Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne cewar Nawwar.

Miracle naci wanka cikin leshi me tsadar gaske kamar Amarya haka na fito sabo da Nawwar ni da Jaririn ya kashe mana kudi wajen kaya,su Star dukkansu sun ci gayu suna dakina wasu a kasa wasu a saman bed, Bilkisu suka ce duk Yara ne a dakin sai iskanci fal ciki suka zauna a Palo da wasu manyan matan Iyamami ma sai yau ta shugo taga jariri ta Koma Palo,Sabreen ta shigo itama an sha gayu ta zauna tana wani basarwa yaron ma Dan lekawa tayi tace ubansa yayi dai kama anyi dangin Miji masu kyau,Rabi tace mu a gaya mana kyau,ke a gidan naku ma ai baki gaji dangin Papa ba can uwarki kika yo,Sabreen tace ai kin san Uwata kyakyawa ce,a hakan fuska kamar takashi ta Kone, Cele anci dauri an sha kyau cikin material me kyau na larabawa,ta Kalli Sabreen tace ke Malama Zaki tashi daga dakin nan wlh muna farin ciki baza ki jawo mana bacin rai ba kizo kina wani jefar da magana ke kyawun naki uban me ya Kara Miki ji nake tun daga Nawwar ko zance ba a Kara zuwa ba mun San komai muna da labarinsa,Star tace chass ko me Keke ba Wanda ya zo mu dai ayi mana shuru suna muke ko mu tashi tsohon tsumi yawwa,Sabreen ta ja wani tsaki duk kishin Nawwar ne ke damunta tace sai naga me fitar Dani daga gidanmu,Cele ta mike tayi Mika tace wayyo Allah ta duka tace sama da ikon Allah cak ta dauki Sabreen ta yo waje da ita ta watsota Palo,Iyamami tace me zan gani haka yarinya daga zuwanki ita da gidan ubanta ke kina da gado ne a gidan nan,Cele tace da laraabci Ilalliqa tsohuwa kar ki jawowa kanki wlh kiyi shuru kishi jikarki take an saketa Kuma sai me? gida yafi karfinta Mijin ma haka,ke Iya kike nan mene baki sa yaranki sunyi ba muna da tarihin ki kishiyarki ma bakin cikinki ne ya kasheta mun San komai,bakin cikin ki shine ya kashe Mijinki,Dan kishiyarki ma haka kika taba jefa shi a tukunyar dambu ko ba ayi haka aka yi ba,kinji kunya wallah sai mun sakata mun Wala a gidan nan Yar uwarmu sai tayi abinda take so Miji nata kina ganin dai ta haifo danta to Antena tayi aiki ai an dinga haifo Miki irinmu kenan jikanki kullum yana cikin jininmu yana antaya Antena Dan bakin ciki sai dai ya mutu,nifa na gama tsanarku ke da Sabreen kuyi hankali Dani badan Baffa ba da Nawwar ba da yau sai nayi tambarin tsinannu da Ku ba ruwana da tsufanki Kun shugo kuna ganin jariri kuna jefar mana da magana wata kutmar....muka muku,daga zuwa cin arziki Ina jinki Iyamami kika ce anzo an cika muku gida ana cinye muku abinci munyi muku kama da mayunta? Kalli jikinmu tsab ba yunwa kalleni Kalli Yan uwana a koshe muke bulbul damu ,wallahi ko da wasa kuka sake fada mana magana baza ku ji Dadi ba,Iyamami baki bude take kallon Cele, Cele tace bani da sauki kin ganni bani da Dadi bana gudun abun kunya a titi ma zan iya fada dake kowa ya min sai na masa,kin shigo kin ci mana mutunci kin turo jikarki zata mana rashin kunya wallahi Dan suna akeyi amma da yau sai ta San ta mana magana Kuma ko ba komai gidanku muka zo shi yasa,Allah yasa bayan mun tafi Rabi ta fada mana Kun zageta zaku ga bala'i, ta juya ta tafi tace haba sai kace ku kuka Fi kowa kudi.

