Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba
Sanadiyar koran Malam Sule me rini a Fada kuma shine, shi ya kasance mutum ne mai san aiki da kula ga hakuri, hakan yasa ya zama babban dogari, abin ka da mahassada sai akai mai sharri wai an gansa da yar Shamaki wai zaiyi lalata da ita, aka kira yarinya tazo ta fada gaskiyar zance, Yarinya kuwa harda barbada gishiri akan zancen shine Sarkin Fada ya basa sallamarsa.
____________

Daga ƙarshe Hafsa shigewarta ɗaki tayı, da tagama dariyanta ta canza kaya.
Jamila ce ta shigo tana gimtse nata dariyan
"Allah Allah nake dare yayi mu fita gaaɗan nan zanga ko Ashiru zaizo hira" Hafsa ce ta faɗa hakan tare da pashewa da sabon dariya
Aiko suka jiyo muryan Mama Lantana tana balbala masifa
Har mangariba tayi Lantana tana abu ɗaya wato masifa
Suna cin abincin dare kowa ya shirya suka tafi Dandali

Acan filin gaɗa Hafsa ta hango Taron maza tsabar jaraba ta tasamma gurin haiƙan tana zuwa tace "a'a manyan samari ina tauraron naku?" Ta ƙarashe tana dariyan mugunta
"Yana gidan ubanki"
Wani daga cikin su mai suna Talle ne ya bata amsa
Bantan Ubancan ubana pa ka xaga ?
Ta ƙara tambayar sa,
dama yan unguwansu sun san halin Talle da neman faɗa Hafsan ma ba baya ba ga kuma rashin kunya
Aiko suka fara zage zage
Atake hankalin kowa ya dawo kansu
Talle ko sai zıga shi ake
Suna shirin fara dambe Su Yaya Lawan da suka zo wucewa ta gun ganin abinda ke faruwa suka zo suka raba (ikon Allah mace da dambe da namiji)
Nan aka watse, kowa sai faɗan albarkacin bakinsa yake
Suka koma gida

Bayan wasu kwanaki da misalin tara da ƴan mintina na dare bayan sun dawo daga gaada Malam Sule mai rini ya tara su babba da ƙarami suka taru
" Dalilin tara ku da nai anan shine akwai wani abokina daya ke zuwa gari gari sana'a toh yace mun zan bishi mu tafi tare saboda haka nake so ku zauna lapiya, kuma sana'ata ta rini tana nan domin Lawan ne zai cigaba dayin shi yabar zaman banza, aƙalla zan iya yin wata kafin na dawo saboda haka dan Allah ku riƙe sana'ar ku kuma (yafaɗa yana nuna su Lantana), nabar abincin da zai ishe ku har na wata hudu, sannan ku kuma Azıma ku ringa zuwa makaranta kun ga dama kun kawo ƙarshe da kun gama sai in muku aure ke da Hafsa da Dije Allah ya muku albarka za ku iya tafiya"
Yaran ne suka mike aka bar iyayen mata suna shawara da Malam Sule
Su Kulu kuwa banda harara babu abinda suke aikawa Mama Zenabu.
Bayan da ya gama musu nasiha
Suka mishi addu'a albarkacin bakinsu suka watse.
Da sassafe Malam Sule yai sammako suka tafi
___
Haka rayuwar ta ci gaba da tafiya musu
Watarana su Hafsa sun tashi a makaranta suka hango wani kamar Malam Sidi a lungu shi da wata yarinya.

