Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

azo a dauki Hafsa a tafi da ita Masarauta.
Kayayyaki suka ga ana ta shigowa dasu, Lawan da fitowar sa kenan ya tsaya a jikin kayayyakin. Har baba suka gama tattaunawar su, su Ibrahim suka tafi masaukin su, su Mama kuma suka shige cikin gida, malam sule mai rini kuwa yayi alola dan lokacin har an kira sallan mangariba.

Lawan ne yasa aka kwashi kayan aka shigar dashi sabon gida, aka ajiye a dakin da nake kyautata zaton na mama Zainabu ne.

__________

Azima kuwa koda ta shiga gida sai ta rabza ihu, har da burburwa, ana ta tambayan ta meya paru sai can yace musu "Ba dazu kunji labari ya zagaye gari Yarima matar sa ta mutu an sa sake bashi wata har an daura aure ba? Nan kuwa suka gyada kansu, toh ba kowa bace amaryar face Hafsa, Hafsan gidan nan ma kuwa. Nan da na suka sake salati hassada ƙarara a fuskokin su, sai daga baya suka kwantar da hankulan su tunda ance matan nasa ma mutuwa suke yi, sai a lokacin zancen sabon gidan yazo kansu Kulu, su dai ko ajikin su, ko da wani abu ya samu Hafsa ai dai sun tsira da sabon gidan su.
Duk abubuwan da ake a kunnen Hafsa da take dakin su, wanda Jamila ce ta taimaka mata ta kaita dakin, ita kanta Jamila tayi mamakin wannan abu, sai bata ce komai ba, ta wuce take ta ɗan riqe mama suka je zaure wai baba yana neman su ita Hafsa ba wannan bane damuwan ta auren da aka mata shine babban damuwan ta, bata taɓa tunanin zata yi aure nan kusa ba, duk da Baba yace daman ze musu aure, amma a rasa waye mijin nata sai Yarima?
Inaaa gaskiya baza ta iya dauka ba, Yarima yafi karfin ta nesa ba kusa ba, da haka baccin wahala ya kwashe ta, Se bayan isha ta farka tayi Sallolin ta, a lokacin Jamila take bata labarin samun en uwan Mama, ji tayi ranta ya ɗan yi sanyi. Baccin wahala ne ya sake kwashe ta cike da saƙe saƙen halin da injiniya yake ciki, dan ta tabbata duk inda yake yanzu kam yaji labari.

_______
Da safiya tayi suka dunguma suka koma gidan siminti. Gida ne babban gaske mai matukar kyau, ko wacce mata saida ta samu daki da dakin shakatawa daidai gwargwado, se dakin sadiqu, sai ta waje sashen Malam Sule Mai Rini, Lawan ne dai yake tsohon gida. Zuwa sha biyu Mama ta aiki Jamila gidan su Habibah taje ta fadawa maman yadda ake ciki, sannan su taho da Habiban
Ba'a jima ba kuwa gida ya fara cika dan labari ya karade ko ina, wasu daman da biyu suka zo, dan suga sabon gida sannan dan suga ko dagaske ne zancen auren, ganin yanda ake shige da fice ne ya gaskata hasashen su
Wanka Habiba ta taimaka ma Hafsa tayi, suka bude jakunkunan da aka kawo jiya suka ga kayayyaki na alfarma da murjanai, nan aka shirya Hafsa aka sa mata alkyabba, da yamma ma yayi aka sake mata wanka ta saka wasu kayayyakin.
Shi kuma baba daman wannan jakan da aka taba kawo Hafsa dasu ya bude, yaga wasika akan cewar ga gida nan na Hafsa sannan ga sulalla, karafuna, kwabbai da sisina suyi amfani dashi, kamar yasan kuwa kudaden zasu musu amfani, dan dashi baba yayi ta hidima har yamma tayi aka zo aka ɗauki Hafsa aka saka a mota, aka tafi da ita

Fadrees 🖋️



>>>>>>>>>>>>>🖋️💻







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss Bello🖋️🖋️
Wattpad; fadrees_20


Page 29



Hakkin Mallaka nawa ne Ni Fatima Idriss Bello
Ban yadda a juyamin littafina ta ko wane irin tsiga ba, ko kuma ayı audio ba tare da izinina ba domin hakan ze iya janyo ma mutum matsala.
Dan haka a kiyaye.





