Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ni sai in warkar da ita, in yaso nan da mako shida daman muke tsammanin dawowan Gopal sai mu kashe ta gaba-daya kawai, duk da na lura malamin da zasu kawo din shima hatsabibin malami ne, yasha kashe aljanu da bokaye, amma dai kamar yanda kika sani, Ni ba kowane kalan boka bane, Ni Boka Gagara Badau ne, duk me iya ja dani sai yayi da gaske, nan ya saki wata mummunan dariya"
Jin abinda yace tasan ya gama magana, tashi tayi ta ɓace abinta, ta koma dakin ta, dama bata yi Isha ba, tana yin sallan ta tayi kwanciyar ta, se kuwa bacci me armashi yayi gaba da ita.

________________

Bayan su Hamisu bawa sun kwana a hanya washegari kusan rana suka isa ƙasar Yobe, da suka yi tambaya aka musu kwatancen mutumin suka ce eh shine, ce musu aka yi ai a garin nangere yake, dan haka suka kama hanyan Nangere, da tambaya suka je su lokacin marece yayi lis, tambaya suka yi ta inda gidan Malam na bakin rafi yake, nuna musu akayi suka tafi, ilai kuwa, gidan nasa a bakin rafi yake, dakyar da siɗin goshi suka samu ganawa da Malam na bakin rafi dan mutanen da suka tarar a gidan nasa basu ƙirguwa saboda yawansu, wasiqa Hamisu ya baiwa malam na bakin kogi, da ganin haka ya amshe su hannu bibbiyu kana ya basu dakin kwana, washe gare da sassafe suka bar kasar Yobe suka kama hanyar Bauchi, kwana ɗaya takk suka yi suka isa, inda aka ma Malam tarba na karamci, ko hutawa beyi ba yaje ya duba Hafsa, yana ganin ta yasan aikin jinnu ne saboda haka ya bata magani me bala'in karfi yanda ko nan gaba baza a iya nasara a kanta ba, bayan ya kwan biyu yana lura da Hafsa a kwana na uku ya kama hanya bayan uban alherin da aka masa a Masarauta, me martaba shi kansa besan iya alherin da ya masa ba, a haka ya koma Kasar sa ta yobe a cewar sa yabar majinyata dayawa suna jiran sa

Daga nan Hafsa ta samu lapiya, suka sake gina sabuwar rayuwa ita da Yariman ta.
Bayan kamar sati biyu suka sake fita cikin gari ita da Yarima akan keken doki, sede kamar wancan karan kayan talakawa suka sanya a jikin su, dan kar suje a dinga basu girmamawa na musamman, da suka je wurin wani me saida su ƙoyaye dasu gasassun kaji Hafsa tace tana so zata ci, yarima yace baza taci abincin kan hanya ba bayan tasan tana dauke da ciki ga abincin kan hanya ba tsafta, nace masa tayi a karshe dai sai da ya siya aka soya musu kwai aka zubo musu gasassun kajin, cewa tayi a baki ze bata, ba yanda ya iya ya dinga bata har ta ƙoshi, shima tace masa se ta basa, yace baze ci, karshen ta dai ɗure ta masa, tsabar yanda suka cika cikin su dakyar suke tafiya, da zasu tafi suka biya wa duk wanda suka zo siyan abu a gun kudi, zo kuga murna a gun mutane, se kirari ake ta musu da addu'o'in Allah yabar su tare, da suka fito suka samu wani waje a waje suka zauna suna kallon wata da taurari, hafsa ne tace masa
"Mijina ka kalli taurarin can yanda suke haskaka sararin samaniya, amma kuma ka lura ai wata yafi haske, su taurarin ƙawata saman suke yi"
Murmushi ya mata dajin haka, kana yace mata
"Kece tauraruwa ta Abar ƙaunata, bazan taba dena sanki ba har abada"
Ita kuma dariya tayi tace
"Ni kuma kaine Wata na, bazan taba dena sanka ba har abada"
Murmushi me cike da kasaita ya sake saki, kana yace ta miqe su koma masarauta dare ya fara tsalawa sosai,
Miƙewa tayi suka shige keken doki har a lokacin suna rungume da juna, acikin keken dokin take ce masa
"Kasan lokacin da kake saka fadawan ka su dake Ni irin ashar din da nake ɗura maka kuwa?"
Murmushi yayi sosai yace
"Na sani mana, ai Allah ne ya dora ki a kaina"
Ya bata amsa
"Wato baza ka bani hakuri ba ma, ai wlh naso dana aure ka in hukunta barau, kawai na kyale sane saboda haƙuri na"
Ta karashe tana hade rai
Dariya yayi a ranshi wai 'hakurin ta', chap in ka taɓo Hafsa ai ka taɓo bala'i.