Dawowa tayi ba Wanda yasan me tayi Rabi tace Cele tsiya kika yi dai amma tace a gidan sunan zanyi fada abin arziki ya kawo mu warning na musu kawai,wai a haka Cele ba fada tayi ba,Yan Palon ba Wanda ya bawa su Iyamami gaskiya akace gaskiya baku kyauta ba ya za ayi su taso suzo Kuma ku dinga jefar musu da magana harda abinci ne ya kawo su,Iyamami da masifa tace da a gidan mayunwatan suke ba,Sabreen sai yanzu ta mike a hankali tace Muje Iyamami wannan bata da mutunci sai ta karya mutum,suka tashi suka fice,Yan Palon mutan unguwa suka dinga Zagin su Iyamami.

Star tana waya tace Dj Yazo,Salma harda shewa yeeee yau akwai ratatin duwawu,suka bita da kallo tace ah dole wani bangare na industry ya motsa a'a Kun iya harka,Cele ta kalleta ta shirya mata mugunta tace zaki ga Industry bari Yan suna su watse,Star tayiwa rada tace maganin sha'awa Babu ne me karfi Wanda mace zata Kai kanta? Star tace ke akwai kinga tsaya yanzu mandula zata zo bari a mata waya ta taho da shi amma da Yar tsada dubu goma ne,Cele tace a kawo tace a ranta yau wannan yarinyar zata Daina iskanci a gidan nan.
Aka bugawa mandula waya tazo da magani tace an gama,masu Dj suka zo kowa aka fita tsakar gida,kafin kowa ya shiga Salma ita ta bude fili,Auta yana shigowa ya ganta ita kadai a ciki sai rawa take tana yiwa kanta liki,Auta yace to masu Dj take yiwa ko su Cele da suke kallonta,Cele bata rawa ita amma yau tace zata yi ta shiga bayan Salma ta dangale kafa wani dungus dungus kamar gurguwa wai rawa take,Rabi tazo tace Dalla matsa ke duk abin arziki baki iya ba sai masifa,Rabi ta daki duwawun Cele tace nan fa ake kadawa, wannan Zaki bari Ahsan yaji dadin ma kuwa gyara ni ki gani,Salma ba ji ba gani rawa take tsakaninta da Allah harda bin wakar,Auta sama ya hau wancen part din da suka kwana yana ta kallon Salma ita kadai Yana daga nesa yana furta a'a'a'a yana bin kidan, su Wise ne suka shiga tun a sannan Cele tace ba karya yanzu nasan anyi bariki a wajen nan ta ja gefe,Cele tace karku cire mazaunan ke me jego sai kin sake yagewa ko,Auta ne ya Kira Nawwar yace Yaya zo kaga abinda suke yi,Nawwar ya leko ya dafe Kai yace uhm ga Rabi can,Khaleel ya taho Shima Auta ya rufe kofar corridor yace matan wasu zaka kalla Babu matarka a nan,Khaleel yace bana son rashin mutunci Sufia ai ta zo akan kwailarka ni me zan gani,Nawwar yace Sufia bata rawa ka hakura kayi zamanka sai kace dole,Sauka yayi da sauri yasa aka kashe kidan,Salma tace rasss,yace mazan sai dai su fita mace tayi Dj,Cele tace gani DJ koya min,aka koyawa Cele ta hau karagar Dj su Kuma suka fita suka Basu waje tunda za a Kara musu kudi,Salma tace bani da fargabar kowa ku matsa yanzu za a fara,Omaira ma ta taho Cele tace kar naga yarinya a nan kidan manyan ne zanci ubanki Idan kika shiga,Omaira ta harari Cele, ta juya baya ta tsaya,Cele ta kunna kida Salma harda dukawa,Wise dariya suke kamar ta sha kwaya yanda take chashewa kamar uwarta ce ta haihu.

