Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cream dinta cike da nishadi,ji tayi anyi wani motsi a cikinta zumbur ta mike,da sauri ya kalleta ganin duk ta firgice,ji tayi an sake motsi sai Kawai ta ajiye Ice ream dinta ta fashe da kuka ta rasa ta yanda Zata Masa bayani bata da lafiya, cikinta ta nuna Masa tayi motsi tace da hausa motsi nake ji haka nake ji a ciki ana matsawa ana zamewa ana yin sama sai ayi kasa,sai naji an koma gefe sai naji ana matsawa a hankali ana zullo,Ahsan yace bai gane ba ta dinga gwada Masa yanda take ji tana hawaye tana nuna Masa cikinta,Riga da skert ne a jikinta Kalar na larabawa sai ta dage rigar cikina ya bayyana Ahsan Kansa ya Dora a saman cikin har da sa kunnensa a saman cikinta, a hankali taji Yana shafa cikin shi Wai dansa yake shafawa,dama kadan Cele take jira matsananciyar sha'awa na damunta ta zaci romancing dinta zaiyi bata zaci dansa shi yake tabawa ba Yana gamawa ya jawo rigar ya rufe Mata cikinta ya matsa,kamshin nasa bata so ya bar hancinta kanta ta tura a kirjinsa tana shakar kamshin,mamaki da tsoro ya kamashi sai kace akuya sai tunkuyar Masa kirji take,Ahsan harda cewa Hajja Haram Haram....Cele tace ni daka taba min ciki fa,ta sake makalkaleshi tana Jin kamshi sai jawo Masa farar jallabiyar take zuwa fuskarta gaba daya.




Ina godiya masu sharhi





AsmaBaffa
[8/9, 10:59 PM] +234 806 192 9616: 🌼'YAR AIKIN KARUWAI 2🌼
MATAFIYA


11-15



Official

By
AsmaBaffa



SADAUKARWA NE GA
ZAINAB USMAN



PAGE NAKU NE
Mom Khalisat
Ummin Sadeeq
Jummai Juhud






Mikewa yayi tsaye da sauri Kamar Cele zata Masa fyade Yana furta Haram...Haram Hajja,da Hausa tace Kai ka kasan wani haram can da yawarka,tsaye ta mike ya fisge zai fece ta shatilo kafafunsa ya fadi a kasa,Ahsan shi da kanshi sai da yayi dariya yana Namiji mace ta kayar da shi har kasa, Cele Yar ta kife komawa tayi ta cakume shi har gashinsa take shinshinawa sai kace mayya sabo da shinshinar kamshi Kawai ta takurawa bawan Allah,karfi ne bai sa ba Yana lallaba cikinta shi bai iya fada bama,cele harda uban nishi na gajiya tana Maganar Yan daba tane cewa yawa kake fa Baabaa kana yawa dalla ka tsaya Kamar wani dan iska ni ba fyade Zan maka ba kamshi kawai tana tura hancinta wuyansa,kyaleta yayi sabo da cikin da yake jikinta,ji tayi ana motsi a cikinta ta mike tsaye zumbur ta dage iya karfinta ta durmawa cikinta duka tace micijin ciki ne ta rasa me zata kira sunan miciji da Larabci Kamar zata yi kuka tace shi yasa nake da ci yanzu ashe micijin ciki ne da ni wayyo ya sake yin zullo ta dage rigarta sama,da hannu Ahsan ya tambayeta mene ne? ta rasa me zata ce cikinta ta nuna tace Sirasil wai kyankyaso ne a cikinta tunda bata san sunan miciji ba da yarensu,Laptop dinsa ya jawo ya koma kujera ya zauna tare da dora system din a cinyarsa ya kirata tare da nuna Mata gefensa ta zauna,da zancen kurame yace ta kalla ya kamo pics din mace me ciki a fili ga jajiririn nan ana gani a waje irin na littafin likitoci ya nuna hoton ya nuna cikin Cele da yatsa yace irin wannan ne fa a cikinta,Cele da sauri ta Bude baki tace Iskanci nayi da ubanwa nayi Iskanci da Zan samu cikin ni ko kirji na ba a taba tabawa ba Ina Zan samu ciki kaji balarabe yo a Oat na Sha? Ko a cikin shayi nasha,Yana kallonta tana ta surutu,laptop din ta karba dai dai wajen Google ta rubuta miciji da hausa sai ga pics din miciji ta kalli katuwar messa anaconda tace itace a cikinta,Ahsan ya dinga dariya ya zaci ta sani tsokanarsa ta ke Yi,Kansa ya nuna da yatsa ya furta sunan Maheerah matarsa sannan ya kamo Mata pics din jariri ya nuna Mata cikinta Wai shine a cikin cikinta,Cele tace wannan baya ganewa, sake karbar System din tayi ta rubuta wakar Kawu Dan Sarki ingallo sai ga waka,Cele tana ji har da kada kai ita bata rawa, Ahsan ya tsura Mata Ido tana ta bin wakar gata video shima Yana kallo sai dariya yake yana kallon wakar, Da zancen kurame yace tayi irinta ya gani,Cele tace sai da ya tashi su gwada tare, da sauri yace lah,wata wakar ta canja harda zabura tayi wani uban tafi tana rawa a zaune harda dafa kai tare da tamke baki irin shegiyar nan.

