Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

me san yayi min magana, ya min ta nan.

Da fatan an fahimta.
Nagode.



>>>>>>>>>>>>>💻🖋️🤍







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss🖋️🖋️
09020588802
Wattpad; fadrees_20


Page 9



Not edited.

Dariyar mugunta me kama da abun tsoro Boka Kafoor ya saki
Halittar seda ta tsorata duk da kasancewar duk sanda ta ziyarce shi se ta iske hakan amma ta kasa sabawa da hakan
Sujjada ta masa na kusan minti biyu kapin tai kokarin dago da kanta ta dube shi, tunda take bata taɓa hada ido da shi ba, cabb to wane ita, ai idan ta haɗa ido dashi sede ta ganta a lahira
Shiru bokan yayi yana jiran abinda zata ce duk da ya ga hakan a cikin tunanin ta, shi dariya ma taurin kan Bil Adama suke basa, abinda ya hanata taje ta aikata saboda ta kasa jiran lokacin da yace ta jira
Duk da yasan mind din kowa a duniyar ko meye kake kitsawa a mind din ka ya sani saboda duk wadanda suke zuwa gurin sa yana karantar tunanin su a kallo ɗaya da yake musu.
Amma yapi san ka furta masa da kanka sbd hakan yapi bashi nishadi.

Ita kanta tasan Kuskure tayi shiyasa tazo ta bashi hakuri
Can dai tayi karfin halin cewar "Yakai wannan hatsabibin Boka, ina me neman gafara a gare ka, ka gafarta wa wannan baiwar taka, nasan na tafka kuskure amma bisa kaidin zuciya ta ne da ta kasa hakura, dan girman tsafinka kai mini gafara"
Dariya me kaman kukan zaki ya saki sannan yace "kije zakiga hukuncinki"
Ihu halittar ta saki tana kuka
Nan take ta ɓace ɓat

_____________

Tun da Asuba su Hafsa suka tashi, gabaki daya a tsorace take, amma se tayi kokarin ta danne hakan, Murja kuwa da ta fahimci hakan ta, ta tisa ta a gaba akan se ta gaya mata me take boye mata, abinda ta fada ya razana Murja dan har ta fita tsurewa, ko karban abincin safe basu tsaya yi ba suka wuce sashen Sarki, suka zauna, duk da kasancewa ko bude sashen ba'a yi ba, a tunanin su idan Yarima ya aika ba za'a same su a sashen su na bayi ba.
_____________

Da safe tayi kuwa, kamar karfe goma Yarima ya farka, se yaji kaman ba shine ba lapiya jiya ba, bama haka ba, ji yayi kamar be taba ma rashin lapiyan ba, gefen sa ya duba be ga Sulaiman ba se yayi tunanin ko yana cikin makewayi, bari ya jira sa ya fito shima ya shiga, ya kara kusan minti goma yaji shiru, nan ya mike ya tura kofar yaga ba kowa a ciki.

Tsaki yayi tuna ko sallama Sulaiman be masa ba yayi tafiyar sa, shigewa bandakin yayi, se lokacin tunanin abinda wannan baiwar tayi masa jiya da daddare ya fado masa, ransa a mugun bace ya wuce gun da aka hada masa ruwan wanka, a gaggauce ya fito, bafaden sa ya shirya sa, take yayi ma bafaden umarni akan yaje ya kira masa jakadiyar Sarki.

Tsakanin Sashen Mai Martaba da Yarima akwai tazara sosai, amma cikin kankanin lokaci Jakadiyar Sarki ta iso, a dakin shaqatawar ta jira, har ya fito a cikin takun sa me cike da ƙasaita, tana hango shi ta duka kasa tana me kwasan gaisuwa a gurin shi tare da yi masa kirari

"Gaisuwa nake dan zaki
Gaisuwa nake dan damisa
Gaba salamun baya salamun"

