Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

waje aka yi har a lokacin jini be bar zuba ba. Allah Sarki Yarima ne ya dinga kwantar mata da hankalin tahar ta dawo normal
Haka dai da dadi da ba dadi aka ƙuƙuta akayi arba'in din Baba suka koma masarauta, lokacin cikin hafsa watan shi shida sannan Bilkisu ta haifa ƴar ta an sanya mata sunan mamar Sulaiman ana kiranta Aimana.

Ranan suna zaune ita da Yarima a dakin shakatawar su, yana bata dan labarai haka, ga kansa bisa cikinta wai sai jariri ko jaririya zasu masa magana akayi musu sallama, da kansa Yarima ya tashi ya leqa yaga wani bafade ne, an aiko da ana masa neman gaggawa a fada, sumbatar goshin Hafsa yayi tare da taɓa cikin ta kana ya fice, a hanya ya hadu da Sulaiman suka wuce tare
Bayan da suka shiga cikin fada suka zube suka kwashi gaisuwa, waziri ne yace musu
"Muna so ku shirya tafiya kasar Mali domin a wancan karan da muka so mu tura ku ƙasar chadi sai aka samu akasi, toh lokacin su Galadima ne suka wakilci wannan Masarauta, toh dai wannan abu daban ne ze kaiku, zaku je ƙasar Mali ne dan kuyi gasar rubutu na duniya wanda ake yin zagaye bakwai dan aƙalla zaku fi wata a can, sannan tafiyarku gobe da safe ne inshallah dan an riga da an shirya muku abun hawa ma, zaku iya tafiya",
Fitowa su Yarima suka yi jiki a sanyaye domin shi yana fargaban yabar matar shi ga ciki, shi kuma Sulaiman matar shi watan ta ɗaya da aihuwa kenan, a haka dai suka tsattsara yanda abubuwan su zai tafi, kana suka raba hanya kowa yaje sashen sa.

Koda Hafsa taji batun tafiyar sai ta dinga yi masa kukan shagwaba shi kuma yana bata hakuri, ranan basu rabu ba kaf, haka suka yi spending time nasu kamar dai yadda kowanne ma'aurata masu ɗauke da soyayyar juna suke.
Washegari sammako suka yi suka kama hanya, kwanan su biyu a hanya suka bugo ta wayar tarho suka sanar da sun isa lapiya
Bayan wata guda lokacin cikin hafsa na shirin shiga wata na bakwai, suna tsumayin dawowar su Yarima a kowane lokaci sannan a cikin en kwanakin nan rayuwarta da kowa a cikin masarautar sai sam barka, ko wanne bayan kwana bibbiyu take zuwa ta gaida surukan ta, hadda Kilishi kuwa, ranan da taje aka sake ce mata wai tana bacci kar a dame ta, tayi niyyan shiga baiwar Kilishi ta hana ta, gashi ciki ne a jikin ta baza ta iya fada da ita ba, shawara ta yanke akan da dare se ta dawo taga me kilishi take ƙunsawa, sannan ina take zuwa, dan wadannan tambayoyin sun jima a ranta ta rasa me bata amsar su, a hanyar ta na komawa sashen ta ta hadu da shamsu da Hayatu gaisawa suka yi ita da shamsu kana ta wuce sashen Bilkisu, hira suka jima suna yi, Hafsa ta dinga daukar yarinyar da Bilkisun ta aifa tana mata wasa, seda marece yayi lis kamin tayi niyyar tafiya, koda ta koma sashen ta tayi mangariba sai bacci ya dauke ta a dakin shakatawar, sai bayan Isha can ta farka ta sallami bayin nata, isha ta gabatar kamin tayi dakin Yarima dan koda ya tafi a dakin sa take kwana saboda yana dauke mata kewar sa sosai.

