Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masa kirari, ran Kilishi ne yayi mummunan ɓaci jin Mai Martaba a gun, bata tsinke da lamarin ba seda taji the same bafade Yana yi wa Waziri nashi kirarin, a lokacin tayi masifar harzuqa, ita tazo nan ne dan ta sake ɓata lamarin, bata dauka wadannan munafukan zasu zo ba, musamman wannan babban baƙin munafikin wato Waziri, sannan bata san ta yaya akayi ma suka ji zancen sarauniya babba ta tara su ba, ko danma daman abu a cikin masarauta baya ɓuya, amma baza ta sare ba, duk da suna nan dinma, zata san yadda zata yi ta sa aci mutuncin Yarima da Fulani.

Abinda Kilishi bata sani ba, ita sarauniya babba daman tun da taji abinda ya wakana, ta aika ma sarki akan yazo ayi komai a gaban sa
Bayan Sarki da waziri sun samu masauki Sarauniya Babba ta fara jawabi kamar haka;
"Na tara ku anan ne bisa ga jita jitan da naji dazu, wanda har yayi silar kulle matar Yarima da akayi, wanda hakan matukar cin mutunci ne ga Yarima, yanzu dai nasa an ciro ta an kaita dakin magani koma dai me tayi bata cancanci a kulle ta a dakin duhu ba, tana matsayin matar Yarima me jiran gado, zuwa nan da anjima zata iso itama muji daga bakin ta, sannan Yarima yayi bulaguro Gashi lokaci ya kure musu sai gobe zasu dawo da da kanshi zai zo ya mana bayanin komai amma yanzun ma bata ɓaci ba, yanzu ina so ke Sadiya ki mana bayani dalla dalla na dalilin da zai sa ki rufe matar Sarkin gobe, ta yaya akayi kika san ta zubda mutuncin ta sannan ta yaya akayi kika san komai, kiyi mana bayani muna saurare".
Su Waziri dai da su Shamsu da kowa ma zuba ma Kilishi ido yayi yaji me zata ce game da abinda ya faru dazun
Kilishi ce cike da munafurci da tunanin kalan Bomb din da zata hada ta kama magana domin wannan maganar ta sarauniya babba ya ɓata mata rai, wai "matar sarkin gobe" mtchewwww se su gani in ze kai goben
"Allah ya ƙara Miki yawan rai, bawai hakan da nayi ina son na tozarta Yarima bane, a'a nayi hakan ne domin kare mana martabar masarautar mu da shi kanshi Yariman, sannan akwai abinda ma ban fada ba, dan da na fada sai ran Kowa anan ya ɓaci, shekaran jiya da aka kawo yarinyar nan satar hanya tayi taje sashe na da dare tayi min rashin kunya san ranta kasancewar ta taba aiki a Masarautar nan tasan ko ina sarai, ni kuma da naga haka nace bazan hukunta ta ba kar ace daga zuwan amarya na mata abu, me makon in hukunta ta, sai ma na sa a saka mata ido, sai jiya da tayi amai ta saka bayin ta kwashewa, su kuma suka tsaya mamakin aman da tayi tana amarya, da taga haka ta karɓo tsumagiya tayi ta dukan su har seda jikin su ya kumbura wai ai sun rena ta, tana matar Yarima, daman kasan ya'yan talakawa basu iya samun guri ba, shine suka gudo guri na wai na nema masu gafarn ta, da na tambaye su dalili suka fada min komai da komai, Haka zalika dazu Nazo wucewa ta gun sashen nata xanje gurin yar uwata Hauwaó najiyo kakarin amai daga in leqa, naga abinda yake faruwa, Niko nasa aka kirawo Larai me magani tazo ta duba ta, tana duba ta tace mana juna biyu gare ta, bata tsaya a hakan ba tamin rashin kunya a gaban bayi, gasu Hauwaó da Samira akan idon su akayi komai"
Ta karashe tana dariyan mugunta a ranta, da sarauniya babba taji haka, sai tace mata
"Toh amma ya akayi kika san bata kawo budurcin ta ba, sannan ba kowane amai bane yake zama ciki"?
Kilishi ce tayi murmushin mugunta a ranta tace 'anzo gurin'
"Ranki ya dade ai na sa jakadiya ta dakko min farin kyallen, gashi nan a cukurkude daga gani kinga alamun an kwanta a kai sede babu jini babu dalilin sa kuma ma an gwada ta tana da juna sannan bayin da suke aikin sun tabbatar da bacci ba kai ba gindi take yi a jere a jere, sannan ai dazu da sassafe aka kawo Miki na Bilkisu nan duk da dama bama tantamar ta ita, dan ta kawo budurcin ta sumul, sede in Yariman za'a tuhuma, ai shi yafi kowa sanin ita ba budurwa bace yaqi fada sede in shine...."
Bata karasa ba Waziri ya galla mata wani mugun harara, bata san sanda taja bakin ta tayi shiru ba, amma tasan da cewa, koma dai meya faru sakon ta yaje shi can inda take buƙatar ya isa.
Kowa shiru yayi na wucin gadi domin wannan babban al'amari ne
Can dai sarauniya babba ta aika Samira ta kira mata baiwar ta, shafa'atu ce ta shigo da sassarfa tana me zubewa tare da kwasar gaisuwa, magana sarauniya babba ta mata kapın ta fice, can sai gata ta taho ita da wata baiwa suna riqe da Hafsa, ita dai shafa'atu mamaki take, badai Hafsa bace matar Yariman da suka gama tsinewa dazu ba, suna ajje ta suka fice, ji tayi Hafsan tace "ki gaida min Murja" wanda ita kadai taji abinta, nan ta kara tabbatar da cewar hafsan ce, ai kuwa ta fice jikin ta a sanyaye.
Tashi Hafsa tayi fuskan ta a kumbure jikin ta duk yayi dabbare dabbare ta kwashi gaisuwa, Ko da Hayatu yayi arba da fuskan Hafsa nan ya tashi a matuƙar firgice, se nuna ta yake ya kasa magana, Shamsu ne ya riqo hannun sa ya zaunar da shi, yana fadin "meye hakan Hayatu ka kintsa kanka mana a gaban Mai Martaba fa kake, ai kuwa nan da nan hankalin en cikin dakin shakatawan ya fara dawowa kansu, shi kuma Hayatu karkarwa ya fara yi yana fadin, "wannan itace matar Yariman?", "Ehh itace ka nutsu" Shamsu ya fada masa yana me zaunar dashi, zama yayi hawaye yana zirara a fuskan shi, kuduri ya dauka a ransa akan baze bar ma Yarima ita ba, Allah ma ya sa da gaske ne abinda ake tuhumar nata, in yaso idan an raba auren nasu shi yaji ya gani ze aure ta a hakan

