Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciki ya kamata tace yanzu haka kake yiwa mutane gyaran targaden har mata?

Cele suna zaune a Palo ita da kaka tana duba yanda ake aikin hajji ingantacciya a cikin wayarta suna karantawa tana koyawa kaka,Kaka yace yanzu dawafin bankwana bazan juya na Kalli ka'abah ba kallon karshe Idan zamu tafi? Cele tace babu kyau Idan akaje dawafin ban kwana ba a juyawa a Kalli ka'abah kana gamawa fita zaka yi ba juyowa fahimtun? Kaka yace Na'am.
Bayan aikin hajji Yazo su Cele aka dauki niyya suka harami suka fita,su Mairo ma duk sun fita aikin hajji,Ahsan ma yana ciki da shi ake aikin hajji bana sabo da Cele,motar da zasu tafi filin Arfa shi yasa karama aka dauke su Basu sani ba,haka suka yi aikin hajji ingantacciya cikin kwana uku kaka yayi aski Cele ta Yanke gashinta dai dai Gabar karamin yatsa sabanin su masu gashi kawai sharbe shi suke yi yanda suka ga dama,Cele anci sa'a dake aikin hajji ne bata yiwa kowa masifa ba sabo da kar ta bata aikin Hajjin ta har sai da suka gama lafiya sun gama duk wani Shirin dawowa Nigeria Cele ta fara zazzabi sosai,Hammad driver Ahsan yana ta Kira ba a daga ba ga Kaka ya tafi yiwa mutanensa Sallama Idan tafiya ta tashi kawai sai dai su wuce,Hammad jin ba a daga ba sai ya tafi gidan ya buga shuru ba a Bude ba,kofar ya Murda ya shiga ya samu Cele tana kudundune a bargo tana rawar Sanyi,dawowa yayi gida da sauri yace Ahsan na samu Cele bata da lafiya tana ta rawar Sanyi da Alama zazzabi take,Ahsan hankalinsa ya tashi ya dinga yiwa Hammad masifa Kuma sai ka taho ka kyaleta haka Idan ta samu matsala ya ja tsaki ya karbi key ya fita da sauri a mota,yana zuwa direct gidan ya shiga,ya Samu Cele ta sume ma bata hayyacinta,hankalinsa tashe ya sunkuceta sai asibiti,aka bata gado yana ta zirga zirga ya rasa inda zai sa kansa.

Komai da sunansa aka cike mata,bata Dade ba ta farfado ta Bude idonta sai ga likita ya shugo bakin fata ne yana jin Hausa sabo da Cele Ahsan ya nemo shi,ya tsaya a kan Cele yace sannu kin tashi jini ne ya Miki karanci a jiki bakya shan magunguna,Cele tace ai na zaci abinci ya Isa jinin yayi yawa,yace ai dole sai kin sha magani,Bai Kai a Kara Miki jini ba amma sai kin sha magani dole,yace Wanda ya kawoki Ahsan dama ya damu yana zaune baida sukuni sai zirga zirga yake ya rasa inda zai sa kansa,Cele tace Ahsan Kuma? Yace ae balarabe ne shine ya kawo ki,yanzu Ahsan ne ya kawo ni? Yace ae bari a turo Miki shi,Doctor ya fito ya samu Ahsan ya rasa inda zai kansa,likitan yace zaka iya shiga ta tashi Dan Allah a kula da ita ta dinga Shan magani,yace Inshallah ya nufo dakin da Cele take a hankali ya turo kofar ya shigo,Cele farin ciki ya cikata amma a zuciyarta,a fili Kuma harara ta watsa masa ta dauke Kai,Murmushinsa me tsada ya sakar mata.