Maman Habiba da uwargidan me anguwa da Lantana ne suka rakata a hakan sai da aka yi rigima da Mama Kulu dan tace itama sai taje, dakyar aka samu ta koma, sai kuma a yammata Habiba da Jamila ne suka je. Itama Jamilan seda ta nace kapın,  sai kuma yaya fati da yaya halime, suma suna kaita suna ganin sashen nata basu jima ba aka dawo dasu gida, tare da yi musu kyauta, ɗan nasihan nan ma da ake ma amare ita Hafsa an manta ba'a mata ba, dakyar kuwa aka raba Hafsa da Jamila, dan ƙanƙame ta tayi sosai, da suka dawo suka dinga bada labarin kyawun Masarautar, Dije harda kukan ta na bakin ciki, Azima ce dai ta danne nata.
Jamila da suka dawo ta wuce dakin maman su, ta dinga tausar ta, dan Mama Zainabu sai kuka take yi, ita tsoron ta bai wuce ace za'a kashe mata ƴa ba, ganin haka har seda maman Habiba tasa baki kan Mama Zainabu tayi shiru.
Da suka kwanta zasu yi bacci, Jamila ta dinga baiwa Mama labarin kyan sashen Yarima, da ma masarautar baki daya, duk da mama itama daga can tazo ai shekaru sun ja, daga baya Mama ta fara murmushi, amma ita tsoron ta daya, tana hakikanin tsoron GIDAN SARAUTA.

___________
A bangaren Hafsatu kuwa wani keken aka sake aiko wa ya dauke ta akai ta harabar sashen Sarauniya Babba, saidai wannan ba na doki bane, akan za'a musu karamar walima, a lokacin har anyi isha ma, tana zaman ta ita kadai wata baiwa ta shigo ta taimaka mata tayi wanka ta canza kaya kana ta fito da ita bayi mata sai take mata baya suke, shiga cikin keken tayi fadawa garada majiya karfi suka daga



Fadawa dauke da Hafsa a yayin da ake tafiya da ita haraban sashen Sarauniya Babba.

Mutane ne a wurin a cike, dukkanin su yan familyn sarauta ne, kowa yasha kayan alfarma, dukkan su dai mata ne, sai kuma masu yi musu hidima, a gefen kujeran Gimbiya Bilkisu kujerar Hafsa take, tana isa kuwa bayi suka kama ta aka ajiye ta aka fara walimar, kide kide kawai kake ji da bushe bushe, bayan anci ansha ne, Sarauniya Babba ta gama musu nasiha aka kaisu gun da Fulani take zaune ita da yan masarautar su suka mata gaisuwa, sannan aka kaisu gun da Kilishi itama take zaune, daga nan aka kaisu gun da mama Zulaiha take zaune itama da nata dangin, daga nan aka dauke amaren aka kaisu sashen mai martaba dan ya musu nasiha
Da suka shiga ba kowa a cikin daga Mai Martaba da kansa sai Baba Waziri.
Nasiha aka musu mai ratsa jiki, sannan aka sallame su, Mai Martaba sai kallon Hafsa yake, tuni yaji ta kwanta masa a rai.

