Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

je sashen Kilishi"
Shiru tayi tayi banza dashi, daka mata tsawa yayi nan da nan ta sauko daga kan gadon tana me durqushe wa a kasa
"Baza kiyi magana ba"?
Ya sake jefa mata tambayar a harzike
"Ni dai ka kyale Ni haba, ya zaka yi tafiya har wata guda kayi tsammanin inyi ta zama anan bana fita ko ina, ai kai kanka kasan dokar masarautar nan, na gaida surukai, ai ba sashen ta kadai naje ba har sashen Fulani naje, itan meyasa baka hanani zuwa ba"
Ta karashe tana me murkuda masa baki,
Tsaki yayi cike da takaici, wlh wannan da wani ne yake masa magana haka ai da ba haka ba, amma yarinyar nan gabaki daya ta rena shi, sannan baya san tana shiga harkar Kilishi dan wannan baza ta mata ta dadi ba.
"Da kika je din me kika ce mata"?
Ya sake tambayar ta
"Wai meyesa kake san kasan abinda ke tsakanina da mahaifiya ta ce"?
Ta jefa masa tambayar tare da cuno baki waje
Fisgo ta tsaye yayi ya kama kunnen ta kamar ze tsige mata shi yace
"Zaki min bayani ko a'a"?
"To ka fara sake min kunne na tukun"
Cika ta yayi yana me zama akan gadon tare da dafe kanshi
Tsintar muryar ta yayi tana cewa
"Ka tashi min akan gado, in kama so kaji komai ka tsaya a tsaye tukunna"
Ido ya sake cike da mamaki, ransa ne yayi bala'in tashi, har jijiyoyin kansa seda suka fito, ganin haka Hafsa ta tsugunna bisa gwiwowin ta tana me neman afuwa, tare da fara magana kamar haka
"Tun ranar da naje aka cemin tana bacci, kuma na shiga dakin ta na ganta idon ta biyu na sa mata ayar tambaya, se kuma mako uku da suka gabata, na sake zuwa aka cemin wai tana bacci, shine fa na sake shiga inga ko wannan karan baccin take ko akasin haka, idan bacci take se in saɗaɗo in gudo in dawo, in kuma bata nan sede in kwana inga ta ina zata fito, gashi kun ƙi ku gaya min bawan da yake sa mata idon, shine fa da na shiga naga tana bacci, Nazo zan fita kuma tayi kururuwa wai Nazo zan mata sata, shine fa na dan mata rashin ɗa'a kadan, amma wallahi ba'a san raina bane domin kamar mahaifiya ta na dauke ta, Seda Fulani tazo tayi mata magana tukun tabar zancen fa"
Ta karashe maganan ta cike da jin haushin abinda Kilishi ta mata, dan yanzu haka hanyan fansa take nema
Bayan jin haka se Yarima yace mata

"Daga yau babu ke babu sashen Kilishi, in har bani na kai ki ba, kar ki sake zuwa sashen ta, Sannan bawan da aka sa yana sanya idanun sa akan Kilishi tsawon wata ukun nan yazo ya ce mana ba inda take zuwa, sese idan ata cikin gidan take zuwa, ko kuma tana canza siffanta ta fita ko kuma ma ba inda take zuwa baki daya, domin shima bawan ya saka yaransa da su dinga bin duk wanda suka ga basu san shi ba, kuma sunyi ta bincike basu samu wata hujja ba saboda haka, daga yau se yau, babu ke babu sashen Kilishi".
"Indai haka ne gaskiya da sharadi"
Hafsa ta fada tana me kura masa idanun ta.




>>>>>>>>>>>>>🖋️💻







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss 🖋️🖋️
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20

Page 40



Hakkin Mallaka nawa ne Ni Fatima Idriss Bello
Ban yadda a juyamin littafina ta ko wane irin tsiga ba, ko kuma ayı audio ba tare da izinina ba domin hakan ze iya janyo ma mutum matsala.
Dan haka a kiyaye.