Wannan karan waziri ne yayi magana yana me kallon Hafsa
"Me zaki ce game da abinda ake tuhumar ki dashi"?
Hafsa ne ta fara magana
"Wallahi ranka ya dade karya ake min duk abubuwan da ya faru sharri ne, Ni bani da wani ciki, kuma ma jiya ba'a dakin Yarima na kwana ba ballantana ace ni na kwanta akan farin kyallen can, sede idan shi Yariman shi yayi ta birgima akai, sannan shekaran jiya ma dana kwana a dakin sa a kasa na kwanta, Ni ban hau wani farin kyalle ba, Wallahi sharri ake min ranka ya dade, sannan dazu da safe da na shiga dakin sa ai kyallen ma ba'a cukurkude yake ba".
Ta karashe tana saka kuka, abu ne ya daure wa en daki kai, ana zargin bata kawo mutuncin ta ba, ita kuma tace bata ma kwana a dakin ba.
Ita Hafsa bata ma san ta kwapsa ba, gaban sarki take cewa wai sede in shi yayi birgima, wai kuma basu kwana tare ba.
Kilishi ce ta dinga jifan ta da harara kamar idon ta ze fado, sede cikin rashin sa'a take tayi dan Hafsa ko kallon ta bata yi ba, ita sam bata dauka yarinyar haka take ba, ta dauka zata amsa laifin ashe kallon biri take mata ita kuma tana mata na ayaba, lalle zata sake shiri, dan yanzu kam ta san wannan kam ya ɓaci.

Waziri ne yayi magana kamar haka
"Tunda kince haka, Za'a daga zaman nan zuwa dawowan Yarima gobe, in yaso shi kuma se muji ta bakinsa, sannan bayin da suka kai maganan nan in ta tabbata karya ne, za'a musu hukunci me tsanani tare da ita me maganin da ta gwada ki, sannan zuwa kurkukun da kika yi, fada tana me baki hakuri, Kowa ze iya tafiya ".
Nan da nan kowa ya miqe ya kama gabansa, Shamsu ne ya kama Hayatu ya wuce dashi sashen Kilishi, tana karasowa ta gan shi, ko bari su mata magana bata yi ba tace masa, "Babu kai babu ita, idan kuma naga akasin haka, se nayi mummunan saɓa maka".
Nan ta shige dakin ta, ta ɓace gun shugaba suka tattauna ya bata surkulluna ta dawo da kudirin ganin bayan wannan ahali.

