Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke wakana,  ai nan take ta zube ƙasa a take, wani irin ihu suka ji an saki, daga nan shigowan sarauniya babba da Maimartaba da Fulani da  kowane member na gidan suka gani nan take Hafsa ta sume dan firgici
Shi kuma gogan tsaye yake ƙiƙam fuskar shi ba annuri kamar kullum, sannan ko da wasa babu alamun tsoro a tattare da shi.
Juyawa mai martaba yayi suka hada ido da Yarima kapın yace kowa ya same sa a bangaren sa bayan Isha.

Fita kowa ya fara yi daya bayan daya aka bar Sarauniya Babba da Fulani
Sarauniya Babba ce ta karaso daf inda Yarima yake tsaye tace masa
"Ka sake yin tunani akan abinda na fada maka, domin a gaɓar da ake ciki yanzu, komai yana iya caɓe maka, Ni kuma bazan iya yi maka komai ba". Da fadin hakan ta juya sai Fulani da ta tsaya tana kallon sa hawaye taf idanun ta, tabi bayan Sarauniya Babba.
Shiko gogan yadda kasan ba abinda ya dame sa, hasali ma shi ba wani damuwa yayi ba kawai dai ya jinjina wa makirci ne irin na Kilishi, kenan duk abinda ke faruwa idon ta akansa yake, wuce wa yayi ya dakko ruwa ya watsa wa Hafsa, a firgice ta farfaɗo zuciyar ta ba abinda yake sai bugawa, tallafa mata yayi ta tashi ya maida ita kan wani shimfida mai laushi dake nan cikin dakin shakatawar, shi kanshi in an tambaye sa dalilin da yasa yake hakan baze iya fada ba, kawai dai yasan cewa yana da sanyin zuciya ne.
Wucewar sa makewayi yayi, dan yayi alola yayi sallan mangariba.
_______________

Ana yin sallan Isha sai ga kowa a sashen Maimartaba an hallara ana zaune, zaman jiran aji mai zai ce.
Can aka ga shigowar sa, kujera ya samu ya hakimce a kai, daga gefen sa Waziri Jafar ne zaune akan kujeran sede girman nasa be kai na Mai Martaba ba, se kuma sarauniya babba da ita ma take a kan nata kujeran, matan kuma akan tumtum suke zaune, sai matasan da su kuma suke zaune akan kafet.

Da addu'a aka bude taron kapın waziri ya fara koro jawabi kamar haka
"Munji labarin komai da yake wakana tsakanin wata baiwa da Yarima, kwanaki munji hatsaniya a sashen Mai Babban daki, akan Yariman Gobir da Hayatu da Yarima akan wata baiwa, wadda dakyar aka samu magana ta lafa a cikin masarauta domin kimar Yarima har ta so ta ragu a idon mutane domin kalar labarin alakar rashin mutuncin da yake tsakanin Yariman da ita baiwar da ake magana, mun kira sa har nan bai ce komai ba, daga nan aka rufe maganar kwata kwata, domin an fara tsegumi mara dadin ji a cikin bayi.
Sai yau kuma da Amaryar Mai Martaba Sadiya ta aika da kowa yazo Yarima yana lalata da wata baiwa, wanda ka'idar masarautar nan ne, bayi mata basa ma yaran sarakuna maza hidima, tsakanin su dafa abinci ne, su baiwa amintaccen bawan sa ya kai masa, sai muka samu akasin hakan domin ita wannan baiwar da ake magana akan ta, ita ke masa ko wane irin hidima. Da Sadiya ta aika da aje sashen Yarima a ga meke faruwa mun dauka kawai dai ta fada ne, domin tace mana tasha kiransa tana masa nasiha ya sallame yarinyar yayi biris da ita, daga karshe har ya so ya mata rashin kunya ma. Toh zuwan da akayi yau kowa ya ga a yanayin da ya gansu, wanda kowa yasan hakan bai dace ba, saidai bamu gansu ido da ido suna aikata wani abinda bashi kenan ba. Saboda hakan ne ma, yasa muka zartar da hukunci akan Yarima da ita baiwar.

