sakin wani kuka

A rude ya mike yayi gunta ya durkusa "Umma dan Allah kiyi hakuri ki dena kuka and lets talk about it please" dakyar ya samu tayi shiru
"If you are ready we can talk about it"
"Hydar, fee_feey really hate me like hell i have no idea what i did wrong to deserve this am trying my very best as her mother but she keep on rejecting me"
Tana magana har a lokacin bata dena kuka ba
"Umma yanxin tana ina?"
"Babu wanda yasan inda take Hydar tabar gidan ni saboda ita nazo ku zamu shaku amma ta hada kayanta ta bar gidan ko kudi bata dashi ni abunda nake tsoro karta shiga duniya ta zubar da mutuncinta"
"Ki kwantar da hankalinki i know fee_feey she won't do something that stupid"
Lallashinta ya ringayi yana kwantar mata da hankali kaman Mamanshi har tayi shiru
Can suka fara hira sama-sama amma shi yanason fadan mata yanason turo magabatanshi amma yana jin hauyinta sosai

"Hydar ya naga ka sauya kaman akwai abu a bakinka"
Murmushi yayi yana susa keya se Mommy ta shigo da plate a hannunta ta daso inda yake da sauri ya mike ya amsa ya kuma ya zauna
Murmushi Mommy tayi tace "baki gane abunda yakeson fada bah" tana magana ta kallonshi
"So yake ya tambaya diyarki"

"Mommy bafa haka bane"
Murmushi Umma itama tayi tace "toh meye idan ba haka bane se yanxin na gano" shiru yayi kanshi a kasa

Hira suke sosai abun sha'awa wani seya rantse da iyayenshi yake amma kuma ya kasa fadan masu abunda ya kawo shi daga baya ya mike ya kawo masu tsaraban daya kawo masu sannan sukayi sallama ya tafi har waje suka rako shi

Ashe Zulaihat ta dade da shigowa anjuwan nasu seta shiga makutansu akwai wata yarinya Hawwatiee a gidan suna shiri da ita
Yana fita ko barin layin beyiba itama ta shigo gida da motanta tana parking ta fito da handbag nata
Tana shiga parlo wani kamshin turare taji wanda bazata taba mantawa dashi ba a rayuwanta
"Hydar!!!" Ta fadi tana juyawa
Umma ce ta fito daga kitchen da cup a hannunta tana shan ruwa taga Zulaihat a parlo duk a rude

" _Zulaihatou!!!_" Umma ta kira sunata tana karasawa gunta
Juyowa tayi tace "Uhmmm"
"Yaushe kika dawo?"
"Yanxin na shigo. Umma waya fita daga gidan nan yanxin?"
"Hydar ne yazo"
"Hydar!! Wannan Hydar din?"
"Jimin yarinya Hydar nawa kika sani? Wannan de shine yazo"
"Meya zoyi?"
"Hala yar jarida kika zama nima bansani ba"
"Wai Umma kece yau a parlo"
"Aradu kika sake min wani tambaya zan mangare ki"
Dariya Zulaihat tayi "habah Umma na me kike sha"
Juyowa tayi tayo kanta zata daketa seta shige dakin Mommy aguje tana dariya
Itama dariya tayi ta zauma a parlo tana kallo
*****

Fee_feey tana tashi daga bacci brush tayi ta sama wani cake a fridge din hotel din ta zauna taci iya cinta sannan ta fito da sauran kudinta tana kirgawa
Saura 30,500 tsaki taja saboda tanason ta fara designing takalma dan tun tana karama take zanawa a papers kuma gashi kudin bazasu isheta ba

_Two weeks later_
A yanxin Umma ta sake jiki sosai amma kullum setayi tunanin halinda yarta take ciki
Hydar kowa sun sama filin da zasuyi building company dinshi agun amma a Abuja ne daga farko cewa yayi baya so amma Daddy ya bashi shawara seya yarda a yanzin har an fara ginin sannan ya fara neman employees din

Ya saka Daddy a gaba wai seya je ya neman mai auren Zulaihat
Dan haka suka shirya shida amininshi sude uku suka tafi da kudin gaisuwa
A lokacin Zulaihat bata nan dan haka suka sama Daddyta da Mommy se Umma
Aka gaisa suka gabatar da kansu sannan suka fada abunda ya kawo su

Daddy yayi shiru danshi besan idan tanasonshi ba dan beda sha'awan yima yaranshi auren dole
Mommy da Umma ne suka ce zasu tambayeta abunda tace zasu nemesu a haka suka tafi kan cewa nan da sati daya zasu nemesu