Juyowa tayi suka hada Ido gabanta ya fadi gaskiya Ahsan karshe ne a kyau ta ko Ina ya hadu ba karya a hankali tace kasan ka hadu,kyakyawa ne Kai,Zan iya lasheka na cinyeka danye, da zan sameka wannan da nayi yanga a Nigeria da Zan sameka to ai da nayi fanka,fari tayi masa da Ido da sauri ya dauke Kansa Kar ya kalli Haram wai, Ahsan ta furta ya juyo a nutse Kamar abin kirki wani fari ta sake Masa harda kashe Masa Ido daya,mikewa yayi Yana cewa Subhannallah Subhannallah,dariya tayi ganin yanda yake gaggawar barin gidan gaba daya kamar Yana Jin me nake furtawa da yarena.
Maheerah yaje ya dakko a hospital parking yayi a hospital din Yana tafiya a hankali likitoci suna ta zirga zirga,asibiti ne hadadden gaske,lift ya shiga zuwa Office dinta Yana kaishi Hawa na shida ya fito tare da takawa har Office dinta ya manta bai Mata knocking ba Kawai ya murda handle a hankali ya shiga gaba daya,daskarewa yayi a tsaye ganin Maheerah da katon balarabe tsohon zaurayinta Hussain shima likita ne suna kissing juna yana murza Mata Boobs da harshen larabci yaji tana cewa ya akayi har yanzu ban samu ciki bane mijina ya kasa bani ciki kaima Naga matarka tana haihuwa ai amma ya akayi ka kasa,Likitan Hussain yace ai ke matsalar a kene baza ki haihu ba mahaifarki baza ta iya daukan ciki ba kin sani kema,Maheerah rungume shi ta sake yi tace zamu ci gaba da Jin dadin mu ko Zan samu na dace mahaifata ta dauka,Ina son mijina sosai amma mijina ya min kadan,Ahsan a hankali ya juya da baya ba tare da sun kula ba,Fitowa yayi tare da fadawa motarsa ya zauna a ciki ya dafe Kansa bai San Sanda ya Fara hawaye ba sabo da bakin ciki da bacin rai dama su kishi Kamar hauka,sai da ya gaji sannan yayi Addua a motar ya goge hawayensa ya Dan huta Kamar ma baiyi kuka ba,waya ya dauka ya kira Maheerah sai da ya kirata sau uku sannan ta daga tare da harshen larabci ta furta masoyina kazo gani nan Wayar ta kashe ta sake yiwa Hussain kiss sannan da kyar Suka rabu ta fito,Ahsan Idonsa ya runtse nan take idonsa yayi ja Kansa ya fara masa ciwo sabo da tsananin bacin rai,abinda yake tunawa yasan Maheerah ce da matsala mahaifarta baza ta iya rike da ba amma ya hakura ya biye Mata Suka Yi dashen ciki gashi taci amanarsa ashe ta ma dade tana cin Amanarsa.