Kujera ya samu a gabanta ya zauna tare da dora hannu a wuyanta Hausa taji yayi yace ya jiki,mamaki ya kamata tace la kaji Hausa,yace yanzu ya jikin? tace da sauki naji normal yanzu za a iya sallamata,yace anjima zasu sallame mu,hannu ta Mika masa ya rike suka damke hannaye waje daya,tace Ina bakar kadara? ba komai yake ji a hausar ba yace dai wa? tace Maheerah,tsaki ya ja yace kar ki sake min zancenta,Hammad ne ya shugo Cele ta Bude Ido tace Karka cuceni masoyina Yazo Karka sake naji bakinka kace kana so na a gabansa ni wannan nake so,Ahsan tashi yayi ya koma gefen Cele ya zauna kamar zai hadiyeta,Hammad zaiyi magana Cele tace ahir Dinka taimakon da ka mana ka kyauta mun gode Dan Allah Karka kashe min aure,dariya Hammad yayi,tace Idan kana yiwa Allah ka kama gabanka harda hawayenta,Hammad yace hear me out please ki saurareni.

Ya fara bata labarin komai yace ni fa bani nake Miki kyauta ba ni yaron Ahsan ne komai kike gani shi ya turo ni,yace har sadakar da aka taba tareku aka baku shi ya tura balaraben,gidan da kuke,siye awararki,kuje Shopping ace an biya muku duk shine ba ni bane,dama sani yayi sabo da ya sake gwadaki kina da son kudi ko babu Zaki so ni ko a'a,sannan ya auna irin son da kike masa,Cele ta Kalli Ahsan tace to bazan zauna a saudiya ba sai dankwali yaja hula Idan kana so na sai dai ka siya min gida a Nigeria ko muyi 50-50 Idan muka yi wasu months a Nigeria sai mu dawo nan muyi watanni sannan sai da kaka a kusa Dani ayiwa kaka bangarensa,Ahsan murmushi yayi yace yanda kike so,yaushe zaku tafi? tace nan da sati biyu,yace a daura mana aure sai ku tafi zanzo bayan satikai,Cele tace ba matsala da larabci,ana sallamarsu daga asibiti.

Aka siya mata magungunan, Ahsan mota ya Bude mata ta shiga ya rufe bayan motar ya shiga shima su biyu a baya,juyowa tayi zata saci kallonsa Shima ya juyo suka hada Ido,Cele tayi fari da Ido,hannu ya Mika mata ta Miko masa hannunta zoben Gold ya zaro a aljihunsa a cikin gidansa ya sa mata a Hannun,Cele tayi masa godiya tana kallon yatsunta
Suna zuwa gida suka iske Kaka yayi tagumi baiga Cele ba,ai ganinta da mutane yace Ina kika shiga batan kai kika yi? Cele tace kasan ka fita bani lafiya ta kwashe labarin komai ta fadawa Kaka, tace Wanda na gani nace maka kamar Ahsan ai kuwa shine din,Kaka yace Alhmdllh Masha Allah,ya bawa su Ahsan wajen Zama suka zauna,,ya Kalli Hammad ya masa ambola dakuwa yace ungo nan,Ahsan ya kalle shi Shima kaka ya masa dakuwa yace Kaci ananinka zaka yi wasa da kwakwalwar mu,Kaka yace Cele to ke yanzu kin yarda Zaki aure shi? Cele tace dari bisa dari Kaka,a nan wajen akayi maganar aure da kaka da kudin da za a kashe.
Kaka yace to mufa duk sharudanmu sai ka cika har lefe,Ahsan yace ba matsala Idan Yazo kasar Nigeria zai taho da lefen karsu damu.
Sai dare su Ahsan suka tafi, Cele tace Kaka na karo wulakanci Yasin,Kaka yace yo ai ba ke kadai ba Nima na karo wulakancin harda rashin mutunci ma, Cele tace dole na gayyaci Yan madugo Yasin suzo suga yanda ake abin arziki.

