Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kuma nace na fasa ui yanzu,Baffa yace bafa na Wasa dakai ka Nemo mace idan zaka Nemo zuwa ka Fara University gashi nan na biya maka awolowo University soon zaka Fara zuwa wani satin.

Tashi yayi ya tafiyarsa Mami bata ce komai ba sai yanzu tace ai dole ayiwa Auta aure, Auta da alama mace yake bukata ai ko yaki wlh sai an masa aure Ina Zan iya wannan iskancin nasa na zabe zabe a haka har ya lalace,Baffa yace kyale dan jakar uba ai na sama Masa Office ya daina yawon banza da kallon ball ko Yana school weekend sai yaje Office,da bangaren Nawwar Zan kaishi amma naga fada zasuyi gwara na barshi a bangarena.
Bangaren Auta dakinsa ya shiga yana takaici ya rasa Sahar, kiranta ne ya shigo wayarsa bai fasa dagawa ba yace hello,Sahar kuka take yi wiwi katuwa da ita ko kunya tace Nawaf dan Allah karka canja wata ka dan jirani ko su Daddyna zasu hakura,Auta yaji tausayin Kansa sabo da ba karamin yaki yayi ba kafin ya samu soyayyar Sahar gata lokacin tana ss3 su suna jss1 har ta Gama degree dinta tsaf Auta yaje Suka Fara soyayya ga yara da iya soyayya su ba aura zasu Yi ba sai su kwacewa babban mutum budurwa sabo da suna da time Basu da aikin yi duk wata kulawa za a bawa mace shi yasa Auta Yana shiga neman Sahar duk ya kori manyan samarinta.

Yace Sahar kiyi hakuri haka Allah yaso idan da rabo Zan aurenki amma su Mami sunce aure za a min kiyi hakuri ki yiwa iyayenki biyayya nima Zan yiwa nawa biyayya muyi Addua Kawai,ya lallaba Sahar sai da Suka gama waya ya jefar da Wayar yace bazan sake fitowa ba abinci ma bazan ci ba gwara na mutu na huta ya sawa kofarsa key sabo da Auta ya sa rai ya samu Sahar an gama Yana sonta shi Kam,Mami taga Auta Shuru Shuru har dare tun safe bai fito ba, Dakinsa ta nufa ta murda a kulle ta Kira sunansa Auta,ciki ciki ya amsa haushin kowa yake ji,Zo ka bude min kofa yaki budewa,tayi tayi sai da kyar sannan ya tashi ya bude Jin Mami tace sai taci mutuncinsa,Kofa ya bude Idonsa duk ya canja alamar kuka yayi,dariya ma ya bawa Mami,tace Autana kukan Soyayya kayi ne? Yace kukan soyayya ai sai mata,hmm to mu fa ba laifinmu bane iyayenta ne Suka ce basa sonka kayi yaro,Auta yace ai ba haka ake neman aure ba daga zuwa sai a kyale su ai sai an lallaba su tukun an musu Nasiha Kawai daga zuwa sau daya shike nan sai ace na hakura ai dama ni nasan ba'a so na,ni bazan auro kowa ba a barni Zan jirata ko zasu yarda su hakura,Mami ta kalle shi Kawai tace babu fa wata Sahar da zamu jira mu wallahi aure za a maka Kama sani wannan iskancin naka bada mu ba,Muje kaci abinci amma ka cire wata Sahar a ranka Wanda bai son mu muma bama sonsa,Mami ta jashi zuwa palonta,da kanta ta zauna tana bashi abinci a baki sabo da Auta ne su Sultana suna ta Masa dariya,Nawwar ne ya shigo gaida Mami ya samu Mami tana bawa Auta abinci a baki,kallonsu yayi yace wannan katon yaron lallai Mami kema,Kai kyale min da Soyayya zata halaka min dana yayi yajin abinci ya kulle Kansa a daki,Mami ta bawa Nawwar Labari,dariya Nawwar yayi yace Auta Wai yasan soyayya Kai duniya gaskiya ayi Masa auren Mami ga kannen Rabia,Auta yace ni fa bana so Cele nake so wlh Indai ba Cele ba to sai dai a barni na zabi wata Ni bana son yarinya kwaila,Nawwar ya kalleshi yace Omaira ai katuwa ce,yace da sauranta bata nuna ba,Mami ce ta make shi tace kaji ko Nawwar wlh aure ko Yana so ko baya so shekara bazai Kara ba Mata ba,Nawwar yace uhm ni ka shirya ma na aikeka Kano gobe zaka Kawai wani takardu,Auta yace to Yana murna ya samu kafa idan ya tafi sai ya zauna ya huta shi bazai kula wata mace ba ma yanzu.
Nawwar na Kira a waya nace Baby Ina ka zauna ne ka taho gida Kai nake jira bacci zanyi,mikewa yayi da sauri yace Mami sai da safe ya fice Yana waya,Auta yace wlh an shanye Yaya itace fa ta Kira na tabbata ko kece bazai wannan saurin ba,Mami tace karfa kaima aga haka Idan kayi aure,Allah ya kiyaye ni da nake tsayayyen mutum ai ba kamarki Mami,Mami tace da zai yuwu ma ai da ka min part Dina na koma,Murmushi yayi yace sai dai ki tafi gidan Nawwar shine babba ai ba kya zo gidana ba,au haka zaka min Auta gidan naka ma bazan zauna ba? to me Zaki Yi a gidan yara mu da idonmu yake a bushe,Mami tace ka nuna min matsayina Auta kishi nake wata zata kwace min Autana,Auta yayi dariya yace wace ma ta Isa ai Kuwa a canja ta,haka Suka Yi ta hira da Mami,Sultana da Nasira ma sun samu mazajen auren su.

