Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wajenta ta nufo tace bari na Fara cin uban Uwarki me warin tafarnuwwa tukun tayi wani mugun tafiya da Babar Maheera Kamar guguwa ta hada kanta da bango,ji kake kummm ta shaketa ta dinga jijigata ta jefar da ita a kasa,Maheera zata gudu tayi kanta Ahsan ya riko Cele ta juyo ta Kai Masa duka ya saketa ba shiri ta damko Maheerah ta gwarata da bango nan take ta Fadi ta sume sabo da kanta ya bugu Kuma cele bata hakura ba ta haye ruwan cikin ta tana dukanta baban Maheerah yazo zai masge Cele Ahsan ya rike hannunsa da sauri cikin larabci yace karka sake ka taba ta dashen ciki tayi mata ba izininta kuma budurwa ce bata San Namiji ba Kuma kudin Dana bata ko kwandala bata bata ba ai zalunci ne wannan, Baban Maheerah ya fisge hannunsa yace sai me akan anyi Mata dashen ciki wasu ma suke zuwa suna karuwanci su haihu bare dashen ciki,ita wacece bakar fata da ita bayi,Cele tashi tayi daga Kan Maheerah ta shatulo kafafun Baban Maheerah dake banbamin masifa ya Fadi kasa tim yaji targade a kafarsa, Ahsan ne ya rike ta ganin duk ta haukace tana ta kuka tana kwacewa tana fisgewa taga Babar Maheerah ta tashi Zata sake masgeta ya riketa sosai Yana lallashinta ya rungumeta sosai a jikinsa yana lallashinta,Kansa ya Dora a dokin wuyanta yana lallashinta Yana Bata hakuri,Babar Maheerah ruwa ta samo ta kwarawa yarta ta farfado Suka tashi jiki ba kwari da kyar Baban Maheera ya iya tashi Suka mike a gigice Suka bar gidan gaba daya.

Ahsan sai da ya lallashi Cele ta dan daina kukan sannan ya shirya ya rubuta takardar saki ya tafi gidan su Maheerah zai Kai misu,Yana tafiya kuma Cele ta tattara nata ya nata kaf ta Masa rubutu da hausa normal ta ajiye a kujera, ta shiga dakinsa ta Bude inda yake ajiye kudade ta iba zasu Kai dubu dari uku a nan Nigeria tayi tafiyarta ta bar gidan,tana Fitowa Mota ta shiga taxi tace a kaita garin Makkah tasan acan Inshaallah zata hadu da hausawa Kuma Nigeria zata dawo baza ta zauna a Saudiya ba ta Gama Zama a Saudiya har abada, so take tana zuwa ta samu me wuce Mata gaba ta dawo Nigeria ko taga Kaka ko Bata ganshi.

Mairo Kuwa watan yarta biyar a duniya baza ma ta bari ta yaye ba akace ga wani balarabe amadina yake zaune bakar fata yake Neman Dan yemen ne zai biya kudi harda sarkar Gold,nan take tace ta yarda Indai zai aureta da yarta,shi dama Local government Kawai yake nema yace ba matsala ya biya kudi aka daura auren Mairo da Mahmud tsohon mijin Mami data Aura ta gudu shi Mairo take rawar kafa zata aura ance me kudi ne zata samu arziki,aka daura aure yau ango yazo ya dauki Amaryarsa da Kansa Yana zumudi ya samu sabo jini.


Ina godiya MRS CHIEF



AsmaBaffa
08061929616l🌼'YAR AIKIN KARUWAI 2🌼
MATAFIYA


BOOK2


36-40


Official

By
AsmaBaffa


SADAUKARWA NE GA
ZAINAB USMAN


MASU AUDIO WANNAN BOOK NA SIYAR DA SHI, BAN YARDA A JUYA MIN NOVEL AUDIO BA





*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*





Page naku ne fans yan
MISSDMK'S NOVELS AND MORE





Ahsan har yayi nisa ya juyo da baya Kamar yayi mantuwa ya dawo gida Kawai ji yayi jikinsa na bashi da matsala komawa yayi ko parking bai dai daita ba ya Shiga duba dakuna gaba Daya babu cele babu alamarta, sai da ya duba ko Ina hankalinsa ya tashi matuka ya fito da sauri har jallabiyarsa tana tadiye shi ya kusa faduwa.
motarsa farar da ya dawo da ita ya shiga ya bar gidan yabi hanya kamar yasan Cele Makkah ta nufa yasan nan ne dandazon baki musamman bakake,gudu yake shararawa Kamar zai tashi sama,Lokacin Driver Wanda ya dakko Cele ya tsaya karbar Sako har Ahsan ya wuce motar su bai san su bane .

