Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ina ma wannan hadadden zai Soni ga kudi ai da na huta,tafiya ta canja ko zata birge shi,Ahsan bai San tana yi ba ma,ya kirata da larabci ya nunawa Samira hoton Cele ya tambaya ko kin Santa? ta gane tsab Cele ce amma bakin ciki kar ko son Cele yake yar uwarta bahaushiya sai tace bata Santa ba tayi tafiyarta
Yini su Ahsan suka yi suna bin layin da suka san Hausawa na zama driver yana Kai su ko Ina amma ba a dace ba,karshe ma a kofar gidan su Cele suka tsaya suna tambaya Babu wacce ta fito daga gidan sai Meenal to tana jin haushin dukan da Cele ta mata sai tace ai na Santa amma jiya jiya nan ta koma Madina,Nan take Ahsan ya juya da mota suka wuce Airport sai Madina a jirgi.

Meenal gida ta koma ta samu Cele tana guga tace yanzu wani balaraben Yazo nemanki wai daga Riyad suke wani kyakyawan gaske matashi wai sunansa Ahsan,Cele ta dago da sauri tace yana Ina? dariya Meenal tayi tace ai nace kin koma Madina jiya,wani bakin ciki ya kama Cele ta kama Meenal ta sake nada mata duka tace bari na karasa Miki dukan jiya Dan ubanki,Meenal tana ihu tace ai indai Ina raye baza kici gababa wlh Zaki gani,sai dai naga Alheri Dan ubanki Abbana ma ya ja Dani ya hakura Cele dashen Allah ce yar iska me Neman mata tun Ina karama ba a so na rayu ba Kuma gashi har na zama budurwa ma Kalli kirji a cike yafi karfinki wannan daga mijina sai Yayana,kwartuwa yanzu sabo da bakin hali Ahsan guda Yazo kika ce bana nan Allah ya tsine Miki inshallah sai an kamaki kin koma Nigeria,takaici ya sa Cele ta dinga fatan tsiya a gidan nan,wannan gidan da muke ciki Allah ka kawo gomnati tayi katafila da shi,Allah yasa unguwar nan gaba daya gomnati ta kwace ta rushe ko Ina ta bajeta Yan iska Yan hassada.
Hajiyan gidan ce ta fito itace me karbar kudin haya tace ke Cele bafa tsoronki muke ba tunda kika zo gidan nan kin Hana kowa zaman lafiya kullum bala'inki ake ji kashe yar mutane zakiyi ko kece kika haifeta? Cele tace bani na haifeta ba amma jiya ta sha nono na Ina bacci ai na shayar da ita Kuma ina mata baki sai ya bita,Meenal baza ki albarka na na daga Miki nono Allah wadaranki kije ga duniya nan ta isheki,na Miki baki ke Kam ke da Albarka shike nan a haka Zaki dai daice ki watse karshe ki mutu kici ubanki,Meenal tace ai ba uwata bace ke ai kin jawa kanki na shayar dake,wallahi Allah ban sha nononki ba ina tabawa ma kika Farka ki tambayi Samira,Cele tace ba ruwansa kin sha yawwa na shayar dake kawai.
Yan gidan suna jin bala'in Cele suma basu yi shuru ba itama bata kyalewa.

Cikin mutanen mu malamai ma Yan tsubbu suna tafiya saudiya takarci suna baje kolinsu na tsafe tsafe da kulunboto,suna samun mahaukatan kudi har larabawa matan aure ake kawo musu suna musu aiki suna biyansu kudi masu yawan gaske suje suna bata musu mutane takari suna koya musu yanda mace zata mallake mijinta ko tayiwa wani ko wata asiri,akwai malamai Yan tsubbu Wanda da dama an kamasu suna can suna prison wasu Kuma an kashe musu passport ba dama su koma kasarsu ko da wasa akwai Wanda Kuma ba a San da su ba suna nan sun cika gari suna tsafe tsafe a can,ko Meenal tana yiwa Larabawa mata hanyar malamai yan tsubbu ana bata kasonta tafi samun kudi ta nan ita,yau ma da wuri taje ta dauki wata balarabiya wai suna yawan fada da mijinta shine aka hadata da Meenal zata mata hanyar malamai,ai kuwa Meenal ta kaita har gaban wani marar tsoron Allah ya Dade a saudiyya yana bata musu Yan gari,suma cikinsu marasa tsoron Allah ke yarda,balarabiyar tayi godiya tace waccen aikin yayi sabo da yana bata kudi yanda ya kamata sai dai Kuma suna yawan fada haka yanzu,Malamin yace an gama yace za ayi yanka,za aje ayi wani aiki a ka'abah ya kissafa makudan kudade balarabiya ta biya harda Kari,bayan ta tafi Meenal ma Malamin ya bata kasonta sannan tace Malam Nima Ina da bukata akwai wata da na gani Ina sonta Ina so na biya butata amma Malam taurin kanta yayi ga karfi wlh ta min shegen duka naji jiki,ni kawai ta yarda Dani duk bukatata kawai ta yarda Dani,Malamin yayi dariya yace bani sunanta ita din banza,Meenal tace sunanta na gaskiya Rufaida,yace na karyar fa? Tace Cele yace tafi abinki zuwa kwana uku kawai ki fara tabata Zaki ga baza tace komai ba zata biye Miki kawai,Meenal taji Dadi ta tafi abinta.