Daukan ta aka sake yi a keken aka kaita sashen Yarima, itama Bilkisu aka dauke ta a nata aka kaita sashen Maigida Sulaiman.
Da isan su Hafsa bayin da ke mata hidima suka dauke ta suka shigo da ita cikin dakin shakatawar Yariman, da sai a yanzu ta kare masa kallo, an canza komai, an saka launuka daban daban, kayan ado da gyaran palon da aka yi amfani dasu da gani zaka san an ɓatar da sulalla, idonta ta sauke akan teburin takaddun sa, shima gun sai kyalli yake, shiga tayi cikin uwar dakan shi, taga shima an canza komai hatta gadon dake ciki an canza, komai da komai zubin sarauta, nan da nan hantar cikin ta ya kada, wannan uban ganima anya ba saida ta akayi ba? Ko dai itama mutuwar zata yi ne?, shiga makewayi tayi, tayi alwala tana kare ma makewayin kallo, shima pa an canza komai da komai.
Can dai da taji shiru bai shigo ba, tayi shimfidar ta a kasa ta kwanta, ita daman tasan sam ita ba tsaran auren sa bace, kila ma yana can rai a ɓace a aura masa baiwa, ko kuma yana can yana tunanin kalan azaban da zai dinga bata, ai nan da nan kuka ya suɓuce ma Hafsa, gashi jiya jiya taji labarin an samu en uwan Maman ta, Allah Sarki Allah ya sa mama ba kuka take yi ba, dan jiya bata yi bacci ba kwana tayi tana kuka, ko yaya injiniya yake ji? Shida yake shirin wai da Baba ya dawo yazo asa musu rana? Allah ya sa bai daga hankalin sa ba. Rayuwa kenan, dubi yadda rayuwar ta ta canza a kasa da shekara, ita idan aka ce mata za tayi aure a yanzu ma, musawa zata yi, amma yanzu da ta tashi auren wa ta aura? Ta auri Yariman gaba-daya garin Bauchi wanda ake sa ran shi zai zama Sarki a nan gaba, wai itace nan gaba zata zama matar babban Sarkin daya daga cikin manyan masarautun Kasarsu. Allah Sarki wa yaga Hafsa sarauniya, cap za'a ga hauka wallahi, motsin bude dakin taki, nan da nan ta matse idanun ta tayi likimo kamar tana bacci. Ta wutsiyar idon ta take hango shi yana kokarin cire rigar jikin shi, ai nan take ta damqe idanun nata da kyau kar tayi gamo. Tana gani ya shige makewayi bai jima ba ya fito, jikin sa sanye da ƴar shara da wando gajere, wayyoooo Allahnta ai a take ta sake damqe idanun nata, itakam meyesa take ta ganin abinda yafi karfin ta ne? Daga karshe harda sa hannun ta a wurin rupe idanun nata, Shi kuwa Yarima ganin haka ya saki murmushi, shi daman tun kallon farko da yayi mata ya gane cewar ba bacci take ba, bai tabbatar da hakan ba kuwa seda yaga ta sa hannu ta rupe idanun ta, gaskiya yarinyar nan akwai wauta, shidai zaiga ikon Allah, shi har yanzu bai san me zai ce game da wannan auren ba, gaskiya ba girman sa bane auren baiwa, toh amma ba wanda ma yasan da tayi aiki a Masarautar, sannan shine silan kawo ta, ƙila da be kawo ta ba baze santa ba, yanzu dai zeyi managing nata ko ba komai zata dinga ɗebe mishi kewa.