Daga mata hannu yayi, akan ya isa haka

"Ina so ki kirawo min baiwar da kika aiko jiya da daddare, yanzu yanzunnan".
Ai be kai ga gama maganar sa ba jakadiya ta fita ta saka wani bawa yaje ya kira mata su Hafsa da su Murja, ba'a jima ba se gasu nan, hantar cikin Hafsa duk ta kada, Murja kuwa kamar kace mata caaa ta saka gudu

Suna shigowa suka zube a kasa, suna masu kwasan gaisuwa, shikam Yarima Idriss kawai kallon Hafsa yake, yana jinjina taurin kai da rashin tsoron ta, amma bari ze koya mata hankali

Daga Hannu yayi se ga wani bakin basamuden bafade, dauke da dorina a hannun sa, nuni ya masa da su Hafsa, ai nan Murja ta kwanta flat a kasa tana roqon sa gafara, alama yayi ma dayan dogarin da ya matsar da Murjan, nan yayi abinda aka umarce sa, Hafsa kuwa bakin ta ya kara yaudaran ta, ta kasa bada hakuri, shi kuwa bafade abun nema ya samu

Ya hau jibgan ta, ba shi ya bari ba seda yaga ta suma, alama Yarima ya ma duk bayin gurin da suyi waje kowa ya fice hadda Murja da ta kusan shidewa saboda kukan ganin yadda aka gama dukan Hafsan

Se ya rage daga Jakadiya se amintaccen bawan Yariman, se kuma Hafsan da take kwance a kasa kamar wata gawa.

Budan bakin Yarima cewa yayi "wannan yarinyar ta dawo aiki nan daga yanzu"
"Godiya take ranka ya dade" fadin Jakadiya tana fita waje dan ta koma bakin aikin ta.

"Ka tabbata ta tashi ta fara aikin ta, sannan ka sallami duk masu yin aiki a nan".
Yana fadin haka yayi hanyar waje, shi kuma bafaden da sauri ya fada wa wani bawa sakon Yarima kapin yaje ya take masa baya

____________

Kilishi ce zaune akan gadon dakin ta, da ka ganta zaka san a firgice take, ita tsoron wannan hukuncin take, sannan kuma tana tsoron kar yaran ta su rasa wannan sarautar, amma zata je tayi yanka dan ta seta komi ya zamo daidai, sannan zata dauki fansa akan Waziri da Yarima, saboda kaf fadin masarautar nan sune masu shige mata hanci

Yanzu bari ta shirya taje ta gaida sarauniya babba, su tattauna akan gasar nan da za'a yi karshen makon nan

Da wannan tunanin ta mike tayi ma amintacciyar baiwar ta alama da ta shigo
____________

Saukan wani ruwa me uban sanyi taji a tsakar kanta
Ai a hargitse ta tashi zata sa gudu, nan ta hada ido da wannan basamuden, harara ya banka mata tare da fadin
"Kin dawo nan da aiki, daga yau har illa Masha Allah, kuskure kadan idan kika yi an bani umarnin in canza Miki kamanni"

Ita ba maganan da yake bane matsalan ta ma, ciwon da jikin ta yake shine matsalan ta, ta ya zata iya aiki fisabilillah tana jin jikin ta kamar ba nata ba, gaskiya da sakel, abun fa da kamar wuya, tukunna ma ina Murja?

"Ina Murja"? Tayi karfin halin tambayar sa
Kamar ba zai bata amsa ba, can dai yace "Wannan kuma ke ta shafa, kowa ya koma bakin aikin sa"

Mikewa tayi dakyar da kama bango, ta shiga kikkintsa gurin, can dai ta nemi guri ta zauna, yunwa yana ta nuqurqusar ta, kai inaa, da taga baza ta iya ba ta mike ta fara da shigewa can uwar dakan Yarima, ta fara dube dube ko Allah ze sa ta samu abinda zata sa a cikin ta, dan Allah ya gani baza ta iya aiki ba in bata ci wani abin ba, dan a yanda take jin jikin tan nan zata iya fadi ma.