Ahsan tunda yaje Madina a nan Kuma yana da abokai sune suka wuce masa gaba dake Madina ma ba a zama musu a state sai yan Makaranta ko wani aiki da shedu ba irin Makkah bace bakaken Basu da yawa Kuma yawancin na kirki ne ko Ina da suka je Babu ita,Abokin Ahsan ya koma Riyad shi sabo da aikinsa, shi kuwa Ahsan yafi yarda tana Makkah sai ya dawo Makkah ya kama hotel yayi zamansa kullum zai fito a mota da driver ya zaga duk inda bakake ke zama amma baiga Cele ba,hankalinsa a tashe yake kullum,yau kwana uku da dawowarsa Makkah da zama ya fito a mota shi da driver yana bayan mota ya harde yanda ya Saba zama Ya sa anyi parking a hanyar Harami yana can yana danna waya Cele ta wuce ta jikin motarsa ta dawo tare da Kaka ya Rakata ta sauke Umrah sabo da aikin hajji ya kusa,yinin ma Ahsan haka ya koma masauki ba tare da ya ga Cele ba.

Zuwa dare Kuma Meenal tasan kwana uku ta cika wacce malam yace ta taba Cele zata yarda da ita, Cele ta gaji da wuri ta kwanta cikin kayan baccinta blue masu kyau,Samira tana danna waya,Meenal ta tashi ta koma kusa da Cele ta haye saman gadon Cele ta kwanta a gefenta kamar wata mijinta,Samira wani kishin Meenal ya kamata bata so ta kula wata sai ita, sai kace Namiji zai mata kishiya kishin na hauka,tace kin san Allah Babu me cetonki yau tam shike nan gani mene amfanina sai kije inda ba a sonki Dan Allah Baby ki Daina min haka,I love you kin sani wannan cin fuska ne a gabana Zaki kula wata bayan kece kika sabar min,kika min kalamanki na yarda dake ashe abinda kike fada min karya ce,Meenal tace ina baki hakuri wannan dandane kawai zanyi zan dawo gareki ai magani sai da tsohuwar Zuma,Samira kamar zata yi kuka sabo da kishi,Meenal ta fara shafa Cele ta dage rigarta ta fito da Boobs dinta nufinta Cele tana farkawa kawai taci Karo da shi su fara lalata,Cele da wuri ta Farka ta bude idonta,tsoro ma dukiyar fulanin Meenal ya bata ta saki ihu tare da furta mene haka Turus a gabana tayi tsalle ta dire kasa ta kunna light me hasken ta ga Meenal ce tace wallahi yau sai na sumar dake sai kin bar gidan nan,ta cakumi Meenal ta kama Na shanunta ta jawo kamar ta dame danko zata harba, Meenal sai da ta sume Nan take sabo da wannan wajen ba a sa masa karfi Cele ta haye kanta ta dinga jibgarta tana sume, da kyar matan gidan suka hadu aka banbare Cele daga kan Meenal,ruwa aka dinga shafawa Meenal har ta samu ta farfado Cele tana ganin ta mike ta sake zubura aka riketa tace wallahi sai ta bar gidan nan ko na halakata ta fisge ta kwaso kayan Meenal ta dinga Watson su waje,Meenal taga masifa matar da tazo ta same su a gida itace wai take korarta kamar gidanta,da kyar aka samu daki a boye aka canjawa Meenal daki aka kawo Raliya dakin su Cele,Itama Raliya sai Cele take birgeta,Samira ma tashi tayi ta koma dakin da Meenal take aka canjo da Ameera yanzu Ameera,Raliya sai Cele su ma Yan masifa ne na gaske sannan Kuma sunfi Meenal ma maita Idan suka kwallafa rai suna son mace,matar me canja dakin tana sani ta kawowa Cele su Raliya haka suke wannan muguntar Idan kinki biye musu sai suyi ta canjo maki mata daban daban ko za a samu wata tayi nasara,Idan kinki Kuma ko ba Dan Allah ba sai su hade Kai sun jefa ka ciki ta karfi.