Motar ta shigo a hankali ta kalle shi cike da nishadi da kulawa ta shafa gemunsa tare da tambaya noorul qalb me ya faru lafiya? tana tambaya da larabci,Kai kawai ya girgiza Mata yace Kansa ke ciwo Kuma ya Sha magani tace Sannu Allah ya baka lafiya tana gyara nikaf Kamar mutuniyar kirki.
Cele tana Palo ta tara Apple a gabanta tana ta faman ci,a fili tace na rasa wannan bala'i da ya sameni a kasar nan nidai ci ci ta sake ballar Apple tace ga dadi har Ido take lumshewa tace na daka bai kalli gari ba garin Dadi ba kusa ba uhmmmm.....tana taunawa tana ci tace ga sha'awa to sha'awar namijin na mene haka, aure nake so ta bawa kanta amsa tace Allah ka hadani da Kaka nace Kawai yayi min aure,to iyayena wasu iri ne nasan Baba ma ko cokalin silver bazai siya min ba bare gashi Kaka ba kudi ba ya zama dole na nemi kudin aurena.
Sallama Ahsan yayi Cele ta amsa ta kalli Maheerah ta rike hannunsa Kawai sai taji ba dadi bata so taga hanunsu rike ba tana shakar mata kamshin abokinta cewar Cele aa fili tana ballawa Maheerah harara tana Jan Tsaki,tafi tayi ta hau murguda baki tana fari da Ido irin na rashin kunya tana gatsinawa Maheerah fuska,karfin hali kenan tashi tayi tayi Kamar kitchen zata je ta tsakiyarsu tazo zata wuce ta tsinka hannun da Maheerah ta rike masa, Maheerah Kamar ta soke Cele da wuka,Cele Kuwa mamaki takeyi yau Ahsan fuskarsa ba Rahma gaba daya ya canja lafiya,Maheerah ce tace muje ka kwanta ka huta Noorul Qalb,bedroom suka shiga Kawai Yana binta sai da ya kwanta a saman bed sannan yace Dan Allah ko zaki iya fita nafi bukatar zamana ni kadai,Maheerah tace ba damuwa Habibi ta juya ta fita,Kansa ya dafe yana Jin azabar ciwon Kai da zazzabi ya rasa ma me zaiyi.
Maheerah Kuwa tv ma ta kunna abinta aka kawo Mata abinci lafiyayye taci abinda take so ko kula Cele bata yi.

Sadiya da mafi yawan matan da Suka Zo duk yanzu sunyi fari tas sun samu man bleaching a wajen takari suna siya suna shafawa sun Zama fararen dole,fari Kuma marar kyau mummunan haske marar kyan gani kana gani kasan farin Mai ne, Sadiya yanzu bakin balaraben Sudan zata aura shima kudi zata samu,yau mairo bata Kai tallanta ba sai ta kasa gumama a gefen kwalta hanyar harami,duk ga takari nan Mata da maza sun kasa musu Kaya a gefen titi abinda basa so,Motar ruwa ce tank tazo Kawai ta saki ruwa a titin Yana tafiya da kayan da Suka kasa gaba Daya Suka hargitse suna faman kwashe kayansu larabawan nan ma'aikata ba abinda ya dame su Kawai sun dauke su wasu banzaye Kawai titin ake wankewa ga motoci masu mopping suna tafiya a hanya ana goge titi ko Ina Kal kal,suna kwashe Kaya askarawa Suka Zo masu kame sai gudu takai takai ko wacce takari ko da Namiji ne sai gudu Kawai ba tsayawa,Mairo da kyar ta Sha sabo da cikinta ya tsufa gaba daya,Samira wacce suka dauki wankan Abaya sun fito kenan Suka samu ana kame wani Dan Sanda ya bisu suka Sha kwana Samira tabi ta wani lungu Wanda ashe baya bullewa Dan sandan Yana zuwa ya riketa tare da zaro waya Yana Kiran yan Uwansa ma'aikata su zo, kafin kace me Samira ta Masa wawan duka a hannun ta hambereshi ta fisge Wayar ta kwashe da gudu ta bar lungun tana gudu a haka ta kashe wayar gaba daya sai gidansu tana cewa na samu waya a banza.

