Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Ko ahaka aka ce muku za kuyi bautar?, ai tunda Yarima ya kawo ku, kuda hutu sai naga dama'
Jakadiyar Sarki ce ke fadin haka
'Kuma wannan kaya me launin shudin da aka baku zakuna aiki ne a sashin Sarki
Da shike ku sabin zuwa ne ba sai kunyi sammako kun fita da sassafe ba amman ku fita da wuri'
'In kun ga dama ku wuce kuje madafar ku na bayi kuje ku karɓa abinci'
Ta karashe zancen nata tana yin ƙwafa kafin ta kade bujen ta tayi waje
'Sannu kunji?'
faɗar Shafa'atu kenan da tsigar tausayi
Nan suka taimaka musu suka mike suna jan jiki a haka suka je da ƙyar suka bi layin karban abincin nan ma kapın suka iyo hanyar ɗakin nasu

_________________

Yau ake saka ran dawowar Malam Sule me rini duba da sakon da ya aiko kwanaki cewar yau Litinin zai yi haramar dawowa
A gidan Malam Sule me rini an yi shara ba laifi kuma an yi masa girki.

Kamar yanda ko wanne magidanci yake tsammanin ya dawo ya samu gidansa cikin kwanciyar hankali da mutunci, to ba hakan ce ta kasance da Malam Sule me rini ba, sakamakon wani mummunan labari da yaji da saka kafar sa a cikin gidan nasa
"Toh yanzu Malam ya zai ji idan yaji halin da Hafsa take ciki kuma kunsan halin yan sarautar nan sarai ba......"
Ai Kulu bata ida zancen ta ba ta hango  Malam Sule me rini yayi mutuwar tsaye, Lawan ne ya taimaka masa ya ida jawo sa cikin gidan

" Me nake ji haka Kulu? Me kika ce?"
Malam Sule me rini ya tambaya
Nan Kulu ta ɓarke da kuka
Lawan ne yaja shi kan tabarmar kabar da aka shimfida masa ya taimaka masa ya zauna kapın ya dora da fada masa duk abinda ya afku
Malam Sule me rini yayi bakin ciki matuka na jin abinda ya faru
Abinci ma ba'a cikin hankalin sa ya ci ba kawai ya kashe yunwa ne. Nan take yayi ma gidan yayan sa, Baffa Musa tsinke.

Da shike Baffa Musa yasan komai nan suka sake tattauna wa akan za suje su Fadan gobe da sassafe talata kenan
Nan sukayi sallama Malam Sule me rini ya bada tsarabar da ya kawo wa yaran Baffa Musan

Komawarsa gida ya same su sunyi cirko cirko
"Me ya faru haka naga kunyi wani cirko cirko"?
Mallam Sule me rini ne yayi maganar nan
Lawan ne yayi magana
"Mama Zenabu ne ta suma"
"Kayi sauri ka kira Isah me magani yanxu"
Malam Sule me rini ne yayi maganar
Aiko nan take Lawan yayi maza ya fice daga gidan
Lawan be jima da fita ba ya dawo da Isah me magani
Bayan sun gaisa da Malam Sule me rini ya fara duba Mama Zenabu
An samu ta farfaɗo kuma jikin ta ya ɗan yi sauki

_____________

Da safe da misalin karfe tara Malam Sule me rini sukayi haramar zuwa fada tare da Baffa Musa da mai Unguwar su Malam Sule me rinin

Ba sune suka isa ba se wajajen goma
Da kyar da siɗin goshi suka samu suka haɗu da Sarkin fada
Suka sanar masa komai tare da fada masa in babu damuwa yayi musu iso gurin me martaba

Sai da Sarkin fadan yaga Lokacin shigewar me martaba cikin gida yayi bi ma'ana azahar, tukunna yayi musu ison shiga cikin fadan
Shigar su suka mika gaisuwa gurin Sarki
"Sarki ya amsa"
Suka ji wani bafade yace
Tukunna suka gaida manyan fada
"Me ke tafe da ku?"
Wannan bafaden da yayi magana da farko ne ya sake tambayar su
Sarkin fada yana gab da fara magana suka ji An kwada sallama ana neman izinin shigowa
Dogarin na shigowa ya zube a ƙasa yana kwasar gaisuwa

