Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai yayi rawa duk da Baffa ya Hana party yace suyi bikin da kidan a gida baya son taron nan.
Duk wani Shirin biki anyi shi Salma dangin uwa suna ta gyarata sosai ta Kara haske da kyau sai kamshi take,ana gobe biki aka mata lalle me kyau da gyaran gashi ita ba kawar data gayyata sai Hajara kawai,Hajara suna tare Amarya ta zuba tagumi Hajara tace wai mene ne haka ne ni wlh Banga abin so a wajen Baso ba da kika nace sai shi,mutumin da sai Shaye Shaye ya iya kullum ya Miki dukan tsiya ya zage ki tas zakunci iri iri mene abin so a Baso gashi kin samu yaro matashi kyakyawan gaske gasu masu kudi Kuma da Alama yana da hankali me kike nema.

Salma ta goge hawayenta tace aure kamar wasan Yara Hajara sabo da masu kudin su zasu yi mana komai ki duba yanda sati daya kacal aka sa bikina Kuma ni yanzu garin ya min nisa ya zanyi da Baso kullum Idan ban Ganshi ba bana jin Dadi,Hajara tace naga Alama baki San ciwon kanki ba Salma Allah ya Miki canji kina hauka,ni to yaro ne fa nawa yake,Hajara tace ke kika sani aure dai ba fashi gobe I yanzu kina gidan Mijinki,Salma tana ta kuka ita sai Baso Kuma baza ta cire shi a ranta ba,Ango kuwa ko a jikinsa mantawa ma yake da ita Idan ya aureta sai Idan yaga wata dai dai da shi irin kalar da yake so sai ya aura abinsa ya huta da su Mami,amma Idan suka bashi Omaira ta karfi zasu sa ya fara sonta ma yace baza a mallakeni ba ga yayarta nan ta mallake Nawwar daga taimako bada ni ba Autan Mami,yace su Aunty Rabi gadon soyayya suka yi sun iya love tunda ji yanda mamansu da Abbansu suka hadu sai soyayya, da sun aureka ka gama yawo soyayyar tsiya ce da su.

Bangaren gidan Baffa Yan uwa da abokan arziki sun zo,Aunty Rukayya da yaranta haka Binta ma da yaranta duk Yayan Iyamami ne basa zuwa sai da dalili sabo da Halin uwarsu Iyamami,Wise kuwa uwar Ango da ita Nawaf yake shawarar bikin,Umman Rabi,NazifaNazira sai Bilkisu sunzo bikin Hadi da ganin gidan auren yar uwar su daga baya Kuma su Omaira zasu zo hutu suma,Wise ma wasu sunzo bikin Auta a danginta,gida ya cika an gama Shiri Auta uban abokai kamar me ko Ina sune a gidan ana ta Dj Su Sultana Amare suma komai tsaf an shirya sun sha gyara,tun ana gobe suka Fara Dj a gidan.
Auta ne ya shugo Ina kallonsa a Palon Mami nayi dariya nace Angon gobe,Kallona yayi yace fadi ki Kara,su Bilkisu ma suna tsokanarsa,Duk inda Auta ya juya tsokanarsa akeyi,Nawwar ne ya shugo Shima Ido muka hada ya kashe min Ido daya Nima na kashe masa nawa,Auta yana kallo yace Allah ya kyauta,Autan Mami Ango Dan banza wallahi sai munga rukonka ya za a Kare cewar Star da shigowarta kenan,kowa yace Auta kaza kaza ana ta dariya,Kasa kasa yace da Wise Mama karama an goge min kayan angwancin nawa? Wise itama kasa kasa tace tun yaushe yace karku min dariya wlh kwaila ce matar itama,nayi gudun gara na afka zago,muka dinga dariya muka ce ai kowa zai gani da idonsa,Seraline ta furta ka shiga uku duk karyar Ina ta Kare gaskiya Auta ka fado,yace ya na iya da kaddara danya ce to ta dai fara alamun bura zata Dan fara nuna kadan,Auta yana ta bamu dariya har shewa muke,Wise tace na siya maka man power Auta,Auta da sauri yace Natural.... Natural... Mama karama ni Natural ne ba sauki,Muka dinga dariya, Nace Auta ya kaga shaddojin? Yace sunyi Aunty ai kin iya zabe akwati guda kika min fa na kayan angwanci nima kin hada min lefe tnx,nace Auta namu ai kadan ne ma,Wise kuwa takalma masu tsada ta siyawa Auta sun Kai set goma,ga su Star an siya masa agoguna da huluna na angwanci komai anyi,Part din Auta a cikin gidan aka canja masa komai da tsari 3 bedroom ne sama 2rooms kasa bedroom Daya,Palo kitchen komai an zuba an kashewa Auta kudi sosai,Mami tace guiding danta zata yi sai ta ga kalar zaman nasu, amma sai take ganin kamar Auta yana boye mata wani abu.