Habibah ƙawar Hafsa itace tace bari ta leƙa taga waye ne
Leƙawan da zatayi sai ga Malam Sidi da Zaliha a cikin lungun hannun Malam Sidi na hagu bisa kafadar Zalihan na daman kuwa yana shirin antaya shi cikin gyauton ta. Ganin su Hafsa akan su a take suka yi wiki wiki da idanu saboda sun san asirin su ya tonu
Me su Hafsa zasuyi banda shewa ai a take ta sheƙa da gudu ta koma makarantar Domin lokacin shugaban makarantar bai tafi gida ba, daman ta tsani Malam Sidi ta dade tana neman hanyan da zata rama dukan da ya mata ta rasa sannan haushin Zaliha take ji na sosai da sosai
Tana zuwa tace 'Malam Habu kazo kaga abinda ke faruwa'
Malam Habu yabi bayan ta suka je suna zuwa sai ga Malam Sidi yana neman hanyar guduwa cikin sa ya birkice
Zaliha kuma kuka ta saka a gurin
"Ku muje Ofishina"
Abinda yace kafin ya juya zuwa ofishin nashi
Su Hafsa kuwa tafiya gida sukayi kowa na tofa albarkacin bakinsa, ita Hafsa harda rankwashin Malam Sidi aikuwa Seda ya saki karan azaba, Zaliha kuma zunguri takai mata a goshi
"Na mutu na lalace"
Zaliha ne ke ta faɗin haka har suka ida shiga cikin ofishin Shugaban makarantar, wanda ransa a mugun haɗe bisa ga wannan mummunan abun da ya faru.

Masarautar Bauchi
________

Ban yadda wani yayi amfani da wani sashe na littafin nan nawa ba, ba tare da amincewa na ba, domin zan dauki tsattsauran mataki akan hakan, dan haka a kiyaye.

Idan littafin nan kake nema, complete ko wani sashe toh ga nan numbern waya na a sama duk me san yayi min magana, ya min ta nan.

Da fatan an fahimta.
Nagode.



>>>>>>>>>>>>>💻🖋️🤍







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss🖋️🖋️
09020588802
Wattpad; fadrees_20



Page 4


"Na mutu na lalace"
Zaliha ne ke ta faɗin haka har suka ƙarasa shiga ofishin Malam Habun
"Kiyi min bayanin ME KE FARUWA tsakanin ki da Malam Sidi"
Malam Habu ne ya daka mata tsawa
"Wallahi Malam shine shine...."
Shine meye Mallam Habu ya ƙara daka mata tsawa
'Shine kullum yake cewa zai bani kudi mu haɗu a lungun da ka gammu'
Salati Malam Habu ya sake yana mai tafa hannayensa tsabar taƙaici
'Abunda dama kake yi kenan Malam Sidi?
Toh daga yau ka tattara naka ya naka na kore ka daga makarantar nan, ke kuma na dakatar dake daga zuwa har sai na neme ki'

Ai a take Mallam Sidi ya rikice ya fara sumbatu har da faɗin wai karya take amma a banza
Su Hafsa da suka koma gida sai nanata abun suke.
Sai bayan mako biyu Mallam Habu ya aika akan Zaliha ta dawo

Tafiyar Mallam Sule mai rini ya ƙara sa ma yaran gidan tabarbarewa a maimakon su nutsu.
Bayan watanni biyu su Hafsa suka kammala sakandare lokacin Malam Sule mai rini ya zo gida anan ne yace su kawo mazajen aure duba da yayyensu da suka riga da sukayi nasu auren harda 'ya'ya
Hafsa rashin kunyar ta yayi tsananin da bata iya saurayi, sai Azıma ce da ta rabu da Ashiru akan bashi da sana'ar yi ne ta haɗu da wani kuma wai Saminu sai Dije da bata da tsayayyen arziki sai shegen ruwan ido, qazantar gidan su kuma sai abinda ya ƙaru.
Wannan kenan

________
"Hafsa kizo kije gidan su ƙawarki Habiba ki karɓo min saƙo a wurin Maman ta"
Inji Mama
"Haba Mama wai Ni kullum ake aika ba ga Jamila ba" tafada tana ƙunkuni
Ita dai Mama Zainabu bata kara cewa komi ba se ma fitan da tayi daga dakin tana fadin
"Saura kuma ki dade"
Tazo fita daga zauren nasu ta haɗu da Sadiqu ai kuwa sai da ta dunde shi kafin ta wuce