FADREES 🖋️.





>>>>>>>>>>>>>🖋️💻







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss Bello🖋️🖋️
Wattpad; fadrees_20


Page 35



Hakkin Mallaka nawa ne Ni Fatima Idriss Bello
Ban yadda a juyamin littafina ta ko wane irin tsiga ba, ko kuma ayı audio ba tare da izinina ba domin hakan ze iya janyo ma mutum matsala.
Dan haka a kiyaye.


Hafsa rai a ɓace ta koma sashen Yarima, da tunane tunanen irin yanda zata rama abinda Kilishi ta mata, sai yanzu ma take jin ashe baya cikin masarautar, wato tafi ƙarfin yace mata zeyi tafiya ai wlh ze dawo ya same ta, dakin da yake matsayin nata ta shige tayi tagumi da sake saken a ranta, daga karshe ma kwanciya bacci tayi zazzaɓi na rufe ta dan ko abinci bata nema ba gashi rabon ta da abinci tun wanda taci tayi aman sa dazu.

Da gari ya waye ma kin fitowa tayi, can taji sallama amma bata da karfin tashi dan ko salla bata yi ba jikin ta yayi wani irin zafi se kyarma take, da aka ji shiru bata amsa ba shine aka Shigo, ashe Mai magani Sarauniya babba ta aiko dan juya da ta ganta kamar bata warke ba, ganin yanayin jikin hafsan yasa matar ta kama ta suka tafi dakin maganin cikin masarautar ta kwantar da ita dan bata a cikin hayyacin ta ma.
_______________
Mama Maryamu ce ta wuce da Mama Zenabu dakin ta suka raba dare suna hira gashi ko nan da nan bata bari Mama Zenabu ta motsa, ji take idan har ta ɗan matsa in ta dawo baza ta same ta ba, Jamila kuwa ta samu ƙawa, dan a dakin ta ma tayi masauki gashi suna kama, nan da nan tasu tazo daya suka yi ta hirarrakin su, Jamila tana bata labarin Hafsa da garin su, ita kuma Suwaiba tana bata labarin nasu garin, ahaka suka yi bacci, da safiya tayi suka je suka gaida Galadima, inda yace su shirya an jima za'a rakasu suje su gano yan uwansu Mama Maryamun, da suka jejje, akayi ta nan nan dasu, har wani Malami yazo ya duba Mama Zenabu yace ai asiri aka mata, ya bata magunguna yace nan bada dadewa ba zata dawo daidai inshallah.
Har zasu koma gida Mama Zenabu tace tana so taje gidan su ta gana da Baba Falmata, da suka je ta dinga kallon gidan Jamila kuwa da Malam Sule sai mamaki suke, yanzu wannan danqareren gidan shine gidansu Mama Zenabu, lalle kam, shi Malam Sule tunanin da yake a ransa ma daban ne, ji yake gaskiya da badan ƙaddara ba, be isa ya auri mace kamar Mama Zenabu ba dan gaba-daya ta masa fintinkau tako ina sese yake a matsayin bawan ta, Iso aka musu suka shiga suka same ta a zaune ga carbi a hannun ta, tana ganin en biyun ta tashi a matuƙar firgice tana nuna su, daga baya kuma ta saka kuka wai su yafe ta, bata so tabar duniya ba tare da ta nemi yafiyar su ba kaman yadda kishiyar ta Fanna ta bari, bada jimawa ba suka ce sun yafe mata, suna fita daga gidan gidan Sarkin Borno suka yi wa tsinke, lokacin har yamma yayi, ya riga da ya shiga gida ma, amma da shike da kanin sa suka je, basu sha wahalan ganawa da shi ba, hakika ya matukar jindadin bayyanar Zenabu har ya kasa boyewa, bayan sun gaisa, matan suka shige suka je suka gaisa da matan Sarki, daman matan sa uku ne, Ya Gumsu itace babbar su, se wani shasshan kamshi suke abinsu, bayan da suka gama ziyara suka tarkata suka koma gida.