Mami ce ta leko taga abinda suke yi ta juya ta tafi Salma ce kawai take bata mamaki yarinya a haka kamar doluwa, Salma zuwa tayi ta radawa Cele wai ta sa speaker ta Kira Auta,Cele tayi dariya ta kashe kidan ta dinga cewa ina Auta ya fito ana nemansa a wannan fili,Autaaaaaaaa......kana Ina.....Autaaaaaaaa Angon Salma bada kanka a sare,Autan a wajen Mami Auta a wajen Salma,Nawwar yace sun rainaka wlh,Auta yace Kai zuwa zanyi ga Santana can Yazo da Jamcy fa Kalli tafiyar Santana Dan Allah an rasa wace macen shi da matar, Santana Yazo yace ah kuce harka ake mu Kam yanzu mun tuba amma da a baya ne ai mu Kam da mun kada idon garin wannan sai ku yanzu ke Jamcy shiga kiyi a Madidina wallahi,Jamcy tace da cikin nawa,Yace gasu nan duk da cikin amma yi suke basa jin jikinsu shiga kiyi a madadina ko Kuma wallahi na shiga Kuma kin san tsab zan kada kugu Dan ba gagarata zaiyi ba,Jamcy tace zan shiga yace ya Fi Miki sai na dawo daukanki sunan danmu guda,kiyi rawar nan da kyau tace to ya shiga mota ya tafi.

Auta ne Yazo waje Salma ta kwace speaker tace takawarka lafiya,a lafiya angona,ba gaba da gaba ba ko ta baya sai an shirya,Auta a gida Auta a waje Auta a waje ni Salma me abin mamaki, Dj Cele da kowa ya dauka yau ake bikina da Ango na Auta sa mana kidan Amarya da Ango,Cele dariya take tana duba wakokin,muma dariya kawai muke muna ganin ikon Allah Auta Kuma ya shiga filin daga shi sai ita wai kida suke Jira,Salma tace Miming zamuyi mu sa mana ta Hausa ko wacce miming zamuyi fa, aka sa musu wakar mudubin dubawa Salma komai ta iya kamar mayya duk abinda ake yi sai data yi,mu kanmu bamu San sanda muke tafa mata ba,Nawwar yana kallo yace ana kuruciya a can wajen,Khaleel ya leko yace Auta ai dama nasan wlh suna jenewa shike nan anga rashin kunya,ai Mami ta samawa kanta lafiya su koma gidansu,Nawwar yace an gama komai ma fa Ina ga kayan kitchen ne kawai ba a kawo ba,amma nan da sati zan Kore su ko baza ta Kore su ba zance su koma,Yafi dai Kam.

Salma sai da suka gama Miming ta karbi Speaker tace da karfi I love you Megidana sai da kowa na gidan yaji har Wanda Suke dakuna,Auta bakinsa ya manna a speaker Shima yana manne a jikin Salma yace I love you more,muka yi tafi,Cele ta jinjina Kai tace Zaki ga love sai kunci ubanku marasa kunya,Auta dai ya fice sai Murna ya shiga mota fiiiiii ya tsaya a can gefen titi yayi parking ya dinga zuba murna a titi,ya sake fisgar mota ya Kara gaba sai da yaje can wani fili fetal ya dinga zaga wajen da mota cikin nishadi,ya dinga Kiran abokansa yana fada musu,ya dauki yaren su Star yace Oven is coming Afif,Afif kamar shine zaiyi ya dinga murna yace aji Dadi lafiya Nima aure zanyi wlh,Auta yace sai Kun taho lokacin Ina da da ko ya.