Gaban ta yaje ya tsaya, yace mata "ki tashi kizo kici abinci" Hafsa yi tayi kamar bata san me ake ciki ba, dan sai minsharin dole take ja, shiko da yaga haka sai yace "toh tunda haka ne, baza ki tashi ba, Ni bari na dauke ki na kai ki gurin abincin" shi da gatse ya fada amma Hafsa sam bata fahimta ba, sai gani yayi wai ta tashi kamar mai bacci sai miqa take tana goge idanun ta da hannun ta, wai da ta ware idanun nata sai tace "Mama waye a kaina? Ya nake ganin kamar suffan bujimi, bujimin ma me kama da wannan mummunan Yariman"
Murmushi ya saki a ransa lalle ma yarinyar nan ta raina sa sosai, wato dai shine mummunan, kuma shine bujimin, lalle kam. Well done.
Samun bakin shi yayi ya furta "fara kyakkyawar budurwa mai hankali da sanin Yakamata, Hafsatu Sule, Ni ne ma mummunan, baya da hakan na koma bujimi, toh Ni yanzu wanne kalan hukunci Yakamata in baki ne? Ya karashe da alamar tambaya yana mai kallon Hafsan, zubewa a kasa Hafsa tayi tana mai neman yafiya, domin in shi bai san menene dakin duhu ba, toh ita ta sani,
"Barka da warhaka Yarima mai jiran gado, Allah ya baka sarautar Bauchi" ta karashe da yin yaqe, wai sai yace mata "zaki so haka mana, ai idan ya bani kece sarauniya ta, shiyasa kika roqa" murkuda masa baki tayi, cikin rashin sa'a sai akan idanun sa.
Giran sa daya ya daga, nan da nan, yasa hannu daya ya dago ta gaba daya ta fada jikin sa hannun sa zagaye a ƙugun ta.
"Sake in gani?" Ta tsinkayi muryar shi
Amma sai Hafsa tayi shiru tare da sunnar da kanta kasa, bakin nata ya mutu
Jikin bango ya kaisu sa'annan ya sake tambayar ta
"Sake maimaita wa in gani?"
Jikin hamsatu ne ya kama rawa, can ya tsinkayi muryar ta tana cewa "Wallahi Ni bada kai nake ba, kuma kai ai kyakkyawa ne ba mummuna ba, nidai ka sake Ni inyi kwanciya na, na fasa sallan" ganin irin kusancin nasu yayi tsanani ne ya sata fadin haka, amma abinda ya mata next ya bata mamaki da tsoro da  kuma kunya.
Yarima ne ya haɗe bakinsa da nata yana mata abinda bata taɓa mafarkin sa ba.

Mu haɗe a na gaba.

Fadrees 🖋️.




30


Ƙafar ta kasa daukan ta yayi, jin irin wannan baƙon yanayin kamar zata fadi yayi saurin riqe ƙugun ta da kyau, shima ɗin hakan ne, dan bai taba tsammanin zai iya yin hakan ba, be san me ya jashi ba, amma dai yasan abu daya, ya kasa controlling kanshi ne, sai da ya gaji dan kansa, kapin ya kyale ta, labban ta nada matukar taushi da laushi, kamar kar ya cika, kuka yaji ta saka ya juyo da fuskan sa saitin nata, ya mata kallon ki cigaba in gani?. Shiru tayi dan dole tana me kuntumo masa launukan ashariya a cikin zuciyarta, ya sata tayo alola suka yi salla, daga nan suka ci abinci, daman Hafsa yunwa take ji, tun tana fulako har ta saki jiki sai diban abinci take, nama kuwa anga na bati ai sai ta Allah kuma
Suna gama ci suka je suka wanke bakin su, suna shigowa dakin Hafsa tayi miqa zata kwanta a kasa, yace mata ta kwanta a kan gadon shi ba bacci zeyi ba, juya wa tayi ta kalli kan gadon, sai yanzu suka ga farin kyallen da aka shimfida musu akan ruwan tokan zanin gadon, dafe kai Yarima yayi cike da takaici, ita kuma Hafsa ganin ya bata dama, yasa take ta cire farin kyallen, toh ita daman ba sanin amfanin shi tayi ba, nan tayi kwanciyar ta, ta juya ma Yarima baya, idan kuma ta tuno da abinda ya faru ba da jimawan nan ba, sai taji kamar ta nitse dan kunya, ikon Allah, wai yau ita da Yarima🤭 sai kuma tayi shiru, kan ta ankara bacci yayi awon gaba da ita sai aikin birgima da take saki.

