Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koma masarautar mu dole ku bani Hafsa domin ta kwanta min a rai".
Se a lokacin Yarima yasan sunan ta Hafsa, wani kallo ya mata ai bata san sanda tabar wurin ba ta koma sashen su.
Shi kuma Yarima se ya share shi, shidai Sulaiman abun mamaki ya bashi, babu yammata ne a Gobir da zai ce wai abashi Hafsa?
Musabaha suka sake yi da Sulaiman sannan suka wuce sashen Yariman daman can zasu je.
Yarima ranshi in yayi dubu to ya ɓaci. Gaskiya Isma'il ya rena sa, har yaga baiwar sa yace ta wani kwanta masa a rai? Jikin sa har rawa ya soma yi se daga baya ya dawo da hankalin sa, nan da nan yayi murmushi tuna irin matakin da ze dauka.

Yanzu kuwa da ya ganshi se ya kara hada ransa, ido ya mata akan ya sallame ta ita kuwa ta kama hanyar zuwa sashen su na bayi, a hanyar ta na komawa ta sake haduwa da wani.
Farko ma ce mata yayi wai tana matukar kama da wata wanda ya sani. Dariya tayi masa tace se dai kama, amma bawan Allah ya sha gaban ta wai shi be yadda aiki take a masarautar ba
"Haba dai kyakkyawar budurwa kamar ki ace tana aiki a matsayin baiwa? Gaskiya da sake" inji matashin me suna Ibrahim da fada.
Ita dai Hafsa share sa tayi, tayi tafiyar ta taje ta samu Murja tace yau an sallame ta da wuri.
Murja dai ta tsaya tana mamaki, tace "Gaskiya Hafsa ban yadda ba, kodai ya baki yancin ki ne, ya sallame ki baki sani ba, in ba haka ba, yaushe rabon da ki zo iwar haka"? Murja ta karashe zancen ta cikin tsananin mamaki domin gaskiya Yarima yana matukar horar da Hafsa, ko gasan nan da za'a yi, ita ya barma ragamar komai, sannan tsabar tsugudidi wai har se yayi bacci tukunna ya yarje mata taje tayi bacci.

Ita dai Hafsa kwanciyar ta tayi ta shaqi bacci, se chan da Murja ta dawo daga sashen me martaba take ce mata wai Yarima ya aiko yana neman ta, lokacin marece ne lis, tashi tayi tana zumbura baki ta dauki kallabin ta tayi waje, ita fa in ba Sallah zata yi ba bata daukan hijabin da aka basu, ji take yana takura ta, sannan ma yau yana daga cikin ranakun da bata Sallah.

Sashen Yarima ta nupa, babu sallama ta kutsa kai, nan taga dakin shakatawan nashi a cike da matasa, da abinci iri iri a zube a tsakiyar dakin, ga abubuwan sha, ga kayan marmari iri iri, kayan jikin matasan kadai ya isa ya nuna maka ko su wanene, daga ido tayi ta ganshi a kishingide akan tumtum ga su Suleiman da su Hayatu ata gefen
"Salamu Alaikum" ta tsinci kanta da yin sallama, se gaba daya hankalin su ya dawo kanta, se ta ɗan ji ta a takure saboda rashin saka hijabin da bata yi ba, nan take ta zube har kasa ta kwashi gaisuwa a gunsu, ƙalilan ne suka amsa se ismail da ya zuba mata na mujiya can se kuma ta yanke shawarar taje gurin sa, isar ta gun nasa seda ta ɗan duqa ta gaida shi ya amsa a yamutse.

