Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Borno dakyar ta saba da rashin Hafsa, rashi na har abada, sede Jamila da Suwaiba suna ɗebe mata kewa musamman in taga suwaiba se taga kamar Hafsan ta ce, kamannin ta daya da Hafsan ta, halayyar su ne ya bambanta.
Koda suka shiga sashen sarauniya babba suka miqa gaisuwa, daga idon ta sarauniya babba tayi tana kallon Suwaiba, zuciyarta a take ta tsinke, maida hankalin ta kan su Mama Maryamu tayi, su Jamila kuwa jiyo sautin yara suka yi, nan da nan suka yi cikin dakin kuwa, hango yara ƙanana suka yi sai tafiya suke, suyi ɗaɗɗaya su fadi, haka dai suke tayi, shafa'atu dake kula dasu sai murmushi take, ganin suwaiban da tayi seda taja da baya, se daga baya ta fahimci ba Hafsan bace, gaida su tayi tayi waje, karasawa dakin Suwaiba tayi Jamila biye da ita, Areef da Areefa na ganin ta suka yi wajen ta suka ruqunqume ta, Jamila se dariya take musu, tana san ta dauki Areef yaqi zuwa gun ta, basu san da shigowan mutum ba, kawai ganin sa suka yi a kansu yasha mur fuskar nan kamar hadari, juyowan da zeyi yayi arba da ita, nan da nan ƙafar sa ta kama rawa


ALƘALAMİN FADREES 🖋️ 🖋️ Ƴar Mutan Yobe.




54



YARIMAN HAFSA
(A Royal Love Story)
Mallakar Fatima Idriss Bello



Arewabooks; Fadrees20
Wattpad; Fadrees_20
Phone No. 0902058802


Haƙƙin Mallaka nawa ne Ni Fatima Idriss Bello, ban yadda wani ko wata suyi amfani da wani sashe na littafi na ba, ko a haɗa min audio ba tare da kwakkwaran amincewa ta ba, idan naga akasin haka kuma wlh baza mu wanye lapiya ba dan haka a kiyaye.
Idan number na kake nema ɗaga idon ka sama zaka ganshi a rubuce



FLASHBACK

Hmm kunsan meye rayuwar da babu masoyin asali? Tohhh ku tambayi Yarima, tunda yaga an rufe ta da ƙasa rayuwar sa ta koma somehow, abu ɗaya ne yasa be bita ba, alƙawarin da ya ɗauka na cewar ze kula da yaransu, dan jinyar da yayi da kyar ya tashi, wannan shine dalilin karfin sa na rayuwa, alkawari yayi ze kula da ya'yan su ta yanda koda yabar duniya ne yasan Hafsa zata yi alfahari dashi, kullum da tunanin ta yake kwana yake tashi, sashen sa ya dade da kaura daga ciki, domin duk sanda ya saka kafar sa ita yake tunawa, ganin haka yasa aka rufe sashen da katoton kwaɗo, har an bashi wani sashe yace baya so, karshen ta anan sashen sarauniya babba ya dawo da zama, dama kowane sashe akwai dakuna a ƙalla biyar, toh yanzu dakinsa na yanzu a jikin na ƴaƴansu shida Hafsa yake, duk wani abinda ze dinga tunawa da ita ya dakko su ya kawo su nan, wasiqun ta da take turo masa kafin suyi aure da kuma waɗanda bayan sunyi aure su yake karantawa ya samu bacci, in kaga yana farin ciki toh yana gun ƴaƴansu ne ko kuma yaje kabarin ta ya zauna yana mata addu'o'i, ganin yawan zuwan sa makabarta ne ya saka me martaba bada dokar kar a sake barin shi ya shiga koda yaje shi.
Daga nan ne aka samu salama, ya ɗan fara dawowa hayyacin sa, sannan yakan samu yaje fada ma, Sulaiman dai sai kokari dashi yake yana ce masa ya rungumi ƙaddara, akwai ranan da har Salman ɗan sarkin Gombe yazo masa taaziyya suka tisa sa a gaba, shidai kawai kallon su yake, dan basu san me ake cewa rashin masoyi bane shiyasa.