Yana ta karewa ko wacce mota kallo motar da ya wuce wacce Cele ke ciki sai yaga Kamar itace ta mirror,Slow yayi ya danna reverse tare da dawowa baya yazo saitin motar yaga Cele tana share hawaye a cikin mota, parking yayi kawai bata sani ba sai ji tayi an bude motar tana juyowa taga Ahsan,mamaki ya kamata Hannu yasa Kawai ya jawota da kayanta,driver ya dawo Yana tambaya lafiya cikin harshen larabci,Ahsan yace matata ce fada mukayi zata gudu,Driver yace yayi kyau tafi da ita ku sasanta.
Cele ta fara tirje tirje sai an saketa ita gida zata koma,hannunta ta fisge ta karfi ta tafi da gudu zata tsallaka titi mota ta riga ta shararo da gudu Kawai ta banke Cele ta zube kasa bata ko motsi,Ahsan yayo kanta da gudu cikin tashin hankali.

Kafin kace me Yan Sanda sun cika wajen da wasu tsirarin mutane,driver din kuma tuni yayi nisa ma ya bar wajen,Ahsan ya tabbata wannan driver din yana sani tunda ko titin cele bata hau ba ya shararo da uban gudu ya gangaro gefen kwalta ya make Cele,Kuma a lokacin yaga motar tayi parking gaban ta su Cele da nisa shine ya taho da uban gudu.

Bangaren driver din Maheerah yayiwa waya Yana dariya yace ai ya kadeta sun ma huta wahalar kasheta da makami ya banke ta da mota ko shurawa bata yi,Maheerah dake Office dinta murna ta kamata tace Alhmdllh
Jini ta kasan Cele yana malala,bakinta jini hanci jini,nan take Ahsan ya sureta yana kuka Ambulance tazo sai asibiti suna cikin Ambulance ana bata agajin gaggawa
Suna karasawa asibiti gado aka basu likitoci Suka dukufa akan Cele wacce bata San inda take ba,Ahsan ya rasa inda zai sa Kansa hawaye ke sintiri a kumatunsa,sun dauki lokaci me tsawo kafin likita ya fito ya Kira Ahsan,Office yaje gabansa na faduwa,Likitan ya kalle shi sosai sannan yace da larabci ina baka hakuri yaron cikinta ya zube,wani farin ciki Ahsan yaji sabo da shi dai wannan zaluncin da aka yiwa Cele ya dame shi ya hanashi sukuni a rayuwarsa,likita yace sai dai ta samu rudewar kwakwalwa,shi rudewar kwakwalwa ba Yana nufin loosing memory bane Kawai ta rude na zuwa wani takaitaccen lokaci Wanda zata rasa a inda take,zata rasa me take yi a Ina take duk ta rude ta shiga faganniya,zata dinga Watarana dai dai watarana Kuma zata Yi abu irin na mahaukata,Ahsan yace to rauni fa? Yace bata ji Rauni ba sai dan kujewa da tayi da zarar ta dan murmure za a sallame ku,Ahsan yaji ba dadi sosai rudewar kwakwalwa ai masifa ce.

Auta Kuwa Omaira ta rakashi gidan su Sagir har dakin Sagir na samari ,ita Omaira duk duniya Sagir take so a rayuwarta shi kuma iyayensa sun ce a'a yaro ne bai Isa aure ba kwata kwata nawa yake baida aikin yi ma,shima Yana son Omaira amma Iyaye basa so sabo da sunce gidan su Omaira basu da tarbiyya masifaffu ne a fili kuma Suka ce dansu karatu yake yaro ne suka hanashi kulata,Sagir yayi aboki ya tarbi Nawaf Hannu biyu biyu.
Washe gari da safe 10am kanwar Sagir Zara ta kawo musu breakfast tea,kwai soyayye da Kuma faten wake,Nawaf tunda yayi Sallar Asuba ya koma bacci abinsa,sai da Sagir ya tashe shi sannan ya shiga toilet yayi wanka da brush ya fito ya shirya cikin Jallabiya arsh wacce ya siyo sabuwa dama kala uku ya siyo shima da boxers.
Suna cikin karyawa suna hira sai ga kanwar Sagir ta dawo Zarah nutsatsiya wankan tarwada,Auta a ransa yace idan sun hanani Sahar sai nazo nan a bani Zarah.
Suna karyawa sai ga Rahma itama da kayan karinta daga gidansu ta kawowa Auta.