Ganin har yanzu idon samarin nan na kanta ya sa Yarima yaji ransa ba dadi, se yaji kamar ya sa ta ta koma amma se ya basar
Alama ya mata da ta shiga uwar dakan shi ta gyara
Shigewa tayi kan Isma'il kamar ya lanqwashe tsabar kallo idon Yarima kuwa kyam akan shi. Nan ta tadda dakin a hargitse ga kaya dinkim akan gadon, ta ma rasa ta ina za ta fara, ga takalma nan birjik suma a zube, nan ta fara mita
"Gaskiya wannan Yariman akwai shi da kazanta, dubi dan Allah yadda yayi da dakin nan se kace wani karamin yaro fisabilillah gashi ba daman ka masa magana yanzu ya sa mugayen azzalumin fadawan san nan su duki mutum a banza, daman na lura sam zuciyar shi babu hasken imani, mummunan Yarima kawai....."

Juyowan da zata yi bata karasa ba ta hange shi yayi folding din hannun sa biyu yana kallon ta, ita sam bata san sanda ya shigo ba ai da tayi shiru, ƙafan ta ne ya ɗan fara kyarma amma se ta kafse, tana hura hanci.

"Maimaita abinda kika ce" ta tsinkayi muryar shi a setin fuskan ta, karasowa yayi daf da ita kamar wanda ze hade fuskan sa da nata, a matukar tsorace ta fara jan baya, kapın ta ankara taji ya janyo hannun ta ta fada jikinshi se karan abu suka ji Dummmm.


Ban yadda wani yayi amfani da wani sashe na littafin nan nawa ba, ba tare da amincewa na ba, domin zan dauki tsattsauran mataki akan hakan, dan haka a kiyaye.

Idan littafin nan kake nema, complete ko wani sashe toh ga nan numbern waya na a sama duk me san yayi min magana, ya min ta nan.

Da fatan an fahimta.
Nagode.





>>>>>>>>>>>>>💻🖋️🤍







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss🖋️🖋️
09020588802
Wattpad; fadrees_20


Page 13


Hakkin Mallaka nawa ne Ni Fatima Idriss Bello
Ban yadda a juyamin littafina ta ko wane irin tsiga ba, ko kuma ayı audio ba tare da izinina ba domin hakan ze iya janyo ma mutum matsala.
Dan haka a kiyaye.


A matuƙar razane Hafsa ta kalle shi, jin sautin abu ya fadi ya sa ta juyawa cike da mugun tsoro ta kalla menene ya fadin, wani Akwati ne yazo faɗawa a kanta shine ya janyo ta jikin shi dan kar abun ya sauka a kan ta.
Wani sassanyar ajiyar zuciya ta sauke tayi lamo a jikin shi kapin ta ankara da abinda tayi.
Nan take ta fara bashi hakuri tare da tsugunnawa, shiko gogan se kallon ta yake, shi tunda yake be taba kusanto mace kamar yadda ya faru yanzu ba, hasali ma shi ba me san sha'anin mata bane, sannan Bilkisu tasha rungume sa amma ba wai shigen haka ba, besides Bilkisu kanwar sa ta jini ce so baze sa ta a lissafi ba se kuma yayyen sa da suke aure a wata nahiyoyin

Daga idon ta tayi ta kalli fuskar sa, Namiji ne shi kyakkyawan gaske, yana da zubin mazajen da kowacce macen da takai mace zata so shi, kamannin sa ta hango da Fulani, yanayin idonsu da bakin su, sai hancin mai martaba da ya dakko, wanda shi kuma ya gaje shi ne daga mahaifiyar sa sarauniya babba.

Aƙalla sun kai minti Uku zuwa biyar suna kallon junan su. Ita Hafsa yaba kyawun sa take, lalle mummunan Yarima kyakkyawa ne, No wonder take jin matan bayi suna yaba kyawun sa, ita dai tana aiki ne a karkashin sa amma gaskiya bata taɓa kallan fuskan sa na rabin minti ba domin kanta a kasa take masa magana, sannan ko ta masa kallon minti dayan ma, ba kallon kyakkyawa take masa ba, kallon goggon biri take masa, shi kuma Yarima on the other hand kawai yana mamakin yanayin ta ne, ashe dai akwai side nata me tsoro, shi kallon fitsararriya yake mata wanda zata iya dambe da maza goma ma (be san zata iyan ba😂🤌), sannan yana mata kallon mara kunyan gaske dan shi tun da yake a rayuwarsa da bayin gidan su babu wanda ta taba yaɓa masa magana kamar Hafsa, babu wanda ta sha masa kuskure ya kyale ta kaman ita. Hafsa ne ta fara janye idon ta se shima ya janye nasa, "zaki iya gyara dakin, kapın nan, ki ware min kayan da zan saka gobe" ya karashe Yana ciccin magani, zama yayi akan wani kujeran katako dake dakin yana me lumshe zara zaran idanuwansa kamar me bacci, se da ta gama kimtsa dakin sa'annan ta ware wasu kaya kala biyu da suka mata masifar kyau

"Gasu nan Ranka ya dade" bude idon sa yayi ya kalla. Amawali da yar shara ce sai wando mai zina da alkyabba mai zaiba, daya kalar ruwan kasa daya kuma shuɗi. Ga rawaninnika daya ruwan kasa daya shudin, Masu shuɗin yafi tafiya da hankalin sa, nan ya sa ta ta kimtsa su a jikin mahangar kayansa, can dai da yaji alamun duk ya'yan sarakunan nan sun watse, se ya sallame ta tare da gargadin ta akan gobe tazo da sassafe.
Fitowa tayi tana mitan yawan aikin da yake sa ta, kiciɓus tayi da Isma'il, durqusawa ta ɗan yi ta gaida shi, shiko se sakin murmushi yake yana ta jan ta da magana se yaba kyawun Hajiya Hafsa yake, nan kuwa se ga Hafsa ana zuba dariya har da tsugunnawa kasa, daga kanta ke da wuya ta ganshi ya sha mur, fuskan shi kamar na mutuwa ai Hafsa bata san sanda ta ruga ba, ko wai waye bata yi se ganin ta tayi akan katifar ta tana maida numfashi lokacin dare yayi already.
Murja ta hango tana shaqar bacci, gefen katifar Murja ta kalla taga akwai kwanon silba ciki kuwa dambu ne kusan rabi, nan take taji yunwan cikin ta ya dawo, ai ba shiri ta fara jefa hannun ta tana mikawa baki, seda taga bayan kwanan kapın ta wanke hannun ta ta kora da ruwa se kuma da taji kiran Assalatu.

Yau Hafsa dambe suka kwasa a gurin wanka dan tace ita zata fara shiga kuma an riga ta, Murja se jan ta take tana fusgewa, kunsan halin mutumiyasss seda tayi kapın hankalin kowa ya kwanta, nan kuwa ta hankada murja ciki ta janyo kofan suka fara chachan baki da yammata sa'annin ta, ganin ba yadda suka iya da ita ne yasa suka kyale ta, gashi babu dogarin da yake dukan ta ballantana su kai karan ta, can sega Murja ta fito suka wuce dakin su suna dariya.
Bayan sun shirya suka karbo abincin su suka zauna suka ci kapın suka fice.

Tun daga sashen su suke jiyo kararrakin tambura, dasu kade kade da kuma bushe bushe.
Ta tabbata yau ne ranar gasa. Sashen Yarima ta wuce ta same dakin a rupe alamun be ma tashi a bacci ba, se a lokacin ta tuna bata mayi sallar asuba ba, nan ta miqe ta iyo sa domin tayi wankan sallah.
Ta ɗan kishingida akan kafet kenan bacci ya fara fusgar ta taji karan bude kofa, nan take ta miqe tsaya, ta gaida shi ya mata alama da ta shigo, abun se ya bata mamaki, domin bata shiga dakin sa a irin wannan lokacin domin kamar lokacin wankan sa ne, ilai kuwa da shigan ta ta gan shi a tsaye dakin ya kaure da kamshi, alama ya mata da ta saka masa kayan, murkuda masa baki tayi akan baza tayi ba, se kuma ta rupe bakin nata da hannun ta tana me zare idanu.
Kallon irin kallon da yake mata ne ya sata daukan kayan nasa cikin sauri ta fara sa masa. A garin saka kayan taje ta gogi fuskan shi da tafin hannun ta, nan ta fara bashi hakuri shiko ko a jikin sa, rawanin ne bata iya daura masa ba, se ga Sulaiman yayi sallama, durqusawa tayi ta gaida shi, tayi waje ta tsaya, can Sega su sun fito nan tabi bayan su, se sashen Mai Martaba, ashe an shirya karın kumallo da za'a yi da dukkanin sarakunan da ya'yan su, sannan an hana bayi shiga se wasu daga cikin manyan bayi, nan Hafsa dake binsu ta dawo daga baya tana dan juye juye, hannun ta aka damqa ta juya da niyan yin masifa taga Murja ce, nan suka samu wani wuri suka zauna suna ta ɗan tattaba hirarraki da gulmace gulmace.

Seda suka dan dauki lokaci kapın suka gama, aka tafi filin polon da za'a yi wasan, girman gurin fadar sa bata lokaci ne ma, tambura da kide kide ya cika ko ina har ma baka jin maganan na kusa da kai ga mutanen gari da waje anzo an cika gurin har ba'a cewa komai
Can aka fara gudanar da wasannin inda za'a fara da harba kwari da baka, yaran masarautu biyar ne suka fara
Nan aka fara yi masarautar Zaria yazo na daya, wasa na biyu kuma da takobi aka yi inda masarautar Kano ta cinye, anyi wasanni a ƙalla kusan goma masarautu daban daban na cinyewa, Seda aka zo wasan karshe, wanda shine idan mutum ya cinye masarautar su ce tayi nasara, wasan doki wato hawan doki.



>>>>>>>>>>>>>🖋️💻







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss🖋️🖋️
09020588802
Wattpad; fadrees_20


Page 16



TARİHİ
Sarki Alhaji Sulaimanu bn İdrissa, shine sarki na Ashirin da uku a garin Bauchi a wancan zamanin. Su goma sha daya mahaifin su Sarki İdrissa ya haife su amma a kap dinsu su biyu suka rage domin duk sauran yaran da ya haife su komawa suke. Sarki İdrissa Yayi bakin cikin rasa ya'yan sa da yake yi, mutane aka dinga cewa ko ya saba ma Allah ne, yasa yake jarraban sa da rashin yayansa.
A lokacin matansa uku da kwarkwarori biyu, amma dukkan su babu wanda bata haihu ɗan ya koma ba, imma mace imma namiji.

Auren sa da Aminatoú yar Sarkin Agadéz ne Allah ya basa dansa na farko da ya rayu wato Sulaiman wanda ake ta jita jitan cewa a kap garin Bauchi a zamanin sa ba'a taba haifan ɗa kyakkyawa kamar sa ba, kasancewar mahaifiyar sa kyakkyawar gaske ce ko a Niger din ma, kasancewar su buzaye da sirkin fulanin asali
Haifan Sulaiman da Aminatoú tayi ya jawo mata bakin jini haikam a gurin abokan zaman ta da ma wasu daga cikin manyan masarautar.
Domin kuwa yaro kwarjini da kyau da hankali gare shi. Ga haiba da cikar zati, duk shi kadai, shekarar sa biyu ta haifo Jafar wanda shima ba baya bane wajen kyau da kwarjinin.

Rayuwa ta ci gaba da tafiya inda shekaran Yarima Sulaiman ya cika Ashirin cif cif, a lokacin ne kuma emmata suke ta rububin samun sa, ciki kuwa harda yar Wazirin wancan lokacin me suna Sadiya.
Aminatoú wacce take amsa sunan Sarauniya Babba a yanzu ne ta sama ma Sulaiman Hauwaó karamar yar yayanta, wacce baza ta wuce shekaru goma sha uku ba, Sulaiman yayi na'am da wannan hadin take suka fahimci juna aka sa musu rana, soyayya suke a tsaftace, Sadiya kuwa hakan da akayi ya bakanta ranta domin har ta samu Jafar a boye ta gaya masa manufarta, toh sanin halin mugunta irin na Sadiya da rashin kamun kai yasa Jafar yaqi taimakon ta kamar yadda ta bukata, instead se yaje ya fada wa yayan nasa, har shi kuma ya mata rashin mutunci, daga karshe da magana takai kunnen me martaba, se yace ya baiwa Jafar auren ta, dan itama baza ta wuce sa'ar Hauwaón ba, koma ta baiwa Hauwaón shekara daya.
Da jin haka Jafar yace shi besan zance ba baze aure ta ba, akayi akayi yaqi yadda, lokacin shekaran yayansa daya da aure, da Sarki İdrissa yaga haka se ya fusata ya aura wa Sulaiman ita, ita kuma ta dauki tsanar duniya ta ɗorawa ahalin, shi kansa Sulaiman din bata kyale sa ba.

Yin auren ta da Sulaiman da wata daya akayi auren Jafar da Zulaiha yar galadiman wancan lokacin, bayan auren su da wata biyu ciwon ajali ya kama Mai Martaba Sarki İdrissa, sati be juyo ba seda yace ga garinku
Nan da nan aka naɗa Sulaiman, kwana biyu tsakani Hauwaó wacce ake kira da Fulani ta aihu ƴa mace aka saka mata sunan Sarauniya Babba, bayan shekara biyu aka haifi Yarima aka maida masa sunan Mai Martaba Sarki İdrissa, a lokacin watan Sadiya biyu da haifan tata ƴar me suna Asiya, sannan Jafar ma matar sa bayan wata biyar ta haifa masa yaro namiji, ya sawa yayan sa takwara.

Shekara biyu da haifan Yarima, Sadiya wacce take Kilishi a yanzu ta haifi yaranta ýan tagwaye, Shamsu da Hayatu, se bayan shakara biyar Fulani Hauwaó ta haifi Bilkisu, wanda yayi daidai da lokacin da matar Jafar ta haifi tata ýar me suna sameera.

Yara sun girma har sun kai munzalin Shekara ashirin da hudu zuwa da biyar, wato Yarima da Sulaiman kenan, domin Aminatoú an dade da mata aure tana masarautar Agadéz, se kuma Asiya da take birnin Sokoto da aure.
Wannan kenan.

_________________

Hafsa kam ko Sallah kasa tashi tayi, sai da Murja taxo ta dinga tallafa mata, abinci ma se an mata ɗure, ta sha wahala matuƙa, Seda ta kwana biyu tana jinya kapın ta samu sauki, a lokacin babu irin jita jitan da ba'a yaɗa ba akan ita da su Yarima, ɗadin abun ma ba'a iya yi a gaban ta, domin kuwa da za'a kwashi yan kallo ne, shima Yarima wannan na daya daga cikin dalilan da yasa be neme ta ba
Yau ta kama Laraba da wurwuri Hafsa ta shirya tayi hanyan sashen Yarima.
Sallama tayi, ta tura kofa ba kowa, nan ta kimtsa ko ina taje madafa ta kimtsa shi shima, alamu taga kamar babu kowa a cikin uwar dakan Yarima, nan ta yanke hukuncin ta shiga ta gyara masa, kutsa kai tayi wani Ni'imtaccen kamshi ya shiga kofofin hancin ta, nan ta shiga ta gyare ko ina tsafff, ta wanke makewayin sauran gyaran gado, gani tayi gadon ya birge ta, yau de kam se ta gwada kwanciya a kai taji yaya yake ji da yake wani huhhura wa mutane hanci, sannan daga gani katifar zata yi laushi, ga nan barguna nan masu matukar taushi da laushi a shimfide.
Wohoho yau zata dandana kapın ya dawo itama.

Sashen dardumar sa ta hango nan cikin ta ya bada kulululu, nan kuwa taje ta fara bude ko wane kwano daya bayan daya, still nan ma taga duk abinda ta bude sunfi karfin ta, kwanon karshe ne taga soyayyen dafaffen dankali da kwai, ga wata jar miyar da bata taba ganin irin sa ba, duk da an fara ci ba wani dayawa aka ci ba, nan ta afka hannu ta fara gabza, hannu bisa hannu ƙwarya. Seda ta cinye tass kapın ta samu salama nan ta kora da wani ruwa me daddaɗan zaƙi se kamshi yake, wanda ko ƙaffara baza tayi ba da inibi aka yi shi, nan take tayi kan gadon ta kwanta ba sai barawon yazo ya sace ta ba? Su Hajiya Hafsatu hadda minshari an wangale baki, ƙafafuwa na kallon kudu da arewa, zani kuwa yana kallon gabas, dankwali kuwa daman tun a gurin dardumar abinci aka ya da shi.
Wannan kenan.

______________________

Yarima na hango ya fito daga sashen Sarauniya Babba, daga yanayin fuskar sa zaka gane ba maganar arziki suka yi da ita ba
Jikin sa har rawa yake tsabar ɓacin rai, sashen sa ya wuce, yana tafe yana saƙe saƙen abinda Hajiya Babba tace, da ya karaso kai tsaye ya shige dakin sa, yana zuwa bakin gado yaci karo da malama hansai ana sharbar bacci, harda ɗan jan dogon tsakin ta, tana zagin Jamila wai ta rena ta. Se sumbatu take tana faɗin
"Wallahi Mama Jamilan nan na lura tana da raini sosai, toh wlh zan koya mata hankali, har Ni zan aike ta taƙi zuwa, da badan ina da hakuri da hankali da hangen nesa tare da kai zuciya nesa ba, ai da kakkarya ta xanyi" shine fa ta karashe zancen tare da jan dogon tsaki.

Kawai kasa motsi shikam yayi, ya ma rasa me yake masa dadi, kawai ya tsaya yana kallon ikon Allah, lalle yarinyar nan ba kyal bace, yanzu fisabilillah wai itace take da hakuri da kai zuciya nesa? Shi da badan hakurin sa ba ai da ya kakkarya ta tun tuni, yanzu akwai ma rainin da ya wuce har ta tsallake dakin shakatawar shi ta shigo har cikin uwar dakan shi ta hau kan gadon shi ta kwanta tayi bacci? Tsabar asara hadda minshari? Ehhh lalle kam dole tace an rena ta, tsaya wa ma yayi yana tunanin wane irin hukunci ze mata tukunna, beyi aune ba ya ɗan gauce kadan, be zame ko ina ba se bisa kan Hafsa da take bacci salamun ƙaulan.

Ban yadda wani yayi amfani da wani sashe na littafin nan nawa ba, ba tare da amincewa na ba, domin zan dauki tsattsauran mataki akan hakan, dan haka a kiyaye.

Idan littafin nan kake nema, complete ko wani sashe toh ga nan numbern waya na a sama duk me san yayi min magana, ya min ta nan.

Da fatan an fahimta.
Nagode.



>>>>>>>>>>>>>🖋️💻







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss🖋️🖋️
09020588802
Wattpad; fadrees_20


Page 17

Hakkin Mallaka nawa ne Ni Fatima Idriss Bello
Ban yadda a juyamin littafina ta ko wane irin tsiga ba, ko kuma ayı audio ba tare da izinina ba domin hakan ze iya janyo ma mutum matsala.
Dan haka a kiyaye.



Zo kaji wani irin ashariya da Hafsa ta danno, domin ita idan abu ya firgita ta, badai tayi salati ba kam, sede tayi ashar saboda tafi karfi a harkan fada. Tukunna ma tsaya, wannan din wane kalan abu ne me nauyi haka da ze fado kanta, sumbatu ta fara yi  "Wayyo mama kiga Jamila ta fado Miki kyauren dakin ki kuma tsabar rashin kunya a kaina? Gaskiya wannan kyauren mugun nauyi gare shi kamar buhu wlh yau Jamila me raba Ni dake sai Lillahi dan Ubanki zanci yau" ta karashe tana kokarin ware idon ta da kyau.
'Gamo tayi, tabbas kuwa gamon tayi, mugun gamo ma kuwa'
Wayyo Allahnta, yau dai kam tasan Yarima Idriss karya ta zeyi ko yasa wannan mugun azzalumin bawan nasa ya karya ta
Yau kam kasa bada hakuri Hafsa tayi domin harcen ta ya sarƙe, wlh ita kanta tasan tayi ba daidai ba, toh me ma ya kaita. ita kam yanzu meye mafita? Nan da nan wani tinani ya ɗarsu a ranta, kawai za tayi haukan karya, ehh kawai cewa zata yi aljanu gare ta. Daman ance tabarmar kunya da hauka akan naɗe ta.

Se yanzu ma ta lura da kyau ai shi kam gaba-daya ma akan ta yake, ita ba wannan bane ba ma matsalar ta, maganganun da tayi ne matsalan ta wanda ko rantsuwa baza tayi ba akan kunnen sa tayi shi, gashi fuskan su yazo kusa sosai da sosai kamar wanda yake shirin haɗe bakinsu wuri ɗaya, kallon juna suka tsaya yi na kusan minti biyar, Hafsa ce ta fara janye idon ta kapin shi, bai san me yake shigen shi ba a yanzu amma ji yake kamar ya rungume ta, se yaga ta mishi kyau, ji yayi baze iya rabuwa da ita ba kamar yadda Sarauniya Babba ta shawarce shi, "Kai ina, sam hakan ma ba me yiwuwa bane" idan ya rabu da ita waye zai dinga yi masa aiki kamar yadda take masa, sannan wa zai sa shi nishadi kamar yadda take sa shi, duk da wannan wani sirri ne daga zuciyarsa da shi kadai ya baiwa kansa sani sai a sa'annan ya gane irin taɓargazar da yayi, na jimawan da yayi a kanta, yanzu ai sai ta rena shi, daman ya lura yarinyar sam bata da kunya ga raini ga shegen rawan kai, a gurin neman fada kam zai iya cewa ita din babbar gwana ce.
Kapın ya Ankara yaji ihun Hafsa, se sumbatu take tana zare idanu tare da kikkifta su kamar wanda ta fara ciwon hauka, kan ya ankara yaji "Dummmm" daidai da faduwar ta daga kan gado kenan. Tsayawa yayi yana ganin ikon Allah
Sai ji yayi tana faɗin "ba zamu fita ba, ka dena kallon godiyar mu" can kuma yaji tace
"Ka tashi kayi waje, kar ka sake dawowa se dare ya tsala"
Nan da nan ya danji wani tsoro, shi dai tsoro yake kar yarinyar nan ta haukace masa ya shiga uku.
Fita yayi dakin shakatawar sa, can zuwa wasu en awanni lokacin har duhu ya fara tsalawa ya dawo ya hango hajjaju se maida numfashi ake, nan yayi tunanin ya tallafa mata ko dakin shakatawar shi ya kaita kar ma Sulaiman ko wani yazo yayi wani tunanin na daban.

Tsugunnawa yayi kamar baze iya ba, dan a ganin shi ba girman shi bane ba, can yayi tunanin yaje waje ko wata baiwa ya gani ya kira ta ta raka ta dakin su se yaga kamar in yayi hakan girman sa ya zube, can dai da yaga ba sarki sai Allah nan da nan ya ciccibe ta, shigar shi cikin dakin shakatawar tashi kenan ɗauke da ita a hannun sa yaci karo da Kilishi zaune akan wani katon tumtum tana taunar tuffa, fuskar ta dauke da wani mummunan murmushi, nan take jikin shi ya saki, Hafsan da tayi likimo a jikin shi ta ware idon ta ganin abinda

Please Login or Register in order to submit comment