PRESENT

Wannan shekara gudan da ya tafi, ya tafi ne kamar ýan kwanaki a gun wasu, sede shi ji yake kamar shekaru dari ɗaya yayi cikin ƙunci, dawowarsa kenan daga fada ya wuce sashen sarauniya babba da yanzu ya zama sashen su, koda ya shigo se yaga da baƙi dan haka se yabi ta kofar baya, dakin yaransa ya fara zuwa, dan ka'idar sa ne da ya dawo daga ko ina dakin nasu yake fara ma tsinke, in ya shiga baya sanin lokaci ma dan in har ya samu yayan sa sun dinga wasa kenan, anan ne zaka ga farin cikin shi, yanzun ma hakan ce ta kasance yana saka kanshi a cikin dakin ya hango bayan wasu yammata a cikin dakin, bayan dayar kamar na Hafsan shi, zuciyar shi Seda ta tsinke da yaji yanayin dariyan ta, koda ta juyo kuwa da yayi arba da fuskar ta, Seda ƙafafun sa suka soma rawa saboda firgici, ko kallon Jamila dake gaida shi beyi ba, tsaya wa yayi yana mata kallon tsanaki, wallahi billahi da badan wannan tawadan Allahn da yake gefen hancin ta ba da ze iya cewa itace, domin suna kama sosai, yanayin hancin su, idonsu duk da alamu ya nuna kaman na wannan ya ɗan fi girma, se kuma yanayin labban su, murmushi yaji tayi kana ta gaida shi, kasa amsawa yayi saboda Kamar Hafsan shi ce, sake lura da wani abun yayi a tattare da wannan da Hafsan shi bata dashi, wato lotsewar kumatu, hafsan shi tana da dimples wannan bata dashi, se kuma Hafsah ai ta ɗan fi wannan jiki amma ba wani sosai ba, bama zaka gane ba se an fada maka, amma bayan haka, yanayin tsayin su kala daya, Jamila ce ta sake gaida shi a karo na uku kana ya amsa yana me maida hankalin sa kanta, murmushi ya sakar mata kafin ya amsa
Budan bakin Jamila se tace
"Yaya Suwaiba ganan yaya Yarima mijin yaya Hafsa, ai kuwa durqusawa suwaiba tayi ta gaida shi ya amsa a daƙile, gurin yaransa ya karasa da niyan ya dauke su, sede me? Yara sam sunƙi zuwa gunshi, mamaki kamar ya kashe Yarima, kyale su yayi, ya fice zuwa dakinsa, sarauniya babba ce ta aika shafa'atu akan ta kira sa yazo ya gaida maman Hafsa, fitowa yayi yaje dakin shakatawar, se ya rasa waye ma Mama Zainabun, musamman da yaga duka suna masa murmushi iri ɗaya, da badan Hafsa ta taɓa karanta musu wani wasiqa da Jamila ta taɓa aiko mata ba har take ce masa maman ta yan biyu ne da yanzu inaga ya tsorata saboda firgici, gaida su duka yayi besan wace maman ba sannan suma basu ce ga maman nata ba, miqewa yayi ya koma dakin sa, se chan dare da ya fito yaje wai ya duba ko su Areefa sunyi bacci ya musu addu'a, se be gansu ba, dakin Sarauniya Babba yaje yana tambayan ta yaran nasa, take ce masa sunbi su Jamila, shi dai mamaki hakan yake basa, yaran suna da bala'in kwiwa inhar bashi ko sarauniya babba ko shafa'atu ba basa yadda da kowa
Yazo fita a ɗakin nasa sarauniya babba tace ya zauna zasu tattauna muhimmin abu
Zama yayi yana me sauraren ta
"Yarima ya kamata kayi wa kanka fada ka sama wa kanka da ma yaran ka mafita, nasan tunanin da kake yi, kana so kace baza ka iya yin aure ka zauna da kowacce mace ba bayan Hafsa, sede an kai gaɓar da mutane sun fara magana, kasan ko wane lokaci mahaifin ka ze iya yin murabus, domin a ɗora ka, kuma kasan ƙa'idar masarautar nan sarki baya zama da mata daýa, ko mutum yaso ko yaqi kuwa, doka ne dole ka bishi, saboda haka tun wuri ka nemo mata a muku aure kaga ka taimaki yaran ka ka nema musu wanda ze kula dasu, ko kuma ka bani dama Ni in nema maka "
Be wani yi ja'in ja ba dan yasan dama ko ba jima ko ba dade za'a tada maganar nan sede be ɗauka za'a masa maganan da wuri haka ba, domin sarki da mata hudu aka san sa ko mahaifin sa da yake da biyu yana da kwarkwarori ne, saboda basa haihuwa ne yasa ba'a taba saka su a lissafi ba, yanzu de ze bata daman ta sama masa wacca zata kula masa da ya'yan sa, amma yanzu yayi wuri gaskiya, sannan ku ya aure ta babu wata macen da ta isa ta maye masa gurbin ta har abada domin;
   İtace mahadin rayuwarsa
         Bashi da tamkar ta
                Yana san ta har gaban abada.
Cema sarauniya babba yayi ta nema masa koma waye kawai da haka yayi mata sallama yayi komawar sa daki yayi kwanciyar sa cike da tunanin Hafsa.

