Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jin irin mugayen kalaman da ake jifan Hafsa dasu
Muryar Kilishi Sarauniya Babba ta jiyo tana cewa
"Haba Allah ya baki nasara, Yakamata ko duba wannan maganan da nayi da kyau ki saka shi a mizani, Yarima yar kwalta ya auro, ki bani goyon baya ki sa hannu ya rabu...." Bata karasa maganan ba idanun ta suka hango Yarima a tsaye yana huci kamar zaki, kofin da yake hannun ta cike da ruwan itacen berry ne ya fadi, ta miqe a razane, tafiya ya fara yi cike da ban tsoro kamar saurayin zaki, idan da zaka taba kirjin Kilishi zaka ji kamar ze fado kasa saboda tsabar bugawan da yake, kaiii ita bata taɓa tunanin tana shakkun sa ba sai yau ɗinnan, karasowa gaban ta yayi ya tsaya, tun kapın yayi yunkurin aikata wani abu yaji ance masa
"Kul, kar ka kuskura"
Su uku ne kap duniyan nan suka isa su hana shi yin abu kuma ya hanu, be dauka zata shigo a irin wannan yanayin ba, amma naɗe bar matar nan ta sha ba, wato sai da taga baya nan zata wa Hafsa sharri?, juyawa yayi ya fice a sashen gabaki daya ya nufi dakin maganin masarautar domin yaga yaya jikin hafsan, domin Seda ya fada idan har ta tabbata yaga koda kwarzane ne a jikin ta, besan iya abinda ze iya aikatawa ba

Sarauniya Babba dai ko a jikin ta abinda ya faru, ita sam bata ga laifin sa ba, idan yace ze yi wa Kilishi abu tasan be dace ba tunda matar ubansa ce, amma still de ita bata ga lefin sa Ba gaskiya, hankalin ta ma ta maida kan Kilishi da take ta huci bakin ciki kwance akan fuskar ta, se Fulani da take kokarin zama domin ta gaida ta.



MİSS FADREES 🖋️ 🖋️
09020588802


Ban yadda wani yayi amfani da wani sashe na littafin nan nawa ba, ba tare da amincewa na ba, domin zan dauki tsattsauran mataki akan hakan, dan haka a kiyaye.

Idan littafin nan kake nema, complete ko wani sashe toh ga nan numbern waya na a sama duk me san yayi min magana, ya min ta nan.

Da fatan an fahimta.
Nagode.





>>>>>>>>>>>>>🖋️💻







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss Bello🖋️🖋️
Wattpad; fadrees_20


Page 37



Hakkin Mallaka nawa ne Ni Fatima Idriss Bello
Ban yadda a juyamin littafina ta ko wane irin tsiga ba, ko kuma ayı audio ba tare da izinina ba domin hakan ze iya janyo ma mutum matsala.
Dan haka a kiyaye.