Washe gari da yamma Ahsan ya dauki wanka na kirki Yazo zance,Cele harda kwalliya aka Saka sabuwar Abaya kamar a Nigeria ta fito tana taku dai dai,Ahsan ta hango shi yake driving ya harde a jikin motarsa yana kallonta yana wani murmushi,Cele tana karasowa dama suma ba ruwansu ba wata doka suke bi ba, ya rungume ta a jikinsa Cele tana shakar kamshinsa me Dadi kiss ya mata a goshi yace ta shiga mota suje yawo,to akwai freedom, ya zaga tare da Bude mata mota ta shiga ya rufe ya koma ya shiga Shima suka tafi,suna tafiya suna Hira yana cewa dagewa yayi ya koyi Hausa wajen Hammad,yace Kuma na shiga Makarantar turanci zalla yanzu Shima yana tsinta.
Wuraren shakatawa ya Kai Cele,suna nishadinsu ,da zasu dawo Cele tace ya kaita tsohon gidan su na yan lesbian,Bai san me zata yi ba ya kaita ta fita ta shiga gidan da gadara ta kwala Sallama tace Yan Iskan gidan nan ku fito Ina gayyatarku bikina ranar Friday daurin Aure kuje za ayi walima,fitowa sukayi tace da gaske nake ana daurawa washe gari zamu wuce Nigeria,yanzu ma tare muke da shi,sabo da gulma sai da suka dinka lekawa suka ga hamshakin balarabe,Meenal tace na yarda ai kin Kai a so ki nima ba gashi Ina cikin jerin masoyan ba,suka ce sai munzo,Cele tace Idan ma baku zo ba kanku kuka yiwa domin za a bankare raguna za a soke rakumi ato, ta juya ta tafi,ta shiga mota ya mata take away na kayan makulashe ya sauketa a gida.

Ranar juma'a kuwa Kaka da Wanda ya sani takari maza suka je masallaci inda Yan uwan Ahsan da abokansa mutum biyu suka taru aka daura Auren Cele da Ahsan akan Sadaki Million Daya a kudin Nigeria,Cele kuwa tayi gayya sosai ranar da yamma takari suka dinga layi,Ahsan ya kama musu wani joint an gasa raguna ga su Madara da kayan ci iri iri Kaci iya cinka ka barshi,da kanka zaka eba ka yanki rago a bankare,Takari banza ta fadi bakin kowa da maiko,Cele taci gayu cikin Arusa rigar Amare fara komai fari an mata make up gashi rigar da kalar mayafinta ta musulman larabawa sai tsada,Kidan labarawa na tashi a wanjen ana laftar raguna,Babu Namiji ko daya a wajen tunda walima ce amma Kaka yana wajen shi yaja gefe yana ta kwasar gara ko magana baya yi,Sai dare suka gama Ahsan Yazo da Kansa ya sha kayansu na larabawa harda Dora Alkyabba golden color irin shigar masu kudin larabawa,Sun zuba pics iri iri,Ahsan yana daukan Cele yace yau tare zasu kwana,Cele tace a'a wallahi ban yarda ba ni,ta fututtuke masa ita bata yarda ba,Ahsan yace mene aciki Matata ce fa ke,Cele tace wlh ban yarda ba ni gaskiya azo ayi min kaca kaca na tafi gida da rubabben fada baza ta yuwu ba,lah..lah.Ahsan yayi murmushi yace to ko romancing? Cele tace zero wallah kayi hakuri kazo can mu gama shirya komai sannan,Ahsan harda wa'azi wai ba kyau ta guji mijinta,Cele tace daga baya sai ka yafe min, wallahi Yasin Ina sam Alqur'an bada ni ba,tana nunawa da hannu, parking yayi a kofar gidansu,har tasa hannu zata fita sai Kuma ta fasa ta juyo ta turo masa baki tace ungo yi kaji,ka ganka harda wani komawa maraya da Kai, ta fada da larabci,yayi dariya ba musu kuwa ya tallafi fuskarta a hankali yana tafiya a hankali da fuskarsa zuwa tata,Cele tace ah naga ta kaina komai sai anyi cikin sanyin jiki haba Salihu komai style baza a tafi straight ba,a dinga komai da jiki,na auri iyayen soyayya ya zanyi dole na koya nan ba kaskon suyar Awara bane ba fa,dole Ina komawa na tafi wajen Nazifa ta koya min slow motion Nima,bakinsa ya hade da nata ya fara mata wani irin kiss na mussamman,Cele tace eho kaji kaina wani yammmmm,duk da bai gane hausar ba yanda ta danyi ihun ya bashi dariya,yaci gaba ta sake janye bakinta tace taratsatsi akeyi a cikin kaina ta rankwashi kanta tace muje zuwa Malam Hafizu,a soyayyar ma Kai Hafizi ne ja muje,Ahsan yaci gaba Cele ta sake kwace bakinta ta sheke da dariya harda bugar jikin motar tace Allah Dadi shegu ashe haka ake ji,ta sake conowa Ahsan baki ,yanda tayi sai da ya dinga dariya,tace wallahi Fada wani zuut zuut take ta karbi kidan,suka ci gaba da kiss Cele harda tafi tace yau Ina karbar darasi wallah yo in da wannan ai masifar ma dainawa zanyi,sai da yayi kissing dinta yanda yake so duk Cele ta zurma ta zauce a kiss kawai,zata tafi harda manta Jakarta sai da ya sauke glass ya Kirata ta dawo ta dauka suka yi Sallama yana ta murna kamar an sashi a Aljanna.