Washe gari daurin Aure Auta wanka yaci ubansa ranar Shaddarsa fara Kal komai fari tas har hular ya sheka kyau yana zuba kamshi,babbar rigar ma ta matasa Yan gayu cass da shi,wasu ma a can jigawa suka kwana wasu Kuma a jirgi suka tafi can Jigawa a gidan Iyaye na gado cikin dangin Salma a nan aka cika aka daura Auren Salma da Nawaf akan Sadaki dubu dari uku,ana daurawa Auta sai murna kamar yana son matar ma haka yake murna,
Baso Kuma ana daurawa yaja Nawaf gefe yace Alhmdllh saura kudina Nawaf ya masa transfer kudinsa Million Daya chas sai murna Baso yake.

A lokacin dangin Salma suka tattara kayanta da lefenta da abubuwan bukata aka hada Salma da mata uku wanda zasu rakata can kudu gidan mijinta,Salma kuka take kamar ranta zai fita ita duk abinda ya dameta Baso ne,zata Daina ganinsa,shi kuwa Baso kiransa akayi a matsayinsa na uban ya Wanda ke rike da Salma akace ya mata nasiha,ya Kalli Salma dake uban kuka cikin lafaya me kyau da tsada,tana kamshi tana kuka,Baso yace kiyi hakuri Dan kutmar....ya duro mata ashar su kadai ne a daki yace ki min shuru ko na farfasa Miki baki,Kuma na fada Miki wallahi kiyi abinda nace kiyi abinda ya dace Idan ba haka ba sai na kusa kashe ki,na rigada na aurar dake ki nutsu ba a wasa da aure karki masa ae yane ko baki gane bane,Nawaf abokina ne yanzu Ina sonsa wallahi karki sake naji an kawo min kararki sai na sassaba Miki kamanni,saura Yazo yace ki Dan buda masa kika ki yarda sai naci ubanki shegiya me suffar aljanu ki min shuru munafuka,Salma tana goge hawaye Umarnin Baso kamar Umarnin Allah haka take jin maganar Baso sabo da so,yace kar naji kar na gani fito na rakaki mota,Ango yana bayan mota a zaune suna jiran Amarya zasu wuce Airport
Kwayar Baso ce ta motsa yace da matan da zasu raka Amarya Dan uwar kowacce gyatuma ta koma gidan mijinta uban waye ya rike min ita Idan bani ba to baku da amfani sai ranar aure sanda muke wahala akwai Wanda ya taba zuwa gidanmu ya tambaya Yaya muke ci muna koshi wanne Hali muke ciki Babu,sabo da bani da kudi ko gidanmu bakwa zuwa ziyara sai Idan mu munga dama mu neme ku,yanzu na aurar da ita lafiya mun rabu lafiya Kun kwaso tsofaffin kafafunki zaku tafi kaita gidan Miji uban me kuka taba taimaka mana,to ba shegiyar da zata Kai min kanwa gidan Miji ni zan kai abata da kaina na damkata Amana,Anji jirgi an taho za aci baza naga shegiyar da na gani a jikin motar nan,ya juye ya Kalli Salma yace ke shiga muje,Salma ita murna take da farin ciki Baso zai kaita har can ko banza ta dinga kallonsa taji Dadi, daga Baso sai Amarya sai Ango da wasu tsirarin abokai tunda har Baffa duk an koma ana daura Auren Sultana da Nasira suma akan Sadaki dubu dari biyu biyu,ana ta shagali ana ci ana sha ga Selfie ana yi ga kida na tashi munyi rawa har mun gode Allah.