Bayan sati daya Cele dai bata ga su Raliya sun nemeta ba sai dai suyi ta lashe lashen harshe suna kallonta,Cele ta fara soya Awara tana kaiwa gidajen bakaken fata a bakin wani gida suke zama,tana uban ciniki Kuma har layi ake mata tun tanayi kadan har ta koma yi da yawa dake ana Kai waken suya suna samu a can,matasa har Wanda Suke haifaffun can bakake suna siya,Katsam Ahsan ya biyo ta wajen da mota yana baya ya kame,yaga an yanyame wata maza da mata tana ta zuba musu abu a Leda tana karbar kudi,hannunta yake iya gani sai yaga kamar Hannun Cele dinsa a wajen yasa aka yi parking,mutane suna yin sauki ya iya ganin Cele ce,shi kadai ya saki wata dariyar da bai shirya ba,farin ciki ya kama shi matuka wani nishadi ya kama shi,Driver yace kamar itace wannan Sir ya furta da larabci,Ahsan idonsa yana kan Cele ko kyaftawa baya yi ya bashi da amsa da ae itace Alhmdllh,yace to kaje wajenta,yace a'a ba yanzu ba so nake sai nayi winning zuciyarta kawai mu Jira ta tashi mu bita naga gidansu,yace to ba damuwa,Ahsan yana ta kallon Cele tana ta ciniki sai masifa take duk Wanda Yazo da rainin hankali sai taci ubansa tana ta musu ba'a yanda ta Saba,wani ne Yazo ta zuba masa ya karba sai ya bata kudin ba dai dai ba ta hau bala'i Kai nifa ba Hajiya Salamatu bace yawwa ba Sallamammiya bace ni ko na maka kama da Sa'ida sanyi kalau ko Saratu ce ni sarkin asara?,ka dawo hankalinka ni ba Sailuba bace wallahi ubanka zanci Karka ga wai ko an haifeka a nan kace zaka rainani naci uwarka da Mai da yaji wallahi kwadon uwarka zanyi na kwadata da Mai da yaji ko nayi kwadon daddawa da ita na ci Dalla matsa Kai gaba daya Kai aka kalla a ka samu sunan Takari Kai Dalla ware,Yaron ya tafi yana dariya irin zagin Cele shi bai taba jin zagi haka bama,Ahsan yana mota wacce ta sha tint fara Kal ya kwanta a kujera ya zubawa Cele Ido yana kallonta cike da
Shauki har saura kadan ta siyar sai ga Meenal tazo ta Miko kudi tace ni Kam na gama siyar da abincina gida zan tafi a bani Awara my love,I love you wallahi Ina sha'awarki, Cele kudin ta fasa karba ta mike taci kwalar Meenal ta wani mugun mata duka a baki Nan take bakinta ya fashe ta hankada ta fadi a gefen kwalta,botikin awarar ta dauka ta bugawa Meenal a kanta sai da ta farfasa daya botikin a kan Meenal,tace wallahi duk ranar da kika sake cewa kina so na sai naci ubanki shegiya mayya marar zuciya,ta dauki Daya botikinta karamin ta rike da kudinta ta zuba a lalitarta,Yan sanda ne suka taho yau ba ranar kame bace amma ganin su Cele suna musu fada a titi suka taho kama su ai Meenal ta Riga Cele ma takewa da uban gudu ita da take yashe a kasa,Ahsan yana mota yana murmushi duk da bai San me ya hada su ba yasan Cele ce da gaskiya bata fada haka kawai,ya furta itace me gaskiya da larabci,ji Ahsan da son Kai.