Fitar ta be jima ba ta haɗu da Zaliha suka fara cacar baki daga nan suka kaure da dambe da kyar aka zo aka raba su
Daman yamma ne kuma kusan mangariba bata tafi aiken ba, sai a sannan ta kama hanya taje gidan su Habiban domin har angama Sallan mangariba, Sun ɗan taɓa hira kafin ta karbi sakon ta fito Habibah ma hijabi ta ɗakko zata rakata, sun fito lokacin har Dare yayi, sun fara tafiya suka hango dandazon mutane an hana kowa wucewa
"Uban waye ya hana mutane wucewa"?
Sai a sannan ne tasan fadin wannan jimlar yasa ta tafka babban kuskure, kuskuren da yake hade da ƙaddarar rayuwar ta
Ashe Yarima ne yazo wucewa da fadawansa gefensu kaɗan kuma wasu mata ne guda uku da maza biyu dukkanin su daga alamu babu mai aure a cikinsu
Wani bafade ne ya hankado ta ya fara lafta mata wani gabjejiyar bulala
"Ku haɗa da ita"
Abinda Yariman yace kenan kafin aka hankada Hafsa cikin wadannan na gefen da ta gani da farko
Habiba kuma zuciyarta ba abinda yake sai bugawa
Dogarawanne suka hankada su suka fara tafiya sai a lokacin tsoro ya tsarga cikin zuciyar Hafsa amma being the Hafsat she is, se bata nuna hakan ba.
Sun dan yi tafiya me nisan gaske kafin su ka iso wani garin
Garin da aka masa lakabi da Masarautar Bauchi

____________
Wai ya Haryanzu Hafsa bata dawo bane" Mama Zenabu ne ke sake sake a ranta
Wasa wasa mangariba tayi suka ga shiru ai hankalin mama bai ƙara tashi ba sai da taga an ƙira isha'i amman shiru, nan hankalin ta ya tashi suka fita ita da su Azıma da su Lawan gidan kuma yayi tsit kowa na jiran yaga ikon Allah, gidan su Habiba suka wuce suka ga suma hankalin su a tashe yake na ganin har yanzu shiru ba Habiba ba labarin ta daga rakiya.

Fita sukayi su ka bi sawun su tare da yan gidan su Habiban sun san daman ba lalle subi ta hanyar da Hafsan ta biyo da farko ba sbd normally haka suke idan aka aiki dayan su gidan dayan se subi ta dogon hanya dan su sami lokaci suna hira.Sun ɗan yi tafiya mai nisa kapin suka hango jama'a daga nesa,
Nan take suka karasa wurin, suna zuwa sukaga Habiba ne a durkushe a gurin tana kuka kamar wanda ake zare mata rai ga mutane an zagaye ta ana bata hakuri
"Na shiga uku na lalace shikenan sun tafi da ita"
Abinda take ta fada kenan ai a take suka sandare a wurin
"Waye?" Lawan yayi karfin halin tambaya
"Hafsa", Yarima Idriss ne yasa fadawa suka tafi da ita?
Ta ƙarashe maganar tana kuka ai nan take Mama Zenabu ta faɗi sumammiya a gurin aka ciccibeta aka ɗaura ta akan amalanken da aka dakko daga gidan su Habiban sai gida.
Ana shigo da ita su Mama Lantana suka sha jinin jikinsu, su Jamila kam ba'a fadan irin tashin hankalin da suka shiga
Wannan kenan

____________

MASARAUTAR BAUCHİ

Masarauta ne wanda yake da ginin siminti irin riqaqqun ginin nan na daa dan akwai jita jitan cewa ma harda mutane aka gine katangin da irin bayin da aka ciyo su a zamanin da, da ake yaƙi.
Babbar Masarauta ce, idan nace babba ina nufin babban gaske, dan girman sa ze kai girman wani garin.
Masarautar ya ƙayatu ta fannoni dabam dabam wanda idan nace zan misalta shi xan bata lokaci ne.
Akwai sashe sashe daban daban bila adadin, wani sashen zaka ga na Sarki ne, wani na Waziri, wani na su Garkuwa, su Galadima su Falaƙi, mabudi, ciroma da dai sauransu, sannan suma da sashen yaran su a cikin sashinan nasu.
Hatta gidan bayi akwai na wadanda suke da aure kuma suke aiki a cikin Masarautar, akwai sashen bayi wanda bayi marasa aure ko marasa yan uwa suke ciki, akwai barga babban gaske sannan akwai inda ake ajje keken dokuna a ko wane sashe na Masarautar in ka cire na bayi se kuma inda ake ajiye motar da Maimartaba ya siya.