Washe gari Auta ya tafi Aiken Nawwar Kano gashi an hanashi kwana ba yanda ya Iya Yana zuwa ya nemi mutumin yace zai turo driver ya dauke shi,Auta yace Kar ya wahalar da Kansa kawai ya Masa kwatance yace yazo Office din da Kansa,Napep Auta ya shiga yaje ya Kai takardun ya fito zai shiga Napep wani matashin mutum zai kai 34yrs ya fanfaro da gudu ya zaga bayan Auta ya buya,Wata tsohuwa tukuf ta biyo shi da bulala tana cewa Baso wato Dan ubanka baka ji baza ka Daina Shaye shayen nan ba yanzu madarar sukudayin din nan kake sha baza ka daina ba, Auta yana kallon ikon Allah katon gardi haka yana buya a bayansa ko kunya baya ji, tsohuwa taci gaba da cewa to ni makwafciyarku ce akwai hakkin makwaftaka a kaina da ku, wallahi Salma baza ta auri wani abokinka ba Dan Shaye Shaye ba,kullum ka dinga kwaso samarin Yan wiwi kana zaluntar yarinya kana dukanta kace sai ta auri wani,Idan an hanaka sai ka kawo wani,itace fa aka baka ka aura wanne hauka ne haka Salma ce ta fito da gudu tace yawwa Inna bazan auri zabin Yaya ba ko zai karshe ni ai ya San shi nake so,yarinya tana murguda baki tana hararar Wanda aka Kira da Baso boye a bayan Auta, Salma ce tazo ta tsaya a gaban Auta ta kaiwa Yayan nata duka ya kauce ta samu Auta,Shima Baso ya kawo hannu ta bayan Auta zai daki Salma ta matsa da sauri ya samu Auta,Auta yaji zafi ya matsa gefe suka bishi Baso yana buya a bayansa ya zuro hannu Salma ma ta kawo nata suka sa Auta a tsakiya suna fada in ya matsa Baso ya sake binsa ya buya a bayansa suka shiga zagaya Auta, Salma ce ta gaji tace zaka dawo ne muje Inna suka juya tare da komawa gida tana cewa wallahi kullum sai ya dake ni na gaji kullum kamar jaka.