Haka rayuwa taci gaba da tafiya, inda yau Gopal ya dawo daga kasar sin, riqe da maganin da yaje dakkowa, sede yana kawowa ya mutu, dan rabin jikin shi ya shanye a garin fafutukar nemo maganin, domin yasha bakar wahala, dan a cikin Sardaunan aljannu she sadauki me sosai Seda yakai inda ake bukata kamin ya tafi, ganin haka aljanu suka fusata suka daura lefin akan Hafsa, boka Kapoor yana karbar maganin ya saka wata razananniyar dariya me ban tsoro tare da yin hawayen jini, kamin yace

"Lalle in ban kashe yarinyar nan nasha jinin ta na baiwa aljannu na jinin ya'yan ta ba ban cika zama shahararren boka 'Gagara Badau kafi kowa ba', na rantse da tsafin kakanni na se na dauki fansar Gopal na sadaukar da rayuwar sa da yayi, dole ne in dauki fansa, fansa, fansa, Hahahahaha"
Ya karashe cike da dariyar mugunta, wani siddabarun tsafi ya fara, kamin ya raba maganin da Gopal ya kawo kashi biyu, kashi daya ya aika zuciyar Hafsa, kashi dayan kuwa dashi ze dinga bawa duk mai neman taimako a gunsa taimako.
Wannan kenan.

FADREES 🖋️🖋️🖋️ Ƴar Mutan Yobe 🤍.




49



YARIMAN HAFSA
(A Royal Love Story)
Mallakar Fatima Idriss Bello



Arewabooks; Fadrees20
Wattpad; Fadrees_20



Ban yadda wani ko wata suyi amfani da wani sashe na littafi na ba, ko ya haɗa min audio ba tare da kwakkwaran amincewa ta ba, idan naga akasin haka kuma wlh baza mu wanye lapiya ba dan haka a kiyaye.



Bayan wata ɗaya, wato watan haihuwan Hafsa ya kama kenan, daman tun da ta samu lapiya sarauniya babba ta kora su daga sashen ta, Sede ganin yanzu tana watan aihuwa yasa sarauniya babbar cema Yarima akan Hafsa ta dawo sashen ta shi kuwa gogan yayi kunnen uwar shegu da ita.

