Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya shiga yana zuwa Idonsa jajir sanye cikin shadda sky ya zauna bayan ya gaishe ta yace Wai kinji Mamin Nawwar tayi aure a Madina? Iyamami tace Kai dai dan nan bari haka naji labari kayi hakuri idan rabonka ce zata dawo ka kalli yanda ka rame akan Salamatu haba Sulaiman duk ka lalace bana Jin dadin ganinka a haka, ko tsohuwar matarka ce tunda bata da wani laifi ka dawo da ita,Baffa yace har abada bazan dawo da ita ba ni auren ma na gama shi har abada bazan sake ba na daina bazan sake aure ba,ai duk ke Kika jawo min gashi nan taje ta auri wani,balarabe me kudi shike nan Sirrina ya gani,wallahi duk Wanda yayi silar rabani da matata bazan yafe Masa ba ko waye idon Baffa ya kawo kwalla ya tashi ya fice.

Nawwar Kuwa tare muka je Airport din Ina gaban mota Muka hango Mami ta rame tayi zuru zuru duk ta wani firgice,Nawwar Yana Fitowa a mota ya dinga sheka dariya a gaban Mami yace me na fada miki,Zan mareka wallahi Nawwar ta furta,Hannu ya Mika Yana faman dariya yace muga takardar sakin? Saki uku ne ko Daya,Ina gefe suna birge ni a Raina nace inama nima Ina da iyaye,mota Suka Shiga Muka tafi gida Ina yiwa Mami Sannu da zuwa Muna hira har Muka je gida,Mami a part din da su Star suka zauna Nan ta zauna gaba daya ta dawo gidan a Nan take idda babu Wanda yasan ma tana gidan sai iya yaranta ko su sulatana Basu San auren ya mutu ba Kawai ance tazo ganin gida ne sai Murna suke kusan kullum sai sun zo gidan har Auta,yau munje part din Mami Bayan Sallar Isha muna hira har Nawwar bakina ya cika da yawu sabo da turaren da Mami ta saka a palon sam bana sonsa duk Kuwa da irin dadin kamshinsa, toilet naje na zubar da yawun na dawo Muna hira minti daya yawu ya Kuma cika na tashi,Mami tuni ta lakanci hakan Kawai sharewa tayi,Nawwar ya kalleni bayan ya fito yace karki sa Mana tashin zuciya irin wannan yawu haka Mami bata da lafiya wurin kwana nawa amma taki yarda aje asibiti,haba dai a'a Rabia kuje asibiti ai gwara a San mene ke damunki Mami ta furta da sauri Nawwar yace bazai wuce ciki bane ai ta Sha Miya ma ta dade Bata samu ba,Kaga Ni bacci nake ji ku tashi ku tafi Mami ta koro mu,muna Fitowa Mami tace lallai Rabi tayi lafiya da dane da yanzu tana fitsara iri iri,Muna Fitowa na harari Nawwar nace ko Ina sai kace ciki ne dani Kai baza ayi sirri da Kai ba ko,shi Kam murna yake sosai Yana farin ciki Ina da ciki tun kafin muje asibiti.

Muna komawa cikin main palo ya daukeni Muka haura sama a saman bed ya direni ya fara murza ni,kicin kicin nayi bana so a rabeni yanzu tunda na fara laulayi, ya kalleni yace wai wannan wanne irin ciki ne yanzu da kyar kike yarda dani da kuwa sai abinda nake so,jiya haka Kika hana kememe,bakya tausayina ne, hakura nayi na yarda haka na bada hadin Kai sosai Kar ya shiga wani hali,washe gari Kuwa asibiti ya kaini aka min duk wasu test lafiya kalau nake Kawai Ina da ciki har 4mnths, Nawwar sai Murna yake fama,a ranar Kuma Malam Abulkhair ya dawo da koyamana karatu kullum a gidana kowaccenmu tana zuwa har Santana.

