Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ahsan ta kula da shi, Maheerah a gabansa ta tsaya tana yatsina Masa Fuska tana galla Masa harara tana masa kallon banza,Hannu takai Wai zata mare shi sai ta fa ta Kai Masa naushi nan ma ta fasa wata uwar harara ta Masa tare da jansa tana Jin haushinsa har yayi wanka da brush tare da abubuwan bukata,Alwala yayi Suka fito ta shimfida Masa Sallaya tana zabga masa uwar harara sannan ta jawo shi saman Sallayar tana kukan karya Noorul Qalb kayi hakuri mutumin kirki da kai an jarabceka da wannan Lalaura gwalo ta Masa ta yatsina fuska ta sake Kai Masa Mari sai ta janye hannunta ta zazzage shi kasa kasa, Sallah ya tayar bayan ya Mata godiya, itama wanka tayi ta fito tare da gabatar da Sallah,bayan ya idar har azkhar cikin larabcinsa yace na gode matata Allah ya bani mace me kaunata me kula dani, Maheerah ta wani yatsina Masa Fuska tace idan ban maka ba wa Zan yiwa amma fa Ina bukatarka sex nake so ni bani da hakuri ka sani,Ahsan yace kina kallo bani da lafiya,oh nufinka sabo da ka makance baza muyi rayuwar aure ba yau kwana biyar fa rabon da ka min wani abu kasan kuma ya nake tunda baka gani ai wannan waje ba sai me Ido ba ma zai gane Hanya,Banda ni bazan gane ba cewar Ahsan,ba sai na saka a Hanya ba,bakinsa ya dan tamke yace bana mood yanzu baki da hakuri ki bari na samu nutsuwa a zuciyata bakya ganin halin da nake ciki.

Maheerah kwafa ta ja ta manta ta kori Ayusha ta kwanta baccinta ta barshi a kasa saman Sallaya, sai 11am ya tasheta yana fada Mata yunwa nake ji ya kamata ki sama min wani Abu naci tunda kin kori mai aikin naki,ko kulashi bata Yi ba Wai bacci take yi bayan tana jinsa, a hankali da lalube ya samu ya fito Palo tare da Zama a kujera,lokacin Cele ta gama girkinta tsaf ta fito ta ganshi yana hamma,tace karka cinye ni da hamma haka yunwa yake ji ne,tarkacenta ta kawo gabansa ta rike hannunsa tace Cele Rufaida,Murmushi yayi tace Sabahul khair,Kai ya jinjina Mata kawai, tea dinta data hada tasa spoon ta rike hannunsa tare da dawo da shi kasa ya zauna saman carpet yanda Suka saba cin abincinsu, Shayin ta ebo a Spoon sai da ya huce ta Kai bakinsa yaji spoon a saman lips dinsa bakinsa ya bude ta zuba Masa ya shanye,Ahsan a ransa yace Anya Kuwa bazan Yi Mata biyu ba,ai Mata biyu sunyi a rayuwa idan wannan ta Bata maka sai wannan ta faranta maka Allah yayi gaskiya mu larabawa da kudin ma Sai dai mutum ya Kara aure a boye bayan ga abinda Allah da manzo Suka ce,Rufaida ta Zama Masa Kamar matarsa sai kace kishiyar Maheerah,a ransa yace gata da tsafta ga tausayi da Imani,nan take ya maida sunan Cele Iman wai tana da Imani, Cele Kuwa tana bashi shayi ga chips da kwai sai da yaci da yawa sannan ya nuna Mata ya koshi, Cele dai harda Dan zuba ruwa kadan a hannunta tare da gogewa Ahsan baki yanda akewa Yara a Nigeria sabo da ko da bakinsu ya baci,Tissue ta sa ta sake goge masa bakinsa Yana ta dariya marar sauti,Cele tana kallonsa tace kaga idan kana gani kayi magana wannan Ido tangararan ace bawa baya gani da su gwara ka sa glass dinka ai sai ka hanani sukuni na zaci kana gani haba Ido fess haka Anya ba salon Iskanci bane wannan amma bari zan kureka sai dakko Allura nazo Zan tsira a idon Indai kana gani ai Zan gane shu'umin bawa.