Zaune Hafsa take, tana me rubuta wasika, yawancin kwanakin nan zakaga tana yawan rubuta wasiqu musamman ma idan Yarima baya nan ya tafi fada, buɗe wani wasiqa tayi taga daga Jamila ne, karantawa tayi tana murmushin jindadi kamin ta maida mata amsa.
Gama rubutawan ta kenan ta afka duniyar tunanin yariman ta, daga cewa zeje ya dawo ta ji shi shiru, zasu haɗu ne ai, ta ɗan rufe idon ta kenan se taji kaman wani abu ya soke ta a ƙahon zucin ta, ji tayi ya fara mata zafi, salati ta fara saki, nan da na ta fadi sumammiya dan zafin ya zarce wa lissafin ta.
Can bayan kamar awa biyar Yarima ya shigo sashen da sallama bisa bakin sa, a kwance yaga Hafsa kamar ma bata numfashi, karasowa yayi gunta, ilai kuwa kwance take jini yana zuba daga hancin ta, besan sanda ya sumgume ta yayi waje ba sai dakin jinyar Masarautar.
Zuwai ce ta fara duba ta da gaggawa, bayan tace ya tsaya daga waje, dakyar ta samu jinin ya ɗan tsaya, fitowa tayi tazo gun da yake, tace masa
"Allah ya baka nasara, nidai a binciken da nayi na kasa gano komai, dan ba nakuda take ba, ina roqon alfarmar da a sake zuwa a kawo wannan me maganin in ba haka ba, ina mai tsoron rayuwar ta yana cikin matsala, dan idan nakuda ya kama ta baza ta iya aihuwa ba, karshen ta zata iya rasa ɗan cikin ta ne".
Da jin haka Yarima ya fice zuwa sashen Sulaiman, tun kafin ma ya isa labarin rashin lafiyar Hafsa ya karade ko ina, koda ya isa sashen Sulaiman sai be same sa ba, dogaran da suke gadin sashen ne suka ce masa yana sashen sarauniya babba, can kuwa ya wuce da sassarfa, yana isa ya hango su suna tahowa da sauri hadda sarauniya babba, daga alamu inda ya fito zasuje, suna ganin sa suka karaso inda yake, tambayan Sulaiman yayi bawan sa Hamisu, ba'a jima ba Sega Hamisu, yana zuwa aka saka su shirin sake zuwa ƙasar Yobe, kwana ɗaya da rabi ya kaisu Yobe garin Nangere inda suka je basu samu Malam na bakin rafi ba, wai yayi doguwar tafiya ze kai mako huɗu ko ma fiye da haka kapın ya dawo, da sakewar jiki suka kamo hanyan dawowa, suka sanar da su Yarima abinda ake ciki, daga nan fa hankula ya sake dunguma ya tashi, nan da nan kuwa masarautar Bauchi ta dinga aika wasiqu zuwa Masarautu daban daban neman masu magani amma a banza, dan ciwon Hafsa sake gaba gaba ma yake, gashi ana tsaka da haka ne ta kama naquda, fadin irin kalar azabar da take sha ma bata lokaci ne, sannan har a lokacin hannun ta na damqe Kyallen can

Bayan mako uku, zan iya cewa Hafsa ta gama galabaita, idan har kai musulmin kwarai ne dole ka tausaya mata, hatta da makiyin ta nasan in yaga kalar azabar da take sha dole ya tausaya mata, an sake aikawa kasar Yobe har yanzu Malam na bakin rafi bai dawo ba, sannan har lokacin kyallen na hannun ta, dakyar yau da siɗin goshi zafin naquda yasa ta saki kyallen shi kuma Yarima sai ya ɗauka a hannunsa yana jujjuyawa, fita yayi ya samu Sulaiman ya nuna masa, se yace masa ai wannan kyallen ya kalla irin sa a cikin kayan wannan bawan da suka saka ya binciki Fulani, shima har yariman yace ya tuna.
Ai kuwa Sulaiman na fita ya aika a dubo kayan bawan, anje aka ga kaya a ƙone, dan ko toka ba'a samo ba, sannan babu kyalle babu dalilin ɓatarsa, ganin haka Yarima ya ajiye na gunsa dan yayi bincike akai.

Bayan mako ɗaya, lokacin Hafsa ta fige ta matuqar ramewa da galabaita, lokacin haihuwar ta har ya wuce amma shiru ba labari, sake aikawa akayi Garin Malam na bakin rafi lokacin duk masu bada maganin gargajiyan kasashe daban daban sunzo sun gwada amma Sede abu ya lafa, bayan kwana biyu kuma ciwo ya sake tashi.
Duk sanda Hafsa ta dawo hayyacin ta zaka ganta tana kuka, Yarima kuma ya dinga rarrashin ta kenan dan baya barin gefen ta, duk laifin kan sa yake gani, da be tafi ya barta ba, da ai ƙila yanzu tana lafiya.
Bayan wadanda aka aika Yobe sun dawo, se suka sanar da basu same sa ba still sede ance musu malam na bakin rafi kwana hudu ze kara ya dawo, Sulaiman ne yace su koma in yaso su dawo tare da malam din.