Bayi, Kuyangu, Fadawa da dogarai ne ke ta zirya kowa yana yin abinda yake gaban sa
Da na shiga cikin masarautar a nan ne nagane cewa ba ƙaramar gari guda bace wannan masarautar



Wannan shi ne hoton masarautar Bauchi

Wata budurwa na hango tana tafiya cike da ƙasaita kamar baza ta taka ƙasa ba bayi na take mata baya
Daga nesa naso nagane fuskar ta sai Dana ƙara matsowa ne na gane ta sosai.
Wannan wanda Lawan yabada labarin tane, yar Waziri ce wanda ta hukunta su Ashiru
Wani ƙaton gida a cikin masarautar dama naga ta fito kuma yanzu naga tana nufan wanda yafi nasu komai da komai tsarin haɗuwa.
Kutsa kai tayi cikin gidan tana mai dakatawa itada da bayinta
Da gudu ɗaya daga cikin bayin ta ta nufa cikin ɗakin shakatawan ( zamu iya alaƙanta ɗakin da parlour kamar yanda mutanen yanzu suke cewa) dan neman mata iso.
An baki izinin shiga ranki shi daɗe
Baiwar ta da ta aika ne ta dawo ta fada mata sakon mai mallakin bangaren.

Shigar ta cikin tapkeken dakin shakatawan keda wuya naga ta zube ƙasa tana faman kwasan gaisuwa
Wata Hadaddiyar mata na kalla wanda a ƙalla ba zata wuce shekaru Arba'in da biyar ba ta ɗago kanta ta sauke idanunta akan wannan budurwa tana mai murmusawa

"An gaishe ki Samira" wata dattijiyar mata a cikin bayin matar ta fada mats
Wani banzan kallon da wacce aka kira da Samiran ta mata ne yasa ta gane ashe tayi kuskure ba'a kiran ta Samira kai tsaye sai an hada da Gimbiya ( niko nace ji ƙarfin hali, babanki yana wazirin🤔).
"Ku bamu waje" inji matar
Nan take kowa ya watse da ɗai ɗai da ɗai ɗai
Dan Allah Umma ki taimaka kisa Yarima Idriss ya aure ni wallahi ina masa son da bazan iya misalta miki ba dan Allah Umma.
Dariyan manya tayi kan tace
"Baki da damuwa Samira indai Idriss ne kamar kin samu" ta ƙarashe maganar tare da jefa fresh tuffa a bakinta, kasancewar fruits ne kusan kala goma a cikin kwandan da ta dauka tuffan a ciki. Sarauniya Kilishi kenan mata ta biyu a gurin Mai martaba Sarki Alhaji Sulaimanu bin İdrissa

__________
Shigar su cikin masarautar ba'a wuce dasu ko ina ba sai wani ɗakin duhu sai da aka ci uban su da duka tukunna aka kyale su ko abincin dare ba'a ba su ba a cewar fadawan lokacin cin abincin dare ya wuce
Kwanciya tayi akan simintin dakin duhun sanyi na ratsa ta ga wani uban yunwa da yake damun ta ga uban sauro
Alokacin ne ta tabbatar wa kanta wannan dare shine daren ƙaddarar ta daren da a dalilin shi tasha wahala kuma a dalilin sa ta san cewa rashin kunya baida fa'ida kuma shine daren da yasa ta zubda hawaye kuma daren da yasa tayi dana sanin abinda tayi da farko
Da bata fada wannan jimlar ba da yanzu tana cikin yan uwanta duk da basa wani shiri
Da bata fada wannan jimlar ba da yanzu tana cikin gidan ubanta kuma akan gadon mahaifiyarta amma daman Hausawa sun ce 'baki shi ke yanka wuya'.
Hakika wannan dare shine KUNDIN ƘADDARAR ta.




>>>>>>>>>>>>>💻🖋️🤍







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss🖋️🖋️
09020588802
Wattpad; fadrees_20


Page 5


A amalanke aka ɗauki Mama Zenabu aka kaita gida, Jamila kuwa ba abinda take sai kuka.