"Ƙiran gaggawa ya taso daga gurin Sarauniya babba (mahaifiyar Sarkin) tana neman Me martaba da Waziri yanzun nan"
Yana gama fada yayi ficewar sa
Ha ila yau wannan bafaden farkon nan ne yayi magana kamar haka
"Sarki ya bar ragamar aikin sa ma wa Galadima!?
A take fadawa suka tashi suka takewa Sarki da Waziri baya aka bar Galadima dasu Malam Sule mai rini
Nan kowa hankalin sa ya dawo kan Galadima
"Meke tafe daku?" Yayi tambayar yana kallon me anguwa
Nan take Me Unguwa ya sanar dashi
Budar bakin Galadima cewa yayi
"Wannan ba hurumi na bane kasancewar Yarima ne da kansa, amma zanyi magana da mai martaba nan da wata uku ka dawo dan a yanda ka bada labarin lallai yarinyar ka ita ce da laifi haka kawai Yarima da ba shiga harkan mutane yake ba bazai taso keyar ta zuwa horar da ita ba, kuma dalilin da yasa nace ka dawo nan da wata uku shine kapın nan ta horu, nikuma insha Allah kamar yanda muka yi magana dakai za'a fitar maka da ita"
"Godiya muke ranka ya dade" dukan su suka fada suna dukawa
Kawai Galadima daga musu hannu yayi

Tun sanda Galadima ya fara magana Malam Sule me rini yayi tagumi yana sauraron sa tare da share ƴar kwallar sa, daman yasan ayi haka yasan Hafsa batajin magana, amma Allah yasa hakan yayi sanadiyar shiryuwar ta

Nan suka sake godiya suka mike suka bar Galadima yana cigaba da solving ɗin matsalar mutane kamar yanda Sarki ya Umurce shi da yayi

___________________

Bayan sun karbo abincin su wato tuwo dan wannan dankararren taliyar baza a ce mishi abinci ba sai dai tuwon kam, suka zauna suna ci suna gabza uban kuka Shafa'atu ce take ta basu baki dan Lantana ko çıkan ku bata ce ba, ita a ganin ta ai iskanci ne ma, in ba hakan ba ta yaya kana bauta a gidan sarauta kace ba zaka jure duka ba? (Niko nace ai su sababbin zuwa ne)

Suna gamawa suka kama tattare dakin Sannan suka bi lafiyar gado domin mangariba da isha'i ma Shafa'atu ce ta tada su suka yi suna idarwa suke komawa suci gaba da bacci

Washe gari da safe bayan sunyi sallar asuba basu koma bacci ba gudun kar suyi wani laipin yasa suka bi layin wanka
A gurin layin wanka sai da Hafsa tajawo fada, dogarai kuma basu fasa dukan ta bah!
( Kujimin ja'irar yarinya gwara da Galadiman ma yace wata uku dan ko fara shiryuwar bata fara yi ba)


Ban yadda wani yayi amfani da wani sashe na littafin nan nawa ba, ba tare da amincewa na ba, domin zan dauki tsattsauran mataki akan hakan, dan haka a kiyaye.

Idan littafin nan kake nema, complete ko wani sashe toh ga nan numbern waya na a sama duk me san yayi min magana, ya min ta nan.

Da fatan an fahimta.
Nagode.



>>>>>>>>>>>>>💻🖋️🤍







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss🖋️🖋️
09020588802
Wattpad; fadrees_20


Page 7


Ta sha bugu kam saboda shegen bakin ta, amma pa bakin be mutu bah!.
Ehe!.

A Gaggauce suka gama shirin su ita da Murja suka yi hanyar madafa aka zuba musu funkasau ɗin da aka dafa sai suka koma ɗakin su suka ajiye da zummar idan sun dawo zasu ci gudun kar suyi latti. Suna ajiye wa sukayi bangaren Sarki. Sun ɗan yi tafiya kam ba laifi ahakan ma da tambaye tambaye kapin su isa.