Hannunsa ta kamo ta Dora a cikinta tace cikina kaji sai tauri yake na shiga uku ni kam,Cele ganin Wai baya gani ta taba boobs dinta tace gaskiya Ina Jin Dadi a gidan nan sai wata uwar kiba nake ji kirjina haka tabashasha dariya tayi tace an cuceka bakwa Jin hausa wlh kalmomi iri iri na iya shege bakwa ji.

Maheerah ta leko taga Sanda Cele take bawa Ahsan abinci kishi kamar tayi ihu,Fitowa tayi Kawai ta shiga dakin cele ta kwaso Mata kayanta kaf tace gashi nan ta dauka ta bar musu gida ciki basa so,Cele ta gane nufinta duk da bata Jin me take cewa,Murmushi Cele tayi tace wallahi Zama daram ba inda zani in tafi inje Ina ai Naga gidan zama inci me kyau Insha me kyau a Sadaka ba tare da na Zama takari ba Zama daram,Maheerah ta nunawa duwawu ta zauna tace Zama dole,Ahsan ne ya musu magana yace su daina fada,Cele ba jinsa take ba sai Maheerah da ta dage tana masifa na gaji kana kallo ai wannan bakuwar tana taba ka yanda taga dama ko Haram baza kace ba dama kana so ta taba maka jiki to sai ta bar gidan Nan,yace sau nawa kike ji Ina ce Mata Haram Haram ba inda zata je wannan ai zulunci ne an sa Mata ciki kuma a koreta to gida nawa ne ba inda zata je ko ta haihu sai ta zabi tafiya ko Zama amma tana gidan Nan,Maheerah tace baza ta zauna min a gida ba tana masifa Ahsan ya farara laluben Maheerah Wai zai mareta tana Raina Masa hankali,Cele ce ta jawo Masa ita ta karfi ta danno fuskarta jikinsa Wai gata ya daketa, Dan Marin ma wani tas kadan ko yaro bazai ma wannan lalataccen Marin na Ahsan ba,amma Maheerah sai kuka tana yarfe hannu ta shiga uku yau miji ya mareta shima Ahsan a Dole Namiji yayi bajinta,Cele taja Tsaki tace Kai dai ko wani Salahu wani Sahanunu da kai wannan Zama a gidanku akwai takaici Yar iskar yarinya tana ma Iskanci ka kasa komai,Kan Maheerah ta juya tace Yi Mana shuru shegen hakora Kamar katangar kwalabe, Dan iskan hakora Kamar kwano yaji lamba dakinta ta wuce tace irn wannan bakin ciki a gidan Ahsan ai ya baci wannan ba karamin dakikin balarabe bane haba.