Suman mama Zenabu har biyu tana farfaɗo wa, daman ance uba da ɗa sai Allah, duba da yadda Hafsa ta cika rashin ji amma da shike ba tanan sai da yan gidan suka ji ajikin su, Bama wannan bane matsalar a'a ko Baba ya dawo bashi da ikon da zai ja da yan sarauta, kai ko fadawa ne bai isa ba ballantana ɗan Sarki, ɗan sarkin ma me jiran gado.
WAYE SHİ ai bai isa bama,
Da haka da suka ga ba sarki sai Allah kuma har kusan sati Uku abu shiru yasa suka dangana, suke addu'a kuma suna jiran dawowan Baban su ji yadda za'a yi.

___________
Fitar Samira keda wuya Sarauniya Kilishi ta kwashe da dariya sai da tayi me isarta, kana ta tafa hannun ta sai ga bayin sun dawo kowa ya kama aikin gaban sa
A zuciyarta kuwa caa take " gwara ki aure san inyaso na haɗa dake, inci Ubanku tare akan abin da mahaifin ki waziri yaimin".
Ɗaga hannun ta tayi sama alamar su bata ɗaya daga cikin kayan itatuwan da take ci
Aiko nan take wannan tsohuwar baiwar ta mika mata inibi hannun ta na ƙyarma
Amsa tayi ta jefa a baki tana taunawa tare da yin wani mummunan murmushi
Kilishi kenan

Fitan Samira sashen Fulani ta wuce gurin Bilkisu.
________

"Shamsu kana ɓata mun lokaci pa"
Hayatu ya pada yana sake haɗe rai
"Yi hakuri dan Allah nakusa fitowa"
Inji Shamsu yana dariya
Aiko sai gashi nan ya fito da shigansa na sarauta shi da Hayatun duk shiga iri ɗaya ce a jikin su
"Muje"
Nan suka kama tafiya, da ka gansu za kaga zahirin Kamar da suke da junansu, kamar sun da har ta ɓaci.
"Gaba salamun baya salamun
Yayan sarki jikokin sarki "duk inda suka taka za kaga ana ta musu ƙirari
Tafiya suke cikin ƙasaita dogarai na biye da su har suka ƙara sa sashen dan uwansu wanda shekaru biyu ne kadai tsakaninsu kasancewar Yarima Idriss ɗin ne babba.

Da shigar su sashen suka sami Sulaiman a zaune yana bubbude wani littafi yana dubawa
"Gafara dai Wazirin gobe"
Muryar shamsu ce ta ƙarade dakin
"A'a sannun ku da zuwa yan tangwaye"
İnji Suleiman ɗin
"Shekara biyu naga ka bamu da kake wani cewa "'ƴan'" 
Hayatun ya faɗa yana mai yatsina fuskar sa.
Ehhh ko minti biyu na baku ai na girme ku bare har shekara biyu'
Suleiman din ya fadi yana ɗaga girar sa ɗaya
Dariya suka saka gaba dayan su
"Wai ina İdi ne yana ɓata mana lokaci pa"
Shamsu ya faɗi
"Sau nawa zance maka bana son sunan nan meye wani 'Idi' 😏?.
Idriss ɗin ya fadi yana fitowa daga uwar ɗaka ransa a hade
Kwashe wa gaba ɗayan su suka yi da dariya
" Muje"
Suka haɗa baki a tare nan suka ƙara pashewa da dariyan banda Idriss

Shi Idriss indai yan uwansa ne yana son su shiyasa ma watarana sukan biyo musu shida Suleiman su tafi pada tare, saboda basu dauko halin uwarsu Kilishi bah.
Nan suka mike suka fara tafiya duk inda suka saka ƙafarsu sai kaga an durkusa ana kwasan gaisuwa ko kuma ana musu ƙirari
Su Suleiman ne ma masu ɗaga hannun su alamun sun amsa amma Yarima Idriss kam ko a kwalar rigan sa.