Hakkin Mallaka nawa ne Ni Fatima Idriss Bello
Ban yadda a juyamin littafina ta ko wane irin tsiga ba, ko kuma ayı audio ba tare da izinina ba domin hakan ze iya janyo ma mutum matsala.
Dan haka a kiyaye.



>>>>>>>>>>>>>💻🖋️🤍







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss🖋️🖋️
09020588802
Wattpad; fadrees_20


Page 10


Not edited.

Daga kai Hafsa tayi tana karewa dakin kallo, daki ne me girman gaske dan yayi ukun dakin su na can gidan su ma a girma, tabe tabe ta fara yi a ciki ko Allah ze sa ta samu abinci, bata ga komai ba tayi shirin juyawa da sauri dan gaskiya tayo babban kasada da ta sako kafarta a cikin wannan dakin, amma se ta tuna aiki zata yi ai nan ta fara neman abinda zata sa a cikin ta, kan dardumar da suka shimfida musu jiya da daddare ita da Murja idon ta ya fada a kai, nan take jiki na kyarma ta karasa wurin.

An tattare gurin tsaf an kwashe kwanukan jiya se wasu ta gani sabbi a gun, nan ta fara bude ko wanne, idan ta ne ya hau kan dafaffiyar kaza, a take ta hadiye muguwar yawu, haka tana ji tana gani ta rupe, duk abinda ta bude se ta ga yafi karfin ta seta rupe shi, daga karshe har ta yanke shawarar tashi, ta ga baza ta iya ba nan ta bude kwanon soyayyar awara da kwai, ko takan miyar bata bi ba ta fara afka su izuwa bakin ta, hannu baka hannu kwarya, tasss ta cinye ta kora da wani ruwa me zaki
Tashi tayi tsaye nan taji ta dawo garau, kwanon ta dauke tayi waje dashi ta hango wani bafade ta tambaye sa ina ne madafar sashen Yarima ya nuna mata ta kai ta dauraye taje ta ajje a cikin kwanukan madafar sannan ta koma dakin ta fara gyara ko ina tsaf, taje ta wanke banɗaki ta shiga dakin hutawar shi ta gyara shi shima, nan ta samu wuri a gun ta kwanta se bacci.

_______________

Bayan su Yarima sunje sun miqa gaisuwa a fada, nan take suka wuce filin polon su suka fara training shi da su Sulaiman da su Shamsu, can dai zuwa azahar yaga yunwa tana neman halaka shi, gashi be ci abincin safe ba, ya dai sa an kai mishi, nan yace musu suje su huta zuwa yamma su sake dawowa, a take kuwa sukayi haramar tafiya, sashen mahaifiyar Yarima naga sun nufa, Seda aka musu iso kapın suka shiga suka duqa suna kwasan gaisuwa
Bayan sun gama su Hayatu suka mata sallama suka fice zasu gurin mahaifiyar su daman ance tana neman su

Fulani ce ta dubi Yarima cike da so da kauna tace

"Ya jikin abokin naka Sulaiman"?
"Da sauki ranki ya dade yanzu ma daga filin polo muke munje training"
Sulaiman din ya bata amsa
"Ku dai kun ki kuyi aure, Allah ya sa Me Martaba ya zaba muku mata in yaso wani shekarar ya zamto mun zamo kakanni"
Fulani ta karashe maganar ta tana kallon Yariman
Gogan kuma ya gimtse fuska, shi shiyasa sam be san zuwa gun Fulani dan da yazo zata kama mishi zancen aure
Shi tukunna ma be yadda da so ba, sannan shi dai gaskiya a iyaka rayuwar shi be taba soyayya ba, ba ma shi da wannan time din, anso ayi mishi hadi da ya'yan sarakuna amma yaqi bada hadin kai, kuma ya lura yawancin su kyan shi ne yake fusgar su, a ganin shi soyayya bata lokaci ne da kuma wani nauyi da ka dora ma kanka.