Baso da Salma a jirgi har garin aka kawo motoci aka dauki Amarya da Basonta ita kadai Ango yana motar Afif suka nufi gida wajen Mami,suna shiga kida na tashi duk angwayen su Sultana anyi hotuna sun tafi, Abokan Auta suna jiransa ga Motar Amarya a baya,suka shugo bayan anyi parking Auta ya fito da zugar abokai duk suka taho ga Kida na tashi ana Dj Auta ba kunya ya shige ciki ya dinga cashewa muna ta masa liki ana dariya,Baso ne ya fito da Amarya Shima ya shige cikin filin rawar yace a kashe,aka kashe kidan kuwa, yace bani kidan Na aurarta lafiya na huta da kaya,Dj da mutane aka dinga dariya ana tambaya waye haka akace ai shine ya kawo Amarya shi ya riketa,Kowa mamaki a haka ma Dan baiyi Shaye Shaye bane sosai,Baso yace ku sa min Kidan na jefar da kwallon Mangoro na huta da kuda,akace Shima Babu yace to wai sai Uban me Allah ya gani dama ba a so na taka,Nawaf ne ya jashi gefe yace zaka bata deal za ace ba tarbiyya please,yace chansa dai chansa dai na hakura ko Dan kudina su tsira,Wise ce ta budewa Salma mota ta fito da ita tana guda ga Amarya ga Amarya.

Kawai Baso mahaukacin ba Wanda ya bawa Amarya ba danginsu ya sulale ya fece,sai Nawaf yayiwa waya shi tuni ma fa yana hanya yabi mota,Nawaf yace to ya sake tura masa dubu talatin ya Kara kudin mota,Baso yayi ta godiya ya koma gidansa yana murna daga shi sai mahaukaci
Washe gari dare na yi Baso ya siyo manyan gasassun kaji da yogurt guda biyu ya bawa Mahaukacin guda da Madara shi ya dauki tasa yana ci yana cewa Alhmdllh na huta da jaraba haba ai na samu na Wala yarinya ta gallabeni da kyar na samu me siyanta sai shegen bakin jini.
Salma kuwa bayan Baso ya fece bata sani ba tana tsaye tana Shan kallon fitsarru muna ta rawa Auta rawa yake kamar me,Salma ta kalle shi tare da tabe baki tace kalle shi kamar Dan Iska aikin banza.

Zuwa dare aka Kai su Sultana Wise da Salma ta dinga tafiya sabo da taga bata da dangi,Mami ta dinga fada me yasa za mu dauki Amarya daga kawota mu tafi da ita Kai wasu Amaren,hakuri muka bayar.
Ranar Salma bata ga Ango ba Shima bai ganta ba a bangarenta suka kwana tare da Hamra,Sabreen da Iyamami sama sama suka yi bikin su ba ruwansu irin suna jin haushin su Mami,Iyamami Kuma wai an bari Auta ma ya auro musu bare ba yar dangi ba,gashi tana jin tsoron Auta wajensa ma baza ta je ba basa Shiri ko kadan gashi bashi da kunya wanke ta yake sol.
Yau duk Wanda Yazo biki na kusa da na nesa duk sun tafi sai iya Yan gidan,Hamra ita tasa masu aiki suka gyara part din Auta tsaf ko Ina yana kamshi ta hana Salma yin aiki ganin ta sawa kanta damuwa tunaninsu alhinin rabuwa da gida ne.
Mami har can taje tayi mata nasiha sosai karshe tace ki dauke mu Iyayenki Dan Allah ba babanci kuyi hakuri da juna aure sai hakuri,Idan ya Miki laifi kizo ki fada min kinji,Salma taji sanyi ko ba komai iyayen Nawaf mutanen kirki ne har mamakinsu take gasu masu kudi amma ba wulakanci,tana mugun son Wise da ni Rabi da su Star sabo da ta ganmu Yan harka ne har wasa muke mata muna tsokanarta.

