Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutuwar sa wlh da besan wane kalan fansa ze iya dauka akan rashin shamsu ba, sannan ashe ita ke kashewa Yarima mata?, meye ma na sake tambayar kansa bayan ta fadi hakan da bakin ta jiya, amma babu komai, daga yau har illah Masha Allah baze sake bijire ma maganar shamsu ba, duk wani manufofin sa ya ajje a gefe domin wanda yake yi domin ita bama ta da lapiya, daga haka ya zauna yayi ta kuka har hawayen sa suka dena zuba idanun sa suka yi jazir.
Bayan kwana uku yaje ya samu Mai Martaban da shima sbd mamaki seda yayi jinya, ce masa yayi yana so yabar kasar gobe gobe ze tafi kasar Sudan yayi yi karatu, Mai Martaba bai ja da hakan ba yasa a shirya tafiyar nashi, dan ƙila hakan ne ze kawo masa sauƙin radadin da yake ji na rashin ɗan uwan nasa da tunda suke a rayuwar basu taba nesa da juna koda na kwana ɗaya bane, sannan barin shi kasar Bauchi shi zai saisaita masa irin kallon da ake masa bisa ga abinda mahaifiyar sa tayi.

________________
Flashback

Kwanaki biyar baya.

Zan iya cewa a kwanaki biyar ɗinnan komai ma ya lafa na garin, Hayatu ya bar kasar Bauchi ba'a san ranan dawowan ba, a ɓangaren Hafsa kuwa, duk yadda akayi da Hafsa ta haihu abin yaci tura, a ranan da aka kashe kafoor da Kilishi a ranan Hafsa ta miqe kamar ba mara lafiya ba, ta cigaba da rayuwar ta dai gashi nan gashi nan, sannan iya tsawon wannan lokacin Yarima baya barin ta ta matsa koda nan da nan ne daga gefen sa, ganin haka ne yasa Mama Zenabu da Jamila komawa gida, su Mama Kulu har an samu bakin zagin Mama wai taje cin arziki Gashi dai karshen ta an koro ta, ita dai bata kula su ba, dan tasan haushin har yanzu ya'yan su basu samu mazaje suke ba. Jamila kuma daman ba'a bi ta kanta dan makarantar ta take zuwa.

PRESENT

Tun daren jiya Hafsa ta tashi da nakuda, fara naqudar ta ya faranta ma mutane dayawa rai dan har Allah Allah ake ta haife abun cikin ta ko kowa ma zai huta, itama kuma ta huta, haba, wata goma har da dan ɗoriya?
Abinda basu sani ba, kowa a duniyar nan da kalar ƙaddarar sa, ashe Hafsa jurewa kawai take yi dan ciwon da take ji a kirjin ta ya zarce wa tunanin me tunani, zafin da take ji yanzu har yafi lokacin da take kan jin ciwon abun, kawai bata nunawa ne saboda kar ta tada hankalin Yarima da ma mamanta da kuma sauran mutanen da suka damu da ita, Sede yau da safe ji take kamar baza ta iya jurewa ba, burburwa ta kama yi, Allah yaso ta da bayi a kanta daman Yarima in zai fita ko nan da nan ne se ya tabbatar da mutum a kanta, baiwar dake zaune a gefenta tana mata massage din kafarta ne taga abinda take, nan take tayi waje da gudu taje ta kira Zuwai ma'aikaciyar jinya, Zuwai tana zuwa da taga yanayin Hafsa sai ta firgita tayi waje da gudu, bata ma san sanda ta isa fada ta antaya ciki ba, lokacin ana zaune ana fadanci sannan ana sallamar Malam na bakin rafi akan ze koma Yobe dan majinyata suna jiran sa, shigowar Zuwai a firgice ne ya tsayar da gabatarwar da ake a cikin fadan, gaban Yarima taje ta zube tana me cewa
"Allah ya baka nasara, Hafsa ce, Hafsa ce......."
Ta ma kasa ƙarasa abinda zata fada ɗin,
Miqewa yayi da hanzari Malam na bakin kogi yabi bayansu shida Sulaiman, suna karasowa suka ga har ta suma, ruwa malam na bakin rafi yace a miqo masa, Zuwai ce ta basa ya karba yayi ƴan tofe tofe kana ya watsa mata, farfaɗowa tayi can tana me sakin ajiyar zuciya, nan da nan ta fara kuka tana burburwa, Malam ne ya baiwa Yarima ruwan yace ya bata tasha, karba yayi ya bata, tana gama sha ta fara ihu tana fisge fisge can kuma ta fara naquda, ganin haka Malam da Sulaiman da shi kanshi Yariman suka yi waje aka bar Zuwai da wasu ungozoma da aka kira daga dakin magani suka zo.