Mami tana gama Idda Auta yaje har dakin Baffa,ya shiga ya gaida shi,Baffa Yana shan lemo a zaune Yana tunanin duniya yace Autan Mami ya akayi ne Naga kana ta smiling yace Albishir Zan baka Baffa amma sai ka bani goro,yace me kake so za a baka idan fa me Dadi ne Albishir din,yace deal zamuyi Zan fada maka amma nima idan na Shiga University zaka Yi min aure,Baffa ya bude Baki yace aure kuma wace matar? yace me rabo ce dariya Baffa yayi ya dauka Wasa yake,Auta yace satin Mami biyu da aure aka saketa fa ta dawo gidan Yaya Nawwar a can tayi Idda yau ta fita,Baffa Yana daga zaune bai san sanda ya mike tsaye ba,yace yanzu Auta tana gidan Nawwar? Ina gaya maka kuma tayi Idda ma ka yarda dani mana,wow Alhmdllh amma naji dadi yanzu ta ya Zan Mata magana ta yafe min ta dawo gidana, Simple cewar Auta abu me sauki idan zaka cika min Alkawari na to Zan wuce maka gaba,Baffa yace Auta manya to Zan cika maka yace to karka je yanzu Baffa ni nasan ya zanyi in lokaci yazo zance kaje,Auta to Ina so na ganta,to ai kaji Kuma Baffa zaka bata show kana da gaggawa,so kake ta ja ma aji ta rainaka kayi zamanka Zan ma magana,Baffa yace to Auta na sanka ba Wasa yace sure ya fice Yana fita wajen Mami yazo,ya iske tana girki yace Mami tace naam ta juyo tace Auta sai taga Auta Yana hawaye shaaaa shaaa tace Kai lafiya,harda sheshekar karya yace a...ab..abin takaici.....Mami ta tsorata tace Wai mene? ...hawayensa ya goge na karya yace ba komai ba sai ma na fada Miki ba tunda nasan baza ki damu ba ke,Mami tace bafa na son Iskanci idan zaka fada min ka fada min which kind madness be this,Auta yace wani satin za a daurawa Baffa aure,Ido Mami ta zaro ta tsaya kamar gunki tace aure Kuma tsofai tsofai da shi sabo da budurwar zuciya,Auta yace Kuma budurwa ce zata Kai sa'ar Aunty Rabi baki ganta ba Wai abokinsa ne ya bashi ya aura,Mami tace Kuma shi baida hankali sai kace yaro ba sai ya samu dattijuwa irinsa ba wannan wanne irin mutum ne, Auta yace bari Ni dai na bar Masa gidansa,Mami tace ya kamata wannan abin a bar Masa gidansa ne wannan ai wulakanci ne aikin banza aikin wofi rashin mace hauka ne Dan wulakanci ma yarinya budurwa ai shike nan ka fadawa Su Sultana su bar Masa gidansa su dawo nan,Auta yace ai Yaya Nawwar ya sani ma yasan da auren Shuru yayi da bakinsa yace tunda ba son Baffa kike ba yanzu mene ma amfanin a fada Miki Kawai yayi aurensa,Mami a ranta tace wato Nawwar baya kaunata ai shike nan a fili tace ba komai Auta jeka kawai, Auta ya juya ya tafi yaga Mami kishi karara ya fito lallai tana son Baffa.