Sun ɗan yi tafiya sannan suka isa fada
Sai da aka sanar da Sarki isowar su tukun ya bada izinin su shigo

Shigar su suka zube a ƙasa suna kwasan gaisuwa a gurin Me martaba da Waziri.
Bayan kowa yayi shiru ne Waziri yake sake tunatar dasu gasan hawan da za'a yi a ƙarshen wata na Dhulhajji wanda ya kasance al'adar masarautar ne kowane karshen shekara suna gayyatar masarautu da dama, kuma suma wasu masarautun zasu iya gayyatar su domin yin gasa kala kala

"Yakamata ku zage dantse dukan ninku domin manyan masarautu tara muka gayyata kuma ko wane sarki zaizo ne da ɗansa da kuma mutanensa saboda haka nake jaddada muku da kar ku bamu kunya"
'Zaku iya tafiya'
Muryar waziri ne ta dakatar dasu daga tunanin da suka fada

Nan suka fito Shamsu da Hayatu suka bi hanyar su, suma Idriss da Suleiman suka bi nasu hanyan suna tafiya suna tattaunawa kan yanda abun zai kasance

Sun ɗan yi tafiya kadan sai ga wani bawa nan yazo ya durkusa a gaban su
"Me gida Suleiman Mama Zulaiha ke neman ka"
Bawan ya fada yana nan a durkushe a gun
"Muje ka rakani Idi Mama ke nema na" inji Suleiman ɗin yana kallon Yariman.
"A'a karka damu akwai inda zani nima" Yariman ya bashi amsa
Sai Suleiman ɗin ya wuce ya koma Gidan su shikuma Yarima ya fice a masarautar baki daya shi da wasu fadawa suna take mishi baya
Sallahn magrib da isha ma a waje yayi
Da shike a kan doki yake sannan fuskan shi a nannade ba lalle ka gane fuskar shi ba, sai suka bi ta wani Unguwa, shi daman abinda yake fitar da shi a wannan lokacin shine idan ya gamu da  bata gari kama su yake sa ayi akai su fada a hora su

Muryan wani yaji yana fadawa abokin sa da suke hira tare cewar 'kaga wadancan maza biyun da yan mata ukun kaf unguwan nan babu wanda ya kai su rashin mutunci musamman mazan sukam nasu sai a hankali dan har kisa nake jin za su iyaa dan... '
Yarima be kaiga jin karashen zancen ba ya je shi daf da wadanda ake maganan nasu ilai kuwa yaga zahiri domin daya daga cikin su sai zage zage yake sauran kuma sai hure masa kai suke
Shine yama fadawan alamun su kama su.
Kama su keda wuya mutane suka fara cika wajen duk wanda yazo yaga waye ne se yaja bakin sa yayi shiru
Can zasu juya yaji wata murya me cike da tsiwa da fitsara tace
" Uban waye ya hana mutane wucewa"?
A lokacin sai ranshi ya baci
Yana juyawa yaga har wani bafade ya fara mazgar ta
Jin muryar shi kawai yayi yace
" Ku hada da ita"
Aiko nan take bafaden ya wurga ta cikin sauran lokacin gurin har ya fara cika, kowa ya shiga matsanancin tashin hankali da tsoro
Nan yasa aka hankado keyar su sai cikin Masarautar Bauchi
Wannan kenan
___________

'Zuuut' 'Zuuut' 'Zuuut'
Ƙara da zuugi da zafin wata arniyar dorina mai baki Ashirin da biyar ne ya farkar da ita daga baccin wahalan da ya same ta ga uban sanyi, ga sauro ga wani uban yunwan da yake damun ta kamar ana kwashe mata kayan cikin ta
ZZuuut'
Ta ƙyara wata uban ƙara, ai bata san sanda ta mike tsaye a gigice ba tana kallon wani wagajejen bafade wanda girman sa ya kai girman Wargaji.
A firgice ta tsaya kallon sa, jikin ta babu abinda yake sai rawa, ga wani uban hajijiya da ya fara kama ta tsabar yunwa dan rabon ta da abinci tun jiya da rana
"Ku biyo baya na"
Wannan mummunan bafaden da ya jibge su ya faɗa
Ai nan take suka fara binshi a baya sai yanzu ma ta lura da yan dakin duhun kasancewar cikin dakin a kwai duhu bata lura da su ba sai yanzu
Mata ne sunkai goma kuma duk zasu girme ta sai wata yarinya ce a cikin su da sai kallon ta take, yarinyar za tayi sa'ar ta
Bata lura da yarinyar ta karaso kusa da ita ba sai da taji ta tace 'sannunki'
Yauwa" kawai ta faɗa
Nan suka ci gaba da bin bayan fadawan daga sun ɗan tsaya sai a zuga musu BULALA
Zungura ƙeyar su akayi sai sashen bayi
Ɗakuna ne zasu yi guda ɗari biyu ko ma fiye da hakan
Kuma ko wane ɗaki mutum huɗu yake dauka
A bakin wani ɗaki bafaden ya tsaya yace mutum biyu su shiga
Nan take yarinyar dake bin Hafsah tayi wuff ta janyo hannun Hafsan suka shiga cikin dakin sauran kuma suka yi gaba
Shigan su cikin ɗakin suka kalli wasu yammatan sai dai waɗan nan za suyi shekaru ashirin ashirin