Fee_feey kowa yanxin an fara desingn takalma irin hills din nan suna kyau sosai ba laifi kuma irin masu tsadan nan ne
Sunan designer ta _Fee _feey_ amma abunda bata gane ba shine maimakon ta ringa samun riba kullum kara kasa takeyi abun na damunta
A yanxin ta kusan gama law school dinta dan saura one month ta gama baki daya gashi ta gaji da hawa napep
Wani dare tana kwance se wayanta yayi ringing idan bata manta number tasan number wanda ya taba bata lift ne
Seda ya kusan tsinkewa sannan ta dauka amma batayi magana ba
"Hello" aka fadi ta daya bangaren
"Uhmm" kawai ta fadi
Gaisawa sukayi sosai tun tana basarwa harta saki baki sunata hira seya tambayeta sunanta
Kaman bazata gayan mai ba tace _Firdausi_ amma ba kowa ya sanni dashi ba ko'a school _fee _feey_ nake using
"Yau nayi sa'a an fadan min sunan. Ni kuma sunana Ammar"
"Okeyy" kawai ta fadi
"Daman ni seriously tun sanda na fara ganinki na fara sonki and serious relationship nake so wanda zamuyi aure"
Wani dariya ya subuce mata amma bata bari yaji ba

"Lemme tell you this. I don't want to hurt you but am not your type cus idan mukayi wani relationship at the end you are the one that is gonna get hurt and i don't want that"
"Hurt" ya fadi alaman be gane ba

"Yeah. So thank you" bata bari ya sake magana ba tayi hanging up tama kashe wayan baki daya
Ita a gaskiya yana burgeta and she's ready to give him a chance and zata iya aurenshi but batasan daga baya yazo ya gane she's not into _guys_ and tasan she's gonna hurt him
Wani tsaki taja seta mike



IG.Tyetyelorh
[23:37, 5/8/2017] ‪+227 90 29 04 44‬: [19:25, 4/13/2017] 1D-Tyetyelorh-❣: ☆☆☆★★★

🌹ZULAIHATOU🌹

Na Tyetyorh

🌹🌹🌹


*175*

Yana shiga da Hydar ya fara karo
Kallonshi yayi da mamaki
Shima juyowa yayi se yace "Daddy harka iso"
Wani huge Daddy ya kaimai "yaushe kazo shine baka kirani nazo na daukeka ba"
"I wanted to surprise you guyx kuma na taho da motana shiyasa"
"Well am so happy you are back, kaga daman jiranka kawai akeyi dan tuntuni suka baka aikin amma a Abuja zakayi"
"Daddy no need ni zan bude nawa company cus bazan iya zama ina aiki karkashin wani ba"

Dariya dukkansu suka saka "Toh Allah ya sanya Alkairi ya baka ikon yi"
"Ameen suka amsa"
Daddy yace "Amma kafin nan hutawa zakiyi?"
"A toh, yanxin de ana neman min filin da zamu jinin building din but before then hutawa zanyi"
"Allah sanya Alkairi"

_30 minute later_
Ta gama hadawa suna zaune a kan dining suna ci Hydar yace
"Yawwa Daddy daman inason muyi wata magana" yana magana yana goge bakinshi
"Am all ears"
"Maganan Zulaihat ne inson a neman min aurenta"
A lokaci daya kawai se Mommy ta kware hannu tayi sauri tasa ta tare bakinta
Daddy kowa kallonshi kawai yakeyi
"Hydar are you kidding" Mommy ta fadi dantayi mamakin abunda yace

"Noh Mommy meyasa kika ce haka"
"Well tun tafiyanka ka nemeta? Ka taba kiranta a waya? Yanzin fa Zulaihat is 22 tana gab da shiga 23 and you think batada mijin da sukayi alkawarin aure dashi"

Kallonta kawai yake se yanzin yayi tunanin abun shima, se yanxin yayi tunani maybe she is angry with him dabe nemeta ba. Amma itama ya kamata ta nemeshi ae shi daya yaketa tunanin nan a zuciya can seya kalla Mommy yace "Mommy i trust her, We made a vow to each so karki damu"
"Toh shikenan Allah bada sa'a" ta cigaba da having lunch nata
"Ameen" shida Daddy suka fadi
Suna gama ci suka dan taba hira kadan seya mike ya dauka key din motanshi ya fita
Wani katon akwatuna ya shigo dasu su biyu agiye daya daga cikinsu yayi a gaban Mommy data dawo parlo ta zauna bayan takai dishes din kitchen
"Mommy ga tsarabanku keda Daddy"
"Inyee dukka Allah maka albarka ya baka mata nagari"
"Amiin, wannan kuma na Zulaihat ne " yana magana yana kokarin jan akwatin wanda yama fi nasu Mommy girma
Murmushi tayi tace "yar gata kenan"
Suka shiga budewa itada Daddy kayayyaki ne kala-kala a ciki duk nasu
Shi kowa dakyar ya haura dana Zulaihat sama ya ajiye a gefan gadonshi seya shiga wanka
Already Mommy ta gyara mai dakin gabadaya se kamshin turare yake kaman tasan ze dawo
Yana gamawa yayi combing gashin shi seya shafa mai ya saka wani three quater wando babu riga a jikinshi (God am really crushing on him)
Packs nashi suka bayyana sun kara girma (hangosu kawai nake aradu)

Wani karamin remote ya dauka naga yayi pointing gun window dakin inda labule yake se naga sun kulle da kansu dakin yayi duhu kaman dare
Seya kunna Ac kawai ya fada kan gadon wani bacci ne ya daukeshi a lokacin