Bayan sun kwan biyu Malam Sule yace wa Galadima zasu kama hanya, shi kuma yace yabar Mama Zenabun anan mana, da yake yana jin nauyin sa se ya kasa cewa a'a, shi kuma Galadiman fahimtar hakan sai bai ja da nisa ba yace su tafi taren kawai, in yaso sai a dinga ziyara, kwana uku suka kara suka kama hanyar Bauchi, inda aka musu goma na arziki, dan tsaraba kam har ba'a magana, wani jaka Mama Maryamu ta baiwa Jamila tace gashi idan sunje Bauchi ta baiwa maman ta, amsa tayi suka yi sallama da Suwaiba ta bata kyautan kayayyaki sannan tace ta gaida mata Hafsa, kama hanya suka yi sai mangariba suka isa.

Ahalin gidan sunyi matukar farin cikin dawowan malam sule musamman da suka ga ya taho da tsaraba me tarin yawa, su Mama Lantana basu tsinke da lamarin tafiyar da akayi ba seda Malam Sule Mai Rini ya basu labarin rayuwar Mama Zenabu, a lokacin idonsu ya raina fata, haka dai suka yi ta tsilla tsilla, har baba dai ya fito da tsaraba aka raba, duk mutanen da suka ji labarin Mama Zenabu kuwa se kaga sun sha jinin jikin su, wasu hadda cewa wai ai kyantan nan ai dama sede yar gidan sarautar, rayuwa kenan.
Da Jamila ta baiwa mama Zenabu wannan jakan se ta bude, kudade ne a ciki tsaba, Allah Sarki, nan da nan ta fada wa Malam Sule, ta bashi kudin tace ya kara akan jarin sa, ta karba kadan daga ciki ta ajiye dan gudun ɓacin rana.
Ranan baccin dadi Mama Zenabu tayi, na kewar yar uwar ta da kuma yar ta wato matar Yarima.

_______________

Yarima kuwa koda suka je kasar Gombe aka yi musu tarba wanda ya dace, bayan sun isar da sakon sarki sun bada gudunmawa suka ce zasu juya su koma Bauchi, Sarki yace faufau, shifa besan magana ba, ko zasu koma su bari se da safe bayan sun gama hutawa.
Badan sun so ba suka yadda
Sashen baki aka kaisu suka huta daga karshe har suka yi abota da ɗan Sarkin, Me suna Salman, haduwa suka yi shida Sulaiman suka dinga tsokanan Yarima ya share su, can dai da dare yayi sosai Salman ya musu sallama yace sun riqe shi yanzu gashi yabar amaryar sa ita kadai a cikin kadaici, Sulaiman ne yace, "sai ka gayawa wanda bashi da aure dan Nima a angwance nake, nabar amarya ta cikin kewa ta, dan kwana biyun nan da muka yi Bama son muyi nesa da juna bamu dai san ko wannan ba" ya karashe yana nuna Yarima, aikuwa suka hadu suka dinga mishi dariya shidai shiru yayi ya kyale su, dan Allah Allah yake gobe tayi su kama hanyar Bauchi.
Bayan fitar Salman, Yarima da Sulaiman suka kwanta, can se Sulaiman yace "gaskiya kai Ni ban saba kwana da garada akan gado ba in zaka bani guri kaban haba" ya karashe yana me yatsina fuska, Yarima ne ya masa kallo bakwai saura kwata yaci gaba da abinda yake, can da yaga baze kula sa ba sai yace "Oho dai nasan tunanin ta kake, kawai kana boyewa ne, dan kar a gane toh na gane, dazu kamar kar ka tafi, na lura dakai sosai, so kake kaje ka mata sallama baka samu dama ba".

Tsaki yayi can kuma kamar baze yi magana ba, se ji yayi yace "kamar ka sani kuwa, Allah Allah nake in ganni a Bauchi".
Ai kuwa kamar ya bude wa Sulaiman bakin zolaya, ya dinga zolayan sa, daga karshe suka koma maganar mutuwar yaran sarakunan da zai aura, Sulaiman yake ce masa ai ya samu wani amintaccen bawa, ya saka shi ya sa ido akan duk wani movement din Kilishi, yace in dai yaga zata wani guri ya tabbata ya bita, dan yafi suspecting dinta kap a cikin gidan
Yarima ne yace hakan ma yayi.
Be jima ba suka kashe fitilar dakin nasu.