Mamakin jin wai tana da sharadi yayi, amma bari yaji menene, Allah yasa ba batun Injiniya zata sake yi mishi ba
"Menene sharadin naki"
"So nake gobe gobe ka sallami Murja"

Kallon ta yayi na tsawon minti Uku kapın yace
"Nima ina da sharadi" domin alamu sun nuna ta damu da wannan Murjan
Kallon sa tayi cike da mamakin jin meye nasa sharadin shi kuma
"Zan sallami kawarki kamar yadda kika bukata, sede ina so mu dinga kwana tare daga yau sannan zaki dena nema min magana a cikin Masarautar nan daga yau" kallon kiyi tunani dakyau ya mata yana me ɗage mata girar sa daya.
Kallon shi tayi, ita dai gaskiya baza ta iya kwana da gardi a guri daya ba, amma kuma in ta yarda kamar ta ma Murja jihadi ne, ko ba komai zata temaki kawar ta ne, amma wallahi ya kuskura ya dora mata kafa se ta mishi musqulin da baze taɓa ma iya daga ƙafarsa ba a rayuwarsa, sannan wannan kwanan da zasu fara yi a tare zata tanadi kalan muguntan da zata dinga masa wallahi dan ita babu ruwan ta dashi ɗan sarki ne, sannan maganan neman magana kuma sharri ya mata, fisabilillah shi me ta masa ma daze mata wannan sharrin?
Can kamar baza tayi magana ba tace masa
"Na amince, sede a cikin kwanakin nan ina matuqar kewar gidan mu, tunda Nazo ba wanda yazo ya duba Ni, sannan ko wasiqa babu wanda ya aiko min, anya ma babu abinda ya faru kuwa, yanzu fa ba bauta nake ba, da za'a ce baza azo guna ba" ta karashe cike da yin kalar tausayi, kama hannun ta yayi ya zaunar da ita akan gadon shima ya zauna, ciro wasiqa yayi daga aljihun jabbarsa, ya miqa mata, data duba kwanan wata se taga tun wata uku da suka wuce ne, sako ne daga Jamila, kukan shagwaba Hafsa ta fara masa tana cewa meyesa be bata ba tun farko, shi kuma ganin yanda take yin ne ya basa dariya har besan sanda ya murmusa ba har haqoran sa masu matukar kyau da daukar ido suka bayyana, kallonsa ta tsaya yi cike da mamaki, dage mata girar sa ɗaya yayi, wanda ta lura da kamar ɗaga giran yana daga cikin al'adar sa,
"Daman Yarima kana dariya? Ni wallahi na dauka fuskar shanu gare ka, dan kwanaki kallon bujimi ma nake maka ashe kana dariya, sannan meyesa baka bani sakon nan ba se yanzu"? Tunda ta fara magana ya haɗe ransa, ya murtuqe fuska.
Can kamar baze yi magana ba, sai kuma yace
"Ni ne banyi niyyar baki ba, Sannan kika ce ina kama da bijimi ko"?
Dariya ta kwashe dashi sosai ganin yanda ya haɗe ran nasa, dan cike da wasa yayi kamar ba Yariman da ta sani ba,
"Nipa ba wai cewa nayi kai bijimi ko Sa bane, kawai dai naga kai kullum ranka a haɗe yake, nidai yanzu ba wannan ba, ka tashi ka tafi dakin ka, idan na canza kaya zan biyo bayan ka" ta faɗa tana adana wasiƙan, dan se tazo kwanciya zata karanta