Omaira kuwa soyayya ta tafi da ita gaba daya tace wallahi Nima sai an min aure na rantse da Allah Kalli Salma sa'ata sabo da tana da Aure ita tana cikin manyan mu an ware mu wallahi Allah sai an min aure ta fashe da kuka ta tsaya a gefe tana goge Kwalla.
Gate aka Bude wata hadaddiyar mota ta shigo me mugun kyan gaske,wani hadadden matashi ya fito a ciki wankan tarwada ya sha shadda Yar gaske sea blue Dunkin zamani dai dai shi,takalminsa abin kallo ne kowa ya kalle shi yasan hutu ya samu yayi kyau da yawa,Salma ce ta kalle shi sosai da kyar ta gane ashe Baso ne,mamaki da al'ajabi ya kamata.

Yana tafiya da takama dama Baso akwai Izza ga wani uban basarwa,Salma buya tayi a bayan Cele kamar bata Ganshi ba,tace boye ni dan Allah kar ya jawo Auta ya tsane ni wallahi ni yanzu Autana nake so,Baso kuwa ko nemanta baiyi ba ya wuce abinsa ciki,Auta yaga surukinsa yasan zai zo dama sunyi waya,ya fito suka shiga ciki tare Auta Baso yayiwa rada yace ai mun dinke yau,yace na ganta tana buya a bayan wata kar na ganta wai,Baso yace naga wata a gidan nan tayi min Auta kasan na nutsu yanzu ya ake ciki ne ko zaka min hanya Karka mini ae yane ka gane ko,Auta yace Yaya Baso wace? yace bana son Bason nan yanzu Omar yafi daga yau kowa ya Daina ce min Baso Idan ba haka sai na tattaka mutum,Auta yayi dariya yace to Yaya Omar,kasan fa kawai hakura nayi na baka Salma Ina sonta wlh ban zaci zan shirya ba a duniya amma sanadin mutumin nan na dace,da kasan da na baka Salma fa sai da nayi Jinya wlh,ba komai bari tazo na bata labarin komai Karka damu Auta ai na Riga na baka ita har abada na hakura da Salma.
Auta sai da kishi ya kamashi yace wace wacce ka gani? Yace wata ce zan nuna ma ita tana nan wata nutsatsiya ba ruwanta ta rakube a gefe kawai kallo take.

Cele ce ta karbi maganinta Wanda zata bawa su Salma,tace iceko har Namiji yana sha? tace ae mana tace Auta da ita zan zubawa a lemo tunda naga na ruwa ne,tace kadan ake sawa ya Isa,Cele tace karyar soyayya zata kare yau sai Auta ya gama da Yar nan bazan ji tausayi ba ko daya,ga Ahsan ya mata waya ya taho Nigeria,tace sai dai ya zo kudu gidan su Rabi ya sameta a nan ita sati biyu zata yi,sai ta Saba da Yar uwarta.