Yana cikin wannan tunanin suka ji sallamar Bilkisu,
Yaya Sulaiman sannu da zuwa, Yaya Barkan ka da warhaka.
Ya dai ji Sulaiman ya amsa mata har yana tsokanan ta, shikam yunwan da yake ji ma baze barsa yayi magana ba

Alama Fulani ta ma bayin ta da su kawo ma su Yarima abinci, ba bata lokaci se ka abinci a jere a gaban su, nan suka hau ci dan shi kan shi Sulaiman din yunwa yake ji, tunanin Yarima tunda yanzu yabar abinci a sashen sa, awaran kawai zeci, tunda shine favorite nasa in ya so se ya bawa bayin sa sauran kamar dai yadda ya saba.
Bilkisu kuwa se zuba take tayi, daga karshe ce mata yayi in baza tayi shiru ba zata iya tafiya, Fulani ko se dariya take

Shine pa suka samu salama, can dai Sulaiman yace mata
"Ina kawar ki ne?, nipa tun jiya ban sa ta a ido ba"
Zare ido tayi cikin mamaki tace "kai yaya Sulaiman kuna gida daya kace baka sata a ido ba tun jiya"? Nan ta saki baki se zuba take

Kawai se gani suka yi ta miqe ta fita bakin ta a zumbure, ashe da ido Yarima ya mata alama da ta fita.
Suna gamawa suka tafi masallaci daga nan suka wuce sashen Yariman

Da sallama a bakin shi ya shiga sashen, se kuma yaji shiru ba kamar yadda ya saba idan ya shigo masu aikin sa su fara gaishe shi ba, nan de ya karasa ciki Sulaiman na biye dashi, shima yana mamakin shirun da yaji
Suna shiga tsakiyar dakin shaqatawar suka hango Hajiya Hafsa a sheme tana kwasar bacci, tayi dai dai da kafafu daya yana kallon gabas daya yamma, kai babu dankwali gashi ya rupe mata fuskan kamar wata mahaukaciya, zani ya taho cinya, ba'a san a wacce duniya ake ba, tsabar baccin ya mata dadi har gyara kwanciya take, Me Sulaiman zeyi in ba dariya ba, shi kuma Yarima ya qule ya qule, wato ita ba aiki taxo yi ba, bacci taxo yi kenan, bari ya koya mata hankali.
Ƙafa ya sa, ya haure mata ƙafan, ita kuma a take ta tashi a matukar zafafe tana me kuntuma wani mugun ashar.
Idon da suka hada ne yasa taja bakin ta shiru tana hararar ƙasa.

________________

(Recap)
Hafsa ce kwance tana mafarkin gata a gida, Mama ta aike ta taje ta siyo musu kosai a gun mama lantana, ita kuma tace wlh baza suci na Mama lantana ba, bayan ta gama tofe yawun ta a cikin kullin wlh baze yiwu ba sede Jamila kije can rumfar iya me kosai ki siyo mana, da Mama taga haka se ta kwace kudin ta wai ta fasa siya musu kosan, ihu suka ji a waje sukayi waje da gudu, wai Sega su dije suna dambe ita da Azima, ita kuma Hafsa taje tana ta ziga su tana dariya, dambe kuwa ya kara rikicewa an kasa raba su, mama ne ta taho da mahuci ta kwalawa Hafsan daidai da taji saukan shuri akan kafar ta kenan, shine pa ta tashi tana zambaɗa ashar
Se kuma tayi gamo, bakin ta yayi laqwas tayi shiru tana hararar ƙasa
Shi kuma mutuwan tsaye yayi.

©FatimaIdrissBello.


>>>>>>>>>>>>>💻🖋️🤍







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss🖋️🖋️
09020588802
Wattpad; fadrees_20


Page 11


Not edited

Wai Allah
Anya wannan yarinyar ba mahaukaciya bace? Ko dai aljanu gare ta, kai wannan sede aljanun ma, idan ba haka ba ina ya taba ganin jaza'i irin wannan?
Farko kwance take ba dankwali gashi a barbaje kaman kan mahaukaciya, yanzu kuma ta tashi tana uban ashar kamar wata bamagujiya.

