Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuwa, Bilkisu hadda karamin cikin ta, ana zaune su Shamsu ne, Sulaiman din kansa da Hayatu hatta da Yarima yana gun, Yarima ne ya lura da Hayatu se yaga kamar kallon ta yake, baya ga hakan kallon ma kamar na kauna ce, ransa ne yaji ya ɓaci, ya tashi tsaye ya kama hannun Hafsa ya musu sallama, tana jin wasu en uwansu suna cewa wai ya zai dauke ta a gun su, wai gaskiya son da yake mata yayi yawa, hakan da akace ya ɓata ran Hayatu, shidai be kula su ba tunda har lokacin ya kasa karbar cewar santa yake yi, da suka fito ma ɗora hannun sa yayi bisa kafadar ta suna tafiya ana ta kallon su shiko ko a jikin sa, sashen sa ya wuce da ita ya dinga ja mata kunne akan Hayatu, a lokacin se ta lura da abu daya, kamar dai Yarima kishin ta yake, kodai son ta yake ne? Kai a'a shi da yace mata shi kallon baiwa yake mata?, sharewa tayi sede ta fara ƙaryata zuciyarta dan washegari da wani abokin sa Salman ɗan sarkin Gombe da yazo yace ya kira masa amarya su gaisa ƙi yayi, Sulaiman ya dinga tsokanan sa wai kishi yake, sannan da ma shi kadai ne kaɗai yake mu'amala da ita.

Yau ma kamar dai kullum, zaune take akan gadon Yarima, dare ne yayi sosai, gashi bata ga ya dawo ba, se taji wani iri sosai, ita ta saba da baya wuce lokacin nan be dawo ba, sannan da ya dawo suke kwanciya suyi baccin su, se can har ta fara gyangyadi, taji alamun shigowar sa, ɗaga kanta tayi ta kalla fuskar sa, se taga kamar bashi bane, kamar wanda wani abu ya shiga jikin sa ne, yana shigowa ya fada kanta kamar wani mayunwacin zaki, bata yi aune ba ya rabata da kayanta, a lokacin yayi mata abinda har yanzu take kokwanton akan sa, ita abinda yake bata mata raima, meye na yi mata faɗe (ita bata san aikin Kapoor bane), idan da ya tambaye ta izinin ta ai zata yadda tunda dai bata saɓa umarnin sa, sannan taci bakar wahala kamar kuma hadin baki farin yadi ne a shimfide akan gadon, da washegari bayi ne suka taimaka mata ta kimtsa suka dauki yadin suka kai sashen sarauniya babba inda kowa take farin cikin kaiwar mutuncin ta, ita kuwa baƙin cikin fyaden da ya mata take, Kilishi ne ta taɓe baki da taji labarin ta kawo budurcin ta lapiya qalau, tun daga lokacin suka fara baya baya da juna ita da Yarima domin dakin ta ma ta koma da kwana, se ta kwana ta wuni bata saka shi a idon ta ba, sede wani abu da ta kasa fahimta shine, ita har yanzu bata tsane shi ba, so take ma su dawo kamar da, amma babu komai zata seta hakan da kanta tunda gashi abinda ya faru dai ya riga da ya faru tun makwanni biyu da suka gabata sannan tun daga lokacin ne sake mata ba daidai ba, kuma ma gashi neman wata bakwai suke yi da aure dole zata gyara tsakanin su, sannan ta yafe masa fyaden da ya mata.

ALƘALAMIN FADREES 🖋️, Ƴar Mutan Yobe.