Baso da muryar yan daba ya Kalli Auta tare da daga masa hannu yace ahhh Abdul'aziz na manta ban gaishe ka ba ina kwana, Auta dariya ta kamashi lallai kwaya bata yi ba,wani Dan yaro baifi 5yrs ba yazo zai wuce nan Baso ya dagawa yaron hannu yace a'a yaro ban gaishe ka ba ina kwana? Yaron ya tsaya yana kallon Baso,Nawaf ya Kalli Baso gaba daya Shaye Shaye ya haukata shi,ya sake kallon Nawaf yace Abdul'aziz bafa mu gaisa ba ina kwana? Auta yana sani ya Mika masa hannu yace ka tashi lafiya yawwa ina kwana Dan Allah ban dari biyar nan,Baso yace Allah Man? Kasan ina da Hali na kirki Dana tsiya ya zaro wata tsohuwar dari biyar ya mikawa Nawaf yace ungo Allah ya baka,Auta yace tsokanarka nayi fa ni na gode, wallahi sai ka karba karya kake Oga dole sai ka karba ko na maka dukan tsiya a nan,Nawaf yaga Baso tsakani da Allah dukansa zaiyi yana wani tangal tangal a hanya,hannu yasa ya karba,yace yawwa abokina kaga gidanmu can muje,Nawaf yace kayi hakuri gida zanje,hannu yasa ya fisgo Auta gidansu a gefen kusa da hanya yake,wani gida kamar shagon Samari dakuna guda biyu sai wani daki kamar kango sai yar Katanga da kitchen na langa langa bandakin ma rabinsa na langa langa ne,kofar gidan Kuma ko kofa Babu sai buhun Leda, Nawaf ya bishi suka shiga ko ina tsaf neat,Salma tana wanke wanke a tsakar gidan ga wani mahaukaci a gefe yana zaune yana wasanni yana soshe soshe gashinsa duguzaza da kasumba babban mutum ne zai kai 47yrs, Auta yana ta kallon mutumin,Baso ya dakkowa Auta benchi dogo ya goge masa yana tangadi yace zauna master,Auta ya zauna shi dai,Salma tana aikinta Baso ya daka mata uwar tsawa ta mike jiki na bari yace kawo masa ruwa,Auta da sauri yace na gode Dan Allah, kai ba a mana musu a nan yawwa ke kawo masa ruwa sai ka sha,Nawaf yayi shuru Salma ta kamfato masa ruwa a randa,Auta ya Dan dodana bakinsa a bakin kofin kamar yana sha yace yawwa Alhmdllh na koshi kai har naji Dadi kishirwa ta tafi,Salma tana kallon wayon da Auta yayi tayi shuru dai.

Auta yace wannan Mahaukacin fa? Salma tace ae a gari ya tsinto shi,Baso ya daka mata tsawa yace zan ballaki munafuka jibarki kina fama da koshoko me zan ci dake Baba ya mutu ya barmin masifa wlh bazan aureki ba bana sonki,Salma taji kuka ya taho mata tana son Baso matuka a duniya bata taba son wani ba face Baso,Auta shi dai Halin da ya gansu yaji Kuma Salma ba muharramarsa bace gata kyakyawa ta karshen karshe gata katuwa me shape komai ya fita a jikinta son kowa kin Wanda ya rasa fara da ita amma ba fara can ba normal normal dai sai kyawun tsiya kamar me,shi Kuma Auta bata dame shi ba Sam Sahar ce a ransa.
Tambayar Salma yayi yace baku da Iyaye ne?Salma idonta ya kawo ruwa tana kallon Baso tana jin tsoro tace ae bamu da su,Yaya na bashi labari? Baso yace cikin dabanci ku kuka sani ko ki bashi ko kar ki bashi duk daya.