Cele da gudu ta shiga gida kaka Yace ya akayi har na rigaki zuwa gida tun dazu Ina kuka tsaya ne? Cele tace Kaka soyayya muka yi,Kaka ya Dafe kirji yace ki bari sai an kaiki dakinsa,Cele tace ai dama ta wuce bedroom ta fada saman bed dinta tana ta murna harda tsalle tace wayyo Allah dadi kashe ni,Guy nan ya hadu matsiyaci kaga kiss,jikin mudubi taje ta tsaya tana kallon bakinta tace ya bani ta nan ya bani ta can a'a,Gaskiya kullum sai munyi,boobs dinta ta kalla ta lumshe ido tace sai naji Ina so a taba su,to Kai kuyi hakuri sai next time ku dai abinda nake so da ku shine ku cika masa hannaye kunga dai tsohuwar matarsa tana da su karku bani kunya kunji yawwa, ta baya baya ta ja ta fada a saman bed tace yau bazan iya bacci ba.
Washe gari Ahsan shi ya Kai su Cele Airport da kayansu,a mota ma sai da suka Kara kiss amma kadan tace sai kazo suka tafi Yana daga mata hannu ,sai da jirginsu ya tashi sannan Ya koma gida Shima zuwa dare ya koma Riyad,Maheerah ta haukace jin labarin Ahsan yayi aure tace ba a Isa wata ta shiga gidan ba ta dauki alkawari.

Mami ce ta shigo da niyyar duba Auta taga ya jikin nasa ta same su a tsaye yana faman lagudewa Salma duwaiwaka tana cewa nan haka nefa,Karar Bude kofa suka ji da sauri Auta ya sulale kasa yana taba kafarsa yana cewa har yanzu kafar nan bata karasa warkewa ba,Salma itama ganin Mami da gudu ta duka tana cewa Sannu ai sai a koma asibiti,Mami juyawa tayi tare da rufe musu kofar su tana mamaki,tana fita Auta yace na shiga uku,Salma tace Kai tafi can dama ba abin kirki kake min ba tunda gashi nan kaji tsoro,Auta ya harareta yana kallon hannayensa yana cewa daga gyara sai ya zama abin tsiya,tace ae Karka sake taba ni bana so,ta juya ta fice abinta.
Tana fitowa suka yi Ido hudu da Mami a zaune tare da Miracle,Sosa Kai ta fara tana maurmushin borin kunya tace Mami Auta gaskiya yana jin jiki sai an dage a Kansa,Mami tace au haba?tace uhm ta zauna tana kame kame Mami yaushe za ki min kitson? Mami tace sai gobe tana ganin kinibibi a fili,dariya tayi a ranta Kuma ita Kam taji Dadi,Miracle tace Salma kina da gaskiya kuwa sai wani soshe soshe kikeyi,da sauri tace Wallahi Aunty Ina da ita ba abinda muka yi bamuyi komai ba,Mami tace kawo min ruwa a kitchen,ta tafi da sauri dama kadan take Jira ta fece.
Miracle ta dawo gaban Mami da kwana sabo da cikin,Nawwar ya hanasu sakat da sintiri watarana ma a nan yake kwana, yau Monday Nawwar yana Office daga ita sai Mami a Palo tana jin ciwo sama sama tace Mami wallahi kamar nakuda nake yi,Mami tace haka ake nakudar lallai baki San nakuda ba ai sai kin tubure mana tukun,Rabi tace to ta tashi da kyar ta shiga bedroom ta kwanta ciwo ya fara maguzata bayan awanni tun tana daurewa har ta gaza ta fito fakat daga dakin tace Mami har yanzu ban tubure din bane? Mami tace ahhh kin tubure kwarai kuwa nakuda ta kankama bakya hayyacinki tunda kika ce haka muje asibiti,a wajen ta tsuguna ta dafe mara tace wayyo Allah, La'ilahaillallahu kasusuwa na suna farkewa suna budewa wayyooo shike nan kasusuwana sunyi warka warka,Salma ce ta fito ta rike Rabi kamar itace zata haihu wayyihuhu jama'a ku kawo agaji,Auta ne ya fito sanye cikin jallabiya,Mami tana hado kayan haihuwa,Auta yana zuwa ya dauki Rabi cak ya fita da ita har cikin mota Salma ta fito da gudu tace ni zan karbi haihuwa ta shige gaban mota,Auta ya rude ya manta ya tafi ya bar Mami,tana fitowa su har sunyi nisa,Salma ta cikin motar ta tsallaka baya tana dannawa Rabi ciki tana cewa daure,cije,manne,ke kamar ba mace ba Nawwar da kike Kira me zai Miki kyale Nawwar ki Kira Allah.