Iyashege bamu fasa ba musamman star,yau ma muna zaune Malam Yana zuba karatu Star sai magana take Masa da Ido Yana kallo shima da idon yake bata amsa,Wise tace Malam Wai ciwon Ido kake ne? Yace me Kika gani ya basar tace naga sai ka dinga ta mintsina ido,Shuru yayi Mata yaci gaba da karatu, Yana karatu Star ta dauki biro tana rubutu yazo har gabanta Hannu yasa a littafin yace da kyau sarkin kokari da Allah ku tafa Mata,Muka kalli juna sannan muka tafa Mata ba dalili,tunda ya aureta kullum sai yasa an tafawa Star sau uku idan anzo karatu,nace mu wato bamu da galibu bamu da gata kullum Star ce me kokari,Star har gwalo take mana.
Ana karatu tayi rubutu a takarda ta dagawa Malam wai Honey ya jiya da dare? Malam Abhulkhair harda sakin Murmushi Yana Kare Fuska da littafi muka ji yace great Masha Allah bamu San me ta rubuta Masa ba,Seraline ce tayi tambaya tace Malam mijina kullum mukan harari juna amma bada fada ba ta sigar soyayya hakan da kyau ba raini? Malam Abhulkhair ya jinjina kai a ransa yace yaran nan baza su shiryu ba Ina ganin Iftila'i nikam,a fili yace Alhmdllh Kinga Kamar Me Sunan Tauraro gaskiya tana da kaifin basira yabon gwani ya Zama dole ba Wai dan Muna da alaka ba ita gaskiya idan tazo dole a fadeta amma ban taba gani the most intelligent girl irin me sunan Tauraro ba,Dole mu jinjinawa Iyayenta da Allah ya basu ikon haihuwarta anyi farar haihuwa,kafin a sameta sai da akayi Addua da alama,dukkanmu Muka bude baki bazai karatun kirki ba sai yabon Star da iyayenta kullum,Yar Zabil tace Malam mufa ba taruwa mukayi ba don a bamu karatu akan Star ba ayi Mana karatu mu tafi,yace bakwa son gaskiya kasar nan ta lalace har kullum mu munfi so a zagi dan uwanmu shine dai dai idan gaskiya tazo dole a fade ta, nutsuwarta ce ta sa,Star tayi mana gwalo, Malam yaci gaba da karatu babin Tajweed

Washe gari da safe Ahsan ranar hutunsa ce baya zuwa aiki ita Kuwa gogar Maheerah ita kadai yau ta Sha fresh milk da snacks ta wuce wurin aiki Ahsan bacci yake sosai abinsa,Ayusha tazo da nikaf da doguwar riga,Cele Kuwa tana tashi wanka tayi tunda tayi sallar asuba ta shirya cikin riga da skert dinta sababbi cikin kayan da Suka siya mata,ta daura wani dankwali irin na larabawa ta fito,kitchen ya shiga Ayusha tunda ta kalleta sau daya bata sake ba sabo da tsoronta , gas ta kunna gefe Daya ta dauki kwai har guda uku ta soya yaji hadin Albasa harda Maggi ta gani wasu Kalar ba irin namu ba,bayan ta soya ta soya dankalin turawanta me yawa ta hada tea me kauri, sai ta Koma Palo tare da kunna kallo abinta ga abincinta ta zauna kenan a kasa Ahsan ya fito ya Sha wanka sanye cikin Jallabiya fara tana uban sheki sai kamshi yake,Murmushi yayi ya kalle ta dai,bata iya gaisuwar su ba tace Salamu Alayk,ya amsa mata Kuwa Yana Murmushi ya kalli abincin da take ci, shayinta cikin katon cup din da ya siya mata dan ita duk rashin ci irin na Cele tafi karfin irin cup irin na su Ahsan.