Suna tafiya Murja take tambayan ta me tayi aka kawo ta tayi bauta, Hafsa ta gaya mata komai tana karashewa da uban zagin ɗebe albarka da ta dinga yiwa Yarima.
Murja ma ta fada mata sharrin kishiyar uwa ne yasa aka kawo ta dan anga uwar ta bata gidan, sun tausaya wa juna hakika.

Nan kuwa bada jimawa ba suka iso.
Sashen Me martaba yapi kowane sashe kyau a kap cikin Masarautar tınba idan ka shiga cikin ba, tun daga farkon sashen suke kalle kalle har suka karasa ciki.

Suna zuwa suka tarad da jakadiya tana hakimce akan wata kujera se kace itace Sarkin sai saka bayi aiki take yi, idan kayi ɗan slight mistake kadan sai ta daka maka tsawa, abu kuma gashi nan a gefen ta amma sai ta kira wata daga çan uwa duniya ta miko mata. Da yake kowa da portion ɗin sa sai aikin ya zamto baya bawa Kowa wuya, Kuma ma Me martaba be yadda ana azabtar da bayi ba
Shiyasa ma wani lokacin da azahar zaka ga bayi sun gama Ayyukan su sai na maraice kuma su sake dawowa.
Sai kuma da daddare bayan isha su kan tafi makaranta inda ake koya musu karatun Allo, Ajami da dai sauransu amma ba ko wace rana ba.

"Kuzo nan, yaya sunan ku?
Jakadiya ta tambaye su kamar ba ita bace aka dake su a gaban ta ba jiya, ko ta sa baki, Gata dai dattijuwa amma sai shegen kwainane
Hafsa ce ta fara fadan sunan ta sannan Murja
"Daman yanzu nake cewa su Laure suzo sudauki abin nan sukai sashen Fulani amma tunda ga ku nan, kuma ba'a baku aikin ku ba sai ku dauka ku kai, kar ku jima pah?"!.
"Tohm ranki ya dade" suka fada a tare suna ɗan russuna mata cike da tsantar biyayya
Aiko Jakadiya ta saki murmushi domin tana son ana girmama ta, har cewa take ''zamu shirya da yaran nan'' a zuciyarta
Ɗauka sukayi suka wuce, buhu ne amma basu san meye a ciki ba

Sashen Sarauniya Fulani nada matukar kyau shima kuma a kusan na me martaban yake shiyasa basu sha wahalan dakon buhun ba.

"Kai ina zaku je?" Bafaden da yake gadin gate ɗin shiga sashen Fulanin ya tambaya da wata razananniyar kara
Ta tsorata sosai pah amma being the Hafsat she is, sai tace masa "ina ruwanka da inda zamu kai idon ka baya ganin aiko mu aka yi ne?
Ashe ran maza ya ɓaci aiko ya sungumi lafceciyar bulalar sa da nufin ya dake ta sai aka rike hannun sa
Dukkannin mu muka juya dan ganin waye da wannan ɗanyen aikin
"Ranka ya dade?"😲
Bafaden ya fada a tsorace

Murja da sauran fadawan da suka ga waye ne sai suma suka tsugunna alamun girmamawa.
Hafsah kuma tana ganin sa ranta ya ɓaci, duk da tsinkewar da zuciyar ta yayi sai gabobin jikin ta suka yaudare ta suka ƙi tsugunnawa su girmama sa, baza ta taɓa manta mutumin da ya sa ta a cikin wannan kangin bautar ba, kawai sai ta saka idon ta cikin nashi bata ko ƙiftawa, wannan shi ya hargitsa Yarima, dan gani ɗaya yayi mata yaji ya tsaneta,

Nan take ya wafce bulalan hannun bafaden ya shiga tafkar ta kaman ya samu jaki.
Sai da hannun sa ya gaji kafin ya kyale ta, amma abinda ya ƙara ɓata masa rai shine duk dukan ta da yake yi ba tayi hawaye ba kuma har yanzu idonta a cikin nashi yake

"Karbi tsumagiyar nan Barau kayi ta tafkar ta har sai ta dena numfashi."
Ya fada a fusace, tare da barin wurin gaba ɗaya
Aiko nan take Barau ya karbi tsumagiyar ya shiga tafkar ta daman yaji haushin rashin ɗa'ar da ta masa nan yaci gaba daga inda Yariman ya tsaya.