Hukuncin mu shine za'a tsare Yarima na wata daya a sashen sa, ba tare da ya fita ba, ita kuma baiwar an sallame ta daga aiki a wannan masarautar.
İdan akwai me korafi zai iya yin magana".




>>>>>>>>>>>>>🖋️💻







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss🖋️🖋️
09020588802
Wattpad; fadrees_20


Page 18


Kilishi ce ranta yayi mugun ɓaci, ita sam ba haka ta so ba, ta so a kwace matsayin sa na Yarima Mai jiran gado a bawa daya daga cikin ya'yan ta, amma hakarta be cimma ruwa ba, dole se ta koma wajen Shugaba, babu yanda za'a yi tabar ahalin nan a haka, dukda tana jin haushin cewa yaran nata suma jinin Mai Martaba ne, amma dai ai ance da babu gwara ba dadi kuma ko ba komai itama ai jinin ta ne, kuma sai yadda ta so tayi da su.

Can dai ranta a hade tace tana da magana
Waziri yace an bata dama
Se tace "İna mai neman alfarmar da ayi ma Yarima sassauci ba dan halinsa ba, sannan ba wai na fada hakan bane dan a tozarta shi, na fada hakan ne dan ayi masa gyara, domin Yarima tamkar ɗa yake a guri na, soyayyar da nake nuna masa ko mahaifiyar sa saidai hakan, na gode Mai Martaba".

Ran Hayatu da Shamsu sai da ya ɓaci jin irin abinda mahaifiyar su ta jawo, abinda tayi wa dan uwansu sam basu ji dadi ba, sannan shi Hayatu shima ai abin ya shafe shi tunda shima ai yace yana san ta, amma da aka tashi aka rufe nasa sai na Yariman da aka fadi

Hayatu ne yace yana da magana, Kilishi wani irin mugun kallo take aika masa, daman tana kule dashi kan labarin da taji akan wai yana san baiwar Yarima, yanzu gashi zai sake kwapsa mata, ita ba abin ta hana shi magana ba, kar ma a zarge ta, shi ko Hayatu yaqi hada ido da ita kar ma kwarin gwiwar sa ta karye.
Waziri ne ya basa daman magana.

Duk abunnan da ake Fulani Hauwaó hawaye take zubar wa ita da Bilkisu, Samira kuwa cewa take in ta hadu da baiwar se na lahira yapı ta jin dadi wlh

Sulaiman kuwa da sarauniya babba idanu kawai suka zuba, Mai Martaba kuwa ba'a gane expression nasa shi kuma waziri idanun sa tausayin Yarima ne fill a kwance. Shi kuwa uban gayyar ko ajikin sa, hasali ma shi ya gaji da zaman da ake, ya matsu ya koma yaga halin da Hafsa take ciki, sannan in ya tuna ance zata bar masarautar se yaji hankalin sa na matukar tashi, gaskiya yana san baiwar shi ta cigaba da masa bauta, shi bai damu da rashin jin nata ba ma.