Shigewa sashen dakunan maganin masarautar yayi fadawa na take masa baya, dogarai biyu ya gani a bakin dakin farkon wanda hakan ya tabbatar masa da Hafsan tana ciki, kapın ya shiga ya aiki bafaden shi ɗaya akan yaje a bincika wadanda suka ma Hafsa haka ayi ta dukan su har se sun dena motsi, ayi musu abinda ko nan gaba aka ce yatsar matar Yarima ba ma Yarima ba sai sun tsorata, kapın anjima yaje ya musu nashi kason na musamman, nan kuwa ya shiga cikin dakin maganin tare da yin sallama can kasan makoshin sa, bafaden kuwa a guje ya ruga dan yaje ya isar da sakon me girma Sarkin gobe.
Hafsa ya hango a kwance idanun ta a rufe alamun bacci take yi, ƙarasawa yayi gun ta tare da kama hannun ta, ɗayan hannun sa kuma ya kai bisa fuskar ta da ya kumbura yana tattabawa cike da kunan zuciya, zaman sa kenan akan gadon da take kai yaga hawaye ya gangaro daga idon ta na dama, a take ya miqa fuskar sa zuwa nata dan ya goge mata hawayen nata, ma'aikaciyar jinyar da Sarauniya Babba ta aika ɗazu me suna Zuwai ce ta fice a cikin dakin da saurin ta ma kuwa ganin abun yana soma fin karfin ta, gashi har sau biyu tana gaida shi be amsa ba, abinda bata sani ba, shi Yarima bai ma san wai da wanzuwar wani mutum a cikin dakin ba, harshen sa yasa akan fuskar ta yana me tanɗe mata hawayen nata, damƙe hannun ta yayi sosai a cikin nasa, yana saƙe saƙen irin hukuncin da ze baiwa dogarawan anjima, da har suka iya saka hannu wai da sunan dukan matar shi, matar sa fa? Kai inaaa.
Motsi yaga ta fara yi jin kamar abu me danshi akan kumatun ta nan da nan ta bude idanun ta waras, kokarin tashi ta fara yi shi kuma ya fara tallafa mata ganin shi da Hafsa tayi ta galla masa mugun harara tare da kwace hannun ta, ikon Allah Yarima ya tsaya gani, toh pa, ita kuma me take nufi da hakan, kodai laifin sa take gani ne?
Tsintar muryan ta yayi cike da tsiwa da rashin kunya tana faɗin
"Ni ka kyale, ai Allah Allah nake ka dawo in rama abinda aka min a kanka, wai har zaka yi tafiya baza ka gaya min ba, in Ni baiwar kace a da yanzu fa? Sannan tsabar wulakanci wai nice za'a ce nayi cikin shege? Naci uban baban cikin, wai ai na zubar da mutunci na a waje, a gidan baban ta na zubda mutuncin nawa? Nifa da kake ganina ko saurayi ban taba yi ba saboda bana jure wani abu wai kalaman soyayya, a gurin mutum daya nake jure hakan, wato injiniya. Injiniya yana matukar so na, duk sanda zezo gidan mu da leda yake zuwa amma dube ka fa ko magana baka cika yi min ba ballantana inyi tsammanin leda, sannan na tabbata da injiniya ne baze bari a min haka ba se ya dauki mataki, amma da yake kai ka tsaneni ai ko murmushi kapı karfin kamin, Ni ba abinda yafi bata min rai kamar yadda dogarawan nan suka damqi hannu na se kace sata nayi, ita kuma wannan munafukar larai take ko waye hadda taba min idona tare da laluba min kirjina wai ina da ciki" se kuma ta karashe zancen nata tana kuka da mugun ihu, jin bayanan ta ya matukar harzuqa Yarima, wato ma dogaran har jikin ta suka taba, jikin matarsa fa imagine, zuciyarshi ce tayi baki ransa ya sake mummunan ɓaci, ita kuma dayar hadda taba mata kirji well done, Bama wannan ba wai Hafsa ce ke yabon wani namijin da ba shi ba a gaban sa kuma.
"Zaki rufe min baki ko sai na kakkarya ki" ya daka mata wani mahaukacin tsawa, ai Hansai ba'a san ma an rufe bakin ba, amma yatsina kam taci gaba dayin shi, sannan ashar ma ta ɗuɗɗura masa ta cikin zuciyarta juya mishi baya tayi sai can ta ɗan waigo wai dan ta kalle shi, se taga baya ma cikin dakin, ita kam taɓe bakin ta tayi ta cigaba da abin take, da taga zaman dakin ya ishe ta, ta miqe ta fice domin yanzu duk ma'aikatan jinya haushi suke bata, sannan ga wani uban jiqe jiqe da ake bata tasha, to wannan in har cikin ne da ita ai ya isa ya ɓarar mata dashi ma, duk inta tazo wucewa sai an zube an kwashi gaisuwa, su hajjaju Hansai harda murmusa wa, daga nan sashen Kilishi ta wuce, bayin ta na ta mata magana tayi banza dasu ta wuce uwar dakan Kilishin, tazo shiga amintacciyar baiwar Kilishi ta toshe hanyan wai Kilishi tana bacci bata san damuwa, bangaje ta Hafsa tayi, gashi dama matar tsofai tsofai da ita, nan ta fadi hadda ƴar ƙaranta tayi shigewar ta ciki, zagaye dakin tayi bata ga kowa ba, abin se ya bata mamaki, leqa makewayin dakin tayi taga shima empty, nan ta tsaya cike da dumbin mamaki.
Can dai kusan minti biyar da taga shiru, sai ta juya tayi ficewar ta a dakin, tana karasa shigowa dakin shakatawar tayi karo da Hayatu, kallon ta ya tsaya yi baya ko kyaftawa, itakam ko kallo ma be ishe ta ba, gurin kofa tayi se kuwa taci karo da Yarima a tsaye yayi folding din hannun sa ya zuba ma Hayatu ido yana mamakin irin kallon da yake bin Hafsa dashi, nan yaji ransa ya sosu, daman fitan da yayi ɗazu yaje gun dogarawan da suka daki Hafsa, yayi handling nasu yadda Yakamata, bayan ya koma dakin maganin se be ganta ba, sai wani bafade ke fada masa yaga tayi sashen Kilishi shine fa ya biyo bayan ta, yana shigowa kuma yaga Hayatu yana mata wani irin kallo, bama wannan ba duk tsawon lokacin da ta dauka ina Kilishin take toh? Da yaga ba me basa amsa sai ya karasa , fisgo hannun ta yayi ya kama janta, se neman kwace wa take ta kasa, nan taci gaba da binsa kawai kamar jela.