Salma ta Kalli Nawaf tace mu yan asalin Ringim ne da babana da baban Baso uwarsu daya ubansu daya,su biyu iyayensu suka Haifa,tun suna Yara iyayensu suka rasu sai yan uwa Kuma suna can kauye,cikin maraici suka taso ba irin wahalar da basu sha ba a rayuwa har suka dawo Kano suna Sana'a suka samu gidan haya suka yi aure a cikin gida daya kowanne da matarsa suna zamansu lafiya kuma matan nasu duk Yan Ringim ne dangi ne,lokacin baban Baso shine Babban Haladu matarsa ta haife shi yaci suna Umar ana ce masa Baso,ni kuwa ko cikina Babu lokacin suna zaune har sai da ya shekara goma sha biyar sannan aka samu cikina,lokacin Kuma Maman Umar Baso ta rasu sai Babansa,ranar da Mamata ta haife ni anyi murna naci suna Salma,muna zaune lafiya har Baso ya cika shekara 32ni Kuma ina shekara 18, watarana Mamana Aisha tayi girki shinkafa da wake lokacin ina Makaranta, Baso kuma ya gama iya secondary an turashi almajiranta har ma yana Shirin dawowa ya zama saurayi sai aure,ni Kuma ina Ss3,Mama ta zubawa Haladu Baban Baso abinci itama ta zuba nata taci ta koshi,Sallar azahar tayi da kyar lokacin cikinta ya fara ciwo tana idarwa ta kwanta daga nan ko tashi batayi ba ta rasu,Ranar Kuma Baso ya dawo ganin gida ya zama saurayi ashe ba karatun yake ba kawaii Shaye Shaye ya koya a almajirantar shi,tun yana yaro a boye yake sha Idan baya gida yana can duk an zaci mutumin kirki ne ashe ya lalace illar tura yaro wata uwa duniya da sunan Almajiranta wasu dai ba karatun suke ba,sabo da Babu me daukan nauyinsu yunwa masifa ce ace yaro bara zaiyi yaci ya koshi,Babu tarbiyya Babu me lura da shi bare lafiyarsa duk sai abinda yaga dama.
Baso yana zuwa ya samu Haladu Babansa yana Shure Shuren mutuwa ina shigowa Nima da Uniform Dina na iske Mamata ta rasu bata motsi na fito da gudu na samu Baso gaban Haladu yana Shirin tafiya lahira.

Haladu Hannuna ya kama ya kama Hannun Baso ya hada waje daya yace Baso gata nan ban muku dole ba amma zanso ace ka auri Salma,ka daure ka auri Salma Kaine kadai zaka rike min marainiya yar Dan uwana da Amana,Karka bari tayi kuka ka aureta ku zauna lafiya ka kula da ita,Karka sake komawa Makaranta ka zauna ka nemi Sana'a kuje danginmu su daura muku aure Karka Kaci Aman....kafin ya karasa rai yayi halinsa, ranar munyi kuka na fitar hankali ni da Yaya Umar Baso, bayan anyi bincike aka gano ashe waken da Umma tayi amfanin da shi ta dafa shinkafa da wake maganin kwarin da aka Saka masa guba ce wacce su dai tafi karfin jininsu tunda wasu sun dafa Kuma basu mutu ba amma su ta musu illa.