Mami zata fice Salma tace ina matar Yayan me gidan nan? Mami tace waye megidan nan a kunyace ta kama Salma tana kasa da Kai tace Auta,Mami dariya tayi wai Auta ne ya zama me gida yanzu ta sake yin dariya tace tana gidanta,au ba a nan gidan take ba? Mami tace ae mana ku ma nan gaba zaku koma gidanku Idan an gama ginawa,Salma tace ina sonta wallahi ita da kawayenta da Wise take suna da kirki,Mami tace Wise Kanin Baffa take aure a takaice ta Dan bata labarin su,tace yanzu dama su Aunty Sultana sun girmi Me gidan nan,dariya ta sake kama Mami Idan tace wa Auta me gidan nan wani dariya ce take kama Mami,tace ai shine Auta,tace uhmm i see amma ya fisu girma ma kamar shine Babban, a ranta tace harda gemu da saje,Mami tace Dan Allah ku zauna lafiya,Salma tayi godiya sanye take cikin Atamfa super black and white tayi mugun kyau dama abinka da me kyau gata yar dagwas da ita matashiya.

Mayafinta ta gyara tare da rufe kanta ciki ta zauna a tsakiyar bed,Wise ce ta shugo tana mata turaren daki iri iri, Salma ita Baso ta tuna sai kuka take,Wise tace kyayi ma Kya gama Yan banzan Yara sai balagar zuci da Miji ya shugo za ajiku lakwas kuna karbar Antena, Salma tana kuka bata gane mene Antena ba.
Auta kuwa wanka yaci cikin wata Gezna ruwan Zuma ya tsula kyau yana kamshi ya gama Shiri ya zauna a bakin gado yana latsa waya a fili yace duk da cewar ba abinda zanyi wa Amarya amma da kunya yanzu kawai sai Mami taga na nufi part din Amarya ai da kunya sai da nace abokaina su rakani suka ce an Daina yayin raka Ango yanzu,Ina zan Saka kaina da kunyar Mami,yanzu Ina shiga shike nan ko banyi komai ba za ace nayi wani abu na zama Dan Iska,wayyo pillow ya jawo ya rungume yana cewa wayyo kunyar Mami waye zai rakani gashi ko kazar ban siyo mata ba ni ta Ina zan fara ne.
Tashi yayi yana gwada yanda zaiyi Idan ya shiga ya sha kunu ya bata rai ya furta kawai cewa zanyi Salamulaykum sannunki,da sauri yace nooooo Sallama zanyi da yanga na ajiye mata ledar kajin nace good night,a'a ai Kuma ba tsari kawai muyi fada tunda ba Sona take ba Nima haka,nooooo Auta nutsuwa zakayi Kaine fa namijin, mijinta a kasanka take behave well,yace uhmm hakane tabbas,yace yanzu zan fita Allah yasa kar na hadu da Mami,a hankali ya Bude kofar yana sanda yana lallabawa kamar barawo wai zai tafi part dinsa kar a Ganshi da kunya,da sauri ya dawo dakinsa kamar Wanda za a kama,sake gwadawa yayi har ya fita ya sake dawowa yana dariya yace wlh bazan je ba bazan iya ba,can Kuma yace haba karya ne Auta Kaine fa Dan zamani haba ka waye kunya ma tuni muka cillar da ita,kwanciya yayi a gadonsa ya ja pillow ya rungume