Malam na bakin rafi ne yace da Yarima
"Yarinyar nan an cuce rayuwarta saboda abinda aka dasa mata mutum baya wuce awa ashirin da hudu yake mutuwa, Sede ita gashi har ta ƙara mako huɗu ma, wanda hakan kamar ishara ya zamo ga Kilishi da bokanta har ma wadanda suke zuwa gurin bokaye, Sede bazan maka alƙawarin zata tashi ba, dan yanzu haka tofin da na mata aljanun da aka tura mata dan su hana ta aihuwa na ƙona, ina tunanin tun sanda ta fahimci wacece Kilishi suka tura mata su, saboda haka Allah ya tashi kafaɗun ta"
Yana karashe wa ya juya da niyan ya bar wajen se ga zuwa ta fito a matuƙar firgice.
"Allah ya ja da nisan kwana, Gimbiya ta kasa aihuwa da kanta"
Sake shiga suka yi lokacin sarauniya babba da Fulani har ma da Mama Zulaiha da Bilkisu sun karaso gurin sede su a ƙofa suka tsaya basu shiga ba.

Suna shiga Yarima ya ƙarasa gunta sai yaga hawaye kwance a idanun ta ga nan jini a malale a ƙasan ta, murmushi na kwarin gwiwa ta sakar masa kafin ta saka hannu ta share masa hawayen daya zubo masa, Malam na bakin rafi ne ya miqo masa wani magani yace ya bata tasha, hannun sa na karkarwa ya karba ya fara bata, dakyar take iya bude bakin ta ta karba, bayan tasha kamar da minti biyar ta fara yunqurin aihuwa, ko minti Uku bata yi ba kan yaro ya taho, hannu ungozoman ta saka ta janyo sa, tana ɗagawa taga namiji ne kuwa, a take ta saka guda me ɗan karan tsayi, sede kuma a Lokacin karfin Hafsa ya riga da ya ƙare, sake nishi tayi kan wani yaron ya sake tahowa, ɗayar ungozoman ce, ta saka hannu ta ciro yaron, tana karasa ciro sa taga yarinya ce, ai kuwa itama ta rangaɗa guda, yadda kasan ba mara lafiya bace a gaban su, nan da nan kuwa jikin Hafsa ya saki, kallon yanda ake naɗe mata yaranta tayi, ga dai su nan ta haifo su Sede baza ta iya daukan su ba, ballantana tasan ya kamannin fuskan su yake, hawaye ne ya kuɓce mata kafin ta saki murmushi, dakyar da siɗin goshi ta samu harfin halin daga hannun ta ta kama hannun Yarima ta saka a cikin nata, kallon ta yayi yana me kai mata sumba a goshin ta
"Ki kalla abinda kika haifi mana 'fara kyakkyawar budurwa mai hankali da sanin yakamata', ki tashi kiga abinda kika haifo mana, suna matukar kama dake, ƴan tagwaye ne Allah ya azurta mu dasu, ki tashi ki gansu da kyau mana Hafsa, meyesa kike haka ne"
Ya karashe yana sakin wani kuka me matuƙar ban tausayi
Murmushi Hafsa tayi har kumatun ta seda suka lotsa jin ya kira sunan ta for the first time a rayuwarsu tare, tuna lokacin da suke zaune a lambu tayi, tana ta yi masa shagwaba wai in ta haifa mace sunan ta za'a saka, shi kuma yace sunan Fulani za'a sa, sede ta jira in ta aihu kamar takwas se ya duba ya gani in zai saka sunan ta, da ta tuna da hakan ta dinga murmushi musamman in ta tuna yanda zancen nasu ya kare da guje guje, tuna sanda tayi aiki a Masarautar nan ita da Murja tayi kana ta tuno da mamanta da kuma Jamila, da irin rashin jin da ta dinga yi da ciwon kan da ta dinga saka mutane, se ta saki dariya har haqoran ta na bayyana, tuno babanta Malam Sule tayi, se ta saki murmushi dan tasan ta kusa zuwa inda yake, juya fuskan ta tayi setin yaranta da ko kamannin su bata sani ba, kana ta maida kan nata kan Yarima, dakyar ta samu ta haɗa kalmomin nan kafin ta furta masa su, dan ji tayi harshen ta ya matuƙar yi mata nauyi tare da sarƙewa.