Shi kuma Yarima tunani yake tayi, yana so ya kamo bakin zaren da ya sa wadanda ze aura suke mutuwa, zama yayi akan gadon yayi tagumi, can dai ya yanke shawarar zeyi maganan da Sulaiman, juyawarsa keda wuya yaga Hafsa tayi miqa zanin ta ya taho cinya, fara ƙare ma fararen cinyoyin ta kallo yayi, daga bisani ya saka hannu ya ja mata zanin ya rupe mata, kashe fitilan dakin yayi kapın ya kwanta ata daya gefen, shima da tunanin abinda ya auku dazu bacci ya dauke shi dan gaskiya yau yaji kunya, baiwar sa ta samu daman raina shi, domin ta kalli gurin baccin sa.
Yau ne a rayuwarsa ya taba kwanciya da mace a gefen sa, sede wannan ba kwanciyan dadi bane domin Hafsa kafa ta dinga ɗora masa daga karshe ma, akan sa tayi masauki, yana jin ta ya kyale ta, daga nan kuma bacci mai nauyi ya dauke sa, har saida ya makara sallan asuba,
______________

Injiniya ne a kwance a dakin sa, yana ta faman zubar da hawaye, yana matukar san Hafsa, so ma na hakika, amma gashi yanzu ƙaddara ta raba su, ko da mahaifiyar sa ta masa maganar Abinda yake damun sa, sai bai boye mata ba, ya fada mata hakikanin gaskiyar abun, nan ta dinga lallashin sa, daga karshe dai izini ya nemo a gurin mahaifinsa kan zai koma ƙasar Mali yaje ya sake bunƙasa karatunsa na injiniyanci, ko da mahaifinsa ya amince, da sassafe yayi sammako yabar Bauchi, kunji inda ta injiniya ta kare masa.
______________
Kilishi ce durqushe a gaban Boka Kapoor, dariya mai kama da kukan zaki ya saka, yace mata "abinda yake ranki muma bamu gani a allon sihirin mu ba, da baza mu bari ayi auren nan ba face saida gawan ta, gashi sharadin abin namu, kapın aure za'a ke kashe matan, yanzu kuwa da aka samu akayi auren, zamu samo mafita, domin muma faduwar mu ne ba ke kadai ba, saboda jinin sarakai dadi garesa, yanzu muna hada wata magani da zai dauki watanni kapın a gama hada shi saboda hadarin sa, sai an samu ruwan maliya kapın haduwar maganin ta kammala, domin sai aljani mai shekara dari ne kadai zai iya debo ruwan sbd haka da an gama za'a baki ki sa mata a ruwa, daga nan zata yi sallama da rayuwar ta, shi kuma za'a maida shi mara karfin iko, domin za'a kwace masa matsayin sa na Yarima Mai jiran gado. Ɗan waziri kuma za'a saka masa cuta da zata yi sanadiyar shi, amma sai na ita yarinyar ya kammala kapın.
Da jin haka tasan boka ya gama maganan sa, sbd haka ta dawo tana saƙa da warwara.
Zata aika baiwar ta, tana sa mata ido akan matar da Yarima ya aura. (Har yanzu su Kilishi basu san cewar wacce Yarima ya aura baiwar can bace, wato Hafsa.)
______________
Sulaiman kuwa ko da yaje ya samu amaryar sa ta jima dayin bacci ga nan farin kyallen da aka shimfida musu ko yaye shi bata yi ba akai ta kwanta abinta, sai shi kuma bai tada ta ba, shi Wallahi mamaki ma yake, idan aka ce masa zai yi aure nan kusa wlh musawa zai yi, sannan ma a rasa wa za'a hada shi auren sai Bilkisu kanwar bayansa, ai wlh shikam tashi ta gama karewa dan raini kam ta gama raina shi. Allah Sarki, gata yarinya kyakkyawa kuma tana da hankali despite cewar ita yar sarki ce bata wulakanta bayi, In Sha Allah alkawari ya dauka kan zai kula da ita. Miqewa yayi yaje gefen ta ya kwanta, tare da dora kanta a saman kirjin sa, sa'annan ya kashe musu fitilan dakin.
______________