Muryar Hayatu akaji yana cewa
"Allah ya baka nasara, idan akwai wani mai laifi toh ba kowa bane, face ni, domin nine na fara tada harzomar nan, dan nine nace ina son ta, shi Yarima ba sonta yake ba ma kawai yana hakan ne saboda aƙidar sa na baya san wani ya mallaki abun sa kuma ko tambayar sa ayi gashi nan zai maimaita abinda nace ne, sannan ko a yanzu ina mai neman iznin Mai Martaba da ya bani dama in nemi auren ta, domin....." Kasa ƙarasawa yayi sbd kallon gargadin da Kilishi take jifan shi da shi idon ta kaman ya fado kasa saboda harara gashi nan yayi jazur dashi sosai, ita ji tayi ba'a taɓa tozarta ta irin na yau ba, da Yarima ne ya fadi haka sai tafi kowa jin dadi, amma jin hakan a bakin gudan jinin ta seda ta girgiza, duk da taji labari a wajen wata amintacciyar baiwar ta bata yadda ba, dan saida ta sa aka hukunta baiwar, yau gashi nan ya gama ci mata mutunci a gaban makiyan ta, babu wanda yapi bata haushi kamar waziri, murmushi ta gani kwance akan fuskar shi wanda ta tabbata ita ba alheri bane a gurin ta, wlh ta tsani wazirin nan, ita wallahi bata ƙi ya dena numfashi ba shida Yariman, ta tsane su wlh tsana mafi muni
Takai sunayen su gun shugaban ta Boka Kapoor, amma komai yaqi aiki a kansu, shiyasa jiya da taje gun shugaban ya bata shawaran tayi da tunanin ta, amma dole zata koma yau, dan ta bada sunan baiwar.

Muryar waziri taji yana magana kamar haka "Za'a sake bincike game da abinda ka fada Yarima Hayatu, domin kazo da abun dubawa, idon babu mai magana kowa zai iya watsewa, hukuncin Yarima Mai jiran gado zai fara daga yanzu".
Nan da kowa ya miqe ya fara fita daya bayan daya.
Aka bar Mai Martaba da Waziri da Sarauniya Babba dan su tattauna.
________________

Kilishi tana shiga sashen ta ta kulle nan ta nan ta dakko turaren ta na tsafi ta turara sai gata a kogon boka Kapoor. Sujjada ta fara masa kapın ya saki wata dariya mai bala'in tsoratarwa can kuma da ya gama shan kamshin sa yace mata "kije bukatar ki tabbatacciya ce" kapın ma ta masa magana taga har ta dawo dakin ta. Ranan kwanan baƙin ciki tayi farin cikin ta daya shugaban ta ya mata alkawarin biyan buƙatar ta.

_____________

Samira kuwa da suka fito ta kama hannun Bilkisu suka ɗan ja gefe, nan suka maida abinda ya faru, Samira tasha alwashin kapın baiwar ta tafi gobe sai ta sa an canza mata kamannin ta, ita kuma Bilkisu cewa tayi "Kawai ki gyale ta Samira, meye amfanin duba bayan hari, gobe in tabar masarautar nan fa har abada baza ta sake dawowa ba".
Budan bakin Samira sai cewa tayi "wane irin baza ta sake dawowa ba? Yarinyar da kika ji Yarima Hayatu yana cewa zai aure ta? Toh wai ma, me take da shi ne da suka rikice haka ne? Ko dai kyau gare ta kamar aljana, kodai asiri ta musu ne bamu sani ba"?.
Bilkisu ne tace "sai Allah, kedai kawai kizo mu wuce ita ta sani". Nan taja hannun Samira suka tafi ba dan ta so hakan ba.

_________________

Shamsu da Hayatu kuwa bayan fitar su sashen su suka wuce, Shamsu se masifa yake wa Hayatu akan meyasa shi baya daukan shawara "kai Hayatu banda rashin hankali ina kai ina baiwa, baiwar ma ta Yarima? Last munyi magana dakai nace ka cire ta a ranka, amma ka ƙeƙashe ka ƙi, yanzu tsabar rashin hankali har da fadin kana san ta a gaban Maimartaba, kai a zaton ka hakan da kayi daidai ne? Sannan Umma baza ta taba yadda da hakan ba, wai shin ko dai asiri baiwar nan ta maka ne nikam"? Ya karashe maganar sa yana zama akan gado tare da yin tagumi.
Hayatu ne yazo kusa da shi ya dora kan sa akan kafadar Shamsu yayi shiru sai can yace
"Ka fahimce Ni mana Shamsu, idan kai baka bani goyon baya ba waye zai bani? Kap duniyar nan bani da wanda ya kai ka, sannan Kai kanka ka gani, Allah ne ya dora min son ta, ba yin kaina bane, idan akwai wanda bai damu da sha'anin mata ko wani abu ba, toh nine, nidai ka bani goyon baya, in mallake ta, sannan Umma tana san abinda muke so itama zan fahimtar da ita, kuma Ni ba wanda ya min asiri, soyayya ce kawai daga Allah" ya karashe yana mai ajiyar zuciya.