43


Wattpad; Fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20


Yau dai tayi niyyar a dakin sa zata kwana
Tun bayan isha da ta gama komai nata ta wuce dakin nasa ta kwanta tare da rufe idanun ta, sede ba bacci take ba likimo tayi, bayan ya shigo ya gama duk abinda zeyi a ransa yace bari yaje yaga ko tayi bacci, dan kullum se ya leqa dakin ta yaga ko tayi bacci ne ko a'a, kamar walkiya kuma, se ya juya kan gadon sa ya ganta a kwance, ƙarasawa gun yayi sai yaga kamar bacci take yi, ƙarasawa yayi ya hau kan gadon ya matso daidai fuskar ta yaga dai bacci take domin in har ba bacci take ba yana ganewa ta yanda take mirtsika idanun ta, tsaya wa yayi yana kallon ta, yana me tuna abinda ya aikata mata mako biyu da ya wuce, shidai yasan bayin kansa bane, daga yaje ya amsa kiran da Kilishi take masa, tunda ya shiga be ma san a yanda ya dawo ba, kawai dai ya bude idanun sa yaga kalar aika aikan da yayi mata, wlh da babu jinin ta a jikin sa ze iya cewa bashi bane ya aikata, wannan shine dalilin da yasa ma ya kaurace mata, domin besan da wacce kalma ma ze mata magana ba dan yasan a halin yanzu babu wanda ta tsana sama dashi, duk da shi bai taba bawa wani hakuri ba, zai fara a kanta duk da shidai a iyakar sanin sa ba laifin sa bane, can dai yana ta sake sake a ransa, ya miqe fuskar sa yaje daidai saitin goshin ta ya ajje mata sumba, haka ma bisa kan karan hancin ta da labban ta, jin haka Hafsa ta mirtsika idanun ta, yana ganin haka yace mata
"Bude idanun naki ko Ni kuma in bude Miki da kaina"
Bata san sanda ta bude idan nata ba kuwa, tana me basarwa
Shiru suka yi na kusan minti Uku suna masu kallon idanun juna, a idanun sa tana iya hango, kewa farin ciki da kuma jin dadi, shima kuma a nata yana iya hango hakan, in takaice muku zance, a wannan daren Hafsa da Yarima suka zamo abu ɗaya, a lokacin ne suka fahimci junan su kamar dai yadda ya kamata, a lokacin suka yiwa juna alkawarurruka da dama, a lokacin ne suka fahimci suna cikin matsananciyar begen junan su, sunyi alƙawarin zasu rayu tare sannan zasu mutu tare da izinin Allah.

Da safiya tayi Hafsa se jin kunyan Yarima take, har bata san ma ta haɗa ido dashi, bayan da suka fahimci junan su ne yake ce mata shifa tun da ya shiga sashen Kilishi besan ma inda kansa yake ba har seda ya tashi da safe, a lokacin Hafsa ta dauki aniyar se ta gano Wacece Kilishi.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya zo a zauna zo a saɓa.

______________

Koda Fulani taji labarin kaiwar mutuncin Hafsa, ba karamin dadi taji ba, lalle gara da ta dauki shawaran sarauniya babba yanzu da anyi abun kunya, sannan ta ƙara gaskata maganar ta da tace mata Idriss dinta zai samu farin ciki.

Yau itace da kwana a sashen Mai Martaba, dan haka tana gama shiryawa tayi sashen nasa, neman mata iso jakadiyar sarki tayi, bayan da ta shiga suka gaisa, suka kama hirar su cike da birgewa da kuma so da ƙauna,
Tambayar ta yayi
"Yau naga kamar kina cikin farin ciki"
Da kamar baza ta gaya masa dalili ba sai kuma ta canza ra'ayi
"Ɗazu a kazo aka ce min inzo ai matar Yarima ta kawo mutuncin ta",  ta karashe da murmushi, girgiza kansa me martaba yayi cike da takaicin wannan al'adar, fisabilillah idan abu ya shiga tsakanin ku a matsayin ma'aurata se an sani?
Amma hakan da ya faru yasan ze wanke ta daga zargin da ake mata a cikin masarautar.
Suna kan maganar ta yake ce mata ai shi rabon da suzo gaida shi tare da Yariman tun wata daya da ya wuce, nan tace masa zata kuwa koro masa su, nan suka fara dariya, se ganin Kilishi suka yi akan su
Daman ta saba musu irin wannan katsalandan din, se suna cikin hiran su a kwanan Fulani se kaga tazo, kuma in ka bincika ba wani abu me amfani bane yake kawo ta, amma ita akwai lokacin da Fulani tazo a kwanan ta, bakar magana kam har seda suka yi tsiro akan Fulani, ita Kilishi dalilin da yasa take zuwa tana tsoron ko wani abu Fulani take ma me martaba shiyasa yafi santa, ita kuma sam ba haka bane tsantsar hakurin ta da biyayyar tane ya jawo mata hakan, ficewa tayi bayan ta gama kare musu kallo kamar dai yadda ta saba, ita dai hakan da take tun suna da kuruciyar su yakan bawa Fulani mamaki, amma sai kuma ta share suka cigaba da sha'anin su ita da Mai Martaba.