Dukda kasancewar a gajiye suke, bacci sam ya kauracewa idon Yarima, tunanin Hafsa kawai yake yi, se wani iri yake ji duk da yasan cewar cikin koshin lapiya ya ganta, amma se ya dinga jin wani iri dai, yaso yau ɗinnan su kama hanya wannan sarkin ya hana su, toh shi meye ma na damuwa, yana namiji dashi me ma ze mata, sannan shi a ganin sa ai hakan tafi so ma, salan taga yana yawan mata magana ta raina shi, gata daman in harkar rashin kunya ne ya lura tafi kauri ata bangaren.
Yasan Kilishi zata aika a bata farin kyalle yau, ai nan da nan ya tashi zaune, a take jikin shi ya bashi yau ba lafiya bane, domin in har taga babu jini a jiki Allah ne kaɗai yasan abinda zata iya aikatawa, gashi shi baya nan, innalillahi, Allah dai yasa basu sa Hafsa a matsala ba, kodanma ai sarauniya babba tana nan baza ta bari wani abun ya faru da ita ba, amma idan ya koma yaga koda kwarzane ne a jikin ta, shi kanshi besan iya abinda ze iya aikatawa ba.

Wannan kenan

© FatimaIdrissBello
FADREES🖋️
09020588802




>>>>>>>>>>>>>🖋️💻







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss Bello🖋️🖋️
Wattpad; fadrees_20


Page 36



Hakkin Mallaka nawa ne Ni Fatima Idriss Bello
Ban yadda a juyamin littafina ta ko wane irin tsiga ba, ko kuma ayı audio ba tare da izinina ba domin hakan ze iya janyo ma mutum matsala.
Dan haka a kiyaye.



Shamsu ne ya kama Hayatu suka wuce sashen su, taimaka masa yayi ya zaunar dashi a bisa kan gadon nasu, muryar Hayatu Shamsu ya tsinta yana me fadin
"Na rasa me yasa Umma ta kasa fahimta na, soyayyar yarinyar nan bani na ɗorawa kaina ba, bansan yaya zan yi ba Shamsu, nikam ba kaine kace min baka da kama ta ba? Me ya sa toh baza ka taimaka min ka cika min burina ba na san mallakar ta ba?, kwanaki da aka kore ta a masarautar nan me kace min? Toh bari Ni in tuna maka da kaina, cemin kayi ka sa an binciko ahalin ta? Yardar umma kawai ya rage min? Da muka zo muka wa Umma maganan tace bata san in sake koda kiran sunan ta bane, yanzu kuma me Yakamata kamin?, kamata naga yayi ka taimaka min in yaqi soyayyar yarinyar nan, ba wai kawai ka zuba min idanu ba, kodan baka san yadda nake ji bane, baka san ya nake jin zuciya ta bane shiyasa" Hayatu ya karashe muryar sa cikin kunci da bakin ciki
Maganan Shamsu ne ya dawo dashi daga kuncin zuciyar da ya shiga,
"Kar kace haka Hayatu, bawai ina kin taimakan ka bane akan wani dalilin, a'a ina yin hakan ne dan ina tsoron maka fushin uwa ya hau kanka, kaga dai umma ba ta san alaqar nan naku, kaga ai be kamata mu saba ma umarnin ta ba, kuma dagaske nake nasa an bincika min ita kawai dai ban wani maida hankali bane akai saboda furucin da Umma tayi, sannan yanzu alaqa a tsakanin ka da yarinyar nan baze yiwu ba domin ta riga da ta auri Yarima İdriss, ko babu komai matar yayanka ce yanzu, be kamata ma ka dinga furta irin haka ba gudun kar ma a jiyo ka a samu matsala, shi kanshi nasan da yasan itace wadda kake so bana tunanin ma zai aure ta, dan Allah Hayatu ina so ka saisaita zuciyarka ka rungumi ƙaddara, sai kaga abu yazo maka cikin sauki kaji? Ni sam sam bana san in dinga kallon ka cikin wannan yanayin, ka cire ta a ranka tunda yayanmu take aure kai kuma sai kaga Allah ya baka wacce tafi ta a komai ma".
Shamsu ne ya karashe cike da san kwantar ma Hayatun hankali.

Ajiyar zuciya Hayatu ya sauke, ba wai dan ya gamsu da abinda Shamsu ya fada masa ba, a'a shi tunanin neman mafita ma kansa ma yake ko ta halin ƙaƙa kuwa, murmushin yaƙe ya sakarma Shamsu, wanda hakan ya kwantar ma da Shamsu hankali har ya sarara tare da kashe musu fitilan dakin suka yi bacci.
_______________
Yana nan yana sake sake a ranshi har besan sanda bacci yayi awon gaba dashi ba.