Sulaiman ne ma ya bashi mamaki da ya ga yana dariya a gaban baiwar sa, wannan ai se ta rena shi ma, se yanzu ma ya tuna ashe ya sallame sauran ma'aikatan sa shi yasa yaji shiru
Tsaki yayi, yayi wucewar sa cikin uwar dakan sa, zama yayi ya hau zagaye a cikin dakin da idon sa, can idan nasa ya fada akan dardumar tare da kwanukan da suke kai
Tuno awaran da yayi ne yasa yayi wurin yawun sa na tsinkewa, har yaje ze bude kwanukan da kansa yaga ba girman sa bane, gara kawai ya bari baiwar nan ta zo ta zuba masa, alamar shigowar Sulaiman ya jiyo, shi kuma ya juya ya masa alama da ya kira baiwar, juyawa Sulaiman yayi ya kirawo Hafsa, ta shigo tana ciccin magani
Alama ya mata da tazo ta zuba masa abinci

Karasowa tayi tana zumbura baki, ji yayi
Kamar ya mangare ta, amma se suka zuba mata ido kawai

"Wanne za'a zuba maka ranka ya dade"? Ta tambaya tana sake haɗe rai

"Ki zuba masa awaran" fadar Suleiman kenan yana karasowa gun Yarima tare da zama,
Da jin haka take hantar cikin Hafsa ta kada, wuri wuri idon ta ya fara, tunani ta fara yi a ranta, 'wai yaushe ta zama mara tsoro ne, sannan shidin wai bashi da baki ne da baze mata magana ba har se ya fada wa wani? kuma ko zata ji tsoron ta rasa a gaban wa zata ji se gaban wannan mummunan Yariman'? Ina hakan baze yiwu ba, kafsewa tayi ta fara bude kwanon daya bayan daya kamar ba ita ta cinye awaran ba.
Se da ta gama bude dukkan kwanukan sannan ta kalli yarima tace
"Babu Awara a ciki ranka ya dade"

Hakikanin gaskiya yayi mamaki, amma kuma se ya bar zancen ya miqe yaje ya ɗan kishingida, bacci ne yayi awon gaba dashi Sulaiman kuma yayi dakin shakatawar Yariman ya zauna yan dan duba wasu littattafai a hakan shima bacci ya dauke shi

Hajiya Hafsa kuwa ta koma sashen su na bayi, ta iske Murja suka je suka amso abincin su suka zauna suna hutawa, kapın yamma yayi su ci su fita yawo.

____________

Kilishi ce tsaye a gaban sashen sarauniya babba, wato mahaifiyar Mai Martaba Jira take a mata iso

Can ba da dadewa ba bayan ta gama shaqan shanya tan da akayi, aka mata iso
Sashen Sarauniya Babba ya matukar tafiya da imani na, kamar ba sashen tsohuwa ba, A kishingide take akan tumtum ta riqe takaddar addini tana dubawa gaban ta kuwa su kayan marmari ne da kuma kayan makukashe, shigowar ta cikin sashen ta durqusa ta kwashi gaisuwa, ranta na matukar suya, na durqusa wan da tayi

Hannu sarauniya babba ta daga cike da ƙasaita wanda hakan ya qona ran Kilishi, ita a tunanin ta yin ƙasaita da ita ta dace tunda ita ce matar sarki amma dubi yanda tsohuwar banzan nan take yi

Baiwar Sarauniya Babba ce ta shigo ta isar da sakon Fulani tana neman iso
Murmushi sarauniya babba tayi ta mata nuni da ta shigo da ita
Be jima ba se gata ta shigo, ta durqusa ta kwashi gaisuwa
Nan suka dan taba hira, sannan suka sake yin magana akan gasar da za'a yi wani satin.
Kilishi se hararan Fulani take yi, domin ta tsane ta, zama ma guri daya da ita ba'a san ranta take yi ba, har Allah Allah take su gama tattaunawar ta kama gaban ta dan ranta a mugun bace yake.
İta da tazo dan wani abu gashi matar nan ta bata mata shirin ta.