_________________

Flashback

A dakin shakatawar sarauniya babba kuwa Fulani ce ta kwashi gaisuwa a gurin Sarauniya Babba ita kuwa ta amsa mata, Kilishi kuwa har lokacin jikinta be dawo daidai ba domin fadawa duniyar tunani ma tayi, yanzu yanzu zata tafi gurin shugaba taje ta fada masa abinda ake ciki, wato Yarima so yake ya kai mata hannu ko meye? Ita shine abinda bata fahimta ba, ba komai ko yayi niyyan yakai mata hannu ko beyi niyya ba sai ta hargitsa rayuwar sa, wallahi billahi sai taga bayansa, wallahi sai taga bayan Hafsa, idan kuwa aka ga ta bar shi yayi sarautar Bauchi sede in bayan ranta, a yanzu ma sai ta hana su zama, zata tabbatar da zaman masarautan nan ya gagari wancan baiwar matar tasa, wlh zata dau fansa, babban fansa ma kuwa, domin shine ma babban dalilin da yasa ta yadda ta aure ubansa, Ta ja da ubansa da waziri ma bare shi karamin alhaki? Wlh zata dau fansa, sarauniya babba ce tace mata 'lafiyar ta kuwa tayi shiru ana mata magana'? Sai a lokacin tayi yaqe ta dawo da hankalin ta kansu ta fara magana kamar haka
"Ba haka bane sarauniya babba, kawai ina mamakin yadda Yarima yayi behaving ne yanzu, me yake nufi kenan, kaimun hannu zeyi ko meye"? Ta karashe cike da nuna tsantar kunci, sarauniya babba ce ta taɓe baki cike da halin ko in kula kana tace
"Toh ai shiyasa Hauwaó take baki hakuri ke kuma bakya ma jin ta"