Mami fasa girkin tayi ta kashe gas din gaba daya ta dawo bedroom ta zauna gefen bed ta saki kuka, Nawwar yau da wuri ya dawo gida Yana taya Mami Murna ta gama Idda ni kuwa palon Mami nazo da abinci iri iri Dana shirya na jera Mata a Dining sannan nayi docoration a dining din Muka kawo cake hadadde Muka ajiye table din yaji adon flowers red, munci gayu ni da Nawwar kayanmu iri Daya shadda Muka sa Fara kal mun zuba kyau,nace Baby ka Kira Mami yau ranar murna ce fa,Nawwar kiss ya manna min a saman lips sannan ya haura sama da sauri Yana Kiran Mami na,knocking yayi Shuru Shuru a hankali ya tura kofar ya shiga tun daga bakin kofa yake Jin sheshekar kuka,da sauri ya karasa Gaban Mami dake zaune a gefen bed tana sharbar kukan soyayya,Hannu yasa zai taba ta a zabure tace karka sake ka tabani munafuki ai ban san baka kaunata ba sai yau,da Kai za a hada baki Kai da ubanka kasan da zancen kaki fada min karka sake kulani,Nawwar yace me nayi Mami hankalinsa ya tashi tace ban sani ba Kai da matarka karku sake Shiga harkata tunda Baku da mutunci,Nawwar ya sake Kai hannu zai riketa ta doke Masa hannu tace get out,Jin Nawwar shiru yasa na taho Nima Ina cewa Baby zamu je unguwa fa ko Mamin bata nan na shiga ciki nima,a wajen na daskare ganin Mami tana kuka Nawwar Yana gabanta yana bata hakuri Yana ta lallashinta yana lallabata ta fada Masa laifinsa, ganin haka na juya Zan fita tace dawo kema munafuka Ina Zaki dawo sai ku zuba ruwa a kasa ku Sha dan Sulaiman yayi aure sai me sai akace muku mutuwa zanyi se waiting? sabo da Baffanka yayi aure nace se waiting? So what sai aka ce muku Zan mutu ko mene,namijin banza namijin wofi ni Namiji ya Isa ya bata min rai,Nawwar yace au Baffa aure zaiyi? Kai dalla rufe min baki gulmamme ai kasan komai ai Auta ya fada min komai yace wani satin zaiyi aure ka San zancen ma da sa hannunka kuke boye min to sai me ance maka Ina son ubanka ne,Sai yanzu Nawwar ya fahimci kishi ne yake damun Mami yace Auta ne yace Miki na San zancen? tace ae Auta baya karya,dariya Nawwar ya boye yace wallahi Wallahi kinji na rantse ban San zancen ba amma dai naji su Sultana suna kus kus da zancen na zaci ai gulmar Mata ce shima Nawwar ya sake shigar da Mami,Nace Kiyi hakuri Mami bamu San zancen ba wlh Kuma Inshaallah kece Zaki koma gidanki ne ke kadai wace ma ta Isa ta shiga gidan nan ban ci ubanta ba ai Baffa naki ne ke kadai,Tsaki Mami tayi a ranta ma tafi yarda da Rabi tasan zata iya Hana auren ko da tsiya tsiya,tayi kwanciyarta ta juya Mana baya,nace Celebration din fa? tace Cele what? Ku tafi ku bani waje baza ayi Celebration din ba,tashi mukayi Muka fito nace kai Mami fa wallahi sun koma Yara abinda sukeyi ko mu baza muyi shi ba,Nawwar yayi dariya yace ai auren da mace tun tana karama ake yi musu tare suke tasowa su girma tare shi yasa Suka fi kowa shakuwa auren da akwai shakuwa,Lallai Auta Dan Iska ne shine yace na san zancen yaron nan haushi na yake ji akan na aurar da Wise ga Papa shike nan ya rainani,Dariya nayi nace nidai a samowa Auta wata Kawai mun shiga Uku da shi ya iya hada bom haka,Nawwar a waya ya Kira Auta yace yazo zai aike shi Office.
Ya manta yayi gulma yazo da sauri Yana zuwa Nawwar ya mammake shi ya dinga cin uban Auta yace ka hadani fada da Mami,Auta yace Sorry Yaya Kuma sai ka mareni ,fita dalla Kar na sake ganinka tunda Kai baka da hankali,Nace haba Kuma sai ka doke shi na Kai hannu Zan ruko Auta Nawwar ya min tsawa yace ke wannan balagaggen yaron Zaki rike to Auta Yana zuwa ki saka hijab,Auta ya juyo ya kalli Nawwar sai da ya bari yaje jikin kofa yace ni me Zan ci da matarka old version ya fice da gudu,dariya nayi nace kaji yaro wallahi sai naci....Shuru nayi,yace Sorry new version karya yake da za a bashi ke karba zaiyi da gudu yasan bazai samu bane abu lutsu lutsu haka,dariya nayi ya jawoni jikinsa.