"FADREES 🖋️
😭😭😥🤧




52



YARIMAN HAFSA
(A Royal Love Story)
Mallakar Fatima Idriss Bello



Arewabooks; Fadrees20
Wattpad; Fadrees_20
Phone No. 0902058802


Haƙƙin Mallaka nawa ne Ni Fatima Idriss Bello, ban yadda wani ko wata suyi amfani da wani sashe na littafi na ba, ko a haɗa min audio ba tare da kwakkwaran amincewa ta ba, idan naga akasin haka kuma wlh baza mu wanye lapiya ba dan haka a kiyaye.
Idan number na kake nema ɗaga idon ka sama zaka ganshi a rubuce



Kunnen sa ya matso kusa da saitin bakin ta
"Ka kula min da su, ina son ku sosai"
Ta furta masa tana sakin kuka, damqe hannun ta yayi sosai a cikin nashi kafin yace
"In Sha Allah tare zamu kula dasu sahibata"
"Zan yi bacci"
Ya jiyo muryar ta.
A'a Ni ban amince kiyi bacci ba, so kike ki barni Ni nasan wayo kike so kimin, kuma in kika yi haka kin karya alkawarin da muka ma juna
"Toh na fasa baccin, zan sha shayi"
Ya sake jiyo muryar ta cikin rauni, miqewa yayi da sassarfa yace mata
"Ki jira Ni yanzu xanje in kawo Miki, Zuwai ya ma ido da tazo ta kula da ita bari ya kawo mata shayin, yazo fita a gun kyaure ya bangaje sarauniya babba, da duk suke tsaye a bakin ƙofar kuma duk suna sauraron abinda yake faruwa

Bayan kamar minti biyu Yarima ya dawo dakin hannun sa dauke da kofin shayi
"Ki daure ki tashi kisha gashi na kawo Miki"
Ya karashe yana kokarin saka mata kofin a baki
"Kaban da kaina zansha"
Babu musu kuwa ganin alamun ta fara samun sauki yasa ya bata kofin, ragowar karfin ta da ya rage ta kokarta ta saka ta riqe kofin ta kai bakin ta, ƙaran kukan jariran su yaji, da se yanzu suka yi kuka tunda aka haife su, juyawa yayi da niyyan ya karɓo su ya kawo mata su, kawai sai jin ƙarar faduwar kofin yayi, yana juyawa yaga tana shirin faduwa, da sauri ya taro ta saidai me? Ji yayi jikinta ya saki, ya kara mugun nauyi, jijjiga ta ya kama yi yaji shiru bata motsi aikuwa da sassarfa ya kwantar da ita, yana me yin waje da gudu dan ya kira Zuwai tazo ta duba masa ita, cin karo yayi da Malam na bakin rafi a bakin ƙyaure ya janyo hannun sa yace
"Yauwa Malam naga matata ta fadi ko zaka duba min ita, na jijjiga ta bata farka ba"
Kasa magana Malam yayi, yana me maida hawayen sa, inaa ba yau ya saba bada magani ba, amma yana tsoron sanar da mutuwa Sede dole ne ya sanar masa"
Maida kansa yayi yace da Yarima
"Ina so ka kwantar da hankalin ka ka saurare Ni Yarima, kasan shi lamarin Ubangiji yana yin abu ne a yanda yaso sannan a sa'adda yaso, kuma ko waye da kake ganin sa a duniyar nan aron numfashi aka bishi, dole wataran lokaci zeyi, sannan wa'adi dole ya cika, saboda haka ina me yi maka taaziyyar rasa iyalin ka da kayi, sannan muna me mata kyakkyawar fata da dacewa a aljannatul Firdausi Inshallah ".
Koda malam ya gama fadan
Kafar Yarima ne ya kama rawa, kallon Malam yayi yace
"Malam ban gane me kake nufi ba, me kake so kace?"
"Ina so ka fahimce Ni, bakin alkalami ya bushe, Hafsa lokaci yayi".