____________________

Da Malam Sule me rini ya koma gida sai ya zayyane musu abinda ya faru suka yi ta Sallallami

Su Kulu baki ya mutu dan ɗan kananu - kananun maganganun sun nan shiru kake ji, kamar gidan makoki.
A haka aka zo akayi bikin Lawan da su Garzali
Su Garzali matan su daman acan Gomben suka samo su
Sai Lawan ne da yanzu yake sana'ar rini ne ya auri Salamatu (wata kawar su Hafsa da su Azima)
Su Hafsa kuma Malam Sule me rini yace su ukun su ze hada auren su idan Hafsa ta dawo, kapinnan yace su ƙara shiga hankalin su su fidda miji nan da dawowar Hafsan.

Bayan wasu kwanaki kowa ya ware ya fara harkan gabansa
Malam Sule me rini kuma ya koma bakin aikin sa ya bar Lawan da Kula da gida
Wannan kenan.

____________________

Saura mako biyu da rabi ayi gasar ta Horse race da ma wasu wasanni kala kala da ya shafi sarauta hakan yasa aka fara shirye shiryen tun da wuri, wanda ya kama yau kwanan Hafsa talatin cif cif da zuwan ta cikin masarautar
Kwana goma sha shida da zuwan mahaifinta da kawun ta, kwana goma sha hudu da tasha bugu a gurin Yarima da Barau
Sauran mata kwana sittin kenan kan Galadima yasa baki a sallame ta
Ta sha wahala sosai pah domin ciccibar ta aka yi aka kaita dakin magani bayan dukan da aka mata
Jinyan kwana biyu kacal tayi, suka koma bakin aikin su inda Murja tana goge gogen dakin hutawar me martaba, Hafsa kuma gyaran ɗakin sa, sai dai dakin me martaba ana sa ido sosai shiyasa duk sanda za'a gyara shi akan idon jakadiya ne.

Yau ya kasance daya daga cikin ranakun da bayi ke fita koyon karatu, Bayan kowa ya gama aikinsa na safe da marece, kowa yayi Sallan Maghrib da Isha sai aka hallara zuwa makarantar bayin, wanda yake da kwakkwaran uzuri kamar rashin lafiya zai iya zama a sashen bayin sai wanda suka je su bada shaidar rashin lafiyar tasa
Makaranta ce babba sosai me dauke da azuzuwa dayawa a ciki wanda yake kunshe da bayi maza da mata, ajin yara ƙanana maza da mata ne a haɗe, na manya kuma maza daban mata daban, tsofaffi da dattijai ma da nasu, mazansu da kuma matansu

A cikin masarautar daman makarantu biyu ne, na Bayi da na ya'yan attajiri i.e The royals

Hafsa ne da Murja na gano sun fito daga cikin sashen bayi a makare, sai hanzari suke yi su isa, kafar Murja kamar zata cire tsabar sauri sai chilla su take kamar zasu tsinke
Suna isa makarantar sukayi sanɗa sanɗa za su shige aji sai ji sukayi shugabar bayi ta fisgo su
Zare ido sukayi suna
''Mama dan Allah ki taimake mu kiyi mana rai''

''Naji, amma kuyi sauri kubi wannan bafaden'' sai ta nuna musu Barau da yake ta wani ciccikowa.
"Ku hanzar ta jakadiyar Sarki ke jiran ku"
Maganar shugabar bayi kenan

Nan suka shiga bin bayan Barau, ''dube shi basamuden banza'' Hafsa ke maganar a ranta, tare da yatsina fuska, Murja ta daga mata gira alamar tambaya, sai tace babu

Shiko gogan sai uban sauri yake, wanda idan ya jefa ƙafarsa daya shine su sun jefa uku tsabar saurin sa, nan da nan suka isa kuwa.