Masu sharhi kunfi kowa birgeni na gode



AsmaBaffa[8/21, 12:13 AM] +234 806 700 7263: 🌼YAR AIKIN KARUWAI 2 🌼
MATAFIYA


BOOK 2

76-80


Official

By
AsmaBaffa


SADAUKARWA GA
ZAINAB USMAN


PAGE NAKU NE
NICE GIRL
HAJJORA 4ALL
MRS ALEEYU
MAMAN WALIDA




Zuwa Yamma Ahsan ya dira a Nigeria ta Lagos ya sauka,Cele bata San shirinsa ba ma,yana zuwa motoci aka kawo Wanda ya siya a nan sababbin gadal masu kyau da tsadar gaske guda uku guda biyu na securities daya tasa,komai nasa aka zuba a booth ya shiga mota suka wuce garin da Cele ta masa address,Hammad ne dai driver da shi suka zo tare,Cele kuwa suna Shan kida ta sa Omaira ta hada mata zobo me sanyi a ciki zata ebi nata na sha zata zubawa Salma magani ita da Auta,Omaira ta wuce kitchen ta dafa zobo da kayan kamshin da abarba a ciki ta barshi ya huce, ni dai miracle Nawwar ya kirani naje wajen baso na iske Auta,Nawwar,Mami,Baffa a ciki na mikawa Baso jaririna ya Ganshi ya mini barka ya zaro kudi sun Kai dubu goma sha biyar ya dora akan kayan dake jikin Jaririn ya Miko min na karba nayi godiya na zauna tare da mikawa Nawwar Baby Abdullah,ya karbi abinsa,kudin na kwashe abina na zuba a Jakata.
Auta ne ya Kira Salma a waya yace tazo,Salma ta tafi inda yake,tana zuwa ta koma ta zauna a gefen Auta tace Yaya sannu da zuwa Ina yini? Yaushe kazo? Su Mami muna zaune Yace ke karki min ae yane ko baki gane bane dama zuwa nayi na fada Miki mahaukaci dai ya warke,Salma ta bude baki tace Allah? Yace dama hatsari yayi kwakwalwarsa ta tabu rannan ya fita mota ta sake bigeshi Allah yasa baiji ciwo ba sai ya dawo hayyacinsa.