Idan aka ce beyi mutuwar tsaye ba anyi ƙarya, zama yayi akan gadon se can kuma yaje gaban hafsan ya tsaya, yana kallon ta yana me sakin murmushi.
Yana gani su Zuwai suka shigo dasu sarauniya babba da Bilkisu da sai rabza kuka take, gani yayi su sarauniya babba suna kokarin ɗaga ta, shi ko yaje da kanshi ya ɗaga musu ita, ya kaita makewayi, yayi fitowar sa ya tsaya daga bakin ƙyaure, Suleiman ne ya dafa kafadan sa, shi ko ko a jikin sa dan gani yake abun kamar almara ne

____________

Lokaci ƙalilan mutuwar Hafsa ya karade gabaki daya masarautar
Sarkin gida ne ya kira masinjan masarauta ya aike sa da yaje gidan su Hafsa ya fada musu abinda ake ciki.
Koda masinjan masarauta yaje gidan su Hafsa, se ya maka sallama a baƙin ƙyaure, Lawan ne ya taho yana me mitar yawan sallaman da ake tayi, yana fitowa yaga mutum da kayan masarauta a jikin sa, musabaha suka yi yace an aiko sa ne daga Masarauta, Ya lawan dajin haka se yace
"Toh mu shiga daga ciki mana, ai zancen masarauta be kamata muyi shi a waje ba"
Girgiza kai masinjan yayi kana yace
"Aa Ni sauri nake ance inzo in tafi da mahaifiyar Gimbiya Hafsa daga Masarauta, Allah yayi wa Gimbiya Hafsan rasuwa bada jimawa ba"
Koda jin haka ƙafar lawan ta kama kyarma
'meye? Allah yayi ma Gimbiya Hafsa rasuwa? Wace Gimbiyar, eh sedai Gimbiyar ba dai Hafsan nan gidan ba'
Juyawa lawan yayi ze koma sai masinja yaje ya jawo sa ya dawo dashi inda suka tsaya daga fari
"Ce maka nayi kaje kayi min sallama da ƴan gidan, ina so mu wuce da mamanta ne in yaso ku sauran kwa taho anjima, da maraice lis za'a mata jana'iza.
Hannu lawan ya daga zai kifawa masinja, masinja yayi saurin riqewa
Lawan ne yace masa
"Kana cikin hankalin ka kuwa, wane irin Hafsa ta mutu, ya za'a yi kazo ka same Ni da wannan mummunan saƙon sannan kayi zaton in yadda da kai?"