A bakin sashen Fulani suka same ta a tsaye tace su biyo bayanta
suna shirin gaidata amma ko takansu bata bi ba, sai abin ya basu mamaki
Har suka isa ba wanda yama wani magana sai zare idan da su keyi

Suna shiga sashen Fulani suka ga hankalin ta a matukar tashe, gefen ta Kilishi ce tana murmushin mugunta.
Yaune rana na farko da suka taba kallon matan Sarki, gaskiya matan sa kyawawa ne musamman ma wanda suka ga hankalin ta a tashe yake sosai, fara ce sosai kuma kyakkyawa dan har tafi dayar kyau ma, nan Hafsa ta fara ƙare mata kallo, Wait!
"😳😳Wlh matan nan da wannan hamshaqin mugun nan take kama. Tabbas itace mahaifiyarsa". Bata gama maganar zucin ta ba taji ance;

"Ku kwashi kayan nan kukai sashen Yarima babba"
Muryar Jakadiyar sashen kenan da ya karade dakin

Nan suka tsugunna a tsanake suka kwashi manyan kwanukan dake a cikin wasu kwando guda biyu,
"Har kwandon za ku hada".
Jakadiya's voice echoed again

Kilishi ce tayi wani mummunan murmushi tana sake sake a ranta
Ita pah dole ne a cikin yayanta tagwayen nan daya yayi sarauta bata damu koma waye bane amma dole de a cikin su daya ne ze zama, shiyasa ma ta fara gudanar da aikin ta yau domin Boka Kafoor ya tabbatar mata da jinin ta ne dole ze mulki wannan masarautar, amman bata yi zaton har aikin nan ze fara tasiri akan sa ba yau din da wurwuri haka, tafi san sai anyi gasar nan da za ayi nan kusa, kimarsu ya dada karuwa tukun, Tabbas a cikin yaranta maza Hayatu yapi Shamsu nutsuwa amma ba hakan ne yake nupin idan samun mulkin yana kan Shamsu ne ta hana shi ba
Ehh ita koma waye ne a cikin su ya samu muddin zata kunyatar da Waziri da ita kanta Fulanin, toh bata da damuwa
Nace tohh pah🙄😆

Alhamdulillah
Let's meet in the next chapter
Fadrees Bello❤️.
09020588802 chat me on Whatsapp




>>>>>>>>>>>>>💻🖋️🤍







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss🖋️🖋️
09020588802
Wattpad; fadrees_20


Page 8


Nan suka kwasa suka yi hanyar sashen, se da suka yi dan tafiya kapin su isa
Duk da a hakan ba wani nisa bane tsakanin sashen Fulanin dana Yariman.

Kwandon abincin kam akwai nauyi amma sanin ba yadda suka iya ya saka su kinkima suka kutsa cikin sashen yariman suka ajiye a harabar katoton dakin shaqatawarshi
Har za su juya Jakadiyar Sarki da basu san da zamanta ba ta tsayar da su
'Ku dauka kukai can cikin uwar dakan'
"Tohm ranki ya dade" suka hada baki gurin amsa mata suna dan rusunawa, nan jakadiyar Sarki ta zabga murmushi, aranta tana cewa "Kai gaskiya yaran nan akwai ladabi wlh"
Ita fa a Rayuwar ta tana so taga ana girmamata, Yes, ita ba yar sarauta bace face Jakadiyar Sarki shugabar Jakadiyoyin dukka jakadai mata na masarautar, itama idan hakane ai ta cancanci girmamawa. Haka ne ma Yakamata kam. Nan ta saki shu'umin murmushi mai ma'ana.

Su kuwa basu ma san tana yi ba sukayi shigewarsu ciki inda tun kafin su karasa suke jin hayaniyan muryan maza.
Knocking Murja tayi aka basu izinin shigowa suka shiga da sallama kansu a kasa

Shamsu ne ya tsaya kallan ikon Allah bama shi kadai ba dukkansu har shi uban gayyar, dan su duk a tunanin su Jakadiya ce zata shigo se suka ga akasin haka
Amma de basu ce komi ba.