Ashe mahaukaci dai hamshakin attajiri ne,shine Kuma sanadin shiriyata,bayan aurenki da sati daya ya warke,sunansa ma Engnr Alhaji Mukhtar Dan asalin Adamawa ne amma a Kano suke zaune,a hanyar kano zuwa Adamawa yayi hatsari ba Wanda ya sani a danginsa ya haukace haka har ya fada gari gari har Yazo layinmu a cikin Kano,Yan uwansa sunyi cigiyar duniya ba a Ganshi ba,an zaci sace shi aka yi,yana da matarsa da yaransa biyu,yace a gaishe ki ma yace a bashi number dinki Kuma watarana zaizo,shine ya bude min shago na gaske a Kasuwar Kwari,ya siya min gida na million goma,mota ma shi ya siya min ita da kika ganta sannan ya kaini gidansa can dake Abuja a can nayi sati uku,duk zuwan nan da nakeyi nan Ina Abuja,ya dorani a hanya ya dinga min fada da nasiha har Allah yasa na Daina Shan komai,naga Shaye Shaye baida amfani a rayuwa face ya haukata mutum ya lalace ya zama dan Iska,Kalli yanda na dawo mutum kuma dake me kudi ne sai naji fadansa da wani talaka ne ko gaskiya ce bazan bita ba sabo da bashi da abin bani, kai duniya amma haka ya dinga zare min Ido yana fada yana min masifa Baso naki Salma shuru ban iya cewa komai ba,da ya warke fa a kan titi sai da Yan unguwa matasa suka bashi labarin abinda nayi masa amma shi bai iya tuna komai ba,Matarsa da Yan uwansa baki gansu ba Salma sai kin wanke hannu kafin ki tabasu.
Yace Kuma abinda kika masa kema har gida zaizo da iyalansa da Yayansa da Kaninsa,Salma tace Masha Allah Yaya na maka murna,yace iceko kin saita halinki? tace ae wallahi,wallahi Allah Yaya na canja Karka sa a bani wani aikin,murmushi yayi yace ai bazan sa ba Salma,ban zaci zan shiryu da wuri ba sabo da kar na aureki na cutar dake shi yasa na bawa Auta ke badan kudinsa ba ni Kam haduwata dashi naji ya kwanta min a rai kawai shine dalilin da yasa na dage sai ya aureki, ba wai dan bana sonki ba Babu Wanda zai ce bai sonki,yanzu Yaya dama kana so na? ya furta na dai soki ba Ina sonki ba,ki gyara zancenki ya soki a da banda yanzu ya daina babu ya kare cewar Auta yana gefe kishi kamar ya kashe shi, Baso yaci gaba yanzu sai dai Yan uwantaka tunda ni a tunanina na cire rai da zan shiryu ma amma wani ikon Allah Ina aurar dake sai Mahaukacin ya warke ba dadewa kuma Allah ya shiryar dani ta sanadinsa,amma bayan na aurawa Auta ke na dawo gida Salma naci Dadi na more kudin da Auta ya bani akan zai aureki Million daya Banda sauran hidima da ya min iri iri,nace sai ya bani million daya zan bashi ke na siyar masa ke tunda kin san lokacin kwakwalwar bata nan ni iya tunanina siyar dake nayi,Auta yace ai dan Adam yatsansa daya ma ko duk abinda ke duniya za a hada baza a iya siyansa ba sabo da Babu me yin wannan abin sai Allah,yace shi dai ba siyenki yayi ba aurenki yayi kudi kawai ya bani ne,bayan Kuma naci kudin nan a cikina nida mahaukacin nan nazo na dinga tunaninki kamar zanyi hauka duk karfin zuciyata sai da nayi kuka duk kayan gidan nan sai da na farfasa komai na gidan ba abinda na bari,har gado sai da babbala su,na fara cuta kamar zan mutu da kyar Allah ya taimakeni Kuma ban dawo nace Auta ya bani ke ba na Riga na aura masa tsakanina da Allah,na sawa zuciyata ko mene Dan Adam ya rasa to ya hakura ya barwa Allah tunda nayi tsakani da Allah Kuma Allah yasan dan shi nayi to nasan zai min canjin Alkhairi inshallah, haka Allah yaso dama,dama Yaya baka yi auren ba? Ba Aure nayi ba ni kawai Dan ki cireni a ranki na samo kanwar Saminu abokina Sayyada ai kin Santa to Sayyada ce ta Miki magana a waya ba Matata ba,ni kin san ban taba kula mace da sunan so ba kawai dai barni da Shaye Shaye na Kuma yanzu Alhmdllh ko taba sigari karya take ta sake shiga bakina Wanda ya kirkireta ma ubansa,ubansa ma ubansa,muka yi dariya muna jin Baso abin alkhairinsa ya taba mana zuciya, Auta ma yayi dariya wannan zagin ai sai Wanda ya taba Shaye shayen,Salma tace Yaya Allah ya baka ta gari,yace kin hakura da Baso kenan? Salma tace uhm Auta yace kiyi magana sai ki zauna gulma,Salma da karfi tace aeeeeeee....na hakura ni Kam tuni ni zan iya tayashi zaben mata ma,Baso yace ni na gani ma da idona wata ce me hankali ta nutsuwa a jikin bango,Baffa da Mami suka yiwa Baso godiya sosai suka ce gaskiya Idan kaga mutum a wani Hali Karka zage shi ko ka tsane shi,Baso yace Almajiranta ce ta jawo min nima Wanda sai kayi bara zaka ci ka koshi yunwa ba abinda bata sawa,wahala ba wacce Almajirai basa sha a duniya dole su dinga lalacewa a maimakon Karatu,a addini ba inda akace sai ka tura yaro Almajiranta sannan zai samu ilimi ,Iyaye mussamman na kauyuka wasu yaran marayu ne,wasu basu da Uwa sai matar Uba,wani Yan uwa ne zasu kasa rike shi su turashi Almajiranta da sunan Karatu gasu nan dai Wanda sai dai Idan ba Allah ne ya tsare ba duk kusan lalacewa suke musamman na yanzu in Banda siyan waya da jin wake wake ba abinda suka iya,Blue films a wayar Almajirai baza su irgu ba Yara kanana,su kunna kida suna yawo da speakers suna chashewa rawa iri iri,Shaye Shaye,sata, iskanci iri iri akan kawai a rike yaro a gida a bashi ilimi da tarbiyya baza a iya ba duk islmiyyoyi da makarantun allo na gida da sauran makarantun dare duk basu Isa mutane su Kai yaransu ba sai dai a dinga tura Yara bara wannan zubar da kimar addini ce,Baso baya jin hanya shi Kam ko tsoro ya mike yace tafiya zaiyi daga Abuja yake ya biyo ta nan sabo da yaji ya ake ciki.

