Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tafiyar su da kwana daya bayan ta mana waya sun sauka lafiya Wise ta fada nakuda sai labari naji an kaita asibiti,kafin muje ma ta haifo danta Namiji katon gaske,Papa sai murna Iyamami tana can ta saduda itace akan gaba duk Halin banzanta ta gaji ta Daina ita da Sabreen sun nutsu,Wise ras da ita Papa sai murna yake ya samu da Namiji ya Kara samu Yaya, Sabreen anyi Kani ana ta murna.
Tunda aka sallamota kullum sai munje,Iyamami ce ke kula da Jaririn da komai na wise ita da Mami har ranar suna tazo yaro yaci Sunan Nawwar sabo da Nawwar shine duk ya wuce gaba,junior muke ce masa,Auta anyi da tsohuwar budurwa ta haihu Gift ya kawo ta gani ta fada.

Kaka kuwa bayan sunyi Umrah dukkansu Cele tace suzo su wuce Riyad yace a Dan Jira yaje wajen abokansa na garin Makkah su gaisa,Cele tace kuyi sauri Kaka Dan Allah muna jiranku a masallaci harami, Kaka da Amarya Zuwaira Mama suka fito suna tafiya cikin nutsuwa Basu san wani kazamin kame ake yi ba,har gida gida ake bin ko wanne takari a kama su,gidan da Cele ta taba zama su Meenal har gida akaje duk an kamasu an kashe musu passport baza su sake shiga kasar ba an dawo dasu Nigeria sabo da haka ko sun dawo Makkah ana Shigar da passport dinsu computer zai nuna an dakatar da su daga shiga kasar,duk Wanda suka kama da laifi a kasar haka suka masa,sabo da haka takari da yawa duk an tsince su,Suna tafiya Kaka ya hango gungun askarawa shi ya San kwanan zancen Mama ce dake bata taba takarci ba bata San komai ba,ya juya da gudu ya bar Mama sai da yayi nisa ya kwala mata Kira Zuwairaaaaaa tashi injin kafarki, bawa kafarki wuta ki taho a millionnnnnnn,Mama taga askarawa sun dumfarota gata da kiba sai gudu, tabi Kaka sukub sukub da kyar take gudu Allah yasa suka Dan buya a wani lungu sai da Askarawan suka koma sannan suka fito suka koma wajen su Cele suna basu labari,Kaka yace Zuwaira ga kiba inda kisan tana taka soson katifa sai ki rantse akan soson katifa take gudu sukuf sukuf,Cele da Ahsan suka dinga dariya,yace ai baza su kama ku ba da Kun nuna musu wannan abin,Kaka yace Kai rabu Dani haka kawai tsautsayi yasa ance masu shedar zama ma a kasar duk sun kame su,Ahsan yana ta dariya yace su tashi anzo daukansu,Driver Yazo da mota aka kaisu Airport suka wuce Riyad.