Salma taci gaba da cewa abinda iyayenmu suka mutu suka bari shi muka tattara muka siyi wannan Dan gidan muna zaune,tace Yaya Baso kayi hakuri zan fadi halinka,yace to yar iska sai kinci ubanki karasa ina ji,Salma tace ni da ka ganni bana jin magana ina da tsokana,shi Kuma Baso kullum Shaye shayensa yawa yake gashi ya iya gyaran machine sana'arsa kenan gyaran machine yana Shaye shayensa amma Kuma ba laifi kullum muna ci mu koshi ko ba Dadi,yana masifa yaki cikawa Mahaifinsa burinsa yace baya so na,ba wacce ya tsana Irina,kullum sai ya dake ni ya zageni ya tsine min ba muguntar da baya min...kafin ta rufe baki a labarinta Baso yace to bana sonki ko dole ne nace bana so, Salma taci gaba tace duk duniya ni ba Wanda nake so Irin Baso ina sonsa a duniya amma yaki aurena,ni ke masa wanki da guga,girki,ebo ruwa,komai da ka sani macen aure tana yi ina masa burina ya aureni,rannan daga tambayarsa yaushe zai kai Sadakina wallahi har targade ya ji min,gashi a haka yana da addini ga taimako,Kaga wancen mahaukacin tun muna Yara kowa ya sanshi a bola yana tsince tsince sai dai baya duka sannan haka zaka Ganshi a unguwa yana bin gidaje da kwanon barar abinci ana bashi sadaka yana ci,Kuma baka Isa ka wanke masa kwanon ba,sannan ko an masa wanka ya dinga ihu yana zubawa jikinsa kasa da bola,sannan baya magana,bashi da inda yake kwana haka zaka ga ruwan sama ya masa dukan tsiya a bola,sauro,sanyi rana duk a Kansa,amma Baso Baba yana rasuwa kaga wancen dakin zaka Ganshi kamar kango to dakine Baso ne ya dakko mahaukacin ya kawo shi,wallahi duk sati sai ya masa wanka,Idan bashi da lafiya shine yake Kiran mutane suna tayashi ya kaishi asibiti ayi masa Allurai,abinci Kuma kullum da kwanonsa ina dafawa zai fito har ya Saba ma.
Dakinsa ne leka ka gani har net ya Saka masa amma dake mahaukaci ne sai ya fincike net din ya kwanta haka sauro yayi ta cizonsa, Dan Allah ai ya cancanci a so shi ko?

Nawaf yana gama ji yace ya cancanta gaskiya ta wani bangaren ma sai wannan ya zama silar shigarsa Aljanna wannan ba karamun jahadi yayi ba,Baso yana ciccijewa yace ke zan tattaka ki wallahi Allah bana sonta ni bana son kyakyawa,Auta dariya yayi ana Neman me kyau shi baya so,yace kai to sai mummuna? Yace ae ni mummuna zan samu na taimakawa,Nawwar yace lallai Shaye Shaye ya maka illa baka ganewa ka haukace ai wannan tayi gata da hankali kalleta fa chaschas chas da ita,Baso matashi son kowa kin wacce ta rasa da shi Shima yana nunawa da hannu yana magana bana so wallahi,Salma ta fashe da kuka tana cewa Idan baka aureni ba mutuwa zanyi Dan Allah ka cikawa Baba burinsa ka biya Sadaki na,a fusace Baso ya mike ya zare belt dinsa ya fara tafkar Salma,Auta ne ya kwaceta da kyar akan kawai tace ya biya Sadaki ta har da fasa mata gefen Ido tana kuka wiwi,Nawaf a ransa yace ya kamata a taimaki yarinyar nan gaskiya zai iya kasheta watarana gasu su biyu a gida Kuma ba muharramai ba wani abu zai iya faruwa gashi shi Umar din Dan kwaya ya fara haukacewa,Nawaf tashi yayi yace zai tafi Salma ta biyo shi tana kuka tana cewa Dan Allah duk da cewa baka da wasu shekaru kamar Yaya ka sa baki ya aureni,Auta yace karki damu zan taimakeki,ta fara murna ta goge hawayenta kamar ba ita aka gama zanewa ba, tace yau kawata Sumayya sai ta ji labarin nan Umar zai aureni tana tsallen murna,Nawaf yayi dariya suka fito har Baso.