Sauke Kwandon suka yi suna shirin fita Suleiman yace "kuyi serving dukkanin mu".
Tare suka rusuna suna fadin
"Angama ranka ya dade"

A take suka zuba musu abincin kowa kwanon sa daban daban sannan suka dora akan wani katon darduman cin abincin da suka dakko sa ita da Murja daga dakin shaqatawa suka kawo cikin dakin
Daganan suka shiga zuba ma kowa shayi
Idon Sulaiman da Hayatu ne ya fada akan Hafsa ko kyaftawa basa yi
Shi Suleiman yana yaba kyawun ta a ransa shi kuma Hayatu ban ma san me zance akan shi ba saboda kamar kallon kauna yake mata
"Ku muje mana"? Shamsu ne ya ankarar dasu Hayatu daga dogon tunanin da suka fada
Akan cewar su karasa kan darduman abincin

Hafsa kuwa nan take ran ta yayi fari, ganin sun sakko daga kan tumtum din da suke kai shi kuma Sulaiman ya taimaka ma Yarima saboda yanayin jikin sa.
Tuna abinda zata aikata ma Yarima yanzu ta huce haushin sa da take ji koda kadan ne ya saka ta sakin murmushin mugunta

Tana ganin Murja ta nupi dayan bangaren ta mika wa Yarima Shamsu da Hayatu kopin shayi, ta dauki kopi biyu itama na Yariman da Suleiman, a cikin kopi daya ta zambada yaji me uban yawa da gishiri da sugar
Ta mika wa Sulaiman kopi dayan mara borkonon a ciki shi ko se kallan ta yake shikuma Yarima ta mika masa nasa me borkonon hannunta har kyarma yake yi tsabar tasan abinda tayi ba daidai bane, amma se bata nuna ba hasalima kalar abin tausayi tayi
Nan Yarima Shamsu yace dasu "Zaku iya tafiya"
Nan kuwa suka yi waje Hafsa har tuntube take
Ai kuwa suka raka su da idanuwa musamman Sulaiman.

Sede kuma wani abun al'ajabin da ya faru bayan fitar su shine da Yarima ya kai kopin shayi bakinsa yaji wani zafi me matukar azaba ga manda me uban yawa ya ziyarce harshen sa a take besan sanda ya furzar dashi ba idanun sa ya firfito besan sanda yayi jifa da kofin ba
Shi tunda yake anya ya taba jin azaba irin wannan?
Shi daman haka yake shan shayi duk zafin sa kurba daya yake masa yasha rabi
Amma wannan shayin da ya sha ji yake kamar garwashin wuta aka daura masa akan harshen sa ta wani ɓangaren kuma kamar ruwan teku ya sha
Nan take suka mike dukkan su shi kuma a firgice ya fara nuna kyauren dakin yana sumbatu se fadi yake
"I sauri Shamsu ka kiramin bayin da suka fita yanzun nan".
Da haramar sa kuwa Yarima Shamsu yayi waje cikin dakin shaqatawar Yariman amma babu su babu alamun su, babu kuma Jakadiyar Sarki.
Nan yayi can waje harabar sashen still babu su babu alamun su sema Bilkisu da ya hango ita da Samira suna nufowa sashen Yariman.

Shi ko sai ya koma ya sanar dashi akan be gansu ba su kuma su Suleiman har lokacin tambayar sa suke akan meya faru.
Kapin yace komi suka ji Sallamar su Gimbiya Bilkisu da Samira
Suna shigowa Bilkisu ta fada kan sa tana fadin
"Madallah Yayana nayi matukar farin ciki da ganin ka haka, naje gidan su Samira ina haramar dawowa ake sanar dani rashin lafiyar ka shine hankalinmu ya tashi nida Samira muka taho pa" ta karashe tana kallon Samirar da ta shagala da kallon sa bata ma san wainar da ake toyawa ba.