Fulani ce tace "kiyi hakuri Sadiya kinsan halin yarin zamanin nan, ka haife su ne baka haifi halin su ba, ai ke me masa gyara ce ba Me fishi dashi ba, sannan yarinyar nan ita ce ta maida shi haka amma dai ki yi hakuri"
"Ba komai kawai, komai ya wuce, Nima tunanin da nake kenan, ba yadda za'a yi Yarima yayi haka dan gashin kanshi, wa ya sani ma ko shanye shi tayi" Ta karshe cike da munafurci domin burin ta bai wuce taga tayi manipulating Fulani ba, dan idan Fulani ta tsani Hafsa burin ta zai cika.
Ita dai Fulani shiru tayi tana dan nazari, ganin haka Kilishi ta miqe tayi wa sarauniya sallama ta fice abinta dan zuwa gun shugaba
Su kuma anan nasiha sarauniya babba tayi ma Fulani tace kar ta dauki maganan Kilishi, ta riqe surukar ta dakyau dan ta lura yarinyar itace ce kariyar Yarima a gun makiyansa, shiru Fulani tayi tana nazarin maganan
Hiran su suka ɗan taba kapın Fulani ta koma sashen ta cike da tunanika kala kala a ranta.

FADREES 🖋️.



38


Kilishi koda ta wuce sashen ta ko takan bayin ta da suke mata sannu da zuwa bata bi ba, kashedi me kyau ta zana musu akan zata yi bacci kar a bar kowa ya shigo bata san damuwa idan kuwa aka saɓa an san halinta.
Shigewa tayi ta tura ƙyauren dakin da kyau, haduwa taje tayi da kafoor, tun kapın ma ta zayyano masa komai shi ya zayyane mata
Abinda ya fada mata next ne ya matukar girgiza ta
Da muryar sa me sauti uku uku taji ya kama magana
"Wannan yarinyar babbar kalubale ce a gare ki, domin yanzu haka tana cikin daƙin ki tana neman ki bata ganki ba"
Kusan targaɗe Kilishi tayi cike da mugun firgici dan har seda ta fadi ma, me kenan? Hafsa a cikin dakin ta, sannan taga bata nan? Innalillahi wa inna ilaihirraji'un
"Ki nutsu, ba'a mana salati anan sannan ta riga da ta fice ma, maganin da nace Miki kwanaki za'a je kasar sin a karbo, toh an sami aljanin da zeje saboda haka ki kwantar da hankalinki, sannan Sulaiman da Idriss sun saka wani bawa ya dinga bibiyar al'amuran ki sbd haka se ki kiyaye"
Mamaki ne ya kama Kilishi wato abin har ya kai haka, wannan kam ba komai bane tunda ita ba inda take zuwa ballantana ya sa mata ido, bata ma sa abun a ranta ba, amma dai gaskiya tayi mamaki, wato yakamata ta ƙara karfin ta kenan dan ta lura makiyan nata dayawa suke, hadda su Sulaiman ƙaramin alhaki.
"Amma shugaba baze yiwu a kashe ta bane gaba-daya yanzu yanzu"?
"Ban san ki da tsoro ba saboda haka iii sake hakuri ki jira, sannan kici gaba da ƙulle ƙullenki kafin maganin ya iso, watakila kapın ma maganin ya kammala kin korata, in yaso se a mata amfani da maganin a kashe ta kawai".
Yana karashe fadar haka, ta san ya gama da ita kuma, nan ta ɓaco ta dawo dakin ta".
Fitowa tayi ta sami amintacciyar baiwar ta, ta aika dogari da yazo ya mata bulala ashirin na ƙin bin umarnin ta da tayi, har tabar Hafsa ta shigo dakin ta, shikam Hayatu ko a jikin sa dan ko A bece ba, abinda ya kawo sa yayi ya fice, wato gaida mahaifiyar sa dan Shamsu ya ɗan zaga gari ne yasa basu zo tare ba.
Wannan kenan
_________________