4days later.
Hafsa ne aka samu ta ɗan yi bacci, yau kwanan ta biyu kenan bata farka ba, da farko da aka ga ta samu hutawa kowa dadi ya dinga ji, har Maman ta da Jamila sun dawo masarautar dan su suke jinyar nata, koda aka ga kwana biyu kenan bata farka ba hankula ya tashi, Maman tane akan ta Yarima ya shigo ya zauna can da yaga dai baccin take sai yayi miqewar sa yaje dakin sa ya dauko kyallen nan ya bude da kyau, shi be gane meye a jiki ba, koda ya fito ze koma dakin hafsan se yaga Sulaiman da Bilkisu a ciki, ido ya ma Sulaiman akan suyi waje, dakin shakatawa suka zo suka tsaya Bilkisu kuma ta shige cikin ɗakin, Yarima ne yake ce masa ya kalla kamar akwai rubutu a jikin kyallen, matsowa Sulaiman yayi suka kama karantawa tare, nan da nan suka gansu a cikin kogon boka Kapoor, abinda basu sani ba Malam na bakin rafi har ya kusa isowa cikin masarautar domin dasu Hamisu suka je sun same sa ya dawo sai suka taho tare kawai, shima beyi wani ja'in ja ba ya biyo su.

Koda ganin su a kogo me matsanancin duhu sai abun ya basu mamaki, daga karanta abu kawai sai su gansu anan?, kutsawa ciki suka fara yi, Kogo ne me girman gaske, tafiyar dawakai suka fara ji, sai kuma suka yo gamo da wani rapkeken zaki sai gurnani yake, fadin Irin tashin hankalin da suka shiga ma ɓata lokaci ne, kansu yayo su kuma suka tsaya, take kuma suka ga ya ɓace, da suka yi gaba suka dinga cin karo dasu damisa ne, kura ce da su Dila, duk dai aljanune suke shigen su da niyar su tsorata su, Sede abu daya ne, duk da sun tsorata a zuciyar su, se basu nuna hakan ba a fili, da kuwa sun nuna da sun rasa rayukansu domin aljanun tsoro suke so su gani a idon mutum dan su cimma mutumin.

Tafiya suka cigaba dayi suka hango haske suka apka gun hasken, ganin saniya suka yi da kan agwagwa, alade da kan mutum, Mami water a siffar maza, duk sharewa suka yi suka kutsa kai suka ci gaba da tafiya, suma shigowa gun hasken suka ga wata halitta a zukunne a gaban wani wargajejen halitta bisa wata kujera da akayi wa ado da kan zaki da kuma kan damisa na gaske, masu rai kuma, ƙafar Sulaiman ne ta kama rawa, zuciyar Yarima kuwa bugawa take fat fat, shidai in har zai sama ma Hafsa magani ya yadda ya rasa ransa.

Magana suka jiyo halittar dake durqushe nayi
"Ya kai shugaba, meyasa yarinyar nan bata mutu bane gashi yau watan cikin ta har goma, kodai an fasa daukar fansar ne? Kodai maganin da aljani Gopal ya kawo ba ingantacce bane, na rantse har da girman tsafin duk sanda na koma ina ganin ta da rai zuciyata baki take yi, sannan maganin da akace daga an dasa mata shi zata fadi ta mutu yau wata daya ake nema da dasa mata shi"

Dariya ya saki da murya uku uku yace
"Da badan addu'ar wani wawan malami wai shi Malam na bakin rafi ba da ta dade da ziyartan lahira, amma ina so ki sani na rantse da tsafin kakanni na baza ta tashi da rai ba, saboda wannan baƙin mutumin ne ai da ba haka ba, sannan shima bazan barshi da rai ba, Ku kuma kun kawo kanku halaka da kafafun ku, daman dan ku ake yin komai"
Ya karashe da razananniyar dariya yana me kallon su Yarima, juyawa halittar tayi wa zasu gani in ba Kilishi ba, sai a lokacin ƙafafun Yarima suka fara rawa.