Star yau fada sukayi da Malam Abhulkhair Wai ya Dade a masallaci bai dawo gida ba,Star tace kaje kayi ta karatu baji ba gani murya kamar ta zakara haka akeyi ai sai a dinga Yi ana bawa iyali hakkinsu,Malam yace ke ai kin rainani kije masallaci kiga yanda ake gaisheni ana girmamani ke Kuwa ina,Star tace ka gama min kukan kullum,kana rokata local government,kazo tumbir zigidir yanda kazo duniya sannan kace Wai bana girmamaka sabo da Allah ai Ina kokari ma su mutanen kaje musu a yanda kake zuwar min ka gani idan zasu sake saurarka,ai wlh bata kamata ma na gaisheka ba,Ni ya kamata ka gaisar kullum kace ya fargaban jiya,tunda a zauce zaka zo min kana ihu gaka ba Kaya ai abin fargaba ne amma sabo da kokarinmu na Mata washe gari harda gaisuwa wlh bazan gaisar dakai ba ai baizo a musulunci dole ba Kaine ma ya Dace ka gaisheni,bazan gaisar dakai ba fa Abhulkhair yawwa kuma body lotion Dina ya kusa karewa ka min transfer,kullum ka Tara min gajiya Kuma kana jira na tashi na gaisheka cab ashe zaka bushe,Malam Abhulkhair dariya yayi kawai yace ke komai naki yayi kinyi a rayuwa amma idan Kika tashi fadanki Kawai bi kike ta kaina,wa yace ka Dade a masallacin anyi karatu an Gama ka dawo muyi namu mana muma nifa baza a cuceni da malinta ba Dole ka bani lokaci na yawwa Kuma kayanka na gaji da ganinsu dinki kala uku ka Kara tun Aurenmu sabo da haka muje a siyi Kaya sababbi sannan kana Nan kaya ka dinga saka min a gidana Ina kallonka Ina Jin Dadi idan ba haka ba zanyi tawaye wlh,Malam Abhulkhair yace ya zanyi tunda na Zama mijin tace shike Nan naji yanda kike so Haka Zan koma amma kana nan kayan a iya gida Zan saka Miki? tace au da nufinka ka fita da su wata ta gani? Ni zaka sawa fa,an gama Aunty ya furta,tace yawwa Banda cin kudin marayu ko tallafin masallaci da ake sakawa a asusu kaci iya hakkinka albashinka na limanci da Kuma business dinka banda taba hakkin wasu,abinda zamuyi iya karfinka shi zamuyi,Yace na'am malama Tauraruwa wannan wa'azin ya shigeni,dariya Star tayi tace ai dai yau nace bazan yi girki ba a waje zamu je mu ci mu Dan shana,yace Inshaallah taso muje ki cudeni,Star tace wanka Mana please ni bana son gargajiyar nan mene cudewa Maganar dattijai,Malam dai sai yanda akayi da shi gaba daya star ta Gama mallake shi,gashi idan ya Mata laifi tayi ta jaraba,shi baida zafi ba ruwansa shi yayi Dace yasan dole baza ka samu Abu yanda kake so ba tunda kowa a duniya Yana da halin kwarai Dana banza Kuma baza kace zaka samu mutun dari bisa dari ba sai anyi hakuri.