Da shigan ta se tayi sallama duk da tasan babu me amsa mata, da mamakin ta tana shiga se taji an rungume ta ta baya ana shafa cikin ta, juyowa tayi zuciyarta na matuƙar bugawa dan taga wanne kalan ɗan iskan aljanine ze mata haka, tana ida juyowa taga Hayatu.
Fat fat zuciyarta ta kama bugawa, kwace kanta ta soma yi sede ta kasa dan baza ka haɗa karfin me ciki da kuma na ingarman namiji ba, dakyar ta samu ta ƙwaci kanta, yana cika ta ta zabga masa wani mummunan mari, masifa ta fara yi cike da ihu da hargowa
"Baka da hankali ashe? Me kake nufi da zaka shigo har ɗakin aure na ka rungume ni, kuma ina ma matsayin matar yayanka?"
"Koma meye kice, abu ɗaya na sani, ke tawa ce har abada, kuma bazan taba yadda a raba mu ba, wlh koma meye za'a yi sede ayi amma wallahi bazan bar ma Yarima ke ba, sannan ba mari ba koma me kimin bazan taba kyale ki ba"
Hannun ta ya kamo cikin nashi tare da dora kansa bisa kafadar ta, har zata yi ihu ta fasa sbd nan masarauta ne, idan tayi ihu asirin ta ne ze tonu dan mutane cewa zasu yi ita ta kirawo sa dakin ta".
"Hayatu kake ko waye ka fita tun kamin raina ya ɓaci"
Ƙeƙam yayi, yaqi koda motsawa ne, sallaman shamsu suka ji, daman tunda yaga yanayin Hayatu dazu yasa masa ayar tambaya, shiyasa ma ya biyo bayansa, yana shigowa yaja hannun sa akan su tafi, dakyar da siɗin goshi yayi nasarar cire hannun sa a jikin na Hafsa, ficewa suka yi a tare, abinda su Hafsa basu sani ba, ashe akwai wata kuyanga ata bayan windown dakin tana sauraren duk abinda aka yi

FADREES 🖋️
Ƴar Mutan Yobe.





46



YARIMAN HAFSA
(A Royal Love Story)
Mallakar Barr. Fatima Idriss Bello



Arewabooks; Fadrees20
Wattpad; Fadrees_20



Ban yadda wani ko wata suyi amfani da wani sashe na littafi na ba, ko ya haɗa min audio ba tare da kwakkwaran amincewa ta ba, idan naga akasin haka kuma, wlh baza mu wanye lapiya ba.