Suna shiga part din su ya shaqe mata wuya kamar ze kashe ya, tari ta fara yi tare da buga hannun sa da nata, kakarin mutuwa ta fara yi, Seda yaga ta galabaita kapın ya kyale ta
"Wannan ya zamto rana na farko da na karshe da zaki sake ambaton sunan wani namijin da bani ba a gabana, kai bama gabana ba, a ko ina ma idan kuma ba hakan ba Ni kaina bansan iya abinda zan iya aikata miki ba" y karashe idanun sa kamar zasu fara ci da wuta tsabar jan da suka yi, Hafsa kuwa saboda bala'in taurin kai, tsintar bakin ta tayi da fadin
"Ehh din na fada, Injiniya yafi ka, ba kasheni zaka yi ba, ka yanka Ni da raina, kuma na tabbata da injini..."
Kasa ƙarasawa tayi saboda ganin a yanayin da yake kusanto ta, kaman Wani Sarkin zakuna, bata ankare ba taji ya bata wani zazzafan sumba, domin labbanta ya kama kamar ze cire mata su, dukan kirjin sa ta fara dan ya sake ta amma yayi biris da ita, zafi sosai ta fara ji a labbunan ta kamar saka reza ake ana yayyanka mata su, hawaye ne ya fara zirara a idanun ta dan bata ma da bakin yin ihu, be kyale Hafsa ba seda ya gaji dan kansa tukun, sannan sam beyi nadaman yin hakan ba, ashariya ta fara surfo masa a cikin zuciyarta tana kallon sa cike da baƙin cikin abinda ya aikata mata, abinda ya fada mata next ya matukar harzuqa ta
"Ina binki a hankali ne dan ina Miki kallon yarinya kuma baiwa ta, amma a yau yau ɗinnan kin nuna min hasashe na ba haka bane, yanzu yanzu zan raba ki da abin naki da kike wani ji dashi"
Ran Hafsa ne ya ɓaci jin furucin shi, wato itace baiwar tasa, toh wallahi billahi be isa ya rabata da budurcin ta ba, wlh se ya sake ta a yau yau ɗinnan ta kama hanyan ta, idanun ta ta rufe tare da manta waye a gaban ta ta fara masa magana cike da hargagi
"Idan har ka cika sunan ka Idriss ka bani takardan saki na a yanzu yanzu"
Shikam dariya ma ta bashi sosai, 'lalle kam ta tabbata taga gurin baccin sa, wai takardan saki, jin yayi banza da ita ne ya sa ta sake maimaita masa, tsaya wa yayi yana kallon ta, tare da tunanin wane kalan hukunci ze bata ne kam ya huce takaicin sa
"Ka bani takardan saki na nace" ta sake maimaita masa cike da jin matsananciyar haushin ta domin lebban ta har yanzu zafi suke mata
Lalle ma yarinyar nan, ai da shi da ita mutu ka raba takalmin kaza, wlh babu wanda ya isa ya raba sa da ita koma waye kuwa, kai har Mai Martaba da kansa, sede idan mutuwa, mutuwar ma baya fatan ta raba sa da ita, yafi san ta dauke su tare, ko kuma ta dauke sa shi ɗaya, kai duk da yasan ba santa yake ba, yasan abu daya, baze iya rayuwa babu ita ba, itace ruhin sa, ita tashi ce har gaban abada, wanda ko yayi gigin cewar ze shiga tsakanin sa da ita hmmmm,
Ina ga bata san tashin hankalin da ya shiga bane da akace masa wai an taba jikin ta, sannan yanzu da yaga Hayatu da irin kallon da yake mata, se yaji ransa yayi masifar ɓaci, ba dan komai ba se dan shi baya san a raɓi abinda yake mallakin sa, wannan shine policyn sa, sannan injiniya da take masa magana akai inaga zai yi mata barazana dashi.