Mami ce ta banko kofar ta shugo dauke da katuwar ledar nama da kayan sha,uhm Auta Dan gata auren gata,Mami tace wai uban me kake Jira ne jiya fa baka je ba sai da Hamra suka kwana ko da matsala ne? kamar kana boye min abu,Auta duk zumudinka ka zauna jiya baka je ba yanzu uban me kake a nan ka bar yar mutane gashi har 10pm sai Wise na tura ta tayata zama,tashi ka tafi muje oya,Auta yace ni dai Mami wayyo yana yarfe hannu,dariya ya bawa Mami yace Mami zanyi kuka nima,muje Mami ta jawo shi ta rufe kofar tace kayanka an Kai can komai yana can muje,suka fito yana wani tirjewa yana sangarta,Mami tace zan mareka muje,suka tafi har bakin kofa ta kaishi tace kayi Addua ungo ta Mika masa ledar ya karba,ya juyo yana kallon Mami tace kaje,Rungume Mami yayi yace I love you Mami Babu kamarki,I will miss you gobe baza kizo ki tashe ni a bacci ba? Dariya Mami tayi tace ga matarka nan,mu kwana lafiya,tsokanar Mami yayi yace Mami ta juyo tace na'am yace hanyar ta Ina zan bi? zagi ta auna masa, ya shige ciki yana dariya har ya rufe kofa ya sake budewa yace Mami da karfi,ta juyo yace Good night kice Ina gaida Baffa,tafiyarta tayi,yana juyawa yaga Wise ta gama turaren tace Ango a bi yar mutane a sannu,Auta yace Mama karama karki bani kuka,Wise ta fice tana dariya ta musu sai da safe.





A dinga sharhi please shine godiyata ni






AsmaBaffa
08061929616
[8/15, 9:51 PM] AMINA KABIR CAPS: 🌼'YAR AIKIN KARUWAI 2 🌼
MATAFIYA

BOOK 2


51-55


Official

By
AsmaBaffa



SADAUKARWA GA
ZAINAB USMAN



*MISKI 3in1 Alfirdaus*🌹 Albishirinku💃 original miski daga *Egypt* miskin da koda yaushe Kuna yabawa dashi yana dauke 1.*Musk oil* ana shafawa agaba bayan gama al'ada inda hali za'a iya ringa sawa Koda yaushe yana maganin infection yana gyara gaban mace sosai 🙈ko yaushe gurin yakasance cikin kamshi 😇bayaga haka sunnah ne amfani da miski
2.*Musk cream* Ana shafawa ajiki gaba daya musamman wajan cinyoyi yana sa jikin mace koyaushe yakasance cikin kamshi kuma yana gyara fata, yasa tayi laushi
3.*Turaren tsarki* wannan turaren karshe ne 🔥 🔥 ba lallai se bayan gama period ba koda yaushe zaki iya rinka tsarki dashi yana gyara gurinnan🙈 sosai, kuma ana shafawa a hammata yana kawar da da wari karku bari abaku labari 🙍♀️👱♀️

Masu bukata ku ne wannan number
09065959708


Page naku ne
Sadiya Muhammad
Zakiyya Bello
Badimahd238
Gwaggonsu
Amina Maman Ibrahim
Dr Suhailat Hussein Armai.






Auta ciki ya shiga tare da haurawa sama direct dakinsa ya bude bata ciki ya dawo daya bedroom din ya tura kofar a hankali ya iske Salma tana uban kuka ita Baso take tunawa,Baki Auta ya tabe ya karasa ciki yace sannu da aiki ya bude ledar ya dauki abinda zai iya ci ya ajiye mata sauran yace ayi kuka lafiya,Salma wani takaici yasa tace sai anyi din Ina ruwanka dani, babu abinda ya shafeka da ni,juyowa yayi yace who even care about you kalleki Dan Allah ya ja tsaki, Salma kuma ta furta Karka sake ka shiga harkata,Ido ya tsura mata yace ni na Miki kama da ajinki? Salma ta juyo ta kalle shi tana yatsina tace Karka zo har dakina kace zaka fada min magana,dariyar yake Auta yayi yace Ina ya zama dakinki? Wa zai bawa irinki daki? Babu ni ba kai na fada maka Karka jawo Aljanuna su tashi na hada ma jini da majina, wani beran masallaci da Kai,Auta ya kalleta kawai wato tsabar lalacewa bera ne Kuma na masallaci ma.