Driver yacewa ya kunna mota su bita a hankali ya San gudu zatayi sabo da masu kame sun zo,kafin ya rufe baki Cele ta rike bokitinta ta take a million suma Yan sanda suka bita tana gudu tana waigen baya tana Zagin Yan sandan, Ahsan suna binta a mota a hankali yana ta dariya har driver tana gudu amma masifa take tana cewa dama ai garinku bakwa son mutane ku da kuka Kori Annabi daga garinku sai hijira yayi ya koma Madina sabo da rashin ta Ido Annabi guda ma Kun Kore shi Ina ga mu,Tana hada larabcinta tana fada musu sun Kori Annabi ma da sahabbansa sai hijira sukayi zuwa Madina su waye da Yan Makkah zasu kyale su,da Hausa Kuma tace ai Kun shiga uku da gori kune kuke da abin kunya a duniya Dan uwanku Annabi guda Mafi daraja kuka kora,tana gudu tana waigen su suna binta kuwa wai ta musu sharri sun Kori Annabi ma,Ahsan yau yana mota dariya kamar me sai lungu lungu suke bin Cele tana gudu ko gajiya bata yi,tana zuwa saitin gidan Kaka ta hango kaka Abayarta ta rike da hannu mayafinta ya zame tana cewa Kaka shiga gida shegun Suna baya ku shige gida,Kafin su karaso duk wani baki dake wajen sun bace ba'a ganin kowa a waje,Kaka ya leko da Kansa yana cewa Shugo nan jikata Ina Cele ta wuce ma ko jinsa bata yi ba,Kaka ya leko da Kansa wani askari ya Mika hannu zai damko Kaka ai tuni kaka ya Kai Hawa na daya da gudu, yana cewa Kai tunda nazo garin nan nake motsa kuruciyata,kuruciyata sai dawowa take, Ahsan a mota suke ta bin Cele da askarawa Ahsan yana ta dariya domin botikin ma ta jefar da shi ta gyara mayafinta tana gudu har tazo kofar gidansu a nan taja birki tana uban haki ta shige daga Dan zauren ta leko da kanta ta zazzagi askarawan da larabci ta shige ciki abinta,suka ce ai sun gane gidan Jira suke gomnati ta basu damar kame gida gida,Ahsan kuwa ji yayi kamar kar ta tafi bai gaji da kallonta ba,a fili Kuma yace yanzu zai fara bibiyarta driver ya shirya.
Layin kasuwar takari yasa aka kaishi a mota yasa Driver ya fita ya siyowa Cele kalar botikin awarar ta gudu biyun da babba da karami,kawai ya samu wata takari ya bata Yan kudi yace ta shiga gidan tace a nuna mata Cele sai ta bata botikan,ta karba kuwa Ahsan shi yana mota hankali kwance ya ga Cele to,takari bakar fatar kawai ta gani suna bata sun ja mota suka bar wajen, ita Kuma takarin ta shiga gidan Neman wace Cele bata San ma balaraben ne yasa a kaiwa Cele ba sabo da yana bayan mota ga Motar da tint,driver ne ya ba.

Auta karatunsa ya kankama sosai ga bikin su Sultana yana gabatowa,Mami da Baffa suka kira shi ya zauna Baffa yace Autana naga Alama baza ka iya zabo matar nan ba mun Yanke hukuncin aura maka Omaira kanwar Rabia,Auta yace gaskiya Baffa a'a nasan Dan kyau tana da kyau ai ba kyau ne so ba,so ba a kyau yake ba kawai ni nasan ta cancanci a sota amma ta min karama,Mami Ido ta zaro tace Auta Omaira 19yrs ce tayi maka karama? Auta yace ae ni babba nake so a samo min kamar Wise matar Papa ko kamar Auntyn Nawwar matar Yaya yawwa irinsu nake so,why? Baffa ya tambaya,yace gaskiya Karka ku sa nayi rashin kunya amma kamar Omaira me zata bani, Baffa yace zaman kudu ya lalata min Yara da a Arewa ne yaushe Auta zai iya fadan haka Okay fine mu dai Omaira ce zabin mu,Auta ya mike yayi tafiyarsa, Mami tace Kar a takurawa Autana Honey a kyaleshi tukun ya samo,wannan yaron za a bari ai kuwa za a ga ba daidai ba tunda Allah ya hore ayi masa shine dai dai,Mami tashi tayi tace bari naje na lallashi Autana,ke kike shagwaba yaron nan wlh,Mami dai ta wuce bedroom din Auta.