A lokacin Kilishi ɗakin ta ta wuce cike da baƙin ciki, wlh idan ta tashi tarwatsa ahalin nan baza tabar kowa da rai ba, sannan kapın su mutu se ta basu azaba me tsananin azaba, kuma baƙin cikin ganin ta mulki masarautar nan ita da ƴaƴan ta ne ze kashe su ɗaɗɗaya da ɗaɗɗaya.

______________

3 Months later

Bayan wata uku wanda ya kama watan Hafsa tara da aure, rayuwar da suke sai san barka, maƙiya kuma sede suji kunya, zaune take a dakin shakatawa ta caɓa ado Yarima ya shigo yace ta tashi su tafi lambu su huta, binshi tayi domin wannan ne zuwan su na huɗu tun bayan da suka shirya.
Da suka shiga lambun ya kaita gurin furanni, domin zuwan da suka yi last gurin ya'yan itatuwa ya kaita, Saka bayi yayi suka kawo musu kayan itatuwa suna sha, miqewa yayi ya dauko mata furanni kala kala bata yayi tana shaqar su tana murmushi. Can daga bisani kuma ya fara yaba kyawun da tayi da kuma yadda sarauta ta amshe ta, yana shirin ya fada mata abu na gaba ta katse shi da tambaya
"Kwanaki da suka wuce a baya cemin kayi bani da kyau, wai ina kama da dodanni ko ba haka bane"?
Ɗaga mata kai yayi alamun eh
"Dan Allah mijina ka fada min gaskiya shin ina da kyau ko kuma dai da gaske ina kama da dodannin"?
Juyowa yayi yanda ze fuskan ce ta da kyau kamin yace
"Da za'a jera dukkan kyawawan matan duniyan nan gabaki ɗaya, kuma da za'a ce in fadi wadda tafi kyau, kece zaki fito a na farko da kuma na karshe, idan kuma maganar kyawawan halaye ake, kece zaki take kowa, halayyar ki kuwa itace abu na farko da ya sa na fara sanki, ina matuqar sonki Hafsa, bazan iya rayuwa babu ke ba, ina me roqon Allah da yasa koda mutuwa ce tazo, ta dauke mu a tare, idan kuma mutuwar ta zama wajibi, na yadda in bar duniyan ke kuma ki rayu, ina matuqar qaunar ki Hafsa, Qauna kuma daga Lillahi, Allah ya bar mu tare har gaban abada".
A lokacin da ya ida fada mata haka sai jikin ta yayi sanyi, wato shi wannan munanan halayen nata na rashin ji shine yake burge sa, inama inama, inama ace itama zai fahimci yadda take begensa a zuciyarta ƙila da zai ga ma kamar tafi san shi, sede tana jin wani iri, tana jin kamar kuma baza su rayu taren ba, ita da kanta ta jefa masa zazzafar sumba wanda kamar haɗin baki bishiyar furannin da suke ƙasan sa ya fara zubar musu da nau'ikan furanni masu kamshi da kuma ban nutsuwa.
Abinda basu sani ba, Fulani da Kilishi tare da Sarauniya Babba na daga nesa suna kallon su daman sunzo ne dan su dan tattauna game da yanayin masarautar suka yi wannan gamon, Fulani juyawa tayi cike da kunya ta koma sashen ta, sarauniya babba kuwa murmushi take saki da faɗin "lalle yaran zamani basu da kunya ko kaɗan" a ranta tare da kama hannun Kilishi na ta saki baki ta zuba musu na mujiya, kafarta har karkarwa yake tsabar baƙin ciki.
Wato ita tana can tana fighting akan nema wa yaranta sarauta daga gunsa, shi ya saki jiki se soyayya yake, wlh yanzu zata gun shugaba ta fada masa tashin hankalin da take ciki, ita ta dauka ai tun da ya mata faɗe basa jituwa.