Auta yace cikin fushi look at this dirty smelling local village girl, idiot ke Idan ban koma Santana naci ubanki ba shege nake useless girl yaja tsaki zai fice Salma tace Kai me nan wajen akuyarka ta kiyayi ramata wlh Nima tsagera ce Baso kawai nake wa biyayya,baki da aikin yi cewar Auta ya fice a fusace ya banko mata kofar kamar zai balla kofar, wani kallon banza ta bi kofar da shi ta ja tsaki ta mike tare da sawa kofar key tazo ta zauna ta baje kayan ciye ciyenta taci ta koshi,Alwala tayi da Sallah tana kallon dakinta a fili tace haduwa kuda a gefen gyambo Inama tare da Baso muke a nan wayyo Allah ta fada saman gadonta tana tunanin Basonta,Auta kuwa ya ja tsaki yafi goma yace Auta ka sa kudinka ka siyo problems da hannunka yace gobe Monday yana da lecture,Alwala yayi bayan yaci ya sha yayi Sallar Nafeela sannan yayi Shirin baccinsa cikin kayan bacci masu santsi Riga me dogon hannu sharara da ita da dogon wasu silver color,saman katon bed dinsa na alfarma ya haura ya jawo wayarsa ya hau Online,Nawwar yana kwance a jikin matarsa ni Rabiah muna danna waya dukkanmu muka ga Auta a Online yayi status ya rubuta Matata tafi ta kowa,Nawwar yayi dariya yace kaji Dan Iskan yaro a wajenka tafi ta kowa yo ta Isa ta fi miracle,nace never sai dai ta bi bayana,wani ya dora na biyu muka kunna muka ga yasa wasu suna chashewa an rubuta yanayi me Dadi,nace ba sabanba yau mun shiga uku,Nawwar magana yayi masa ta private yace Idan ana jin dadin a bar Online mana,Auta dariya yayi ya tura masa ya ranka mu babban Kai ne ba irinka ba an gama da Kai abu kadan sai ka rude mu kuwa sai an sha fama,Kai kuwa an wanke an baka ka shanye,Zanci ubanka wallahi cewar Nawwar sarkin masifa,Auta yayi voice yana cewa Yaya sai ya tsaya yace kashe light please sai Kuma yace sorry Yaya good night munyi can mu, waye yace kayi aure da wuri ka shanye dadinka kazo ka dameni ya kashe wayar gaba daya ya kwanta bacci abinsa..
Nawwar yana jin muryar Auta yace lallai yaron nan ya rainani yana magana da ni yana wani ce mata kashe light ya rainani na Daina wasa da shi,Nace chill man mene abin raini,dariya Nawwar yayi yace Allah Yan Makaranta abu kadan yanzu sai turanci nan gaba ma naga Alama Hausa Zaki daina,dariya nayi tare da makalewa a jikinsa,yace ga cikina yana ta girma Allah yasa a haifo min mace na fi son mace,Nace Ameen Allah ya bamu me albarka.