Shamsu ne ya nisa kapın yace "idan Yarima bai Amince ba fa"?
Sai Hayatu yace "ai shi ba sonta yake ba kawai dai aƙidar sa ce, sannan shima zan fahimtar da shi, kaima sai ka taya Ni fahimtar da shi din".
Shamsu sai ya sauke ajiyar zuciya yayi masa tambayar da ya girgiza shi "idan kuma Yarima son ta yake kuma yana da niyyar auren ta fa kawai dai bai fahimta bane?"
Hayatu shiru yayi ya qurawa Shamsu idanu baya ko kiftawa.

_________________

A bangaren Yarima kuwa, shida Suleiman da masu take musu baya suka wuce sashen Yariman. Suna shiga suka tarar da Hafsa har yanzu a kwance take a inda ya ajiye ta koh motsi bata yi.
Ruwa yaje ya dakko ya watsa mata ta tashi a firgice, zata yi ihu ya daka mata tsawa, har se da ta firgita, da Sulaiman yaga haka nan ya dafa kafadar sa alamun ya sassauta.


Hakkin Mallaka nawa ne Ni Fatima Idriss Bello
Ban yadda a juyamin littafina ta ko wane irin tsiga ba, ko kuma ayı audio ba tare da izinina ba domin hakan ze iya janyo ma mutum matsala.
Dan haka a kiyaye.

>>>>>>>>>>>>>🖋️💻


19



YARIMAN HAFSA
(A Royal Love Story)
Mallakar Fatima Idriss Bello



Arewabooks; Fadrees20
Wattpad; Fadrees_20
Phone No. 0902058802


Haƙƙin Mallaka nawa ne Ni Fatima Idriss Bello, ban yadda wani ko wata suyi amfani da wani sashe na littafi na ba, ko a haɗa min audio ba tare da kwakkwaran amincewa ta ba, idan naga akasin haka kuma wlh baza mu wanye lapiya ba dan haka a kiyaye.
Idan number na kake nema ɗaga idon ka sama zaka ganshi a rubuce



Hafsa kuwa kallon tsoro take masa, ita wallahi tun abinda ya faru dazu har taga mai martaba, wlh a tsorace take, a tunanin ta cewa zai yi ta tashi a wuce da ita dakin duhu ne sai kuma taga kamar ba haka ba
Alama yayi ma Sulaiman da ya basu guri, shi kuma yaqi motsawa ma ballantana tafiya, da Yarima yaga haka sai ya share sa
Shi kuma Sulaiman ya fara magana kamar haka
"Abinda kike ta fatan samu, yau Allah ya kawo sa, a yau dinnan Mai Martaba ya baki sallama, gobe da sassafe zaki bar masarautar nan, yanzu muna zuwa Yarima ya sa jakadiyar sarki ta kirawo kawar ki ta maida ke dakin ku, saboda haka saduwar alheri, zaki iya tafiya". Ya karashe maganar sa yana mai kallon Hafsan, miqewa tayi amma sai ta fadi kasa, nan take hawaye ya fara kwaranya a idanun ta tana tuna moment din da suka yi ita da Yarima, lokacin da ta cinye masa awara tace ita bata ga awara ba, da lokacin da yasa barau ya zane ta bayan shi ya gama dukan ta, har tayi jinyan kwana biyu, da lokacin da ta fara masa aiki, ya rinqa bata wahala ita kuma ta dinga masa su rashin hankali, Allah Sarki rayuwa, daman ance komai yayi farko zai yi karshe, ita a rayuwar ta ma bata taɓa tunanin cewa wataran zata zo cikin wannan masarautar ba har ta yi aiki, sai gashi Lillahi ya kawo ta, har da farko ta dauka baza ta iya rayuwar ciki ba, sai ga shi ta saba, yanzu kuma da Maigida Sulaiman yake fadin zata tafi gobe da safe, sai taji kamar zata bar wani sashe na jikin ta ne, hakika za tayi kewar murja da yan dakin su, dukan su sun riga ta shigowa cikin masarautar amma zata riga dukkanin su fita, hakika zata yi kewar makarantar su na bayi, zata yi kewar dambace dambacen da take yi da mutane da dukan da ake sa dogarawa daban daban su mata idan tayi damben. Hawayen ta har yanzu bai daina zuba ba.
Kamar walkiya ta hango Murja ta Shigo cikin dakin shakatawar, ta zube ta kwashe gaisuwa, wanda Maigida Sulaiman ne kaɗai ya amsa mata, Yarima kuwa tsaye yake kamar mutum mutumi yana bin su da idanu.