________________

Bilkisu ce ta shirya ta tafi gidan waziri gurin Samira, Da yi mata iso ta samu Mama Zulaiha ta kwashi gaisuwa sannan ta wuce dakin Samira ta same ta shame shame tana kwasar bacci
Daka mata duka tayi, ta tashi a firgice se zare idanu take, me Bilkisu zata yi in ba dariya ba. Can dai ta tashi suka sha hira, anan suke hiran gasar da za'a yi, Bilkisu na cewa Allah ya hada ta da kyakkyawan Yarima ta aura, ita dai Samira cewa tayi se sun gani. Sai da suka ci abinci kapın Samira ta raka Bilkisun.

________________

Tashin Yarima a bacci yayi daidai da lokacin sallar la'asar miqewa yayi, yayi alwala yayi Sallah ya miqe da nufin yayi wa wannan baiwar yarinyar da ko sunan ta be sani ba magana tazo ta ta zuba masa abinci, to shi meye damuwarsa da sanin sunan ta ma, dubawa yayi ko ina be ganta ba, shigowar sa dakin shakatawar sa ya hango Suleiman a sheme yana bacci, tada shi yayi yace masa yayi Sallah, sannan ya tambaye sa ina baiwar, shi sai yace ya barta a dakin, wucewar sa makewayi yayi, yabar Yarima Idriss da qunan zuciya, gaskiya yarinyar nan, ta wuce tunanin shi, wato be bata izinin tafiya ba shine zata tafi? Lalle ze koya mata hankali.
Bayan Suleiman yabi ya zauna a dakin yana kumbura fuska, shi ala dole an bata masa rai, bada jimawa ba Sulaiman ya fito a makewayin ya gabatar da Sallah sannan ya jawo hannun Yariman suka dawo kan dardumar ya fara serving dinsu
Sunci sun koshi sannan suka yi haramar fita training, a can suka hadu da su shamsu sune basu dawo ba se dare.

Nan suka dunguma zuwa sashen Mai Martaba zasu masa sallama
Bayan an musu iso suka tadda shi, shida Waziri, nan suka musu nasiha, sannan aka sake tunatar dasu akan gasan da za'a yi wani makon da yardan Allah.
Da suka fito sashen Sarauniya Babba suka je suka zauna suka dinga hira, se tsokanan Yarima suke amma yayi fuska, ita ko se cewa take su kyale mata miji ya huta.
Nan Sarauniya ta ringa basu labaran yanayin sarautar su lokacin da take budurwa.

Seda dare ya tsala tukunna ko wannan su ya nupi sashen shi da niyan yayi bacci. A yayin da wasu suke haramar bacci a lokacin wasu suke tashi. Bayyana wannan halittar ta sake yi a gaban Boka Kapoor, tayi masa sujjada, ta kora masa dukkanin bukatun ta, shi kuma ya bata tabbatuwan nasara.
Nan ta zama wata kalar halitta ta bace.

_________

Kilishi ce kwance akan gadon ta kamar mara rai, domin sam bata motsi ko kadan, can se ga wani abu a ta sama shiba aljani ba shi ba fatalwa ba. Tsira masa ido nayi da kyau domin gane ko menene, can dai abun yazo ya shige jikin kilishi, nan take ta sauke ajiyar zuciya ta miqe
Hakikanin gaskiya na tsorata, tashi tayi taje gaban wani madubi dake jingine a dakin nata tana kallon kanta, ta cikin madubin kuwa mutum ce kamar tsohuwa me matukar ban tsoro, dariyar mugunta ta saka sa'annan ta rikida ta dawo ainihin siffanta.
Wannan kenan.