Ɓata yayi a cikin kallon ta da tana dariya, hakika rai da ruhin sa suna matukar bukatar ta, sede shi ya kasa fahimtar hakan kwata kwata, shi a zaton sa kawai yana zama da itane dan ta ɗebe masa kewa.
Hannun ta ta sa ta tsokane masa idon sa, murmushi taga yayi kapın tace
"Kasan yanda murmushi yake maka kyau? Ko kaifa? Wallahi kana da kyau kaine baka san hakan ba inaga"
"Ke din baki da kyau ne"?
Ta tsinci muryar sa
Cappp Ni dinne bani da kyau? Wlh nafi ka kyau sosai, duk yanda ake cewa kana da kyau wlh nafi ka, kasan a lokacin Sallah en mata har taruwa suke wai dan su kalle ka, Ni lokacin har haushi suke ban wlh, sannan Nima din da kake wani rena Ni kasan yanda samari suke so na kuwa, se mun ɗan fara magana se su dena kulani wai banda kunya kasan wani abu"?, girgiza mata kai yayi hankalin sa gaba-daya akan ta, "akwai wani wai Ayuba da ya taba cewa wai yana so na, kullum In zezo hira da leda yake zuwa ranan da bezo da leda ba dambe muka yi dan dakyar su Azima suka rabani dashi tun daga nan ba'a sake cewa ana sona ba, wai kyan dan maciji gareni, sannan Mama cemin tayi wai Ni mummuna ce, ai kuwa ranar Seda na ma Jamila dukan tsiya, ta kare da farin ciki
Murmushi ya saki yana kallon ta cike da bege, sede kuma injiniya ya sha cemin ina da kyau da sura me kyau
Taɓe bakinsa yayi, yana me tsaki, shidai be san meyesa yaji wannan injiniyan yana basa haushi ba sosai wlh
Can ta kara cewa
"Amma Yarima ka fada min tsakanin ka da Allah, shin ina da kyau? Ta fada tana me matsowa kusa da fuskar shi tare da lotsa kumatun ta (dimple) jin Muryar sa tayi yace
"Gaskiya baki dakyau ko kadan, ke nifa farkon kallon ki da nayi na dauka dodo ce ke, se daga baya na gane ke halitta ce me matukar ban tsoro ga al'umma, gaskiya injiniyan nan da yace kina da kyau ba ƙaramin makaho bane" ya karashe cikin halin ko in kula
Ɓata ranta tayi tace
"Nidai ka fita waje kaje ɗakin naka zan samo ka acan zan saka kayan bacci ne kawai inzo", ta karashe tare da hade fuska, daman me take expecting a gun sa? Meyesa ma ta ɓata bakin ta wajen tambayan sa, Shiko maqe kafadar sa yayi akan baze fita ba, ita kuwa ganin haka ta tashi ta dauki kayan da zata saka ta shige makewayi ta canza, tana fitowa ta dauki wasikarta ta wuce dakin sa tayi kwanciyar ta akan gadon ko ta mishi magana.
Shigowa yayi yaje ya rage kayan jikin sa, ganin haka Hafsa ta juya masa baya, makewayin shima ya shiga can ya fito da wasu kayakin, yazo ya zauna a bangaren da take kwance,
"In baki ce komai ba bazan barki ki kara zuwa gida ba"
Da jin haka kuwa ta juyo a hanzarce tace, "Ni karka dameni wasika zan karanta"
"Ki karanta a fili Nima inji"
"Hmm Ranka ya dade kenan, ai ko baka ce ba a fili zan karanta dan kaji haushin kai ba wanda ya taba turo maka wasiqa.
Maƙe kafadarsa yayi
Ita kuma ta fara karantawa kamar haka;