Yarima ne bai farka ba saida yaga haske ya fara fitowa, da farko da ya tashi yaji an riqe shi sosai, har ba ya iya motsawa yayi yayi ya kwaci kanshi ya kasa, dan wuyan shi aka rungumo sosai da sosai, wanda har hakan ya fara basa wahalan numfashi, mamaki ne ya kama shi dan shi shaff ya manta wai an masa aure jiya, sai da ya ware idanun sa da kyau ne ya ga ashe Hafsa ne ta shaqe se, dakyar dai ya samu ya kwaci kansa yayo alola sannan ya tada ta, saida tayi ta sumbatu sannan ya samu ta tashi, wannan dai da wahala kawai aka hada shi, tana shiga makewayi ya tada kabbara, can se gata ta fito ta fara sallan ta, da ta gama ta gaida shi se da yayi kusan minti Uku kapın ya amsa, ganin yana ji da sarautar sa ne, Hafsa ta tashi ta haɗa masa ruwan wanka, da yayi ita ya sata ta shirya shi, sai kanne kanta zuwa kasa take tayi, gama shirin shi kenan itama ta shige taje tayi wankan, Seda ta gama ya nema abinda zata daure jikin ta ta rasa, gashi Allah ya gani baza ta iya maimaita kayan da ta cire ba, dan lekowa kadan tayi, sai kuwa suka hada ido, gira daya ya daga mata alamar tambaya, sai tace masa dan Allah ya miqo mata kayanta, shi kuma a ransa cewa yayi lalle yarinyar nan taga gurin baccin sa, wato shine ma zai miqa mata abinda take so, ranshi a dan bace ya miqo mata hijabin sannan yace mata kayanta suna dayan dakin, yana fada mata haka ya miqe yayi gurin kofa, har zai fita ya canza shawara, ya tsaya daga jikin kofan ya harde hannayensa, ganin haka da yayi ranta sai ya ɓaci, tun farko yasan akwai wani daki shine bazai fada mata ba?
Fitowa tayi tana jinta a tsarge dan hijabin da ta sa ji take kamar yana bayyana suran jikin ta, tana fitowa sai tayi hanyan kofan dan taje dayan dakin ta sanya kayanta, tazo wucewa ya tare, sai tabi ta gefen sa ta tafi dayan dakin, duk tana jinta sukuku, tana shiga tayi hanyar durowan kayayyakin cikin dakin, ilai kuwa, nan taci karo da kaya masu yawan da har saida ya bata mamaki, in za'a hada kayan ta na gida dana Dije da Azima da Jamila duk baza su kai wannan yawa ba, ciro wani doguwar riga tayi dan ta sa, Yariman da bata san da shigowar sa ba ya riqe.
"Ni zan sa Miki tunda Nima ke kika sa min" ta tsinci muryar sa, karkarwa ta fara yi kapın tace "Ni bana so ai kai kace in sa maka, sannan ba'a san raina na sa makam ba, saboda haka Ni bana so" ta karashe tana mugun hade rai dan haushin shi take ji, shidai bai sake ce mata komai ba sai kokarin yaye hijabin jikin ta yake, ihu zata sa masa ya rufe bakin ta da nasa, nan ya fara aika mata da wasu irin zafafan abubuwan da bata taba sani ba, hannunsa taji yana yawo a jikin ta, sai kokarin kwace wa take amma ta kasa, sallaman da suka ji an doka ne, ya tsayar da Yarima daga abinda yake shirin aikatawa, fita yayi yana me saita kanshi, sai yaga ashe jakadiya ce, duqawa tayi ta basa gaisuwa kapın ta fada abinda yake bakin ta, wanda lokacin yayi daidai da fitowar Hafsa
"Allah ya ja da ran Yarima, Kilishi ce ta aiko Ni akan in tafi da farin kyallen za'a je a nunawa sarauniya babba".