Ganin haka Hafsa sai ta zauna akan gadon Yarima tana me maida numfashi, wannan wane kalan abu ne, qanin miji da son matar yayan sa?, miqewa tayi kuma da nufin taje har sashen mahaifiyar sa takai mata karan sa akan ta jawa danta kunne, isarta keda wuya taga amintacciyar baiwar ta, a kofar gun tana gyangyadi, Hafsa ne tace mata tazo gun Kilishi
"Tace duk wanda yazo ace tana hutawa kar a dame ta"
Inji baiwar
Hafsa ne ta cika da mamaki, yanzu fa karfe takwas na dare ne, in hutawa zata yi ta bari sai dare yayi mana, ita dai yau tayi alkawarin wlh seta shiga dakin ta taga ina take zuwa, sannan ta ina take zuwa, ko kuma taga ta inda zata dawo.
Bata yi wani cece kuce da baiwar ba tayi waje abinta, ganin ta fita baiwa ta koma ɓingira baccin ta cikin kwanciyar hankali, dama kashedin da Kilishi ta mata, specifically akan Hafsa ne, ita kuma Hafsa yi tayi kama ta tafi ashe ta tsaya ata gun ƙyauren tana kallon sanda baiwar ta ɓingire da yin baccin, tana ganin haka tayi wuff cikin sanɗa sanɗa ta bude ƙyauren uwar dakan Kilishi ta shige, da shigan ta se taga ba kowa a ciki, leqa makewayi tayi taga ba kowa still, tsayawa tayi, can kuma se ta kama dube dube ko zata ga wani abinda ba shine ba, karkashin gado ta leqa taga ba komai, can kuma taga wani guri kaman an shafe da taɓo, nan da nan ta zura hannun ta ta fara tono gun, wani kyalle ta ciro, wai ta ɗan ɗaga shi kadan taga jikin sa da rubutu sede bata san meye ma'anar kalaman dake jiki ba, karanta wa ta soma yi, se gata a kogon boka Kapoor.
Wa yaga tashin hankalin da ba'a sa mata rana.
Ɗaga idonta ta fara yi taga gun duhu ne zalla babu alamun haske, gashi ko tace zata koma ma bata san hanyar da zata bi ba, fara tafiya tayi tana ta kutsa kanta a cikin kogon, wai ko zata samu hanyar komawa, dan ita kam ta fara tsorata da lamarin Kilishi, ta hakura da bibiyar ta kawai, cigaba tayi da tafiya, tayi tafiyar kusan minti ashirin sa'annan ta hango alamun wani haske, kutsa kai tayi kana tabi gun hasken, Ya subhanallahi me zata gani, sai ba ga Hafsa ta fara cin karo dasu kayukan kwarangwal ba, wani gun taga hannu ne ba jiki, wani gun kuma jiki ne ba kai ba hannaye suna motsi wasu har zuwa gunta suke da niyyar su tsorata ta, abubuwan dai da ta gani na ban tsoro basu ƙirguwa a gun, ci gaba tayi da tafiya, nan ta fara ganin launukan aljannu, wasu kamar rayuwar ruwa wasu kamar dodanni, tana isowa gun wani katon abu shi girman sa yafi na drum, leqawa tayi se taga kamar wasu mami water ne suke shawagi a ciki, wata halitta ta gani a durqushe tana bauta wa wani wargajejen halitta da yaje zaune akan wani wargajejen kujera da kan Giwa da kuma kan zaki ata bisa kujeran, wai da juyowan matar ba sai ta kalla Kilishi bace?, kafar tane ta fara rawa dan ji tayi kamar ma wani abu na bin ƙafan ta, ita tunda take zata iya rantsewa da Allah bata taɓa ganin tashin hankali irin wannan ba, kai ko a labari bata taɓa jin irin wannan ba, sannan ita ko a lokacin da take rashin jin ta Mama tasha ce mata wataran ai seta mari ɗan aljani sbd muguntan da take wa yara, amma bata taɓa ganin aljanin ba sai yau kuwa, wani mahaukacin tsawa da dariya aka saka a tare wanda seda hantar cikin ta ta kaɗa, wargajejen halittan ne ya fara dariya da Muryar sa me uku uku sai kuwa aljanun suka fara taya shi, ita Hafsa mamakin abinda ya kawo Kilishi nan gun take dan a yanayin da taga kilishin taga kamar ta saba zuwa nan, tsaya, kodai cewar da take zata yi bacci kar a dame ta nan take zuwa su kuma in suka je se suga ba kowa a cikin uwar dakan nata.

"Gane ganen ki da kwakwaf ɗinki ya jawo miki bala'i yarinya"
Ta jiyo murya me uku uku ta mata magana
Nan take tsoro ya kama Hafsa ta fara addu'a
"Addu'ar ki a banza yarinya, duba kiga nan, ta daga idon ta taga inda yake nuna mata, gata nan a kwance akan gadon Kilishi
"Kamar dai yadda kika ga nan, ruhin ki ne ya taho nan, gangar jikin ki yana nan akan gadon ƴar ɗagas (wato Kilishi kenan)
Saboda haka keda komawa masarauta har abada domin kushewar ki kika zo da ƙafan ki, sannan daman kin jima kina ɓata mana shiri dan haka a cike muke da ke, sannan gangar jikin ki zeyi ta zama a dakin ƴar ɗagas babu wanda ze taɓa tambayar ki har abada ciki har da uwarki kuwa da ta haife ki bare wani karamin alhaki wai shi Idriss

Shimfide wa kilishi tayi a ƙasa, tana me neman afuwa
"Dan girman tsafin ka shugaba kayi mata rai, in yaso sai a rufe bakin ta ita, domin idan aka ce za'a rufe bakin kowa ina me tsoron kar bakin sarauniya babba yaqi rufuwa"