Suna fitowa kofar gida Salma taga me siyar da madarar turare da yawa zai wuce da abinsa a Kansa,Salma tace tsaya me turare,ya kawo ya sauke kwandonsa na turare,Salma sai da ta samu Wanda zai wahala a samu a wajensa dama haka takeyi Idan taga me turare wai Dan ta samu na banza,sai ta Kira Wanda babu ma sunan turare haka wai malam kana Umarsal? Sunanta ta hada Dana Baso Umar ita Kuma Salma shine Umarsal,Bai taba jin sunan turare haka ba bashi da shi yace Hajiya Babu,tace a'a dole kana da shi Muji na wajenka,Me turare ya dinga Bude turarukansa tana dangwalawa a hannunta kala yafi talatin tace gaskiya Babu kayi hakuri jeka,shi me turare sana'arsu ce haka dole sai an dangwala kaji irinsa,yace to ya tattara tarkacensa ya tafi,yana tafiya ta murje a hannunta ta shafe hijab dinta da kayan jikinta har wuyanta ta shafe tace Alhmdllh naci banza ina fita za a ce na Faso gari,Auta yana tsaye yana kallon ikon Allah dariya ta bashi da son banza yace ke turare 500 baza ki iya siya ba? Salma tace rufa min asiri ban iya almubazzaranci ba shinkafa bata ishe ni ba ina naga ta kamshi ta wuce tayi tafiyarta ta bar Baso da Auta.

Baso yace yawwa ta tafi yanzu kai Dan inane? da Alama ku masu kudi ne Kalli shaddarka Kalli ma fatarka wallahi kayi hankali yan Hisba suna ganinka a Kano sai sun aske maka wannan gashin na kanka da ka masa wani aski mu a nan easy dai easy dai abokina Allah wallahi,Auta yayi dariya yace Sabreen tazo ga Dan uwanta wannan ya girmi kanta,Umar Baso yace yawwa wani Deal zamu yi,kai kaga da Alama kana da kudi,ni so nake na samu kudi na alkinta rayuwata gashi gyaran machine nake yi,Dan Allah Oga ko zaka lallaba ka rufa min asiri? Zabura yayi ya sake ja da baya yana gwadawa da hannu yace kaga master asiri zaka rufa min ya sake kankame hannayensa kamar me jin sanyi ya makale a jikin Katanga yace wani taimako zaka min kaga kullum sai na roki kudi wajen me duka kaga na roki trillion dari,billion bakwai,na dawo million talatin, na sauke farashin zuwa dubu dari biyar,dubu dari,dubu hansim har na dawo dubu biyar to abin sai godiya kudin sunki zuwa,jari nake nema Dan Allah ko zaka siyi Salma ni ka siyeta duk yanda zaka yi kayi da ita,Idan ma za a iya maka aure kazo na baka ita ka bani million daya gata nan.

Auta yace ba ruwana ya juya zai tafi abinsa amma Umar ya tare masa gaba yana karkace baki yace ya haka yawa kake Oga haba abokina,haba Yayana to ka aureta ka bani dubu dari biyar,kai dubu dari uku ma ya Isa ai baza tayi tsada ba tunda ba a gidan masu kudi ta taso ba,Nawaf yace to naji kawai ya furta sabo da ya kyale shi ya tafi,yace Yayana bani number ka zamuyi Business din ko baka gane bane ey kar ka Yi mini ae yane ka gane,Nawaf ya bashi number dinsa suka rabu Umar Baso yana ta uban murna zai rabu da kaya ya huta ga kudi zai samu,Nawaf Kam Airport ya wuce yana tunanin lamarin Baso shi Kam ba ruwansa bazai iya ba zai Jira dai Sahar dinsa.
Bayan ya koma gida da kwana daya Baso ya addabi Nawaf da Kira a waya Nawaf kuwa yaki dagawa abinsa ya share Kiran yaki dagawa Sam.