Kallon cup din yake da irin shayin dake ciki yana kunshe dariyarsa a cikinsa,wani sabon bread data dakko a kitchen din me kyau ga laushi haba har lumshe Ido take tana korawa tana ci Kamar Wasa yaga ta cinye komai ta shanye komai,ya zaro Ido Yana kallonta ya gani ko zata iya tashi sai yaga ta mike tsaf ta kwashe kwanikan ta Kai kitchen ta wanke komai ta adana ta dawo kitchen dauke da ruwan roba tana sha,a ransa yace har space ne na ruwa a cikinta duk abincin da ta cinye, sai satar kallon cikinta yake shi jaririnsa yake ji Kar a kashe shi da abinci,gashi yana son taba cikin amma ba damar hakan,ita Rufaida bata San ma tana da cikinsu ba a jikinta Kawai dai bata Jin dadin jikinta ta rasa dalili.

Da Hannu ya yafito Cele wai taje,zuwa tayi ta tako gabansa tana tafiyar Yan sarauniyar kyau ta rike kugu tana harde kafafu Kamar dai yanda masu gasar sauniyar kyau suke Yi tana zuwa gabansa ta tsaya tare da tsuke dan bakinta,Murmushi ya saki ba shiri kujera ya nuna Mata ta zauna nesa da shi kadan gaba daya kamshinsa ya tafi da imaninsa ji take idan bata shaka ba Kamar zata suma ta baza hanci harda Mika wuya tayi dogon wuya,mamaki yake a ransa yanda take clean haka,a haka aka kawo Masa abinci yaci sannan agogon hannunsa ya kalla me tsada ya tashi ya fice abinsa,yau shi yayi driving kansa,ita dai Cele tashi tayi ta shiga kitchen ta iske Ayusha tace da Hausa ke Wai me ake nufi dani ne a gidan nan? na rasa dalilin kawo ni gidan nan an sato ni maimakon Naga ana gallaza min azaba iri iri amma anyi Shuru sai zaman lafiya nake yi,ga me gidan sai kirki yake min wai me ake nufi Dani ne,Hannu tasa ta daki sink tace me ake nufi ne wai an rabani da Kaka ko Yana wanne hali ban sani ba,Ayusha mukus tayi tana Jin tsoro haka Cele ta gama masifarta ta fice ta koma dakinta.

Kakan Cele kuwa tunda Agent ta kwashe su har garin Makkah unguwar Shari mansir inda dandazon bakake suke inda mutanen mu sun gama kashe musu unguwar, Kaka sai Alfarma ya roka wajen Zama dakinsu su wajen mutum goma a nan ya samu ya raba,karfinsa ya Kare bazai iya sana'ar komai ba,yayi zaune yayi tagumi Allah yasa ma Cele ta bashi wasu kudin a hannunsa da su yake lallabawa Yana cin abincin takari, yau ko wanne matashi ya fice Neman kudinsa sai shi Daya a daki ya zuba tagumi yace Ina amfanin Zama na a kasar nan babu Jikata gatana itace komai nawa mene amfanin zuwana kaddara ta kawoni gashi an sace min Rufaida ta maganin Kuka na,na gama Shan kaddarata tun Ina yaro har na tsufa na Gama amsa jarabawata ta rayuwa gashi yanzu kaddarar Cele ta shafeni Ina Zan Sa kaina me zanyi da ya wuce bara bai sai Sanda ya Fara hawaye ba yace Allah yasa a kamani a maidani kasata Najeriya Banga amfanin zamana ba,tashi yayi ya fito da katuwar rigar shaddarsa ya mike titi Yana tafiya sai ya samu inda yaga askarawa Yan Sanda sai yaje cikinsu ya tsaya Wai Dan a kamashi a dawo da dashi Nigeria amma sunki kula shi, Kuma Yana kallo zasu bi wasu takarin da gudu su zuba tsere amma shi basa kulashi,a haka Kaka yake gararinsa a kasar har ya samu ya sauke Umrah Cele ta Sha Addua a dakin ka'abah Allah ya bayyana Masa ita,ba Wanda ya Kama Kaka kamar Dan kasa haka yake harka har kudinsa Suka Kare ya Fara bara a hanyar zuwa Harami wato dakin Allah a hanyar yake zama ana ta bashi sadaka da haka yake ci yana Sha,so yake a kamashi a dawo da shi Nigeria amma anki ga Wanda basa son a Kama su amma sai kamasu ake banda shi.