Ɗaga allon sihirin sa yayi, da niyyar ya kashe su Yarima sai yaga abun baya motsi, wai ya ɗaga kanshi dan yaga wanene ya masa wannan katoɓarar se yaga Malam na bakin rafi a tsaye a gaban sa cikin ɓacin rai.


FADREES 🖋️ 🖋️ 🖋️ Ƴar Mutan Yobe.



50



YARIMAN HAFSA
(A Royal Love Story)
Mallakar Fatima Idriss Bello



Arewabooks; Fadrees20
Wattpad; Fadrees_20



Ban yadda wani ko wata suyi amfani da wani sashe na littafi na ba, ko ya haɗa min audio ba tare da kwakkwaran amincewa ta ba, idan naga akasin haka kuma wlh baza mu wanye lapiya ba dan haka a kiyaye.



FLASHBACK

Su kansu ganin malam na bakin rafi a gun ya matukar basu mamaki Sede sun samu relief sosai dan har seda Sulaiman yayi murmushin jin dadi tare da sakin ajiyar zuciya

Ashe koda Malam na bakin rafi ya iso masarauta aka kawo sa sashen Yarima direct, da ya shigo shine yaga yariman da sulaiman din kowanensu a zaune akan tumtum guda daya Sede kamar babu ruhi a jikin su, karasowa yayi kusa dasu, Hamisu na biye dashi, ganin hannayensu duka biyu yayi riqe da kyalle ɗaya daukan kyallen yayi ya karanta, daga karantawa shine ya ganshi shima a kogon.

_________________

Ganin allon sihirin sa ya tsaya ba ƙaramin mamaki boka kafoor yayi ba, juyowa yayi gun Kilishi yace mata
"Yau kwata kwata ban baiwa allon sihiri na jinin bil'adama ba, sannan Wannan allon sihiri shine gaba daya tsafi na, ina so ki sama min jinin wani yanzu yanzu"
Ya karashe yana me kallon Malam na bakin rafi cike da tsana.
Shikam malam na bakin rafi taɓe bakinsa yayi dan yau kam ba jini ba ko meye zasu yi Sede suyi dan se ya tarwatsa su, shi daman hanyar da ze same sa yake nema, kuma gashi cikin sauki ya same san, toh ai Barka, ya kuma gode Allah.

Kilishi ce ta kalli shugaba tace,
"Ga wadannan shugaba ka dauki jinin dayansu kasha" ta karashe tana me nuna sulaiman da Yarima, hantar cikin sulaiman ce ta kaɗa ganin abinda Kilishi tace, shi a rayuwarsa be taɓa tunanin Kilishi haka take ba, yasan cewar ita makira ce amma be taɓa zaton bata da imani ba sai yau, ashe dama azzaluma ce? Ashe dama mushrika ce? Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, shi kanshi Yarima abinda ke ransa kenan, gaskiya yayi underestimating din Kilishi sosai, ashe ita so take taga bayan su, Allah me iko.

Muryar shugaba ne ya dawo dasu daga duniyar tunanin da suka fada
"Wannan aikin da zamu yi dan ke zamu yi shi yar tsogai, sannan jini me ƙarfi muke bukata, gashi wannan tsohon banzan ya ma wadannan wasu siddabaru, in dai har kin amince kina san burin ki ya cika, Sede ki bada jinin ɗaya daga cikin ya'yan ki"
Sanda ya karashe fadan haka Seda Kilishi taja da baya, meye????😳😳
Ta bada jinin ya'yan ta inaaa, toh amma fa burikan ta zasu cika, kawai ta hakura da daya, ya zata yi.
"Ka dauki jinin dayan su kayi kawai"
Suka jiyo muryar Kilishi cike da tabbatarwa, wallahi wallahi Seda Yarima ya kusa faduwa da yaji batun ta, Seda Sulaiman ya riqo shi, wallahil Azeem Kilishi ba bil'adama bace, sam sam ita ba mutum bace, ɗanta fa fisabilillah, ɗanta na cikin ta fa, suna kallo ta cikin madubin sihiri sanda shugaba ya aika aljanin sa ya dauko masa ƙurwan Shamsu ya shanye, gani suka yi Shamsun yana ta burburwa kapın yazo ya dena motsi gaba daya.