Ni Kuwa Ina zaune abina Ina Jin su Omaira da Umma suna ta zuba hira Ni ban Saba da su ba suma basu saba da ni ba tunda nazo zancen Cele Kawai suke Yi da sauran yan uwa ni ba a shaku dani ba Nima ban shaku da su ba,idan Umma taga nayi shuru ne sai tace lafiya dai ko? Murmushi nakeyi nace lafiya,suna labarin Yan Uwa ban San kowa ba ni Kam na matsu Auta ma ya shigo muyi hira yafi min,Umma ce tayi magana tace ki tashi kiyi wanka a rakaki gidajen yan uwa nace to,Allah sarki Uwa me dadi abinda nake so take dafa min da kanta, Omaira aka sa ta zuba min ruwa naje nayi wanka na shirya.

A kofar gida na tsinci Nawaf shi da Abba suna hira,Nawaf Yana ta tsarinsa yana tsara Abba yace, Abba I got yah, I got yah, Wai baza ace you ba sai Yah shi ga bature, yana magana da salo but ka fahimta Abba in this life kowa yaci gaba an waye da ne ake ganin Mata Basu da daraja lokacin Jahiliyya amma yanzu Ilimi ya wadata malamai suna ta wa'azi akan darajar mata shi yasa ake so kullum mutum ya kasance Yana saurar wa'azi,Abba yace duk Ina ji na sani Kawai ni ne bana so,kana adawa da fadar Allah kenan,shi yasa akace mace idan da Aurenta to karta bari ta samu ciki ta zubar maybe wani hamshakin me kudin ko na gari ne a cikin ta watsar ta bar lalatattu Wanda zasu sa ma zuciyarka ta buga,Abba yace to itace ai kullum mace mace Dan nan baza ta sirka min da Namiji ko Daya ba sai da na Kara auren Mata biyu amma ko haihuwar basuyi ba bare na samu namiji, Auta yace you see.. you see hakki ne yake binka itama ba itace ta bawa kanta ba Allah ne waye ya Isa ya ja da Allah,shi fa Allah ba mate din kowa bane da za a dinga yiwa mutum baiwa Yana rainawa wannan shishigi ne da Butulci ake wa Allah,Allah waye ya Isa yayi abu ya zauna yana cece kuce me yasa da ya baka ji da gani ya baka iska kyauta kana shaka baka ce laifi bane,sannan ya saukar da ruwan samu muyi shuka mu samu abincin ci shi wannan duk dai dai ne ya baka haihuwar Namiji shima dai dai ne amma mace ita ba Allah ne yayita ba,ka godewa Allah ma da ya baka yaran idan ka mutu ka samu me maka addua.

To Addua ma tana yankewa bawa idan ka mutu mutane da yawa zasu dinga tuna halinka na kirki suna maka Addua da Yan Uwa da yaranka,bayan nan kowa ya manta da kai a hankali sai yaranka ko Wanda kuke uwa daya uba daya a Zamanin nan ba kowa zaiyi Sallah ya tuna da Kai ya maka Addua ba sai yaranka daka bari Ashe baza ka godewa Allah ba?