Wasila kuwa ta dakko soyayyun kajinta zata Kai gidan bakake Kawai sai ji tayi an dauke daron kajin dake kanta tana juya taga Yan Sanda sun juye kajin a cikin shara suna cewa da larabci bata rufe abincin ba duk Kura da cuta ta hau Kai zata siyarwa mutane Suka taka zasu kamata itama ta kwashe da gudu tana gudu ta hadu da Khulsum itama takari ce Suka kwashe da gudu tare suna gaba Suka rankaya da wasu takarin Yan Sanda ta ko Ina sauran sun hakura sunga su Wasila baza su kamu ba amma wani Dan naci mutum daya ya bisu har layinsu ai Kuwa takarin Suka hadu tare da Masa dukan tsiya Suka kwace Masa waya da kudin Dake aljihunsa Suka fece,Wanda aka Haifa a can Kuwa Wanda ake Kira da Yan agulla suke yiwa babaken mu Yan uwansu dan Kira Kamar su ba bakake bane sabo da Kawai su sun Zama Yan kasa in Suka ga wasu ko aikin Hajji Suka je sai su dinga musu dariya Suna musu Dan Kira da fito kana ganinsu kasan basu da tarbiyya duk gashinsu sunyi kitso wasu sun Masa gyara na Yan iska.
Bayan kwana biyu Sadiya ce ta fito da Yamma likis zata je siyayya ta hango dandazon Yan agulla sunyi dandazo wasu a saman mota a zaune sunyi parking sun saki kida suna ta rawa wasu Kuma suna tsaye suna ganin Sadiya Suka Fara nunata suna sheka dariya suna siiiiiii,tsautsayi yasa Sadiya ta juya ta kalle su sai kuwa Suka Fara daga Mata gira suna kashe mata Ido,da larabci ta zage su duk Suka biyota tana gudu suna binta sai da Suka kamata Suka Mata dukan tsiya sannan Suka tattabe Mata nono Suka barta nan tana kuka suna ta dariya tare da tafawa Yan Uwa bakaken fata haifaffun can.