Alƙalamin Fadrees, ƴar mutan Yobe.




44


Wattpad; Fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20


Basu suka bar gun ba seda la'asar, sashen sarauniya babba ya raka ta, inda suka iske Sulaiman da Bilkisu, Bayan Yarima sun gaisa da Sarauniya Babba, suka wuce masallaci shi da Sulaiman din, suma su Hafsan sallan su suka yi, aka kawo musu abubuwan taɓa baki suna ci suna hira a tsakanin su, a lokacin suka fahimci juna ita da Bilkisu, ashe tana da saukin kai da kirki, ita ta dauka duk yaran sarki masu girman kai ne, itama Bilkisun a lokacin ta fahimci wacece Hafsa, nan kuwa suka ɗinke gashi ma cikin ta yayi nauyi, zata ce ma Yarima ya dinga barin Hafsa tana zuwa sashen ta suna debewa juna kewa.
Suna a haka Shamsu ya shigo ya jona su, Hafsa da shamsu suka hade kai sai tsokanan Bilkisu suke da katon cikin ta, ita kuwa kamar zata yi kuka, sarauniya babba ce ke karɓan mata.
Karan budewar kofa suka ji, tare suka juya gaba dayan su, suka ga ashe Hayatu ne, nan kuwa Hafsa ta haɗe rai dan bata manta da kashedin Me girma Yarima ba, shiko kamar ya samu tv ya dinga kallon ta har Bilkisu ma mamakin kalan kallon da yake ma hafsan take, shamsu ne da ya lura da hakan ya ɗan buga sa ya masa ido, duk akan idon sarauniya. Can sega su Yarima sun shigo, shamsu ne suka gaida su, Yarima kam ko amsawa beyi ba se Sulaiman, yana ganin Hayatu kuwa a gun yace ma Hafsa ta tashi su tafi, sarauniya babba ce ta hana ba'a san ransa ya zauna ba, da mangariba ma hada kai suka yi suka fita salla, da suka dawo aka kawo musu abinci da abubuwan taba baki, basu ne suka koma sashen su ba sai bayan Isha.
____________

Kilishi bata zame ko ina ba daga lambu sai dakin ta, Seda ta tabbatar da ta tura ƙyauren dakin nata da kyau kana ta ɓace kogon boka Kapoor, tana bacowa gunsa ya daka mata tsawan da Seda ta girgiza, Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, tayi salati
Ita da ta kawo masa kara kuma ya mata tsawa? Ita da ta kawo korafi? Toh me ya faru, Allah dai yasa lapiya, in dai ba lapiya ba ta shiga ukun ta, domin yaune rana na farko da ta taɓa bata masa rai, yau kam baza ta iya bacci ba sam
Muryar sa wacce take echoing uku uku ne tayi magana kamar haka
"Wannan shine karo na karshe da zan sake tuna Miki da kar ki sake ki sake yi mana salati anan, Kina ina da rashin kulan naki ta ɗauki ciki?", girgiza zuciyar Kilishi tayi
'Ciki kuma? Kai inaa wannan ƙarya kenan, ita ta tabbata bayin da ta saka su aikin sama Hafsan ido baza su taɓa mata ƙarya ba, gaskiya da sake'
Maryar sa me matuqar ban tsoro ta ƙara tsinta yana me cewa
"Gashi a dalilin rashin kulawar ki ta ɗauki ciki sannan baze yiwu a zubda ba, in aka zubda abun ze shafe ki, kawai yanzu za'a jira Gopal ya kawo maganin a aika mata kawai daman yanzu watan shi uku da tafiya, ki ɓace min da gani"
Ya karashe cikin rikitacciyar ƙara.
Ɓaco wa dakin nata tayi ran ta a matuƙar haɗe, bari zata san yanda zata yi ta zubar da cikin kawai.