"Wallahi ba karya nake ba, taya zanyi inyi karya da mutuwa, wallahi bada jimawa ba ta mutu bayan ta aifi en tagwaye"
Shiru lawan yayi, sai can ya shige gida, bada jimawa ba sai ga mama da Jamila sun fito sunbi bayan masinja, ashe da Ya Lawan yaje ce musu yayi Hafsa tana naquda maman ta taje su tafi masarauta. Bayan yaga sun shiga keken doki se ya koma cikin gida ya taradda duka en gidan suna tsaye a tsakar gida hadda matarsa, yana ƙarasawa inda suke ya samu kujera ƴar tsugunno ya zauna akai kowa kuwa yayi shiru ya zuba masa idanu, can bayan kamar minti uku yace
"Allah ya yiwa Hafsa rasuwa yanzun nan bada jimawa ba, a garin haihuwa".
Ihu azima suka saka ita da su Dije, kan kace kwabo makwabta sun fara shigowa suji dalilin wannan ihun da ake, kowa idan yazo yaji abinda ake wa ihun se kaga yaja gefe ya raɓe jikin sa yayi sanyi.
Kuka mutan gidan suka fara yi, Irin kukan da kowa yake a gun se an baka tausayi, musamman sadiqu da ya raɓe a gefe guda yana kuka sosai
Karasowar yaya fati dasu halime ne, ramatu, murja da kuma Habiba da zaliha ne sukaaka buɗe sabon babin kuka
Kamar haka suka sha kuka sanda Malam Sule ya mutu, yau kuma ranar ta Hafsan Yarima ce.

Wato in nace muku ba'a girgiza ba nayi karya, kowa idan yaji Hafsa ne ta rasu se yayi kuka, ashe haka zukatan mutane suke dauke da soyayyar Hafsa? Duk da kasancewar tasha jibgan yaran su a baya be hana su kuka ba, dakyar aka samu su Azima suka shirya suka tafi masarauta, koda suka isa duk inda suka bi se suga jama'a ne ta ko ina, suna zuwa sashen Yarima yayi daidai da lokacin da aka fito da gawar ta a cikin makara, jikin ta a nannade a cikin likkafani, su Dije basu yadda da cewa Hafsa bace seda aka buɗe musu fuskan ta, gata nan kamar me bacci da murmushi akan fuskar ta kamar ka kira sunan ta tashi, koda murja tayi arba da fuskan Hafsa a take ta fadi sumammiya, ba ma ita daya ba, habiba ne tabi bayan ta kapın Azima da Dije, su Mama Lantana baki ya mutu murus, hakikanin gaskiya mutuwan Hafsa ya doke su, dan mutuwar matashi akwai girgizawa, ko sanda Malam Sule ya mutu basu girgiza ba kamar haka, sannan lokacin da Malam Sulen ya rasu tazo ta suka dinga kuka tare, ashe dai ita zata bi bayan sa nan ba da jimawa ba

(Allahu Akbar Kabiran
Kulli Nafsin Za'ikatul Maut, ko wane rai sai ya ɗanɗani mutuwa, kowa yaje ya gama iskancin da yaga dama karshen ta dolen dole ne kabar duniyar, domin duniyar nan ba matabbata bace, wasu nasan zasu ce me yasa Hafsa ta rasu? Sede ina me baku hakurin haka labarin yazo shi, kamata yayi kowa ya karba da hannu bibbiyu, daman dan a bada darasi ake rubuta takadda, sannan in kun lura Kowa da ƙaddarar sa, ita tata ƙaddarar kenan, muma in tamu tazo Allah ya sa mu cika da imani baki ɗaya. Ameen).

FADREES 🖋️🖋️ Ƴar Mutan Yobe.


53



YARIMAN HAFSA
(A Royal Love Story)
Mallakar Fatima Idriss Bello



Arewabooks; Fadrees20
Wattpad; Fadrees_20
Phone No. 0902058802


Haƙƙin Mallaka nawa ne Ni Fatima Idriss Bello, ban yadda wani ko wata suyi amfani da wani sashe na littafi na ba, ko a haɗa min audio ba tare da kwakkwaran amincewa ta ba, idan naga akasin haka kuma wlh baza mu wanye lapiya ba dan haka a kiyaye.
Idan number na kake nema ɗaga idon ka sama zaka ganshi a rubuce