Rabi ta samu Salma ta kankameta tana jijjigata ta buga kan Salma da jikin glass din mota sabo da azaba tana cewa wayyo Allah Nawwar wayyo zan mutu,Salma ta dafe Kai tace ka Kira Mami zata sumar Dani,Auta ya dinga dariya yace uban wa yace Miki ana zuwa a dinga yiwa me nakuda katsalandan,Salma zata gudu Rabi ta riketa Kam tana cewa Idan kika tafi mutuwa zanyi wayyo Allah,Salma Idan kika tafi mutuwa zanyi ki rikeni ta Miko hannu,Salma ta riketa Rabi ta fisgi Salma kamar zata karyata,Salma ta fashe da kuka tace Nima zata aikani lahira,Mami sai driver tasa ya kaita can,Auta ya kirawo su Star kafin kace me duk sunzo har Wise,Nawwar kasa driving yayi sai Auta ne yaje ya dakko shi,gaba daya ya haukace ya rude,Santana har da shi ya wani falfalo yana wayyo miracle yau za a yabawa aya zakin ta,da a baya ne ai nine zan karbi haihuwar lokacin Ina Hajiya Santana ta,yanzu kuwa na koma Kai maimakon ke.





Kuyi hakuri wallahi bani da lafiya zabbabi nake malaria da kyar nayi typing.






AsmaBaffa
08061929616🌼'YAR AIKIN KARUWAI 2🌼
MATAFIYA


BOOK 2


66-70


Official

By
AsmaBaffa



SADAUKARWA GA
ZAINAB USMAN



Adashin kudi kamar haka
20k kwasa 200k
Slt 1 2 4 7 8 9 10

30k kwasa 150kslt1 2 4 6 8 9 10

50k kwasa 500kSlt1 2 3 4 5 7 8 10

10k kwasa 100k Slt2 3 2 4 7 9 10
Mebukata yaneme wannan numbern👇
09049197049

Munayin adashi kamar haka👇
Kayan daki set na kujera da gado
Kayan kitchen
Freezer fridge
Injin wanki
Gas
Dasauransu
09049197049



Page naku ne

Ummu Minnah
Ummu Annur
Aunty Nurse Zariah
Princess
Maman Ahmed
Mrym
Maman Aslam an Abdul
Mamar Bintou
Ummey Muhammad
Maman Murtalah
Sumayya Auwal
Ummu Lateefah
Mommy Sadiq