_________________

Kilishi ce a cikin kogon boka Kapoor.
Muryar sa mai echo uku uku cike da ban tsoro ta jiyo yana fadin
"Wannan maganin, ki tabbatar da ya shaqe sa, toh zeyi mata aika aikan kamar yadda yake a cikin tsarinmu, domin watan jibi aljani Gopal ze tafi birnin sin domin ya dakko mana maganin, domin tafiyar yana daukan kimanin shekara ɗaya da rabi, idan kuma aljanin me sauri da sa'a ne se kiga a kasa da shekara ma yaje ya debo maganin, idan kuma ba me sa'a bane tun daga kogin Mami watern ze margaya, ke yanzu aikin ki ki tabbatar da ya shaqa shi ɗaya, sannan da ya shaqa aikin mu ya qare kenan dan dole ze aikata mata fyaden, mu kuma a lokacin zamu saka mata mafarin aikin a jikin ta, in yaso da Gopal ya kawo maganin zamu aika mata da karshen aikin, shikkenan ita kuma tata ta kare, sannan ina so in ja Miki kunne, ki tabbatar da ciki be shige ta ba, sannan ki tabbatar da babu abinda ze kuma sake shiga tsakanin su, domin in ta ɗauki ciki za'a iya samun saɓani cikin aikin, shi kuma wanda aka sa ya bincike ki da kin koma za jiki ana shelar mutuwar sa, domin yanzu haka yana ta bayan dakin ki yaga sanda kika ɓaco nan gurin, zaki iya tafiya
A tsorace Kilishi ta tsugunna ta dauki maganin da bokan ya bata ta ɓaco cike da murmushin samun nasara.


FADREES 🖋️ 🖋️.




>>>>>>>>>>>>>🖋️💻







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss 🖋️🖋️
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20

Page 41



Hakkin Mallaka nawa ne Ni Fatima Idriss Bello
Ban yadda a juyamin littafina ta ko wane irin tsiga ba, ko kuma ayı audio ba tare da izinina ba domin hakan ze iya janyo ma mutum matsala.
Dan haka a kiyaye.



Not edited

Ɓacewa tayi ta koma dakin ta cike da matsanancin farin ciki da kuma gamsuwa, gaskiya shugaba ya gama mata komai a rayuwar ta, shine dogaron ta, ɗan jinin bayin da take salwantar wa ba komai bane ita a gunta, sannan ita ji take kamar ma bata biya sa ba in ta bashi jinin mutum daya, karamin zoben gunkin dake hannun ta ta kalla tace, yau shugaba ka dauki jinin bayi biyu, mace da namiji, daman dare ya tsala sosai, nan kuwa ta kwanta tayi bacci cikin jindadi.

Da safe masarauta ta tashi da mutuwar bayi guda uku, maza biyu, dayan wanda ya san sirrin Kilishi ne wato wanda su sulaiman suka saka da ya dinga bibiyar Kilishi, ita kuma macen ashe Lantana ce, yar dakin su Hafsa da Murja, wato dai ƙawar Shafa'atu.

________________

Hafsa ce ta bude wasiƙan, rubutu ne cikin ajami kamar dai yadda ko wane wasika yake, fara karatun wasikar Hafsa tayi cikin ɗaga murya kamar haka;

Da sallama zan fara bisa addinin musulunci

Barkan ki da warhaka, da fatan kina lapiya, yaya kike yaya mijin ki da kuma dangin mijinki, da fatan duk kuna cikin koshin lapiya
Abu biyu ne ya sa na rubuta Miki wannan wasikan, na farko dai albishirin ki, Mama ta samu ahalin ta daga Masarautar Kanem Borno (nan ta zayyano mata komai tun daga farko har karshe), sannan Kinga me kama da Maman? Sunan ta Mama Maryamu tana matukar kama da Mama, kamar an tsaga kara, sannan ƴar ta tana da kirki, da zan taho har ta bani abubuwa da dama wasu ma har tace in kawo Miki, sannan tace in gaishe ki
Abu na biyu an saka auren kawarki Habibah nan da wata uku, ta samu wani ɗan me unguwar su, da fatan dai zaki zo auren nata sannan na hadu da Zaliha kawarki wai in gaida ki tayi kewarki.
Kowa da kowa yana gaishe ki a gida, nida su Dije, Azima da kuma Sadiqu muna so Muzo amma Baba ya hana mu zuwa, waima inji en unguwa sunji dadin wannan auren da kika yi yaransu sun dena zuwa musu gida da kuka, in dai har kin kalla sakon nan ki maido min da amsa
Zan tsaya daga nan, Mama tana gaishe ki sosai, tace ki rika addu'a sannan ki yi ma mijin ki biyayya domin abubuwan da yayi mana basu ma faɗuwa.