Daka wa Kilishi tsawa kafoor yayi, kapın yace mata
"Ba'a katse mu idan muna magana, munfi karfin kowa a duniyar nan bare wata tsohuwar banza, amma tunda kince haka , sannan kina bin dokokin mu, za muyi considering Naki, saboda haka za'a rufe bakin nata yanda baza ta iya gayawa kowa ba, zuwa nan da wata biyu lokacin da gopal ze dawo kenan, sede aljanu na sun kwadaitu da wannan ƴan biyun da suke cikin ta, dan kinsan nasha ce miki jinin sarakai daɗi gareshi, sannan wadannan naga taurarin su masu matukar haske ne sosai, in yaso da an dasa mata maganin a kirjin ta se su shanye jinin jariran in yaso zata bakunci lahira"

Ajiyar zuciya kilishi ta sauke, durqusawa tayi, ta ma shugaba Godiya, nan da nan suka ɓaco ɗakin nata, numfashi gangar jikin Hafsa ya ja, nan da nan ta miqe tana me kokarin zama, sake tunano abinda ya faru yanzu tayi, Innalillahi ashe dama Kilishi kafira ce? Toh wallahi basu isa ba dan ƙundun ubansu, daga ita har bokan duk tafi ƙarfin su, wlh a haka zasu barta su kyale ta, ƙurwar ta ƙur, daga zuwa ta mata kashedi akan danta se ta wani ce wai cikin jikin ta nasu ne harda cewa wai ƴan biyu ne a cikin ta?
Can dai daga bisani kuma da ta dawo daga duniyar tunani ta kalli Kilishi cike da baƙin ciki da kuma tsoron Allah, ta jefa mata tambaya kamar haka
"Meyesa? Meyesa kika saida imanin ki Kilishi? Akan abun duniya. Har yanzu Kyallen kuma yana hannun ta.

Dariyan mugunta Kilishi ta saki kapın tace
"Da farko babu ke a cikin lissafi na amma ganin kin sako kanki da kanki ina maraba da haka, farko daman na tsani waziri, sannan na tsani me martaba, yanzu jira nake in fara gama wa dake dan yanzu kece matsala ta, in yaso zanzo in kashe su ɗai ɗai da ɗai ɗai, in kwace Sarautar in baiwa ɗaya daga cikin ƴaƴa na, sede kuma na fara tantama, gaskiya bana so in baiwa ƴayána domin har yanzu jinin me martaba ne zai mulki masarautar nan, inaga kawai zan mulki ƙasar Bauchi da kaina, amma kuma jama'an ƙasar Bauchi baza su yadda ba koh? Toh inaga zan rupe bakinsu da taimakon shugaba, amma kuma ina san ƴaƴa na zan dai duba in gani".
Ta karashe cike da sakin wani ƙayataccen murmushi.

To say that she's shocked is understatement, bi ma'ana idan akace Hafsa bata kaɗu ba ma ɓata lokaci ne, wato dai kallan kitse take yi wa rogo, Haƙiƙanin Gaskiya Kilishi ba mutum bace, sam sam ita ba bil adama bace, sai dai wata halittar daban

Ba tare da tace mata komai ba ta sake damqe Kyallen a hannun ta da kyau ta miqe da ɗingishi tayi hanyar fita, har tazo gun ƙyauren tace wa Kilishi
"Ki hawai ɗanki Hayatu kunne, domin yana shiga gonar da ba tasa ba"
Tana karashe fadan haka ta wuce sashen ta, tana zuwa wani bafade yace sarauniya babba tace ta koma sashen ta da zama daga, tana kan hanyan tafiya taji ana maganan ta ita da Hayatu.
Wannan Kenan

FADREES 🖋️ Ƴar Mutan Yobe.



47



YARIMAN HAFSA
(A Royal Love Story)
Mallakar Fatima Idriss Bello



Arewabooks; Fadrees20
Wattpad; Fadrees_20



Ban yadda wani ko wata yayi amfani da wani sashe na littafi na ba, ko ya haɗa min audio ba tare da kwakkwaran amincewa ta ba, idan naga akasin haka kuma, wlh baza mu wanye lapiya ba dan haka a kiyaye.