Ni ka ganni magana ta Allah kullum tunanina yanzu ya za ayi nayi aure da matata da yarana, mu maza shine a ranmu Mata Kuwa kullum iyayensu da danginsu suna ransu,me yasa kake fito na fito da Allah ba a fito na fito da Allah wlh baza kayi karko ba tuni zaiyi fata fata daku gwara tun wuri ka tuba kayiwa yaranka Addua na gari ake nema ba wani sai mace sai namiji,in Banda karfin hali ma Abba karka kace na maka rashin kunya gaskiya ce Kai fa Kawai manniyi ka zuba Allah ne yayi sauran aikinsa har ya tantance Da a ciki ka samu mata ba abin a gode Masa bane wa zai iya wannan aikin sai Allah iyakaci fa kawai kaji Dadi ka fitar da kazanta Allah yayi halitta Kai in ba Allah ba sauro wannan wa ya Isa ya halitta bare Dan Adam me daraja Kuma mace haba Abba ai mace duniya ce, mace ta haifeka ta raineka ka girma,kazo ka auri mace kaji Dadi da ita ta baka farin ciki sannan aka zo aka sake baka Yara Mata ka musu tarbiyya ka aurar da su bi Allah a saka a Aljanna,ga Jin Kan iyaye su taimakeka su tallafa maka su share maka hawaye,gaskiya ka daina yiwa Allah tawaye ba a ja da Allah magana ta gaskiya fa.

Abba yace gaskiya ka fada yaro kana da hankali Kuma ban taba ganin yaro me tunani irinka ba amma ni zuciyata tafi son namiji,Auta yace shike nan Kai da Allah ba ruwana,Abba yace Kai yaro dalilin da yasa fa kaga na tsaya Ina saurarka sai dan Kai Namiji ne Ina son Yara maza shi yasa nake saurararka me ka sani ma a duniyar yaushe aka haifeka?
Abba yana ganin wasu yara maza Yan dagwai dagwai na makwafta ya kafe su da Ido Yana sha'awa Yana wani washe baki,yace Yara manyan gobe kaga mazaje yace kuzo,Suka karaso ya basu hamsim Hamsim kyauta sabo da Kawai maza ne,har awara da alawa zaka ga Yana siyawa Yara maza,Yan mata Kuwa idan ya gansu tsakaninsu harara ce da bakar magana.

magana nayi nace Auta jiranka fa nake Yi kazo mu tafi ko baza kaje gidan su Aunty din ba,yace gani nan ya taho Muka rankaya tare,Rahma da Raheema,Omaira tana gida tana aiki,Auta na mikawa jakata nace ungo kayi duty din yayanka,karba yayi yace ya zamuyi an mallake mu duk kin Mana barbade mun cinye a abinci,an rubuce mu tsaf an shanye,dariya nayi nace Auta wai a kannen nawa baka zabi wata bane ciki? yace ai kunyi sake an riga ku Sahar nake so ni,na rigada na fada Mata Kuma ni bana yaudara,idan Kuma ba a bani ita ba na sake ganin kanwar Sagir Zarah sai na dawo,shike nan Yaya Nawwar Yana aurenki nima sai na sake dawowa gidanku dama Cele tana nan ita Zan so,shi Auta baya kula Yara dai dai shi sai ya samu katuwa yace ita yake so,nace Cele din ai Kuwa da Watarana kaci duka,yace haba sai dai idan ba so amma ko kallon banza ta Isa ta min taji aiki, Wanda ta Raina zata yiwa,Kinga da munyi anko da Yaya Nawwar tunda baku da banbanci da ita irinku daya sak har ba a gane ku shike nan an daina min gani gani nima.

Auta ne ya kalli Raheemah yace ke Yar tsugula kiwa Allah ki daina sa fitted gown din nan wallahi bata yiwa sirara kyau Kara kankace mace takeyi mace ta fito kamar sanda Sam sirara basa kyau a ciki amma mutanenmu sunki ganewa da Kinga wata ta saka tayi kyau kema sai kice Zaki saka ayi ta yayin Abu mutum bazai duba abinda zai Masa kyau ba Kawai daga ganin wata tayi kyau sai kace kaima sai ka Zama irinta,Nace wlh kuwa Auta wata ma fara zata gani Allah yayita haka sai tace sai ta koma wannan farar dole,gasar masifa musamman kwaikwayon Yan fina finai, da jaruma tayi Abu sai a fara yi kowa ,fitted gown dinma yawanci duwawun ciko ake sawa ayi cikon karya wacce bata yi ba sai a ganta Kamar muciya da zani mu dinga yin abinda Muka San zai Mana kyau dai dai da jikinmu,Raheema tace to ni Ina so ba wanda zai hanani ai Umma tasan na sa katon mayafi,Auta yace mayafin da kina Fitowa Kika dangale abinki,dariya Raheema tayi ta gyara tana cewa amma ka cika Dan sa Ido yanzu kaga Sanda na dage ashe, Nawaf yace Ina kallonki Mana ke sai anga kin hadu dole,Gidan Aunty Bilkisu Muka fara zuwa,Mijinta Kamar zai goyani ka rantse nice kanwar tasa ko su Bilkisu basuyi murnar da yayi ba har mamaki ya bani ya siyo Mana lemo da ruwa