Ahsan a gidansu ya fara sauka a dankareriyar farar mota driver na jansu daga airport,gidane hadadde Yan uwansa larabawa maza da mata suna ta murna ana tarensu,wasu a ciki Basu so ya auri ba Yar kasar ba wasu Kuma ba ruwansu,Cele tana rike a hannunsa suka shiga katon Palo ya gaji da tsaruwa,ga girki kala kala an shirya, masu son auren sai rungume Cele sukeyi da Ahsan suna musu pics,Bayan anyi gaisuwa irin ta larabawa Ahsan ya gabatar da Cele ya Basu labarin abinda duk ya faru tsakaninta da Maheerah har auren Cele,Wanda basu so aka auri Cele ba ma a nan suka narke suka koma Sonta,ya gabatar da kowa nasa a wajen Cele sannan aka ci aka sha duk da cewa Kaka,Mama da Cele ba komai suka iya ci ba,Basu Saba ba suna haka sai ga Maheerah ta shigo tana balbala masifa anci Amanarta,Cele ta mike tsaye tace sai ma an Kore ki daga aiki Zaki San an ci amanarki ta fada da larabci,Maheerah tazo ta cakumi Cele,Cele ta kwasheta da gigitatten Mari ba shiri ta saketa,Larabawa sai Subhannallah Subhannallah suke furtawa,Ahsan yaji dadin hakan da Cele tayi,ya rike hannunta dama a tsaye take ta mike zasu tafi ya jata zasu shiga mota Maheerah tana kuka ta zube a kasa ta rike kafafun Ahsan tana bashi hakuri,Cele ta hankadeta suka shige mota da su kaka suka wuce gidan Ahsan sabon gidan da ya canja a wani layin daban na masu hannu da shuni,gidane na gasken gaske yaji kaya komai me tsada,Cele tana ta uban murna,yana shafa cikinta yace gidan yayi? tace komai perfect,sai me aiki Cele tace a'a ni zanyi komai da kaina Ina wani aiki a nan garin da ba kura, daukanta yayi suka wuce Bedroom suna soyewa,Cele tace Antena Dadi,yayi dariya sosai yace amma da kince zafi,Cele tace na tuba dama a farko ne nace yanzu na gane gaskiya na tuba ranki ya Dade karya nake wane mutum,Kaka kuwa yana bedroom din da Ahsan ya Basu shi da Mama yace da Mama azo a Adana ni,Mama tayi dariya yace amarci zanyi a Saudi yau sai na ajiye tarihi.

Bayan haihuwar Wise da wata Daya Star ta haifi yarta mace taci suna Nawwara wai sabo da Wise tayi Nawwar shine ta Saka Nawwara,Ba a dade ba Seraline ta haifi Namiji itama yaci suna Ahmad,Yar Zabil da Mandula kuwa sai bayan wata biyu Mandula ta haifo Mace taci Sunan mamanta Aisha suna ce mata Waheeda,Sai Yar Zabil bayan sati biyu da suna ta haifo Namiji itama aka Saka sunan babanta Usman suna ce masa Aabeed.

Salma kuwa cikinta yana ta girma sosai sai gani akayi ya fito a hakan ma boyewa take yi Idan zata je unguwa hijab har kasa kowa yasan da cikin amma sai boyo suke ita da Auta,Yau Auta yana wajen Mami tace Idan kun gaji da boyon ai cikin ya tsufa sai ka dawo da ita gida nan ta haihu,Auta yace wlh ni bazan iya barin Mamatata ta dawo nan ba,ni na karbi haihuwar,Mami ta kalle shi tace munga Rabi ma me boyon nono,Auta yayi dariya yace kawai a raba mutum da matarsa ayi ta gargajiya ni bazan yarda ba,Mami tace Karka dame ni Kuma kaje Allah ya bada sa'a yace Ameen .
Salma tana ta tiri tiri da ciki gashi ya tsufa sosai,Auta yace ya dai ya kalleta tana hawaye tace Allah cikin nan ya isheni wlh hakuri kawai nake yi,Auta ya fara lallashinta yace sorry Autana kin kusa ai Yana shafa cikin tayi Turus a zaune tare da mike kafafu.
Cele kuwa cikin yana shiga watan haihuwarsa cif cif sai gata sun dira a Nigeria ita da Mama da Kaka sai Ahsan,lokacin an gama musu hadadden gidansu na gagara,Kaka da Mama anyi kiba anyi jajir,Cele da Ahsan ma haka,Kaka suka sauka a Kaduna gidansu har Cele sai da suka zaga dangi sannan Ahsan ya dauketa suka dawo kudu a jirgi,Gidansu nasa Yan aikin sun gyara an zuba furniture da komai na haduwa an shirya musu kawai tarewa suka yi a gidansu abinsu.
Kusan kullum Ina ziyarar Cele sabo da cikin ya tsufa,nace gaskiya ya kamata Uwa tazo ta zauna da ku,Cele tace wacce Uwa ga Mama matar Kaka zasu taho gobe,nace Allah ya kaimu ai yafi Idan da manya,nace kinji Omaira tana da ciki Omar dinta ya Bude mata shagon boutique,Cele tace ta fada min.