Ashe wanda ta laɓe tana jin conversation nasu da Hayatu har taje ta baza a cikin masarautar.
Tashin hankalin da ba'a sa masa rana kenan
Bafaden ne ya hadu da wasu fadawa biyar suka raka ta sashen sarauniya babba, zuciyarta ba abinda yake sai bugawa, dan wannan babban al'amari ne, yanzu idan suka mata mummunan fassara fa? Ƙarasawa cikin dakin shakatawar sarauniyar tayi jikin ta a sanyaye, koda ta saka kafar ta, se taga Bilkisu a zaune ga aimana a hannun sarauniya babba tana mata wasa
Zubewa tayi ta kwashi gaisuwa a gun Sarauniya Babba, tambayar ta tayi ya nauyin jiki tace mata da sauki, sai a sannan suka gaisa da Bilkisu tana ta tsokanan ta wai maman jinjira.
Ita dai shiru tayi tana mamakin dalilin da yasa basu nuna mata komai ba dangane da abinda ya auku ɗazu ba, wanda ko ƙaffara baza tayi ba labari ya riga da ya iso musu, sarauniya babba ce tace mata tazo ta zauna a kusa da ita, matsowa gunta tayi sede silent treatment din da ake bata ya fara gundurarta
Muryar sarauniya babba ta jiyo tana me ce mata
"Kar ki saka hakan a ranki jikata, domin na saka wani bawa akan ya dinga kula dake, toh akan idon sa aka yi komai shine yazo ya sanar min, sannan jakadiyar sashen nan tazo itama ta sanar min sede ita akasin hakan ta fada min"
Nan da nan Hafsa ta sauke ajiyar zuciya, haduwa suka yi suka dinga hirarrakin su har seda dare ya tsala kapın suka shige wani ɗaki a sashen nata da ta ware musu su biyu suke kwana a ciki.
Wani abinda ya damu Hafsa kuma shine dakyar tayi bacci dan se ganin waɗannan aljanun da ta gani a kogon Boka Kapoor take tayi, wlh ikon Allah ne kaɗai yasa bacci ya dauke ta, a baccin ma babu kalar mafarkin da bata yi ba, haka ta dinga zabura har seda Gimbiya Bilkisu taje ta kira sarauniya babba suka mata addu'a
________________

Kilishi dariyan mugunta tayi jin abinda Hafsa ta gama fadi yanzu
'Wai ta ja ma ɗanta kunne'

Wato ta raina ta ma, kenan tana nufin ko kapin taga kogon boka Kapoor da haka zata gaya mata? Tana matsayin Kilishi, matar babban Sarkin da yafi sarakuna da dama martaba da sarauta? Lalle kam
Daman tayi niyyar yiwa Hayatu tsakani da ita koda bata same ta da hakan ba, amma samun nata da tayi da hakan ma ya taimaka, domin ƙara tsanar ta tayi, inba ƙaddara ba me zeyi da ita, ko yanzu yace yana san ya'yan sarakuna mata har goma a take ze samu ai, bare ita wata wawiya ƴar talakawa? Kyau ne kawai zata nuna musu, ba komai ba, sai kuma jakanta dan ta lura yarinyar jaka ce kuma makira ce
Toh ita meye nata na ɓata rai ma akan Hafsan da ta kusa ziyartan lahira? Meyesa za tana wani ɓata ranta, mtchewwww🙄
Miƙewa tayi tayi sallan Isha kamin tayi kwanciyan ta abun ta, bata jima ba kuwa bacci yayi awon gaba da ita cike da mafarkai masu dadi domin burikan ta da tayi shekaru tana alwashin çıkan su sun kusa cika da yardar shugaba.