Bayan anyi haka da wata guda, Kilishi ta baiwa amintacciyar baiwar ta wani magani tace a tabbatar an zuba a abincin Hafsa sannan a tabbatar da Hafsan ta ci shi idan ba haka ba hmmmm, boka ne kaɗai yasan me zata iya aikatawa.
Karɓan maganin baiwar tata tayi hannun ta na matuqar ƙyarma

________________

Zaune Hafsa suke ita da Gimbiya Bilkisu a dakin shakatawar Yarima, daman kusan kullum ita ke zuwa sashen Gimbiyar duba da yadda tayi nauyi, shine yau ta aika mata akan baza ta samu daman zuwa ba, shine ita Gimbiyar tazo ta, suna cikin hirarrakin su aka kawo musu abincin rana, da aka buɗe kwanon farkon wata funkasau ce abun birgewa, ai kuwa se ya shiga ran Hafsa a take, gashi funkason ɗan kaɗan ne, kapın tace a zuba mata, Gimbiya Bilkisu tace a zuba mata ita, Hafsa ne tacewa Gimbiya "Dan Allah Gimbiya ki bar min inci Ni, wlh ya biya raina sosai da sosai, har ina jin in banci ba za'a samu matsala", itama Gimbiyar cewa tayi se taci yaron cikin ta yana sha'awar funkasau, ana haka se Hafsa tace toh suci tare mana, Gimbiya tace ita ɗaya zata ci
Gimbiya ce tace
"Haba matar yaya ki dubeni da tsohon ciki baza kiji tausayi na ki bar min in cinye ba"?
"Wallahi Gimbiya ya shiga raina ne, ji nake in banci ba akwai matsala".
Hafsa ta bata amsa tare da marairaice wa
Jin haka se Gimbiya Bilkisu tace mata "Toh ki cinye din, amma baza kici naman zabuwan nan ba"
Ta karashe da haɗe rai, dan bilhaqqi ya shiga ranta sannan duba da yadda Hafsa ta nace zata ci ne yasa tabar mata, dan bata taɓa mata tana san abu sosai har haka ba sai yau.
Can bayan sunci abinci suna ɗan hutawa lokacin har marece yayi suna kan hira Hafsa ta fara muqurqusu, kafin kace meye Hafsa ta fara ihu tana kuka, kan susan me yake faruwa suka ga jini ya ɓalle mata, lokacin bayi ne kuyangu ne gaba ɗaya an taru ana jira meke faruwa, da ikon Allah ba wanda yayi gigin taɓa ta, Gimbiya Bilkisu se ihu take ma bayi akan su dauki Hafsa amma an rasa me taɓa ta, su tsoron Yarima suke, saboda watannin baya da bayi suka taɓa jikin ta ya basu azaba me tsananin gaske, hadda larai me magani da take mace kuwa, shiyasa dukkanin su suka kasa taɓuka komai.