Santana a kitchen yake yana taya Jamcy girki duk wani shaye shaye ya gama sa wa Jamcy Ido bata Isa tayi kwakwaran motsi ba Yana kula tun bata Saba ba har ma ta saba, Jamcy tana kallonsa tace oh ashe haka ka iya girki? Santana ya kashe Mata Ido daya yace ai mace ma Sai dai ta biyo bayan mu,Saura kadan fa Dangote ya dauke ni na dinga Masa girki a gidansa Allah ya tsare Nawwar yazo yace Sam aure zaka yi Santana ban yarda ba,to abinka da me kudi Santana ya tafa hannaye yaci gaba da cewa nace sa ranka a inuwa Nawwar an gama Indai Santana ne ruwan sanyi ne,shine na taimakeki nazo neman aurenki Kawai dan muga karshenku ke da Sabreen Amma Allah ya taimakeki local government ta fanshe ki kina da sweet kin tafi da zuciyar Santana idan kinyi biyayya ba abinda bazan Miki ba amma idan Kika tsaya shirme da shaye shaye kishiya farilla,dariya Jamcy take yanda yake magana harda wani iyayi yake mata,lips ta turo Masa tace ungo ya bata kiss muahh tare da furta ko ke fa amma ki zauna kina shaye shayen banza kina biyewa Sabreen me kugun lion haba abu wani tsukakke ,Jamcy dariya take wato Sabreen ce me kwankwason Lion Zaki kullum sai Santana ya Mata gorin shaye shaye,Yana gama girkin ya kalleta yace to Yar kwaya a tayani kwashe abincin,Jamcy tace ni bana son sunan nan gaskiya yar kwaya fa,idan kinyi zuciya ki daina,ai na daina ka bini a hankali yace better dakko muje muci kizo ki goyani,kana namijin Ina Zan iya,yace yau wlh sai kin daukeni gaki nan katuwa ni Ina Naga nauyi,Jamcy tace hmmm Kawai a ranta tace Ina ganin kaddara a nan.
Suna gama cin abincin ta mike tace to Zo na daukeka,Santana yaje ya dane Jamcy dama gata katuwa sai data iya daukan Santana sabo da rashin kibarsa,dalaf ta dauki Santana harda juyi da shi,yace Amma kin taba aiki a gona ko? Jamcy tace Kai karfi ne dani,yace harda karfin kwaya ma gaskiya,dariya tayi tare da ajiye Santana,sake daukan Santana tayi tana nishi,Sabreen ce ta shigo dauke da sallama,Baki ta saki me Zan gani haka? Santana ya karasa Mata Namiji da suna Hajara ko,soyayya ake ke tunda kin kasa,ke Yar nan rufawa kanki asiri ki samu Wanda zaiwa local government dinki aiki,Kinga ki kiyayi kwayar nan baza kizo ki maida matata ruwa ba gashi na samo kanta har goyani take karki zo ki dinga dagula min iyali ato,Sabreen dariya ma ya bata Zama tayi ta ajiye Jakarta a gefe Santana yace gata nan kuyi Hira Amanatun Amana wallahi idan Kika bata kayan maye yau sai kinci dan banzan duka a gidan Nan,Sabreen tana kallon ikon Allah ta saki baki.

Wise ce taje da sassafe part din Iyamami zata gaisheta sabo da ta hanata zaman lafiya duk da tana zuwa gaisheta gwara ta sake dagewa ko zata samu ta kyaleta ta zauna lafiya,ta sameta a Palo Baffa Yana gefenta shima Papa Yana zaune,Wise ta durkusa tace Ina Kwana Iyamami,kallonta Kawai tsohuwar tayi tana tabe baki tace yau Kuma kinibibi ne ya tashi wato sai da Kika ga Ina tare da yarana Kika Zo gaisheni sabo da suce kina da biyayya ke ta gari ce,Baffa yaji ba dadi Iyamami taki shiryuwa yanzu abin ya koma Kan Wise,tashi yayi ya bar part din ma Sabo da takaici,Shima Papa yaji haushin irin wulakancin da Iyamami ke wa matarsa tashi yayi kawai ya bar palon,Wise tana tsugune tace Dan Allah Iyamami idan wani Abu na Miki ki yafe min mu zauna lafiya...da wa Zaki zauna lafiyar? Karuwa ballagaza,na taba ganin marar tarbiyya irinki kinzo kin makale Mana a gida sabo da Kinga arziki ko? to abinda Kika Zo samu baza ki samu ba Karuwar banza Karuwar wofi,fasika,Wise ranta ya baci tace Ina ganin girmanki amma ki gyara kalamanki ni ba karuwa bace yanzu ba Kuma fasika bace aure nakeyi nan Kuma gidan mijina ne karki ga nazo Ina Baki mutunci kice Zaki takani wallahi bazai yuwu ba never ai ba aurenki nake ba Kuma ba zamanki nake Yi ba,sabo da kin samu ma na gaida ki sabo da fa mahaifiyar Mijina ce ke kema idan da Kara ai Mahaifiyata ce ....wani ihu Iyamami tayi ta dafe kirji tace ni na Zama uwarki Allah ya kiyaye ban haifi karuwa ba Kuma ki sani bana sonki tare da dana sannan bari kiji tunda Baki San muhimmancin uwa ba,Baki San zafin haihuwa ba dole ki fada min abinda kika ga dama sannan mu zuba ni dake Zan fito Miki da asalin ya nake kin daina Jin dadin aurenki,Wise tayi Murmushi tace to shike nan Naga yanda za ayi ni Kuma na kasa Jin dadin mijina tunda Yana so na Ina sonsa Ina jiranki ta juya tayi tafiyarta.