___________________

Koda Galadima yaga su suwaiba sun shigo da yara se ya tambaye su ko sune ya'yan Hafsan aka ce masa eh, gani yayi sun makalewa Suwaiba abun har ya basa tsoro dan da ya gwada karban Areef a hannun ta kuka ya saka se kyale shi yayi.
Koda Mama Maryamu ta same sa da maganar ko sunyi magana da Mai Martaba yace mata a'a se gobe in Allah ya kaimu, daga haka ta wuce dakin su, ta barsa zeje sashen dasu Talba suke.

Koda safiya tayi bayan an karya, yara dai suka sake makalewa su hudun nan, ko mayar dasu sashen sarauniya babba ba ayi ba kuma basu yi daru ba, hana rantsuwa da suka ji yunwa sun danyi kuka amma koda aka hada musu madara mama Maryamu ta basu basu sake damun kowa ba.

Galadima ne can zuwa azahar ya kira Mama Zenabu da Mama Maryamu akan yana so su tattauna muhimmiyar magana, zuwa suka yi suka same sa kana yace
"Mun yi magana da me Martaba akan jama'ar masarauta suna ta magana akan Yakamata Yarima yayi aure, shi kuma yana ganin kamar yayi kusa yaushe ma matar sa ta rasu, sede mutane sunƙi saurara har an cewa Falaqi da ya bada yar sa a Yarima, shi kuma na lura Falaqin kamar baya san hakan, saboda haka na yanke shawarar basa suwaiba, ita kuma Jamila na bata Abubakar, yanzu zamu tafi da yaran da sunyi shekara uku za'a dawo dasu se ayi bikin Yariman da Suwaiba in yaso sai ta dawo tare da yaran ta tare baki daya, yanzu dai an yanke shawarar nan da shekara biyu auren, amma nace masa se nayi shawara daku, idan kuna ganin hakan beyi ba zaku iya fadar ra'ayin ku musamman ke Maimunatu Kinga na hada auren Jamila da Abubakar bansan ko kina da wani ra'ayin ki ba"
Ce masa suka yi komai yayi daidai babu komai nan suka watse.

AFTER SEVEN YEARS.


FADREES 🖋️.