Nice ƴar uwarki me matukar kaunar ki,
Jamila Sule.
Bissalam.

Da Hafsa ta kawo zuwa nan, se ta fashe da kuka, Allah Sarki, wlh tayi missing gida, rabonta da gida tun makwanni sha uku baya, tayi missing Mama sosai, rufe idanun ta tayi tana shesheka, jin danshin abu tayi bisa kumatun ta, buɗe idanun ta keda wuya taga Yarima ya mata rumfar da ƙirjin sa, harshen sa bisa ƙuncin ta, miqe wa Hafsa tayi a ɗan firgice, take ta sauka akan gadon tana me zare idanu, suna hada ido da shi ta rufe fuskar ta wai ita kunya, da gudu tayi dakin shaqatawa zuciyarta na matsanancin bugawa, Wayyo me haka? Me kenan, ji tayi tsigar jikin ta ya tashi sannan fitsarin dole ya kama ta, makewayin dake cikin dakin shakatawar ta shiga, sai can ya fito tana me ajiyar zuciya, gaskiya ita baza ta iya komawa dakin ba, wallahi ita kunyan sa take ji sosai da sosai, tsayawa tayi a bakin kofar dakin, ta ɗan leqa kaɗan, ta hango baya dakin, ajiyar zuciya ta sauke kana ta fada cikin dakin da sanda sanda, ji tayi an ɗaga ta sama cidak,  baki ta bude zata ƙwalla ƙara yace mata, "ke nine fa"
Shiru tayi ta fara wutsil wutsil
"Ni dai ka sauke Ni"
Ƙin sauke ta yayi har seda yakai ta kan gadon kana ya kwantar da ita, dora matashin kanta tayi ta rufe ido ta juya masa baya,ita mamakin halin da Yarima ya tsira kwanan nan take, gashi shi kamar ko a jikin shi ma, Ya Ilahi, itakam kunya ma take ji, amma tsaya yaushe ta fara jin kunya ma, anya kuwa, gaskiya da sake
Wasiqan ɗazu ta tuna, wai Zaliha yadda cewa wai ita kawar ta, wato dan tana auren dan sarki ko? Ita dariya ma abun ya bata, gobe dai inshallah da safe zata rubuta mata amsa in yaso sai ta baiwa Murja takai musu tunda gobe za'a sallame ta.
Bata san sanda bacci yayi awon gaba da ita ba, koda ta tashi sallan asuba gani tayi tabar bangaren da ta kwanta da farko tana ɓangaren Yarima mamaki abun ya bata, ita da ba ma wani birgima take ba? Miqewa tayi dan bata gansa a cikin dakin ba, makewayi take tayi alola ta fito tayi sallan ta, ta koma abun ta, da safe hayaniya ne ya tada ta, ta miqe yaje tayi wanka ta gama shirin ta ta gyara ko ina kana taje dakin shakatawa, ta zauna akan teburin Yarima tare da rubuta ma Jamila wasiqa, da ta gama ta rubuta ma Habiba ma, ajiyewa tayi akan wani wasiqan daban, kamar kar ta bude se kuma ta bude, ashe wasikar sallamar Murja ne Yarima ya rubuta, murmushi tayi ta daga kenan wani wasikan ya sake fadowa
Tana budewa taga abinda yake kunshe a ciki ta saka murmushi domin rubutu ne kamar haka

"Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.

Da fatan kin tashi cikin koshin lafiya, a rage rigima koh?, fara kyakkyawar budurwa mai hankali da sanin Yakamata?

Mijin ki abin alfaharin ki
Idriss".