Mairo cikinta ya girma tunda taje kasar take sana'ar tuwon shinkafa tana kaiwa gidajen Baki masu zuwa aikin hajji Hausawa, ita kuwa Sadiya tana zuwa taji hausawa takari ana samo musu mazaje suna aura,duk aure daya za a baka kimanin dubu dari biyar wasu sana'arsu kenan sai kiga mace a kankanin lokaci tayi aure goma ma Sabo da wannan kudin, Sadiya tace ita baza ta iya siyar da abinci ba aka samo Mata Balaraben Yemen aka daura aure ta samu dubu dari biyar cas ta tura da kudin gida,babarta sai Murna take daga zuwa arziki ya zo bata ma San aure tayi ba,Sadiya wani wulakantaccen gida ya ajiyeta me dauke da daki Daya tal komai a ciki toilet da kitchen,sabo da ya dauki bakakenmu Basu San me suke ba sannan kudi suke biya suna auren dandane da su, ana Kai Sadiya ya Fara sassakarta ba ji ba gani,gashi bata Saba ba,bata hutawa da Antaina ko 2 weeks bata cika ba ta fito Amma tana yin Idda ta sake auren wani Dan kasar Siriya,shima dubu dari biyar,Ashe shi Kuma burinsa Kawai ya auri bakar fata ya dinga kallo Yana dariya shike nan burinsa, Sadiya ta tare ya shigo yace tayi tsirara haka yake so ya ganta,haka tayi to tasan kudi ya biyata ta tube Kaya ya zurawa surarta Ido Kamar Yana gidan zoo sai ya sheke da dariya yace ta juya ta juya Nan sai dariya hahaha Yana muzantata,yafi karfin ya taba nononta da hannu sabo da haka ya jawo sandarsa ta karfe da yake yawan rikewa dake ya Fara manyanta ya zauna da sandar yake sawa Yana zungurar dukiyar Fulanin Sadiya,kullum aikinsa kenan Yana shigowa gidan zai hau dariya Yana kallonta Yana nunata da yatsa,Sadiya abin ya isheta ta Fara Masa rashin mutunci tunda tana Jin turanci shima Yana ji,dama abinda Basu fiye so ba ka zagi uwarsu Indai ka zagi uwarsu to har abada su da kai,ko dai su koreka ko kaci ubanka,ta zagi uwarsa da larabcin data Fara koya,domin ita Sadiya ita da Mairo suna zuwa cewa Suka Yi zagi Kawai za a fara koya musu,takari Suka koya musu zagi da larabci iri iri,da su Sadiya tayi amfani sabo da son kai shi duk abinda yake Mata na cin mutunci bai gani sai shi sabo da ta zagi uwarsa,ai Kuwa anyi rashin sa'a Sadiya sai da taci dukan tsiya sannan ya saketa ya koreta.
Mairo ma Allah Allah take ta haihu ta fara aure auren kudi,tana da ciki sha'awa tana damun Mairo gashi ta Saba da namiji,a cikin takari da wasu bakin larabawa suna Neman Mata me ciki akwai Wanda su sai me ciki suke zina da ita suna biyanta makudan kudade,Tuni Mairo ta fada Harkar tana dafa tuwonta na siyarwa tana Neman maza da cikinta ana biyanta kudi musamman da taga bata da girman ciki idan tasa babbar Abaya ma ba a ganinsa sai ka zaci kiba ce kawai.