Washe gari da asuba Auta ya tashi mutumin da kullum sai an tasheshi ya tafi masallaci Sallar asuba indai Mami bata je ba bazai tashi ba sai rana ta fito yawanci yake Sallar safiya amma yau harda tashi da asuba,Light ya kunna yace to ya zanyi na zama Mijin wata Idan ban tashi ba ace banyi hankali ba,brush yayi da Alwala ya fito sanye cikin jallabiya harda rike carbi fari ya tako dakin Salma ya Murda handle kofar ta Bude ya Dan tura kofar a saman Sallaya ya isketa zaune yace cab duk sammakon ka wani a tafe ya kwana munafuka itama Dan tayi aure ne wai ita ta gari bayan mata da yawa basa Sallah akan lokaci wasu ma sai suce sai su gama ayyukansu suke hadawa,juyawa yayi ya rufo mata kofar tana jinsa domin a fili ya furta maganarsa tace Dan kawai Addua nake ne da na rama amma zamu hadu ne.
Yau Mami tana sa Ido ta Samanta ta leka part din Auta ta gani ko zai fito Sallah ko uban baccin nasa zaiyi sai kuwa ta Ganshi ya fito harda carbi da jallabiya,Baffa ta Kira tace zo kaga Auta me gida,window din ya karaso tare da rungume Mami ta baya suna kallon Auta suna dariya,Baffa sahu daya suka yi da Auta yau,sai da aka idar da Sallah ya tsaya harda azkhar sannan suna fitowa yace Baffa barka da asuba Ina kwana? Baffa yace sai kazo ma gaisa a hanya zaka gaishe ni,yace ni fa yau bazan zo ba bacci zan koma 12pm Kuma ina da lecture,au yau ma baza ka hakura da school ba kana Angon,yace me zan mata to shike nan sai na dinga zama,Baffa ya Kalli Auta yace Auta Anya kuwa kana son yarinyar nan duk mugun son aurenka,Ina sonta mana ya furta a ransa yana cewa karya nake bana sonta,sai da zasu rabu kowa zaiyi bangarensa yace ka gaida Mami,Baffa yayi dariya yace to zata ji ya tafi,Yana komawa bacci ya kwanta ya dinga bacci,Salma kuwa tuni ta koma bacci,sai 10am tashi tayi ta gyara gidan tace wallahi bazan gyara masa daki ba,wanka tayi taci kwalliya cikin leshinta na lefe brown and golden color tayi kyau,mayafi ta yafa ta fita taje part din Mami ta isketa a kitchen a kasa ta durkusa tace Ina kwana Mami,Mami taji Dadi taga hankalin Salma,ta amsa da fara'a,bayan nan ta fice tace zata je ta gaida Sauran tana mikewa Baffa ya fito cikin Shiri zai fita,ta sake zubewa a kasa guruf tace Ina Kwana ya amsa tace an tashi lafiya ya amsa da fara'a dama Baffa ya tsani gaisuwar zamanin nan da akeyi mussamman yaran yanzu ana ganin wayewa ce ko wacce Ina kwana wasu ma kafin ka amsa sunyi gaba Babu mutunci ba girmamawa Ina kwana kawai sai yarinya ta wuce ta barka nan,Baffa yace Honey zan fita,Salma kunya ta kamata a ranta tace bariki kan Uba tsofai tsofai a gabana cab wai honey,tana tsugune taga Mami ta rike hannayensa tana kwarara masa Addua,Salma tana satar kallon su ta mike sum sum ta fice kunya ta isheta ita Kam,part din wise ta shiga dauke da Sallama a bakinta Papa ya wani kwantar da Kansa a kirjin Wise suna Palo kuma,Baffa ganin surukarsa ce ashe ya tashi da sauri,Shima durkusawa tayi ta gaida shi ya amsa da fara'a ya tashi ya koma bedroom,tace Aunty Ina kwana? Wise tace ai ni kawarki ce yarinya tashi ta jawota saman kujera tace da Alama kalau kike wlh Auta ba abinda yayi gaskiya Ina Jira nazo gashi,Salma tana jin kunya tace sai kace wata

2 Comments On YAR AIKIN KARUWAI Book 2
avatar
zainab-ibrahim-8

11 months ago

Reply

Thank

avatar
ghh

10 months ago

Reply

Replying to zainab-ibrahim-8

Yayi kyau?

Please Login or Register in order to submit comment