Anjima kadan ya kawo kifi da nama yace ayi musu girki,tare Muka Fara aikin girkin,Auta harda yanka mana Salat ana ta hira da shi,yaran Aunty Bilki sai kallona suke suna dariya sun zaci Cele ce sabo da tana kawo musu awara tana zuwa ma ta dauke su,Babban ma harda zuwa ya zauna a cinyata Yana dariya,Nace ka sanni ne?ya zaci fa Cele ce cewar Aunty Bilki,Rahma nayiwa magana nace ke tashi ki musu wanka ku gyara gidan nan tunda Naga yanzu ma suka karya,Gidan Aunty Bilki me Dan kyau ne karami dukka dakunan uku tiles ne da kitchen da toilet tsakar gidane Kawai siminti.
Rahma tayi musu wanka Auta ya shafa musu Mai sai kace mace,karamin ma yace kawo pampers a like Masa Duwawu Kar ya ishe mu da fitsari Bilkisu tayi dariya tace sai kace Gum ta dakko sabuwa ta bashi ya sa masa da kayan ma shike nan Yara Suka likewa Auta sunga Namiji dan uwansu gani suke Kamar babansu ne.

Nazifa ce ta Kira Bilkisu a waya tace wato shine aka min danwaken zagaye Ina nan Ina jiransu shine Suka sauka a gidanku kice da Rabia wlh tun wuri su taho nan,Aunty Bilki tace to mayya zasu zo ne jaraba uwar naci ta kashe wayarta,Minti kadan sai ga Nazira ma ta shigo gidan dake ita gidanta Basu da Nisa da Bilki tace salamu Alaykum Wai Ina bakuwar ne sabo da Allah ance za a zo tun safe nake jira,dariya Suka bani wannan naci haka ashe dai suna so na na furta a raina Ina Jin dadi,Nazira sai kace irin munyi shekaru tare sai ta dage labile ta leko palon ta kalleni Muka hada Ido tace shegiyar kaya kice nan Kika baje katon tumbi Ina can Kun barni a lalace shi yasa na kwaso Yan matan kafafuna nace bari nazo na gani ashe kunzo, har mijina na tura gidan Umma yace ance Kun taho ashe nan kuka yo,Ina dariya nace ai ta nan Muka fara,to Dan ubanki baza ki gaishe ni ba nafa girmeku ke da Cele, nace Ina kwana tace lafiya lau nan mu muna da tarbiyya ba a kudu kike ba ki nutsu gashi nan hausarki duk ta lalace kina wani badan badan,dariya nayi ni bana ji ma hausata ta Fara canjawa, tace Ina su Star shegun kaya kunyi waya? Nace ai da safe dukkansu sun kirani Allah sarki kice Muna gaisuwa,juyawa tayi tace sai Kun shugo to nace to Aunty ta fice.