Cikin matan da suka Zo da Cele Kuwa gidan Samira da Wasila aka kaisu yaran Mata ne Suma hausawa sunfi su talatin a gidan duk matasan Mata ne gaba dayansu Harkar lesbian suke madugo har matan larabawa suna Neman su suna biyansu aikinsu kenan, Samira tuni Suka jata cikinsu Suka fara Yi da ita,Wasila Kuwa sunyi sunyi amma taki yarda sannan Allah ya tsareta,tace Neman kudi nazo ba lalata nazo ba na rasa inda zan Yi sabon Allah sai nazo har dakin Allah,dama ta iya lalle iri iri ta iya kitso Kawai ta Fara sana'arta ta siyo kayan yi ta Fara Neman kudinta Kuma Allah ya sa Mata Albarka tana mugun samu kudi har ma ta tashi ta bar gidan inda su Samira suke Alfasha ta koma gidan takari mutanen kirki Wanda su dama kudin suke nema sun maida Kai Kuma ta hanyar halak suke nema dama wasu ke bata wasu.

Bangaren matasan Mazan da suka Zo tare da Cele Abdul,da Naziru bread suke sarowa suna siyarwa bakin gidajen Alhazawa sosai suke abinda ya kaisu,Musty kuwa Wanda ya taba kaiwa Cele hari shi tuni daga Neman Mata sai ya shiga kungiyar Yan luwadi,an samu lalatattun larabawa da suke Yi da su suna biyansu kudi yanzu zaka ga mutum ya Zama me shegen kudi layin Musty ya dauka shi.