Koda Mama Zenabu suka je suka ga Hafsa ne ta rasu har an mata wanka ma, se ta zauna tayi shiru ta bude fuskan ta tana ta jero mata addu'a, hawaye se zuba yake daga fuskan ta
"Na yafe Miki Hafsa, na yafe Miki duniya da lahira, Allah ya sada ki da mala'ikun rahama Ameen.
Tana karshewa ta fashe da kuka me tsuma rai, yaushe ta rasa mijin ta, wata biyar ne fa a tsakanin su, innalillahi.
Suna zaune can su Sulaiman suka shigo shida su yaya Lawan, makara suka kawo aka saka ta a ciki, bayan an rufe fuskar nata, wucewa dakin shakatawar Yarima akayi da ita, mutane suka dinga suma, Jamila kam tunda taga fuskar Hafsa a likkafani ta suma.
Can akazo aka kama makaran aka fita da ita waje, Yarima na hango yana tafiya kamar wani mara hankali, shidai gashi nan dai za'a ce amma baya cikin hayyacin sa.
Daman akwai makabarta a cikin masarautar dan haka can aka nufa.
Yana tsaye yana ganin sanda aka zura ta a cikin kabarin nata da daidai ita aka haƙa shi, se a lokacin ya yadda da komai, sannan ya kasa motsi kwata kwata, yana gani aka zuba tukwane aka shafe da kasa kana aka tsaya aka dinga jero mata addu'o'i.
Shidai kawai mamaki yake, wai yau Hafsa, Hafsan shi ce kwance a cikin ramin nan har an zuba mata ƙasa bisa kanta?
Allah Sarki, da kam be yadda ba, amma yanzu ya yadda
  Hafsa ta rasu,
      Ya karɓi hakan
Sede baya tunanin rayuwa shima.
Bayan kamar minti arba'in aka gama addu'a kowa ya fara watsewa, aka barsa da su Sulaiman da su yaya lawan, zama yayi ya dora kan sa akan kabarin ya fara hawaye yana zubo mata addu'o'i, yafi awa yana abu guda, gashi mangariba har ta iso, ganin baze tashi bane Suleiman ya riqo hannun sa Lawan ya riqo dayan, suka kama fita dashi daga makabartar dan su Mai Martaba tunda aka gama addu'ar farko suka yi gaba.

Suna shiga cikin masarauta suka ji ana shirin shiga sallan mangariba, alola suka yi suka je suka bi jam'i
Bayan da aka gama Sulaiman ya wuce da Yarima sashen sa dan sashen sa da jama'a, sannan Bilkisu ta koma sashen sarauniya babba, tare da jariran da Hafsa ta haifa, a can Bilkisu tace a bata su zata shayar da su tunda itama shayarwa take, sarauniya babba ce ta hana tace mata baza ta iya shayar da har yara uku ba, tayi tayi sarauniya ta bata ita kuma ta hana, se ta hakura a karshe kawai tabar maganar.

__________________

Bayan bakwai da kowa ya watse, Mai Martaba ya kira Mama Zenabu, yace mata ya rada wa yaran da Hafsa ta haifa suna Jafar da Aminatoú wato sunan kanın sa waziri da kuma mahaifiyar sa sarauniya babba, Waziri daɗi kamar ya kashe shi, nan kuma ya mata explaining din situation din da ake ciki, akan baze yiwu a bata yaran ta tafi dasu ba saboda hatsarin da rayuwar su ze iya shiga duba da sune yaran Yarima me jiran gado, sede in zata dawo zama a Masarauta ta kula dasu.
Koda jin haka se Mama ta ɗan yi jim, ita dai tana so a bata su, toh amma ina zata kaisu? İta daman tun kafin Hafsa ta rasu take so ta koma Borno, toh yanzun ma hakan take, baze yiwu ta kai yaran nan gida daya dasu Kulu ba, sannan Bornon ma bata san taje ta ɗora musu dawainiya, sannan ai baze yiwu ta dauki yara har biyu da Jamila ta uku suje gidan auren yar uwar ta su zaune musu ba, duk da tasan bata da matsala da hakan sede be kamata ba. Can dai ta nitsa kana ta kalli me martaba tare da sunkuyar da kanta ƙasa tace masa
"Allah ya baka nasara gobe gobe daman nake san barin ƙasar Bauchi zan koma ƙasa ta ta haihuwa Borno, idan naje zanyi shawara da yar uwata da kuma mijin ta, duk yadda muka yanke za'a ji daga gare mu, daga nan zuwa da shekara ɗaya İnshallah".
Koda jin haka sai Mai Martaba ya aminta da abinda tace masa sannan ya yaba da hankalin ta kana yace toh Shikenan bari yasa a aika gidan su a kwaso mata kayanta in yaso gobe se ya shirya mata tafiyar Tata, tunda dai surikin nata da Yakamata ya mata hakan har yanzu baya a cikin hayyacin sa, shidai kawai rayuwa yake yi hakanan.