Nadewa tayi ta ajje a inda yakamata, nan ta miqe da zummar ta leqa waje idan da hali ma taje sashen Kilishi sai taji an budo kofar dakin shakatawar da matukar ƙarfi, daga kanta tayi dan taga wane dan renin hankalin ne haka, kawai se taga Murja ce ta shigo tana kuka kamar ranta ze fita, da gudu ta karasa fun murjan tana riqo ta se cewa take
"Meya paru ne Murja meya same ki haka"
"Lantana ce ta mutu"
Murja ta fadi tana sakin wani razanannan kuka, Hafsa ne ta zube gwiwan ta a kasa, tana sakin kuka itama, ficewa suka yi suka wuce sashen bayi, har an mata wanka ma, Allah Sarki daman bata da ƴan uwa, shafa'atu ce daman ahalin ta suke cikin masarautar, ita kam lantana daman marainiya ce, karfe goma sha biyu aka kaisu can makwancin su, karshen ta a dakin shakatawar Yarima aka koma karban gaisuwar Lantana, su Hafsa da su shafa'atu ansha kuka an koshi, baya ma shafa'atu da suka saba sosai, dan duk inda zata je tare suke zuwa, kawai gun aikinsu ne daban, ita shafa'atu tana sashen Sarauniya Babba ita kuma Lantanan tana sashen Kilishi, sannan lafiyan ta kalau dan ko ciwon kai bata yi ba, kawai an wayi gari ne anga already ta sheqa.
Wannan kenan
________________

Yarima da Sulaiman kuwa mamaki suka yi, nan suka ce gaskiya mutuwan nan kamar da biyu, daman an saba dauki dai dai na mutuwa akan bayin cikin masarautar, amma yau har mutum uku? Sannan kwana sha hudu kenan da wani ya mutu a Masarautar, amma dai zasu bincika suga ko natural death ne, dakin su bawan da aka kashe Sulaiman ya aika aje a bincika kayan sa ko za'a ga wani abu, nan da nan kuwa aka je aka kawo dukkan kayan sa ba'a ga komai ba sai wani dan kyalle hakan nan, basu wani maida hankali akai ba kawai aka mayar da kayan nasa, da niyan zasu dai bincika suga ikon Allah.