Umarni Sulaiman yayi wa Murja da ta dauki Hafsa su tafi, gyada kai Murja tayi tare da miqar da Hafsa ta kama kafadar ta, sun zo fita daga cikin dakin shakatawar ta juya wai ta ɗan saçı kallon sa sai taga shima ashe kallon ta yake, idon shi kamar hawaye ne kwance amma bai zubo ba
"Sai na zo" kamar almara taga bakin sa kamar motsawa yayi, ya furta jimlar a lokacin Murja ta janye hannun ta suka fice daga dakin shakatawar. Ita ji take kamar kawai imagination nata ne, if not, tho ina zai zo? Idan ya zo din ma mai zai mata? daga nan suka fice daga sashen nasa gaba-daya

Suna fita Hafsa ta saka kuka, ita ji tayi bata ma san tafiya, ta gwammace a kai ta dakin duhu a hukunta ta, duk da bata san laifin me ma ta aikata ba, amma ba yanda zata yi. Murja ce take ta lallashin ta har sai da tayi shiru, kan su isa take bata labarin abinda ya faru a sashen sarki wanda ya jawo mata da sallamar, ita har mamaki take ko wane ɗan gulman ne ya jiyo wannan babbar maganar. Sannan ta tausaya wa Yarima kwarai na wannan dokar da aka kafa mishi, shida ya saba fita wajen gari kullum yaya zai yi rayuwar har wata daya a kulle. Allah Sarki.

Suna isa mutane suka dinga zuwa gulma dakin nasu, Lantana kuwa ta musu wulakanci ta kora su. Hafsa daren nan ko abinci bata nema ba, da ta kwanta akan katifar ta tayi kuka sosai wanda bata taba yin irin shi ba, idan kuma ka tambaye ta kukan me take cewa zata yi ita kanta bata sani ba.
Tasan gobe idan ta tafi su Mama zasu fi kowa farin cikin ganin ta, Allah Sarki Mama, da Jamila da su Azima.
Tana nan tana sake sake bata san sanda bacci yazo ya kwashe ta ba.

______________

Yarima kuwa a bangaren sa, Wucewa cikin uwar dakan sa yayi ya kwanta akan gadon sa tare da rufe idon sa, karar shigowar Sulaiman yaji, yana ji sulaiman din ya kashe fitilan dakin, yaje shi gefen gadon nasa yayi kwanciyar sa tare da rufuwa da bargo can yajiyo Sulaiman din yana jan numfashi a hankali wanda ke alamta cewar bacci yayi awon gaba da shi.
Yarima kuwa bacci cewa yayi besan yana yi ba, domin kaurace masa yayi kwata kwata.
Nan ya tino lokacin da Hafsa zata tafi, shi sam bai ji dadi ba, shidai harga Allah ba son ta yake ba, ta yaya ma za'a yi ace yana son baiwa, ai hakan ba me yiwuwa bane, kawai dai yana jin wata irin shakuwa ne da ita bayan haka ba komai, sannan duk sanda hukuncin shi ya ƙare ze je ya nemi gidan su ya mata alheri me tarin yawa, shidai baya san yaga tana cikin matsala, dazu ma da yaga hawaye a fuskar ta kamar yaje ya share mata, kuma ya tabbata saboda tsabar tausayin ta da yake yi ne.