Ni Kuwa Rabi laulayi nake yi sosai,aiki ma ba komai nake yi ba,ga Nawwar bai zama aiki ya rike min shi kullum sai dai waya Yana tambaya ya jikin,Mami ce ke kula dani,ko Riga bana so na saka sabo da jikina ji nake kamar ana rura min wuta kullum da kyar nake saka vest da skert kullum Ina cikin toilet Ina shiga cikin ruwa na Zama Kamar kwaduwa ko nace agwagwa,Mami bata sanin wani abin Dana ke aikatawa bata San har akan kankara kwanciya nake ba, yau ma tunda na samu Nawwar ya fita na dakko Kankara katuwa a fridge dama ruwa nake samu na zuba a bowl din silver da wuri take min kankara,na dawo bedroom dina,na cire kayan jikina sabo da tsiyata ko pant babu na zuba kankarar na barbazata a kasan tiles da ruwan sanyin ga wata Ina Sha sannan na kwanta a Kai Ina malelekuwa a saman kankara Ina Jin dadina Ina tauna wata kankarar Ina lumshe ido, Nawwar ne ya dawo yayi mantuwa ya kamani a Haka kankara ba kadan ba, Innalillahi wa Innailayhirraju'un ya furta tare da Dora hannaye a Kai ni ya tsoratani ma da katuwar kankara a bakina nace lafiya? yace kashe kanki zakiyi shi yasa kullum mura taki Kare Miki kin San idan sanyi ya kamaki wlh munga ta kanmu shike Nan dana Nimoniya ta kamashi Allah ya tsare Hannu yasa ya dagani Yana fada yace dan Iskanci harda yin tsirara ki kwanta haka,Allah ya shiryeki,kankarar dake bakina ya kwakwule da hannunsa,nace ni gobara akeyi a jikina kullum sai naji wutar ta Kama a jikina ko ina, Fitowa yayi yasa aka kwashe gaba Daya fridge din gidan ya maida su bangaren Mami ya fada Mata,yace karki bari Rabiah ta dauki ko ruwan sanyi a fridge,Mami tace haba shi yasa kullum sai naga ta saka ruwa a silver sau biyu sau uku a Rana Ashe kankarar take dauka bata San Illar hakan ba,ganin su Mami sun gama da matsalar sai na koma na samu Kaya me kauri na jikata da ruwa sharkaf na saka kayan haka Ina Jin dadin jikina,Nawwar yana sake kamani sai ya tasa keyata tare muke shiryawa ya tafi dani Office, a can din ma fada muke Yi a tiles nake kwanciya,ga karatunmu Muna Yi duk mun Fara gogewa Kawai sai ya kaini makaranta ya sani a Ss3 kuka wiwi nake yi, yace tunda kullum bakya Jin magana ke sai kin shiga sanyi ai gwara na saki a makaranta ki godewa Allah ba Jss1 na kaiki ba, kuma idan baki karatu ba ki ci duka,a Dole nake saka uniform harda Hijab na tafi school,sai gashi an kawo su Sera dukkanmu ajinmu daya banda Wise ita tana da degree ma
Ni idan naje makarantar ma bana ganewa sabo da laulayi kowa yana sit ni Ina kasa a zaune a haka nake karatun Yan aji suyi ta kallona, gajiya wasu matan Suka Yi Suka ce Rabia kalau kike kuwa ke kullum a kasa,nace ciki ne da ni mijina nane ya min ciki,Yan aji sai dariya suke suna Jin kunya wata a ciki tace ai ba sai kince mijinki ne ya Miki ba,a'a ai karku kaini inda banje ba kuyi zaton na shege ne to da ubansa Ina da aure ku Kuna ganina kun San ni ba sa'arku bace,babban Kai ce ni na ja tsaki na kwanta a kasa sosai Kamar ina dakina har aka tashi ni yau na kasa tashi ma Sabo da kwailo irin nawa,Star sun gaji da halina sun kyaleni tafiyarsu Suka yi, Nawwar daukana yazo yi da Kansa yaga har Yan school sun Kare bai ganni ba,wata Yar ajin mu ya tambaya yace Rabiah fa? Tace a aji muka barta ta kwanta a kasa kullum a kasa take kwanciya ko ta zauna ka tambayi ma kawayenta su Star kaji ,motar ya bude ya fito duba ajujuwan har ya hangoni a ajinmu a kwance jakar makaranta tana gefe Ina ta bacci na, Yana zuwa ya tashe ni yace Wai me yasa ke gaba daya baki da dauriyar wahala Kamar a kanki aka Fara ciki,tashi mu tafi kalli uniform dinki duk yayi dirty Kamar Yar pre nursery, tashi nayi Ina harararsa nace wlh da Zan iya sai na dawo maka da cikinka jikinka duk waye ya jawo min wannan halin da nake ciki idan ba Kai ba,Ni na taba lalura irin wannan ma Sai a gidanka,dariya yayi yace nima da Zan iya kwace yarona zanyi karki kashe min shi da sanyi,Jakar tawa ya daukar min na fito Muka tafi,Muna komawa gida komai shi ya min har wanka,ana wanka sai dadin ruwan nake ji ruwan sanyi ne nace dan Allah Kar a gama wankan nan, sabo da muguntar Nawwar sai ya danna ruwan zafi ya sirka ruwan ya dawo me dumi da wuri nace an gama ya Isa na fita tas, a toilet din ya rikeni ya dinga aika min da sakosa na soyayya dukkanmu ba Kaya a jikinmu ya rungumeni tun bana maida Masa martani har na saki jiki sosai Muka jiyar da junanmu Dadi sannan Muka sake wanka tare da tsarkake kanmu muka fito.