Su Mami suka yi suka yi ya kwana yace shi sai dai ya kwana a hanya suka masa Allah ya tsare,muka koma wajen kida,Nawwar yace to ko wa ya gani yake so Auta Idan ka raka shi kaji,yace ae zanga wace me hankalin nan suka fito suna hira da Baso sai Star ta wuce yace yawwa gata nan ita na gani,Auta ya dinga kyalkyala dariya harda rike ciki yace wannan tana da aure baka ga cikinta ba karami Kai baka gane ba,Baso Bai San Star rawa tayi taji Dan cikinta yana juya ta fita ta tsaya a jikin bango ta makale ta nutsu ta koma Yar kallo wai a haka shine yace nutsatsiya ce,Auta ya nuna masa Omaira dake tsaye a gefen Cele yace na zaci waccen ma ka gani,Baso yace naga kamar zata yi wulakanci ni Kuma ban son yanga da Iyayi yaran nan,Auta yace Allah tana da hankali ka aureta, Baso yace ba ruwana waccen matar manya ce Idan mutum zaiyi aure an Fi so ya auri dai dai shi amma Idan ka auri mace take ganin kamar alfarma ta maka to ka shiga uku ni ba yaro bane irinka,Auta ya dinga cusa masa Omaira Baso yace Kai rabu da ni da fetsararrun yaran nan,Auta yace inshallah sai ka aureta wallahi Kun dace itama a chake take Baso Hamra ya gani yace ga wata me kama da Kai can,yace Yaya ta ce yace ahh to wannan ma tayi amma waccen da ganinta Omaira kace ko to baza tayi mutunci ba,Auta yace Hamra yayata ai tana da Mijin aure itama ta kusa aure,Baso yace to bani da sa'a a gidan nan amma waccen omaira Idan na kalleta ma nasan ba sauki, yace bada ni ba ya bude mota ya shiga yace Allah ya hada kowa da rabonsa ba ruwana,Auta yace to shike nan tunda Kaki Omaira ta shiga uku tayi bakin jini,Wanda ma take so an hanashi aurenta,Baso har yaja mota ya tsaya ya Kira Salma tazo ya bata kudi dubu ashirin yace gashi nan Idan kina son wani abu ki fada min a waya zan tura miki,Salma tace to Yaya na gode ka gaida gida Allah ya tsare,yaushe Yan uwanmu zasu zo? Yace sai kin haihu,tace Allah ya kiyaye hanya yace Ameen.

Cele zobonta ta hada tasa a fridge,wuraren Nagriba duk kowa ya tafi gida sai iya su Cele da yan gidan kawai Yan aiki sun gyara ko Ina dake bai baci ba tunda ba wani taro akayi me yawa ba,ni me jego wanka nayi dake an gyara ko Ina gadona cike yake da gift na jariri Jakata ta cika da kudi gasu nan dai kyaututtuka daban daban gasu nan,Jaririn Cele tazo ta dauka nace wallahi bani abina,wanka zan masa ko ya huta nace bana so ki karya min yaro bada ni ba,fushi tayi ta bani abina,nace zo ki kwashe kudin nan ki gyara bed din Nawwar zai zo mu gaisa,Cele tace baza a gyara ba ta fice,nayi dariya na Kira Omaira nace gyara gadon nan ki kwashe kayan ki zuba a can ma'adanar kaya inda Babu kaya a ciki duk ki shiryasu a ciki,Omaira tace Aunty nima Allah ya bani Miji na gari nayi aure na huta,Na kalleta nace Ameen Omaira kema auren kike so kenan?

2 Comments On YAR AIKIN KARUWAI Book 2
avatar
zainab-ibrahim-8

11 months ago

Reply

Thank

avatar
ghh

10 months ago

Reply

Replying to zainab-ibrahim-8

Yayi kyau?

Please Login or Register in order to submit comment