Nan da nan shugaba ya zama wani halittan da ba'a taba tsammani ba domin ido baze iya jure ganin hakan ba, girma ya kara sosai kusan sau hamsin har kogon ya so ya matse shi, Kilishi kuwa wani murmushin mugunta ta saki, imani yana ƙara fita a ranta, koda ganin haka Malam na bakin rafi shima ya fara nasa addu'o'in suka shiga fafatawa shida boka Kapoor, ganin haka Kilishi ta dauki wani kifiya tayi hanyan Yarima da Sulaiman zata Çaka musu, da gudun su suka yi bayan shugaba, dan wani bahaguwar karfi ne Kilishi take dauke dashi, ganin haka ta kasa tunkarar shugaba se taja baya tabar ma shugaba su, kafoor yana yin wani siddabaru ba sai aljanu suka fara fitowa ba ana yin faɗar dasu? Gasu da manyan akaifu ga mugunta, Malam na bakin rafi ne ya taimaka ya fara basu wasu addu'o'i suka fara yi, dakyar da siɗin goshi suka samu suka fi karfin shugaba, dan seda dukkanin su suka ji ciwo hatta Malam na bakin rafi da kanshi, koda malam ya gama kashe su saura shugaba da Kilishi, gashi kafoor din ya galabaita, ƙona allon sihirin shugaba Malam na bakin rafi yayi, yana ji yana ta ihun azaba da radadi yana me fadin
"Ni Boka Dan boka jikan boka tsatson bokaye nafi karfin kowa, wayyoooo kayan tsafi naaa, wayyoooo, nan da nan ya fadi matacce"
Ganin ya mutu Malam na bakin rafi yace Sulaiman da Yarima su kama Kilishi kar ta gudu, ai kuwa suka damqe hannun ta tana ta zillewa ta kasa, a take kuwa ya ƙona kogon, bayan yaga kogon ya kone kurmus neyayi addu'a suka koma dakin shakatawar Yarima, already daman ya saka yaron shi ya fara duba Hafsa, koda suka iso falon, fada suka wuce da Kilishi, suna shiga fada suka ga a cike tam da mutane, ana cikin alhinin rashin Shamsu, kowa da kowa jikinsa a sanyaye yake, sai gani sukayi Malam na bakin rafi ya shigo shida su Yarima ga Kilishi riqe a hannu, sannan duk jikin su a raunace, ganin haka yasa Sarkin gida ya aika da ayi kiran kowa da kowa na cikin gidan, nan da nan kowa ya cika fada, masu kuka nayi, masu jimami nayi, kuma duk akan mutuwar shamsu da ya riske su yanzu yanzu, Malam na bakin rafi ne ya fada abinda ya sani game da boka da kuma Kilishi da kuma niyyar su ita da bokan
Koda Kilishi taji haka sai ta saka dariya me ban tsoro kana tace
"Kai a zaton ka Sulaiman zan bar ahalin ka haka ne, a'a, na aure ka ne saboda fansa, fansar abinda kuka min kaida Jafar, sannan yanzu da asiri na ya tonu, nasan zaka ce zaka hukunta Ni ne, toh nafi karfin hakan, wlh Ni Sadiya nafi karfin bin umarnin ka na iska bare wani hukuncin ka, kai bari ma kuji abinda baku sani ba, duk wani mutuwa da ake yi a cikin Masarautar nan, nine nake sadaukar da su ma boka na domin ya cika min burina na san daukar fansa, hatta da mutuwar da ɗana yayi yanzu nine na bada jinin ba, wlh billahi ko bayan raina fatalwa ta baza ta barku ku huta ba, musamman ma ke Fulani, wallahi wallahi na tsane ki, na tsani me san ki, na tsane ki kema sarauniya babba, kai ɗaya ne na taba maka so na gaskiya Sulaiman, Sede ka watsa min kasa a idona a lokacin da nake muradin ka, Sede har yanzu ina son ka, amma kuma na tsane ka na tsane ahalin ka, kai kumaYarima na tsine maka, kuma wlh alqawari na maka seka rasa farin cikin ka na har abada kuwa, kai kuma Hayatu, ina so ka daukar min fansa sannan ina so ka mulki wannan Masarautar hhhhhhhh"
Ta karashe da wani mugun dariya, gaba ki daya kowa seda ya saki salati a cikin fadan harda me martaba, Bilkisu kuwa ita da sarauniya babba da Fulani bakin su kasa rufuwa yayi saboda mamaki, wai duniya ina zaki damu, Kilishn da suka sani ce haka? Kai ina wannan ba ita bace anyi mata musaya da aljan dai.
Suna a haka sai gani suka yi ta ciro wani abu daga rigar ta ta saka shi a baki tana me dariya mara kan gado me cike da tsana, minti Uku bata yi ba tace ga garinku, jini nata fitowa daga bakin ta, Hayatu ne yayi kanta yana kuka, kowa a fadan kuwa kasa motsi yayi saboda firgici, wai rashin imani har haka?
Ficewa akayi aka fitar da gawan Kilishi, me martaba ne ya bada dokar kar wanda ya sallace ta, ai kuwa kowa ya gudu yaqi yi mata salla, Hayatu ne ya saka bayi suka kinkimeta suka je suka mata salla aka binne ta, suma ba'a san ransu suka matan ba dan umarnin yariman su ne shiyasa, da suka dawo ya sake zuwa kan Shamsu dake kwance a dakin nasu yana sakin kuka me matukar ban tausayi da kuma tsuma rai, hakika yayi rashi, ya rasa mahaifiyar sa da kuma dan uwan tagwaicin sa, ji yayi inama inama, inama shima ya bisu, sannan wai mahaifiyar sa daman haka take, ashe mahaifiyar sa azzalumace har zata iya kashe masa ɗan uwa, ɗan da ta haifa da cikin ta? Kai kaicon shi shikam, nan ya zauna ya dinga kuka a gun kamar karamin yaro, can zuwa yamma akayi wa Shamsu sutura aka kaishi makwancin sa.