________

Hajiya Hafsatu kuwa kwanan dadi tayi ranan, domin yawo ta dinga yi kusurwa kusurwa tana me neman tsokana, duk inda ta samu kuwa kaga fada ta kaure, da kanta seda ta gaji sannan suka koma daki, Murja kuwa se dariya take tayi, tana mamakin taurin ran Hafsa da kuma rashin tsoro
Da dare yayi suka koma gun karban abinci suka karbo suka ci abun su. Hafsa tsabar taurin kai ƙin komawa sashen Yarima tayi, tana ganin Murja taje sashen sarki ta dawo.
Da dare tsabar gajiya ko fitina bata tsaya nema ba bacci yayi awon gaba da ita, da asuba ma kin tashi tayi wanka tayi, Seda wajen karfe tara ta tashi tayi wanka taci abinci kapın tayi haramar tafiya sashen makiyin nata.

Taku ce Fadrees.



>>>>>>>>>>>>>💻🖋️🤍







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss🖋️🖋️
09020588802
Wattpad; fadrees_20


Page 12



Gobe ya kama Asabar ranan da za'a yi gasar da ake ta tsumayin zuwan ta, tun ranar laraba sarakuna suka fara zuwa,
Jiya juma'a kuwa ko wane sarki da ake expecting zeyi participating shida mutanen sa sunzo. Manya manyan ɓangarori aka ware ma sarakunan suka sauka da tawagar su.

Hafsa na hango tana bin Yarima kamar jela, duk inda ya saka ƙafarsa itama nan take saka nata, ko wane aiki ita yake saka wa, ba ƙaramin azaba Yarima yake baiwa Hafsa ba, amma in ta tashi abun ta, yi masa take yi bata jin ko ɗar, to tasan karshen ta yace ze sa a zane ta ne, ko a hana ta abinci. to amma dukan har an gaji an kyale ta, yanzu idan tayi abu a cikin sati biyun nan da suka gabatar tare sede ya sa mata ido, gashi shi ba mutum bane me san magana.
Ranan da ta kular dashi shaqe ta yayi har seda yayi danasani dan har suma tayi amma da ta samu kanta, abun nata gaba ma yayi.
Ranan da taqi zuwa aikin nan da taje kusan kashe ta wani dogarin sa yayi da duka amma ina Hafsa ce pa. Sede kuma tana aikatuwa iyakar aikatuwa.
Hutu da take dashi se in bacci ne ya dauke shi amma ko tsinke ze dauka ko da kuwa yana kan cinyar shi ne, se ya kira Hafsa ta miqa masa. İyakacin ta guna guni ne, idan ta harzuqa sa kuma ya sa a zane ta.
Tasha kwana a sashen shi saboda yawan aiki dayake saka ta, wani abun ma is unnecessary amma se ya sata tayi shi. Murja kam har tausayin Hafsah take yi amma ita kuma sam kamar abun be dame ta ba.

Yanzu ma fitowar su kenan daga sashen mahaifinsa suka yi kiciɓus da wani ɗan Sarkin Gobir da ya nace wa Hafsa, idan ya hango ta yayi ta kallon ta kenan, ranan da ya ganta ita daya ya tsayar da ita yana ta jan ta da labari tana murmushi sega Yarima kamar an jeho shi, shida Suleiman, hakikanin gaskiya ransa yayi matukar ɓaci daya ga Hafsa tana murmushi, shipa ya tsani yaga tana cikin jin dadi, daga kai yayi yaga ɗan Sarkin Gobir din yana mata wani irin kallo, se yaji ransa ya ɓaci, ta ya za'a yi baiwar sa me yi masa aiki zata tsaya tana kula wani sakarai? Gaskiya hakan kamar zubewar aji ne a gareshi.
Ranshi a mugun bace yake kallon su su dukan su, shi kuma ɗan Sarkin wanda yake da suna Isma'il, se zuba surutu yake can da ya daga kai yaga Yarima da Sulaiman din, a take ya mika musu hannu suyi musabaha, Yarima yaqi bashi hannu, shiko Sulaiman ya basa nasa, a Lokacin Hafsa ta dago idon ta suka hada ido da Yarima, jikin ta har kyarma yake tsabar rudanin ganin irin kallon da Yarima yake aika mata.
Budan bakin Isma'il keda wuya yace "Gaskiya Yarima in zan

Please Login or Register in order to submit comment