Kwanan Cele biyar a gidan larabawan Maheerah matar gidan tsakaninsu sai harara da kyama, Ahsan ne kadai yake saurarenta shima Kuma ba zama yake Yi ba a gida, ko me aikin Ayusha itama wariyar launin fata take nuna mata,mamakin da Cele take Yi me Suka ajiyeta suke Yi da ita a gidan Kuma game da abinci sai abinda taga dama take dafawa abin Yana daure Mata kai a haka Cele ta cika wata guda cif bata taba ko leka tsakar gida ba kullum tana kulle a gidan kofar ma baza ta budu ba tayi tayi ta Gane amma abin ya gagara,tana haka Kawai sai taji ba abinda take bukata sai Namiji bata San tana da ciki ba,sannan ga kwadayi dake damunta abinci sai ta zaba,sha'awar tafi takura mata,sannan turaren Ahsan da yake sawa ji take idan bata shaki kamshinsa ba kamar zata mutu sai yawan bacci da kasala da Suka taru Suka Mata yawa,ta kasa gane kanta ta rasa me ke damunta, ana haka sai Cele taji tafiyarta ma ta canja tana Jin wani nauyi a jikinta tafiyarta kamar agwagwa haka take Jin tanayi amma a fili babu me ganewa,ita kadai tasan me take ji Kawai tafiya tayi nisa kwanaki na ja sai ta Fara jin kamar anyi motsi a cikinta ai da gudu ta fito,wani wawan birki ta ja ganin Yan uwan Maheerah suk zo ganin me cikin da aka yiwa dashen ciki su biyar da su Mata uku maza biyu a matan akwai dattijai guda biyu daya itace Maman Maheerah sunanta Fatima suna ce Mata Ummu Omair,Su Uku ne yaran data Haifa Omair shine Babba sai Maheerah sai kanwarta Jasmin wacce tana cikin Wanda Suka zo,Daya macen Kuma Babba ce itama kanwar Maman Maheerah ce Najwa.

Mazan biyu kuma baban Maheerah ne Omair sai dayan Wanda kanin Baban Ahsan ne Rayyan zaune zagaye suke da abinci iri daban daban irin nasu na larabawa ai sai ci suke suna labarinsu da larabci akan cikin,Maheerah ce tace tana basu labari da harshen larabci tace ai da amincewarta kafin ma a kawota gidan Nan sai dana biyata wajen million uku sannan idan ta haihu za a biya wasu,Basu sani ba ashe Ahsan ya bata kudi ta cinye sisi bata ba Cele ba,Kanin Baban Ahsan ne yace amma ta taba haihuwa ko na ganta tayi karama ne,da sauri Maheerah tace haihuwarta uku yaranta biyu a Nigeria Daya Kuma a nan ta haife shi a Saudiyya amma da yayi wayo sai ta kaishi Nigeria wajen iyayenta, suna ta Jin dadi suna murna ana ci ana sha,Kanin Baban Ahsan Rayyan shine ya yafito cele taje Wai,ta taka taje har gabansa tare da tsugunawa Kawai to ita bata Jin yarensu,Yana Murmushi ya dafa kanta kallonsa tayi tana Masa murmushi,Dangin Maheerah kuwa in banda hararata ba abinda suke Yi gaba dayansu musamman Ummin Maheerah sai kallon wulakanci suke min,ba boye boye Ummu Maheerah tace me yasa bata sa Hijab da nikaf a gida ta zauna haka tana shiga yanda taga dama ga mijinki a gidan yana kallo,Ahsan yace tunda an dakkota bai dace a takura Mata ba,masu ciki suna yawan Jin zafi ba sai ta sa komai ba tayi shigarta shi bai da matsala ai na Dan lokaci ne zata haihu ta tafi,ita dai Cele bata San meke faruwa ba gaba Daya Bata Jin me suke cewa tashi tayi ta koma bedroom sai yamma likis Suka tafi,Maheerah tana da aikin yamma Kawai Ahsan ne ya kaita ya dawo, Yana dawowa har da su Ice cream ya siyo wa Cele,dakinta yayi knocking ta bude tare da Fitowa ledar ya Mika mata ta karba ta duba Ice cream ne da zam zam da wasu abubuwan na ci,taji dadin ganin ice cream din tana ta murna nan take ta dauki roba daya ta bude ta fara sha,Hannunta ya riko ta fito ta zauna a kujera sannan ya kunna mata kallo tana Shan Ice

2 Comments On YAR AIKIN KARUWAI Book 2
avatar
zainab-ibrahim-8

11 months ago

Reply

Thank

avatar
ghh

10 months ago

Reply

Replying to zainab-ibrahim-8

Yayi kyau?

Please Login or Register in order to submit comment