________________

Washegari da tashin hankali aka tashi dan Hafsa fusge fusge ta dinga yi, lokaci ƙalilan kaga tana a hayyacin ta, lokaci ƙalilan kuma kaga ta birkice, mutane suka dinga cewa rashin mahaifin ta ke damun ta, wasu kuma suce kewar Yarima ne yake damun ta.
Rashin lafiyar Hafsa har ya kaiga tana yin abu taga kamar bata yi ba, sannan wani abin sai taga kamar tayi su, bayan bata yi hakan ba, sede akwai abu guda, baza ta iya gayawa kowa hakikanin damuwar ta ba, dan tasan ma ɓata lokaci ne hakan, akwai wai sanda ta dauki aimana da niyyan tace 'kogo' wai tunda yarinya ce ai bata san me ake nufi ba, amma kamar me? Bakin ta se ji tayi ya liqe ta kasa furta komai, da Kilishi tazo duba ta harda ƙwallan ta na munafurci, Fulani kuwa tashin hankali suka shiga ita da sarauniya babba, nan aka fara neman mata magani, dan likitocin masarautar sun kasa shawo kan matsalan nata, a haka dai wannan yazo ya gwada wannan ma, sede ta ɗan samu sauki amma tana samun sauki in ya tashi tashi mata se yafi na jiya, akwai ranan da ta kwana ta wuni ma bata san inda kanta yake ba
Kuma duk hakan aikin Shugaba ne, idan suka bude madubin tsafin su ma suka ga yanda ake shan wahala da ita, sun dinga dariya da aljanun sa kenan.

BAYAN SATI BIYU

Bayan makwanni biyu su Yarima suka bugo wayar tarho suka sanar da dawowar su nan da kwana biyu, bayan tarin nasarori da suka kwaso wa ƙasarsu ta Bauchi, ilai kuwa, kwana biyu suka kara se ga tamburan kiɗe kiɗe da kuma bushe bushen dawowan su, garin Bauchi ne ya hargitse da jama'a na tarban yariman su da yayi makwanni da barin kasar.
Suna shigowa masarautar aka wuce fada dasu, daman rana ce me martaba be bar fada ba tukunna, bayan sun miqa gaisuwa suka gabatar da sakamakon sakonnin da suka kawo, bayan an sallame su suka raba hanya kowa ya wuce sashen sa
Fadawa ne a bayan Yarima suna take masa baya, yana zuwa sashen sa yaga da kwaɗo har gun ya ɗan fara kura kamar ba kowa, juyawa yayi ya fice yaje sashen mahaifiyar sa, gaida ta yayi, suka ɗan taɓa hira duk hankalin sa baya jikin sa, gashi baze iya tambayan ta Hafsa ba, can dai da yaji bata masa magana ba sai ya miqe da niyyan yaje sashen Sarauniya Babba ya tambaya ko dai lafiya, ita kuma Fulani a zaton ta gun Hafsan ma ya fara wucewa shiyasa ko maganar ta ma bata masa ba, dan bata so ta karya masa gwuiwa, dan a yanayin da ya shigo zaka fahimci kamar hankalin sa baya jikin su
Fadawa ne suka take masa baya har ya karasa sashen sarauniya babbar, yana shiga yaga Bilkisu da mijinta suna zaune a ɗakin shakatawar tata, hannun Sulaiman din dauke da aimana sannan a lokaci guda suna hiran su ƙasa ƙasa, ƙarasawa gun nasu yayi gaishe shi Bilkisu tayi ya amsa a sanyaye, karɓan aimana yayi yana ta kallon ta yana me sumbatar goshin ta, hakika shima in Hafsa ta haifo musu nasu haka ze dinga ɗaukan ɗan ko ƴar yana mar wasa, ji yayi kawai bari ya tambaye su ina sarauniya babbar ko Hafsa, yayi kewarta sosai, kullum da ita yake kwana yake tashi, sannan yana so yaga yaya lafiyar jinjirin su, yana so yaga shin suna cikin koshin lafiya ne?, be gama tunanin da yake ba yaji an fara ihu daga wani daki ata gefen uwar dakan sarauniya babba, ko karan hauka ne ya cije shi yasan Muryar Hafsa.