Samun Auta tayi ya zauna yana kunci,tace Babyna,baki ya turo gaba tace ni na Daina kulaku tunda da abinda zaku Saka min kenan,Mami tace Auta abinda zan iya cewa mun baka sati daya ka kawo mace kana gani biki saura sati biyu kacal me kake Jira,Why are you so stubborn? Sai kace dole nace na fasa auren,wallahi baka Isa ba Auta aure zamu yi maka,Auta ya bude baki,wayarsa ce ta dauki Kara ya duba yaga Baso yace Mami zanyi waya,amma kafin nan ni a wanne gidan zan zauna? Mami tace gidan da ka zaba a Gina maka shi ake maka amma tunda dama yaro ne Kai ga part guda nan za a baku a gidan nan ku zauna da Amaryarka kafin muga kamun ludayin naka muga ya zaka rike yar mutane Idan munga normal sai a karasa gidan ku koma gashi yanzu Alhmdllh ranar da ba lecture kana zuwa Office har weekend Masha Allah saura matar muga yanda Auta zai riketa, dariya yayi ya furta 9 months dai dai ta haihu Mami Idan Ina sonta Idan kuwa bana sonta shekara Tara maybe Kya samu jikan Auta ya furta yana dariya,Mami dariya tayi tace Oh Auta ko kunya ai shike nan zamu gani ta mike ta fita,Baso ya Kira back yana dagawa ya jishi a cake ga Salma nan tana ta ihu a gefensa,yace kazo ka siyeta ko na aikata lahira ta isheni bana sonta tam,Auta yace Kai wanne hauka ne wannan muna da danganta ne da zaka dame ni ya ja tsaki ya kashe wayarsa.

Washe gari kuwa Salma ce ta durkusa a gaban Baso jiki na rawa yana zaune yana fushi ya harde hannaye a kirji,a Hankali tace kayi hakuri indai akan nace ka biya Sadakina ne kake wannan fishin kayi hakuri ga abincin Dan Allah Kaci,kayi hakuri na Daina cewa ka aureni Dan Allah Kaci abincin kaji,ya kalleta ransa a bace yace karki sake cewa kina so na Idan ba haka ba bazan sake cin abinci ki ba ko mutuwa zakiyi banza kidahuma ana soyayya dole ne? nace bana sonki ko dole ne mayya, Karar tsaiwar mota suka ji a kofar gidansu, Auta ne Yazo motar ma ta Abokin Nawwar ne ya karbo bayan ya sauka a jirgi,uban Swagga cikin kana nan kaya wando duk a farfashe pencil me shegen kyau da tsada arsh,sai Riga fara me dogon hannu ya dora top a Samanta marar hannu maroon and arsh,takalminsa Snickers me kyau arsh wandon nan harda sarka a gefe Daya gashi ya zazzago shi boxers dinsa a waje suma taci kudi sai sheki take an mata wani shegen gyara,yana kamshi ya fito da wayarsa a hannu ya mugun haduwa.

Tafiyar gayu yake yana taku dai dai ana wani bubbudawa irin na Samari masu tashe, sallama yayi ya shiga gidan Kai tsaye,Baso yana ganin Nawaf ya mike yace bros yana ihun murna yace Oga chansa chansa Chau Chau sa'ade ya wani yin ta Yan daba,Auta dariya yayi ya mikawa Baso hannu suka gaisa sannan Baso ya jawo masa benchi ya zauna ya masa tayin abincin yace ya koshi,Auta yace na shugo ne ya deal dinmu? Baso ya sheke da dariyar murna yace yana nan Idan ka shirya,ya kwalawa Salma Kira yace baki ga abokina ba ne? Salma tazo tana murguda baki ita Baso take so ala dole ta durkusa tace ina kwana? Auta ya kalleta a banzance yace I'm good ya shareta,Baso sabo da kar a ji sirrinsu ya ja Nawaf kofar gida yace nawa zaka siyeta? yace Million daya a Hakan ma kafin na roki Baffa ya bani sai na sha wahala kasan ni dan Makaranta ne sai yanda aka yi Dani,Baso yace Allah mutumina to ka gane Kace Baffa ya baka dubu dari uku,Yayanka dari uku Mama ma dari biyu a haka Zaka hada kudin a saukake,Nawaf yace kamar ka sani haka nayi a Hakan ma da kyar kowa cikinsu ya bani,yanzu ya za ayi nan da sati fa za a daura aure ka samu manya ka sanar musu,amma kana ganin zata yarda Salman? Baso yace ita din banza na karyata kuwa,ai ka kwantar da hankalinka yanda nace haka zata bi kawai ayi komai na biki sai ka bani kudina ranar Kuma a Kai maka amaryarka,Auta yace Iyayena ne fa zasu zo bincike karka yi shaye Shaye please kar a samu matsala Dan ni taimakonta zanyi kaima na taimaka maka kawai ba wai sonta nake ba, Auta har ga Allah taimakon Salma zaiyi ba wai ko yana jinta a ransa bane kawai dukan da ake mata gata marainiya gashi Baso baya kaunarta abin ya mata yawa shine dalilinsa na aurenta amma shi Kam ba abinda zaiyi da ita ya fiso ya samu su Mami su kyaleshi tunda Idan yayi auren hankalinsu zai kwanta shi Kuma a hankali sai ya samu zabinsa katuwa nunanniya ya auro abarsa ya sha soyayya,haka suka gama tsare tsarensu da Baso da zai tafi har dubu ashirin ya bawa Baso,yana komawa gida yace wa Mami ya samu mata,tace har kayi wata budurwar? Karya yayi yace ai sun Dade tare kawai yaga karama ce 19yrs tazararsu ba yawa amma ya duba yaga tana da hankali,ya Basu Address,Baso tsabar bukatar kudin da yake baiyi Shaye Shaye ba,ya samu Salma yace Salma aure fa zan Miki,da mamaki Salma ta kalle shi,ya bata rai yace kinga karki zubar min da damata kudi zan samu sai na samu babbar sana'a na Gina mana gida daga baya yace zai sakeki sai ki dawo muyi aurenmu Muji Dadi,Shima yaron iyayensa ne suka takura masa sai yayi aure shi Kuma baya so a masa auren dole sai nan gaba zai sakeki ya auri zabinsa kinga Nima sai na aureki lokacin nayi kudi abinmu ya kika ce?