Cele ta budewa Kaka shagon siyar da kayan Masarufi sannan ta sake gyara masa gidansa sosai,sai su Bilkisu ni da Cele mun hada kudi mun Basu jari babba suna juya abinsu, komai Alhmdllh kowa Yana zaune lafiya da yaransa Babu talauci kowa da rufin asirinsa dai dai gwargwado.
Mairo ta shirya bayan ta yaye yarta ita da Dagaci da Gwaggo da Gaji suka samu Iyayen Najib bayan sun gaisa suka ce yarku muka kawo,Najib aka Kira Yazo ganin Mairo da yarsa sai hawaye ya durkusa a gaban Mairo yace ki yafe min Dan Allah,Mairo tace ba komai na yafe maka Albarkacin yarka gata nan sunanta Madina,Najib ya dauketa sannan ya fara rokon Mairo akan ta aure shi yace wlh Ina sonki Dan Allah ki aure ni,Dagaci ne yayi magana yace sai dai kayi mata gidanta daban sabo da gudun gorin kishiya,Baban Najib yace indai wannan ne ba matsala,Mairo dai haka ta amince gwara ma ta auri Najib din ta huta musamman sabo da yarta Madina.
Bayan sun koma gida ba a dade ba suka kawo komai na aure aka sha bikin Mairo itama aka kaita gidanta Dan madaidaici me kyau itama ni na mata kayan daki dukkan su sunci albarkacina Yar tsuntuwar da suka raina tayi musu rana a duniya

Maheerah kuwa asibitin da take aiki Ahsan yakai kararta suka koreta daga aiki gaba daya,tayi kuka tayi bakin ciki gashi Ahsan ko saurarta bai yi,kwarton nata ma sunyi fada gashi su can ba a samun Miji da wuri ta rasa Mijin aure sai gantali a gari kawai bata a tsuntsu bata a tarko,in Banda tarin nadama da Dana sani ba abinda take yi a rayuwarta.

Yau cikin dare Salma tana kwance ta tashi ta zauna ta tashi Auta tace Auta ka tashi Dan Allah zan mutu kana ta bacci ai gwara na cika a gabanka,Auta ya tashi yace ko dai Nakudar ce ne? Salma tace itace gaskiya ni ban taba jin irin wannan ciwon ba,mu Dan Kara Jira ayi Sallah sai mu tafi asibiti,Salma ce ta sakko daga kan gadon tana rike mara tun tana Dan kokari har ta kasa tace Autaaaaaa da karfi yace na'am kamar abin arziki tace Auta ubanka,wayyo Nawaf zanci Ubanka,Auta yace ba lafiya mata ta zagi mijinta me Antenar ban girma, tashi mu tafi ya dauketa da tarkacen Salma da suka hada abinsu na haihuwa sai asibiti,Auta yaki fadawa kowa Kuma suna asibiti tun asuba har yayi Sallah rana ta fito Salma bata haihu ba,Mami ta kirashi da hantsi amma bai fada ba yace lafiya suke,sai 12pm sannan Salma ta haifo yarta mace katuwar gaske kyakyawa,Sai da aka gyarata Auta ya shiga ya dauki yarsa yana ta jin Dadi yana uban murna ya rasa inda zai sa kansa,sai da Salma ta huta ya fita ya samo mata abinci take away taci ta koshi yamma karfe hudu aka sallame su,Auta yana zuwa ya hada mata ruwan zafi da kansa ta shiga tayi wanka,ta fito ta shirya cikin doguwar rigar material marar nauyi ya Mika mata turaruka yace shafa jego sai da turare tayi dariya,yace gashin nan iceko ya wanku fes tana taje gashin tace wlh bani da karfi komai karfin Hali nake yi kasusuwana sunyi rugu rugu,Auta yace a Kira Mami ko Zaki iya yiwa my Lovely Baby wanka?Salma tace na iya ya hada ruwan suka wanke yarsu mutum biyu akan jaririya daya Auta ya riketa Salma tana wanke ta,Auta yana cewa a hankali karki daye mata fata na shiga uku Yar nan kamar raina haka nake jinta ki goga a hankali,a haka suka mata wanka harda mata ruwa biyu wai tafi fita,Auta ya zubar da ruwan ya sake wanke toilet din,Yazo ya gyaran gidan neat yayi wanke wanke sabo da tun dare suka tafi duk da ma gidan ba dirty sharp sharp ya gama komai yayi wanka ya fito ya shirya cikin jallabiya arsh yana kamshi,Salma ta shirya yarta harda hada garwashin wuta dama sun tanadi gawayinsu,Auta ya dawo ya zauna yace ya kama gawayin? tace gashi yayi Jajir tana fifitawa da littafi,yace a gasa mata cibin,suna ta faman gashi ba ji ba gani Auta yace ayi mata sosai tayi sauri ta soye,kamar zasu kashe yarinya da gashi suna ta abu daya,Salma tace shi yasa nace a siyo gawayi kaga yayi amfani mun tanadi abun mu,Auta yace yaushe za a fara mata kwalliya,tun yanzu Kuma a barta ta kwana biyu tayi Kwari yace haka ne ya matsar da wutar gefe yace ko Zaki gasa local government dinne again? Salma tace ta gasu ai dazu sai dare Kuma,Abu kadan sai budewa yarinya cibi a gasa a gasa a ajiye ta,cikin kaskon wuta Kuma na kasa a ciki suka zuba gawayinsu sai da suka Nemo abinsu tun cikin Bai girma ba,Auta ya zauna a gadon yace kamar kar a Kira kowa muyi ta kallon Yar mu,Salma tace ae wlh a bari sai dare a fada musu,Suka zauna suna ta kallon yarinya ba ji ba gani.