FADREES 🖋️ 🖋️





42


Wattpad; Fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20




Yau watan lantana uku da mutuwa.
Wanda ya kama watan Hafsa shidda da en kwanaki a cikin wannan masarautar
Abubuwa da dama sun faru, kama daga  sallamar Murja, zuwan su Azima da kuma fyaden da mijin auren ta wato Yarima Idriss ya mata wanda hakan yana ɗaya daga cikin nasaran aikin Boka Kafoor.
Bayan bakwai na lantana Murja ta bar masarauta a matsayin me enci, daman Hafsa ta rubuta mata wasiqa akan ta baiwa Jamila, sannan tace mata idan har gidan su ba'a karbe ta ba taje gidan su tayi zamanta har karshen rayuwarta, sede kuma wani abun mamaki da taje gidan nasu mahaifin ta ya karbe ta da hannu bibbiyu, ba abinda taji dadin gani kamar mahaifiyar ta da aka dawo da ita gidan, da ta tambaye babarta se Babanta yace mata sun jima da rabuwa, nan tayi zaman ta a gidan su cike da jin dadi da farin ciki tare da iyayen ta, bayan kwana biyu ta nemi gidan su Hafsa taje ta bada wasiqan da ta bata hadda na Habiban da yanzu watan ta uku da yin aure.
Anyi haka da kwana ashirin ƴan uwan ta suka zo gidan ta, su Azima anga gida me kyau se hassada kuma, Jamila ce ta dinga bata labarin abubuwan da ya faru da bata nan, wai an rushe gidan su an sake gina sabo, sannan daman gidan simintin da suke me kyau ne sosai, wai suma yanzu a unguwar su dasu ake damawa, Baba yace su Dije su ciro miji an rasa me auren su, yanzu yace ze bada su sadaka kawai, Hafsa da jin haka hadda dariyan ta su Murja kuwa se hararan Jamila suke, da farko a gidan su an dauka itace baza ta samu miji ba saboda rashin kunyar ta, amma da ta tashi one time tayi auren ta abinta, sannan wa ta aura? Yariman gabaki ɗaya ƙasar Bauchi, shi daman haka Allah yake, yana yin abu ne a yadda yaso sannan a kuma lokacin da yaso.
Jamila ce take ta bata labarin tsarin masarautar Borno, ce mata tayi
"Wallahi Hafsa da kin kalla tsari da kuma yanayin masarautar Borno zaki ce yafi wannan masarautar komai da komai, sannan kinsan wani abu"?
Girgiza kai Hafsa tayi
"Waima sunan Mama na asali Maimunatu ne, wlh Hafsa mama kamar da suke da Mama Maryamu har ta ɓaci, sannan yar ta Suwaiba kuna kama da ita sosai"
A lokacin Hafsa murmushi tayi tana ta jin dadin labaran, tana hango su Azima da Dije sai cin abun duniya ake, tare da saka bayi aiki, sadiqu kuma se taɓe taɓen sa yake, duk dai bata masu magana ba.
"Yauwa Hafsa kin san me"?
Ta sake jiyo muryar Jamila
"Wai Jamila baza ki dinga cemin Yaya Hafsa ba, nifa matar aure ce, ko sai na sa an Miki bulala ne"?
Hafsa ta karashe tana me dariya
A lokacin Jamila cewa tayi tana dariya itama
"Toh kiyi hakuri Yaya Hafsa, yayata ta kaina, daman ce Miki zanyi Yarima yana zuwa ya gaida su Mama har yana kai mana abubuwan dadi nida su Sadiqu"
A lokacin wani feeling me daɗi ta dinga ji a game da Yarima, lokacin da suka tafi sai suka bar ta da kewar su musamman Jamila, tun daga lokacin ta dauki damarar faranta masa, tare da kiyaye duk abinda baya so, duba da yadda yake nuna girmamawar sa ga ahalin ta, duk da kasancewar shi din ɗan sarki ne amma dai tasha satar hanyar zuwa sashen Kilishi sede ba dama, amma rayuwarta tsakanin ta da Yarima ya gyaru sosai da sosai, dan hakanan tana zuwa tana gaida mahaifiyar sa kusan kullum sede ta lura kamar mahaifiyar tasa bata da matsala kamar yanda ta dauki zafi da farko, hakan nema yasa take zuwa gaida su ita da sarauniya babba, Kilishi kuma in zata je tare suke zuwa da Yarima .

Sede zuwan da suke tare ɓata ma Kilishi rai yake, dan so take ta watsa wannan garin maganin ya shaqa, ranan kuwa ta aika tana kiransa tun kapın yaje ta hana bayin ta su shigo, tana jin karar sa ta watsa maganin, dadin da taji da ya kasance shi ɗaya yazo ba tare da Hafsa ko Sulaiman ba baya misaltuwa, daga lokacin ne kuma yaje ya aikata me afkuwar gaba daya.
Sede kuma Hafsa bayan faruwar abinda ya aikata mata ta fara janye jikin ta daga nashi, domin ya mata abinda har ta koma ga mahaliccin ta baza ta manta ba, yanzu ma da take zaune tuna yadda abin ya faru take, sede tasan abu daya, ta yafe masa sannan tana kyautata masa zato.

______________

Flashback

Sati biyu baya rayuwa suke ita da Yarima cike da mutuntawa domin Yarima yana matukar faranta mata, idan ze dawo yana kawo mata abu me dadi, randa be kawo ba kuwa da fushi take kwana shi kuma ya dinga murmushi kenan, zaman lafiya suke kamar me domin sai a lokacin ta fahimci waye shi, shi mutum ne me matukar zafi da sanyin rai a lokaci daya, ta lura da wani abu ɗaya, yana da kirki sosai ga kyauta da tausayi, sannan baya san wani ya raɓeta sam, baza ta manta ba a lokacin auren Samira kanwar Sulaiman, da taje sashen Gimbiya Bilkisu ta tadda dukkan ya'yan Sarki sunzo, wato yayun su Yariman kowa yana gun ana ta raha harda wanda take aure a Nijer

Please Login or Register in order to submit comment