Suna zaune a fada an kira su shida Sulaiman akan Mai Martaba zai aike su ƙasar chadi, wani bafade ya shigo ya fadi yayi gaisuwa
"Tuba nake ranku ya dade, Gimbiya Hafsa ne a kwance rai a hannun Allah"
Yarima be san sanda ya miqe zeyi waje ba, riqo sa Sulaiman, kana ya neman musu izini daga fada suka wuce sashen Yariman
Yana shiga ganin halin da take ciki besan sanda ya ciccibe ta yayi hanyar dakin maganin masarautar ba, bayi kuwa sai ƙus ƙus ake tayi sede ba me iya magana a fili.
Da sauri Zuwai me magani tazo ta fara bata taimakon gaggawa tare da koran su Yarima da su Gimbiya waje, jiƙa wani sassaqen ta tayi ta bata tasha  a take jinin ya tsaya, fara bincika ta tayi, a ƙalla takai kusan awa tana abu daya, su ko su Yarima da su sulaiman sunyi jugum a waje
Can sega ta ta fito, gaishe da sarauniya tayi dan bata ma san sanda ta zo ba, kallon su Bilkisu tayi kamin tace
"Cikin jikin Gimbiya ne ya kusa zubewa amma da yardar Allah be ƙarasa zubewa ba, za'a barta anan har ta samu lapiya domin kwata kwata juna biyun nata na mako huɗu ne"
Kowa Seda ya cika da mamaki da jin wannan bayani, bayama sarauniya babba da ta kasa gane Hafsa nada ciki bayan ko shekaran jiya Seda suka wuni a sashen ta ita da Bilkisu
Bilkisu da mijinta Sulaiman kamar sun fi kowa murna dajin wannan batu, suna shirin su taya Yarima murna suka neme shi suka rasa, ashe shi har ya shige dakin, yana kokarin ɗaga ta, ma'aikaciyar jinyar ta hana shi, tace masa yanzu ba'a so tana motsa wa, zuwa nan da nan domin cikin ze iya ɓarewa, daɗi kamar ya kashe Yarima wai shine ze zama uba, ita kuma Hafsa da taji labarin cikin da take ɗauke dashi, jikin ta mugun sanyi yayi, nan da nan hawaye ya fara zuba mata, wai yau ita ce Hafsa yar Malam Sule Mai Rini take ɗauke da cikin Yarima, ikon Allah, wa yaga Mama Hafsa amma fa ɗan zega hauka wlh 😂
Fadin irin farin cikin da masarautar ta dauka ɓata lokaci ne, Fulani da me martaba daɗi kamar ya kashe su, on the other hand Kilishi kuma zamu iya cewa saɓanin hakan take a wajen ta.

Seda Hafsa tayi wata guda cur kapın aka sallame ta tare da saka tsattsauran tsaro akan cimar ta da ma komai nata, bayan kwana biyu tace wa Yarima tana so taje gida, da farko ya hana ta dan yana gudun a taɓa lafiyar ta ita da cikin se daga baya ya kyale ta ta tafi, tare da saka kwakkwaran tsaro akan ta domin wasu wani slight chance suke nema dan su taɓa ƙimar sa.

FADREES 🖋️.




45



YARIMAN HAFSA
(A Royal Love Story)
Mallakar Barr. Fatima Idriss Bello



Arewabooks; Fadrees20
Wattpad; Fadrees_20



Ban yadda wani ko wata suyi amfani da wani sashe na littafi na ba, ko ya haɗa min audio ba tare da kwakkwaran amincewa ta ba, idan naga akasin haka kuma, wlh baza mu wanye lapiya ba.