Sai a sannan maganar da suka yi shi da sarauniya babba ya dinga dawo masa, da yaje sashen ta.
Da yayi sallama sai ya tarar da ita da Sulaiman da Bilkisu da Samira suna ta shan hiran su, daman ya saba zuwa ya tarar da ita da yammatan, in yaje sai ya kore su, toh yau ma hakan ne ta kasance yana shiga bayan da suka gaishe shi ya musu ido da su fita, nan suka miqe suna ta ɓata rai, ba ya ma Bilkisu da take ta zumbura baki
Bayan ficewar su ya kwashi gaisuwa a gun kakar tasu, ta amsa masa cikin sakin fuska, Sulaiman kuma na cewa Ni baza ka gaida Ni ba kenan sai wannan tsohuwar zaka gaida? Rankwashin sa kakar tasu tayi sannan tace da Yariman ya zauna daman tana jiran ya zo, akwai maganar da take so su yi da shi
Zama yayi, ya hakimce cike da sarauta, ya zuba mata ido
Sakar baki suka yi ita da Sulaiman suna kallon shi budan bakin ta kuwa sai cewa tayi "Bantan uban ka ungo nan, hala baka san cewa Ni ma yar sarki jikar Sarki kuma matar sarki bace da zaka zo kana mana shan kamshi? Sannan shi Sulaiman din da ka rena ya pi ka kyan gani dan Ubanka, tunda dai shi kullum fuskar sa na dauke da murmushi, kai kuwa fuskan ka yadda kasan fuskan shanu wajen rashin fara'a, banza kawai". Ta karashe tana zungurin goshin Yarima, shiko taɓe baki yayi abinsa Sulaiman kuwa mai zeyi in ba dariya ba.
Can da suka natsa ta maido da hankalin ta kan Yariman tace masa "Mijina, ina so ka bani hankalin ka kaji abinda zan fada maka, ranan husumar da aka yi a dalilin ka banji dadin hakan ba, sannan Kai ka ƙi cewa komai, munyi magana da su wancan Isma'il yake ko waye, a gaban dai Sulaiman gashi nan a nan, aka yi komai, duka sun tabbatar min da baiwar ka ce kurum. Saboda haka naga ya dace ka fita a harkan yarinyar, nayi bincike an cemin a sashen Mai Martaba take aiki, ka maida ta can taci gaba da aikin ta, kar hakan da kayi ya jawo mata matsala, duk da kace kai ba cewa kayi kana san ta ba, kawai kai baiwar ka ce".
A lokacin har Sulaiman yace wa sarauniya babba "Toh idan kuma son ta yake pa"? Sai ita kuma ta dauki mahuci ta kwala masa tace "shi ba son ta yake ba, me zeyi da baiwar sa"
Yanda ta fadan har sai da Yarima ya daga ido ya kalle ta, dan kamar ta shiga zuciyarsa ta gani ne, ita kuma ganin irin kallon da yake mata sai suka saka dariya ita da Sulaiman
Yanzu da yabi shawarar ta da zai dinga kallon Hafsa a kullum, yanzu ma bata ɓaci ba, dan kamar freedom din kallon ta kullum aka bashi
Yana nan yana sake sake har barawon yazo yayi awon gaba da shi.

Let's meet in the next Chappy
Don't forget to, follow, vote, comment and share it pls
Ghost Readers🙄.