55 (ƘARSHE)



YARIMAN HAFSA
(A Royal Love Story)
Mallakar Fatima Idriss Bello



Arewabooks; Fadrees20
Wattpad; Fadrees_20
Phone No. 0902058802


Haƙƙin Mallaka nawa ne Ni Fatima Idriss Bello, ban yadda wani ko wata suyi amfani da wani sashe na littafi na ba, ko a haɗa min audio ba tare da kwakkwaran amincewa ta ba, idan naga akasin haka kuma wlh baza mu wanye lapiya ba dan haka a kiyaye.
Idan number na kake nema ɗaga idon ka sama zaka ganshi a rubuce




AFTER SEVEN YEARS

Abubuwa da dama sun faru a cikin shekarun nan, na dadi da ma akasin haka.
Bari mu fara waiwaya wa gidan su Hafsa. Har a lokacin rayuwar jindadi ƴan gidan suke domin rayuwa daman cigaba yake da zaran wadanda aka rasa sun jima da barin duniyar, Yaya Lawan shi ya dauki ragamar kula da su baki ɗayan su da taimakon Yarima, su Azima da Dije sunyi aure shekaru shidda baya, da yaransu uku uku suna zaman jindadi da kuma girmamawa da mazajen su, dan su yaya fati fada suka musu me kyau kan a kaisu gidajensu, Su kansu Yaya Fati da Yaya Halime zaman lafiya suke a gidajensu, Yaya Lawan yanzu shine ya maye gurbin Malam Sule me Rini, ya rabu da matar san nan mara kunya ya auri wata suna zaman su bisa salama sannan ya sa kannen sa Garzali da Adamu sun dawo ƙasar Bauchi da zama dan sunyi aure ma da duk iyalansu a cikin gidan, yanzu sadiqu ne kaɗai matashi ɗan shekara ashirin a gidan, shima kuma ba zaman banza yake ba sana'a yake yi sosai kuma Allah ya ɗaukaka sa, sannan harda shi ake taimakon kula da lamuran su Mama Lantana da kuma Mama Kulu a gidan.

İdan muka dawo bangaren ƙawayen Hafsa kuma, suma duk sunyi auren su, Murja ta auri ɗan me unguwar su yaranta biyu mace da namiji suna zaman jindadi, macen takwara ta yiwa Hafsa, haka zalika Zaliha ma tayi aure sede tana da kishiyoyi ita, amma suna zaman lafiya, Habiba kuwa yaranta uku, tayi ma Hafsa takwara itama, sannan zaman lafiya suke yi ita da magidanta da ya zama Mai Unguwa bayan mutuwar mahaifin sa shekaru biyu baya.
Dukkanin sun nan, Yarima yana yi musu alheri albarkacin Hafsan sa da yake maqukar so da bege.

_________________

A ɓangaren ƴan Kanem Borno kuwa, Jamila tayi aure shekaru biyar baya, ta auri Yaya Abubakar ɗan gidan Galadima wanda auren su ya kasance rana ɗaya dana Suwaiba da Yarima, kuma yanzu haka yaranta biyu, Maimunatu da Hafizu (sunan Galadima), sannan sashen su suma a cikin masarautar yake, a gefen na Mai girma Galadiman.
Mama Zenabu kuwa shekaru huɗu baya aka daura aurenta da Mai Martaba Mai Borno, a babban masallacin fadar garin Borno, inda ta aifi ƴan tagwaye mace da namiji masu shekaru uku uku, ana ce musu Hafsa da Bukar (sunan babansu, ita da Mama Maryamu, tsohon Wazirin Borno)