Iyamami mikewa tayi ta bita har part dinta Wise bata sani ba ma tana shiga Papa yazo ya rungumeta ta kankame shi suna dariya tace murna nake Zan haihu,ai na fuki murna Zan sake samun yara Alhmdllh yayi kissing dinta suka sake rungume juna sai ga Iyamami ta shugo tana zuwa tsakiyarsu ta Shige tare da Jan hannun Papa tace muje Dana Ina son magana da Kai tana zuba Murmushi Kamar wata kishiyar Wise,Papa juyowa yayi hannunsa Yana cikin na Iyamami tana jansa Yana yiwa Wise signa akan tayi hakuri karta damu,ta bangaren Iyamami idan suka hada Ido sai ya washe Mata baki irin ba matsalar nan, sai da ta kaishi har bedroom sannan tace yaushe zaka kaini gidan Nawwar ne papa bai San me Iyamami zata Yi ba yace yaushe kike so? tace gobe,Allah ya kaimu ya furta sannan taci gaba da takalo hira, Wai dan Kar ya kula Wise,Wise tana tsaye sororo a palo tace hmm mu a gaya Mana bariki mu da Muka fito daga can tunda baza ki ja girmanki ba Zaki gani wlh na gaji, Papa ne ya fito Iyamami tana gefensa ya zauna a kujera itama Iyamami ta zauna,Wise Dining ta koma ta zauna tare da juya musu baya ranta in yayi dubu to ya baci,Papa ya juya ya kalli Wise data juya baya ransa ya sake baci da halin mahaifiyarsa, Wise tashi tayi ta ebo shinkafa sai ta zuba mai da yaji tana ci abinta,Papa yace Ya Naga kin San mai da yaji? Wise tace kasan cikin nan da kayi min ne yanzu abinci sai da yaji Iyamami hankali tashe tace ciki? Papa hankalinsa ya tafi Kan matarsa, Suka rabu da Iyamami suna hirarsu,Wise tace ya fara motsi ma,farin ciki ya ishi Papa ya manta ma Iyamami na nan yana washe baki yace ke ki bari dan Allah? Sosai fa hmm baka ji ba da alama Dan kwallon kafa zamu haifa akwai Chinese, Iyamami ji take Kamar bakin ciki ya kasheta ta mike tsaye da Niyyar tafiya tace dama ka haukace ta juyar maka da kwakwalwa, Papa yace Dan Allah kiyi hakuri Iyamami ba yanda na iya halittar Allah ce so,Kauna abin ne ba a iya Masa komai dagiya ,Digiyar ubanka haka na baka tarbiyya mutumin banza,ke Kam kinyi asara karuwa tirrr ta juya ta fice,Wise tace bana son sunan nan da take kirana da shi Karuwa,Amma ai ba ita bace ni na San ba karuwa bace ke cewar Papa Yana lallashin Wise yace karki tashi hankalinki akan wannan kina da ciki Kar a samu matsala please,shike nan ya wuce ta furta sannan ta mike Suka koma bedroom Suka tsunduma cikin rayuwar aure.