Shi ko cewa yayi "dan Allah Ni ki sake ni Bilkisu ke bakya taba girma ne? Ko so kike ki karasa ni ne"?
Shamsu ne ya keçe da dariyar mugunta yana kallon Bilkisun tare da fadin
"Ai wallahi maganin ki, kina gani na kika shareni ki kayi gurinsa gashi nan ai, mutumin da ba'a masa gwanin ta"? Ya karashe yana mata dariya Ita kuwa ta tsaya tana hura hanci se kallon Hayatu take da Sulaiman amma basu ce mata komai ba, nan ta maida hankalinta kan Samira tare da bubbuga ta
Se a sannan Samira ta dawo hankalin ta, ta gaida su suka amsa baya ma Sulaiman da yake mata kallon mamaki na kallon Yariman da yaga tana yi, sam Samira baza ta taɓa canzawa ba

"Ya Yarima kai ka jefar da wannan kopin haka? Fadamin a garin yaya? Ko de Ya Shamsu ne ya ture maka ya fadi? Bilkisu ta sake tambayar Yarima Idriss
Se a sannan abinda ya wakana ya sake dawo masa, aransa yana tunanin gobe gobe in Allah ya yadda ze sa Jakadiyar Sarki ta nemo masa yarinyar ya hukunta ta, ze mata hukuncin da ko sunan sa aka kira nan gaba se ta suma, da wannan tunanin ya dubi Bilkisu yace mata
"Kinga ƙanwa ta nazo tashi tsaye kawai na ture a bisa kuskure ba Yarima Shamsu bane" ya fada yana kallon Shamsun da se harara yake ta aika mata ita kuwa tana mishi gwaliyo.
Bayan sun gama cin abincin yace su bashi wuri ya huta, badan komi ya fadi hakan ba se dan surutun da Bilkisu da shamsu suke yi ne, gabaki daya sun sa masa ciwon kai
Ya Ilahi
Bayan fitar su ne Sulaiman yake cemasa akan yau anan ze kwana gudun kar jikin sa ya kara tashi

Su Hafsa kuwa seda suka yi tafiya me nisa da zummar su wuce makarantar bayin se kuma suka canza shawarar wucewa dakin su kawai tunda lokaci yaja, kila ma suna zuwa su tarar an tashi.
Hafsa kuwa zuciyarta ba abinda take banda bugawa can kuma ta saki murmushin mugunta, Murja ce ta tambaye ta dalilin yin murmushin nata, can dai tayi niyyar fada mata se kuma ta fasa saboda tasan idan har Murja ta sani toh shikenan watan yin baccin ta ya kare a ranar.
Can sun kusa isa Bangaren bayin Murja take ce mata
"Ke baki ga yanda Megida Sulaiman yake kallon ki bane"? Nace kode kode??😆
"Uwar 'kode' ɗin" fadin Hafsa kenan tana sakin tsaki. Niko na zaare ido na
Murja kuwa me zata yi in ba dariya ba.
Suna isa suka cinye sauran tuwon da suka rage kowa yabi lapiyar gado
A gurin Hafsa kuwa ba haka bane dan bacci cewa yayi be san ta ba se tunanin wanne kalan hukuncin Yarima ze mata take, can taji Sallamar su Lantana, sun shigo suna ta mita akan wani bafade wai yana san Shafa'atu, abun de abun dariya amma haka Hafsa ta gimtse kanta
Bata san sanda barawon yazo ya sace ta ba.

_______________

BOKA KAFOOR ne zaune a cikin katoton kogon sa wanda tsabar duhu zaka dauka kamar a cikin kabari mutum yake, gaban sa wani katon abu ne kaman drum, sede wannan ba drum bane dan abin kamar kwalba haka yake, cikin abun kuwa wasu unimaginary abu ne a ciki kamar Mami Water se shawagi suke a cikin kwalbar

Tadi suke yi cikin nishadi shida aljanun sa masu yi masa aiki suna basa labarin wata baiwar Allah da ta gagare su amma sun yi maganin ta

Se gani yayi kasa yana girgiza bisa ga dukkan alamu wani ne daga cikin mabiyansa yake neman iso a gurin sa, nan wata halitta ta ɓaco cikin kogon cikin baƙaƙen kaya
Halittar dai gata nan kamar bil adama kamar kuma aljanun amma dai mace ce tabbas.
Shin wacece wannan halittar?🤔

Ban yadda wani yayi amfani da wani sashe na littafin nan nawa ba, ba tare da amincewa na ba, domin zan dauki tsattsauran mataki akan hakan, dan haka a kiyaye.

Idan littafin nan kake nema, complete ko wani sashe toh ga nan numbern waya na a sama duk

Please Login or Register in order to submit comment