_______________

A cikin masarautar Bauchi kuwa, zan iya cewa lapiya da akasinta, a gun su Fulani da su sarauniya babba lapiya take, gun Yarima kuwa sam sam ba haka bane, kullum da ita yake kwana da ita yake tashi, duk da cewar yanzu shekarun sa biyar da aure da kuma me tsananin kama da ita, sede abun ba haka yake ba, duk da wannan tana masa kamanceceniya sosai da sahibarsa sede ba itan bace, domin in ka cire kammanin su da yanayin ƙirar su, sam sam zaka gane su mutane ne mabanbanta halayya.
(Fadrees)🤍
Kasancewar Hafsan sa mafaɗaciya ce da kuma surutu, wannan saliha ce dan magana ma bata dame ta ba, sannan akwai sarauta a jikin ta sosai kasancewar ta ɗiyar sarakai sannan tana da bala'in hakuri, Ehh hakuri mana wacce mace ce zata yi aure mijin ta ya kasance gangar jikin sa kawai ta aura? Sannan kuma bata taɓa complain ba tunda dai yana bata kulawa yadda ya dace wadanda suka rataya akan sa, bayan haka kuma akwai wani abinda take burge sa da shi, tana kula musu da yaransu shida Hafsa, sannan suma yaran suna matuqar santa sosai dan su a zaton su itace mahaifiyar su ma kuma har yanzu basu sani ba, ze bari se sanda taga daman fada musu ta fada musun, ko sanda suka tafi Borno a gunta suke sannan tana jin dadin kasancewa dasu, duk da bata yi rayuwa da Hafsa ba tana santa sosai, shiyasa ma tayi Wannan shahadar, sannan tana enjoying zaman ta a masarautar nan dan kowa yana santa a masarautar, tana shiri da Bilkisu sosai, dan kusan kullum zaka gansu tare, ita Bilkisun ji take kamar Allah ne ya dawo musu da Hafsa, sannan tunda ta haifi yarinyar tan nan da ya maida wa suna Hafsa yake ganin ƙimarta, tana respecting iyayen shi hakan yana burge shi, inama inama
Inama da Hafsan shi ce, miƙewa yayi tsulum ya wuce dakin Hafsa da tunda aka rufe bayan bakwai dinta be sake budewa ba, yau kimanin shekaru ɗai ɗai har bakwai kenan.

Ɗakin yayi ƙura sosai ga gidajen gizo gizo ko ta ina, gashi lokacin dare ne ba daman ya sanya a gyara masa dakin, amma kuma a haka ya kutsa kansa ciki, tsaya wa yayi yana me qarewa dakin kallo, yana tuna sanda ya biyo ta lokacin tayi zuciya tsabar dakin sa yazo ya same ta a daidai inda yake tsaye, tafiya ya fara yi a hankali ya karasa gun drowar kayan ta ya buɗe, take yayi arba da wani hijabin ta da ta taɓa sawa lokacin bata da kaya a dakin sa, farkon auren su da ita kenan, murmushi ya saki kapın ya kai hijabin hancin sa ya kama shinshinawa, tabbas itace, haka kamshin jikin ta yake, Hafsar sa ce wlh, rungume wa yayi a jikin sa tsam, can kuma ya buɗe akwatin ta, kayayyakin ta ya gani, ya so ya kyautar dasu kuma yaga in ya barsu za suna tuna masa da ita, kayan ya fara ɗagawa daya bayan daya, can ya hango wasiƙu dayawa a ajiye a ƙasan

Daukan ɗaya yayi ya bude se yaga Poem ne ta rubuta masa kamar haka


RABUWA

Babu abinda ya kai kalmar nan ta 'Rabuwa' zafi,
A lokacin rabuwa.....,
Za kana tuna lokacin da kuka yi cikin jin dadi a baya,
Domin....,
Lokacin da kuka yi a cikin jin dadi a bayan,
Za kayi tunanin baka da kishiya kamar kalmar nan ta 'rabuwa',
Amma yanzu da rabuwar tazo ta,
Se ka rungume ta da hannu bibbiyu,
Domin....,
Babu kalma, ko hawaye, kai koma meye da ya isa ya gyara ta,
Haƙiƙanin Gaskiya....,
Wata rabuwar itace zata yi silan samun farin cikin ka a cikin rayuwar ka na baƙin ciki.