Ummin Sadeeq
Ina gaisuwa




Santana sai safa da Marwa yake kamar matarsa,yace yanzu ba dama a shiga,Nawwar ya watsa masa wata uwar harara ba Shiri yayi mukus,Mami har Salma ta Koro waje,duk suna waje,na danji dama dama tace a turo min su Wise, kunyar nake ji suruka zata kalleni ni gwara su Wise,ciwo yana dawowa nace ni bana son surukata ta ganni,Mami tace ashe kuwa sai in baza ki haihu ba su sun San haihuwa ne,Rabi ni dai sai tattale kafafu nakeyi,na mike daga kwanciyar na sakko kasa nayi goho nace a haka zan haihu irin tamu ta gargajiya,naji wahala nace wallahi ta asibiti zanyi na dawo na kwanta akan gadon ina bude kafa,ban San sanda ma na cire kayan jikina ba ina tattale kafa,kan yaro ya taho yaki fitowa sai ya fito ya koma,likitoci suka zo suka agaza har ya fito,sai kuka inya inya,Su Wise suna ji sai shewa yeeeeeeeeeeee,Nawwar ya harare su yace ai Kwa bari dai aji lafiyarta ko, nan da nan aka gyara Miracle ba kayan komai a jikina wahala tasa na cire,ta hada gumi sharkaf duk,na manta ma da suruka na nan,sai da aka gyarani tsaf aka gyara dakin neat nurse tace Hajiya sai a sa kaya ko,kunya ni Miracle naji Mami an goge jariri an nade shi aka Mika mata,ta mika min zani tace gashi maza ki daura daki za a canja mana sai ki wanke jikinki mu tafi,nan da nan aka canja mana daki,abinka da private komai Kal Kal yana kamshi,Mami tace ruwan zafi fa,na fara wani yarfe hannu Mami ta fita ta Kira Wise da Star suka shigo tace kuje ciki ni kunyata take ji ku tabbar ruwan zafi ta sa,Ai kuwa suka shiga sai kace Yan iska a tsaye ma
Nayi wanka na danyi gashi sama sama nace sai anje gida na fito,bani da karfi sosai,Abaya Wata Maroon me kyau Mami ta bani na Sanya na shirya kaina sosai na kwanta a saman gadon ina huce gajiya,Mami ce ta fito tace Zaku iya shigowa.