Auta yace wannan hancin nawa ne,Salma tace wlh nawa ne kana gani gashi nan daga karshe yayi tsini,yace bari dai a Kira Mami Dan darajar jaririyata suzo su tayamu murna,Auta ya Kira Mami yace Mami tace Naam,Yace albishirinki,tace goro Auta,yace to kinyi jika yarki Salma ta haihu,Mami harda guda tace Auta yaushe me aka Haifa? Yace Mace Mami tun 12pm ta haihu muna gida fa muna ta kallon Yar mu shi yasa santin Baby ya kwashe mu muka ce baza mu fada da wuri ba,Mami tace gani nan amma kuruciyarku tayi yawa Auta,ta zaci ma ba a yiwa yarinyar wanka ba,su Wise ta fadawa ta fadawa Iyamami,Ina jikin Nawwar a kwance Auta ya Kira Nawwar ya daga,yace Yaya ku taho na haihu dazu tun 12pm,Nawwar yayi dariya yace Allah kace kaji jiki me ka Haifa? Yace wata zukekiyar mace ce da gani wannan sai Dan sarki Amma dai zan hakura ta auri Abdullah muyi manage,Nawwar yayi dariya kamar me,yace to gamu nan,Auta yace kuyi sauri kar ta huce ku kalleta da duminta,Ina jinsa Ina ta dariya nace to fa Auta yayi Baby mun shiga uku Kuma yanzu,da Kansa duk ya Kira su Star ya fada musu,Ya kira su Umman mu ya fada musu,Baso ya Kira yace ta wajenka ta haihu,Baso yace akwai burar....a gidan nan sai munzo zan Kira Salma,Omaira tana ji tace Salma ce ta haihu? Baso yace ae fa ki shirya akwai suna ba yawaa,Omaira tace saura namu yace ba Yawaa zai zo inshallah, Allah yasa kar Nakuda ta miki ae yane kin gane,Auta Baffa ya sanarwa da Papa.