Sanda Hafsa taje gida sai taga kamar komai ya canza mata, sai nannan ake da ita, sannan wannan ne zuwan ta na farko tun bayan da tayi aure, Mama Zenabu kuwa sai ɓoye farin cikin ta take, Habiba itama tazo sun wuni suna hira, itama da tsohon cikin ta, haka zalika Murja da tazo har kwana Seda tayi, Zaliha ma tazo ta, se sussunnad da kai take a haka ta koma, kuma dukkannin su da suka zo gunta Seda ta musu alheri me tarin yawa.
Su Azima kuma biyayyar dole suke mata, ita har mamakin su take, Baba ma sai nannan da Hafsa yake yana sa mata albarka, su Mama Kulu munafukan Allah har kosan siyarwar su suke kawo mata wai ko zata ci ta dena zama da yunwa sannan dama Baba ya hana su sana'ar yanzu yace musu tunda sun samu buɗi su huta amma sunyi kunnen uwar shegu da shi shiko ko a jikin sa dan harkar gaban sa take yi
Kwana goma tayi a gidan nasu, sede ko wane rana Yarima yana kan hanyan zuwa gidan su, wata rana da yazo ƙin fita tayi saboda kunyar Mama dan zuwan nasa har yaso ya kauce wa muhammadiyya, amma shi kuma wai hadda yin fishi, Jamila kuwa an samu abun fada, su Mama Lantana kuwa so suke ma yazo dan alheri yake musu sosai sannan so suke suma ƴaƴan su su samu kamar yariman koma wanda ya fi shi wai sede ba dama, a haka dai aka ƙuƙuta ta samu ta koma.
Bayan komawar ta wata sabuwar soyayyar suka ƙulla ita da Yarima kullum suna manne da juna kamar wasu mayu, wataran ya shirya musu keken doki su zagaya gari, ko su fita da dare suje guri daban daban a cikin garin Bauchi, akwai ranan da suka yi ɓadda kama suka je cin abincin kan hanya, Hafsa ne fa duk take nun nuna masa ire-iren gun nan, hakikanin gaskiya sunyi matukar enjoying, bata mantawa da aka zubo musu yaqi ci wai baya cin ire-iren abincin nan ai kuwa Hafsa a gaban mutane ta dinga basa a baki akayi ta kallon su gwanin ban sha'awa, da suka dawo gida ranan baccin dadi suka yi, duk sanda tayi wani abun farin ciki sai tace a ranta ko su Mama ma suna farin ciki? Oho.
Gaskiya tayi missing ɗin Mama sosai ita da Jamila, har ma da Baba kuwa, sannan kwanan nan sai mafarkin sa take sosai, har ranan tace wa Yarima zata gida, be so ba, ya kaita dai, Kilishi ta dinga baqaqen maganganu wai yawon Hafsa yayi yawa, ba'a haka sam a Masarauta.
Da taje taga Baba yana ta shirye shiryen komawa garin da yake sana'a akan idan yaje zai siyarda kayan sa nacan daga nan baze sake komawa ba ze dawo gida da zama
Kamar ta hana sa tafiya take ji sai kuma ta kasa, a haka ta koma masarauta cike da tunanin sa, lokacin cikin jikin ta watan shi biyar.

Washegari tazo ma dukkan ahalin Malam Sule Mai Rini cikin alhini da baƙin ciki domin gawar Baba aka kawo musu kwance a cikin jini, ashe fatake ne suka tare su a hanya shi da abokan tafiyarsa suka yi musu kisan gilla, an bi bayan su babu su sama ko ƙasa, har aka kaishi aka dawo Hafsa bata sani ba, sede zuciyarta sai tsinkewa yake.

Tana zaune a ɗakin shakatawa tayi tagumi Yarima yayi sallama, gaida shi tayi ya amsa sama sama, se taga yanayin sa kamar jikin sa a sanyaye , ce mata yayi tazo zasu fita, tashi tayi da ɗan cikin ta ta fito ta ɗauki alkyabba ta ɗora akan ta suka yi waje, gani tayi an faka keken doki a kofar sashen nasu, shiga suka yi taga sun nufi hanyar zuwa gida, kirjin ta ne ya fara bugawa da sauri da sauri sede ta kasa ce masa komai, suna karasowa layin su taga kofar gidan su a cike makil da jama'a, fitowa tayi ta shige cikin gidan nasu, taga gawan Baban ta a ajiye za'a yi waje dashi, nan ta zube a gun, dan ko kuka ta kasa yi, ɗaga ta yaya fati tayi suka kama kuka tare, fitar dashi

Please Login or Register in order to submit comment