Kaka yau ana kwalla rana yayi Niyyar Umrah yaje ya dakko niyya da hiraminsa ya sake zuwa ya sauke Umrah ranar kwanansa uku a masallaci dakin Allah sai Ibada Kawai yake sai in yaji yunwa ya fito harabar masallaci ya siya yaci ya koshi ya koma,Addua yake kawai akan Allah ya bayyana masa Cele dinsa sannan Yana Addua Allah ya bashi kudin da zai dauki nauyin Kansa ba tare da yayi bara ba, yana zaune sai ga wata matar sarkin kasar Yemen,da masu take Mata baya mutum uku tazo Ibada,kana ganinta kasan akwai kudi,Kaka Yana zaune kawai yaga ta duka a gefensa ta zube Masa wasu makudan kudade Wanda dollars ne Kawai ta zube Masa Sadaka ta wuce ko kallonsa bata Yi ba,mutane suna kallo wasu suna cewa tsoho ya washe,Kaka ya daga hannu Yana Addua yaga kudin nan yace Allahu Akbar sai ya sauke Hannu yace Alhmdllh Alhmdllh Addua ta Kare ya kwashe kudi jiki na rawa ya mike maimako ya karasa Ina farin ciki yasa bazai iya ba tashi yayi yabar masallaci yace sai gida, a hanya ko gabansa baya kallo sauri yake yaje gida,sai ya hadu da askarawa suna kame yanzu sabo da ya samu kudi baya so su Kama shi duk askarawan Nan sun San Kaka yawanci sabo da duk inda ya gansu sai yaje ya Mika musu Hannu akan su kamashi sunki Kuma,wannan karon suna ganinsa daga ganinsu sai ya kwashe da uban gudu Kamar ana gudun fanfalaki tsoho dashi ya iya uban gudu haka,gulma sukayi Suka to ya Fara Jin dadi a kasarsu dole su Kama shi duk Sanda suka ganshi back to Nigeria, tun daga ranar Kaka da Askarawa Suka sa kafar wando daya, baya ma Fitowa daga masallacin layinsu sai gida,abinci ma a wajen takari yake siya masu kawowa gidansu Yana daki sai masallaci ko keyar Kaka Basu sake gani ba sabanin da Wanda kullum sai yaje wajensu, suyi ta labarin Kaka suna dariya,wani ogan askarawan kame a cikinsu yace Dan Allah ko sun ganshi Kar su kamashi su kyale shi ai tsoho ne dukkansu ya musu fada Kar su sake su Kama Kaka su kyaleshi ai rayuwarsa ta Kare ya tsufa kadan ya rage ya karasa sabo da ya tsufa,suka ce to Suka kyale Kaka idan ya fito ma har zuwa suke su Mika Masa hannu su tafa su dariya yake basu tsabar harkalla da hausawa wasu larabawan masu shaguna da masu kame suna Dan jin hausa,Yan kasuwar ma Kamar sun zauna a kasar hausa haka Suka iya sosai.

Wani Askari ne da Hausa ya tare Kaka a hanyar masallaci yace kazo Ni Zan baka aiki zaka iya? da hausarsa lalatacciya yayiwa kaka magana,Kaka yace wanne iri? Yace Ina da mota Zan baka ka dinga tukawa taxi Zan maka takardu da komai ka iya mota? Kaka yace ai ni tsohon driver ne a Nigeria na Iya mota,yace idan baza ka iya yawo ba Ina da motar Yogourt Zan baka Ina da company na Madara zaka dinga kwaso Madara kana kaiwa wani kantuna da address Zan baka zan sa a koya maka aikin,Kaka yace na gode zanyi wannan ai ba na wahala bane suka tafa da ba askarar nan
Bayan kwana biyu tsakani wani balarabe yazo daga wata state daban da gani kasan Yana da Naira ba askaren nan ya nemo Kaka,shi dai Kaka yana tsaye Yana jinsu suna ta larabci dake baya ji sai dai dai yake tsinta Kaka Bai sani ba ashe siyar da shi akayi akan kudade makudai Kamar wani Zamanin bayi anyi cinikinsa bai sani ba,Kaka ya yarda da wannan Dan sandan ya dakko kayansa yabi wannan mutumin balarabe a motarsa tunaninsa aikin za a koya Masa Suka tafi,Kaka yaga kamar hanyar Jeddah aka Yi da shi kawai dai Yana mota amma a jikinsa yaji kamar ba Alheri bane,suna uban gudu a mota Yana kwarara Addua.