Mami ce ta fara zuwa ta shigo har bedroom din Salma ta iske Auta a zaune a tsakiyar gadon shi da Salma da Baby dinsu sun sata a tsakiya,Mami tace yayi masu 'ya haka ake haihuwar ta ganganci baku San komai ba kuka ki fadawa mutane,Auta yace ga waya me takeyi a Nan muke browsing mu gani yanda ake yi,zo ki ganta Mami,Mami ta leka tace to a bani ita mana,yace bacci take yi ya daukota cikin kaya pink masu kyau ya mikawa Mami a cikin showel,Mami tace Masha Allah,Me jego boyon ciki Kuma ya kare yau gashi abinda ke ciki ya fito,Salma harda jawo mayafi ta rufe fuskarta,Iyamami,Sabreen,Wise sune suka zo suma ana ta yiwa Salma tsiyar boye ciki,tayi shuru ko Allah ya raya bata iya amsawa wai ita kunya,Auta ne ya mata rada yace Idan ance Allah ya raya ki amsa a zuci,tace ai Ina amsawa a hankali cikin rada ganewa ne ba a yi,Mami tace ai kunyi kokari Auta wlh da kuka iya aikin nan,yace Yar tawa na kasa gyarata Ina bazan iya ba ai zagewa nayi Mami Ina kallon kan Yar ya fito daga local government,Kai Mami kunyi kokari ku duba Yar wannan kafar yaro guda ya taho,Mami ta Kalli Auta tace wannan rashin kunya haka Auta wlh zaka bar dakin nan, Iyamami tace Dan bantan Uba marar kunya ka tashi ka fita Kaki fita yau naga jaraba,Baffa kuwa Auta ya ishe su da Kira wai ya akayi yaga shuru ne Basu zo ba,Baffa suka zo da Papa suka ga Baby suka tafi.

Mami tace to yanzu dai ai dole na zauna a gidan nan tunda ba Babba ko Iyamami ta zauna,Iyamami tace rabani da fitsararre amma tunda ke da Mijinki ki je gida na zauna haka Kuma wlh yaro ya min rashin kunya ubansa zan ci,Mami tace me za a kawo Salma na ci? tace wlh yunwa nake ji dama a kawo min tuwo ,Ina Shirin zuwa nida Nawwar na gama shirya girke girke na, Auta ya sake Kirana wai me kuke yi ne a gida ni ba'a son jinina Anki kulamin Yata,Nawwar yace gamu nan fa a hanya tunda Yar har an bawa Abdullah ai munyi suruka,Auta yace kar kuce Ina Neman Kai da Yata Idan bata sonsa bazan mata auren dole ba,haka muka tafi da Abdallah Wanda har tsaiwa yana yi.

Su Star dukkansu suna ciki Cele kuwa sai waya suke da Auta tayi nauyi,tace Auta Yaya Baby din? Shike nan ku Kun huta Inama nice Auta yace saura ke Kam munyi gaba mu,tace Allah sa na haifo Mace muyi takara da Kai wajen Neman auren Abdallah,Auta yayi dariya yace ai mu sai dai azo ace ana so,Muna shiga Auta ya dauki Abdallah yace Dan banza inye yaro yayi goshi tun yanzu sai farin jini yake ana ta son aurensa Allah yasa baka gaji babanka ba wajen Kaunar local government ka cuci Yata a banza,Star dariya harda bugar kafa tace Amma Auta anyi Dan Iskan yaro,Iyamami tace yaron nan ba ya jin kunyar kowa,Nawwar yayi dariya ya dauki Yar Auta ya mata Addua yace gata kuwa so cute,Auta yace mu ai ba na wasa bane kalleni Kalli uwarta,Salma ta gyara hancinta da hannu tace wallahi,Aka kwashe da dariya.

Muka zauna muka kafa dabar hirar Antena,Star tace ai ni sati biyu da haihuwa Ina samun lafiya da nayi wanka Abhulkhairi ya fara buga harka,Wise tace ni kuwa ai ni na Kai kaina Kun San ni ba hakuri, Seraline tace ni kuwa har yanzu,Mandula tace an barki a kwana yarinya,Yar Zabil tace bare ni ai tuni na Mika Kai,Iyamami sai Yar ta dauka ta bar dakin,Salma kuwa sai labarin haihuwa take bamu muna Shan dariya tace ai na zaci mutuwa zanyi yau Auta yasha zagi ban San ma Ina zaginsa ba,sai dare sosai muka tafi abincin da na Kai shi Salma taci Auta ma haka da Iyamami tuwon shinkafa na mata miyar danyar kubewa sai farfesun naman kaza.
Da sassafe ma lafiyayyen Kari Wise ta kawo gidan,Iyamami ta Hana Auta kwana a dakin Salma itace take Hawa bed din dole bedroom dinsa ya koma amma kullum da shi ake yini ana karbar barka yana cikin mata.