Ganin ya shiga duniyar tunani Hafsa tayi abinda bata taɓa masa ba, wato taba jikin sa da hannun ta,
"Ko dai ka mutu ne a tsaye"? Ta tambaye sa tana me shafa fuskan sa, a lokacin ya ankare ya dawo tunanin sa
Kallon ikon Allah ya mata se can yace mata
"Ba kince in baki sallaman ki ba? Toh ai mu ba'a saki a Wannan masarautar"
Duk da Hafsa najin matsanancin kunyar sa bisa ga abinda ya faru yanzu a tsakanin su, be sa ta kasa basa amsa ba
"Toh sai a fara daga kanka"
Giran sa daya ya daga zai bata amsa suka ji ana knocking din kofar dakin shakatawar, Hafsa ne taje ta bude, taga megida sulaiman ne, durqusawa tayi tare da gaida shi, amsawa yayi tare da cewar
"Nine ai Yakamata in gaishe ki sarauniyar gobe, kodai in koma ne, naga kamar na shigo a lokacin da be dace ba"
Murmushi tayi tace masa "a'a Wlh ranka ya dade, sannu da shigowa"
har zata shige dakin ta taƙi shiga ta tsaya, ayi koma me za'a yi a gaban ta"
Tana jin su suna ta maganar Abinda ya same ta, Sulaiman ne yace ta karaso ze mata tambaya
Karasowa tayi tana me hararan Yarima, akan idon Sulaiman kuwa, aiko seda ya murmusa, zama tayi akan kafet din falon ya fara da tambayan ta 'Me taci kapın tayi amai?'
Tace masa "shinkafa da miyar naman dawisu, sannan da baiwar ta zuba min ma seda naje na leqa dakin WANNAN inga ko yana nan yazo muci ban gansa ba, har makewayi seda na leqa baya nan, da na fito har nayi zuciya akan bazan ci ba naje Naci, sai bayan kaman awa hudu na kama jin wani gigitaccen amai, dana fara yi kuwa seda nayi kusan minti sha biyar ina abu daya ina fitowa kuwa naga su Fulani a cikin dakin shaqatawar.

Sulaiman ne da Yarima suka jinjina kansu cike da gamsuwa
Muryar Sulaiman ta tsinta
"Ni ina tunanin an zuba Miki abu ne a cikin abincin naki, amma yanzu xansa a binciko min"
Hafsa ce ta kuma cewa "Sannan Me gida Sulaiman, yanzu da naje sashen Kilishi aka cemin tana bacci da na shiga cikin kuma bata nan hatta makewayi seda na duba bata nan",
"Kar ki damu da wannan na saka Bawa ya sa ma Kilishi ido duk inda zata je daga yanzu akan idon mu ne, zaki iya tafiya".

FADREES 🖋️

_________________





>>>>>>>>>>>>>🖋️💻







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss 🖋️🖋️
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20

Page 39



Hakkin Mallaka nawa ne Ni Fatima Idriss Bello
Ban yadda a juyamin littafina ta ko wane irin tsiga ba, ko kuma ayı audio ba tare da izinina ba domin hakan ze iya janyo ma mutum matsala.
Dan haka a kiyaye.


Kin tafiya tayi da Sulaiman yace mata ta tafi gashi shi so yake su dan tattauna su biyu,
Muryar Sulaiman tajiyo a karo na biyu "Zaki iya tafiya Malama Hafsa"
Cuno bakin ta tayi tana hararan kasa, shidai gogan kallon ikon Allah yake mata, wai bayan rashin kunyan da ta masa wai shine ma take addressing nasa da wai 'wannan' Wato ma shine 'WANNAN' din, ya Ilahi🤧 kenan bata san sunan sa ba, amma in be manta ba ai dazu ta gama kiransa da sunan sa na yanka wato 'Idriss' akan ya sake ta wai.
Yana gani ta shige dakin ta har a lokacin sumbatu take ita daya, girgiza kansa yayi domin shikam Allah ya jarrabe sa da auren mafaɗaciya.
Ɗaga idanun sa yayi wai yaji me Sulaiman din zece masa, se yaga Sulaiman din kallon sa yake yana dariya ƙasa ƙasa, kallon lafiya kuwa? Ya jefe shi dashi, shi kuma Sulaiman se bece komai ba suka ci gaba da tattaunawa, da hantsi suka je sashen me Martaba, suka samu ya tara iyayensu mata da kuma sarauniya babba, waziri ne ya tambaye sa shin gaskiya ne abinda ake zargin matar sa dashi, ƙaryata wa yayi, me Martaba ya sallame su daga nan barga ya wuce yaje ya samu favorite dokin sa ya hau yana ta sukuwa yana tunanin zancen Hafsa, wai injiniya ya fishi komai, bari ze seta mata tunani ai.