Salma mamaki ya kamata da tsoro tace Idan kana so na Baso ta ya zaka bawa wani ni ya aura? Baso a ransa yace Dan baki sani bane siyar dake nayi,Gaskiya baka so na nidai bana son wannan yaron Kai nake so wallahi ta fashe da kuka,Baso ya hade rai yace wallahi zan karyaki ni na baki Umarni amma kice baza ki ba,nifa Zaki taimaka ashe karya kike bakya so na,Idan kina so na ai Zaki so farin cikina,kiyi acting kamar film karki sake ko ya aureki kice Zaki masa fitsara a hankali zai sakeki kawai ki bada hadin Kai kamar dama kina sonsa,Salma tana goge hawaye tana shesheka tace to zanyi sabo da Kai amma ka tabbatar zaka aureni nan gaba? Baso yace ya zama dole kawai kiyi abinda duk na tsara Miki,tana shesheka tace Allah bana son tafiya na barka,bana so nayi nesa da kai har kudu fa haba,Baso lallabata ya shiga yi abinda bai taba to ba yace kiyi hakuri zan dinga zuwa Ina ganinki kema Zaki dinga zuwa karki ji komai,haka ya dinga lallaba Salma da karya da gaskiya har dai ya samu ta amince zata Auri Auta amma Sabo da Baso Kuma da sharadin ana sakinta zata dawo ya aureta ba abinda Kuma Kuma zai shiga tsakaninta da Auta.

Mami,Baffa, Papa da Nawwar suka zo gidan su Baso sunga gidan sunga Salma Kuma sun basu tausayi matuka,Salma ce ta sauke su da girkinta da ruwa da lemo da Baso ya siyo,Baso harda basu kabarin tarihinsu amma sai yace muna zaman mu da Kanwata Ina ji da ita Ina matukar kaunarta Ina fata dama Allah ya bata Miji na gari Kuma Alhmdllh ta samu yaro yana sonta tana sonsa,Salma dai daki ta koma tana rusa uban kuka ganin da gaske fa auren zata yi,Baso da shi aka tafi cikin dangi can jigawa,bayan sun gama komai Baffa sai da ya sake bincike ya samu suna da asali me kyau Papa ne ya koma ya Kai kudin aure aka Yanke biki saura sati daya za a hada Dana su Sultana, abinka da talaka Wanda komai yi masa za ayi to fa sai yanda akayi da shi, lefe sai da aka kawo akwati goma cif kaya na kece raini komai me daraja aka yiwa Salma sabo da dama su Mami sun shirya dole da Auta za ayi auren shi yasa komai da shirinsa akayi,Auta sai gayya yake ba ruwansa da wani ba soyayya bai so a gane murna yake nunawa a fili yace ranar ma

2 Comments On YAR AIKIN KARUWAI Book 2
avatar
zainab-ibrahim-8

11 months ago

Reply

Thank

avatar
ghh

10 months ago

Reply

Replying to zainab-ibrahim-8

Yayi kyau?

Please Login or Register in order to submit comment