Da sassafe suka farka, aka kawo musu abun karin kumallo suka karya, basu jima da karyawa ba sai ga Salman yazo bayi na take masa baya, bayan sun gaisa suka kama hanyar zuwa sashen Sarkin Gombe, iso aka musu suka shiga suka kwashi gaisuwa, bayan haka suka yi masa sallama suka wuce gun abun hawan su, bayan sunyi bankwana da Salman ya musu alkawarin in Sha Allah wataran ze zo Bauchi suka kama hanya

Seda suka kama tafiya hankalin Yarima ya kwanta dan Allah Allah yake ya ganshi gashi a cikin Birnin Bauchi, tafiyar awa biyar ya kai su garin Bauchi me tarin albarka, suna shigowa Yarima yace da Sulaiman akan zeje sashen sa ya dawo
Sulaiman ne yace masa "Gaskiya baza ayi haka ba Yarima, tunda gamu a kusa da fada can yakamata mu fara zuwa, mu bayar da sako sai mu wuce uzurirrikan mu, kar ka manta Nima fa banga matar tawa ba tun jiya, dan Allah ka jure muje kapın".
Ba'a san ransa yabi Sulaiman ba, dan hakan shine daidai amma wlh so yake yaje yaga yaya ake ciki.
Wucewa fada suka yi suka miqa gaisuwa bayan haka suk bada sakon da suka dawo dashi tare da fadin irin karramawar da aka musu a can ƙasar Gombe, hakika fada taji dadin wannan karamcin nan da nan ta sallame su da suje su samu hutu, sallama suka yi suka fice, Yarima ya wuce sashen sa.

Ko da Fulani taji labarin Yarima ya dawo har ya wuce sashen sa be neme ta ba for the first time, se taji ranta ya ɗan sosu, duk sanda zai yi bulaguro indai ya dawo toh sashen ta yake fara zuwa kapın yaje fada ma, amma yau guda taga sauyi ba ma haka ba, yarinyar da yake yi domin ita, ba tashi take ba, amma babu komai zata ci gaba da a'a masa idanu.

Tafe yake cike da ƙasaita da çıkar zati, ƙira ce ta jiki da Lillahi ya bashi me kyau ma kuwa, domin yau se naga ya kara min kyau sosai da sosai, hancin sa a miqe ras idanunsa kuwa har wani sake shudanye wa suke yi tsabar kyalkyali farar fatar nan tasa kuwa sai walwali take, duk inda ya gifta zaka ga ana ta kwasan gaisuwa, sede yau fuskar shi ba kamar ta kullum nace domin ranshi a mugun haɗe yake, ganin yanayin nasa na yau yasa mutane shiga taitayin su domin a asalin Yariman sa ya fito yau, wato Yarima Idriss me jiran gadon kasar Bauchin Yakubu, ko da ya isa sashen nasa se yaga kofar a bude, babban dogarin da yake masa gadin sashen nasa ne yace, "Allah ya baka nasara makullin sashen naka yana hannun sarauniya babba", ya karashe kansa a kasa, bece komai ba ya wuce sashen nata, yau masu gulma ma babu daman yi, dan yanayin fuskar sa in kayi magana ma zaka iya kwana a dakin duhu

Ko da ya iso ko neman iso yau beyi ba ya antaya cikin sashen nata, ganin haka fadawan da suke take masa baya suka koma can bakin gate din sashen nata domin su jira sa a ciki, abinda ya samu yana faruwa ne ya sa kafafun sa rawa
Muryar Kilishi yaji da Sarauniya Babba suna magana
"Yanzu ke Sadiya me kike so in Miki, bayan cin mutuncin da kikawa matar Yarima be ishe ki ba, kika sa aka kulle ta a dakin duhu, duk da haka kina so in sa Mai Martaba ya kore ta a wannan masarautar?, karki manta yarinyar nan fa yanzu haka tana kwance rai a hannun Allah bata san waye akan ta ba, kuma koda cikin shegen tayi kamata yayi a bincika komai a natse, bawai ki wani zo ki same Ni kina roqon wai insa ya sake ta ba, ko dai kina so kimar Yarima ya gama zubewa ne a gaban kowa da kowa na Masarautar nan"?.
Sarauniya Babba ta karshe ranta a kuntume, ita koda yarinyar ta zubda mutuncin ta a waje a hakan take san taci gaba da zama matar sa, amma ta lura wannan matar tana so ta shige mata cikin hanci, bari zata yi maganin ta kuwa.
Kar ku manta duk wadannan maganganun da ake yi akan kunnen Yarima, ya kasa motsi ne saboda

Please Login or Register in order to submit comment