Ai kuwa da sassafe Mama Zenabu da Jamila suka je suka yiwa sarauniya babba da Fulani sallama, tana kallon jikannun ta dakyar ta sake su, Yarima ma yazo sunyi sallama shida Sulaiman sede ta lura kamar baya cikin hankalin sa, well, bata ga laifin sa ba, ita kanta da take uwarta karfin hali take yi.
Suna fitowa suka ga me martaba ya shirya musu goma ta arziki a cike da kekunan doki har uku, suna cikin na hudun, har bayi seda ya zaba musu wanda zasu raka su.
Nan da nan kuwa suka kama hanya sai Borno.

______________

1 YEAR LATER
MASARAUTAR KANEM BORNO

Suwaiba ne da Jamila a zaune a ɗakin shakatawar Mama Maryamu, hira suke ɗan taɓa wa kaɗan kaɗan dan dukkanin su ba masu san magana bane musamman Suwaiba, ita sam magana bata dame ta ba, wai fa zaman jiran su Mama Maryamu suke akan su fito su kama hanyan zuwa masarautar Bauchi, tun dazu suka ce musu suna fitowa amma sunji shiru, shine suka zauna suke hiran yaran Hafsa da zasu je su gani anjima In Sha Allah
Jamila ce tace
"Kin san wani abu Yaya Suwaiba? Wlh kina matukar kama da Yaya Hafsa, wlh dazu da asuba da nagan ki seda na tsorata, kawai dai yaya Hafsa ta fiki jiki kaɗan ne"
Jamila ta karashe idan ta da hawaye, tunda ta rasa Hafsa take cikin kunci amma samun Suwaiba da tayi ya matukar ɗebe mata kewar Hafsa, suna matuqar kama da junan su, harda itanma Dukkanin su ukun kamannin mamannin su suka dauko
Suwaiba ce tace
"Tunanin me kike Jamila"
Firgigit Jamila tayi kana ta fuskance Suwaiban, tana shirin bata amsa suka jiyo muryar yaya Abubakar yana ce musu suyi waje.
Keken doki ɗaya suka shiga suka zauna, can sega su Mama Zainabu sun fito, kap a cikin shekarun nan da suka yi tare mutane sun kasa dena kallon su in sunzo wucewa tare saboda tsananin kamar da suke, musamman ma yanzu da Mama Zenabu take rayuwar jindadi sulalla sun zauna mata, bata aikin fari bare ja, fatar ta ta saje da na Mama Maryamun.
Nufo keken dokin da su Jamila suke ciki suka yi, shiga suka yi daman gun zaman mutum takwas ne, Mai girma Galadima kuwa dayan keken dokin ya shiga shida Talban Borno da kuma Shettiman Borno, dayan keken dokin su Abubakar da su Ibrahim ne a ciki.
Tafiyar awanni goma sha biyu suka yi suka shigo masarautar Bauchi, wani numfashin baƙin ciki Jamila da Mama Zenabu suka shaqa, direct masarauta suka wuce, aka yi musu tarba me matuqar girmamawa, aka basu sashe sukutum suyi sharing, Galadima kuma sashen da aka ba su Talba yake.
Can da dare kamar karfe goma su Mama Zenabu suka shirya suje sashen sarauniya babba dan su miqa gaisuwa da kuma godiyan irin karamcin da aka musu, on the other hand tana so taga jikannun ta, taga yaya suke, tana so taga yanda suka ƙara girma, dan rayuwar da tayi a kasar

Please Login or Register in order to submit comment