Bayan Wata Uku

Wanda ya kama watan Hafsa uku da zama matar aure, Abubuwa da dama sun faru a cikin watannin nan uku, ciki kuwa harda dawowan Murja sashen Yarima da aiki, wanda hakan ya kasance cikin aikin Hafsa ne, sannan daman bayi hudu aka ware mata dan su dinga mata hidima, murjan se ta zamto ta cikon biyar din, yau daman jiran sa take ya dawo ya bawa Murja takaddan sallaman ta, duk da tasan za tayi missing Murja gara kawai ta sallame ta dan tana tsoron kar Kilishi ta haɗa da Murja a cikin shirin ta, dan ranan da shafa'atu taje ta sami su Murja da Lantana ta fada musu cewar Hafsa ce matar Yarima ba karamar girgiza suka yi ba, tun daga lokacin Murja take ta neman hanyan da zasu hadu da Hafsa har Allah ya bata nasara ranar da Sulaiman yazo suka fice shida Yarima, shine ta samu tayi sneaking ta shigo ciki, da farko da tayi knocking ƙin buɗewa Hafsa tayi, ita kuwa taci gaba da buga kofar, sai a sannan Hafsa ta buɗe da niyan yin masifa, sai kuma ta gamu da Murja, janyo ta tayi ta rungume ta suna tsallen murna, ƙaran tafiya suka ji, Hafsa ta juya taga waye se taga ashe suma su shafa'atu sun biyo sahun murjan, nan kuwa ta bude musu suka shigo suka zauna, suna ta hiran yaushe gamo, Hafsa ne ta lura da yanda su Lantana suke ɗar ɗar da ita, ita kuwa ko a jikin ta tace su saki jiki da ita, can sega bayin da suke mata hidima sun shigo da kwandunan abincin dare, karba tayi ta zuba musu su kuwa suka dinga ci, daman yunwa suke ji kamar suyi me, sai can da dare suka mata sallama inda tace musu duk sanda suka ji yunwa suxo suci anan, Murja ce tace mata ai yanzu an maida ta sashen madafa da aiki, Hafsa najin haka ta ce mata, toh daga yau ta dawo nan kenan da aiki, wanda ba kuma aikin take yi ba, hiran su suke sha, se dare take komawa, Yariman ma ba ganin ƙafarsa take ba, dan tafiya sukayi shida Suleiman seda suka yi wata kamin suka dawo shekaran jiya, sannan tunda ya dawo sau daya ta sashi a idanun ta, yanzu ma jiran sa take ya dawo suyi ta ehe.

Sai can dare bayan su Murja sun jima da tafiya tajiyo karan bude kofa, likimo tayi kamar me bacci, shi kuma har ze wuce dakin sa yaga ya dace ya duba Hafsa, sannan yana so ya mata kashedi bisa ga abinda yaji ya faru da baya nan, dole ne yana mata kunne
Ilai kuwa bata yi bacci ba kamar yadda yake tsammani , sai murtsuke idanun ta take ita ala dole bacci take, kunnen ta ya kama yaja da karfin sa, ihu Hansai ta saka yadda kasan ranta ake cire mata
Hararan da ya daka mata ne ya sata shirun dole tana sumbatu a kasan makoshin ta.
Tambayan da ya mata ya bata mamaki, kenan da aka ce akwai en gulma a masarautar ashe da gaske ake, akwai su sosai
"Da izinin wa kika fita kika

Please Login or Register in order to submit comment