31



Kasa furta komai Yarima yayi, ita kuwa jakadiyar ta sake maimaita masa abinda ya kawo ta
Yanzu shi cewa zai yi babu abinda ya faru tsakanin sa da Hafsa? Kai ba girman sa bane hakan, toh idan ta tafi zuwa zata yi tace ai Hafsa ba budurwa bace, yana dai ta sake sake a ransa can ya samu amsar da zai bata
"Wane kyalle kike magana"?
"Farin kyallen da Kilishi tasa aka shimfida a saman gadon ka jiya Allah ya baka nasara"
Ce mata yayi shifa baiga kyalle ba in kuma za taje ta duba da kanta ne, ganin haka sai tayi mamaki, kuma bata isa tace zata je ta duba ba, sai yanzu ta lura da Hafsa, kare mata kallo ta fara yi, itako Hafsa ta galla mata harara har seda ta ɗan tsorata.
Ficewa tayi taje sashen Kilishi ta fada mata abinda ya faru, hakan da ta faɗa ya bata ran Kilishi, nan da nan tasa ta akan aje a sake shirya wani farin kyallen akan yau ma a sake shimfida musu ficewa jakadiyar tayi ita kuma, har alla alla take ace amaryar Yariman nan, ba budurwa bace, Wallahi sai ta sa zaman masarautan nan ya gagare ta, sannan zata sanya ido sosai a kanta.

Sallama aka mata daga waje, baiwar ta taje ta bude kofan, wani dogari ya shigo har kasa ya durqusa ya kwashi gaisuwa, ido ta ma bayin ta da duk su fice su bata guri nan da nan kuwa suka fice kapın kiftawa da bismillah.
Magana bafaden ya fara cike da tabbatarwa;
"Ranki ya dade, Mahaifin ta da bafade ne aka kore sa bisa ga abinda yayi wa yar shamakin wancan lokacin(nan ya bayyana mata komai hadda ƙara gishiri), sannan mahaifiyar ta ma tayi bauta anan din daga bisani ya aure ta ya dauke ta dan ita annoba ce(nan ya sake zayyano dalili), ita kuma yarinyar ita ce baiwar da aka sallame ta akan Yarima, Yarima Hayatu da kuma Yariman Gobir. Sannan nayi bincike akan yarinyar, sam bata da tarbiyya gata fitsararriyar gaske ce wacce ta addabi kowa a unguwar su, wannan auren da aka mata shine samun zaman lafiyan yan unguwan nasu iya abinda na samo kenan", nan da nan Kilishi ta dauko tsantsar azurfa ta basa yana godiya da jin dadi ya fice.
Tayi masa kyauta da azurfan nan ne dan ba'a taba kawo mata labarin da ya burge ta irin na yau ba, ta so ta sa a zane sa saboda ya saka Hayatun ta a cikin shirmen sa, amma sai ta kyale sa sbd wannan daddaɗan labarin da ya kawo mata, idan ta lura da kyau wato ta jefi tsuntsaye dayawa ne da dutse daya tak.
Nan ta saki wani mummunan murmushi, ta lumshe idanun ta cikin salama.
Baiwar da ta jima tana nema Allah ya kawo ta cikin sauki, sannan ta tausaya ma Fulani domin surukannin ta gabaki dayansu bayi ne. Wannan information din da ta samu ya isa tayi amfani da shi ta hana Hafsa zaman lafiya a cikin wannan masarautar.
Tuno irin makircin da zata yiwa Hafsa gobe yasa ta sakin wata bahaguwar ajiyar zucciya.

______________

Hafsa ne ta tsinci kanta da fadin, "Kyallen me take magana ranka ya dade, kodai wancan farin kyallen da na naɗe ne jiya, meyesa zaka yi karya bayan kyallen yana a cikin dakin

Please Login or Register in order to submit comment