Kwano Hafsa ta hango ai batasan sanda tayi wufff tayi kan kwanon ba ɗayar yarinyar ma jona ta tayi suka kafa kai sai jibgan wata dankararriyar tuwo suke yi yan dakin kuma ido suka zuba musu. Sai da suka gama suka fara sauke numfashi
Sai yanzu ma suka lura da yanayin dakin
Dakin yana da filin sa kuma a siminte yake
Ko wannensu da katifarsa. Katifarda  da ita da babu uwarsu ɗaya ubansu ɗaya
Yarinyar da suka shigo tare ne tace "sunana Murja"
Tun farkon saka ki a ido na naji kin kwanta mun rai sannun ki
Ke meye sunan ki?
"Hafsa"
Hafsa ta bata amsa
Sai yanzu ta lura da yarinyar sosai, tana da tsayi amma ba can can ba kuma bata da haske sosai
"Kema sannun ki "
'daga yau mun zama ƙawaye babu yaudara, babu cin amana.'
Murjan ta fada tana saka hannun ta cikin na Hafsa
Murmushi kawai Hafsan ta mata itama ta rike hannun Murjan sosai
"Toh ƴan ƙannen mu mu baza a tambaye mu sunayen mu bane bayan an gama cinye mana abinci?
Wata daga cikin ƴar ɗakin su biyun ta tambaya.
"Wayyoo kuyi hakuri gaba daya hankalin mu baya kan ku ne ga yunwa ayi mana afuwa "
Murjan ta bata amsa
"Ayyah babu damuwa sunana Shafa'atu ƙawata kuma Lantana"
Ta fada tana nuna ɗayar
"Yauwa yanzu tunda an kawo ku ɗakin ku ku yi sauri ku fita ku karbo kayan bayi kapın wadannan yahudawan masu jibga jibgan jikin suzo su jibge ku"
Ai nan take Murja ta mike tsaye sukayi hanyar waje tare da Hafsa




>>>>>>>>>>>>>💻🖋️🤍






🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss🖋️🖋️
09020588802
Wattpad; fadrees_20


Page 6



fitar su keda wuya suka haɗu da wani dogari suka tambaye shi ya musu kwatancen gurin

Gurin Sai ka fita daga sashen bayin ka ɗan yi tafiya kadan kafin ka kalla wani tafkeken guri, a cikin gurin akwai manya manyan dakuna (halls) sosai.
A kofar shiga suka haɗu da dogarai a tsatsaye suka tambaya tukun aka nuna musu hanyar da zasu shiga daya daga cikin halls din
Shigar su suka kalli kaya ne a jibge bila adadin
Karasawa suka yi suka bi layin har yazo kansu, sun tafka babbar Sa'a da aka basu kaya iri ɗaya wanda hakan ke nuna wuri ɗaya zasu yi aikin
Shudiyar zani ne da riga da dankwali kala huɗu huɗu da hijabai guda bibbiyu
Suna amsar kayan suka kama hanyar shiga sashen bayin kai tsaye dakin su suka wuce suka samu su Shafa'atu sun yi cirko cirko a tsaye kamar jiran shigowar su suke
'Jakadiyar Sarki yanzun nan ta zo bakwa nan zakuyi bayani ...'
Ai Lantana bata kaiga gama maganar taba aka bankado kofar Jakadiyar ce dai da dogarai guda biyu ai kafin su san me yake faruwa saukar dorina suka ji

Sai da suka jibge su iya san ransu har numfashi suke sauke wa tsabar mugunta kafin Jakadiyar Sarki ta ɗaga hannun ta alamar ya isa hakanan
'Na hukunta ku ne saboda kunje kunyi zaman ku,

Please Login or Register in order to submit comment