Se kusan 6pm ya tashi alwala yayi se yayi sallah sannan ya saka wata jallabiya ya sauko kasa babu kowa a parlo seya sama waje ya zauna ya dan kwantar da kanshi a jikin couch din da remote yana chanja channel amma hankalinshi bema kan tv kawai chanjawa yake yana nan yana tunanin Zulaihat dinshi cus he missed her like crazy
******

Itama tana zaune a kan gadonta shi kawai take tunani wayanta ta dauka se tayi typing number shi dan baxata taba manta number ba a rayuwanta saboda shine password nata na abubuwa kala-kala da kuma sunanshi

Tana gama typing se kuma ta tsaya tana kalla can tayi saving number kawai tana kallon wayan ne se taji an banko mata kofa tana daga kai taga Fee_feey
Seta maida kanta zuwa kallon wayan da takeyi
Dan ita tension dinda ke damunta yafi duk abunda fee_feey tazo dashi

Gabanta tazo ta tsaya amma da taga bata dagu ba se abun ya bata haushi buge wayan da take kalla tayi ya kuma gefe guda
Daga kai Zulaihat tayi ta kalleta se kurum ta mike ta bar mata dakin gabadaya
Ita kowa abunda ya bata haushi kenan ta shiga hargitsa mata dakin
Dayake babu kowa a gidan su biyu ne kawai ita Umma ta tafi bakery nata while su Daddy suma sun fita

Saukowa tayi ta sama waje a parlo ta zauna se Fee_feey ta sake biyota a gabanta ta tsaya
"Ke!!!" Ta kira ta a tsawace
Shareta tayi bata kulata ba
Seta dungure mata kai "Dake fa nake magana wlh yau-"
Bata karasa ba taji ta hankada tayi baya ta nunata da dan yatsa
"Fee_feey na gaji da abunda kike min ki fita daga harkana and mind your business please"
Seta kama hanya zata wuce
Hankadata back fee_feey tayi"How dare you zaki tureni low class bitch"
"Low class bitch" Zulaihat ta maimaita seta dawo tayi wani murmushi
"Tell me a cikin nida ke who is the real low class here am so tired of you i have been ignoring you but you still don't understand toh barin fito maki yadda kikeso, Fee_feey all this belong to me. Mee. gayan min who is the real daughter? Me, na gaji da abunda kike yi a gidan nan fisabillilah ji yadda Umma ta rame kaman ba ita ba kawai duk saboda ke kin gama sakata a damuwa Mommy ma haka ku kulata kin denayi and kalla Daddy dan Allah abunda kikeyi kin kyautawa kenan. Am just doing you a favour amma ranan da zaki kaini bango wlh i promise you sena fadan ma kowa who you really are sena gayan ma kowa ke gay ce" tana gamawa ta haye sama

Ita kowa Fee_feey tana tsaye a gun ta kasa motsawa ta janyo ma kanta dan tasan duk abunda Zulaihat ta fadi is all true itama ya kamata tayi accepting cewa she's not the real daughter
Kuka kawai ta sake yanxin harya kai a ringa mata gori kukanta ta ci daganan ta mike wai zata bar gidan tana shiga dakinta su Mommy suka iso dan sun biya sun dauko Umma

Kayanta ta shiga hadawa ta deba kusan rabi sannan ta dauko wallet dinta ta saka a handbag nata da key din motan ta
Wani gyale ta yafa ta fito tana jan akwatinta
Tana zuwa gun kofan parlon taci karo dasu Mommy daure fuska ta sakeyi tana neman hanya da zata wuce
Riko hannunta Daddy yayi"Fee_feey ina zaki"
Fashewa da kuka ta sake
"Zan bar maku gidan ne kuda yarinyanku seku cinyeta am tired na gwanmace na zauna ni kadai akan na cigaba da zama a gidan nan"
Mommy najin haka ta matso kusa da ita"why are you saying this bayan fitan mu meyafaru"
"Why don't you go and ask your daugher" tana fadi ta fuzga hannunta zata wuce
"Fee_feey" Umma ta kira sunanta a hankali kaman zatayi kuka. Dakatawa tayi amma bata juyo ba
"Am begging you fee_feey dan Allah badan ni ba karki bar gidan nan please"

Juyowa tayi a hankali tayi mata wani disgusting look sannan ta cigaba da tafiya tana jan akwatin
"Fee_feey!!" Aka sake kira amma a tsawace wannan karan Mommy ce
"Karki kuskura ki fita kina fita wlh---"
"Zakiyi blocking credit card dina kuma ki amshe keys dina koh" ta katseta
Ajiye akwatin tayi seta bude wallet dinta ta ciro credit card din sannan ta dauko key din ta wulla mata "Gashi no need ki amsa after all it all belong to your daughter not me And insha Allah zan sama sana'a na nakaina i will take care of myself and bazan dugara da kowa bah"
Daukan akwatin tayi ta fice Umma ce tayi sauri ta bi bayanta cus she can't bare losing her daughter
Suna fita ta riko mata hannu "Let go of me" ta fadi ta fuzga hannu da karfi
Hawaye ne ya fara zubu

Please Login or Register in order to submit comment