Mairo ciki ya tsufa Haihuwa ko yau ko gobe gashi takari asibitinsu ma Basu da gata a can ba kowanne asibiti suke zuwar musu ba Basu da yanci tunda basu da ingantattun shedar Zama a kasar su, Mairo kullum kudi Yana tafiya a biyan bashi Dan Wanda ta Tara shine taje siyayyar kayan jariri wani shagon larabawa,tunda taje larabawan Suka fara kus kus da sauran yaran shagon,Mairo tana zuwa Suka dinga washe Mata baki Suka ce ta shiga ta zaba ta shiga ciki ko Ina kayane iya kallonka Hanya ma a ciki kadan ce, ogan me shagon Yana bayan Mairo,yaran shagon Kuma wasu suna bayan ogan wasu mutun biyu sun tare gaban Mairo sun tsaya a gabanta wato sun sa Mairo a tsakiya kenan,Ogan ta baya Yana sosa Antenarsa gashi dattijo su Kuma yaran nasa Basu fi 20yrs ba shi kuwa zai Kai 60yrs ma amma sabo da zubar da girma da yaran suke hada baki,Mairo taji Antena tana guganta ta baya ga ciki tsoho ga yaran sunki matsawa sun tare Mata gabanta wani dan iska ma juyowa yayi shima Yana gogawa Mairo Antena ta gaba ogan ta baya,Mairo ta rasa yanda zata Yi ta tura ta tura sunki matsawa gashi sun matseta a tsakiya mararta sai ciwo ta fara,Yaron Dake gabanta ta samu ta galla Masa Mari ta nausheshi tana zaginsu da larabci Suma suna ramawa Wai me yasa Suka Zo musu kasa sun bar kasar su sunzo Iskanci kasarsu,Mairo sabo da su takari ne suna harka da mutane a garin har sun iya larabci ba laifi wani uban naushi ta Kai Suka rike hannunta Kuma basu fasa Mata gogen ba,yaron ta samu ta gartsawa cizo a goshinsa sai da ta fasa Masa goshi,ba shiri ya bata hanya ta fice da gudu gudu tana rike mararta ta fito bakin shagon ta tsuguna a wajen tana murkususu,Allah ne ya kawo su Sadiya Suka ga Mairo tana nakudar dole ta kamata Suka dauketa zuwa asibitin da za a iya dubata basu dade da kaita ba ta haifo yarta Mace me Kama da Saurayin da yayi kidnapping dinta ya Mata cikin, takari ba abinda ya dame su wannan ba sabon Abu ne ba ka haihu ba miji a wajensu,murna suke ta zuwa suna taya mairo, Mairo ta samu Sadiya ta bawa kudin Suka siyo Mata dukkan kayan bukata nata Dana jariri, zuwa dare aka sallamota ta dawo gidansu da yarta,Mairo sai Murna take yi tana kaunar yarta harda kissing dinta jinta take Kamar ranta,aka zaro nono Kamar ta taba shayarwa dake da lafiyarta ta haihu aka yo bismilla aka sawa jaririya nono a baki ana shafa Kan jaririya tace sunanki Madina kinji Yar lelena da larabci Zaki tashi kinji a lahira kin huta duk tambayar da za a Miki a lahira Zaki amsa abarki ba gargada bare Ina ina mu ki kyale mu ko ta yaya ma amsa tamu,Sadiya suna Jin Mairo,Sadiya tace in Banda jahilcinki Mairo larabci ko bakya ji a lahira ai Allah zai sa kiji dole da shi Zaki magana ba sai Wanda ya iya ba,Mairo tace ke rabu dani gwara ta iya tun a duniya.

Bayan kwana uku Cele ce kullum ke kula da Ahsan,Maheerah tayi zuciya tunda tace ta kori Cele ya hanata tafiya to ta barwa Cele shi tayi abinda take so,Ahsan shima ko a jikinsa wanka ma Cele ce ke kaishi tana gwada Masa komai da ta gaji tace zata koya Masa ma yanda zai gane da Kansa ya dinga kai Kansa.
Washe gari Maheerah sai data bari cele tana dakinta Ahsan Yana Palo yayi zuru sanye da makeken glass sai kuwa Maheerah tayi waya da Saurayinta yace gashi ma a gidan ta Bude Masa kofa,da sauri ta fice ta gaban Ahsan taje compound tsalle ta daka ta dane jikin Saurayinta tana murna tace da larabci my life ya makance zamu ci duniyan mu,dariya yayi

2 Comments On YAR AIKIN KARUWAI Book 2
avatar
zainab-ibrahim-8

11 months ago

Reply

Thank

avatar
ghh

10 months ago

Reply

Replying to zainab-ibrahim-8

Yayi kyau?

Please Login or Register in order to submit comment