Hawaye ne ya kwaranyo masa daga idanun sa, gaskiya ne abinda ta rubuta, sede shi kuma rabuwar sa da ita be sama masa farin cikin komai ba sema ƙuncin da yake ciki, sede kuma wani sa'in yana ɗan jin nau'in farin ciki in ya tuna da yaran su, wani lokaci ya tuna sanda suka hadu a gidan gonan Sulaiman lokacin da aka sallame ta daga Masarauta, murmusawa yayi tuna lokacin cizon shi tayi, tace masa ta rama abinda yasa su barau suka mata ne, sake tuna wani lokacin da suke yin ɓadda kama suje cikin gari yayi, in sunje gun saida abinci cewa yake baze ci abincin waje ba, ita kuma ta dinga basa a bakin sa mutane su yi ta sha'awar su.
Tuna wani lokaci yayi sanda suka je lambun cikin masarauta suka zauna ya kawo mata furanni, sai murmushi take yi a lokacin, ashe dai zata barshi ne, murmushin mata na lokaci ƙalilan ne.


Miƙewa yayi ya hau kan gadon ta yana me share yanan da yake daidai inda ze zaunan, daga yau ya yanke hukuncin anan ze dinga komai nasa
Be damu da ƙuran dake cikin dakin ba yayi hayewarsa kan gadon nata, yana me shaqan kamshin hijabin ta da ya dakko, wasikun da ya kwaso ya buɗe ya fara karantawa, wasu har dariya yake inya karanta, dan har haqoran sa suna bayyana, wani wasiqan ta ya gani, a ƙarashen ta rubuta, 'DAGA FARA KYAKKYAWAR BUDURWA MAI HANKALI DA SANIN YAKAMATA'. Dariya yayi anan da ya tuna asalin yanda ta fara amfani da wannan jimlar, lokacin farkon wasiqar da suka fara musanya ne a tsakanin su.
(Fadrees)🤍
Wasikar ta ta ƙarshe seda ya zubar da ƙwalla, dan kamar Poem ne ta rubuta masa, sannan Poem din ya tuna masa wani lokaci da suke kallon wata da taurari a tare, sake karantawa yayi.


MASOYA DUNIYAR WATA
"Idan na daga kai na na kalli sama
Ina iya hango taurari masu matukar haske a sararin samaniyan....,
Hasken su ka iya sa mutum ya manta da kansa,
Sannan ya ɓata a cikin tunanin sa,
Ko kuma ya ji shi cikin begen dan uwansa.
Haƙiƙanin Gaskiya....,
Hasken su mai matukar daukar ido ne,

Na sake daga kai na a karo na biyu na hango hasken wata kuma....,
Sai naga hasken wata yafi taurarin haske,
Domin....,
Hasken wata ka iya saka rai cikin aminci, zuciya kuma cikin salama
Daga nan se na yanke hukuncin,
Ina nan tare da kai a duniyar wata
Domin....,
Duniyar wata itace duniyar Masoya,
Sannan itace duniya me cike da dimbin haske".

Da murmushi akan fuskarsa a lokaci guda kuma zubar hawaye ya rufe idanunsa, yana me tuna lokacin da ta kira sa da watan ta, shi kuma ya ƙira ta da tauraruwar sa, bacci na me masa wata makauniyar runguma cike da tunanin Hafsa da kuma ranar da shima zeje ya iske ta, se kuma tunanin yaransu, da kuma Suwaiba da Hafsa ƙarama.
(THE END)



ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH !! ALHAMDULILLAH!!!.

Nagode Allah da ya bani daman fara littafin nan me suna 'YARIMAN HAFSAA' cikin ƙoshin lafiya da kuma kammalawa cikin ƙoshin lafiya, Abinda na rubuta daidai ina fatan za'a yi amfani dashi, kuskuren da yake ciki kuma ina neman gafara gurin Allah
Ina yiwa dukkannin masoya na godiya na bibiyar wannan littafin nawa me albarka da suka yi, duk da a karshen littafin ran wasu beyi dadi ba amma dai an jajirce an cigaba a hakan.

Ina me jiran ku a sabon littafina na biyu me suna *TSANI* wanda ya kasance littafin kuɗi ne, domin wannan ba kalan wancan bane, And please it's a happy ending Book.
Thank you.🤍


ALƘALAMIN FADREES🖋️🖋️🖋️ Ƴar Mutan Yobe.



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment