Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka"?
Harara ya banka mata har seda kafar ta ya kama rawa, can kamar baze yi magana ba taji yace
"Kina so kisan amfanin kyallen"
Gyada masa kai tayi da wurwuri tare da kura masa ido
Sai yace "to ki jirani zuwa dare zan fada Miki", gama fadar sa kuwa nan da nan ya fice a sashen nasa ita kuma sai mamaki ya kama ta, meyesa bazai fada mata yanzu ba sai dare yayi? Toh ya fada da kar ya fadan duk uwarsu daya ubansu daya, amma ma, sai ya fada din, yana fita kuwa aka kawo abinci, itakam zaman ta tayi ta dibi abinci da ta gama ci tayi shigewan ta dakin da akace nata ne, tayi kwanciyar ta, da taso taje ta gyara dakin Yariman, sai bayin da suka kawo abincin suka dinga roqon ta akan ta bari suyi aikinsu kar ta jawo musu matsala, da ta kwanta akan gadon ta ta fara sake sake, kodai ta sa su kira mata murja ne, nan da nan ta canza shawara, tana kwanciya can ba'a jima ba bacci yayi awon gaba da ita, cike da tunanin su Mama da Jamila

___________

A can gida kuwa, yau Mama da Baba da Jamila da su Ibrahim suka kama hanyar zuwa masarautar Borno dan sammako suka yi ma, dan tun asubahi suka kama hanya. Ba su suka isa ba sai da mangariba, gidan Galadiman Borno suka wuce direct, an musu tarba na musamman, a dakin shakatawar baki,  sai bayan isha da suka natsa sa'annan mai girma galadima ya samu isowa, da ya shigo ya samu guri ya zauna nan suka kwashi gaisuwa, tsaya wa yayi yana kallon Mama Zainabu, meyesa take masa irin wannan gaisuwan? Meyesa take tare da wadannan mutanen a zaune ma a kusa da wani namijin sannan meyasa take sanye da kaya marasa daraja?, sannan ba tace masa yau ita baza ta samu fitowa ba, ba girkin ta bane sannan bata jin dadi? Ko ma abun gaggawa ne ya kama ai dai ba ta saka wannan kayan ba, sannan shi dai a cikin kayayyakin ta in bai manta ba babu mara daraja haka ma,
Kar ku manta ita fa Mama Zainabun wai a haka ta zabo kaya mafi kyau daga cikin kayayyakin ta ne, su Ibrahim ne suka shigo, nan suka kwashi gaisuwa, Abubakar ne yayi magana "Baba nasan mai kake tunani, amma kadan jirani kadan ina zuwa, hakan da ka gani yana da alaqa da tafiyar da na ce maka zanyi zuwa ƙasar Bauchi, amma ban fada maka dalili ba" ficewa yayi can sai gashi sunyi sallama sun shigo da Mama Maryamu, malam sule mai rini ne ya miqe cike da kaɗuwa, bayan shi Jamila da Mama Zainabu ne suma cikin tsigar tsoro.
Ita kanta Mama Maryam din seda taja da baya, galadima ne kaɗai bai kadu ba a gun amma Seda ya kasa motsi tsabar mamaki, se su Ibrahim da suka riga da suka san komai.
Kasa motsawa Mama Maryamu tayi, Seda Abubakar yaja hannun ta ya karasa da ita, Suwaiba yar Mama Maryamu wacce ke biye da ita ne ta kwalla kara tare da yin baya zata afka a guje tsabar tsoro Ibrahim da yake gun kofa ya damko hannun ta, kowa da yake wajen ya kadu iya kaɗuwa, Mama Maryamu ne ta karasa wurin Mama Zainabu ta zuba mata ido, kallon kallo suke ko kyaftawa basa yi, kare musu kallo nayi, kamar su ɗaya sakk, babu abinda ya raba su sai kayan jikin su, kamar su tayi mugun baci, rungume juna suka yi, musamman Mama Maryamu da take cewa ina kika shiga Maimunatu? Babu inda ba'a duba ba, ba gun neman ki da ba'a bi ba, ba'a samu ba, Har buga ƙasa akayi akace kina raye, Baba ya mutu da kewar ki, ya mutu da baƙin cikin rashin ki, ina kika shiga Maimunatu? Se kuka Mama Maryamu take tana me yiwa Mama Zainabu mugun runguma, ita dai ido ne nata dan wani banbaraƙwai take jin abun domin bata san maganan me wannan matar me kama da ita take yi ba, sede jikin ta yayi sanyi, mugun sanyi ma kuwa, sannan ita gaskiya bata jin komai a game da matan, ita a ganin ta kama ce kawai suke yi daga Allah, duk da cewar baza ta iya tuna Asalin ta ba, ai be kamata tayi concluding kan cewar wannan yar uwar ta bace, yanzu misali idan ta amince yar uwar ta ce akayi bincike aka gane akasin hakan fa?
Se tayi yaya kenan? Amma kuma tsaya, taji wannan matar da aka kira da mama Maryamu ta kira ta da wani suna, sunan wanene kenan?
'Maimunatu'?.
A ina ta taba jin sunan nan, nan da taji hajijiya na shirin kama ta, tabar tunanin.


FADREES 🖋️ 🖋️ Ƴar Mutan Yobe





>>>>>>>>>>>>>🖋️💻







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss Bello🖋️🖋️
Wattpad; fadrees_20


Page 32



Hakkin Mallaka nawa ne Ni Fatima Idriss Bello
Ban yadda a juyamin littafina ta ko wane irin tsiga ba, ko kuma ayı audio ba tare da izinina ba domin hakan ze iya janyo ma mutum matsala.
Dan haka a kiyaye.



Galadima ne ya tsawatar tukunna aka tsagaita da yin kukan da ake
Bayan da kowa yayi shiru sai Mai Girma Galadima yace da Mama Zenabu da ta bada tarihin rayuwar tun daga farko har yanzu da suke zaune a nan gurin, Labarin ta ta bashi daga lokacin da ta bude ido ta tsinci kanta a matsayin baiwa a cikin Masarautar Bauchi, da duk sanda tace zata zurfafa tunanin wai ita waye ce sai tayi ciwon kai har zuwa inda ta hadu da Malam Sule da yanda ya aure ta har zuwa shekaran jiya da yar ta ta auri Yariman Bauchin da kuma zuwan su Ibrahim gidan su da fadar bukatun su, bayan ta gama Galadima yace da Malam Sule me Rini da ya fada me ya sani shi kuma, shima ya maimaita sak abinda Mama Zenabu tace, bayan haka ya tambayi su Abubakar da Ibrahim, Ibrahim ya fada part nasa na ganin kamar da Hafsa da Suwaiba suke ne yasa ranan cikin sa'a yazo gun Abubakar ya kalli Suwaiba ya kara kallon ta da kyau ya ga tsantsar kamar da take da Hafsa, cikin ikon Allah yaga Mama Maryamu itama yaga tana Kama da hafsan sosai da sosai shine ya same sa da kudurin sa, shima kuma Abubakar jin niyyar Ibrahim bayan yazo ya same sa ne yace ze bishi ya nemo ma Mama Maryamu en uwan ta, kasancewar ba ita ta haife shi ba, bata taɓa zaluntar sa ba, hasali ma ta riqe shi kamar dan da ta haifa a cikin ta wannan dalilin ne yasa ya dauki haramar bin nashi domin ya faranta mata rai domin kullum cikin kunci yake ganin ta, shine abokin su dan gidan hakimi yace ze bisu, bayan Galadima ya gama jin jawabin su, nan ya umurci Mama Maryamu da ta baiwa yar uwar ta da mijin ta labarin rayuwar su a matsayin su na tagwaye kuma ya'yan Wazirin Borno na wancan zamanin.
Baba ne da Jamila suka zare ido cike da kaɗuwa domin ji suke kamar kunnen su beji daidai ba, ita kuma Mama Zenabu baka iya gane reaction din ta.
Mama Maryamu ne ta fara magana kamar haka;

_________________

Yarima bashi ya dawo ba se da dare ya tsala, ko ta kan Hafsa baibi ba, ya wuce dakin sa, shigar sa keda wuya ya sake cin karo da wani sabon farin kyallen da aka sake shimfidawa akan ido, wannan har daukan ido yake dan har kyalkyali yake, shi abun har ya so ya bashi dariya dan seda ya murmusa ma, lalle kam gaskiya kilishi tana da naci, ko ina ruwan ta da sha'anin sa, ko danma ba tun yau ya lura da tana neman hanyan kunyata shi bane, ya riga ya san ƙiyayyar ta a gare shi amma shi sam ya rasa me ya mata haka ta tsane shi? Ko dan bata so yayi Sarauta ne? Se yaga kamar ba haka bane, ya dade da fahimtar ta tsani Baba Waziri ma amma kuma shi gaskiya baze ce ga abinda suka mata ba, can dai da yaga tunanin ba zai amfane shi da komai ba yasa ya tattara hankalin sa yayi abinda yake gaban sa, ko da gama abubuwan sa, sai ya haye kan gadon sa yayi shiru yana sake saken maganan da suka yi shida Suleiman yau, game da kisan da ake ma matan da zai aura dan yasan wannan ba natural death bane, yanzu dai sun yanke hukuncin zasu sanya wa kowa dake cikin masarautar idanu dan kowa ba abun yadda bane, kuma Hafsan ma yasan ba kyale ta za'a yi ba dan duk wanda yake kashe masa matan duk inda hankalin sa yake toh ba a kwance bane domin auren hafsan da yayi zai hana shi sukuni.

Kashe fitilar dakin yayi ya rufe idanun sa amma bacci ya kasa daukan shi, tunanin Hafsa yake, ko me tayi yau da baya nan, Allah ya sa bata jawo masa fitina ba, abinda ya faru da safe ya tuna, se yaji duk ya muzanta, lalle baiwar sa ta tabbata zata raina shi, can ya bude idon sa ya sake rufewa, ji yayi baze iya bacci ba, ba tare da ya leqa yaga halin da Hafsa take ciki ba, tashi yayi ya kunna fitilar dakin tare da dauka a hannun sa yayi hanyar kofa, yana fita ya hango kofar dakin ta a bude, leqawa yayi ya hango ta tana ta sharar bacci abin ta, yau kam zanin ta ba cinya ya taho ba yana can gefe a jefe tsabar birgima, ƙarasawa cikin dakin yayi, ya gyara mata kwanciya tare da kashe fitilar dakin yayi waje.
Dakin sa ya koma ya kashe fitilar sa, nan da nan bacci yayi awon gaba dashi

>>

Safiya nayi yayi sammako zuwa sashen Mai Martaba dan jiya yaji zancen baiji dadi ba, da zuwan sa ya nemi iso, bayan ya fadi yayi gaisuwa, ya ma Mai Martaba ya jiki, ganin jikin nashi da sauki yasa ya miqe da niyyan tafiya, nan Mai Martaba yace dashi yana so yaje kasar Gombe shida Sulaiman sukai wani sakon gudunmawa, yanzu haka ma an shirya musu abin hawa gudummawar ma yana cikin abun hawan, nan kuwa yayi godiya ze miqe ya tafi me Martaba yace dashi ya zauna yayi karin kumallo, zama yayi yana ci suna ɗan taɓa hira, me martaba na tambayar amarya, yaƙe ya dinga yi har ya ida ci, yana gamawa ya fito da niyan yaje ya nemi Sulaiman ya hadu dashi a kofa shima yazo gaida Mai Martaban kapın su tafi, bayan da Sulaiman ya fito suka shige cikin abun hawan, nan suka dauki hanya, dan daga nan zuwa kasar Gombe tafiya ce da bata wuce awa hudu zuwa biyar ba harma zasu je su dawo a yau, shi tunanin sa ma, be wuce na samun ganin hafsan da beyi ba sunyi koda sallama ne amma inshallah da ya dawo ze je gun ta.
Suna kan hanya suka cigaba da tattaunawar abinda ke faruwa a cikin Masarautar.
_________________
Kilishi ce zaune wasu bayi su biyu durqushe a gaban ta se karkarwa suke, da alamu dai barazana ta gama musu, wani leda ta dakko ta ba ma dayar baiwar tace, "ki tabbata taci a cikin abincin ta, idan kuma kika kuskure a bakin ran iyayen ki, haka zalika in wannan sirri ta fita", ganin haka yasa baiwar sake karkarwa, karban maganin tayi hannun ta yana jijjiga, fitar su keda wuya kilishi ta saki wani mugun murmushi tare da fadin,
"Yanzu wasan ya fara".
Kallon amintacciyar baiwar ta tayi tare da mata alaman da ta kira sauran su dawo bakin aikin su.
_________________

Hafsa ne naga ta fito dakin shakatawar Yarima, da ganin ta kasan tayi wanka ta shirya, yi tayi kamar taje ta dubo Yarima taga ko ya tashi, sai ta fasa, can dai tana zaune ta miqe kafa akan tumtum tana tunanin gida taga wasu bayi su uku sun shigo dauke da kwandunan abinci, a gaban ta suka dire, zuba mata dayar tayi har zata fara ci tace bari taje taga ko Yarima lafiya dai? Sallamar bayin tayi tace su bata wuri nan suka fice da dan tsoron su, Hafsa ganin yadda suka yi Seda ta dara, wai Allah, wai yau ita ake girmamawa dan ta auri dan sarki, ai kuwa zasu sha aiki in dai ita ne, A take ta miqe tayi hanyan dakin sa, knocking tayi taji shiru, nan da nan ta kutsa kanta ciki, ganin wayam tayi ba Yarima ba alamun sa, dube dube ta soma yi har makewayi bata ganshi ba, farin kyallen ta zubawa idanu tace a ranta, "hadda cemin ze gaya min meye amfanin abin nan ashe karya yake". Fitowa tayi, taje hanyar fita a sashen taga dogarawa, nan ta tambaye wani ya tabbatar mata da ya fita, nan ta koma dakin shakatawar tana me yatsina fuska, abincin ta ta hango a ajje a inda ta barsa, da kamar zata wuce dakin taki ci, in yaso idan yazo suyi drama sai ta fasa, ta wuce gun abincin ta zauna ta fara ci, shinkafa ce da miyar naman dawisu, gefe guda kuwa wani ruwan kayan itatuwa ne me bala'in zaƙi, ci take tana santi, tana gamawa ta ɗan kishingida
Can zuwa kamar awa hudu taji zuciyarta yana tashi, nan ta fada makewayin cikin dakin shakatawar ta fara kwara amai, takai minti goma tana abu daya, a galabaice ta fito bayan ta kuskure bakin ta, saka kafar ta a dakin shakatawar kenan taga yan gidan sarautar dukkan su a cikin falon fuskar su dauke da mamaki, fitowa jakadiyar jiya tayi daga dakin Yarima hannun ta dauke da farin Kyallen da aka cukurkuda shi, Muryar Kilishi Hafsa taji tana magana cikin tsare gida.
"Larai ki duba ta muga me ya saka ta amai"
Wacca aka kira da larai ce ta miqe taje ta riqe hannun Hafsa tana dubawa, tare da kurawa idon Hafsa nata idon
Jin Muryar Larai akayi tace
"Ranki ya dade yarinyar nan tana dauke da juna biyu har na tsawon mako shidda".
Hafsa cike da mamakin farucin larai ta daga hannu zata kwadawa larai mari dukda laran zata yi sa'ar Mama Kulu.
"Dakata"
Kilishi ce ta daka mata tsawa.
Jin muryar Kilishi tayi tace
"Ashe watsatsiyar yarinya aka auro domin wannan farin kyallen ya nuna mana yarinyar nan bata kawo budurcin ta gidan nan ba, sannan gashi har da guzurin cikin shege".
Karkarwa kafar Hafsa ta fara yi, baya ma da taga irin kallon mamakin dasu Fulani suke mata, nan da nan ta zube a ƙasa sumammiya.

Fadrees ce.




>>>>>>>>>>>>>🖋️💻







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss Bello🖋️🖋️
Wattpad; fadrees_20


Page 33



Hakkin Mallaka nawa ne Ni Fatima Idriss Bello
Ban yadda a juyamin littafina ta ko wane irin tsiga ba, ko kuma ayı audio ba tare da izinina ba domin hakan ze iya janyo ma mutum matsala.
Dan haka a kiyaye.



Kamar yadda kuka ji an ambata Wazirin da ya rasu kapın wannan da yake ci a yanzu shine mahaifin mu nida yar uwar tagwaici na Maimunatu.
Mu uku Allah ya basa a duniyar nan da kanin mu, Mahaifin mu dan asalin nan Kanem Borno ne, kuma history ya nuna da can kakan kakanninmu daya yayi sarautar Borno ma, a haka dai kasan sha'anin sarauta tana iya fita daga gidan ku, Mahaifiyar mu kuma yar kasar Sudan ce, ita marainiya ce gaba da baya domin daga gidan marayu ma ya dakko ta lokacin yaje karatun hikaya gata, kyakkyawar bala'i ce dan yaran sarakunan su na kasar Sudan sunyi ta kawo harin su akan ta basu samu ba sai shine yayi sa'ar samun ta, saboda shima dan sarauta ne, sarautar ma na Kanem Borno, In maganar sulalla ake toh ba'a barin su a baya, da ya taho da ita nan Najeriya, itace matar shi ta uku, sanda ya auro ta anyi ikirarin cewar kap kasar Borno babu wanda ya kai ta kyau hadda kuwa shuwa Arab din da suke a nan kasar tamu ta Borno, saboda haka kishiyoyin ta suka hana ta sakat, sunsha ɗana mata tarko Allah be basu dama ba, sanda suka gane tana da ciki kusan hauka suka yi gashi su har lokacin basu taba ko da batan wata bane dakyar dai suka barta tasha, dan a haihuwar mu ta kusan rasa ranta, da ta haife mu muma kyawawan gaske ne dan tun muna kananu ya'yan Sarkin Borno na wancan lokacin suka nuna suna son mu, inda Ni na auri daya gashi nan shine Galadiman yanzu, dayan kuma wanda Yakamata ki auran shine Sarkin Borno na yanzun (nasan da Hafsa tana nan cewa zata yi Allah ya isan ta Malam Sule ya jawo musu talauci😂).
Tunda Anna ta haife mu tayi bankwana da zaman lafiya, basu kyale ta ba har se ranar da tabar duniya, lokacin da ta haife kanin mu kenan, shima kwana shida yayi ya bita domin babu dumin uwa a tare da shi sannan mu lokacin shekaran mu goma baza mu iya kula dashi ba, gashi bayin da suke kula dashi azzalumai ne, Baba yayi bakin cikin rashin Anna domin Seda yayi jinyan da sede a kwantar a tayar da haka dai ya dangana. Baba yana matuƙar nuna mana kauna domin in ya ganmu mahaifiyar mu yake tunowa shiyasa baya barin muyi nesa dashi, sannan ko sauro ne ya kwarxane mu se an hukunta shi, wannan dalilin yasa matan baban mu suka yi niyyar raba mu ko ta halin ƙaƙa.
Watarana da bazan taba mantawa ba a rayuwa ta shine ranar da muka cika shekara sha takwas a duniya mun dawo daga gidan kakannin mu babar mu Uwargidan me suna Falmata, ta bamu wani naman tsuntsu ta samu dole se munci wai idan bamu ciba seta kashemu, Maimunatu ce ta wafce nawa ta jefa a baki tare da nata ta cinye kasancewar tasan Ni bana cin naman tsuntsu ganin Haka kusan hauka Mama Falmata tayi dan seda ta mata dukan tsiya.
Da safe kuwa da muka tashi aka nemi Maimunatu sama da kasa aka rasa, wannan yasa mahaifinmu ya yanki jiki ya fadi, yana a kwance yayi ta tara malamai suna addu'a wasu suna bugar ƙasa duk dan a samu inda kike amma ba labari, daya ne daga cikin malamin yace kina raye baki mutu ba, bayan shekara biyu mahaifin mu yace ga garinku, Baba Falmata kamar jira take ya mutu ta taso Ni a gaba wai sai na auri wani bawa, Allah maji ƙan bayin sa Sarki yace in koma gidan sa da zama, wata na biyu aka mana aure da Galadima.
Da haka naci gaba da neman ki amma ban samu ba, se na dangana na barwa Lillahi komai, se kuma yau da nake kallon ki dan ji nake kamar mafarki ma nake"
Ta karashe da hawaye, Mama Zenabu ma se kuka take kaman ranta ze fita, seda Galadima ya tsawatar suka sarara.
Nan da nan ya salllami kowa yace suje su huta da safe sa karashe maganar
Nan aka bar Malam Sule a nan sashen su kuma su Jamila suka bi Mama Maryamu da ta riqe Mama kamar zata mayar da ita ciki


Mama Maryamu da Mama Zenabu da suka zo wucewa masu hidima suka dinga kallon su cike da mamaki, domin wannan kamar da suke da junan su ba kowane en tagwaye bane suke samun wannan baiwar kaman.
_________________

Kilishi bata kyale ta a iya haka ba, seda tayi umarni da a kawo mata ruwa me bala'in sanyi, nan da nan kuwa muguwar baiwarta ta miko mata, tana amsa ta sheka ma Hafsa a jiki a razane Hafsa ta miqe tana kallon su daya bayan daya, cike da tsana da rashin mutunci, wani dogari ne ya shigo Kilishi ta nuna masa Hafsa tare da fadin
"Kaje ka kulle ta a dakin duhu, sannan ku bata azaba me radadi, Fulani ce ta juya ta fice idanun ta a cike da hawaye, Samira na biye da ita.
Wannan wane kalan ƙaddara ce fisabilillah, bayan mutuwan da matan sa suke yanzu kuma ya aure mara kamun kai?, da farko ta so taqi zuwa gayyatan da Kilishi ta mata amma jin cewar na gaggawa ne kuma a sashen Yarima ne ya sata ficewa taje, duk da cewar yanzu aka zo aka sanar da ita kan cewar Yariman yayi bulaguro zuwa ƙasar Gombe shida Sulaiman, daman tun a hanya da zata je taji ana cewa wai matar da Yarima ya aura bata kawo budurcin ta ba, shigar ta sashen nasa kuma suka jiyo ta tana ta kwara amai, har wata baiwa a gun cewa tayi wai jiya ma wuni tayi tana abu daya, daga amai sai bacci kamar kasa, wanda yake cikin alamomin masu ciki. Sashen ta ta wuce tana me takaicin wannan aure da danta yayi, ko da ba'a saki idan ya dawo sai ta sa shi ya sake ta, dan tabbas taga alamun rashin kunya a idon yarinyar dazu.