Washe gari Iyamami Driver ya kawota gidana,Ina Palo a tsaye Ina Shan ruwan sanyi,Nawwar baya gida Mami ma ta fita,ko sallama Babu ta fado nace a'a ai na zaci me gidan ne har zance Ina Islamiyyarsa take Naga Kuma shi ba jahili bane Dole zai min Sallama,Iyamami ce ta nuna ni tace ubanki ne Jahili Yar iska karuwan banza karuwan wofi asirin da kuka yiwa jinina sai ya karye algunguma duk kece kike hada jinina da kawayenki karuwai algunguma marar mutunci Yar cikin shege Yar tsuntuwa ai dama wacce aka tsinta a kwararo Ina zata Yi Albarka,ai cikin Shege shi ake Haifa a jefar sabo da gudun abin kunya,Ido na runtse sabo da maganar ta min zafi matuka har ban San ma me zance ba,nace Hmmm Iyamami kenan ai ke sai an Miki Uzuri tsufa ya kamaki dole ki dinga haka Sannu ke Kuma tsufan naki da hauka ya zo,uwarki ce mahaukaciya,nace a'a fa Kinga ya isheki karki jawo na fusata nayi sama dake na nunawa Allah,barikin Nan ba Gama sakina tayi ba mu bata sake mu ba har yanzu tana jininmu aure ne yasa ma muke hakuri dake ba yanda zamuyi Amma idan da a baya ne wlh da yanzu mun nuna Miki Alkibla,Nifa ba danki nake aure ba bare kice Zaki iko dani kinga ki juya inda Kika fito billahillazi Zan iya kina zagina Zan rama ba kunya ce dani ba,Sanda nake gida lokacin ne nake Rabi yanzu miracle nake bazai yuwu ki hanani zaman lafiya ba,bariki Kuma kiyi ta fada ki hau sama kiyi ihu ki sanar Rabi matar Nawwar karuwa ce,Iyamami tace dama nasan ba tun yau ba ke kinfi matar Yusufa fitsara baki da kunya,nace dama ni Ina Naga kunya ko nace Miki Ina da kunya ne ni? kullum jikanki Yana cin dadina ta ya za ayi nayi kunya ai kunya tayi nan munyi can, ba abin kunya bane in Miki zigidir a gidan nan....da sauri Iyamami ta bude baki tace ni din? ah ke dinfa Dan kina kakar mijina sai kizo ki dinga takura min kina zagina wlh bani da mutunci ki Kama kanki tun kafin ki kaini bango,ai dama ke ba Yar arziki bace Yar iska karuwa me bin maza,Nace ae awajen mijina ba Kinga ma ciki nayi wlh gashi har ya fito ai da jikanki nake yin iskancin ga sakamako kin gani na shafa cikina da ya fara girma,Iyamami ce ta juya ta fita tana Jan kwafa,nace ikon Allah sai kace uwar mijina kinbi kin dameni da zagi akan Kawai na auri jininki,Nawwar na Kira yana dagawa na fashe da kuka ya rude Yana tambaya lafiya? Ko cikin ne? Nace da ciki ne ai da sauki Iyamami ce tazo ta zazzagi iyayena tana ce min karuwa me bin maza ,fisabilillah igiyarka uku a dinga min kazafi ko a baya ban taba Iskanci ba sai yanzu tazo tana sheganta min dana tsakani da Allah an min adalci kenan, calm down ya furta ka dawo Kawai ka bi min hakkina na sake fashewa da kuka,Wai meke damun tsohuwar nan ne Ina ruwanta da Iyalina, nace Ni dai Kawai ka Mata magana Kar nayi loosing temper baza a ga da kyau ba Zan iya fasa motarka,yace ki bari dai idan kin siyi taki kya fasa amma ba tawa ba nasan halinki fa kece za a ciwa mutunci ki bari ai ba ke ba Kam na sanki Baby Kamar yunwar cikina,Haka kace ko? Yace nasan kin Mata rashin kunya na sani na sanki fa, tunda Kinga haka ya fi Miki shike nan kiyi ta yi,Iyamami fa Itace ta haifi Baffa ai ko Kara sai ki yiwa Baffa,ke baza ki dinga hakuri ba,kaji zagin data min kuwa,please aiki nake yi I'm busy ya kashe wayar,mamaki nayi nace iyye wato ni ba kowa bace nasa sune masu gaskiya gwara dana rama,na zauna saman kujera Ina dariya nace shegiya ni Rabi.



2 Comments On YAR AIKIN KARUWAI Book 2
avatar
zainab-ibrahim-8

11 months ago

Reply

Thank

avatar
ghh

10 months ago

Reply

Replying to zainab-ibrahim-8

Yayi kyau?

Please Login or Register in order to submit comment