Santana ma Yazo da Jamcy dinsa itama tana ja cikin ya tsufa.
Ana gobe suna Auta ya dauki Salma da Baby da Iyamami ya kaisu can gidan Baffa wai kar a bata musu gida, Baso Yazo tare da Omaira da Dan cikinta Kato,Baso ya ga jaririya yayi murna siyayyar da yayi me yawan gaske ya hadowa Salma kaya da nata dana Baby,ranar Suna Baby taci Sunan Mami Salamatu wato Salma Kuma sunan matar Auta uwar yarinya,Auta yace Baby za a dinga ce mata Babyna ce,,da yamma Auta hole ya kama me kyau muka dauki wankan Anko kamar ana party na biki haka Auta da Salma suka hade a high table ana cashewa anci an sha an cashe.
Bayan kwana uku da suna Ahsan Yazo yaga Babyn Auta ranar Kuma Auta ya dauke matarsa da Iyamami suka koma gidansa.

Bayan sati daya da Suna Kaka da Mama suna gidan Cele da Zama ta fara nakuda,Cele ce ta fito kamar an jefota tace Kaka ka taimakeni Kaka,bazan sake Shan maganin mata ba,har Umma na sawa a lemo na bawa Auta ya sha,Cele tana ta tonawa kanta Asiri Kaka yace ni maganin nan yayi min kici gaba da bani wlh ko ya kika ce Zuwaira? Zuwaira tace wlh wannan ai abin a siya ne, sun Saba Cele tana yawan siya musu kala kala suna shoshalewarsu,Mama Basu san Nakuda take ba sai da suka ji tana ta maganganu ita kadai kamar me Aljanu,tace Sanda na hadawa Salma mugunta na sawa Salma maganin sai muguntar ta dawo kaina ranar Ahsan yayi min ciki Allah Kaka, Mama tace Kai ba lafiya ba ta Kira Ahsan yana daki ma yana bacci tace tashi Cele nakuda,bai gane da Hausa ba sai da zancen kurame Mama ta nuna masa yayi zumbur ya mike ya fito ya dauketa da gudu,Mama ta dakko kayan haihuwar,suka tafi driver ke Jan motar kaka yana gida shi Kam,Ahsan sai kuka yake ya rike Cele ,dama su akwai saurin kuka sai kuka yake yana Kiran Allah,ya Allah,yana yiwa Cele kiss a goshi Cele ta dirka masa duka a kirji Dan iska ka barni naji da kaina aikin banza kayi min ciki ka hanani sakewa ko wani zaka sake yi min yanzu to sake yi min na gani,kawai ba tausayi ba Imani kawai ka dawo kana min kiss Ina wani halin, kiss din banza,Ahsan yace kiyi hakuri ciwo ne,tace bazan hakura ba wlh bazan hakura ba Mugu kawai,wayyo zan mutu Zuwaira zuwairaaaaaaaaa....uwarku gaba daya, Ahsan dan iska.....Koda suka je asibiti ma Cele cewa take likita uwarki,Likitar burar....ashar dazagi ba Wanda basu sha ba,wata nurse tace Kai wannan da bala'i take haba Babu Wanda bata zaga ba,a lokacin Kuma Santana an kawo Jamcy ta haihu harda dafe Kai yana ihun murna ,ya Kalli Ahsan yace sorry woo ta kaina nake yi nima, ya shige ciki abinsa.