Sai da Muka ci Muka koshi sannan Muka je gidan Iyayen mijin Bilkisu Muka gaishe su ta nuna ni a wajensu suna ta Mata murna,muka tafi gidan Nazifa itama,Muna yin Sallama Muka sameta tana ta turaren wuta mijinta Yana Shan tea, Yana Mana Sannu da zuwa Muka shiga,Nazifa tace Auta kaga da Yar nan tawa ta girma baka ita zanyi ka aureta kalleta kyakyawa da ita,Auta ya ganta tana Wasa Fara kwal da ita taci ado gashinta yasha style na kitso,Auta yace ai yanzu Kam sai dai ki min Addua Allah ya sa na haifi kamarta da tayi tsada sai Wanda ya Isa shi zai auri 'yata yasa hannu ya dauketa Yana cewa wlh Kamar na gudu da ita,Mijin Nazifa ana yabon yarsa har wani dadi yake ji, Bayan mun gaisa Mijinta ya fita Nazifa tace miracle ko ai nan gaba har gidan Dagaci zamuyi gayya har Umma muje amma sai mun lallaba Abba idan ya yarda sai mu sa lokaci mu je Dagaci yasan kema kina da gata kowa a cire Masa shakku cewar ke ba Yar shege ba ce,Ina dan mijin naki kyakyawa me kama da Auta,Nace Yana can tun jiya ma bamuyi waya ba Naga kiransa da safe lokacin Ina bacci,Kuma Baki kirashi back ba? Nace ae ai zai sake Kira ne, Nazifa tace baki da hankali dalla kirashi ai Wanda ya damu da Kai to ka damu da shi,dariya ta bamu Kamar itace ta hada mu harda masifa,Kiran Nawwar nayi ya daga yace an samu Yan Uwa an Mata da miji nace ni na Isa,zamu hadu ne ai taraki nake yi, ya furta,Nazifa tace bani shi mu gaisa ta kwace Wayar tare da furta Hello Kanina Auntynka ce Nazifa Nawwar yayi dariya yace ahhh Allah ya tsare Mana Aunty Ina kwana,ta amsa Suka gaisa tace a dinga hakuri da kanwar nan tamu bata ji,Nawwar yace Inshaallah Aunty ai bata ji tace zamu saitata ne Naga Kamar taci Kai, Nawwar dariya shi dai yake yi yace na gode Aunty Allah ya Kara girma,ta Mika min wayar Muka danyi hira ya kashe .

Sai yamma Muka wuce gidan Nazira, Muna zuwa harda rungumeni itama gidanta yaji gyara Dan karami me kyau,Mijinta yafi na kowa surutu da shi Muka Sha hira sai dare Muka fito tace gobe sai Dangin Umma da Abba haka zamuje a nuna ki nace Allah ya kaimu.
Washe gari Kuwa sune Suka rakani Dangin Abba Dake garin muka gaisa duk da su basu damu ba basa son Mata amma dai munje sun ganni,a kwana na Uku kuma Muka je wajen abokan arziki na Umma duk Yan uwanta suna Taraba state su sai nan gaba zamu sa lokaci muje dukkanmu da gidan Dagaci sai Kuma Dangin Abba dake Nasawara duk zamuje da su Nawwar sabo da danginsa shima suga asalina na huta da Jin kunya,Yau Auta cewa yayi Rahma,Raheema,Omaira su shirya zai Kai su yawon shakatawa,Afif da Yamma yazo da mota Suka cakare Suka tafi,ai Kuwa ba su ba mu na gida ma mun samu tsarabar kayan dadi.

Nawwar ma Yana komawa ya sanarwa da Baffa,Mami da Papa sai Iyamami tana ji tace karya ne Kawai dan ace Ina da iyaye ne ba shegiya bace, yaushe za a jefar da yaro tun Yana jariri kuma ace an ga iyayensa ai karyane.

Umma dai ana ta tayata murna ranar da nayi kwana na hudu sai ga Santana,Star, Wise,Seraline,Mandula,Yar Zabil ma da mijinta Suka Zo min a ranar suka samu su Bilkisu duk sun zo Muna hira sai gasu.
Star ce ta shigo ta Sha shadda nace Yan banzan sun dira,Wise ta shigo itama taci wani material me tsada,Sera ansha leshi,Mandula Kuwa Arabian gown ta Sha,Yar Zabil ta Sha material,Suna shugowa Nazira me kaunar su Star tace Ina tauraruwa take,Na nuna mata Star ta ruko hannunta ke shu'uma ta wajena shugo,dariya ta Kama mu,Umma tace ita Nazira ai bata San tayi abu kadan ta hakura ba,Star ta kalleni tana dariya tace Aunty ce wannan? Nace ae ta tsaya a gaban Nazira ta Mata yanda sojoji keyi tace I salute you ta

2 Comments On YAR AIKIN KARUWAI Book 2
avatar
zainab-ibrahim-8

11 months ago

Reply

Thank

avatar
ghh

10 months ago

Reply

Replying to zainab-ibrahim-8

Yayi kyau?

Please Login or Register in order to submit comment