@fadrees_20.





🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss🖋️🖋️
09020588802
Wattpad; fadrees_20


Page 20



Da sassafe Hafsa ta gama shirin ta, suka je suka karbo abincin su na safe wato dambu. Tana ta lura da Murja, ta ga tun jiya jikin ta a sanyaye. İta dai bata ce komai ba bayan sun gama cin abincin nasu, wanda shima sama sama suka ɗan taba, nan Hafsa ta ɗan kishingida akan katifar ta da zata yi ban kwana dashi ita kuma Murja ta zabga tagumi.

Sallamar shugabar su ta bayi suka ji a cikin dakin nasu, nan take jikin su shafa'atu ya sake yin sanyi. Kallon ki biyo ni shugabar bayin nasu ta ma Hafsa, nan da nan kuwa ta miqe tsaye ta dauki damin kayanta tabi bayan ta, su Murja, shafa'atu da Lantana har ma da wadansu daga cikin bayin na biye da Ita.
Sunzo gurin fita daga babbar gate din masarautar aka dakatar da su Murja, anan pa aka fara draman, kamar ansan zasu yi taurin kan kin tafiya sai ga dogarai da bulalu, duka suke kaiwa bilhaqqi, Hafsa nan take ta saka kuka, ba wanda zai baka tausayi a gun kamar murja, wlh yanda take kuka kamar za'a raba ta da ranta ne, nan bayin da suka rako Hafsa suka janye Murja suka koma da ita, tana ganin su shafa'atu sai kuka suke yi, Murja sai ihu take tana waigo ta har suka shige kofa na biyu, bayan tafiyarsu ne dogaren dake wurin suka ce Hafsa ta fita daga cikin masarautar ɗayan hadda daka mata tsawa wai tana sa su jinkiri wajen aikin su.

Hafsa na saka kafar ta a wajen masarautar ta shaqi iskan ƴanci, yau dai gata ƴantatta, Allah Sarki Murja, In Sha Allahu zata nema mata mafita da izinin Allah, in yaso sai ta dawo gidan su da zama tunda dai ga yanayin gidan su su.
Fita tayi ta fara tafiya, yau watan ta ɗai ɗai har guda biyu da sati biyu bata saka en gidan su a idon ta ba, ji tayi gaba-daya kanta ya juye ma, kamar wanda ta shekara bata je gida ba, toh ita tun da take bata taɓa zuwa wani gida wai dan ta kwana dayawa haka ba, hana rantsuwa sunje gidan su halime ita da su Azima sun yi kwana biyu da ta haihu. toh yanzu ita bata san ina zata fara dosa ba ma, wasu matasa ta gani a gaban ta har guda hudu, ce mata kawai suka yi an aiko su dan suyi mata jagorana ne, bata ce musu komai ba har suka kaita gida.

Sadiqu ne ya fito zashi yawo kamar dai yadda ya saba, ya sawo wata rigan sa ruwan bula, wanda taci duniya har ta gaji, sannan rigar har tayi fari fari ta dafe tsabar jimawar da take ba'a wanke ba, idan aka tashi wanke ta kuwa se taji Omo ta gaji, wandon kuwa har gwiwar ta babbarge tsabar karambani da wasan banza, cin karo yayi da Hafsa sai kuwa yaja da baya yana mai matukar zare idanu, sakin kuwwa yayi tare da fadawa cikin gida yana ihun yaga fatalwa, su Mama Lantana zanin ta har faduwa yake garin gudu, sai zauren gidan nasu yake nunawa da hannu yana cewa "fatalwa, fatalwa" Lawan da gidan shi yake gefen na su Hafsa ne ya leqo a hanzarce ƙafarsa ko takalmi babu, daman an fasa masa kofa ta cikin gidan nasu, sannan gidan da yake dayan gefen nasu shi kuma wadanda suke ciki sun bar unguwan to yanzu an daga

Please Login or Register in order to submit comment