Hafsa kuwa ganin dogarin na neman taba ta tace "Wallahi ka kuskura ka taba jikina sai Naci bantan Ubanka, sannan ke kuma uban wa yace miki ina da ciki, sannan uban wa yace Miki Ni fasika ce, wlh yau se nayi Miki abinda har ki mutu baza ki manta dani ba, baki san wacece Hafsa ba" ta karashe cike da dimbin rashin kunya idon ta a cikin na Kilishin, ita wallahi har ta dena tsoron ta ma, lokacin da take baiwa ance musu su tsorace ta amma wlh ta dena tsoron ta daga yanzu.

Kilishi ne ranta yayi mugun ɓaci domin baiwa bata taɓa sa'insa da ita ba sai yau, yau dinma a gaban yan uwanta bayi kaskantattu, wlh yau in har anga tabar Hafsa da rai toh ba ita bace.

Alama tama dogarai biyun da suke tsaye a bayanta da su kama ta
"Kuje kuyi ta dukan ta har se kun tabbatar ta fada muku a ina ta watsad da mutuncin ta sannan ku tabbatar da wannan shegen dake ƙunshe a maran ta ya margaya"
Kamar kiftawa da bismillah suka kama Hafsa suka tisa keyar ta har dakin duhu, suna ajje ta suka fara jibgan ta baji ba gani, basu kyale ta ba seda suka tabbatar da ta suma.

Kilishi kuwa sashen ta ta wuce tana me kunan ran iskancin da Hafsa ta mata a gaban bayin ta, dadi taji da taji labarin Yarima baya gari, tasan ko babu komai yau ɗaya ta jefar da Fulani a kasa, dan taga kalan disappointment din da yake kunshe a fuskan ta, sallama baiwar ta tayi tare da larai a bayan ta.
Duqawa suka yi suka kwashi gaisuwa kana baiwar ta fita.
"Aikin ki yayi kyau Larai, sannan ina so ki sani kome ta banjama dake anan gaba kiyi kuka da kanki domin kinsan baki isa ki sani a cikin shirgin ki ba koh"?
Kilishi ta karashe tana me mummunan murmushi, da yake itama Laran makira ce sai cewa tayi "babu ma abinda zai faru ranki ya dade, nasara tana tare damu"
Murmushin gefen baki Kilishi tayi tana me daukar tsabar karafuna masu matukar daukar ido tare da nuna mata ta dauka
Ai Larai bata san sanda ta saki murmushin jin dadi ba ta kwashe karafunan tayi waje tana me matukar farin cikin yau take sallan ta.

Kilishi ce ta aika aka kira mata en tagwayen ta suka yi ta hira abunsu, daga karshe har Shamsu yake cewar ta taimaka a saka baki a ciro matar Yariman kar ya dawo yaji ba dadi amma tayi biris dashi
________

Samira kuwa sashen Sulaiman taje ta bama Bilkisu labarin abinda ya faru suka hadu suka dinga kwashe mata albarka.


Cannnn zuwa mangariba magana yaje kunnen sarauniya babba, a take hankalin ta ya tashi tace a hada mata meeting din gaggawa bayan Isha kowa yaje.


Fadrees.




>>>>>>>>>>>>>🖋️💻







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss Bello🖋️🖋️
Wattpad; fadrees_20


Page 34



Hakkin Mallaka nawa ne Ni Fatima Idriss Bello
Ban yadda a juyamin littafina ta ko wane irin tsiga ba, ko kuma ayı audio ba tare da izinina ba domin hakan ze iya janyo ma mutum matsala.
Dan haka a kiyaye.


Bayan Sallan Isha kowa ya hallara a sashen Sarauniya Babba, in ka cire Bilkisu da take amarya kuma take jinyan jikinta, har Mama Zulaiha Seda taje gun, bayan gaishe gaishe Sarauniya babba zata fara jawabin dalilin tara sun da ta sa akayi suka ji wani bafade yana sanarwar isowan Mai Martaba tare dayi

Please Login or Register in order to submit comment