Yana dakinsa a kwance Mami ta shugo tace gobe dai kasan zaka fara zuwa University an gama komai ko? Yace ae na sani Mami,kallonsa tayi tace ko tunanin Sahar dinne? Kai ya daga mata wai ae ya furta please Mami kije ki ji min ko zasu yarda ni nafi sonta,hmm amma Idan naje suka ce a'a shike nan ka hakura? Yace ae na hakura amma kije,to shike nan cewar Mami.
Bayan kwana hudu Mami ta shirya tare da Nasira da Sultana suka siyi kayan kwalliya masu kyau da turaruka driver ya tafi kaisu da yardar Baffa.
Mami suka ga gidan su Sahar masu kudi suma,iso aka yi musu,Sahar dince ma ta tarbe su tana Palo tana kallo dama Nawaf ya fada mata sun taho,taci kwalliyarta sosai ta sha Atamfa me tsada,har kasa ta durkusa ta gaishe da su Mami tace bari na Kira Hajiyanmu ta haura sama da sauri,tana uban murna Hajiyansu tace sun zo kenan? Sahar tace ae,shi yasa naga kina murna kamar Zaki tashi ki sani wallahi baza ki auri wannan yaron ba yaro karami wani aure zai iya rikewa,ga saurayi na kirki babban mutum me hankali me kudi na Kansa ba Wanda ya dogara da kudin Iyaye ba,wallahi Idris Zaki aura nutsatsen yaro ni da mahaifinki ma ki sani baza mu yarda da wannan yaron ba karki ce ban fada Miki ba.
Hajiya fitowa tayi wajen su Mami da fara'a suka gaisa sosai,sunyi hira Mami tace dama akan maganar Nawaf ne da Sahar...kafin ma Mami ta rufe baki tace ai an Riga anyiwa Sahar Miji Idris shi zata aure,ina Sahar ina Nawaf wannan ai yayi kankanta sai dai karatun ai,ya tafi Makaranta wannan ai Gigi ne na Yara haba Kuma sai ku biye masa shirme ne wannan,Baban Sahar ne ya fito zai fita Hajiya tace Mamin Nawaf ce yaron nan da aka dinga rikici da shi yana hurewa Sahar kunne,to...to.to Allah sarki ai kin fada musu anyi mata Miji Ina Sahar ina wannan,Sahar tana gefe ta labe tana kuka wiwi bata da bakin magana face kawai ta kyale Nawaf yayi kokari yayi iya yinsa,Mami ta gama jinsu irin rashin iya magana ta iyayen Sahar tace ba komai Allah ya hada kowa da rabonsa suka ce Ameen suka watse suka bar su Mami su kadai a Palo da ruwa da lemo a gabansu,Sahar ce ta fito tana cewa Dan Allah kuyi hakuri,ba komai wlh baki da laifi ke amma kinji abinda suka ce kiyi hakuri kiyiwa Iyayenki biyayya Dan Allah karki sake Kiran Nawaf ku hakura da juna Allah bai so ba.
Sahar tana goge Kwalla ta raka su Mami har mota suka bata abinda suka kawo mata tayi godiya ta koma ciki bata da bakin magana iyayenta sun gama da ita.

Mami tana komawa Nawaf ya tareta a Palo yana tambaya Yaya? Mami ta Mika masa waya tace ji da kunnenka shi yasa na maka recording sabo da Karka dameni,Nawaf ya kunna ya gama jin komai a kunnensa Sultana tace sai kaga ma irin wulakanci da suka mana wallahi Auta amma Sahar bata da laifi,Nawaf yace sai na Riga yar tasu aure inshallah auren huce takaici zanyi,Mami tace ko kai fa kayi hakuri ka nemi wata amma tare da bikin su Sultana za a hada da naka tun wuri ka nemo mace wlh ko mu zabo maka ni da Baffanka,Auta yace yanzu Mami ai dai sai ku bari na huce ko ku sanda na hadaku kuka shirya haka nayi muku? Auta zaiyi hawaye yace Mami daga cewa ina son aure shike nan sai kuce ko ban samu wacce nake so ba zaku zabo min Hakan yayi kenan? Baffa Shima ai ba haka mukayi

2 Comments On YAR AIKIN KARUWAI Book 2
avatar
zainab-ibrahim-8

11 months ago

Reply

Thank

avatar
ghh

10 months ago

Reply

Replying to zainab-ibrahim-8

Yayi kyau?

Please Login or Register in order to submit comment