Basu dade ba Cele ta haifo yarta mace kuwa,tana samun kanta tace a Kira Miracle,aka kirani na tafi asibitin duk muka Kira Yan uwa da abokan arziki sannan tace Kira min Auta ki fada masa kice tawa Abdullah zai aura jinin larabawa kalleta gaba daya Ahsan tayi wlh,Nace au ku yanzu akan Abdullah kuke takara da Auta nace Antenar yarona lafiya ku jawo min masifa ya girma da wuri wlh ku Daina wannan iskanci ke da Auta,Cele tace to shi a dangin Uba ni a dangin Uwa naga Dan Iskan da zata auri Abdallah din,na dinga dariya nace Dan Allah ki koma ta auri dan gidan Wise wlh bazan hana Yar Auta Dana ba,Muna ta dariya akan Yara kanana muke wahalar da kanmu, da wuri aka sallamomu Ahsan ya ishishire Shima ba kunya ba komai kamar Auta yarinya tana hannunsa,gashi da taurin Kai, Mama tayi fadan har ta gaji,sai Cele ta masa magana ma da lallabawa sannan yake hakura,Cele tace Miracle Nima a tanadar min magani wlh planning zanyi Ahsan yace bai yarda ba shi Kam shi Yara yake so sai an haifar masa biyu ko uku Cele zata huta shi Sam bazai yuwu ba,Cele tace jaraba sai kayi ta yi ai indai local government ce gata nan zan gyarata ni naga irin wannan masifa haka.

Ranar Suna yarinya taci Noor Cele ta dinga masifa wai sunan yaso yayi kama da na Maheerah,Ahsan ya dinga dariya yace mene hadin Noor da Maheerah? ai da R a sunan kawai kace kana son tsohuwar matakarka shine zaka sawa Yata,haka ya gaji da masifar Cele ya kyaleta,Auta ya zama Abokin dabin Cele akan Abdullah kullum musunsu kenan kowa yace yarsa zai aura,Jamcy mun sha sunan danta Namiji Raheel,bayan sunan Cele da sati biyu ita da Ahsan suka tafi Saudiyya abinsu,kaka da Mama suka koma Kaduna.

Auta kuwa a ranar da yasan Salma ta fara Sallah bayan tayi arba'in ranar ya samu Iyamami a Palo tana shirya Yar Baby,Yace Iyamami My life ake shiryawa ne? tace ae yace da kyau ya kamata kema ki shirya kanki kiyi gida yau, Iyamami ta bude baki tace ba sannu ba na gode? Auta yace to Matata ta fara Sallah kar muzo mu cika Miki kunne da ihu mufa a ko Ina harka muke karki ce ban fada Miki ba ni ba tsayawa zanyi na jiraki ba Antena bata Jira Idan Kuma so kike ki kalla to,Iyamami tace a'a me yayi zafi ungo yarka Auta ya karba yana dariya a boye ta kwaso kayanta,Auta yace muje na kaiki,Salma ta fito da kaya ta hadawa Iyamami sha tara ta arziki,Iyamami Auta yana sauketa ta fada wajen Mami tace sun Koro ni,wai Ina sa musu Ido,taje ta fadawa Baffa ma tace karshen duniya Yazo la'ilahaillallahu Auta ya gama fitsare kafafunsa har Kansa ya fitsare ba iya kafafu ba.
Auta yana dawowa ya samu Salmansa ta wani cakare cikin kana nan kaya shegu,Yace Salma Maman Salma ga surukarta Salma matar Auta,Autar Auta Kuma ga wata Autar,Salma tana dariya tace ai sai mun huta zamu sake ko? Auta yace Idan na Kalli yarinyar nan gaba na faduwa yake, da wuri zanyi suruki na shiga uku Auta da suruki yanzu yarinyar nan ranar data fara zance ya zanyi,Salma ta sheke da dariya,tace Kai dai bari ni kaina Ina hango abin nan,Auta yace gaskiya Kano zan dinga kaita gidan

2 Comments On YAR AIKIN KARUWAI Book 2
avatar
zainab-ibrahim-8

11 months ago

Reply

Thank

avatar
ghh

10 months ago

Reply

Replying to zainab-ibrahim-8

Yayi kyau?

Please Login or Register in order to submit comment