Sun Riga me abin shiga ma Nawwar ya tsaya yana kallon ikon Allah yace sai kace Dan su to ku gama ni na shiga kowa yana daukan jiririn Kato da shi yana masa Addua,Inna da Seraline suka iso suma har da abinci lafiyayye a manyan flasks,Star tace kice girki kika tsaya yi,tace wlh shi na tsaya yiwa Me jego harda tea yaji hadi aka zuba min na shanye nan take sabo da yunwa, Mami ganin Nawwar shuru bai shigo ba ta fito masa da jaririn ya karba yana murna kamar zai tashi sama kafin ma ya masa Addua yace Mami ya take? tace abinci ma fa take ci kalau take fes da ita kawai karfi ne bata da shi sosai kuma wannan dama Idan mutum ya haihu yana jin hakan sai a hankali a dawo dai dai,sunyi mata Allurai da magunguna gasu ka siyo mata,ta Mika masa takardar, Mami iceko sun mata wannan abun Wanda ake kwashewa mace jinin dake mararta ni bana so a dade ana wani jini abu yaki ci yaki cinyewa,Mami tace to fitsararre marar ta Ido abinda Kai kasa nurse suka mata ai sun fada mana,dariya Nawwar yayi yace Mami sauki na nema mata fa,kaga yiwa yaro Addua ni,Nawwar ya masa Addua sosai yanda addini ya koyar sannan ya mikawa Mami yace kice su fito dan Allah ni zanga Matata wannan masifa haka duk Auta ne ya jawo da ya Kira su,Sai ga Auta ya dawo da ledojinsa na kayan marmari da nama da su Madara tarkace dai,dama yana kawo Nawwar ya bar asibitin,Nawwar ya kalle shi yace Auta ikon Allah ,Murmushi yayi kadan yace sai Aunty ta haihu zanyi dariya,yace ai kayi Da Autan Mami ta haihu tun yaushe kana can gantali,Auta yace haba ana ganinta? Yace ae mana an canja mata daki ma har taci abinci,Auta yace nayi Da shike nan na zama Daddy ya shiga ciki da Sallama suka Amsa,yace Masha Allah Aunty ya jiki? tana cin abinci tace Alhmdllh Nawaf,ya karbi yaron a Hannun Mami ya masa Addua yace kamar Yaya Nawwar kamar Aunty miracle suka yi dariya,Santana ma ya shigo yaga jariri ya tafi, sai da suka gama rubibinsu Mami tace duk su tafi gida suka fito suka tafi Banda Salma yar anace kamar danta ta karbe shi harda jijjiga shi,tsokanar Rabi tayi tace bari a masa rawa,da sauri na nunata da yatsa ina karkadawa uhm..uhm..uhm wai kar ta sake tayi masa,Auta yace to anyi da Kuma ba Saban ba,Nawwar ne ya shigo suka mike suka fito duka har Mami,ni kuwa na durfafi abinci sai yi nake,ya kalleni kawai yace sannu ya jikin? Nace da sauki na ajiye plate tass na cinye abinci,na bude ledar Auta na dauki yogurt sai da na kusa shanye roba guda,na dakko fruits nan ma naci wannan naci wancan sai da naji na koshi sannan na sha ruwa Faro nace Alhmdllh,sai lokacin na Kalli Nawwar dake tsaye yana kallona,nace zauna mana,ya sake cewa ya jiki nace da sauki lafiya nake,nace Baby local government ta fafe Yasin ta afka ai wani ruftawa tayi Kai naga bala'i,dariya Nawwar yayi, na dafa kafadarsa nace kaiiiiiii haihuwa da wahala yanzu su Wise nake tausayawa zasu dandana kudarsu, Nawwar ya zuba min Ido kawai, ina uban bashi labari na nuna kugu na nace aka rike ni ta nan,aka damki nan,aka tattaro marata aka yamutsa aka yamutsa sai naji kamar kasusuwana sun watse, Subhannallahi sai yanzu nake jin kunyar Mami tsirara nayi a gabanta,dariya Nawwar yayi yace shike nan ai kayan danta ne dan ta gani ba komai ai Larura ce,duk da haka da kunya Allah,itama ai mamanki ce ko? Nace ae mana,Allah yasa an mana hutun school Nawwar yace ai naji dadi nima,ki Kara hutawa zuwa yamma a sallamemu bari na Kira Umma,na Kira Umma ta daga nace Umma na haihu,Umma tace Masha Allah me aka samu? Namiji Umma,tace to Allah ya raya bari gobe su Omaira su taho ko kafin manyan su zo,nace to zan turo musu kudin mota,Umma tace akwai kudi fa,nace ai baza a kwashe naki ba Umma zan tura musu,to Allah yayi Albarka Ina me gidan, nace gashi bari na bashi ta mikawa Nawwar waya,ya karba suka gaisa ta masa Allah ya raya yace Ameen Ameen Umma.

Bacci na kwanta na fara shakar uban bacci tun safe bayan na haihu har 5pm sannan na tashi,Mami tace dama ke muke Jira ki tashi an sallame mu,nace to na mike a hankali ina yatsina fuska,Salma tana wajen ta kalle ni tace rauni kika ji a wajen? Mami tace shegen baki kamar kinci aku,dariya Salma tayi tace Mami yanzu ai kuna so na ko? Mami tace dama muna sonki ai horaki aka yi dauki kayan mu tafi,Nawwar ya dakko flasks da sauran tarkacen Itama Salma ta dauka suka dawo gida abinsu,bangaren Mami a sama aka bawa Rabi daki,Suka shiga na

2 Comments On YAR AIKIN KARUWAI Book 2
avatar
zainab-ibrahim-8

11 months ago

Reply

Thank

avatar
ghh

10 months ago

Reply

Replying to zainab-ibrahim-8

Yayi kyau?

Please Login or Register in order to submit comment