Da hanzarin sa ya ƙarasa shiga ɗakin yayi kiciɓus da abinda ya matuƙar daga masa hankali fiye da tunanin me tunani.
Hafsa ya gani tana ta fusge fusge, tana ta sambatu, ƙarasawa yayi gun ta, alamun ta ya nuna kamar ma bata san waye akan ta ba, hawaye ne ya fara zirara daga idanun sa, juyawa yayi da niyar ya fita, zeje shi duk inda yakamata yaje dan ya sama mata lapiya, yazo fita Sulaiman ya riqe masa hannu, fita suka yi Sulaiman ya kira wani amintaccen bawansa yace masa suyi shiri shida tawagar sa yanzu yanzu su kama hanyan Ƙasar Yobe, yaji labarin akwai wani shahararren malamin gargajiya da dadewa acan, duqawa bawan ya masa, shi kuma ya jinjina masa kai alamun ya amsa, ko awa ɗaya basu kara ba amintaccen bawan nasa me suna Hamisu, suka kama hanyan Yobe.

FADREES 🖋️🖋️🖋️




48



YARIMAN HAFSA
(A Royal Love Story)
Mallakar Fatima Idriss Bello



Arewabooks; Fadrees20
Wattpad; Fadrees_20



Ban yadda wani ko wata suyi amfani da wani sashe na littafi na ba, ko ya haɗa min audio ba tare da kwakkwaran amincewa ta ba, idan naga akasin haka kuma wlh baza mu wanye lapiya ba dan haka a kiyaye.



Kama hannun Yarima Sulaiman yayi suka koma dakin, Mai Martaba da kansa ya aika a kira masa limamin garin, yana zuwa suka fara ma Hafsa addu'o'i shida almajiran sa, se can maraice lis, Hafsa ta farfaɗo, a take kowa ya fice a dakin bakin su dauke da fatan alheri da kuma farin ciki
Wani wawan runguma Yarima ya bata, kamar wadda ake shirin kwace masa ita, da Hafsa ta raba jikin ta da nasa sai taga hawaye yana zirara daga idanun sa, Allah Sarki tayi missing nasa sosai, so take ta fada masa halin da ake ciki akan Kilishi sede ba dama, itama hawaye ne ya ziraro a fuskan nata, ya shiga goge mata, suna a haka sarauniya babba ta shigo tana tambayan sa ya jikin Hafsan yace mata da sauki, cewa tayi yaje yayi Sallah lokacin mangariba yayi, ficewa yayi yana me waiwayen ta, Allah Sarki Hafsan sa, ashe jinya take yi shi kuma yayi tafiyan sa ya barta a cikin wahala.
Sai da ya jira akayi Isha ya dawo, sarauniya babba ce tace masa yabar Hafsa a sashen ta zuwa sanda Malami daga Yoben zai zo kapın nan zasuga abinda Allah zeyi, be musa mata ba ya gyara musu shimfida shida Hafsa suka kwanta, dora kanta tayi bisa kirjin se shi kuma hannun sa bisa cikin ta, bacci ne me dadin gaske ya kwashe su basu ma sani ba, sarauniya babba ce ta ɗan leqo taga yaya, da taga haka ta juyo da baya, ta koma dakin ta itama ta kwanta, Bilkisu kuwa tun da akayi mangariba suka musu sallama suka wuce sashen su.

____________

A kogon boka Kapoor kuwa ransa ne ya ɓaci ganin daga dawowar su Yarima har sun fara aikan nemo malamai, bayan da kansa ya rufe tunanin en masarautar gabaki ɗaya akan kar ma ayi zancen nemo wani wai malami, Kilishi ce ta ɓaco, ta kwanta flat har ƙasa ta kwashi gaisuwan sa, tare da fada masa wai an tafi ƙasar Yobe dakko wani babban malamin gargajiya dan a duba me yake damun Hafsa

Dariya me matukar ban tsoro da Muryar sa me uku uku ya saka kana yace
"Gobe nan da marece ma bayin suna gaban malamin, sede har yanzu shawara ne ban yanke ba, shin in kashe malamin ne ko in bari yazo ya kuma kasa bada maganin? Kawai zan barshi yazo ya bata maganin,

Please Login or Register in order to submit comment