FADREES 🖋️ 🖋️ 🖋️ Ƴar Mutan Yobe



51



YARIMAN HAFSA
(A Royal Love Story)
Mallakar Fatima Idriss Bello



Arewabooks; Fadrees20
Wattpad; Fadrees_20
Phone No. 0902058802


Haƙƙin Mallaka nawa ne Ni Fatima Idriss Bello, ban yadda wani ko wata suyi amfani da wani sashe na littafi na ba, ko a haɗa min audio ba tare da kwakkwaran amincewa ta ba, idan naga akasin haka kuma wlh baza mu wanye lapiya ba dan haka a kiyaye.
Idan number na kake nema ɗaga idon ka sama zaka ganshi a rubuce



HAYATU P.O.V

Allah Sarki, ɗazu fa da safe shamsu yake ce masa yau duk jikinsa a sanyaye, sannan fitar da yace zeyi ya fasa dan wani iri yake ji, a lokacin dariya Hayatu yayi Allah Sarki dama je ko ina ba, dan fita yayi yaje barga ya dawo, sede dana sani na bayan ƙeya
Tuna lokacin da suka taso tare yake, lokacin da suke ƙanana, shi shamsu shine magananne shi kuma Hayatu shine shiru shiru, wallahi billahi be taɓa tsammanin mutuwa wai zata riski Shamsu a hakan su ba, duba da kalan burikan dake a gaban su, amma kash, hausawa suka ce mutuwa mai yankan kauna, tabbas yau ya yadda da hakan, Sede kuma wai umma ce tayi sanadiyar mutuwar nashi, sannan har tana iƙirarin wai ya daukar mata fansa, wallahi da ba umma bace tayi sanadiyar

Please Login or Register in order to submit comment